yanason yaji zancen me akaiwa Aliyun ganin yadda aliyun ke murmusawa cikeda jin dad’i daga k’arshe ma Aliyun mik’ewa yayi yai ficewarsa balcony kotakan Modu dake faman k’walla masa kira bebiba...
_*WASHEGARI_*
Da safe Mai Alooma Ghaji yahau flight yatafi kano, bayan mai martaba yagama yin yan hukunce hukuncensa a fada waziri yacewa yacigaba da sasanta k’ararrakin da aka kawo shikuma yakoma sashensa ya aika aka kirawo masa Aliyu Hydar,Aliyu Hydar yagayda mahaifin nasa duk a rud’e cikeda fargaba k’irjinsa se dukan d’ari d’ari yake atsorace yaxauna a k’asa kansa a sunkuye yak’i barinma su had’e ido da mai martaba shide mai martaba yana lura dashi yabasar dashi yafara magana;
“To madAllah Aliyu kaci darajar Kawu dahar na amince da aurenka da wannan yarinyar dakake k’ulafucinso to kamar de yadda nace amatsayina na mahaifinka ina neman amincewarka wajen had’aka aure da Amina y’ar uwarka dade kake neman bad’amin k’asa a ido kabad’ama sede kar a kuma...”
Be k’arasaba ya tsaya yana d’an bubbuga k’irjinsa da alama ciwo yake masa,kan Aliyu a k’asa da sauri yad’ago wanda kana gani kasan yagama shiga hali na rikita cikeda tausayawa yake fad’in;
“Sannu baba Allah ya sawwak’e...”
“Ameen Aliyu”
Yad’an jima yana maida numfashi sannan yacigaba daga inda yatsaya;
“Ina kuma fatan haka baxe xamo cutarwa ba ga rayuwar d’ayanku kasani banida burin tursasaka ko a farkon maganata dakaima ban tursasa kaba seda nace kakawo y’ar mutunci Aliyu,amma gani kake banyi dedeba ko?to kasani najanye maganata baxan tursasa kaba tunda kazabi _*son ran ka_* ni najanye _*zab’in iyayen_* da mukai maka tunda kana ganin ba gaata mukai maka ba daman zumunci naso had’awa”
Mai martaba yai shiru yana duban Aliyu wanda gaba d’aya yagama lulawa duniyar tunani bashida niyyar magana ahankali Mai martaba yace;
“Kana iya tafiya...”
Kasa mik’ewa yareemah Aliyu Hydar yayi gaba d’aya yakasa gane a farin ciki yake ko bak’i?! Se magana yake shi kad’ai a zuciyarsa,
Meenah fa?! Meenah fa Wannan trouble maker d’in yarinya k’arama kome yasa baba yakeson had’a ni da ita a matsayin abokiyar rayuwa?! Aliyu kaikuma taka k’addarar kenan wata zuciyar tace masa,ya ilahi yasake furtawa a zuciyar tasa seda ya kwashi kusan mintoci uku kafin yace;
“Baba kayi hak’uri Allah ya huci zuciyarka na... na.. Na amince baba”yak’arashe xancen dad’an rawar murya
Cikeda jin dad’i mai martaba yace;
“Alhamdulillah Nagode Nagode Aliyu Allah yamaka albarka kaji?”
“Ameen baba”
Aliyu Hydar yafad’i hakan a kunyace ganin yadda mai martaban yakemai godia dukse kunya ta lullub’eshi gefe d’aya kuma dad’ine yamamaye zuciyarsa na irin tarin albarkar da mai martaban yake saka masa kullum ahankali mai martaban yashiga jan Aliyun da hira har seda yaga yasaki jikinsa tukun sannan ya sallameshi shikuma yakoma fada aka cigaba da fadanci...
