dignity d’in mace shine mutuncinta which is true,muba turawa bane let’s hold our honor kuma...”
Bata k’arasa ba Layla taja tsaki tana yatsina fuska,
“Ba wa’azi nace kimin ba,dan zaki aure shine zaki fara wani soki burutsu pls let me be nangaba bayi zanyi ba”
Jin abinda tace yasanya Basma shiru kawai batare data sake ce mata wani abun ba mik’ewa Layla tayi tai ficewarta,ahankali Basma tabita da kallo had’e da girgiza kanta kawai...
_*Yola(jimeta)_*
“Guy kaide kanaso katsigewa yarinyar nan gashi kode shine favorite part d’inka a jikinta??”
Siririn tsaki yareemah Aliyu Hydar yaja batare daya bashi amsa ba yacigaba da danna wayarsa,Modu yatab’e baki sannan ya cigaba da cewa,
“Guy gobe zamuyi tour na yola har emirs palace semunje da museums muga abubuwan Fulani culture,I just can’t wait”
“You better not”
cewar Aliyu Hydar yakuma sha kunu kamar bashi yai maganar ba,baki galala Modu yabishi da kallo cikeda jin meyasa yace,
“Saboda me fa??”
“Saboda we are leaving yola first thing tomorrow morning insha Allah”
“No Aliyu Meyasa?”
“Saboda mungama duk abinda akace muyi”
“And so...?!”
“Nide nagama magana idan kai xaka xauna to that’s ur very own cup of tea”
“But Guy...”
Be k’arasaba Aliyu Hydar ya karb’e zancen,
“For goodness gracious guy yakakeso nayi uhm?! Yarinyar nan trouble maker ce ta ajin k’arshe beside kwata kwata abubuwan maza takeyi I wonder why?to nikam gaskia baxan iya da childish stuff d’inta ba thank goodness ma wai seta gama makaranta”
Daria Modu yafarayi hardasu rik’e ciki,ganin haka yasa yareemah Aliyu Hydar mik’ewa yabar masa d’akin had’e da wurga masa harara.....
_*Bornu(Shehuri)_*
“Yanzu jakadiya mangu kina nufin kice dole wannan hanyar itace mafita?!”
Cewar hajja gajiram dake faman huci kamar tsohuwar zakanya kaida kaganta kasan a firgice take kallo d’aya xakai mata kagano tana cikin tsantsar damuwa,cikeda gasgata abinda tace jakadiya mangu tasake duk’ar dakai ahankali tace,
“Narantse da Allah uwar d’akina wannan shine abinda yace babu dad’i babu k’ari”
Dogon numfashi hajja gajiram taja a zuciye tace,
“Kikuma sake binciko jikin Ngari kifad’awa boka na sambisa bisaga umarnina yasake k’aimi wajen ganin lapiar Ngari bata samu ba,sa’annan kice masa munji mun amince zamuyi kamar yadda yace d’in”
“To uwar d’akina godia nake Allah shi taimakeki na barki lapia”
Ta k’arashe maganr had’e da sake rissinamata sannan ta mik’e ta fice tabar hajja gajiram rafke da uban tagumi se sak’awa take tana warewa.....
