Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 2017 _Hafsat👑: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 ( A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI,WANNAN LITTAFI ME SUNA A SAMA K'IRK'IRARRENE BA FARUWA YAI DAGASKE BA,SUNAYE DA GARURUWAN CIKI DUK NASANE SABODA NISHADANTAR WA,SABODA HAKA A KIYAYE KADA A CANXA MIN LITTAFI KO DAUKAR WANI B'ANGAREN NA CIKINSA DUK WANDA YAI HAKAN............! • Wannan littafi SADAUKARWA ne agareki; cutest mommah😘(Xarah bukhar) _TUKWICI ne agareku;billyn abdul (Tawan)tareda my ya hajja😘💯 nanahafsat.wordpress.com Particular thanks gs to you uwar d'akina, daga shafi na d'aya zuwa na biyar duk nakine (Ummi A'isha)😘💞thank you for working on this book in various ways... Banmantaba dakeba Dota feedhom😘😘gaisuwa mai tarin yawa agareki,Allah ya albarkaci rayuwarki aduk inda kika shiga😘💞 _1_ OXFORD UNIVERSITY ENGLAND; "Sugar boo,yanxu haka xaka tafi kabarni?!" Wata budurwa me kimanin shekara ashirin da biyu Ruwan wankan tarwad'a tanada kyau dede gwargwado Ke fad'in haka yayinda tasauke idanuwanta dake d'auke da fix lashes akan wani kyakkyawan saurayi dake sunkuye yana d'aure mad'aurin takalminsa samfarin designer din zara da alama dashi take magana... *D'ago dara daran idanuwansa yai wa'enda suke d'aukar zuciyar duk wanda yakalleshi ya d'ora akanta,cikin sanyayyar muryar shi me kamada sanyayyar ruwan sanyi ahankali kuma anutse Kamar ana busa sarewa yace; "Basma yakike so nayi uhm?! baaba yakira waya yace Lalle nakoma Nigeria yau, Kuma I have no choice" yak'arashe xancen yana mik'ewa tsaye.. Kan Faffad'an k'irjinsa dake tafiya da ita tafad'a tana rusgar kuka tana shak'ar k'amshin turarukan jikinsa dake cakud'e da k'amshin designers tana magana ahankali cikeda shagwab'a.. "To baby se yaushe kenan?! Nikawai bari in shrya inbika kawai inyaso Idan an d'aura auren semu da......" Bata k'arasa abinda xata fad'a ba yasa hannu yatureta daga jikinsa idonsa yakad'a yai jawur muryarsa har rawa take yafara fad'in; "Basma for how many times xance maki kibar xancen xaki bini muje gidanmu tare?! nace kidinga kama kanki, wallahi kika kaini k'arshe zan mugun sa..." Caraf basma tacafe xancen taname had'a hannuwanta guda biyu alamar hakuri.. "Shikenan sugar boo, Allah yakaika lapia , karka manta ka kirani Idan ka isa plss" "Naji..."shine kawai abinda kyakkyawan saurayin yafad'a Cikeda azama basma tad'au jakarsa had'e da jan akwatinsa samfarin designer d'in giogio Armani da d'ayan hannunta.. Suka fice waje inda motar daxata kaishi airport ke jira.. Saurin sallama yai da abokansa dake jiransa awajen berkley Nottingham hall yayi sannan ya juya yashiga mota ko kallonta beyiba yashiga maxaunin owners corner yaxauna bayan driver yabud'e masa.. Idonta yaciko taf da hawaye se binsa take da kallon soyayya cikeda fargabar karta rasa sahibin nata da take dakon soyayyarsa kowacce rana.. "Sugar boo"tace hakan muryarta tana rawa ,idanuwanta na fitar da ambaliyar hawaye Shikwa driver harya saka key xe tashi motar, saurayin yatsaidashi; "Hold on a second," Kyakkyawan saurayin yace hakan yana me juyar da dubansa xuwaga basma "Yass basma, we r running out of time ?! What is it now uhm?!" "Yareema haydar... Please take care of my love for you, you know I love you, sugar boo I'm so so afraid that...." "Ssshh! Basma nothing can separate our love,kece _Son Rai na_" "But sugar boo..." Saurin katseta Aliyu Hydar yai don baifiya son magana ba don ma Itace shiysa haryake bata amsa.. "Say no more plsss,I