Share this page
nanahafsat.wordpress.com This chappy is all urs dota *billy s fari*I love you beyond your wildest expectations love and endless amounts of blessing momma hearts you muchos.......! *51* *D*aga nan taro ya fara watsewa kamar yadda yareemah Aliyu hydar da Basma suka je a mota d'aya yanzu ma haka aka yi Modu indimi ne ke jansu yayin da layla ke gefen shi mamaki layla keyi ganin yadda Oud d'inta keta faman kakkauda kanshi tamkar baya son ya dinga ganinta,ji tayi kamar ta fasa ihu dan takaici sai dai ba yadda za tayi amma cikin ranta fal yake da d'inbin tambayoyi game dashi. A baya kuwa Basma ce ta lafe jikin yareemah Aliyu hydar shi kuma sai faman murza yatsunta yake jikin shi duk yayi sanyi domin ya hango lokacin da hajja gajiram ta dafe kai tana cizon lips har ta fita daga cikin taron shi kuma yasan farin ciki ne bata yi na jin cewar za'a bashi sarauta gobe sai kace duniya aka ce za'a bashi,d'an k'aramin tsaki yaja wanda bema san yafito fili ba sai da yaji Basmah ta d'an d'ago tare da kafeshi da idanuwa alamar sonjin k’arin bayani. Murmushi ya sakar mata tare da kuma maida kanta saitin chest d'in shi, har suka k'arasa cikin shehuri babu wanda yayi magana suna fitowa Modu yayi saurin shiga cikin abokan su yayin da layla jikinta yayi sanyi ta rab'a jikin Basma inda aka shigar dasu sashan Ammi, Suna zuwa aja janye Basma cikin bathroom aka shiga da ita wani ruwa ne a cikin jacuzzi da wasu fulawowi a ciki nan aka ce ta shiga tayi wanka, kamshin ruwan da dumin shi ya sanya Basma yin Bacci a ciki dama duk ta gaji ta sha wahalar zama, muryar wata mata taji hakan ya sanyata saurin tashi tayi wanka ta fito, cikin wani guri aka kuma sanya ta shima sai tada kamshi yake aka gama turareta kafin a fito da ita mai makeup aka sanya tayi mata sannan ta sanya bridal gown d'inta tayi masifar yin kyau jikinta sai kamshi yake tashi irin na turarukan Kanuri, farfesu Ammi ta bata wanda da kyar Basma ta iya sha sabida na magani ne ta shanye ruman daga nan aka wuce da ita wajan Maimartaba inda ya sanya mata albarka tare da yi mata nasiha sosai daga nan aka tafi apartment d'in hajja yakolo. Da kyar hajja yakolo ta samu ta seta nutsuwar zuciyarta kafin ta yiwa Basma 'yar nasihar da bataje zuciba daga na tana gamawa suka wuce na hajja gajiram,tararwa suka yi bata nan zama suka yi amma shiru shiru bata dawo ba suka tashi aka nufi katafaren apartment d'in sarkin gobe wato yareemah Aliyu hydar, abin sai dai ace Masha Allah domin tsayawa bada labari kauyanci ne kawai dai reader's kowacce ta kissima a cikin ranta, part biyu ne duk iri d'aya sai dai guda d'ayan ba'ayi mai paint ba na Meenah kenan kasan cewar ita ba alokacin zata tare ba an barshi ne sai gabannin zata tare itama. A can k’awayen amarya suka kwana kasan cewar al'adar sukenan, Meenah kuwa ciwon kanta be barta yin komai ba har washe gari, *Safiya ta gari* Misalin k'arfe 9:30pm aka yiwa yareemah Aliyu hydar nad'in sarautar sarkin BORNU,taron daya tara manyan masu muk'amin ciki da wajan Nigeria ciki kuwa harda shugaban k'asa me ci a lokacin (president), A gurin aka yiwa yareemah Aliyu hydar nad'in kamar yadda aka sabayi seda aka warware nakan mai martaba sannnan aka nad’awa Aliyu Hydar shi sannan governor ya sargafa mai sandar girma kawai sai ya saki kuka wanda ba zai iya cewa ga dalilin yin shi ba. A hankali ya juya yana