_*safiya ta gari_*
“Eh Ammi yau xamu dawo Insha Allah,okay i will yawwa se mun iso nabarki lapia”
Katse kiran yareemah Aliyu Hydar yayi had’e da duban Modu dake faman cin indomie a hankali kamar wanda aka tursasawa yaci dole tab’e baki Aliyu Hydar yayi had’e da mik’ewa tsaye in an i don’t care tune yace,
“Idan kagama kasameni ninayi gaba”
Modu be bashi amsa ba shima Aliyu Hydar besake cewa komai ba yafice yana murmushi ganin k’iri k’iri Modu se fushi yake tun jia akan yace yau zasu tafi sashen aunty majiiddah yafara zuwa seda suka gaysa sund’an tab’a hira sannan ya mata sallamar kan yau zasu tafi bewani jimaba yanupi sashen aunty yafendo gidan gaba d’aya yayi tsit da alamar yara suntafi school yana shiga sashen tundaga corridor daxe sadaka da main parlor na gidan yafara jin taken sautin wak’a a tv yana tashi,se rafka sallama yake amma a banxa harze hau stairs sekuma yafasa jin sautin wak’ar daga parlorn k’asa yake tashi tura k’ofar yai ahankali girgiza kai yai cikeda da takaici don dama zuciyarsa taraya masa itace,
Bayanta yahango a tsaye take a kan center table na parlorn sanye cikin party gown blue se glittering take hannunta d’auke da maburgi na miya taseta shi dede bakinta kamar loudspeaker tanabin wak’ar cartoon d’in ‘frozen let it go’gashinta tagyarashi kamar irin na Queen Elsa ta frozen sebin wak’ar take tana tafiya akan center table d’in cikin muryarta me dad’i take bin wak’ar,
“No right no wrong no rules for me... I’m free let it go,let it go can’t hold it back any more,let it go let it go turn the way and slam the door”
tak’arashe fad’in slam the door had’e da sauka daga kan center table d’in tanupi k’ofa xata rufe kamar yarda elsa d’intai a ice castle dede nan idanuwanta suka sauka akan yareemah Aliyu Hydar dake jingine da k’ofar hannuwansa a hard’e yazuba mata manyan idanuwansa masu kamada sleepy eyes yana binta da kallo tundaga sama har k’asa cikeda k’asaita yace mata,
“Switch off the TV set”
Inda inda tashiga yi saboda gaba d’aya a rud’e take daka mata tsawa yai,
“Now”
Bashiri jikinta na b’ari ta isa gaban TV set d’in mekakwan takashe tsabar tsoro ma extension wire d’in ta tsige gaba d’aya har ze sake daka mata wata watsar sekuma ya kyaleta ganin yadda jikinta ke rawa,atsorace taxo xata wuce hannuwanta akanta ta damk’e tulin gashinta saboda tasan duk muguntarsa a gashin kanta yake k’arewa cike da isa yakai hannu ze damk’o gashin nata tai hanxarin tsayar dashi,
“Nikam gashina ciwo yake wancen karon kwana uku nai ina jinyarsa jiama daka jashi aswr har yanxu yanayi”
Tak’arashe maganar had’e da pouting lips d’inta,bin d’ankaramin cute red lips d’inta yai da kallo yadda take wani cunosu gaba daria ma taso tabashi sekuma yabasar a dake yace mata,
“Meyasa bakije school ba?And karkimin k’arya you knw the consequences”
“Kobah malamin mu bane yabamu wani assignment nikam nakasa kuma yau yace xa’ai submitting shine nacewa aunty banda lapia”tak’arashe xancen had’e da sake zumb’oro masa baki
“What the fuck,wane course ne oh i mean wani subject ne?”
yak’arashe xancen had’e da rik’o hannuwanta ya murd’e cikeda xafin muguntar dayake mata tace,
“Wayyo kobah mugun maths teacher d’inmu bane Aliyu Hydar yabamu wani banxan quadratic equation kuma he’s so mean,cruel and selfless he shows no mercy akan duk wanda basuyi assignment bafa”
Tab’e baki yai had’e da sake damk’o tulun gashin nata k’ara tasaki yasa hannu ya sakar mata rank’washi a k’wanyar kanta saitin kunnenta kamar me rad’a yashiga yi mata magana cikin zazzak’ar muryarsa kamar ana busa sarewa yace,
“Meyasa bakyasa d’ankwali uhm?!”yace hakan in a romantic style
Kamar tai hauka haka takeji ga hannunta yaa murd’e ga tulin gashinta shima ya damk’e gakuma ya matseta da k’ofa yana mata magana rad’a rad’a banxa tai dashi tak’i bashi amsa ganin haka yasa yasaki hannuwan nata had’e da kamo red lips d’inta ya murd’e cikeda fad’a yace,
“Baxaki magana ba?!ba’a shunning d’ina idan inatambaya get that into ya head kuma kidena kallona da wannan idanuwan naki kaman na owl kafin na kwasheki da mari dak’ik’iya kawai”
Ganin tak’i maganar ne yasashi sake damk’ar gashin nata akaro na biyu yadda xata fujin xafi ganin yana neman rabata da gashin tane yasata magana cikeda tsiwa tace,
“Aini ba y’ar iska bace”
Tafad’i hakan tana k’ok’arin kiciniyar k’wace kanta ido ya gwalalo jin abinda tace cikin xafin nama yasake damtse gashin nata tasaki k’ara ya buge bakin cikeda kallon tuhuma yace,
“Waye d’an iskan?!”
