Umma ta zubowa Husna dumamen shinkafa da wake da kunun tsamiyar da suka karya dashi ta kawo mata.
Jikin Husna har rawa yake ta karba ta fara cin abincin da sauri sauri.
Umma ta ci gaba da wankinta zuciyarta cike fal da tunanin rayuwa.
Tas Husna ta cinye abincin ta shanye Kunun sannan tace “Umma nagama nagode.”
“to kin koshi ko a ƙara miki? saida Husna tayi murmushin jin daɗi sannan tace “na koshi, Umma nagode.”
Wannan kuma tarbiyar Mama ce duk abinda kayi mata sai tace maka ta gode walau babba ne ko yaro, dan haka Husna da Yayan ta Baffa suka taso da tarbiyar komai kayi musu sai sunce maka sun gode duk kankantar sa kuwa.
Saida Umma tayi murmushi sannan tace “ to ungo wannan zanin kidaura saiki cire kayan jikin ki na wanke miki duk sunyi datti.”
Husna ta karɓi zanin ta daura ta cirewa Umma kayan jikin ta. Tuni ta ware ta hau yiwa Umma hirar Mama da Yaya, har Umma ta gama wankin ta zuba ruwa ta wanke mata kanta fes sannan tayi mata wanka tace “tom ki zauna idan kayan naki ya bushe saiki saka ko?”
Husna ta washe mata baki tace “to Umma nagode.”
Anan ta shantake har Umma ta gama girkin rana, suna zaune suna hira, su Bishira suka dawo daga makaranta, Bishira na ganin ta tace “lah Husna Uncle Abba yana ta tambayar ki.”
Husna najin haka ta bata fuska cikin rashin jin daɗin rashin zuwanta makarantar tace “ai dan Mamana da yaya basa nan ne shi yasa ban jeba. Amma Umma tace na rinƙa zuwa muna tafiya daku tunda Baba yanzu ya daina rakani.”
Umma tayi sauri ta katse zancen iyaka nan ganin har ta fara kuka.
“yi shiru Husna kinji, kuma na faɗa miki Babanki bai daina raka kiba, aiki ne yayi masa yawa.”
Sai kuma ta juya wajan su Bishira tace “ku kuma maza kuje ku cire uniform azo aci abinci.”
…….tare dasu Bishra Umma ta zuba musu abinci bayan sun gama ci suka fita kofar gida kasan katuwar biyar Darbejiya suka kafa dabar ƴar carafke da sauran yaran makota.
Husna ta sake sosai a cikin yara, kamar yadda babu wanda ya neme ta a gidan su haka ita ma bata sake komawa gidan ba tunda ta fito, gaba daya saita manta da Nana da matsalolin ta, sosai ta sake a cikin yara sunata yar carafke ana zuba uban musu.
Can wajan karfe biyu da rabi na rana taji ana ƙwala mata kira tana ɗago wa taga Ni’ima ce mai kiranta tana tsaye a ƙofar gidan su, Husna ta taso ta biyo Ni’ima tana cewa su Bishira “ina zuwa.”
Ganinta da ɗaurin zani a ƙirji Ni’ima tabi jikinta da kallo sannan tace “kika tsaya min aka, Nana ce ke kiran ki tana dakinta.”
Tana gama faɗin haka tayi ficewarta daga gidan dama gidan su ƙawarta zata.
Da sallama Husna ta shiga ɗakin Nana na zaune a bakin katifar ta da wata mata da bata santa ba, da alama bakuwa tayi. Nana da bakuwar ta suka bi Husna da kallo a wulakance babu wanda ya amsa mata sallamar bakuwar tace “au wai dama wannan ce Ma’un? Yo ni ai na ɗauka ma wata uwar mata ce da naji kinata maganar ta, yanzu Nana akan wannan abar kike mita da ɓata bakin ki, kai amma wallahi kin bada ni. Hmmm! Wannan da batafi ƙarfin na zaune ta ba, duka duka ma nawa take wannan yarinyar?”
Nana ta tari numfashin bakuwar ta da cewa “kayya Zahira dan bakisan munafunci da makircin wannan yarinyar bane, in kikaga kaɗifiri da uwar matan da yarinyar nan take yi in taga ubanta abun saiya baki mamaki, yadda kikasan Beyerabiyar uwarta saida ta karanta mata komai kafin ta fice.
