Hydar ciki harda meenah dake faman gatsile gatsile suna had'a ido da Aliyu Hydar ta rafka masa harara ta cikin mudubin mota tana pouting k'aramin red lips d'inta girgixa kai yareemah Aliyu Hydar yayi axuciyarsa kuwa maganarta yake yarinya sekace aljana,100k yaxaro yamik'o hannu tacikin window daniyar rabawa yaran caraf meenah ta wafce ta arce da gudu bataliyar yaran suka bita masu kuka nayi masu mita nayi dede lokacin motarsu tafuta daga gidan Aliyu Hydar ya girgiza kai ahankali yafurta;
"Trouble maker......"
Tafiya suke ahankli har airport bawanda kewa wani magana har suka shiga cikin jirgi suka d'aga yerwa fato motoci a tawaga sukazo d'aukarsu har shehurin....
_*MAIDUGURI_*
(_*SHEHURI_*)
Suna shiga cikin masarautar k'irjin yareemah Aliyu hydar ya fara bugawa fatan shi d'aya Allah yasa mai-martaba yace bazai saurare su yanzu ba sai gobe domin yanzu idan yayi mai batun zai iya shiga wani yanayin. Farin cikin Mai-martaba ya gaza b'oyuwa ganin d'an uwanshi a kusa dashi kowa ya ganshi yasan lallai yana cikin nishad'i dajin dad'i.
Tun sanda suka shigo jakadiya ta zari k'afa tayi sashan hajia yakolo, tana shiga sai da gaban hajia yakolo ya d'an buga saboda tabbas tasan ganin jakadiya ba alkairi bane dan bata tab'a zuwa musu da alkhairi amma tunda su sun kasa tsaida zuciyar su guri guda dole suso jin gulmarma hakan yasa basa k'in zuwanta tunda ta gurinta suke samun duk wani makirci da suke k'ullawa.
Gurfana tayi gaban hajja yakolo tana mik'a gaisuwar ban girma tare da yi mata k'irari kamar yadda akasan anayiwa duk wani jinin sarauta
Saida jakadiya ta gama fadancinta sannan hajja yakolo ta kalleta tana daga kishingid'e taci kwalliya kai da ka ganta kasan Matar sarki ce, tamkar bazata yi mata magana ba sai kuma ta motsa baki da k'yar cikin isa da k'asaita tace.
"Jakadiya lafiya, meke tafe dake yanzu haka?" Hajja yakolo ta fad'a tana yatsina fuska tamkar tana kallon abin k'yank'yami a jikin jakadiya,
"Allah ya temakeki ki dad'e ki k'arko, dama yanzu ne naga bak'in motoci toh sai na tsaya naga ko suwaye ashe su yareemah Aliyu hydar ne da Modu indimi da kuma Mai Alooma Gaji shine nace ko dama kunsan da zuwan nasu, yanzu haka dai naga sun nufi fada baki d'ayan su."
Jakadiya ta fad'a tana k'ara sunkuyar da kai tamkar zata yi mata sujjada, cikin tashin hankali hajja yakolo ta mike tsaye tana kallon jakadiya cikin tsananin rud'ani tace;
"Shin kin sanarwa da hajja gajiram?"Hajja yakolo ta tambaya tana kallon jakadiya wadda kanta ke k'asa, cikin tsananin ladabi jakadiya take magana;
"A'a rankishi dad'e ai yanzu suka shigo nan gurinki na fara zuwa." Jakadiya ta fad'a cikin k'ask'antar da kai a gurin hajja yakolo.
"Kije kice mata ganinan zuwa."
Da sauri jakadiya ta mik'e tana kuma kai gaisuwa, bata dad'e da fita ba itama hajja yakolo ta mik'e tayi side d'in hajja gajiram bayinta na biye da ita a baya har cikin katafaran parlorn da hajja gajiram ke zaune a hakimce tamkar itace sarkin. Zama tayi a kusa da ita bayan hajja gajiram ta sallami bayin dake kusa da ita suna matsa mata k'afa, suna fita hajja yakolo ta kalleta cikin yanayi na damuwa.
