Share this page
Yayan nasu mai tarin alkhairi da tausaya wa a gare su wanda ya daɗe da zame musu makwafin uba tun kafin rasuwar mahaifin su haka bayan rasuwar mahaifin su shiya zame musu gata. Tausayin ta dake taso masa ya danne ya kama hannayen ta yana sakar mata murmushin da bai kai zuciyarsa ba yace "Safiyya ina rokon ki dan Allah kiyi haƙuri ki gwada fahimtar mu, ki yarda baza mu cuce kiba haka baza mu taɓa cutar da Husna ba, ba lallai nasan yadda kike ji a zuciyar ki ba amma ki yarda nima ubane, uban da yasan daraja da ciwon ƴaƴan sa, sannan ni Yaya ne da bana iya jure kuka da shiga damuwar ƙanne na, haka Safiya ni ɗane da bazan iya ɗaukar cin mutumci da lalata wa gidan mu da iyayen mu suna ba." Baba Habu yayi shiru na ɗan wani lokaci ɓacin ran dake taɓa zuciyar shi yake son hanawa tasiri amma abun ne da ciwo a sako maka ƙanwa da ƙaramin ciki a wulaƙance a kuma muzanta maka iyaye da asali. "Baki da cikakkiyar lafiya kinji abinda likita yace kina buƙatar hutu da kwanciyar hankali, sannan ki taimaka wa abinda ke cikin ki, dan Allah ki karɓi Ƙaddarar ki da hannu bibbiyu kiyiwa Allah godiya karki butulce masa, sannan Safiya babu wanda zai raba ki da Husnah duk inda taje kuma a duk inda take ke ɗin dai Safiya Abdulkadir Mai Shinkafa kece uwar ta ke kika haifeta duk duniya kuma babu wanda ya isa ya canja wannan. A yau in kin rasa dama da alfarmar riƙe Husnah Inaso ki daga hannu ki gode wa Allah daya baki damar rike Baffa da abinda ke cikin ki. Banyi miki alkawarin zamu rinƙa sawa Husnah ido a rayuwar digan mahaifin taba sai dai munyi miki alkawarin duk wani abu na taimako zata same sa daga gare mu, nasan Abdullahi yana son ta zai kula da ita yadda ya kamata, dan haka ki kwantar da hankalin ki kiyi min alkawarin daga yau zaki barwa Allah amanar ta ki nutsu ki bita da addu'a." Ya dakata da maganar yana kallon Safiya dake haɗiye kukun ta amma kukan yaƙi tsayawa tana share hawaye wasu na sake zubowa, hannu Baba Habu yasa ya daga Husna dake kwance akan cinyar ta da sauri tasa hannu ta dafe ta tana kuka Baba Habu ya saka idanun shi cikin nata a hankali ta sake ta tana komawa baya. Husna da bata wani gane kan maganganun da ake ba dan sun wuce fahimtar ƙananun shekarun ta, hannu Baba Habu ya miƙa mata yace "Zo Mamana muje wajen Baba ko?" Kamar tasan me za'a mata ta koma baya ta sake maƙale Mamanta, miƙe wa yayi yana duban Yaya Kemi da jikin su yayi sanyi yace "ɗakko ta muje Mansura biyo ta ku same ni a mota." harya juya sai kuma ya wai wayo ya kalli Maman Sama yace "Mamana kiyi haƙuri komai zai wuce." Bai yarda ya sake kallon inda Safiya take ba ya fice daga ɗakin. Aunty Mansura da wayo ta cire Husna a jikin Safiya sun zo zasu fita ta juya ta kalli Maman ta da tayi wani iri hannun ta ta kwace ta juya da gudu zata koma wajen ta Yaya Kemi ta tare ta suka fito daga ɗakin tana fashewa da kuka. "Wayyo Allah ni bazan je wajen Baba ba, bana so Yaya da Mamana nake so, ni bazan koma gidan Baba ba, Mami nace miki na fasa zuwa da Mama zamu je ko Yaya, ni ki sake ni na koma wajen Mamana." Wannan kuka da ihu da Husna keyi lokacin da suke fita da ita daga gidan ya sake tada hankalin Safiya su Aunty Sakina gaba ɗayan su kukan tausayin Husna suke, Maman Sama kuwa Safiya ta rungume suna kuka, duk dauriyan Momma data jiyo kukan Husna saida ta zubar da hawaye. "Allah al-Maliku ka duba rayuwar wannan yarinya Allah ka