kallon Mahaifinshi dake zaune sai faman murmushi yake mai yana jinjina kai alamar tabbatarwa,alama yayi mai da hannu cewar ya share hawayan ya dake karya bashi kunya yareemah Aliyu hydar ya goge sannan yayi k'asa da kanshi be sake d'agowa ba har aka kammala komai aka fara watsewa sannan shi kuma aka jashi zuwa wani extra room.... <><><><> A fusace hajja gajiram ta shiga cikin bedroom d'in yareemah babagana, zaune ta ganshi ya kifa kanshi a gefen bed d'inshi sai ajiyar zuciya yake saurin matsawa tayi wajan shi cike da tausayi ta d'auka shima rashin samun sarautar ne yasa shi kuka kanshi ta fara shafawa a hankali cikin sigar lallashi ita da tazo da masifa tace mai, “Duk laifinka ne babagana me yasa tun sanda nake binka akan kazo mu had'u ayi duk yadda za'ayi ka samu ka d'are kan kujerar mulki amma kak'i?sai yanzu da komai ya riga yazo k'arshe sannan zaka zauna kana yiwa mutane kuka” Shiru yareemah babagana yayi zuciyar shi tamkar zata fito yafi minti ashirin yanayi kafin ya d'ago ya kalli hajja gajiram; “Mami yazanyi?mami bata sona,bata son ganina kojin muryata na zame mata tamkar dodo me neman rayuwarta, idan ta ganni Mami guduwa take yi wallahi ina sonta idan ban aureta ba Mami mutuwa zanyi zaki rasani” Kuma fashewa yayi da kuka yayin da hankalin hajja gajiram yayi mugun tashi, kallon shi tayi cike da mamaki jin maganar dake fitowa daga bakin d'an nata da takeji dashi take kuma son farin cikin shi,hankalinta a mugun tashi tace mai, “Yareemah ban fahimci inda maganar ka ta nufa ba,kana nufin ba bak'in cikin rashin samun sarauta kake yi ba?!” Yareemah babagana ya kad'a kai alamar ehh sannan yaci gabada kuka, a hassale hajja gajiram ta ce, “Sakarai kawai dama mace ka zauna kana yiwa kuka? Wallahi ka bani kunya da mamaki kamarka kana yiwa mace kuka sai kace yaron da aka doka beson laifinshi ba,toh 'yar gidan waye me takeji dashi da har zata kalleka tace bata sonka harma yasa ka shigo d'aki kana kuka....?!” Kusa da ita ya koma ya zauna,hannunta ya kama ya damk'e cikin nashi kamar mutumin kirki yayi k'asa da kanshi, “Mami bilkisu,wallahi idan ban aureta ba toh kema rasani zaki yi,itace farin cikina,jin dad'i na walwala ta da duk wani motsina in fact Umma I can’t do with out Bilkisu” Mtwww hajja gajiram taja wani k'atan tsaki tamkar bakinta zai ciro cikin takaici ta mik'e tsaye tare da cewa, “Kaima baka santa tunda na tambaye ka 'yar gidan waye a garin nan ko ince cikin fad'in Nigeria amma kayi shiru sai wani cewa kake min Bilkisu,idan ka tashi sanar dani waye uban....” Bata k'arasa ba taji yace, “Mami wannan yarinyar cefa wadda kika...kika ganmu kwanaki anan d'akin.” A razane ta juyo tana mai wani mugun kallo,shima had'e rai yayi ganin zata kawo mai matsala,yadda taga yayi ne yasa ta sassauta fuskarta dan tasan zai iya sauke mata nashi rashin kunyar tace mai; “Kai yanzu babagana akan wannan watsatsiyar yarinyar zaka zauna kana kuka?!” “No Mami ba watsitsiya bace nine nan watsatse domin nina b'ata mata rayuwa, wallahi Mami idan baki sa’an nemomin auranta ba zan bar muku gidan ba zaku sake ga.....” Da sauri hajja gajiram ta rufe mai bakinshi tana faman share hawaye,ita kam tashiga uku daga wannan sai wannan yanzu komai babu nasara indai tayi sai ya lalace ko wani abun daban ya sameta ko wani nata, “Kace bata sonka bata son ganinka toh ya kake son ayi maka yareemah?!” Tashi