"Yayya kinji labarin zuwan Mai Alooma Gaji?"
A razane tana daga hakimce sai gata a tsaye tana kallon kishiyar ta kuma aminiyarta cikin tashin hankali tace;
"Mai Alooma fa naji kina ambata to me yazo yi kuma?"
"Wannan shine abun tambayar,kuma gashi duk bamu sani ba amma tunda gidan yazo dole zamu ji yanzu ina jakadiya ita ce zata yi mana wannan aikin?!"Fad'in hajja gajiram da har gumi ya fara karyo mata tamkar babu na'urar sanyaya d'aki,gajikin ta dake ta faman rawa dan tsananin fargaba tana tunanin ko zancen sarauta zasu yi ita dake burin ace yau babagana ne da sarautar.
_________
*T*sananin murnar da Mai-martaba ke ciki ne yasa ya manta da komai sai ta d'an uwanshi, suna shiga fada Mai-martaba ya mike tare da kamo hannun Mai Alooma Ghaji suka fito. K'aton apartment d'insa suka nufa har sai da suka kusa shiga Mai-martaba ya juya yana kallon mutanen dake binshi a baya yayi musu umarnin da su dakata daga nan,ya kuma kallon su yareemah Aliyu hydar da Modu dake faman yin k'asa da idanuwa yace;
"Modu ya kamata kuje ku huta tukunna,gobe idan Allah ya nuna mana sai muyi magana."
Da sauri yareemah Aliyu hydar ya riga Modu amsawa "Toh baba mungode Allah ya nuna mana."
Nan suka juya Mai Alooma yayi dariya saboda yana da saurin fahimtar yanayin da mutum yake ciki musamman idan ya zauna dashi.
Apartment d'in yareemah Aliyu hydar suka wuce direct ya wuce kan soofa ya fad'a yana mai rintsa idanu kanshi na wani irin juya mai,yayin da k'irjin shi ke tsananin bugawa yana tsoran gamuwar su da Mai-martaba, gashi indai Ammin shi taji sai tafi kowa shiga b'acin rai dan haka yanzu yayi saurin mik'ewa zaune yana kallon Modu indimi dake kokarin cire socks hydar yace;
"Inajin kunyar lokacin da baba zai kira mu,bari naje na cewa Baffa na hak'ura zan auri wannan yarinyar kawai, Modu idan Ammi taji cewar na watsawa baba k'asa lallai ina cikin hatsari dan denama kulani zata yi,tana son mu kyautatawa Mai-martaba domin duk cikin mu 'ya'yansa bama yi mai adalci barinje kawai"
Yareemah Aliyu hydar ya fad'a duk jikin shi yayi sanyi, banza dashi Modu yayi ba tare da yayi mai magana ba sai ma k'ok'arin shiga bedroom yake mamaki ya kuma dulmiyar da yareemah Aliyu hydar. Tashi yayi yabi shi a baya cikin jin haushin yadda yayi mai banza.
"Kanaji ina maka magana sai share ni kake yi?!"
Kallon yareemah Aliyu hydar Modu yayi tare da yatsina fuska yana cewa;
"Ohh sorry guy ashe magana kake?!" This time around kai ne ka wakilceni a surutu ka zama parrot magana ta babu gaira ba dalili kake yi,and kaje na barka kaje kace ka hak'ura da rik'eka nayi?! You're free to go yareemah ni yanzu babu inda zani tunda Mai-martaba yace mu bari sai gobe..."