“la la ni bana mamakin duk abinda akace wannan abar tayi, hmmm! Ke bakisan illar irin wa ƴan nan ƴaƴan ba, to wallahi in bakiyi da gaske ba wannan da kike ganin ta a raine a raine saita koreki daga gidan nan, ke zaman kano gaba daya saiya gagare ki, yawwa nadai fada miki gwanda kisan abunyi tun wuri.”
Nana na jin ance zaman Kano zai gagareta ta dafe girji tare da zare ido waje “me kika ce Zahira? Ina wannan bazai yiwu ba.”
“a to nadai fada miki.”
Husna dai na tsaye tana jinsu da kallon duk abinda suke yi, Nana ta kalleta a wulakance tace “gidan uban wa kika tafi tun safe? Oh gani shegiya ko kin fasamin botiki da sanyin safiya na kyale ki, shine kika fice tun safe baki sake shigowa ba sai yanzu da aka kiraki.”
Husna dai ba ta ce komai ba sai kanta data sunkuyar ƙasa.
Wani mugun tunani ne ya fado ran Nana, shedan ya kitsa mata "kawai ki fara aiwatar da shawarar Zahira tun yanzu, inba haka ba da gaske zaman gidan nan saiya gagareki."
Nana ta ɗan sanyaya murya tace
“Hmmm! Kinga ni maza cire wannan zanin na jikinki ki saka kayanki gasu can kizo na aike ki ɗorawa.”
Husna taji maganar wani iri dan ita dai tasan bata da kayan sawa a ɗakin Nana amma ganin rigarta a gefan katifar ta saita tsaya tana kallon Nana. Ita kuma a zabure tace “zaki cire wannan baƙin zanin ki ɗauki kayan ki kisa ko saina taso.” Nana ta daka mata tsawa tana nuna mata doguwar rigarta data ajiye a gefan katifar ta. Ko yaushe tazo nan ɗin kuma oho?
Abinka da yarinta ga tsoro da rashin wayo, kawai Husna sai ta kunce daurin kirjin da Umman Bishira tayi mata dazu.
Daga ita sai pant ta karasa wajan kayan tasa hannu zata dauka ke nan taji an fincikota tayo baya kanta gama fahimtar meke shirin faruwa taji saukar bulala a bayan ta, ta buga tsalle ta juyo tana sosa baya tayi ido biyu da Nana tsaye da wata zabgegiyar dorina mai baki biyu, ko a ina ta same ta oho? Dan ita dai tasan Babanta bai taɓa siyo dorina ba.
“badai ke tantiriyar mara mutumci ba, yau zanci uwarki a gidan nan.”
Nana ta faɗa tana sake yowa kanta. Husna na ganin haka ta kurma uban ihun neman taimako.
Nana ta fincikota ta kayar a tsakar ɗakin ta fara lafta mata dorinar babu tausayi babu duban shekarun ta, jibgarta take kamar wacce Allah ya aiko ta, da ƙyar Husna ta mike a rude tayi cikin ɗakin da gudu tana ihun kuka tare da neman gurin ɓuya, amma ina babu matsira Nana ta bita tana duka suka rinƙa zageye ɗakin tana gudun neman ceto ita kuma tana binta tana duka, wajan bakuwar tayi da gudu tana roƙon ta cece ta dan Nana ta rufe kofa ta hanata fita daga ɗakin, tana zuwa jikin bakuwar ta tureta gefe tana faɗin
“kinga yarinya zata kayar dani dan Allah matsa can”
Ta hankaɗata tsakar ɗakin, Nana ta sake yin kanta da duka, tun Husna na kuka da ihun neman taimako har ta gaji ta kwanta a tsakar ɗakin muryarta ta dashe saboda ihun data rinƙa yi, saida Nana tayi mata lilis ta farfasa mata jiki san ranta sannan ta kyale ta a yashe a tsakar ɗaki.
Ta daga katifa ta saka Dorinar hannunta tana maida numfashi tace “shegiya gobe ma inna aikeki ki ƙara yimin mugunta, munafuka jinin masifa da bala’i, zaki tashi ki barmin nan ko saina sake turmusheki.”