yayi tsaye tare da yace, “Kizo muje gidan kiyi musu bayani nasan zasu yadda su aura min ita koda bata sona idan yaso in munyi aure zata soni daga baya.” “Toh naji zanje amma ka bari sai komai ya nutsu sannan sai muyi maganar.” Hajja gajiram ta fad'a tare da ficewa daga d'akin dan karma ya kuma yi mata magana. Komawa yayi ya zauna zuciyar shi na kara cusa mai kaunar Billy yana jin tamkar zai mutu saboda rashinta a kusa da shi,shi kam ya d'and'ano wa kanshi bala'i dan tun ranar da yayi raping d'inta be kuma samun nutsuwa ba. <><><><><> Yareemah Aliyu hydar kuwa bayan ya d'an huta aka wuce da shi cikin gida tsakanin shi da Modu sai dai kallo daga nesa kasan cewar manyan mutane ne ke rik'e dashi,a harabar gidan aka tsaya nan fa yaran gida da jikoki harma da tattab'a kunne duk suka fito anata taya yareemah Aliyu hydar murna, Ammi kam kasa fitowa tayi sai tayi alwala ta fara nafila tana yiwa d'annata addu'a da fatan alkairi ya kareshi duk sharrin mutum da aljan gabas da yamma kudu da Arewa, Kutsawa kawai take har saida ta samu ta ganta a tsakiyar su,hannushi ta rik'e tana girgiza shi alamun ya kalleta a hankali yakai idanunshi kanta yayi saurin zare idanuwa yana kallonta.Murmushi tayi mai sai d'age kafa take tana son yin magana a kunnanshi, “Wallahi kayi kyau ban ganeka ba sai da gid'ad'o ya nuna minkai...” Kalle kalle yareemah Aliyu hydar ya fara yi a hankali dan mulkin ya k'ara karfi sarautar ta fara aiki kokarin zame hannunshi yayi daga nata amma ta damke sai dashare mai hakora take,yakaka ce ta fara ganinta taje ta shunowa aunty yafendo gabaki d'aya mamaki ya rufesu yayan ta Ahmad suka hango aka gaya mai alama yashiga ya fito da ita aunty yafendo tayi apartment d'in Ammi da ita, “Sakarai kawai kefa yanzu ba yarinya bace kin zama matar shi amma kike wannan sakarcin daga samun lafiyarki." Yakaka ta fad'a cikin k’uluwa bayan sun shiga cikin bedroom,kallonta kawai aunty yafendo tayi ganin sai k’unk’uni take tasa aka nemo mata su Affy da Aysa ta had'a su tare sannan tace karsu fito sai an gama komai, Wajan k'arfe 10:00pm aka yiwa yareemah Aliyu hydar rakiya zuwa apartment d'in su,daga bakin k'ofa abokan shi suka tsaya Modu ya rab'a dai-dai setin kunnan shi yace, “Mr arrogant!Yau girma biyu ya hau wuyanka,idan ka shiga ciki ka ajiye duk wani abu ka rungumi matarka idan ka fito sai ka maida rigar sarautar ka dan mata ba'a yi musu mulki a cikin gida,ka more kafin zuwan Meenah” Modu na fad'a ya juya da sauri yana mai dariya har da 'yar kwallah ya share saboda gani yake kamar sun rabu,shi kuwa yareemah Aliyu hydar lumshe idanuwa yayi sannan ya doshi cikin parlon wanda keta tashin k'amshi tamkar anyi b'arin turaruka, a center corridor ya tsaya dan besan inda zai nufa ba kasancewar besan yadda tsarin gidan yake ba,upstairs ya nufa kai tsaye ya shiga wani d'aki yana b'ud'ewa ya hangi Basma zaune a tsakiyar gado an rufeta da wata tsadaddiyar alkyabba mai matukar kyau, Samun kansa yai dabin d’akin da kallo sosai d’akin yayi masa kyau k’atotan d’akine d’auke da italian royal bed dayaji zanin gado na alfarma ga pillows kusan ashirin ajere akan gadon hardasu rumfa gadon yake dashi purple and white komi na d’akin harta sofas k’wara biyu dake gefe da gefen d’akin babu abinda d’akin bejiba ciki harda kayan kallo bana k’aramin kud’i ba, Sallama yasa kyayi akaro na biyu tacikin