Kwanciya yareemah Aliyu hydar yayi a kan makeken Italian bed d'inshi tare da cusa yatsun hannunshi cikin sumar kanshi,tunani ya shiga yi dan a zahiri baya son wata Meenah shi kanshi be ga abin soba ajikin yarinyar duk da cewar tana da kyau amma bata da k'irar mata k'irjinta ma yanzu suke fitowa kosu Affy da Aysa sun fita girman na shanu, bata da shape ga tsawo kamar bulala "ohh my God!" Ya furta a fili yana furzar da iskar bakin shi.....,
____________
Mai Alooma Ghaji ne zaune kan kujerun da aka kewaye gurin dasu fuskarshi cike da nishad'i ya kalli Mai-martaba;
"Ina son sanin wacece yarinyar da yareemah Aliyu hydar keson ya aura?!"
Yanayin Mai-martaba ne ya canza daga murmushi zuwa b'acin rai,kollon shi Mai Alooma Ghaji yayi yana nazarin shi cikin damuwa da b'acin rai Mai-martaba yake magana;
"A can gurin karatun shi suka had'u yarinyar sam batada tarbiya dan har night club take zuwa da marasa kunyar yara,nasa an bincika min ita hakan yasa nace tunda beson ya kamata ba gara na bashi wacce nasan halinta nasan usulinta, naso idan ya kawo min yarinyar arziki mai cikakiyar tarbiya sai na had'a ita Aminan da yareemah babagana,toh shima sai yaje ya kwaso min kwashi kwarab dole na muka zab'a mishi mafita dani da mahaifiyar shi."
Kuma gyara zama Mai Alooma Ghaji yayi yana faman girgiza kai alamar hukuncin Mai-martaba beyi ba,cikin nuna halin dattako ya fara magana;
"Lalah ba haka ake yiba,idanka duba yanzu kai ya riga ya waye.ilimi ya yawaita idan aka yiwa namiji auran da baya so zuciyoyin da ake son gyarawa sune zasu b'aci domin zaman lafiya da jin dad'in da muke son ayi baza suyi shiba saboda zaman lafiya a gida mijine ke fara samar dashi,yana da wadda yake so sai abashi ni da kaina zan kuma bincikawa akan ita yarinyar da yake so."
"Nariga nayi duk binciken da za'ayi an kuma tabbatar min da hakan,sannan hatta yaron nan Modu da idanunshi ya ganta,ka kuma san bazai min k'arya ba..." Cewar Mai-martaba cikin tabbatarwa,yana son d'an uwan nashi ya fahimta ya kuma bashi goyan baya akan had'in da yake son suyi.
"Duk da haka dai zan sake bincike akanta,banason a dinga yiwa yara dole bayan nan gaba sune manya. Karka damu dan ta Ameenatu me sauk'i ce saboda ita macace bata da wuyar tank'warawa"
"Kawu bawai jayayya nakeso nayi dakaiba a'a sam bahaka bane kawaide nariga nayanke hukunci ne kuma ina mai farin cikin son wannan abu yatabbata"
"Karka damu insha Allahu komi ze tafi yadda kakeso inde xancen Aminatu ne kad'auka kamar anyi angama ne se abu nabiyu kuma akan d'ayar yarinyar da Aliyu ke so nizan k'ara bincike akai kuma idan har kayadda wannan abu yatabbata ba k'aramin jihadi kaiba saboda kaceto ran dake shirin fad'awa halaka wallahi kaji rantsuwar musulmi aurenta da zeyi ze zamo silar rabuwarta da miyagun k'awaye da duk wani aikin alfasha kuma ba k'aramin lada xaka samuba kai yanxu misali ace Aminatu ce ke haka kuma sai shi Aliyu yadage akan ita yakeson ya aura tsakani da Allah ba rufawa juna asiri zamuyiba ayi Auren hakane ko bahaka bane?!"