Hawaye na tsiyaya daga idanunta tace,
“Kobah Aunty yafendo bace tace mana nidasu afrah kada mubari namiji yatab’a mana hannunmu inba hakaba zamuyi ciki mu haihu gashi yanzu nasan haihuwa xanyi shikenan nashiga uku..”
Tak’arashe xancen cikeda shesshek’ar kuka,ai yareemah Aliyu Hydar besan sanda yaturata gefe ba yadafe cikinsa yashiga daria ba k’akk’autawa harda hawaye dake silalowa daga idanuwansa saboda tsabar daria komawatai gefe tana harararsa ambaliyar hawaye kuwa se zuba suke daga idanunta naganin shikenan yanxu tasan tayi ciki se haihuwa,
Tsawaita dariyarsa yai bayan yadau mintina k’alilan yanayi,itakam ta k’agara yabarta ta tafi can kuma ta tsinci muryarsa,
“How old are you?!”
Yace hakan tareda binta da kallon k’urilla cikin kumbure kumbure da hawaye shab’e shab’e asaman fuskarta kamar baxatai magana ba sekuma tayi ganin yanxu seyaci zalinta tahanyar damk’ar gashin kanta cikin sauri tace,
“I was born in the year 2003”
Sake fashewa yareemah Aliyu Hydar yai da dariya ba k’akk’autawa yanayi yana pointing d’inta da yatsa yanaci gaba kaikace ba arrogant prince Aliyu Hydar bane ke faman b’abb’aka dariya kamar sabon mahaukaci,
Bud’e idanu meenah tai tana dubansa sekuma tai saurin sadda kanta k’asa tana mai cigaba da kuka ciki-ciki....!
Team#YareemahAliyuHydarLovers🤝
BASMAH AUR MEENAH?!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*
💖?👨👩👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(_*Home of expert and perfect writers_*)
*Devoted to*
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
*Tukwicine agareku*:
*Billyn Abdul*(Tawan) & my beloved sis(ya *Hajja ce*)
*particular thanks goes to my two adorable daughters*:
*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari*
_44:45_
This page is urs *Aunty sis* Allah yaraya newly baby boi cikin k’oshin lapia..!
nanahafsat.wordpress.com
____________
_*University of Oxford (United kingdom)_*
“*H*ello Amma!lafiya lau,ok Amma love you too,Aha bye.”
Basma dake waya ta sauke a hankali tana kallon layla dake wajan mirror tana makeup,tsaki ta d'an ja kafin ta kuma kallon layla tana fad'in;
“Daddy sun sauka yanzu,Amma tace daya kammala abinda ya kawo shi zai zo ya d'auke mu and kinsan dai....”
Layla tayi saurin katseta ta hanyar d'aga mata hannu,cikin yatsina fuska ta isa wardrobe tana d'aukar kaya tana cewa;
“Ni duk gashi nan kinja min wani komawa Nigeria, komai zaka yi ana sama ido ba wani freedom duk abi a dameka.”
Tayi maganar tana cillo kayan da zata saka a kan gado,Basma ta kalleta sama da k'asa sannan ta zuro kafafuwanta itama ta shiga bathroom ba tare da ta kuma kallon inda layla take ba.
Sai misalin k'arfe 3:15pm daddyn Basma yaje cikin University d'in su apartment d’insu ya nupa suna zaune shi kawai suke jira dan haka suna ganin shi suka tashi bare ma Basma da gudu taje tare da fad'awa jikinshi tana murna kamar yarinya k'arama.
“Daddy I love and miss you.!”
Basma ta fad'a tana d'agowa daga jikinshi,yayi murmushi kawai tare da kallon inda layla take tsaye sai faman nok'ewa take yi kamar ta Allah.
“Daddy ina yini?”