Zahira tayi dariyar nishaɗi tana jinjinawa Nana tace “a’a barta haka karkiyi kisa kija mana masifa, ai ko yanzu ta daku ina faɗa miki gobe kome kikace mata haka zatayi miki shi babu musu, kuma duk abinda kika hanata bazata sake yi ba, ai bakiyi mata da wasa ba, kuma haka shine dai-dai dan irin waɗan nan yaran saida haka, ƴaƴan miji ai masifa ne, Nana tsaf zasu fidda ka daga ɗakin ka in bakayi da gaske ba, sai da irin haka ake bi dasu.”
Tsawa Nana ta sake dakawa Husna da har jikinta yayi zafin zazzabi, da kyar ta iya jan jikin tabar dakin, mai makon ta shiga ɗakin su kawai saita fice daga gidan a halin da take ciki, tana tafe tana sauke numfashi da ƙyar dan azaba ta hanata kuka, jikinta banda zafi da raɗaɗi babu abinda yake mata, ji take kamar ana zuba mata yaji a jikin ta babu ma kamar bayanta da take jinsa kamar wanda ta kakkarce.
Umman Bishira na zaune a tsakar gida tana aiki kawai sai ganin Husna tayi ta shigo tana layi daga ita sai ɗan pant kamar wacce aka koro, hankalinta a mugun tashe tayi kanta tana salati.
“ke yar nan meya sameki haka?”
Husna ba baki sai hawaye da wata irin ajiyar zuciya da take sauke wa, Umma nayin ido biyu da gadan bayan Husna ta kurma ihu tana faɗin
“na shiga uku ni Barira Husna waye yayi miki wannan dukan?”
Umma tayi tambayar tana kankame hannun ta, Husna naso tayi magana amma kuka da zafin da takeji a bayanta da jikinta ya hanata tayi wa Umma bayani.
Suna cikin haka su Bishira suka dawo daga aiken da Umma tayi musu, suna ganin jikin Husna suma suka fara kuka, cikin abinda baifi minti biyar ba jikin ta yayi wani irin budir budir bayan ta kuwa gaba ɗaya ya farfashe babu kyan gani, haka hannayenta da cinyoyinta duka shatin bulala ne a kwakwakwance kamar zanen layi.
Ita kanta Umma share hawaye take, ko takan aiken da tayi wa su Bishira bata biba tace wa Fa’iza kanwar Bishira maza ta ɗakko mata wayar ta a daki ta kira Baban su.
Akan taburma ta kwantar da Husna da jikinta yayi zafi sosai. Lokaci ɗaya kuma zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta.
*****
_ABUJA_
Duk yadda yankin na Zuba ya kasance wajene ma tattarar jama'a, ƴanci rani maza da mata masu saida abinci da sauran mutanen gari da baka rabasu da wajen ko dare ko rana, sannan ga tashar hawa mota wanda hakan ya sake taimaka wa wajen cikowa da haɗa gosulon ababan hawa sosai, duk da babban titine wajen baya rabo da gosulon ababan hawa saboda yawan kaiwa da kawowar mutane, zaka samu yankin na Zuba cike da jama'a sunata harkokin su, yankin ya zama Bariki (Kazo nazo)......amma yau duk wannan cunkoso na Zuba babu shi yankin yayi fayau, saboda abunda ya faru ɗazu bayan sallar isha'i tsakanin jami'an tsaro, da masu lefi, da kuma mazauna wajen.
Bayan sallar isha'i kaɗan mutane sunata harkokin gaban su, sukaji ihu da gudun ababan hawa, masu lefi sun kutso cikin mototin mutane da gudun gaske jami'an tsaro kuma sun rufo musu baya, mutanen da kekan titi sunata ƙoƙarin sauka su bawa jami'an tsaron da suka koro masu lefin hanya su wuce, jin tsahin harbin bundugu da masu lefin keyi yasa mutane suka sake rudewa tuni suka fara fitowa daga cikin motocin su suna guduwa don neman mafaka, jin tashin harbin ya sake rikita mutane dan wasu harsun fara taka fararen hula da mototin su, ganin motar masu lefin ta sauka a titi ta kutsa cikin mutane da masifar gudu yasa Jami'an tsaron na NDLEA cin wani mugun burki saboda ganin muguwar barnar da masu lefin ke yiwa mutane, babu imani suke bi takan duk abinda ya tsaya musu a hanya su wuce, ganin haka jami'an suka tsaya basu ankara ba motar bayan su tazo ta wucesu fit da mugun gudu ta mike titi sai kuma ta sauka a hanya da alama shan gaban masu lefin take son yi ganin haka suma sauran motocin suka fara kokarin bin bayan waccan motar amma abun mamaki duka tayoyin motocin nasu sai suka sace lokaci ɗaya, abin yayi mugun basu mamaki dan lafiya suka tsaida motocin sannan basu taka komai ba, amma abun mamaki tayoyin harda wanda suka fashe kamar ansa abu mai kaifi an yanka, nanfa hankalin su yayi mugun tashi dan dole suna buƙatar bin bayan jam'in su da yabi bayan masu lefin akan lokaci.....