D*a yammaci Mai Alooma Ghaji yadawo daga kano ganin yamma tayi besamu damar ganawa da mai martaba ba se bayan magrib sunyi sallah sund’an tab’a abin motsa baki sannan mai Alooma Ghaji yashiga zayyanewa mai martaba komai daya wakana a kano gidansu Basma na irin karramawar da akai ya k’ark’are da;
“Kuma Alhamdulillah babu maganar auren kowa akanta,munyi da mahaifin nata nanda sati biyu zamuje ayi maganar sa rana da yadda za’a gudanar da bikin tunda kaga yadda afno (hausa) Ke bikin aurensu mu bahaka muke yiba dukda de yacemin mahaifiyar yarinyar bafulatanace y’ar wudil wani local government dake kano d’in”
“Masha Allah! To Allah yatabbatar da alkhairi”cewar mai martaba cikeda jin dad’i
“Amiin Amiin,gobe nakeson komawa can yola akwai wasu contracts daxanyi signing”
“To Kawu mexe hana kukoma dashi Aliyun sesu sake sasanta kansu da Aminatun tunda banajin ita tasanma da wannan maganar ko?!”
“Eh hakan yayi,se suka dake sanin juna,don dama Aminatun banyi mata maganar ba sonake sena koma tukun”
“Babu de matsala ko kawu?!”
“Babu bulama,ai Aminatu yarinyace saboda haka saurin tank’warata tayi abu bame wahala bane beside ita kad’aice ta ragemin ban aurar ba kuma dukda k’arancin shekarunta aitana gani duk akayi auren yayyunta,karka damu kanka inde tanan b’angaren ne”
“To Allah yashige mana gaba kawu”
“Amiin Amiin”
Da haka suka shiga wata hirar zumuncin tayaushe gamo har dare yayi lokacin bawa bacci hakk’insa sannan sukaiwa juna sallama kowannensu yatafi makoncinsa.....!
_*SAFIYA TA GARI_*
Wuraren k’arfe tara saura kwata mai Alooma Ghaji yagama shirinsa fada yawuce wajen mai martaba nan sukaci abincin safe sannan mai martaban dakansa yai masa iso wurinsu hajja gajiram da yakolo suka gaysa dan tunda yaxo ko hanyar sashensu beyiba bayan sun gaysane yanemi su Aliyu su rakashi gidan Ammi itama su gaysa yakuma yimata sallama b’angaren baa Ngari suka fara zuwa nan suka tarar da Ammin tana bashi ruwan zam zam bayan tayimai tofi gefe d’aya kuma wannan ruwan ganyen magaryanne da alama tagoge masa jikinsa dashi ba lefi jikin ngarin yayi sauk’i nesa ba kusa ba tunda yana iya juya jikinsa duk inda yakeso yana kuma d’aga hannuwansa harma yana d’an tsakurar abinci yanaci ba lefi abinse wanda yagani Lalle k’arfin addua yafi sihiri...
Gaisawa sukai da Ammin sunjima suna hira sannan suka mata sallama suka tafi bayan Ammin tak’ara jan kannuwan Aliyun sosai tagargad’eshi da kada yasake tafka wani kuskuren kada kuma ya kuskura ya wulak’anta mata y’ar yar’uwarta dayake da Ammin da aunty majiiddan sun had’a relation ta iyayensu dake can T’chad,kodah su Mai Alooma suka koma shehurin basu wani sake b’ata lokaci ba sukai sallama da mai martaba suka hau jirgi suka tafi yola....