kyautata rayuwar ta kayi mata albarka." Momma ta faɗa tana shigewa toilet ɗin ɗakin ta dan bata son jin kukan da Husna keyi yana ɗaga mata hankali.... Tsawan kwana biyun nan Mai Kano bai fita kasuwa ba yana gida yana fama da kanshi, wasa wasa zazzaɓi ya kada shi har saida yasha ruwa laida biyu banda allurori. Tsawon wannan kwanaki kuma bai taɓa mantawa da Safiya ba burin sa yanzu yaji a wanne hali take ciki amma babu dama. "to wazai faɗa masa?" Ya dau waya sau babu adadi yana son gwada kiran Abdussamad yaji halin da take ciki amma kunyar abinda ya fatu saiya hana shi kira. Yau daya ji jikin nasa da sauƙi ya tashi da alwashin komai zai faru sai yaje ya duba Safiya, yana son sanin halin da take ciki, ko badan cikin shi dake jikin taba ita ɗin uwar ƴar sa ce. Yasan dole zai fuskanci matsala da kalubale daga wajen yan uwanta wata kila ma har ita kanta dan tunda yaga babu wanda ya neme shi a cikin su yasan lallai an kai su inda bazasu iya jurewa ba. "To su kiraka suce maka me? Aure ne tsakanin shi da yar uwar su ya ƙare, babu bukatar su tambaye dalili tunda komai ya faru agaban ƴan uwanta shaƙiƙanta ya faru. "to miya rage tsakanin ku?" "Babu." Amsar ta fito daga kasan zuciyar shi, yana cikin wannan halin tunani kira ya shigo wayar sa, wayar ya zaro daga aljihun gabar rigar sa. "Baba Habu." Sunan mai kiran ya bayyana akan screen din wayar, Mai Kano yaji kamar Alhaji Ƙadiri ne ke kiran shi saboda tsabar ruɗewa har wayar ta katse bai daga ba.Wani kiran ya sake shigowa a wannan karon bai bari kiran ya katse ba yayi ƙundinbala ya daga. "Assalamu alaikum Abdullahi kana gida ne?" Baba Habu ya faɗa muryar shi normal kamar babu abinda ya faru, da kyar Mai Kano ya amsa Sallamar ya haɗa da cewa "Um....eh ina gida." "To Alhamdulillah muna ƙofar gidan ka." Dummmm yaji saukar maganar a sama dan baiyi zaton jin haka daga bakin sa ba, yayi dawurwuri a tsakar ɗakin kamar me neman wani abu sai kuma ya juya da sauri ya fito ya wuce Su Nana a tsakar gida Dije nayi masa magana amma ina baiji taba yayi waje. Duk kunya da sunkuyar dakan da Mai Kano ya fito dashi Baba Habu yayi kamar bai gani ba ya miƙa masa hannu a sake kamar yadda suka saba yace "Barka da rana Malam Abdullahi." "Yawwa barkan mu dai, ya wajen iyali?" Shima ya dake ya faɗa. "Lafiyan su Alhamdulillah." Yaya Kemi ta fito daga motar riƙe da hannun Husna da har yanzu take kuka, Aunty Mansura ta fito ranta a cunkushe dan itafa Abdullahin ma haushi yake bata. "Baban Husna ina kwana?" Yaya Kemi ta faɗa, Mai Kano ya amsa yana kallon Husna da tayi kamar bata ganshi ba. A ciki ciki suka gaisa da Aunty Mansura ko kaɗan baiga lefin taba tunda da ai ba haka take masa ba yanzu kuwa kamawa tayi. Baba Habu yabi bayan Aunty Mansura da tayi gaba kanta tsaye ba tare data jira ya yiwa Mai Kano bayanin dalilin zuwan nasu ba, kai ya girgiza sai kuma ya mai da hankalin shi kan sa yace "Abdullahi na dawo da Husnah ne kamar yadda kuka buƙata na zaɓi na kawo ta da kaina saboda nine makwafin mahaifin mu yanzu, wata ƙila da yana raye shi zai kawo ta da kanshi." Baba Habu ya ɗanyi shiru yana kallon Abdullahi da tunda ya fara maganar yayi ƙasa da kansa. "Nataho dasu Kemi ne dan su haɗa kayan Safiya in sun gama Abdulganiyyu zai zo da mota su kwashe, Mamana zoga Baban ki." Ya ƙarasa maganar yana juyawa wajen yaya Kemi ya kama hannun Husna amma saita koma bayan shi ta ɓoye, tace "Ni bana son nan." Mai Kano yaji wani iri da furucin Husna, yarinyar da indai yana gida bata kula sabgar Maman ta amma yau ita ake fama tazo wajen shi tana ƙi. Yaya Kemi tabi bayan Aunty Mansura, sai lokacin kuma Mai Kano ya dubi Baba Habu yana Murmushin da yafi kuka ciwo yace "Bani da bakin dazan baku haƙuri amma duk da haka ina haɗa ku da Allah kuyi haƙuri ku tayani bawa Safiya haƙuri, Baba Habu Iya uwata ce mahaifiya bani da yadda zanyi da ita, wallahi ba ason raina komai ya faru ba." "Abdullahi mun sani su Sakina sun faɗa mana duk abinda ya faru, babu komai shi Aure ai raine dashi zaman ne ya ƙare, ga wannan takardar tabbacin samuwar cikin Safiya ce ka ajiye ta a wajen ka ya zama shaida saboda nan gaba original ɗin tana wajena nasa Ja'afar ya bude File akai, Allah ya rufa mana asiri." Mai Kano yasa hannu biyu ya karɓa yana jin babu daɗi a ranshi, wai yau cikin sa da Safiya ake ajiye shaidu saboda maganar Mahaifiyar shi, ko a mafarki bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba. "Karka damu Abdullahi nina fahimci halin da kake ciki amma bazam ɓoye maka ba naji zafin abinda akawa Safiya, a matsayina na mutum mai iyali kuma na tayaka jin babu daɗi, iyayen mu dole zamu bisu Allah ya raba mu dasu lafiya." Sosai maganganun Baba Habu yasa Mai Kano yaji wani abu ya sauka a ranshi, tabbas ahlin Alhaji Ƙadiri mutanen arziki ne wanda suka san ya kamata. Baba Habu nata fama da Husna ta sake shi ga Baban ta amma fur taƙi yarda sai da Mai Kano ya shiga gida ya fito da mashin yace tazo su tafi yawo ba zai kaita cikin gidan ba sannan ta saki Baba Habu ya tafi yana jin tausayin ta na kama ranshi. *****Su Yaya Kemi suka shiga gidan babu wanda ya tanka musu, suma bayan sallama basu ce komai ba suka wuce ɗakin Safiya da tuni Aunty Mansura ta buɗe ta shiga. Dije ce ma taso tayi musu tijara tana haɗa ido da Aunty Mansura ta kama kanta dan ance wasa ma waje ya samu, bata ga wajen yi ba shi yasa taja bakin ta tayi shiru, aranta dai tace "daga ganin wannan ba irin su Tawakallatu bace tsaf zata kalmashe tsufana ta miƙa min abina, babu abinda ya dame ta." Suna shigewa ciki Nana tayi shewa sai kuma ta miƙe tayi ɗakin ta tana waƙoƙin habaici. Abanza man kare dan wanda take yi domin su ɗin ba gane abinda take faɗa suke ba... Tas su Yaya Kemi suka haɗe kayan Safiya na Husna kuma a wata babbar akwati suka haɗa mata sauran suka zuba a ɗaya daga cikin jakun kunan data rage. Abdulganiyyu ya iso da motar da zata kwashi kayan, Yaya Kemi ta fita suka shigo tare da wasu samari, cikin ƙanƙanin lokaci suka kunce kayan gadon suka fita dashi, ƙaramar katifar Husna kawai suka bari a ɗakin sai kayan ta, kayan Mai Kano ma a kan katifar Husna suka barshi Yaya Kemi taso su miƙa wa Nana Aunty Mansura tace "Kina son muyi rigima kan mubar gidan nan ko?" "Wacce irin rigima kuma Mansura daga miƙa kaya?" "Hmmm! To kibar masa kayan shi anan in yazo ya kwashe inba haka ba kika je kai kaya nan waccan matar tashi da bata da tsarin mata ta faɗa mana magana wallahi sai na hau ruwan cikin ta." "Zaki aikata Mansura kaiwar ai ba dole bace bassu anan muje ya kwashe inya dawo." Yaya Kemi ta faɗa suna fitowa daga ɗakin. Yadda suka shigo haka suka fice babu wanda suka yiwa magana. ******Mai Kano kuwa kasuwa ya wuce da Husna acan suka wuni kuma tadan sake amma ya sha tambaya. "Baba daga nan wajen Maman zaka kaini ko?" Baya bata amsabsaidai