lullub’i Basma ta amsa a sanyaye jinta amsa yasashi fita daga d’akin Basma kwa cikin zuciyarta se kwararo du’ai take na Allah yasa ba fushi yaiba dontasan halinsa me wuyar fassaruwane,yana fita yashiga d’akin kusada nata komi na d’akin cream and blue ne yayi kyau ba k’arya kayan jikinsa yarage yashiga wanka yafito yasaka pajamas d’insa bayan yabi kowane lungu da sak’o na jikinsa yafeshe da turaruka mild, Harya d’akko waya xe fara dannawa seya tuno yabar y’ar mutane kilan kuma bataci abinci ba gashi dare yayi,k’asa yasauka kan doguwar kujera yaga ledoji na kayan k’walam da mak’ulashe da alama Modu ne yakawo hamdalah yai had’e da d’akko plate da cup yahaura sama d’akin Basma tana nan inda yabarta cikin daddad’ar muryar shi yai sallama had’e da janyo table d’in dake tsakiyar sofa yadawo dashi kusada Basma kayan k’walam da mak’ulashe ya zuzzuba akan plate d’in had’e da tsiyaya mata lemo yatura mata gabanta bayan yasa hannu yayaye alkyabbar data rufe mata kanta cikeda kunya tad’ako tana dubansa sekuma tasake maida kanta k’asa wai ita a dole kunyar amarci, “Woww....!” Ya fad'a cikin sanyin shi bayan ya d'aga alkyabbar fuskarta ta bayyana tasha makeup,sunkuyar dakai ta kuma yi tana murmushi k'asa-k'asa a hankali ya matsa kusa da ita har suna gugar kafad'an su sarki Aliyu hydar ya bud'e ledan ya ciro fresh milk sannan ya bud'e bank'ararun kajin yana jin kamshin yayi murmushi dan ya gane aikin Ammi ne, cup 2 yayi musu na fresh milk d'in ya mik'a mata,hannu tasa ta karb'a yabi nallenta da kallo yana jin wani abu na yawo cikin jikin shi wanda be son ko menene shi ba, Basu ci da yawa ba ya saukar da kayan daga kan gadon sannan ya saci kallonta, so yake yace mata tayo alwala amma ya kasa wata irin kunya yakeji gani yake kamar zata fassara shi,dakyar sarki Aliyu hydar ya kawar da kai sannan yace mata, “Ammh jeki alwala muyi sallah dan mu gode mai mu nuna mai farin cikin mu...” Sakkowa Basma tayi daga kan gadon bayan ta cire alkyabbar jikinta ta tattare doguwar rigar jikinta tayi hanyar da take tunanin toilet ne,da kallo yabi bayanta idanuwansa suka dira a wajan hips d'inta nan da nan yaji fad'uwar gaba tare da d'auke kai daga kallonta.Tashi yayi yafita shima yayo alwalar sannan ya dawo inda take, pray mat ya shimfid'a musu sannan ya shiga yajasu jam'i suka yi raka'a biyu kamar yadda annabi (s.a.w) ya koyar da al'ummar musulmai ya dad'e yana addu'o'i wanda har sai da Basma ta fara jin bacci sannan ya juyo yana kallonta; “Kije ki kwanta nima zuwa zanyi na kwanta duk na gaji sosai...” A d'an razane Basma ta ware idanuwa kafin tace, “Sugar boo a ina zan kwanta?!” Da mamaki yake bin fuskar ta da kallo yace mata, “Anan d'akin mana me yasa kike tambaya ta kuma?!” Kamar Basma zata yi kuka cikin nuna alamun tsoro tace mai, “Ni dai gaskiya tsoro nake ji muje ka rakani wajan su Ammi na kwana acan baxan iya kwana ni d'aya anan ba....” Sarki Aliyu hydar ya shafa quarter million d'inshi dake kwance luf-luf a kyakkyawar fuskar shi, ya za'ayi ya barta taje wajan su Ammi bazai yiwu ba dan haka ya kuma kallonta, “Kije kiyi bacci ai nima anan zan kwana.” Murmushi tayi yadda bazai gani ba sannan ta k'arasa wajan da kayanta suke wata sleeping dress ta gani mai matukar yauk'i red color, sanyawa tayi sannan ta haye gado idanuwanta cike da bacci tun tana jiran taganshi ya hau har ta fara damuwa shi kuwa