_*YOLA(JIMETA)_*
lokacin dasu Mai Alooma Ghaji suka isa yola motocine har guda uku suka taresu a airport suka kaisu gidah,suna shiga parking space meenah tafito da gudu jin horn d’in motar baffanta,sanye take cikin doguwar riga yar kanti purple color da k’aton zanen barbie doll ajiki anrubuta ‘princess’ boldly,kanta ba d’ankwali bak’in dogon gashinta yabayyana ankitsashi cikin kalba k’wara biyu k’arshen jelar and’aure da ribbons bak’ak’e masu d’igo d’igon purple color suma yatsunta na hannu da k’afafuwanta sunsha nalle sunyi maroon dasu k’afarta sanye cikin sandal na maxa daka gani kasan banata bane k’afarta se yawo take aciki,
Se washe baki take tana jiran fitowar baffan nata bata masan ko dasu wa yake tare ba itade burinta taga baffan nata,k’ofar motar aka bud’e da sauri ta doshi k’ofar sekuma taja baya da sauri ganin waye shikansa Aliyun sedata bashi daria kamar wanda taga dodo komawatai b’angaren d’ayar motar tana jiran fitowar baffan nata hakan yabawa yareemah Aliyu Hydar damar k’ara mata kallo sosai yakebinta da kallo hardasu murmushinsa kona meye oho
Fara ce ba irin dadau d’innan ba sede farinta me shek’i da kyawune,Kana ganinta kasan tana hutawa y’ar hutu ce,doguwace sosai a iya shekarunta hancinta becika sirantaka ba bakuma xaka sanyata a layin marassa hanci ba tanada b’ular hanci a dama kamar irinnasu Affy,
dayake kaman gado kowacce mace a familyn tana dashi tanada manyan idanuwa tubarkAllah kamar zasu fad’o don girmansu bak’aramin k’arawa fuskarta kyau sukaiba,bakinta d’an mitsitsine me d’auke da jajayen labb’a (red lips) batada k’iba ko kad’an kamar za’a busheta ta fad’i haka take,daka ganta kasan tanada k’arancin shekaru sosai alamun yarinta yabayyana atattare da ita.......,
Mai Alooma Ghaji yana fitowa daga mota,meenah ta tatafi da gudu ta rungumeshi hartana take yatsun k’afar Modu da takalminta ta mak’alk’ale baffan tana murna cikeda farin cikin ganinsa tace;
“Jab’b’ama Jab’b’ama Baffa”
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 19/12/2017, 8:31:20 PM: MISS XOXO: _*SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!_*
💜?👪
_*A STUNNING LOVE STORY_*
_*NA_*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(_*Home of experts and perfects writers_*)
_* Devoted to_* :
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_* :
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_*36/37_*
nanahafsat.wordpress.com
_______
G*abaki d'aya ta rasa mafita,ta rasa ta ina zata kamo bakin zaran,ta k'arasa saitin da jakadiya ke zaune tayi tamkar zatayi tamole da ita zuciyarta na tafasa yatsina fuska tayi tare da cewa;
“Jakadiya ina son ganin hakan bata kasance ba,sanin kanki ne mun dad'e muna k’ok’arin ganin yadda za'ayi babagana ya d'are karagar mulki,amma yanzu lokaci guda ace komai ya rushe? Inason in k'ara tabbatar da wannan zancen naki,idan har da gaske ne toh dole ne shima yareemah Aliyu hydar yabi sahun d'an uwanshi Ngari, i need a prove jakadiya cinkin ‘yan kwanakin nan dan inason samawa yareemah babagana farin ciki kije ki sake tabbatar min da mafarkinki,dan wannan zancen naki mafarki ne.”
Hajja gajiram ta fad'a tana wuwwulk’ita idanuwa a cikin d'akin,cikin tsananin kad'uwa da shiga tashin hankali jakadiya mangu tayi k'asa da kai tare da mik'a gaisuwa da jinjina gurin hajja gajiram sannan ta mik'e tabar d'akin cike da fargabar taya zata tabbatar musu da cewar da gaske takeyi yareemah Aliyu hydar shine magajin sarki.ganin babu mafita yasa ta cigaba da bincike ta yadda zata je musu da k’wak’waran dalilin da zai sa su yadda da ita...