_*WRITING.....✍🏻*_
*_MUTUWAR AURE.....!_*
_(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_
*_Kanawa ne👌🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
_BOOK 1_
*_FREE PAGES_*
________________
*_WHATSAPP GROUP👇🏻_*
https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t
https://wa.me/+2348064789370
_________________
_EPISODE 2_
A can jam'in da yabi bayan masu lefin nan kuwa, ta cikin fruit market suka bi kai tsaye yabi bayan su, suna shiga cikin kasuwar tayar motar shi tayi wani irin bundiga motar tayi tangal tangal zata kifa da kyar ya iya riƙe ritiyarin motar ya take burki ji kake "ƙuuuuuuu." Ya tsaya ƙura ta bule wajen, saboda tsabar taurin zuciya irinta jami'in motar bata gama tsayawa ba ya diro daga cikin ta, yana neman hanya yana kade kurar gaban sa da hannayen sa saboda kurar data tashi.......yana cikin wannan yanayin yaji an buga masa wani abu a ƙeya saida yayi gaba yayi baya saboda tsabar azabar da yaji ta shigi tsakar kansa, sai kuma luuuu ya zube akan kafafunsa dan jiri ne ya kwashe sa jini ya wanke masa fuska take idanunsa suka fara rufewa dan ba ƙaramin bugu aka yi masa ba......sama sama yake jiyo dariyar mutane a kansa cike da karfin hali irin na jami'in tsaro ya fara ƙoƙarin ciro bundigarsa yaji an take masa hannu tare da sauke masa wani gigitaccen mari ta hagu da dama.
"Kuyi sauri bamu da lokaci, oga yace ayi masa sabon kayan nan mu ware."
Wanda yayi maganar ya jefawa wan da ya take masa hannu wata jaka ya cafe jami'in dake jinsu can nesa kamar a mafarki ya fara yunkurin kwatar kansa amma ina sarkin yawa yafi sarkin karfi, yana ji suka danne sa wani da baisan ko waye ba yayi masa allura a dantsen hannun sa, cikin abinda bai kai second biyu ba jami'in ya nemi hankalin sa ya rasa, bai kuma sanin abinda ke faruwa dashi ba saidai can cikin jikinsa yake jin wani abu mai kama da tashin wuta yana bin jinin jikinsa da masifaffan gudu, su kuwa suna ganin haka suka kwashe da muguwar dariya sai kuma duk suka watse kowa yayi hanya daban daban, motar da jam'in ya biyo kuwa babu ita babu alamar ta a wajen da alama ta dade da barin gun.
Cikin abinda baifi minti 10 da faruwar rikicin ba mutane kowa ya gudu inda yake ganin zai samu mafaka, wanda suka ji ciwo kuwa suna yashe agun, cikin ɗan kankanin lokaci yankin na Zuba yayi shiru kamar mutuwa ta gifta, bakajin komai sai tashin jiniyar motocin jami'an tsaro, mutane kowa yayi luf a mafakarsa dan tsoro da gudun fadawa lefin da ba naka ba, sannan komai na iya faruwa da duk wanda aka samu a wajen, wannan dalilin yasa yankin ya sake daukar wani irin shiru naban mamaki, kai kace a tsakiyar burtalin dake can cikin kololuwar jeje kake ba cikin jama'a ba, tsabar shirun da yankin ya ɗauka baka iyajin motsin komai, titina kuwa tuni jami'an tsaro suka kashe su,
MM da wasu yaransa sun iso wajen cikin kankanin lokaci dan Chike yaronsa yana faɗa masa sun samu matsala ya baro gida Faisal dake tare dashi a lokacin shima ya biyo sa da gudu, dama ya zo ne suna magana akan yadda suka samu jita jitar an fara shigowa da kayan da suke shirin kamawa wannan satin ta barauniyar hanya, saidai ya tura yaransa su duba meye gaskiyar maganar, suna cikin maganar labarin abinda ya faru ya same sa, da gudun wuce iyaka ya iso wajen cikin kananun mintina, yana zuwa ya bada umarnin wasu su tsaya a nan wanda suka ji ciwo kuma a kira motar asibiti, wasu yaransa suka shiga motar da suka zo da ita sukabi bayan jam'in, tuni MM ya fara duba SC ɗin jam'in yadda samun sa zai yi musu sauki, dan baima san waye a cikin yaran nasa yabi bayan masu lefin ba, haka bai tambaya ba dan yanzu ba lokacin tambayar bane.