yace "zakije in sha Allah." Bayan Sallar la'asar gaf da Magarba suka baro kasuwa suna tafe yana janta da hira har suka zo gida nan fa ta coge a kofa taƙi shiga, da ƙyar ya samu ta bishi cikin gidan bayan tasha lallashi. Yana riƙe da hannun ta suka shigo Husna na riƙe da ledar Popcorn da tace tana so ya siya mata, a tsakar gida suka samu mutanen gidan. "Baba sannu da zuwa." Ni'ima ta faɗa tana matsawa daga kusa da Dije ta bashi waje ya zauna. Nana tayi masa Sannu da zuwa ya amsa yana zama a kusa da Dije. "Mai Kano an dawo?" "Iya Allah yayi mana dawowa." "To mun gode Allah." Sai kuma ta kalli Husna dake tsaye a kusa da shi kamar zata koma Cikin sa tace "ita kuma wannan yaushe suka kawo ta? Ko kaine kaje ka ɗakko ta?" Ta faɗa tana tsatstsare shi da ido. "A'a Iya ban jeba ɗazu ai tare suka zo dasu Baba Habu." "Oh shine ka sata a gaba kuka tafi tare tunda kabar Mayu a gidan kada mu cinyeta kan ka dawo." "Subhanallah! Wallahi Iya ba haka bane kinsan Husnah da rigima kuma naga tana ta kuka shi yasa na tafi da ita." "Kai dan Allah matsa can indai akan Safiya da ƴaƴan tane ba'a kada kai, komai aka faɗa kana da amsa, kuka ai aiki ne inka tafi ka barta inta gaji zata daina, dan kar tayi kuka ga ƴar gold saika rinƙa sata a gaba kuna tafiya tare?" "A'a kiyi haƙuri Iya baza a sake ba." Mai Kano ya faɗa yana jin ranshi babu daɗi. "Ai ko baka faɗa ba daga yau an gama, munafuka kika tsare ni da ido." Dije ta yi maganar tana warce ledar hannun ta. Faifai tasa Ni'ima ta miƙo mata ta zazzage guggurun ta kasa shi gida huɗu, bata da haƙorin ci fa amma dan jaraba saida ta ɗibi nata ta miƙawa Nana ta ɗauka Ni'ima ma ta ɗauka sauran kaso ɗayan daya rage kuma ta dungura wa Husna. "Gashi nan saiki ɗauka, ai ba fin sauran ƴaƴa kikayi ba, kika riƙo leda kika hana kowa gaki mai uba to ya haifi wasu kafin ki, ni dama da a nan zan zauna da saina saita miki zama dan bazan ɗauki wannan iskanci da sakalcin da suka koya miki da sunan so da gata ba, yarinya ba'a isa ayi miki magana ba ƴar firit dake sai fi'ilin tsiya da sanabe, to wallahi maza ki kama kanki." Washegari akwai makarantar Boko mai Kano da kanshi ya tashi Husna ya shirya ta, saida ya rakata har makaranta sannan ya dawo gida ya iske Nana tayi fam yadda kasan kububuwa jira kawai take ya tanka mata ta juye masa abinda ke ranta shi kuma daya fahimci haka sai yayi kamar bai gane abinda take nufi ba ya shige ta a tsaye ya fara shirin fita dan yau Dije zata koma ƙyauye kamar yadda ta faɗa masa da asuba daya shiga gaishe ta. *****Sha biyu da rabi ake fitowa break kowa ya fito da abinci yana ci banda Husna data riƙe ledar wainar shinkafa da Baban ta ya siya mata tana kallon sauran yara suna ta cin abinci. Tunda safe yake tunanin abin da zai bata ta tafi makaranta da shi yaso yi wa Nana magana tayi mata wani abun amma sai yayi tunanin bata san ya tsarin yake ba karya ɗora mata wahala zai bari zuwa karshen Time ɗin inya saka Ni'ima sai tanayi musu tare, wannan yasa a hanya ya siya mata wainar shinkafa da yawa ya haɗa mata da ruwa da biskit. Tagumi Husna tayi tana kallon yara abokan ta sunata wasa dan basa komawa aji sai ƙarfe ɗaya in sunyi Sallar Azahar. Bishira tayi juyin duniya da Husna ta tashi suje suyi wasa amma taƙi tashi, baiwar Allah duk ta damu saboda ita a tunanin ta dukan ta su Salma suka yi tunda sune abokan faɗan su a makarantar kuma basa shiri da Husna saboda