"Hakane Kawu"cewar mai martaba jikinsa duk yayi sanyi
Ganin jikinsa yayi sanyi yasanya Mai Alooma Ghaji gyara zama yashiga yi masa nasiha mai d'imbin ratsa b'argon jiki ya k'ark'are da;
"Karka manta har ma'abota littafi Allah ya halarta mana mu aura danmu karkato hankalinsu izuwa ga addinin islama dukkoda tarin k'azantar dake tattare dasu na rashin musulunci,kaga yamin ita wannan yarinyar bata fisu ba?!"
"Tafisu Kawu"yafad'a murya a raunane
"Toh wannan shine abinda nakeso ka fahimta har kullum idan d'an uwanka musulmi yana shirin fad'awa ga aikin halaka sauri kake kai jihadin ceto rayuwarsa da duk abinda yakamata,tunda har yarannan suna son junansu yakamata mu mara masu baya wata k'ila hakan shine silar canxuwar rayuwar ita yarinyar muna fatan hakan da yardar Allah,Ina fatan kafahimta??"
"Eh Kawu"
"To Allah ya k'ara maka lapia da nisan kwana,Insha Allahu gobe idan mai duka yakaymu da rai da lapia nizan fara gudanar da bincike akan gidansu yarinyar yaya cikakken sunanta yake??" Mai Alooma yace hakan with confidence
"Wai Basma Basheer Mai_Kano"
Murmushi fad'ad'e a fuskar Mai Alooma yace;
"Atoh komai yazo da sauk'i kenan domin Basheer Mai kano yaro nane yyi aiki a k'ark'ashina lokacin ina ambassador bazan mantaba bayan nayi retire nine naje har can kanon wajen gwamnan dayake shima nad'anyi mashi alkairi lokacin campaign nace dan Allah yabawa Basheer d'in aiki me tsoka yaron kirkine hakan kuwa akayi yabashi commissioner of finance"
"Allah sarki..." Mai martaba yace hakan cikin jin dad'in daga gidan mutunci Basman tafito...
"Saboda haka kabarmun wuk'a da nama komi ze dedeta insha Allah..."
"To Allah yasa..."
Mai martaba yace hakan tareda yin k'asa da kansa alamar tunani ajiyar zuciya yasauke shide Mai Alooma bece masa komaiba yanade naxartarsa,d'ago kansa yai ahankali yace;
"To kawu Ameenan kuma fa.......?"
Murmushin Mai Alooma ne ya fad'ad'a a nutse yace.........
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXOđ
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
đ?đȘ
_*A STUNNING LOVE STORY_*
_*NA_*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
ÂźHASKE WRITERS ASSOCIATIONđĄ
(_*Home of experts and perfects writers_*)
_* Devoted to_* :
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_* :
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_34/35_
Ina kike _*walicious walee Amarya?!_* To ki matso kusa ga page dâinki sukutum ke kadâai tawanđâ€
nanahafsat.wordpress.com
____________
âYallijam Aminatu?!â Mai Alooma Ghaji yace hakan yana shafa kanta...