Layla ta fad'a cike da ladabi kai kace bata aikata wasu abubuwan,amsawa daddy yayi tare da tambayar su karatu daga nan suka wuce inda suka ajiye trolley bag d'insu aka zuba cikin taxi suka wuce airport, karfe 4:00pm dai-dai jirgin su ya d'aga zuwa Nigeria, inda ya sauka garin abuja daga nan suka wuce kano ta dabo jallah babbar hausa bayan sund’au awanni goma shabiyu asararin samaniya
*KANO*
Suna sauka driver yazo ya d'aukesu Amma sai murna take ta kuma k'agara taga Basma matar prince sarkin gobe. Suna shiga kuwa yayunta da k’annenta da 'ya'yan yayan daddyn ta duk suka fito suka yi mata oyo-yo,farin ciki ya cika Basma har ta manta tana cikin damuwa.
Bayan sun zauna an huta tayi wanka ita da layla suka zauna a k'atan parlorn su Ana ta hira har bayan asubah kasancewar hud’u suka iso na dare sannan kowannensu ya tafi makwancin sa wanda Basma da layla d'aki d'aya suka zauna,kwanan su biyu sannan Amma ta samu damar keb’ewa da 'yar tata can cikin bedroom d'inta,kallonta tayi cikin kulawa sannan Amma tace mata;
“Basma ya yareemah Aliyu hydar d'in komai yana tafiya normal ko?!”
Kuka Basma ta saki tare da fad'awa jikin Amma bubbuga bayanta Amma keyi cike da tashin hankali,har sai da Basma taci kukan ta sannan tayi shiru cikin ajiyar zuciya take fad'in.
“Amma ni yanzu bana son shi I hate him,.. Ya...ya yama za'ai dan wulakanci tunda be sanar min ba sai yanzu zai ce min mu biyu zai aura? Ni dai Amma ku gaya musu na hak’ura na barwa cousin d'in tashi suje can su k’arata.”
Murmushi Amma tayi irin nasu na manya, juyo da fuskar Basma tayi suka kalli juna cikin ido Amma ta sauk'e ajiyar zuciya tace;
“Ashe Basma ke sakarai ce?a haka kamar wayayya ashe kawai a fuskar kine toh bari kiji mahaifin Aliyu hydar ya nemi yayi aure ne saboda yana son ya gaji sandar shi,idan baki san matsayi da darajar sarauta ba ina son kije kinemo tarihinta.Ashe bakya son ki zama matar sarki?,
ki samu d'aukaka ta musamman kuma gashi kinyi sa'a shine da bakin shi yace ke yake so yake buk’atar aura?sai kinyi hak’uri koda kin aure shi saikin daure domin Allah ne ya yarjewa maza yin auran mata har hud’u kinga kuwa sarakuna ma harda k’arin k’wark’warori sukeyi,ke ba abin dad'in ki bane kije a matsayin uwar gida a gurin shi ba?Idan mafarki kike Basma ya kamata ki dawo cikin hayya cin ki don k’arin mutuncinki ne da namu baki d'aya.”
A hankali Basma ta dinga sauke ajiyar zuciya cikin karayar da kai ta kalli mahaifiyar ta idanuwan sunyi ja tsabar kukan da tayi tace;
“Amma wancan fa daban,wannan fa at d same time za'a d'aura wannan ai cin mutunci ne ni dai gaskiya na hakura.”
Tayi maganar cikin sanyi kai da kaji kasan kawai na kishine,Amma ta mik'e tsaya tare da fad'in;
“Toh shikenan bari naje na sanarwa da mahaifin naki sai ya sanar musu kinga kinyi asarar matashin saurayi sarki mai nutsuwa dan nima nasa an yi min bincike akan shi.”
Tana kaiwa nan tabar d'aki yayin da tabar Basma da fad'awa zuzzurfan tunani ta dad'e a gurin kafin ta koma gurin layla ta fad'a kan bed tare da sakin wani kukan dan ta kasa hak’ura gani take yi tamkar wulak’anta ta yake shirinyi.muryar layla ce tasa ta tsaida kukan da take;
“Your sugar boo ya bugo miki sai dai na d'aga nace mai kina tare da mumcy d'inki,idan kinga zaki iya toh daya bugo ki d'auka kar ki tsaya kishi wallahi ya tattara ya barki gabaki d'aya”
K’in amsawa layla maganganunta tayi itama bata sake mata magana ba ta cigaba da sawa faratanta jan farce,ba dad'ewa kuwa sai ga shi ya sake kiran ta taki d'auka sai da takusa yankewa sannan ta d'aga tana yatsina fuska;
Duk suka yi shiru shi yareemah Aliyu hydar kambun mulkin ne ya motsa ita kuma tsananin haushin shi da take ji ya hanata yin magana,sai da suka dad'e a haka shiru ba magana sannan taji yace;
“Okay fine,bye!”
