kai Aliyu yace,
“Amin baba..Nine da godia nagode kwarai Allah ya kara maka lapia da nisan kwana”
Godia umma takara yi masu sosai don dama abinda takeson ji kenan ko kadan batason Aliyun ya rabu da Basma se gashi addu’onta sun karb’u Aliyun yadawo da Basma dakin aurenta...
Sallama ta masu sannan tafice fuskarta d’auke da murna tabarsu Aliyu da mahaifinsa suna d’an taba hirarsu..Tana fita takira Basma tamata albishir k’arar da Basma ta saki ta murna har seda umma tacire wayar daga kunnenta domin k’arar kamar xata faso dodon kunnenta,taji dadi ba kadan ba takuma godewa umman akan namijin k’ok’arin datai mata domin abbanta cayai baxe iya tunkarar mahaifin Aliyun da wannan abun kunya ba don aganinsa abunda Basman tai saki uku ta cancanta ba d’aya ba aranar da ummah ke gaya masa matsalar da Basman ta samu da mijinta fada yahau su dashi duka su biyun bayan ya shararawa Basman mari sau biyu a kuncinanta tareda hargagin kai mata duka,se gashi an kaiwa umman invitation cards na biki to ta haka tasamu damar da har tai tattaki xuwa bornun tai magana da mai martaba mai murabus...
***
Da asubar fari hajja gajiram da yakolo sukai asubancin tafiya wani kauye acancikin kauyen gombole dan motar da suka tafi kauyen ma tasha aka d’akko masu ita bata gidah suka dauka ba...
K’it hajja gajiram ta katse kiran data gama amsawa tare da dubar yakolo dake bin dokar dajin dasuke luluk’awa da kallo,
“Tace nanne wai kwanar Farko datai hagu xamubi”
“To yayya..”cewar yakolo
Sannu ahankali suna k’arasa har cikin kasurgumin dajin Allan daba kajin komi se kukan tsuntsaye,wata katuwar bukka ce a tsakiyar dajin da aka xagayeta da bakaken karare cikin sauri suka k’arasa cikin bukkar wata razanniyar kara bokan yasaki dake jeme agefe jikinsa duk layoyi gabansa kuwa wata katuwar tukunya ce dake tafarfasa ita kad’ai batare da temakon garwashi ko ice na wuta ba,
“Ku shigo ta baya sannan ba a mana sallama domin bama bukatarta anan wajen...”
Yawun tsoro dukkanninsu suka hadiye sannan suka fita suka shigo tabaya batare da sun sakeyin sallama ba kallon su bokan yai cikin isa yace,
“Kowannen ku yacire d’ankwalin kansa..Sannan nan gaba idan xaku xo kada wanda yasake xuwa da irin wannan kayan da kuka saka ajikin ku bakin kaya kawai xaku dinga sawa duk sanda xaku xo sannan tunda ga bakin bukkar xaku cire dankwalayen kanku Ina fatan kun gane?!”
“Mungane boka”
Y’ar daria yai kafin yace,
“Sunana boka shaharuzzaman d’an sarkin bokayen dake duniya wato faharuzzaman nasan meke tafe daku tun kafin isowarku”
Kad’a kai sukai kamar kadangaru amma kowannensu da irin tsoran dake cikinsa duba da irin wani marayen kuka dake tashi shi kad’ai batare da kaga wanene ke yinsa ba..
“Abunda kuke tafe dashi abune mai sauk’i wanda inde kuncika kaidar abun xakuga aikinsa acikin kwana d’aya da yini kacal shin yaya xaku iya ko kuwa ?!saboda da xarar kun yadda tofa ba makawa se kunyi shi”
Saurin kad’a kai hajja gajiram tai alamar sun yarda cikeda zumudi kamar tasan menene tace,
“Eh boka..Zamuyi”
“To shikenan keda kika amsa ke xaki yi..”