will call u Idan na isa,take care of yourself,read hard and study well..." Bata Iya bashi amsa ba sema kuka dayaci k'arfinta don gani take Idan yatafi shikenan sun rabu har abada don Ita kanta tasan ita take dakon soyayyar Hydar ,kusan rabin yan matan makarantar sonsa suke ita d'ince de yake kulawa sama sama saboda azababban nacin datake masa,bawa driver umarni yai dayaja sutafi,, suna xuwa airport aka bud'e mashi private jet yashiga ciki ,wanda ko'ina ajikin jirgin anrubuta _H_R_H SB(his royal highness,shehun borno),, mintina k'alilan jirgin yai booting sannan yad'aga xuwa sararin samaniya, shikam yareema Hydar gyara kwanciyarsa yai akan doguwar kujerar dake luntsumewa don laushi yaiwa kansa matashi da pillow ya lumshe idanuwansa yana tunanin neman me baaba yake masa?! Allah de yasa lapia ...cike da tunani barkatai bacci yai awun gaba dashi ciki harda na'cac'can nacin da basma take masa Kamar ba mace ba!!!! WANENE YAREEMA ALIYU(HYDAR)?! Aliyu (Hydar) Shehu Bulama Goni saurayi ne d'an shekara talatin,me d'auke da kyawu wanda duk ko yaya ka d'ora idonka akansa seka furta kalmar tubarkAllah,d'a ne ga mai martaba shehu Bulama,sarkin Borno state, mahaifinsa mai martaba yanada mata guda uku hajia gajiram sheriff itace matarsa tafarko se hajia Hajjagana Ali Itace matarsa ta biyu se hajja yakolo bukar Itace amarya tak'arshe,Hajiya gajiram matarsa tafarko tanada y'a y'a uku,mata biyu namiji d'aya; babagana,falmata sekuma ayiya.. While hajia hajjagana tanada y'a y'a hud''u: usman(Ngari) se Aliyu(hydar),Aisha wacce suke kira da (Aysa)sekuma auta affy, amarya hajja yakolo kuma tanada yay'a biyu; fannah da kuma Rukymamah...! __Mai martaba shehun borno mutum ne me halin dattako da sanin yakamata da darajta al'umma da kula da hakk'ok'insu, shiyasa mutan borno suke sonshi, bakuma ya nuna son wani b'angare akan wani b'angare dukkan yaren garin yana mulki dasu kan zuciya d'aya kama daga kanuri,babur,Fulani da sauransu sosai yake yin mulkinsa na kanem empire bisa yadda yagada daga hannun mahaifinsa marigayi Bulama Goni.. *hajia gajiram sherrif uwargidansa tafarko da amaryarsa hajiya yakolo sune suke xaune a masarautar while hajia Hajjagana mahaifiyar su Aliyu Hydar tana xaune ne acan wani b'angare a jihar maidugurin cikin d'aya daga cikin tanfatsetsen gidan na shehurin(shehun borno palace) a unguwar damboa road dake garin na maiduguri hakan yafaru ne tun wata matsala da tatab'a faruwa lokacin yareema Ngari(usman)ne kawai d'anta aduniya! **Awanni masu yawa ne suka kai yareema Aliyu hydar gidah Nigeria.. sannan suka d'aga xuwa garin maiduguri,suna xuwa airport motoci a tawaga sukaxo d'aukarsa ,kowacce mota d'auke da tambarin h_r_h SB ajikinta har guda biyar,ajere suke tafiya har shehuri(palace d'in sarkin borno)....! [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com _2_ ***Shehuri(shehun borno palace); convoy d'in motocin su yareema Hydar nashiga fadawa sukazo suka taso suka saka bayan babbar rigunansu suka kareshi suka shigar dashi cikin masarautar, agajiye yake lik'is ganin mai martaba na fada suna meeting da wazirinsa yasa kansa tsaye ya wuce cikin gidah part d'insu, yana xuwa ya xaro handkerchief d'insa yai hanxarin toshe hancinsa as usual parlor d'in anyi littering d'inshi da leftovers na abinci se robobin lemuka kala kala duk a barbaje ga kwalin aspen taba awajen kamr parlorn mahaukata,dogon tsaki yareema Hydar yaja ganin haryanxu step brother d'insa yareema babagana yananan da halinsa na k'axanta da shaye