âJam Baffa,kasiyomin?!â
âAi banje France dâinba tukun Aminatu Bornu naje gidansu yayyunkiâ
yakâarashe maganar yana nuna mata su Aliyu,shide Modu yana sunkuye kansa a kâasa yasa hannu yana mulmula yatsunsa da meenah tataka,jiyowatai tana kallonsu yayi dede da dâagowar kan Modu yagasa mata harara saboda mugun haushinta yakeji ganin yadda tatakeshi amma ko ajikinta bin kyakkyawan takalminsa tai da kallo ganin shatin takalminta cikeda tsoro tace âsorryâWanda idan baka kulaba baxa kace tayi magana ba saboda labbâantane kawai suka motsa ajiyar heart Modu yasauke ganin tabashi hakâuri ,shiko Aliyu lokacinma danna wayarsa yake,kadâa kanta tai bayan tabisu da kallo sannan tacigaba da magana;
âAmma baffa nikadâaice banda iPad acikin friends dâinah,they r always making fun of me...âtakâarashe maganar cikeda tausayi wai dan baffan yatausaya mata,
âAminatu kefa kika lalata iPad dâin ko..âbe kâarasaba ta cafe,
âBaffa nida gidâadâo ka siya mana guda dâaya fa kuma baya bani shysa nafasa ta kowa yarasaâ
Ganin surutun nata bana kâare bane yasanya Mai Alooma Ghaji kadâa kai kawai batare da ya bata amsa ba anutse yace;
âJeki cewa mummies dâinnaki mundawo ko??â
Meyakwan tace to tatafi aiken seta kuma sako wani zancen;
âTo Baffa warra bout the iPad??â
âKije Aminatu kifadâi aiken dana ce kiyiâ
yakâarashe xancen hadâe da fara tafiya xuwa sashen da aka warewa su Modu sukuma suna binsa a baya harta fara tafiya sekuma tadawo;
âBaffa aunty kawai xan fadâawa seta kira yayya awaya tafadâa mata kaji?!â
âMeyasa bakyajine Aminatu?!â
Shiru tai tana wasa da jelar gashinta sukuma su Aliyu da Modu suka zuba mata idanuwa suna jiran amsar da xatace,ido baffan yaxaro mata yana sake tambayrta;
âAminatu badake nakeba?â
âBaffa koba ya Gumsu bace jiya taxo da system dâinta akwai wani cartoon âdeepâsunanshi danake dying akansan ganinsa tahanani....âsekuma tai shiru,
âSekika fasa mata laptop dâinko kokuma kikai yaya?!
Oh ni Alooma mekikai kuma yanxu?!
Daria Aliyu yafarayi saboda bakâaramin dariya abin yabashi ba lalle yarinyar nan trouble maker ce tsayawa tai tana kallonsa hadâe da turo bakinta gaba ta harareshi shi a shagwabâance tace;
âBaffa kaganshi yanamun dariya ko?!â
Murmushi mai Alooma yai ahnkali yace;
âTo ai abin dariyar kikai Aminatu,kuma sunanshi baa Aliyu Hydarâ
âCab taceâhadâe da tabâe baki sannanta kuma cewa;
âSunan mugun maths teacher dâinmu kenan... I so much hate himâ
Kadâa kai kawai mai Alooma yayi yana adduar Allah ya shrya masa meenah a zuciyarsa,
âBaffa formatting system dâin nayi nadawo da ita kamar yadda aka siyota sabuwa,tatas nai deleting komi nd nasan ya gumsu tanacan tana nemana xata kashe niâtafadâi hakan tana dâaga kafadâa
Jin jina kai kawai mai Alooma yayi atakâaice yace ;
âJeki kice gidadâo yaje yafadâa mataâ
Sude su Modu zuba eyes kawai sukai suna kallonta
Ware ido tai jin abinda baffan yace komawatai gabansa tana kadâa kai ahankli cikeda tsoro tace;
âBaffa shima nemana yakeâ
âDa akai yayakuma?âcewar mai Alooma agajiyance
âBaffa takalman daka siyo mana tun wancen tafiyar ya bâoye wai baxe sakaba se babban sallahâ
âTo ina ruwanki aminatu?â
Sunkuyar dakai tai hadâe da dâago kaftara kaftaran takalman maxan dake kâafarta tace;
âTo aishine naje nadâakko a closet dâinsa nasaka dama nace masa nikuma Wlhy idan baze sakaba to ni sena sa,baffa wannan ai tsumulmula ce ko abu tun last year fa ko?!â
âYa ilahi! Aminatu jeki kawai xankira bulama yafada musu, kinji?â
Kadâa kai tai alamar toh sannan tafece aguje,cike da takaicin isarsu datai mai Alooma yadubi su Modu yana fadâin;
âKuyi hakâuri kâanwar taku ce kamar parrot haka takeâ
âBakomi Baffaâcewar Modu
Shide Aliyu Hydar beyi magana ba yade lula duniyar zancen zuci nayadda yaga trouble kala kala awajen meenah harta zarce expectations dâinsa,kowa da tunanin dayake ahaka suka kâarasa cikin apartment dâin da aka tsaftace masu se kâamshi yake,mai Alooma yace su huta anjima saje su gayda iyayen nasu
âToh Baffa mungode Allah ya huta gajiyaâ
âAmeenâmai Alooma yace
sannan ya wuce nasa sashen..