Tashi yayi ya d’akko wata Bakar leda da kullun laya acikin ta se wani garin magani shima davan ya Mika mata,
“Ungo nan Wannan abun karka ki wasa dashi idan xeyiwu adaren yau xakiyi shi kuma kada ki kuskura aganki kinayi ko asan Kin aikata idan har ba’a ganiba kikai komai kamar yarda nace to ina me tabbatar maki da cewa adaren zuriyar hajjagana seta lalace ta ta’axxara sesun shiga cikin ha’ulai ke sarki Aliyun ma kurciya xeyi ita kuwa matar tasa xamu gusar mata da hankaline gaba d’aya shikwa dayan marar lapiar xamu raba shi da iska matan kuwa guda biyu xasu shiga duniya suyi karuwanci amma duk wannan bayanin dana miki sefa har in kin aikata aikin nan dede,
“Amma idan har kika kuskura aikinnan ya baci to ina me tabbatar maki da cewa kome xe iya faruwa akanki da kuma yayan ki baki d’aya... da farko de wannan laya xaki binne tane da dubura a tsakar farfajiyar gidan sarki Aliyun kuma babu kaya ajikin ki xaki,wannan garin magani kuwa xaki barbada akan layarne bayan kin bunne ta sannan sauran ki xuba a’abincin mijin naki wato shi mai martaba mai murabus kenan ki tabbatar yaci abincin babu basmala na uku kuma daga yanzu xaki dena duk wata salla da adduoin neman kariya har se kingama aikin naki kin dawo nan naji sakamako tukun,Ina me tabbatar maki da cewa da xarar komi yayi shima mijin naki yaci abincin da garin maganin nan to kisa aranki ko cakikai mijin naki ya sunkuya ya miki sujjada xeyi domin gaba d’aya komai nasa a tafin hannun ki yake..”
Gaba d’aya hajja gajiram da yakolo mutum mutumi suka xama kawai suna duban bokan ita kuwa gajiram jinta da ganinta tanema tarasa na yan wasu lokuta,cikin zuciyarsa kuwa dana sanin xuwa take ta yaya ma xata aikata wa’innan abubuwan batare da an ganota ba gashi tarigada ta amince xatayi nanma idan batayin ba to fa reverse is d case,muryar bokan ce tasake dawo mata da jin nata,
“Ina fatan kingane komai”
“Nagane boka sede...”
Saurin katse yai,
“Tur tur da halin ki yake muguwa haihuwar asara,shaharuzzaman baya magana biyu,bana gindaya sharudda ayi watsi dasu dole ne sekinyi su idan kuma baki yiba tofa duk abinda yasa meki ked’in ce kika jawa kanki..”
Da sauri hajja gajiram tai gurfane baki na rawa tana bashi hak’uri dakyar ya hak’ura sannan yadubi yakolo da jikinta ke rawa gudan karfa itama yabata irin nata aikwa bata gama xancen zucin data keba ya mika mata wata leda hannu na kakkarwa ta karba,
“Wannan can gidan kishiyar taki xakije wato hajjagana mahaifiyar sarki Aliyu kixuba a farfajiyar gidan sannan kije sashen yareemah Ngari ki xuba a makoncinsa ma’ana akan abinda yake kwana..”
Salati yakolo ta saki tana tafa hannuwa kafin tafadi abinda xata ce boka ya lailayo ashar ya dura mata cikin takaici yace,
“Ta kwarankwatsa sekinyi asararriya kawai yau ga xancen wofi karki bari shaharuzzaman yanuna maki gaskiyar fuskarsa da wallahi ba xaki koma shehuri lapia ba fyace an binne gawar ki a dajin nan”tsaki yasaki sannan ya jefa mata ledar maganin
“Ku tashi ku tafi”
“Boka kudin aikin ka fa”cewar gajiram jiki na rawa
“Bana bukata harse aiki yaci,amma ga wata tukunya can a gefan bishiyar can kowannenku yai fitsari aciki kafin yafita amma kada ku kuskura kuyi tsarki har sekun bar dajin nan sannan kudawo jibi idan kun gabatar da komi”
“Toh boka angama”cewar gajiram
Hakan kuwa sukayi kowannensu yai fitsari cikin tukunyar babu batun tsarki suka fice suka hau mota suka kama hanyar cikin gari har suka tafi babu wanda yai magana cikinsu kowanne tsoro ne cunkushe a cikin zuciyarsa gaba d’aya kallo d’aya xakai masu kasan basa cikin hayyacinsu kai dama tunaninsu..