_*YOLA(JIMETA)_*
Mai Alooma Ghaji ne kwance akan 3sitter ya d'aura k’afafuwan shi akan cinyar aunty Maijidda tana matsamai su a hankali yayin da aunty Yafendo ke zaune a k'asan carpet d'in dake malale a parlorn tana yanka musu fruit suna hira cikin kwanciyar hankali mata ne da suka fuskanci juna hakan yasa basu da matsala a zaman takewar su hankalin mijin su kwance dan bashi da fargaba ko wacce yana sonta babu wadda yake banbantawa hakan yasa bazaka gane wacce yafi so ba. A hankali ya bud'e idanunshi wad'anda suke a lumshe saboda yadda yakejin dad'in matsar da ake mishi.Kallon aunty Yafendo yayi tare da sakin k’ayataccen murmushi yace;
“Albishirinki..?!”
Tayi dariya bayan ta d'ago sun had'a ido tana yanka tuffa tace;
“Goro fari ‘kalk’al.”
Mai Alooma ya gyara kwanciya bayan ya k'ara turawa aunty Maijidda k’afafuwanshi shi,ya kuma gyara muryar shi cikin nishad'i yace;
“y’arki tayi kasuwa,aure za'a yi mata hope zaki bamu had'in kai sannan zaki tayamu campaign?”
Mai Alooma ya fad'a tare da juyawa ya kalli aunty Maijidda wadda take murmushi k’asa k’asa amma batayi magana ba. tab'a baki aunty yafendo tayi tana k’ok’arin d'aukar b'arin tuffa guda d'aya takai cikin bakin Mai Alooma ya d'an gutsira sannan ta zauna tana cewa;
“Me zai hana indai anzo an nemi soyayyar mu?,ina ganin wannan ba matsala bace adai nemi amin cewar mu.”
Dariya aunty Maijidda da Mai Alooma suka yi suna kallon aunty yafendo da tayi kicin-kicin ita a dole anzo neman auran 'yarta.Tashi yayi zaune yana dariya sosai dan indai yana tare dasu wani nishad'i yake ji,cikin jin dad'i yace;
“Toh shikenan amma fa ba ita kad'ai zai aura ba su biyu ne at once.”Yayi maganar cikin tabbatarwa.
Ba aunty yafendo ba hatta aunty Maijidda sai da zuciyarta ta harba dan tsananin kad'uwa dajin maganar,sai dai ita aunty Maijiddah tayi kawaicin yin shiru tunda d’iyar tace batare da tayi magana ba sai aunty yafendo ce tayi ta hanyar cewa;
"Ah haba dai! Wannan zancen kawai tatsuniyace amma ya za'a ce abawa mutum ya auri mata biyu tashin farko ba tare da anyi mai d'aya anga yadda zaman zai kasan ce ba,gaskiya bazai yuwuba sai dai ya hak’ura da Meenah dan ita bazata iya zama da kishiya ba tashin farko.”
Aunty yafendo tayi maganar cikin had'e rai fuskarta ta canja daga farin ciki zuwa damuwa kallon shi ya maida kan aunty Maijidda ya gani ko zata ce wani abun sai yaga kamar ma batajin abinda suke cewa hakan yasa shi sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ya kalli aunty yafendo yana cewa;
“Mai martaba shine yake son had'a jinina da nashi su kara had'uwa ta hanyar bawa yareemah Aliyu hydar Meenah,idan baku sani ba ya kamata yanzu kuji sannan ku sani yareemah Aliyu hydar yana da *SON RAN* shi ni kuma bazan bari a zalince shiba hakan yasa nace to sai dai a had'a mai biyu saboda Meenah *ZAB'IN IYAYE* ce kunga anan babu wanda zai ce anyi mishi ba dai-dai ba.ya Kama ta ku k'ara k’arfafa min gwiwa wajan ganin mun k'ara k’ulla kanmu nida d'an uwana,kamar yadda Ameenatu take 'yata shima Aliyu hydar d'anane kuma duk ina son su ina alfahari dasu, ku bani goyan baya sannan itama Meenah anjima zan sanar mata ina fatan zaku taya su da addu'a?!”