ta rena su tun randa Uncle Abba ya kirata ajinsu yace ta faɗa musu abinda suka kasa ta rena su, babu dama su haɗu sai tace musu "yan aji 6 masu ƙwaƙwalwar farar Mama." Husna badai tsokana ba silent killer ce tasan neman magana amma inka ganta shiru shiru saika ɗauka sharri ake mata ga baki kamar aku ta tsokane ka ta fika iya tsari. Bishira tayi mata magana kuma ta hayayyaƙo mata karshen faɗan ya koma kanta su zuba gaba har sai Yaya ko Umman Bishira ta shiga zancen sannan za'a shirya. Ana kiran sallah Husna ta buɗe jakar ta ta saka wainar duk yunwar da take ji taƙi ci saboda ita taci da safe. Yau har a ka tashi suka kamo hanyar gida bata kula kowa ba ko a aji da Uncle Abba yayi mata tambaya cewa tayi bata sani ba. Sannu a hankali Husna ke rayuwa a gidan su maganar daɗi kam wannan babu, danma babanta na iyaka ƙoƙarin sa wajen kulawa da ita yayin da hakan ke kona zuciyar Nana, dan haka ta shirya makirci ta samu Mai Kano cikin nuna tausaya wa da kwantar da kai ta kalallame sa harya yarda ya miƙa mata ragamar kula da Husna, kamar gaske Nana ta riƙe sha'anin Husna ganin haka hankalin Mai Kano ya kwanta gidan ma saiya daina dawowa da wuri wanda hakan yana cikin makircin Nana. kwanakin da suka biyu baya a wajen Husna kwanaki ne marasa daɗi da fasali, rayuwa tayi mata kunci gidan yayi mata zafi, a hankali komai ya fara ƙwace mata, babu Babanta ba arabi babu Boko, babu nutsuwar zuciya ba tsaftar jiki, kuka kuwa tayi shi harta bawa uku lada, wata irin rayuwa Husna ta tsinci kanta a ciki mara daɗi da fasali, ƙarfi da yaji kuma Nana ta fara juya tunanin Ni'ima abu kadan Husna in tayi mata sai zagi dacin mutumci, wajen kwanciya kuwa tuni yafi ƙarfin ta dan Ni'ima ta hana ta kwanciya akai, da farko zanin ta take shimfiɗawa a ƙasa ta kwanta kafin daga baya Nana ta bata taburmar Kaba take kwana akai, Baban ta kuwa raban data sashi a idon ta harta manta dan baya dawowa gida sai tayi bacci da safe kuma kanta tashi ya fita.... Nana ta samu dama sosai take cin karanta babu babbaka akan Husna, yayin da Mai Kano ke can yana sabgogin sa hankali kwance da tunanin Nana na kula masa da ita, kullum kuma inya dawo akwai kalar labarin karya da makircin da Nana zata bashi akan Husna wanda zai sa hankali sa kwanciya. Yau kwanan Husna bakwai bataje makaranta ba, takwas na safe saura Nana ta shigo ɗakin su, tana bacci taji an huri kafar ta firgigit ta tashi tana zare ido Nana tace "Dalla Malama tashi na aike ki ɗorawa ki siyo min koko saura kuma in kinje ki daɗe kiga yadda zanyi dake a gidan nan." Nana ta faɗa tana murɗe kunnen Husna data dafe kanta saboda zafi. Ko ruwa bata sawa jikin taba ta karɓi ɗan fallasan botiki da kuɗin kokon ta tafi siyowa, fuskar ta duk yawun bacci.....! _CIGABAN LABARI._ _*WRITING.....✍🏻*_ *_MUTUWAR AURE.....!_* _(Ƙaddarar wasu ƴaƴan)_ *_Kanawa ne👌🏻_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._ _BOOK 1_ *_FREE PAGES_* ________________ *_WHATSAPP GROUP👇🏻_* https://chat.whatsapp.com/LaVfMaCQz1C2WcC7zGfSL3?mode=gi_t https://wa.me/+2348064789370 _________________ *Mutuwar Auren iyayen ta ya zama sanadi na jarabawar rayuwar ta, komai ya canjawa Husna rayuwa ta juya mata baya, a sanda Nana ke ganin taci ribar ruguza rayuwar Husna a lokacin Allah ya kawo shi cikin rayuwar ta, a wani yanayi da kowa ke gudun shi, rashin wayo, kyawun zuciya da tausayi yasa ta kusance shi cikin rashin sani, yayin da ta maida shi abokin hirar ta harta kira sa da Yayan ta, a sanda kowa ke dugun shi Husna ta huda zuciyar da batasan ta waye ba, da ruwan zinare ta rubuta tarihin da bata sani ba. Yayin da ya shirya riƙe hannayen ta dan su tsallake ramin Ƙaddarar ta sai ta ɓace masa ƙaddara ta rabasu sun yi nesa da juna cikin makahon sabo, saidai yayi alƙawarin nemo ta a duk inda take a faɗin duniya....!