(To Allah ya kara tsare mana imanin mu yasa mu ketare duk wata hanya da xata sa mu sab’i ubangijin mu...Rabbi ka kara mana tawakkul acikin zukatanmu katsare mu da zuri’armu baki d’aya Amiin..Domin duk wanda ya had’a Allah da waninsa Wannan shirka ce,Rabbi kasa mufi k’arfin xukatanmu domin abinda ke faruwa a zamanin yanzu kenan)
*Modu’s*
Zaune yake shida kiara a gefan sa hannunsa d’auke da iPad d’insa suna kallon film din the message aciki har a kare sannan yadan gyara xaman kiara dake jikinsa yana shafa gashin kanta cikin harshen turanci yace da ita,
“Babe,nakai ki d’aki kamar bacci kike ji..”
Tashi tai daga jikinsa tana duban sa hannunta d’aya tana shafa kwantaccen gemun sa ahankali tace,
“Ba barci nake jiba honey pie,naji dadin film dinnnan sosai akwai film din nana Aisha da akai itama?!”
“No babu gaskia banajin akwai babe...”
“Inason sunanta Aisha...baxe yiwu adinga cemin Aisha ba saboda banason kiara dinnan”
Murmushi Modu yai hade da sake matseta jikinsa yana sumbatar goshinta kafin yace,
“Baxe yiwu ba babe sede idan harkin musulunta tukun seki xab’a sunan da kikeso adinga ce maki”
“Dagaske?!Well honey pie inason musulunta inaso inaso inaso yanxu plssssss kaji?!”
Dan murmushi Modu yai kafin ya tallabo bakinta yashiga sumbatarta yana Shafa ko’ina ajikinta dakyar yacire bakinsa daga nata sannan yace,
“Naji dadi kwarai babe,Allah ya miki albarka..Zan kaiki wajen baba ya musuluntar dake seki xabi sunan da kike so”
Ya k’arashe xancen hade da daukarta cak yatafi d’akinsa da ita seda yasami nutsuwa sannan ya kyaleta yana shafa gashin kanta hade da sumbatar goshinta lumshe idanuwa tai tana me jin dadin abinda yake mata,
“Honey pie inason xuwa wajen layla...”
“Uhm yan biyu kenan mexaki fada mata banaga jia ma taxo ba?!”
“Inason gaya mata xan musulunta ne ko na kyaleta?!”
“No kifada mata bari muyi wanka tukun se muje gaba d’aya”
Band’aki suka shiga suka tsafta ce jikin su sannan suka fito bayan Modu ya dauro alwala sallah yatayar yanayi ta nafila ita kuma kiara kamar kullum ta xabga tagumi tana kallon yadda yake sosai takeson taga itama tana sallah harta karatun alqur’ani don duk sanda takejin karatun alqur’ani setaji peace of mind atattare da ita.,
Koda ya idar atare suka shrya cikin kaya masu kyau shi Modu kananan kaya yasa ita kuwa kiara abaya tasaka harda nada dankwalinta kaika rantse baturiyar musulma ce sosai tayi kyau..
Ita tai driving dinsu har gidan layla sannan suka shiga ciki kowannensu murmushi d’auke a fuskarsa don zama ne suke yinsa cikin lumana da mutunta juna...
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_*👌🏼
[4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```Edited by```:
```Ya hajja ce```
```nanahafsat.wordpress.com```
*73*
*A* cikin kitchen suka jiyo motsin ta dan haka can kiara ta nufa da saurinta tana kiranta da,
“Sister where are you?!”
Da sauri layla ta ajiye knife d'in hannunta tare da juyawa tafita,kusan cin karo sukayi da juna gaba d'aya suka sakarwa juna murmushi kiara ta bud'e hannuwanta suka rungume juna suna dariya, a hankali kiaran ta kai hannunta saman cikin layla cikin gwarancin hausarta da ta fara iyawa yanzu tace,
“Sister yaya babyn mu hope yana mosi?!”
Da sauri Modu ya girgizawa laylan kai alamar tace a'a aikuwa layla tayi kalar tausayi da fuskarta kafin tace,
“A'a sister 4 day's kenan banjin komai am scared.”