Ya fad'a yana kallon su da k’yar aunty Maijidda ta tsaida zuciyar ta guri d'aya sannan tace;
“Insha Allahu Allah yasa hakan ya zamar musu mafi alkairi a rayuwa.”
"Amin..!"
Mai Alooma ya fad'a sannan ya maida kai wajan aunty yafendo gani yayi tayi shiru alamar bata da niyar yin magana,ya kalli gefen shi tare da bubbuga kusa dashi yace mata;
“Kema dawo nan,ki gaya min abinda kike tsoro har yasa kika k'i bamu goyan baya taho ki zauna.”
Da k’yar aunty yafendo ta mik'e ta koma inda yake nuna mata,sai da ta zauna sannan yayi murmushi har hak’oran sa suka bayyana yana kallonta yake cewa;
“Yafendo amarya,yafendo tawa ta kaina,amarya bakya laifi koda kin kashe Meenah.”
Da sauri ta kalleshi tana zaro idanuwa yayin da aunty Maijidda ta tuntsire da dariya tamkar ba itace ke cikin damuwa ba. Mai Alooma ya juya yana kallonta har da 'yar hararar wasa sannan ya kalli aunty Yafendo wadda ta saki baki tana firfito da ido jin yace koda ta kashe Meenah.
“Sanar dani kinji Maman Meenah.”Mai Alooma ya fad'a cikin sanyin murya.
“Ina tsoran karya wulak’anta min yarinya sanin kanka ne Meenah yanzu take sanin menene rayuwa,sannan yanzu ne take karatu na tabbatar wadda yareemah Aliyu hydar yake so tafi Meenah girma, ilimi,wayewa,wayo da dabara,
Meenah ba abinda ta sani na rayuwa bare aje ga batun rayuwar aure,kawai tana jin shine amma bata san ya yake ba bare tasan muhimmancin shi.Meenah rawar kai,fitsara,rashin kunya ni ba abinda yake bani takaici irin rashin tsoronta kwata-kwata banga abinda take tsoro ba.”
Aunty yafendo ta fad'a tare da tallafo hab'arta ta rik'e. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cire mata tagumin da tayi yace;
“Karki damu da wannan, koda anyi bikin baza ta tare gidan shiba sai ta kammaka karatunta na secondary school a gurin Ammin shi kinga lokacin ta k'ara hankali kuma rawar kannan ina saka ran zata denashi so worry not kinji?!”
Cikin jimami aunty yafendo tace;
“Allah yasa alkairi ne zamu ci gaba da yi musu addu'a insha Allahu.”
“Amin nagode muku ina alfahari daku a cikin rayuwata,nasan ko bayan raina bazaku tab'a watsan k'asa a ido ba.”
Murmushi suka yi dukkan su kafin suci gaba da hirar duniya cikin so da shak’uwa...,
*Z*aune suke a wani waje da aka ware cikin gidan mai masifar kyau gurine da za'a iya kiranshi da love garden saboda yadda aka k’awata shi harda zanan heart a k'asan grass carpet d'in dake gurin.Modu ne da yareemah Aliyu hydar kishingid'e cikin wasu lafiyayyun kujeru da aka kewaye gurin dasu ko wanne manne da waya a kunnen shi kai da ka gani kasan hirar soyayya suke.
Meenah ce ta doso wajan kasan cewar taje neman Modu har apartment d'insu ta tarar baya nan tazo wucewa ne suka had'u da Bulama take tambayar shi ko yaga su Yaya Modu yace mata suna garden shine ta tafi harda wak’ar ta.
"Yaya Modu..!"