kunya ce fal cikin zuciyar shi be ma san ta ina zai fara ba dan haka ya dad'e zaune sai yayi kamar ya bugawa Modu waya sai ya fasa dan yana gudun raini a wajan Modun, Da kyar ya koma gadon ya kwanta yana jiyo daddad'an kamshinta a cikin sand'a ya mik'a hannunshi jikinta ya rungumeta lokaci d'aya yaji ta sakar mai jiki hannunshi yakai setin na shanunta ba tare da ya fargaba, tun a sannan Sarki Aliyu hydar ya fara aikawa Basma zafafan sakwanni wanda be ma son yana yiba bare ya tambayi kanshi a ina ya koya _*ni miss xoxo nace a movies_*ranar sai da Aliyu hydar yasan lallai shima ashe lafiyayyan namijine kamar kowa sabon sarki sabon aure sabuwar rayuwa, Sunjima suna raya daren alkhairi kafin daga bisani mai martaba Aliyu Hydar ya farga daga aika aikan dayayi a d’ari yatashi a kunyace ya sunkuceta se bathroom yatemakamata ta tsaftace jikinta,atare sukai wankan tsarki sannan suka canxa duvet ranar baisamu fita masallaci ba don narke masa Basma tai tana shagwab’a shikuma sai sanya mata albarka yake atare yajasu sukai sallar asubah sannan suka koma baccin gajiya basu suka tashiba se wajen goma shima wayar Basma ce ta tatashesu da kuka, Cikin sauri ya k’arasa shirinsa yasauka k’asa itakuma Basma tafad’a band’aki don shiryawa tare sukai having breakfast sannan sarki Aliyu Hydar yafita xuwa sashen babansu wato mai martaba mai murabus shamakinsa yana take masa baya gefe da gefansa kuwa dogaransa ne dake tsare shi, “Hello babe,shegs to ya ranki kede k’araso kawai wallahi yafice tun d’axu” Basma nagama wayar ta ajiyeta agefe sannan tacigaba da murxa d’aurin d’ankwalinta wanda ake kirada indimi style sanye take cikin atamfa daviva purple color me design bak’i tasha d’inki kuma ya amshi k’irar jikinta ba lefi riga da skirt ne samfarin d’inkin Senegalese yayi kyau k’warai,bin jikinta tai da turaruka sannan tagoga jan baki tanayi tana murmushi ita kad’ai kome take tunawa oho, Jin k’arar door bell yasanyata tashi tasauka k’asa tana murmushi sanin layla ce saboda dama da ita tagama waya yanzu tana bud’e mata sukai hugging juna, “Uhm Uhm amarsu kenan kinji wani k’amshi dake tashi ajikinki kuma de wannan ba k’amshin ki bane” Cewar layla tana d’agewa Basma gira d’aya, #SRKZBI?! _*Zuwaga masoya makaranta wannan littafi kwana biyu banyi posting ba hakan yafaru ne sanadiyar bikin k’anwata da akai dakuma wani uzuri nawa nadaban damasu kirana damasu mun text Alhamdulillah lapiata qalau lokacine kawai da bansamuba Nagaisheku gaisuwa mai k’ima Allah ubangiji yabarmu tare Nagode k’warai da kulawarku#AnaTare💖_* WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE* 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 *Home of expert and perfect writers* DEVOTED TO: *XARAH BUKHAR* TUKWICI: *TAWAN(Billyn Abdul)&MY YA HAJJA CE* PARTICULAR THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DOTAS: *BITTI FEEDHOM&DOTA BILLY S FARI* nanahafsat.wordpress.com *50* This page is urs my very own bitti I love you beyond your wildest expectations dota *feedhom*,you are truly one of the most amazing people I knw. momma loves and cares for you more than just to the moon round and back,May you be forever blessed dota....! <><><><><> *“K*ankine ke ciwo?!” Aunty yafendo ta tambayeta fuskarta d’auke da damuwa. Gyad’a kai kawai Meenah tai ahankali batare da tace komaiba, “Sannu barin samo maki pain reliever