Gaba d'aya hankalin kiara ya tashi ta rud'e tare da jan hannun layla ta fito da ita daga cikin kitchen d'in ta kamo na Modu ma tace,
“Let’s go to the hospital please ina son wannan baby muje aI check up .”
Dariya taji sunyi gaba d'aya hakan yasa tabisu da kallon mamaki kafin ta had'e rai,Modu ya zame hannunshi daga cikin nata sannan ya kamo kumatunta yana kallon cikin idanuwan ta yace,
“Sorry my dear lafiyan baby fine and good it was just a joke,we are kidding you m sorry”
Ya fad'a yana kuma yin dariyar,dukan wasa takai mai gaba d'aya suka dara sannan layla ta koma kitchen ta samo musu abin motsa baki ta dawo parlorn ta zauna suka ci gaba da hirar su tamkar ba kishiyoyi ba anan ne kuma kiara ta sanarwa da laylan cewar tana son musulinta layla tayi murna sosai harda hawaye dan dama abunda yake damun ranta kenan kin musulintar ta amma yanxun sai taji wani farin ciki tamkar yau ta haihu.
“Toh sai muje a sanar da baba ko honey?!”
“Yap abinda nace kenan nasan zasuyi murna sosai idan suka ji wannan zancen.”
“Sister ina son idan na yi musulma asa sunana Nanarh Aisha ina sonta sosai.”
“Alhamdulillah sister insha Allahu as you wished Allah yasa ki amfanar da addinin musulinci Allah kuma ya karb'i tubanki.”
“Amin.”
Cewar Modu daya karkatar da hulan kanshi kowaccen su kokarin faranta mishi takeyi shi kuma sai k'ara narkewa yake kamar wani k'aramin yaro.
*SHEHURI*
Kuka Meenah ta dingayi tamkar bazata bari ba,da kyar ta iya motsa hannunta tana laliban wayanta so take ta kirawo aunty yaruwaiya amma wayam babu ita a inda ta ajiyeta,hawaye na zubar mata ta mik'e da kyar tana ci gaba da neman wayan amma bataganta ba wayar kuwa kamar sarki Aliyu hydar ya sani ya d'auketa ya tafi ta ita bedroom d'inshi nan ta ci gaba dayin kukanta har wajan asuba sai a sannan ta mik'e da kyar ta wuce bathroom babu abinda yafi d'aga mata hankali irin jinin da ta gani ya fito mata sai ta kuma sakin kuka lokacin sarki Aliyu hydar ya shigo d'akin yana sanye cikin wata jallabiya mai masifar kyau.
K'arasawa yayi bak'in k'ofar bathroom d'in jin kukan da takeyi cikin muryarshi mai sanyi yace mata,
“Meenah bud'e min na shigo karki bari na kuma yin magana indai kin yadda cewar ni mijinki ne.”
Haushi da takaici suka cika zuciyar Meenah a hankali ta zare sakatar sannan ta b’uya bayan kofar,shiga yayi sannan ya kalli bathtub d'in da ta kunna famfo na zafi dana sanyi ya kuma maida kallonshi bayan k'ofar data b’uya daga ita sai towel ta cure hannuwanta a fuskarta ya kalleta yace,
“Oh wai har yanzu haushina kikeji?hakkinki ne na aure fa na baki ko sokike yi na fara sab'awa Allah daga zuwanki?!”
Meenah tayi mai shiru ta kuma ki bari su had'a idanuwa ganin haka yasa shi matsawa wajanta tare da sanya tausasan hannuwanshi ya janyota jikinshi ta kuma kankame jikinta saboda wani irin tsoranshi takeji ganin haka yasa shi d'aukarta daga ita har towel d'in ya tsilmiya cikin kwamin kwankan aikuwa ta saki wata razananniyar k'ara tare da kankame hannayanshi dama tuni towel d'in ya cire sarki Aliyu hydar yaki fito da ita daga ruwan har saida taji ta farajin dad'in ruwan sannan ta sakeshi da sauri tare da janyo towel d'in ta kara shi a jikinta.
Zama yayi a gefen bathtub d'in sannan ya sanya hannunshi cikin ruwan yafara d'iba yana zubawa a jikinta gaba d'aya jinta take a takure ga haushinshi gashi yazo ya hanata sakat muryarta a sark'e ta turo baki wanda ya zame mata jiki tace,
“Dan Allah ni kafita.”