Meenah ta kwad'a mai kira cikin kunnan shi kasan cewar idanuwan shi rufe suke bega zuwanta ba sai kiran da tayi mai wanda ya kusan kashe mai dodan kunnen shi.da sauri ya mik'e yana murza cikin kunnan shi ita kuma sai dariya take mai hakan yaja hankalin yareemah Aliyu hydar ya zare wayar a kunnen shi bayan ya yanke kiran.
“Meenah meye hakan eh?!”
“Yaya dawa kake waya hakan sai wani murmushi kake kana girgiza k’afa?!”
Hararar ta Modu yayi tare da cewa;
“idan kinzo muna tare ba gurina zaki fara zuwa ba sai kinje kin gaida shi sannan ni kina jina?!”
Yatsina fuska tayi tana mai wani irin kallo mai cike da ma'anuni da yawa sannan ta d'anyi tsaki kad'an ta zauna gefen shi tana cewa;
“Ni wallahi kai zan kula ai kaine kawai kake kulani shi wannan baya magana wallahi bana son marar yiwa mutane dariya.”
“Meenah yayan kine fa dole ki dinga gaida shi.”
"Tabdijan..!"
Meenah ta fad'a tana hararar side d'in yareemah Aliyu Hydar wanda shima ya had'e fuska dan karta kawo mai raini. Modu yayi mai signal da girarshi alamun ya saki ranshi sai ya k'ara had'e fusa tare da mik'ewa tsaye yabar musu gurin.Meenah ta bishi da kallo tare da kallon Modu indimi tace;
“Yana da kyau amma baya dariya dan Allah kace ya dinga yi zai fi k'ara kyau."”
Mik'ewa Modu yayi tare da fad'in;
“zo muje ki gaya mai ni baya jin magana ta.”
Idanuwa Meenah ta zaro tare da dafe talin gashin kanta tana rintsa idanuwa dan bata manta damk’ar da yayi musu ba,kallonta Modu yayi yana mak’ale dariyar shi yasan ba k’aramar damk’a yareemah Aliyu hydar yayiwa gashin ba,suna tafiya suna hira sai ga gid'ad'o da gudun shi ya k'araso gurin Meenah yana nishi tare da kama hannunta yana ja yana cewa;
“Meenah kije inji Baffa yana sitting room yana jiranki.”
Ya fad'a yana nishi dan ba k'aramin gudu ya sha ba,ta kalli Modu tare da sakar mai murmushi tace;
“Na tafi Baffa na kirana,idan na dawo zaka kira min su Affy a waya mu gaisa.”
Modu ya d'aga mata kai,suka kwasa da gudu itada gid’ad’o yabi su da kallo yana girgiza kai tare da hango yareemah Aliyu hydar da ita a matsayin matarsa(sungul amama d'an shilan gwangwani).
Tana shiga ta haye kan kujera tana nishi Mai Alooma ya bita da kallo yana girgiza kai.sai da ta huta sannan ta kalli Mai Alooma tana murmushi tace;
“Baffa gani,Allah yasa sak’on aka siyo min?!”
Kallonta yayi tare da cewa;
“Dawo nan magana zamu yi,kai gid'ad'o jeka cikin gida kafin mu gama tazo ta sameku acan.”
Juyawa yayi yana turo baki ganin an ce banda shi.yana fita Mai Alooma ya kalli Meenah tare da shafar kanta zuwa fuskarta yace;
“Ameenatu itace mahaifiyar manzon Allah (s.a.w)wato fiyayyen halitta kinji de a tarihi shine d'anta to da ace tayi nisan kwana tare dashi to da baxe k'ijin maganar ta ba komai tasa shi xeyi mata,koda wuta ta had'a tace ya shiga bazai ji tsoro ba zai shiga saboda yana da biyayya dabin nagaba dashi tsira da aminci sutabbata agareshi,ina fatan kema zaki yi min biyayya a duk abinda zan ce mike kiyi dan nima nayi alfahari da sunan da na samiki ranar lahira kuma insha Allahu ke d'in 'yar aljanna ce?!”