kisha insha Allah xeyi sauk’i kinji” Tana gama magana ta mik’e da hanxari tafita,ita kuma meenah takoma ta kwanta tacigaba da jan kukanta ahankali, Aunty yafendo nafita ta nupi sashen aunty maijiddah kasancewar anan first aid box yake xaune aunty maijiddan take baibaye da yan uwa anata karakainan hidimar biki dukkoda ba wani taron biki akeba kasancewar ance ba yanzu xa’ai events d’in bikinba harse tak’are secondary tukun,d’aurin aure kawai akai amma dayake mai Alooma Ghajin da iyalinsa masu hidimane shiysa gidan yacika mak’il da mutane ciki harda yan gayyar sod’i da sukazo kwasar wara... Aunty yafendo tana cikin duba magungunan khadija wadda suke kira da yakaka babbar ‘yar Aunty maijiddah a mata tashigo d’an corridorn da aunty yafendo ke duk’e tana karanta prescription d’in maganin,hannun khadijan d’auke da serving plates da folks akai, “Aunty kinga ga abokanan ango can suna jira wai sunason sud’au hotuna da Amarya ko kinsan ja’irar yarinyar nan an karad’e gidannan tsaf ba’a gantaba” Yakaka tak’arashe zancen tana k’wafa alamar inta ganta seta faffasa mata baki, d’agowa Aunty yafendon tai hannunta d’auke da magunguna na pain killers, “To meenah de ba inda taje da kinduba d’akinta ma tana ciki baiwar Allah ma batada lapia yanzu haka magungunan daki kaga ita xan kaiwa taxama feverish wlhy kanta yanata sara mata, Bakiji jikintaba yad’au zafi ko magana batayi kuma Kema kinsan ciwon daxe hana meenah magana ba k’arami bane” Cewar Aunty yafendo sannan tai gaba batare da tajira cewar yakaka ba da sauri yakakan tabi bayanta, “To aunty yaxanyi da abokanan angon?!” “Yakwa xaki,kinsande baxan bari haka kawai yarinya ba lapia tafito ba ko?! Ai anyi me wuyar tunda and’aura insunsa hak’uri ma yau zamu tattarata mu mik’a musu” “Kai aunty bakison lefin ja’irar yarinyar nan” “To ai gaskiyane khadija yanzu de aiba wani abun taiba batada lapia kuma de ciwo yasan gidan kowa ko shi Aliyun ne baida lapia ai baxa’a takura masa ba ko?!” Itade khadija daria tai kawai ita kuma aunty yafendo tai sashenta hankalinta duk atashe cikeda sassarfa take amsa masu tsaida ita suna mata Allah yasanya alkhairi harta isa sashenta da hanxari taciro gorar ruwa a carton d’insa tahaura sama d’akin meenah tana kwance kamar yadda tabarta har yanxun hawaye basu dena tsiyaya daga idanuwanta ba, “Sannu meeno nah tashi kisha maganin kinji?!” Tace hakan tareda temakawa meenan tatashi xaune daga kwancen datake,ahankali tab’allo magungunan tabata tasha sannan tace karta kwanta tukun tabari yai diluting, Bata jimaba da kwanciya bacci yad’auketa ganin haka yasanya Aunty yafendon tashi tafita daga d’akin had’e da rufo mata k’ofar tana sauka k’asa ango da groomsmen ne suka shigo kowannensu cikin babbar riga sunyi masifar kyau gefe d’aya kuma George okoro ne da maigaskiya photographers kowannensu yatsaya hannunsa d’auke da camera d’insa, Gaishe da Aunty Yafendo suka shiga yi ciki harda yareemah Aliyu Hydar dake d’an kalle kallen gefe gefe cikin zuciyarsa kuwa ba addu’ar dayake zabgawa seta Allah yasa kada trouble maker d’innan taxo ta b’ata moment d’innan don yak’i jinin guys d’insa su ga jaririyar da aka d’aura masa aure da ita, Ganin shiru ba Meenah ba alamarta yasanya Modu yin karaf yatambayi Aunty Yafendo had’e da juya kansa gefe dan karma Yareemah Aliyu Hydar yai interrupting d’insa, “Aunty ina Amaryarmu?!” “Wallahi