Yiyayi tamkar bejita ba ta kuma kankamewa shidai ruwan yaci gaba da d'iba yana wanke mata bayanta dashi ganin sunab'atawa juna lokaci yasa shi mik'ewa tare da d'aukan bucket ya tari ruwa a cikinshi na zafi dana sanyi sannan yaje ya fitar da ruwan da take ciki a hankali yace mata,
“Kiyi sauri ki wankan tsarki zamuyi sallah.”
Duk da cewar tasan sallan asuba yake nufi amma duk da haka sai da kirjinta ya buga gani takeyi tamkar irin na jiya za'ayi da ta idar da sallah ya kuma yi mata abinda yayi,shi kuwa yana gama fad'a yafita ya koma kan sofa ya kwanta yana zaman jiranta,sai da ta dad'e a cikin bayin sannan ta fito ko kallanshi batayi ba tasa kayan da tagani akan gado wanda da alama shine ya d'akko mata Arabian gown ce golden color sai kyalli take da kamshi ta zura yana kallonta har ta kammala sannan ya koma bathroom din yayi alwala yazo yajasu jam'i.
Suna idarwa ta koma ta makure yanzu kam Meenah duk wannan bakin tsiwar sarki Aliyu hydar ya d'inketa babu ita sam, a hankali ya waigo yana kallonta kafin ya saki murmushi ya mik'a hannu zai janyota tayi saurin jan baya juyawa ya kuma yi yana murmushi tare da d'aga hannu yayi addu'a ya dade yana yi daga bisani ya shafa ya kuma waigowa sai ya tarar tana gyangyad'i ya mik'e tare da d'aukarta cak saboda ba tada wani kiba kamar ka doketa da bayan hannu ta fad'i k'asa wanwars,ai tanajin ya kaita gado tayi saurin mik'ewa tana zaro idanuwa tana bashi hakuri cikin kuka.
“Baah...Yaya...yallab'ai...rankaya dad'e dan..dan Allah karka kuma yimin komai wallahi kaji na rantse maka na dena yi maka duk abinda zai b'ata maka rai,wallahi hatta yawo babu d'ankwali baxaka sake ganin nayiba kayi hakuri kaji yayana sarki me adalci me tausayin Meenatu kanwarshi...!”
Sosai yaji ta bashi tausayi jin sumbatun da take tayi dan haka ya janyota yasa kanta a k'irjinshi yana d'an bubuga bayanta alamun rarrashi ita kuwa tayi lamo a jikinshi sun jima zaune shiru kafin a hankali ya kwantar da ita shima yabi bayanta ya kwanta a jikinta murya k'asa-k'asa yace,
“M sorry Meenah bazan miki alkawarin cewa na denaba domin wannan abun shine tushen auren sannan yanzu ke kad'ai gareni duk da cewar a daran jiya kafin na shigo nan na dawo da Basmah amma bansan ranar da zata dawo ba,infact ma dai ko ta dawo banajin zuciyata zata iya yarda da ita domin akwai abinda nakejin tsoro,please Meenah karki dinga guduna wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa ban bari wai sai kinyi wasu kwanaki a gidannan ba saboda nasan koba dad'e kobijima ked'in tawace koma dole sai nayi so kiyi hakuri kinji.”
Jikinta ne ya cigaba da yin rawa hakan yasa Sarki Aliyu hydar cewa,
“Kiyi kwanciyarki ni babu abinda zanyi miki yanzu.”
Sam kasa yadda tayi dashi ta kasa yin baccin duk kuwa da cewar tanaji amma tsoro da fargaba sun hanatayi,har kusan k'arfe 8:00am Meenah ta kasa koda kwakwaran motsi sai da taji ya tashi a hankali ya sumbaci goshinta sannan yafita daga d'akin ya koma nashi sannan ne Meenah ta sakko ta ruga da gudu tasawa kofar key ta koma kan gado tayi kwanciyarta.Tunani ta fad'a tana ta mamakin shi dan sam batayi tunanin zai iya yin wannan abunba koda kuwa a mafarkine lallai maza basu da kunya ta dinga ayyanawa da haka bacci b'arawo yayi awan gaba da ita.wajan misalin karfe 10:15am aka aiko musu da breakfast d'insu anan dining table ya gani lokacin shima fitowarshi kenan ya nufi bedroom d'in Meenah yana murd'awa yajishi a kulle ya san saboda shi ta kulle hakan yasa shi yin murmushi sannan ya koma parlor ya zauna yana duba wata jarida.