Murmushi tayi tana k'ara shigewa jikinshi,kallon shi tayi tare da cewa;
“Baffa ka gayamin ko menene zanyi nima kodan na shiga aljanna naga larabawa da hurul inn wallahi Baffa bana son wuta bare ma idan ya sayyadi yana yi mana tarihi har cewa yayi ta lahira tafi ta gawayin mangal.”
Ta fad'a cikin gazgatawa tana jimamin tunowa da tarihin da tayi.wani farin ciki ya rufe Mai Alooma ya matseta a kirjinshi yana jin kaunarta na ratsashi cikin lallami da karya murya yace mata;
“Ameenatu ina son kiyi min biyayya kar kuma kice baza kiyi minba domin kinga ni mahaifinki ne, ina son had'aki aure da yayan ki shi yasa muka dawo tare dasu dan ku k'ara fahimtar juna.”
Zaro idanuwa tayi tana kallon Mai Alooma dake faman shafar bayanta cikin ranshi yana addu'ar Allah yasa karta k'i yadda sai yaga tayi murmushi tare da rufe fuskarta cikin dariyar ta mai kyau tace;
"Hahaha Baffa ai yana da kirki wallahi yafi d'ayan shi bamu tab'a yin magana da shi ba baya dariya.!"
Wani farin ciki ne ya kama Mai Alooma yayi saurin d'ago da fuskarta yana murmushi yace mata;
"Ashe ma kuna magana to Alhamdulillahi komai yazo da dad'i Allah yayi muku albarka."
Ya fad'a ita kuma ta kad'a kai tare da cewa;
"Yanzu mafa muna tare dashi muna hira gid'ad'o yaje yace kana kira na, wallahi Baffa Yaya Modu yafi Yaya Aliyu hydar d'in nan kirki."
Shiru Mai Alooma yayi yana nazarin ta,can! Ya gyara zama tare da kallon fuskar ta yana cewa;
"Toh ai Ameenatu ni yareemah Aliyu hydar d'in nake nufi ba wai Modu ba,da Aliyu hydar d'in za'a had'aku aure kwanan na ma."
Bakinta ta turo cikin shagwab'a ta fara murzar idanuwa alamar zata yi kuka be ankara ba kuwa sai ganin ambaliyar hawaye yayi suna bin kuncinta, sai ya shiga damuwa ya janyo ta jikin shi cikin lallashi yake cewa;
"Ya isah Aminatu ba zan yi miki dole ba kinji?!"
Hawayen ta share cikin sanyin murya tace mai;
"Toh Baffa na yadda zan aure shi nima inason nayi koyi da annabi (s.a.w) amma dama ba shi bane,dama Yaya Modu ne."
Tayi maganar cikin shagwab'a,jin ta amince yasa shi farin ciki tare da sanya mata albarka mik'ewa tayi ta fita yayi murmushi tare da janyo phone d'inshi yana neman layin yareemah Aliyu hydar...
Team#MEENAH AUR BASMA👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*
💖?👨👩👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(_*Home of expert and perfect writers_*)
_*Devoted to_*
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_*:
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_38/39_
nanahafsat.wordpress.com
____________
*Y*ana d'agawa yareemah Aliyu hydar ya fara gaida shi cikin girmamawa harsai da suka gama gaisawa sannan Mai Alooma Ghaji yace mai;
“Aliyu kana kusa ne?!”
Da sauri tamkar yana gaban shi yayi k'asa da kai yana fad'in;
“Eh Baffa ina apartment d'in mu,ko na zo kana son ganina?!”
Yareemah Aliyu hydar ya tambaya yana d'an fito da idanuwa waje,Modu ya d'auke kai daga kallon shi da yake yi dan karma yace yazo ya raka shi,Mai Alooma yayi murmushi yace;
“Eh Aliyu ka k'araso zuwa parlor na,ina son yin magana da kai.”