*****
Tunda suka iso wajen tsawon minti biyu har yanzu suna tsaitsaye akan motar da jam'in yake ciki, wanda suka tabbatar da babu shi acikin motar, har yanzu yana tsaye akan kafafunsa bai motsa daga yadda yake ba yaransa na zagaye dashi ko basu faɗa ba zukatansu na cikin damuwa, amma abinka da jami'an tsaron da suka samu goge wa akan aikin su ko kaɗan bazaka gane hakan akan fuskokinsu ba.
MM ta cikin gilashin idonsa daya boye asalin halittar ƙwayar idan yake ƙare wa wajen kallo, sauran yaran nasa kuma suna tsaye a gefe ko wannen su da abinda yake tunani, saida ya gama lissafa wajen kaf sannan ya juya gefansa na dama ya kalli wanda ke kusa dashi ba tare da yayi magana ba jami'in ya amsa da
"Sagir ne a cikin motar Sir."
ya faɗa da sauri yana duban MM dan kobai faɗa ba yasan kallon sa da yayi yana nufin san sanin wanda ke cikin motar ne.
"Sagir."
Ya maimaita sunan cikin san danne abinda ke zuciyar sa.
"Yes Sir."
"Okay."
Bai sake cewa kokai ba ya kalli Faisal dake gefan sa, ya daga masa kai, Faisal yayi gaba inda motar take.
Ganin haka sauran yaran MM suka sake gyara tsayiwar su mutum biyu a cikin su kuma suka juya sukabi bayan Faisal....
Yana daga inda yake yana kallon yadda suke lalume motar data kife, Faisal ya duga ƙasa yana leken ƙasan motar, sai kuma ya kwanta da sauri yana sake leka kanshi kasa kamar dai yadda bakanike keyi.
"Oga Faisal akwai matsala ne?"
Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana Ƙarasowa inda Faisal ɗin yake kwance a ƙasan motar yana kokarin tura hannun sa ta inda motar ta kwanta amma yaƙi shiga saboda ta kife sosai ta bari ɗaya, ga motar ta fara hayaki da alama zata iya kamawa da wuta daga yanzu zuwa ko wanne lokaci, ganin haka yasa shima dayan jami'in zuwa wajen da sauri.
"Sir ba muga komai ata nan bafa, anya basu tafi da shiba?"
Wani daga cikin mutum biyun da suka bar wajen dazu ya faɗa sanda ya iso inda MM yake tsaye.
Mai makon ya ba shi amsa kawai sai yayi gaba ba tare da yace komai ba, ganin haka suma suka rufa masa baya da sauri.
Yana isowa inda suke Faisal ya tashi tsaye yana kade jikinsa, cikin damuwa yace
"gaskiya MM inaga sun tafi da Sagir dan baya cik......"
Faisal bai karasa maganar da yake ba ya zare ido cikin mamaki yake kallon MM daya ɗora hannun sa akan motar yana sunkuya wa jikin ta sai kuma yadan kasa kunne, Faisal ya yunƙuro zai sake magana ya ƙada masa yatsu biyu da sauri alamar yayi shiru....
Cikin zafin nama ya dago kansa tare da faɗin
"akwai mutum a kasan motar."
Ba tare da sun sake tunanin komai ba suka fara ƙoƙarin ture motar gefe, dan cikin ko wanne lokaci tana iya kamawa da wuta, cikin ikon Allah suka ɗaga motar kaɗan, mutum biyu suka leƙa.
"Innalillahi."