shaye... Compound yakoma na sashensu, a sukwane bayi/dogarai sukayo wajensa had'e da yin gurfane inda yake... "Gaisheka yareema Hydar d'an sarki jikan sarki,d'an g...."basu k'arasaba yareema Hydar ya tsayar dasu.. "Sarkin gidah inaso kazo da dakaran tsafta yanxu kuyi hanxarin gyaran sashenmu...." "Angama yareema Hydar kaga d'an sarki wanda xe gaji g..." Basu k'arasaba yai saurin d'aga masu hannu don inda sabo yasaba jin wannan kirarin... A sukwane suka kwasa aguje sukai cikin gidah b'angaren su Hydar.Gyara sukahau yiwa wajen seda suka gyarashi tatas sannan suka bar sashen,se asannan ya shiga cikin sashen nasu yai hanyar d'akinsa,tafkeken d'aki ne komai fari had'e da parlor aciki kujerun blue da kayan kallo,band'aki yashiga yai alwala yai wanka sannan yai sallah, yad'akko abin turaren wuta ya jona ya bulala turaren wuta tuni d'akin yahau k'amshi ,ba'a jimaba mai martaba yak'are meeting sannan yareema Hydar yaje suka gaisa har sukaci abinci tare sanin halin kishiyoyin uwar tasa ba bashi xasuyiba seda yad'an caccakuna yaci ba lefi dayake ba ma'abocin abinci bane sannan mai martaba yace yaje wajen sauran iyayen nasa ya gaishesu ... Sashen hajia gajiram yafara xuwa wacce itace uwargidah, kafin yashiga seda jakadiya tai masa iso Kamar wani bak'o,yashiga ko ajikinsa had'e da d'an tsugunnawa cikeda girmamawa cikin harshen kanuri yace; "Yayya inda dubdo?!(Ina yini yayya?!"yafad'a hakan cikeda ladabi.. Seda Hajja gajiram tacika ta batse kafin ta amsa da kyar kamar me ciwon magana; "Kelewa selai...(lapia Alhamdulillah)" tak'arashe maganar cikeda tsana tana kuma wurga masa harara ta k'asan idonta Bedamuba ya mik'e don yasan hakan xata faru inda Sabo yasaba ganin beyond hakama,sashen hajja yakolo yanufa itama ya gaidata same abinda tamai kenan, ko ajikinsa itama Haka ya mik'e yakoma sashensu,yana xuwa yaciro sim d'insa yasaka yai dialing number mahaifiyarsa hajia hajjagana ringing d'aya biyu tad'auka... "Salaam alykm Ammee inda dubdo?!" "Kelewa selai Hydar,kazo garine?!" Ammee tafad'i hakan cikin nutsuwa da dattako "Ehh Ammee" "Dafatan komi lapia de?!" "Lapia Lou Ammee,bamuyi magana da baban bade may be se xuwa da safe" "To baranem(barka de)Hydar, dafatan kaci abinci ?!"tace hakan with care saboda tasan halin kishiyoyin nata "Ehh ammee munci da baba.." "To shikenan Hydar kaje ka kwanta seda safe xamuyi magana" "Okay Ammee Allah tashemu lapia.." Katse wayan yai yakoma yakwanta akan gado had'e da lumshe idanuwansa,basma ce tafad'o masa arai,siririn tsaki yaja sanin alk'awarin dayai nakiranta, dialing number ta yai yasa a handsfree ringing d'aya be gama ba tad'auka sounding so happy tafara magana kafin ma ya kulata; "Sugar boo... "Taja boo din cikin sigar soyayya "Basma" shine abinda yace kawai "Kaxo lapia sugar boo?! Yasu baaba?!" "Komi qalau Alhamdulillah... It's kinda late here, so goodnyt" "Sleep tight boo boo,I love you beyo...."bata k'arasaba ya katse kiran had'e da jan duvet yarufe kansa saboda sanyi dagarin yai dakuma sanyin split dake d'akin daya k'ara sanyaya d'akin.. Cikeda takaici da naci irin na basma haka bacci yad'aukeshi.. Da asubah yareemah Aliyu Hydar yatashi daga bacci band'aki yafad'a yayo wanka had'e dayin alwala,bud'e akwatinsa yai yaxaro jallabiya fara k'al yasaka yafita cikin d'akin parlorn daxe sadaka da qofar fita yaga yareema babagana akwance a rigingine hannunsa rik'e da kwalbar guiness wine da alama yasha ta'isheshi se surutai yake shi kad'ai kamr zaucacce,cikeda takaici yareemah Aliyu Hydaryad'an