Sai da suka kusa shiga babban parlorn sashen kawai yareemah Aliyu hydar yaji kamar anabin bayansu hakan yasa shi dakatawa tare da waigawa yaga Meenah ce ke bin su,mamaki yayi amma ya shiga ciki beyi mata magana ba dan kar tayi mai rashin kunya. A zaune yaga Modu har yabi lapiar kujera yaxauna yana sauke ajiyar zuciya, yana shiga itama ta shiga fuskar ta kâunshe da fara'a tayi sallama cikin siririyar muryarta mai dad'i;
"Assalamu alaikum!" Ta fad'a tana kallon cikin parlorn tamkar bata son yadda yake ba.
"Wa'alaikum salam."
Modu ya amsa tare da mikâewa zaune yana kallon Meenah,Aliyu hydar kuma yayi shigewar shi cikin bedroom komai tsab-tsab tamkar basuyi rayuwa a ciki ba an gyara shi komai neat.
Zama Meenah tayi kusa da Modu tana dashare mai kâananun hakâoranta farare tass dasu tace mai;
âAshe daman ku agidan su Affy da Aysa kuke ?wallahi ban sani ba har sai da kuka tafi aunty yafendo take gaya mana, wai kuma shi wancen yayan sune d'an Ammi ne shima?!â
Kallonta kurum Modu yayi jin yadda take surbid'a mai zance tamkar kiranta yayi,cikin rashin damuwa da amsar da be bata ba Meenah ta cigaba dayi mai magana;
âAllah sarki Affy ai dana sani har letter zanyi musu na baku kukai musu,dan dai baku kiramu munyi hiraba har kuka tafi.â
âUhmm Meenah sunanki ko?â
Modu indimi ya tambayeta yana rik'e hab'ar shi tare da kâura mata manyan idanuwan shi,
âHahaha Eh mana suna na Ameenatu shine ake kirana da Meenah ammafa family ne kawai ke fadamin haka, friend's d'ina kuma suna ce min baby queen.â
Tayi maganar tana dariya tare da wasa da k'asan rigarta.kallonta kawai Modu keyi daga sama har k'asa sannan ya kwashe da dariya yana rik'e da ciki itama taci gaba da tayashi dariyar dan ta d'auka maganar da tayi ce tasa shi dariya,ganin haka yasa shi sassauta dariyar yana kallon kyakyawar face d'inta yana cewa;
âYah sisterâs dâinsane su Affy, ai farkon zuwan mu rashin kunya kika dinga yi mana that's why muma bamu shiga harkarki ba but this time around zaki zama kâawata ko bakya so...?!âYa tambayeta bayan ya gyara zaman shi.
âEh sosai ma ai wancen xuwanma dan bamu sanku bane, kuma kai ba ruwanka akan wancan daya ke son ciremin gashi,kwana na uku ina jin zafin gurin daya rik'emin.â
Modu yayi murmushi tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya,gyaran murya yayi yana kallonta;
âWaye saurayin ki Meenah?!â
Yatsina fuska tayi alamun tambayar bata burgeta ba tace;
âbabu!ni bana harkar love aunty yafendo ta hanamu cewa tayi karatu zamuyi kaima kadena yi min zancen karnaje na gaya mata wallahi.â
Idanuwa ya fito dasu jin daga tambaya zata ce zata gayama yafendo ,cikin basarwa ya mik'e tsaye yana tafiya bedroom inda yareemah Aliyu hydar ke ciki yace mata;
âAh sorry daga tambaya?tashi ki tafi kinga yanzu muka zo zamu huta muyi wanka anjima sai mu had'u.â
Yana fad'a yayi saurin shiga cikin d'akin ita kuma ta mik'e tana hararar shi ganin yak'i tsayawa ya bata labarin su Affy juyawa tayi tabar parlorn da d'an gudun ta tabar apartment d'in.