Faisal ya faɗa da wani irin sauri zuciyar sa na bugawa, Faisal bai gama rufe bakin saba yaga MM ya duƙa ƙasan motar cikin yanayin sa na shanye wa ya fara ƙoƙarin jawo Sagir dake kwance a ƙasan motar cikin jini yayi ruf da ciki, farar rigar jikinsa tayi kaca kaca da jini, ganin haka Faisal ya fara taimaka masa suka zaro sa, saida zuciyar su ta doka sanda suka sauke idanunsu akan Sagir dake kwance cikin jini fuskarsa tayi mugun sauyawar da inba farin sani kayi masa ba baka isa ka gane waye ba...
"Nan da 3 to 5 minutes motar nan zata iya kamawa da wuta, zamu bar nan yanzu." MM yayi maganar cikin yanayin da kai baka isa ka gane a wane hali yake ciki ba, sai dai kana jin yadda muryarsa ke fita kasan akwai damuwa da ɓacin rai kunshe da zuciyar sa...
Sauran yaran nasa jikinsu a mugun sanyaye suka saka Sagir a motar da suka zo da ita cikin abinda baifi minti ɗaya ba suka far wajen da mugun gudu....saida suka daidai ta akan titi sannan sukaji saukar muryarsa yana faɗin
"Asibiti."
Mamaki ya kashe yaran nasa dan sunsa abunda yake nufi da faɗin hakan, tunanin su shi ne meye amfanin zuwa asibitin dan gaba ɗaya sun ɗauka Sagir ya mutu, me kuma zai kai su asibiti....wanda kejan motar ya ɗauke titi zuwa asibiti, Faisal dake zaune kusa dashi sun saka Sagir a tsakiyar su ya kasa hakuri saida yace "amma MM ya mutu fa."
Saida ya kalli Faisal ta cikin gilashin idonsa sannan ya maida idan sa kan Sagir dake kwance cikin jini a hankali yace "Bai mutu ba."
Tsaf Faisal yaji saukar maganar tasa cikin kunnen sa da sauran yaran basu ji me MM ɗin yace ba, cikin neman tabbaci Faisal ya sake kallon Sagir sai kuma ya kalli MM yana son yin magana yaga ya tsare sa da ido, koda baya ganin idanunsa ya fahimci baya buƙatar ya sake yin maganar ne, dan haka sai yaja bakin shi yayi shiru yana ta lissafin yadda hakan zata yiwu.....har suka iso ɗan ƙaramin private hospital ɗin babu wanda ya sake magana a cikin su.....
Suna isowa asibiti aka shigar da Sagir ciki, Asibitin ƙarami ne amma tun daga waje zaka sheda sunada tsari, komai na su a tsare yake dai-dai da walwalar majinyya tansu.
Tunda Likitoci suka shige da Sagir su Faisal suka samu waje suka zauna MM kuwa wata nurse ce tayi masa rakiya zuwa gallery ɗin ɗakin da suka shiga da Sagir ɗin yadda zai iya ganin komai dake faruwa, ta sama ya tsaya ya zubawa cikin dakin ido yana kallon yadda likitoci suke ta kokarin ceto rayuwar Sagir, sun kai wajen minti ashirin suna ta kokarin ganin numfashin sa ya dawo daidai amma abun ya gagara, Dr Sadiq ne ya kalli sauran dectors ɗin dake tare dashi cikin sanyin jiki yace "gaskiya zai yi walaha mu iya controlling matsalar sa, kamar yadda kuke gani wannan bugun na kansa ba shine ya sashi cikin wannan mawuyacin halin ba, ina ganin akwai abinda ya shaka ko sha wanda ni kaina na kasa gane mene ne."
"Nima nayi tunanin haka Dr, amma yanzu mene abun yi?"
Wani a cikin likitocin ya faɗa, Dr Sadiq da shi ke leading sauran Drs ɗin ya numfasa sannan yace "yanzu ya tsallake matakin farko, akwai allurar dazan masa cikin wasu yan awanni zai iya motsawa, amma gaskiya bani da tabbacin zai iya tsallake wan......"
Kamar wanda aka tunawa wani abu sai ya kasa karasa maganar ya daga kansa sama idanunsa ya sauke akan MM dake tsaye hannun sa zube cikin aljihun wando yana kallon duk abinda ke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 31