Sai misalin k'arfe 11:30am sannan Meenah ta farka kodata tashi ma kukan ta cigaba dayi ta dad'e tanayi kafin ta wuce bathroom tayi brush tana fitowa sama-sama ta dinga jiyo hayaniya a parlorn farko hakan yasa tayi saurin k'arasawa wajan mirrow ta shafa powder da lipstick ta kuma fesa turaruka a jikinta sannan ta bud'e k'ofar a hankali tayi hanyar da dake jiyo manar su yaya gumsu dasu aunty yaruwaiya su Aysa tana zuwa dai-dai matakala suka had'a idanuwa da gid'ad'o yana yi mata wani kollon rainin hankali ta juya suka had'a idanuwa da yayah gumsu taga tana kallon kafarta gaba d'aya sai ta tsargu cak kuma ta tsaya ta dena sakkowar da ta farayi,ji take kamar ta juya ko ta tsalar ihu amma sai taji zuciyarta tak'i yi mata ko guda d'aya shi kuwa gogwan ya wani maze fuskarshi baza ka tab'a gane cikin yanayin da take ba aunty yaruwaiya tace,
“A'a Meenahta a sakko mana ko bazaki iyaba na k'araso?!”
Tayi shiru still tana tsaye sai wasa take da ring d'in yatsanta, juyawa yayi a hankali yadda babu wanda zai gane ya kallota akayi sa'a itama lokacin tana kallon gurin sai ya lumshe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana turo baki,Aysa ce ta mik'e tana cewa.
“Ah aunty Meenah ko har kambunci sarauniya sun fara aiki ne?bari nazo na take miki baya.”
Aysa ta fad'a tana taka matakalar dad'an gudu tana zuwa ta riko hannunta suka sakko Meenahn sai faman had'e rai take yi.
“Ikon Allah Meenah wai ko mutashi mu fitane sai wani faman had'e fuska kikeyi?!”
Yayah gumsu ta fad'a tana harararta cikin rawar baki Meenah tace,
“A'a wallahi yayah kiyi hakuri nifa fad'owa nayi daga kan gado.”
Aka kwashe da dariya shi kuma sai ya kalleta da sauri a tunaninshi gaskene amma taki had'a idanu dashi gid'ad'o yace,
“Ikon Allah anji gado ba irin na house ba harda su fad'uwa.”
“Eh d'in banza kawai.”
Nanfa suka fara harsai da aunty yaruwaiya tayi magana sannan suka yi shiru,shi kam sarki Aliyu hydar tashi yayi ya basu gurin saboda sun isheshi da hayaniya..
Bayan Aliyu yabar parlorn aunty yaruwaiya ta dumamawa gidado dundu abaya ba shiri ya fice yana daria,jan hannun Meenah aunty yaruwaiya tai suka shiga wani daki dake kasan..
Suna shiga Aunty yaruwaiya taja hannun Meenan ta xaunar da ita a kusa da ita sannan tafara mata magana,
“Aminatu...”
“Na’am aunty.”
“Maganar mu ta jia karfa ki manta kidinga yi sosai xakiji k’arfin jikin ki bawai ruwan xafi ainun ba don shima idan yayi xafi da yawa yana illa sannan tsarkinma da ruwan xafi xaki nayi ki yawaita shan fruits sosai dan Allah aminatu su gaf gaf d’innan duk karki wasa dasu..”