Yareemah Aliyu hydar ya mik'e yana gyara wuyan rigar shi dan kar ma Modu yayi mishi rashin mutunci yasa yayi tafiyar shi gurin Baffa ba tare daya ce yaraka shiba tafiya yake yana sake'saken kome Baffa zai gaya mai Allahu a'alamu gawai be ankaraba yaji yayi tuntub'e da abu a k’afarsa yayi saurin kallon gurin sai yaga Meenah a tsugunne tana tsintar 'yan tsakuyoyi bugetan da yayi ne yasa ta kifawa a k'asa cikin masifar ta tayi saurin mik'ewa tsaye tana fad'in;
“Kai! Kakai kakai!! Tab' to wallahi bazan yadda ba ai babu abin da nayi maka zaka turani na fad'i.”
Meenah ta fad'a tana kallon yareemah Aliyu hydar daya d'an dafe goshi alamar shima ba haka ya soba,ta kalle shi tare da rik'e k’ugunta tana turo mai baki da yayi niyar bata hak’uri sai ya fasa ya wuce ta gefenta cikin daddad'ar muryarta ta juya tana cemai;
"Yaya Aliyu hydar take a look at this ...!"
Be kawo komai ba ya d'auka wani abun zata nuna mai yana juyawa kawai yaji ta watso mai duwatsun data tsinta tare da rugawa da gudu tana mai dariyar mugunta.
Wani tukuk'in takaici yaji ya makale mai a wuya,da k’yar ya samu ya had'iye shi tare da nufar hanyar parlorn Baffa. Bayan yayi sallama Mai Alooma ya amsa mai tare da cewa ya shiga.Sai daya samu guri ya zauna sannan ya kuma gaida Baffan nashi cikin girmamawa.
“Aliyu na kiraka ne daman dan na sheda maka cewar na sanar da Aminatu kuma cikin hukuncin ubangiji ta yadda ta amince,ina fatan Aliyu zai rik'eta amana kamar yadda zaka kula ka rik'e Basmah *SON RANKA*,ko Yaya ne Aliyu ka daure ka fita hakk'in Aminatu nasan ita d'in ba *ZAB'IN KA* bace zai yi wahala ka yadda da ita musamman yadda take da rashin ji da kafiya akan abu,shi yasa tun anan zan rok'eka alfarmar kula da ita daidai gwargwadonka. Mahaifinka na san mu k'ara zama abu guda d'aya hakan yasa ya kafe akan had'aka da k’anwarka,za'a d'aura muku aure sai dai bazata tare a gidan kaba har sai lokacin da ta kammala secondary school inasha Allahu.”
Mai Alooma ya fad'a yana nunawa Aliyu hydar cewar ya daure yayi biyayya.Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke jin cewar har sai ta kammala secondary school za'a kawo mishi ita wani farin ciki ya sauka cikin zuciyar shi har yaso ya fallasa kanshi ya dai daure da k’yar yana sunkuyar da kai.
“Toh Baffa insha Allah zaku sameni me biyayya a gareku nagode Allah ya k’ara girma."
“Amin Aliyu tashi kaje sai ka nemi kanwartaka idan ka fita ko?!”
“Toh Baffa zan nemeta na gode Allah ya kara girma da lafiya.”
“Amin.”
Mai Alooma ya amsa yana murmushin jin dad'i yareemah Aliyu hydar ya mik'e yabar parlorn zuwa apartment d'insu ko takan neman Meenah beyi ba...
_*BORNU(SHEHURI)_*
Gabaki d'aya hajja gajiram ta matsawa kanta ta hanawa rayuwarta jin dad'i fatanta da burinta be wuce yadda zata ga sun kawar da yareemah Aliyu hydar ba domin boka na sambisa ya tabbatar musu da cewar shine sarkin gobe. A fusace tayi apartment d'in babagana ko kuyanginta bata bari sun bitaba,tana zuwa ta tura k'ofar
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 35