* _EPISODE 12_ _CIGABAN LABARI...._ Bayan su Nana sun tafi Mai Kano cikin gida ya koma ya kwanta wayar shima kashe wa yayi dan baya so a dame sa, cikin ikon Allah kuma yana kwanciya tun yana tunani har bacci ya ɗauke shi. Bai tashi daga baccin ba sai bayan sallar la'asar ya fito daga gidan bayan yayi wanka ya shirya tafiya Birget duba jikin Husna tun yana kan hanya yake kiran Abdussamad yaji ko yana gida amma baya dagawa. Lokacin da ya iso tsamiya saida ya tsaya suka gaisa da ƴan majalisar Ubale Mai nama sannan ya tsallaka kofar gidan Alhaji Ƙadiri yana tunanin wanda zai tura ciki yayi masa iso kiran Abdussamad ya shigo wayar sa ya ɗaga wayar da faɗin. "Assalamu alaikum." Abdussamad ya amsa Sallamar suka kaisa a takaice yana cewa "ka kira bana kusa." "Eh, dama inaso naji ko kana gida ne?" "wallahi ina Lagos naje clearance ɗin kaya." Mai Kano ya ɗanyi shiru dan ba haka yaso jiba sai kuma yace "Allah ya bada sa'a." suka kashe wayar a tare. Mai Kano ya daɗe tsaye yana tunani, yasan dole yadda yake shiga gidan Alhaji Ƙadiri yanzu ya canja kamar yadda ya fuskanci canjawar alaƙa tsakanin sa da Aminin sa Abdussamad cikin abinda baifi sati biyu ba komai na tsakanin su ya canja. Ya dade tsaye a ƙofar gidan kafin ya samu shiga cikin gidan, a babban Falo ya zauna Maman Sama ta zauna suka gaisa ya tambayi Momma tace bata daɗe da shiga ciki ba ta ɗan kwanta. Yaso yaga Safiya ya sake bata haƙurin abinda ya faru sannan ya kuma ji ya lafiyar ta, amma sai bai ga fuska ba dan ko Husna Maman Sama ce ta tashi ta kawo masa ita. Da farko ma ƙin zuwa wajen shi tayi tasa kuka ta rakaɓe a jikin Maman Sama. Mai Kano ya dubi yarsa dake mugun sanshi da amma wai yau shi ne take gudun zuwa inda yake, zuciyar sa babu daɗi ya sunkuyar dakai yana jin ɗacin abun har cikin zuciyar sa, da ƙyar Maman Sama ta lallaɓa ta taje wajen Baban ta shima bata wani sake masa ba, ganin haka sai ya dube ta yana Murmushin da yafi kuka ciwo yace "Husnah ya jikin ki?" Kai ta ɗaga masa tana kallon Maman Sama dan gani take kamar tafiya zai yi da ita. "Baza kimin magana ba Maman Mamanta?" "D...da.....da..sauƙi." ta faɗa a rarrabe tana son saka masa kuka. Safiya dake tsaye a bakin window ta cikin ɗakin Maman Sama duk abinda ke faruwa tana kallo su, ta share hawayen daya zubo mata na tausayin tilon ƴar ta da Ƙaddarar rabuwar iyaye ya jefa rayuwar ta cikin garari, ya sauya ta daga yarinya mai walwala kuzari da son mutane zuwa yarinya mara walwala kuzari da tsoron raɓar mutane. "Wai yau Husnah ke gudun Babanta." Safiya ta faɗa a fili tana juyawa ta koma bakin gado ta zauna, cikinta ta shafa murmushi ya kuɓce mata wanda ya fito tare da zubar wahaye. "Shi kuma abinda ke ciki na koya rayuwar shi zata kasance?" Ta ɗanyi shiru tana jin babu daɗi sai kuma a hankali tace "Allah yayi maka Albarka." Kamar yadda Mai Kano ya saba yau ma saida ya ajewa Maman Sama Ihsani dai-dai ƙarfin sa ya bawa Husna tsarabar daya siyo mata sannan ya dube ta yace "Yayan

Chapter 11 of 31