Cikin k’asa da kai da kunyar data cika Meena na maganar da aunty yaruwaiya ke mata tace,
“Insha Allah aunty”
“Yawwa ta waje nah,haka ma duk sanda Aliyu ya neme ki a shimfidarsa karki guje masa duk koda nasan baxa kiyi hakan ba”
Tuno daren jia Meenah tai yadda Aliyun yadinga sarrafata kamar yasamu yartsana cikin zancen zucin da take ta sake jiyo muryar Aunty yaruwaiyan,
“Kinji Aminatu?!sannan duk abinda ya shige maki gaba ki kirani ki gayamun pls”
Kad’a kai kawai Meenah tai,ganin taki sakin jikinta yasanya aunty yaruwaiyan ce mata ta tashi su koma parlor nan suka tarar har ankawo masu abinci xubawa Meenan aunty yaruwaiyan tai seda ta tabbatar taci sannan ta xuba mata wani tace takaiwa Aliyun parlorn sa sannan sukai mata se anjima suka koma sashen su kancewar xasu dawo su mata sallama kafin su tafi tunda duk an soma watsewa sena gida gidah kawai..
Cikin cuno baki Meenah ta tura k’ofar parlorn sarki Aliyu Hydar tashiga bakinta d’auke da sallama kamshin split dana rasasin turaren jikinsa ne suka cukada suka bada wani irin kamshi me dan karen dadi amsawa yai batare daya dubeta ba xaune yake cikin royal chairs komi na parlorn Royal ne kalar golden and white hannunsa d’auke da remote yana rage volume din news da ake a bbc,
Cikeda yarinta tace,
“Gashi inji aunty yaruwaiya”
Dan murmushi yayi na jinjina irin yarintarta hade da bin warmers na abincin da kallo,kunsan mutumin naku idan kambun mulkin suka motsa,
“Zuba mun kad’an” ya fad’a cikin husky voice d’insa
Plate ta janyo tashiga xuba mashi duk abinda ke cikin flasks din doya ne da kwai da sauce na kayan ciki gefe d’aya kuma funkaso ne me xafi da yaji miyan taushe da kuma kunun gyada se kamshin kayan kamshi yake sosai parlorn ke tashin aroma na abinci,
Sakkowa Aliyu yai daga xaunen daya ke ya janyo plate din gabansa yanaci bayan yayi basmala se yatsina fuska yake se kace ba cikin sa xe kaiwa ba kallonsa Meenah tai hade da tab’e baki lokaci lokaci take saton kallonsa ta gefen ido,
Bayan ya dan cicci ba lefi ya rufe plate din hade da sipping kunun sau biyu sannan ya turashi gabanta cikin harshen kanuri yace d ita,
“Zimme gone yay(sakko ki dauka ki sha)”
Idanuwa ta zaro tana dubansa,
“Kob...”
Bata k’arasaba ya watsa mata wani kallo cikin muryarsa sanyayya shi aganinsa kamar fada yake mata yace,
“Kika sake kika fad’i kobah dinnan ba sena baki mari haba it’s so annoying zimme gone yay woko(nace ki dauka ki sha ko?!)
Ganin bada wasa yake ba yasanya Meenah daukar cup din takai bakinta har ga Allah batashan kunun gyada amma shi gani yake kamar karya take ko menene oho?!
“Uncultured kawai komi kice bakya sha ko bakya ci”
Bata kulashi ba tai kurba uku dakyar shima seda ta d’auke numfashinta tukun sannan ta ajiye hade da burning face don karma yace seta shanye daria ce ta taho masa ya gimtse kawai yana dubanta zulum ta mike tai dinning area ta wanke bakinta ganin baya kallonta yasa tafara sanda xata gudu ya kirawota,
“Zo nan ...from trouble maker to uncultured”
“Uhm de gwara ni definitely arrogant kawai”
“Kikace mene?!”yace da ita yana ware idanuwa jin abinda tace..
“Kobah da newscaster nake ba..”
“Lier”
Cikeda turo baki ta k’araso wajensa tana yatsina fuskarta cinyar sa ya nuna mata,
“Zo ki xauna anan magana xa muyi yawwa da punishment d’inki kuma for calling me definitely arrogant asif m your mate”
Ware idanuwatai alamar yaya haka kamar yasan abinda take magana kenan a zuciyarta yace,
“Mrs Aliyu kar ki manta jia da dare(yesternight)komai na...”
Be k’arasaba ba se ganin Meenah yai a cinyar sa hannunta d’aya a kan bakinsa ta rufe shi alamar karya k’arasa maganar dan murmushi yai bayan ya xame hannunta me d’auke da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 35