"Guy yarinyar nan akwai surutu,zaka sha fama gaskiya ina tausaya maka, tana da kyau sosai matsalar d'aya bata da suffar mata amma idan aka yi muku aure kana bata kulawa ta musamman wow komai zai yi zam-zam sai dai zaka sha kiyo dan kiwan ta ba na kâananun shekaru bane....â
Yareemah Aliyu hydar yayi mai banza lokacin yana taje gashin kanshi, Modu ya kalleshi cikin b'acin rai yana cire riga yace;
âwai kanaji ina ta faman magana shine kayi min banza ko? Toh wallahi akwai ranar k'in dillanci zaka zo ka nemeni arrogant guy kawai.!"
âYou are sickâkawai Aliyu Hydar kawai yace cikin basarwa
âKaji dashi kaida banxan daily silly annoying words dâinka kaide ba American bane gat that into ya head cabbage head kawaiâ
Murmushi kawai yareemah Aliyu Hydar batare daya tanka masaba,bayan sunci abinci sun huta ne suka nupi gayda su aunty yafendo sannan suka wuce sashen Baffa harseda lokacin bacci yayi tukun sannan suka koma sashensu don sauke gajiya...
_*SAFIYA TA GARI_*
_*BORNU(SHEHURI)_*
âDagaske kike jakadiya mangu?! Kada kibari labâbâanki su furta kalmomin da zasu iya janyo miki rasa rayuwar zamanki a shehurinnan domin idan har shirya zancenki kikai,ina mai tabbatar miki dacewa zan iya salwantar da rayuwarki bake kadâai ba har danginki kaf,kifadâamin gaskiya shin meke tafe dake?!â
Hajja gajiram ta kâarasa maganar cikin tsananin firgici da rikita,jakadiya mangu dake raba idanuwa a rakubâe a kâasa kamar tsohuwar kura tace;
âKwarankwatsa dubu ba shrya zance naiba uwar dâakina,boka na sambisa yatabbatar mun da cewa har aljanun dake cikin tekun maliya yanemi temako suka kuma tabbatar masa da cewa lalle yareemah Aliyu Hydar shine ze gaji gadon sarautar bornu bayan haka kuma har haske biyu yagani hakan na....â
Bata kâarasaba taji saukar mari har sau biyu a lomatstsun kuncinta harseda taga wuta a hargitse cike da tashin hankali hajja gajiram tace;
âKâarya kike makâaryaciya yâar gidan matsiyataâ
Baki na kakkarwa hadâe da dalalar yawun daya rine ya zama ja saboda tsabar cin goro hancinta se xubar majina yake idanuwanta suna kawo ambaliyar hawayen azabar marin datasha,hannu bibiyu tadâago dakâyar alamar hakâuri tanamai duban hajja gajiram dake watsa mata harara cikeda tsoro tace;
âUwar dâakina narantse da Allah duk zancen danayi maki babu kâarya acikinsa,Allah ya kâara miki lapia da nisan kwana wallahi bakeba uwar dâakina wani acikin masoyanki ma baxan musu wannan mummunan fatan ba amatsayin kâarya,dama na bincikone saboda aiwa tufkar hanci...â
Shiru tai bayan tace haka,ita kuma hajja gajiram tamikâe tashiga xagaye parlorn dayasha tum tum da kilisai tana neman ina mafita?!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXOđ
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
đ?đȘ
_*A STUNNING LOVE STORY_*
_*NA_*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
ÂźHASKE WRITERS ASSOCIATIONđĄ
(_*Home of experts and perfects writers_*)
_* Devoted to_* :
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_* :