tana d’aki ba lapia sakkowata kenan nabata magani tasha bacci yad’auketa kuka shigo” Wayyo kamar yazuba ruwa a k’asan terrazzo d’in dake parlorn yasha haka yaji wani mugun dad’i ya baibaye zuciyarsa bawai don batada lapia yake murna ba a’a don kada taxo ta kwafsa mai agaban guys d’insa, “Allah yabata lapia” Modu da yareemah Aliyu Hydar suka fad’i haka atare,sauran abokanan angonma sukai mata adduar Allah ya k’ara sauk’i, Main parlorn suka koma aka shiga d’aukar hotuna dasu Aunty yafendo da Aunty maijiddah da sauran ‘yan gidan sannan sukai masu sallama suka koma yerwa ciki hardasu gid’ad’o da sauran mazan gidan su Aunty yafendo sukai masu addu’ar Allah yasauke su lapia had’e da fad’in suma anjima kad’an zasu hau jirgi su iso, Duk wannan abinda ake har aka gama Meenah na bacci bata tashiba ganin lokaci yana k’urewa ne yasanya Aunty yafendo tashinta jin jikinta yayi sauk’i tahad’a mata ruwan zafi had’e da turarukha irin su bathing khumrah tasata tashiga band’aki tayo wanka, *KANO* *B*asma ce ke tsakiyar iyayen nata sunata mata fad’a had’e da jan kunne irin wanda iyaye sukewa ‘yayansu in xa’a kaisu gidan miji,sunkuye kanta yake a k’asa k’asan zuciyarta kuwa inbanda tunano yadda event d’in wushe wushe d’in daza’ai agidnsu Aliyu Hydar ba’abinda take muryar daddynta ta tsinkayo yana dukan dodon kunnenta, “Ina fatan kingane?! Kada ki wasa da addua domin addua makarin mumini ce ga duk wasu ababen cutarwa kama daga mutum ko aljan” “Nagane daddy insha Allah zan zamo kamar yadda kace” “To Allah yamiki albarka,Allah ya albarkaci gidan aurenki ku xauna keda abokiyar zamanki cikin lumana da mutunta juna, Kingade yar uwarsa ce koba aure akwai jinin ‘yanuwantaka a tsakaninsu kada kishiga abinda ba’asada ke ba yinayi bari nabari” “Insha Allah” Basma tafad’a kanta a k’asa tana wasa da zoben gold din hannunta sanye take cikin ubansu French lace peach yasha stones na baby blue tasa komi blue ba k’aramin kyau tayiba,haka iyayen nata suka gama ja mata kunne sannan ‘yan d’aukar amarya sukazo jirgi d’aya aka warewa dangin Amarya daga kano zuwa yerwa ba lefi tad’anyi kuka na rabuwa da iyayenta sannan aka b’anb’areta daga jikin Ammanta aka shiga mota da ita akaja se airport jirgi yalula dasu zuwa yerwa, *Yerwa(shehuri)* K’atotan tent ne acikin masarautar me barazanar cinye mutum dubu ake decorating d’insa da gold and black color kowane table me cin kujeru biyar ne babu abinda babu akan table d’in na decoration gefe d’aya kuma masu abincine aka d’akko su musanman dan occasion d’in kowane kalar abinci na al’ada an tanadeshi agurin, Bugu da k’ari kuma serve ur self ne banda k’amshi na aroma da scent na turaren wuta ba abinda ke tashi a tent d’in wurin dama anyishine saboda babban taro na bukukuwan masarautar kode wani babban taron daya shafi shehurin, Cikin lokaci k’alilan aka d’akkosu Basma daga airport xuwa shehurin taraina kanta k’warai matuka ganin shehurin was beyond her expectation ba ita kad’ai ba har sauran friends d’inta su goma da ‘yan uwanta da suka rakota tare sunyi mamakin masarautar sun rena kansu, Shisshiga akaida Basma wajensu hajja gajiram tagaishesu sannan aka wuce da ita b’angaren Ammi kasancewar anan za’a shiryata don lokacin da akasa za’ai wushe wushen ya gabato da sauri akai mata kela tul kamar yadda al’adar kanurin take kafin ayi wushe wushe se

Chapter 13 of 35