fara doka kujerar da yareemah babagana yake; "Baa(Yaya)babss(Dayake haka sukece dashi),baa babss wake up, lokacin sallah yayi fa.." Babagana cikin matogagin giyar dayasha yafara magana; "Those boobs..inkaga yarinyar nan oh bouy kaya dey oooo..."babagana yafad'i hakan yana D'aga hannayensa sama yaname sake tuttulawa cikinsa giyar Dogon tsaki yareema Aliyu Hydar yaja had'e da ficewarsa zuwa masallacin fadar,cikeda takaicin halin yareemah babagana ashe yananan da xuwa club d'insa da harkar mata, bayan sunyi sallar asubah and'an tab'a karatu yareemah Aliyu Hydar yaraka mai martaba zuwa sashensa dayake har gari yayi haske wajajen bakwai,sake gurfane yai ahankali cikeda ladabi yasake gaishe da mahaifin nasa cikin harshen barbarci/kanuri; "Baba inda watu?"(Ina kwana baba?!) "Kelewa selai,ka tashi lapia Hydar ?!" "Eh babaa Alhamdulillah!" "To Masha Allah, jeka samu bacci Hydar xuwa wayewar gari xamuyi magana da kai dalilin dayasa nasa aka d'akko ka daga makaranta...." "Shikenan baaba,Allah ya kaymu anjiman"yafadi hakan cikeda ladabi da girmamawa "Allah yamaka albarka Hydar" "Ameen Ameen baba"sannan ya mik'e yatashi yafita..! Cikeda so da k'auna mai martaba yabi d'ansa da kallo,hak'ik'a duk cikin y'ay'ansa babu wanda yake masa ladabi da biyayya irinsa,tattausan murmushi mai martaba yasaki ahankali yasake furta ; "Allah yamaka albarka Hydar.....!" WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of expert and perfect writers) nanahafsat.wordpress.com 3 Kodah yareemah Aliyu Hydar yakoma sashensu haka yatarar da yareemah babagana inda yabarshi ,kwalbar guiness wine wulle a gefensa se munshari yake da alama yasha yayi tatul dashi,siririn tsaki Aliyu Hydar yaja had'e dashiga d'akinsa ya rufo k'ofar kan gadonsa yakarkad'e da addua had'e dacire jallabiyar dake jikinsa yakwanta bejimaba da yin addua ba bacci yad'aukeshi bashi yatashi ba se shad'aya saura kwata shima k'arar ringing d'in wayarsane yatasheshi.. 'Basma Oxford' shine sunan dake yawo akan screen d'in iPhone 7 d'insa,swiping yayi yad'auka had'e dasawa a handsfree fuskarsa a d'aure dagani yaji haushin kiran nata,cikeda zumud'i tace; "Hellurh sugar boo..,Hellurh boo boo.. Bab..." Bata k'arasaba yai saurin katseta "Basma ya akai ne?!" "Sugar boo nayi lefi dana kirakane??" Cikeda takaici yace; "Basma you cut my sleep when I needed it most" "Boo boo I missed u so damn much," Ajiyan xuciya yai yana mamakin basma,shide yasan ba sonta yakeba kawaide yana tausayintane yana kulata amma Ita takasa ganewa muryarta ce ta katse mashi tunanin zucin dayake; "Honestly I think bout you ol the time, in the morning at the night, and in the middle of the day ,it's you it's just always you" Tace hakan cikeda shagwab'a... Girgixa kai yayi kamar tana ganinsa; "Basma I just left yesterday..." "Sugar boo wallahi dagaske nake" Yad'an jima yana tunani kafin yace mata; "Wane statement ne last danai maki alokacin daxan taho?" Yar daria tayi kafin tace; "Kace I should focused on my studies" "Then meyasa bakiyiba??" "I always spent my time with u yareemah Hydar nd u knw right .. Kuma wallahy I tried my possible best but nakasa komi ,I always think of you" "Hmmm Lalle"shine abinda yareema Hydar yace kawai sannan yakatse kiran had'e da shutting wayar down.. Kodah basmah taga yareemah Aliyu Hydar yakatse Wayan bata damuba sema sake gyara kwanciyan ta datai, friend d'inta dake kusa da ita kusan age mate ne su biyun tace; "Babe kina bani mamaki wallahi..." Rolling eyes d'inta basma tai tanabin