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_32/33_
Wannan shafin nakune; _*sis(pherty xarah)my momma(kausar m hassan)& my beloved big sis(Maman Shakur)Allah yak'ara maku basira da zak'in hannu_* đđŒđđ
nanahafsat.wordpress.com
____________
âRan sarki yadadâe karka manta da Aliyu da Ameenatu duk yâayane agurinka saboda haka kamar yadda kakeso ka kâara kâulla dankâon zumunci tsakaninmu ni Alooma na amince da hannu dubu bama biyu ba ina kuma fatan Allah yasanya alkhairi aciki yakadâe fitnah....â,
âAmeen ya rabbi Kawu,Nagode kâwaraiâcewar mai martaba,
Sunjima suna hira sannan Mai Alooma yakoma masaukinsa domin hutawa bayan ya wartsake gajiyar tafiya ne yaâaika a kirawo masa yareemah Aliyu Hydar,lokacin da dâan aike yakaiwa yareemah Aliyu Hydar sakâon Mai Alooma Ghaji suna tare da Modu,tsaye Aliyun ya mikâe yana gyara links dâin rigarsa yabi Modu da kallo dake kwance male male akan gado yana chatting da wayarsa se murmushi yake a hankali Aliyu yace;
âGuy muje ko??â
âWhere to??âcewar modun dakebin Aliyu Hydar da kallon tara saura kwata,
âGurin Baffa manaâ
Tsaki Modu yaja alamar Bakada amsa sannan yacigabada danne dannensa,
âDakaifa nake guy kake shunning dâina...â
âDa dâan aiken yazo cayai ance da Modu?! No.. yace kaje inji Baffa yanzu,dan Allah guy count me outâ
Azuciye Aliyu Hydar yafice be tanka masaba hadâe da bugo kâofar daria Modu yai hardasu doddoka kâafarsa akâasa,Aliyu nafita yawuce sashen da aka sauki Mai Alooma Ghaji azuciyarsa kuwa yankewa kansa damar kâarfar kowacce magana ce baffan zemai walaâAllah hakane destiny dâinsa cikeda kâarfin gwiwa ya kâarasa cikin parlorn da baffan ke xaune sake gaisawa sukai da baffan sannan yanemi waje daga gefe a kâasa yaxauna,
Gyaran murya baffan yai yafara magana;
âTo Aliyu munyi magana da mahaifinka akan ita yarinyar daka keso wani abin dadâinma shine mahaifin yarinyar nasanshi farin sani dattijon kâwarai kuma kamar yadda nadâau alkâawari xan kâara duba hallayar gidansu naji,nakuma tambaya ko da maganar aure akanta?!Saboda kaga baâa neman aure akan aure tunda budurwa ce kila iyayenta sunyi mata miji ko kamar yadda musulunci yace ko kuwa?!â,
Kan Aliyu Hydar a kâasa yace;
âEh Baffaâ
âNasan kila mahaifin naka ze neme ka saboda haka haka kada kanuna ma munyi wata magana kaji ko?!â
âEh Baffaâ
âYawwa toh Allah yamaka albarka xaka iya tafiya kuma duk yadda ake ciki de i will let you knwâ
âToh Baffa Nagode Allah yasaka da alkhairi nabarka lapiaâ
Yakâarasa maganar hadâe da dâan rissinamasa alamar girmamawa sannan yafice cikeda jin dadâin wannan daddadâan labarin tuno meenah dayai murmushinsa yafadâadâa at last ancire maganar trouble maker,haka ya wuce apartment dâinsu cikeda jindadâi kotakan Modu bebiba shima yashareshi,modu uban son hira sebin Hydar din yake da kallo,Aliyu hydar na lura dashi yai banza sema dariya dayake bashi ganin yadda modun dukyabi ya gigice
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 35