k'awar tata da kallo sannan tace; "Danayi me?!" "Kin mutu akan wani da be damu dakeba,haba babe this is so not u... Upon all the guys da suka mace akanki kirasa wanda xaki dying for se wannan guy d'in me kallon mutane Kamar kashi" Daria basma tayi kafin tace; "Duk abinda yayi karkiga lefinsa, lefina xaki gani beside he's a prince .. Candy boo ingaya maki bantab'a son wani d'a namiji aduniya ba kamar Aliyu Hydar d'ina shine _Son_Rai na_"tak'arashe maganar tana lumshe ido "Bangane prince ba,kina nufin kicemin d'an sarki ne?!" "A finals d'insa yake... Yana karatun petrochemical engineering,Idan Kinga yadda babes ke rushing akansa xaki mamaki" "Osheey dole yai haka,Kinsan jinin sarauta,k'asaita ajikinsu take,kumafa seda kika fad'a na lura har wani xama yake irin nasu na masu sarauta xaki gansu a kishingid'e.. Kice kinkusa xama sarauniya"tak'arashe xancen tana daria.. "I pray so.. Gimbiya basma matar yareemah Aliyu Hydar how ds it sound?!" "Cool.. Allah ya tabbatar da alkhairi babe.." "Ameen candy boo,shiyasa na matsu yadawo naji kiranme babansa yake masa,don gaskia banason sharing d'insa da kowacce mace,ina kishin abuna" "Babe yace xe aureki ne?!" "K'arewarta ma cayai nice _Son_Ran sa_"basma tace hakan tana murmushi "Uhm uhm romantic couples kenan,Allah yasade har zuciyarsa"tace hakan tana mik'ewa tsaye "Layla(sunanta kenan)karki cemin komawa xaki yanxu bayan bahaka mukai deal ba" "Babe,akwai slaying yau,a Kentucky fried chicken (kfc)na wurin downtown abey hills and clubbing"tafad'i hakan tana wani girgixa jiki ... "Kice club xakije.." "Uhm can xani babe kema yaushe kika dena xuwa ?!beside romancing ne kawai babu wani abu daxamuyi bayan kisses and hugs ..."tace da basma hakan taname gogawa lips d'inta nude lipstick din Kylie a jikin mirror "Babe Allah ya shryeni yanxu .." "Hakade kikace,to nima Allah xe shryeni idan lokacina yaxo"Layla tabawa basma amsa tareda sakawa k'afafuwanta takalma samfarin boot!!! "Lalle shegs.. Who's the date ?!"basma tace da Layla "Wani guy ne me shegen kyau,a Cambridge muka had'u munje outing daganinshi kinga kanuri... Wlhy babe ko ina ajikin shi k'amshi yake ga kyau ga tsafta kamar me"tak'arasa xancen tana wani lumshe ido Da sauri basma ta mik'e tana murmushi ,Layla ta kalleta itama tana murmushin,kafin basma tayi magana Layla ta rigata ; "Babe kinsan shi ne?!" "No not at all,kintunomin da sugar boo d'ina ne,yareemah Aliyu Hydar wato ko company d'in designer na Calvin Klein bekai jikinsa k'amshi ba,kullum k'amshi yake ,apartment d'insa kullum da k'amshin turaren wuta (incense)da Kuma turaruka designers ke har turara kaya yake kamar amarya" "Oh my,, just like my baby,gidan k'amshi kenan" "Yo ai dole Aliyu yai k'amshi kinsan d'an sarkin borno ne kuma barebari ne" "Nima baby na nasan baxe wuce d'an can ba... Oh babe lokaci yana k'uremin na tafi mekikeso nataho miki dashi?!" "Cold Stone ice cream da cheese burger" "Alright then sena dawo..."Layla tace da basma hakan sannan tafuta daga d'akin nasu Ita kuma basma ta gyara kwanciyarta akan mini bed d'inta tana me sake kallon hotan yareeemah Aliyu Hydar dake baje akan screen d'in wayarta ya bud'a baki yana daria inda kyakkyawar wushiryarsa ta bayyana... __normal d'aki ne irin na college(university a state(outside country)kenan ,komi pink and purple ne har gadajen nasu k'wara biyu dayake basma da Laylan childhood friends ne tun a gidah Nigeria agarin nasu na kano,suka k'ara shakuwa tahanyar course mates da roommates dasuka xama... Komi atare sukeyi basa b'oyewa juna sirrikansu...! _Maiduguri_ Yareemah Aliyu Hydar na tashi daga bacci........ • 💡HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of expert and perfect writers) WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfect writers) nanahafsat.wordpress.com 5 Rungumesu yai shima yana jin son k'annen nasa na ratsa b'argon jikinsa, seda Affy da Aysa suka gaji da rungumar da sukai masa dan kansu sannan suka sake shi suna aika mashi da sak'on murmushi Daka gansu kasan yan uwan junane kamarsu d'aya sede Aysa tad'an fisu hasken fata Ita kuwa Affy kamarsu d'aya da Aliyu Hydar har kalar jikinsa kamar yayi kaki ya tofar..... Rik'e hannayensu yai atare suka shiga cikin gidah, lokacin da sukaje Ammi na sama tana wanka, haka su Affy suka tasashi suna zuba masa surutu dayake dama akwai su da labari,Affy k'aramar ciki shekararta goma sha biyu ita kuma Aysah shekararta sha shida... Ammi tad'an jima sannan tafuto sanye cikin dangasho blue anyi mata rigan bubu se k'aton mandil data yafa, kamarsu d'aya sak da Aliyu hydar sede ita tad'an manyanta kuma tafishi hasken fata, murmushi fal a fuskarta tafara sakkowa daga stairs d'in cikin parlorn tana magana cikeda nutsuwa; "A'ah Hydar kaine ka k'araso?!nide ince naji ihun su Affy sama sama"tak'arasa cikin parlorn had'e da xama a doguwar kujerar 3 sitter k'irar royal! Sakkowa Aliyu Hydar yai daga kan kujera yad'an durk'usa; "Ammi inda watu?? Ahh u belan amma tusen gei"( Ina kwana Ammi?! Eh nashigo amma ban dad'eba) "Okay to Allah yamaka albarka Aliyu sannu da zuwa" Sund'an jima suna hira,kafin daga bisani ma aikatan gidan had'e da dogarai da kuyangu d'aya bayan d'aya suka shigo suna d'aukar gaisuwa,nan aka jere varieties na abinci akan makeken dining table se k'amshi ke tashi, "Taso Hydar kaci abinci nasanka sarai dak'incin abinci kamar ba cikinka xaka kaiba,taso kaci" "To Ammi ,baa Ngari(usman)yatashi kuwa?,su Affy sunce yana bacci" "E likitansa be dad'e da barin gidan nanba yai mashi allura yasamu bacci" "Allah ya k'ara masa lapia" "Ameen ya mujeeb,zo ga abincin me xa'a zuba maka?! sokake kabagarar daxancen cin abincin nasanka sarai" "Ammi komi ma aka xuba" "Gashi akwai ingaji (brabusko),kimoniye(farfesun kayan ciki),indalayi,kisre ga miyan kub'ewa,yakuwa,peppered chicken se kunun gyada" "Abani kisre da kimoniye" "A'ah Hydar haryanxu kananan da rashin cin abincinka?!kisre kuma dabaya wani rik'e ciki Baride a k'ara maka da kunun ko?!" "To Ammi" Zuba masa abincin shidasu Affy tai seda sukaci suka k'oshi sannan su Affy suka tafi wajen malamin dake koya masu karatu a study room... sun d'an tab'a hira da Ammi sannan ya gyara xama a hankali a kuma nutse yace; "Ammi,munyi magana da baba d'axu" "To Allah yasa muji alkhairi Hydar"Ammi tace hakan getting more interested ... "E farko de yafara min magana akan ciwon lupus d'insa wai zeyi murabus thou nibansanme hakan ke nupi ba..sekuma ...,," Be k'arasaba Ammi tafara magana ; "Maganar lupus tabbas munyi dashi,saboda harta tab'a masa kidney ,k'arshen zuwanmu Germany ganin dr,dr d'in yace se anmasa dashen k'oda,kafin ayi dashen k'odar ma se anfaraiwa wajen remedy tukun" "To Ammi yanzu ni mexanyi anan ko?!" "Hydar mahaifinka yana nuna maka cewar kaine xaka gaji gadon sarautar " Seda gaban yareeemah Aliyu Hydar yafa'd'i murya na rawa yafara fad'in; "Ammi... Ba.. Ga..baa babss da baa Ngari(usman) ba" "Kaima Kasan usman baxe iya mulkar garin nanba ,tunda bashida lapiar jiki,shikuma babagana shiriritarsa

Chapter 1 of 35