Yana kaiwa nan ya katse kiran Basma tabi wayar da kallo,wani guntun text message taga ya turo mata;
“Zan dawo gobe.”
Tunani ta fara yi,
“Ina zai dawo London?oh no ni ai na dawo kuma be saniba”
Samun kanta tayi da kiranshi,kamar bazai d'aga ba sai taji ya d'aga tare da yin shiru kamar yadda yayi mata d'azu,cikin muryar alamun yin kuka tace mai;
“Ina kano na dawo gida.”
Yareemah Aliyu hydar ya sauke ajiyar zuciya,cikin daddad'ar muryar shi taji yana cewa”
“For real kina Kano? Oya send me your home address asap,inason gobe nazo insha Allah”
K’it yakatse kiran,tana jin yace zai zo ta zabura ta mik'e da sauri,wani farin ciki ne ya saukar mata ta ruga da gudu tayi wajan Amma,rungume ta tayi cikin farin ciki tamkar ba ita bace ta gama kuka ba,Amma tace;
“Karfa ki kayar dani Basma,me aka gaya miki haka yasa ki farin ciki a cikin zuciyar ki?!”
Amma tayi maganar tana dafa saman kujera dan sauran kiris Basma ta kaita k'asa.Murmushi tayi sannan ta kamo hannun Amma ta rik'e gam tana cewa;
“Amma gobe zai zo, yace min zaizo na tura mai da address.!”
Cikin rashin fahimtar maganar ta Amma tayi ajiyar zuciya tana fad'in;
“Waye kuma zaizo Basma?!”
“My prince...!”
Ta fad'a tana rungume hannu a k'irjin ta kai da ka ganta kasan tana cikin farin ciki marar musaltuwa Amma tayi mata wani irin kallo bayan ta tab'e baki tana kallonta tace;
“Au zaki aure shinne? Ni da har naje nasanar da daddyn ku cewar kinfasa auran,kuma inajin ya sanar da kawun mahaifin Aliyun ta yiwu akan zancen yace miki zaizo.”
Amma ta fad'a tana k'ok'arin barin wajan Basma ta zaro ido tana bin Amma tana cewa,
“Kai Amma nifa bada gaske nake yiba wallahi ina...ina...inason abuna fa ya zaki min haka?!”
Tayi maganar cikin inina kamar zata saki ihu,ita kuwa Amma tayi wucewar ta bedroom cikin rashin damuwa take cewa;
“Ah toh gani nayi Basma kina neman maida mu k’ananan yara,kinga maganin kada ayi toh karma a soma dts y.”
“Nashiga uku Amma ya zanyi? I swear I love him shine son raina Amma kitausayamin koda na fad'a ma lokacin kishi ne dan Allah ki....”
Amma tayi saurin tsayar da ita ganin duk ta damu sannan tace;
“Lallai to ni wasa nake,nasan dama k'arya kike kina sonshi kawai kishi ne ya rufe miki ido, yanzu sai ku fara shirya-shiryan tarbar shi.”
Farin ciki ya kuma dirarwa Basma ranar haka ta yini tana nishad'i ita da sauran yara aka hau gyara da tanadar abubuwan da za'a sauki yareemah Aliyu hydar....,
_*BORNU (SHEHURI)_*
*M*aimartaba ne zaune a cikin parlorn shi gefen daman shi hajja yakolo ce hagun kuma hajja gajiram ce, kowacce sai faman shan kamshi tak'eyi shi kam yayi shiru dan jira yake ya gama karantar fuskar kowa sai dai hakan ya tagayyara domin kowacce sai faman hura hanci take,kishingid'a yayi akan tumtum dake kusa dashi sannan yayi gyaran murya yana kallon kowacce ya fara musu magana;
“Inason in shaida muku da cewar d'anku zai yi aure kwanan na,sai ku fara shirye-shirye domin mata biyu zai aura a lokaci guda.”
Gabaki d'ayan su saida suka nuna razana zuciyar su na bugawa hajja yakolo ce ta samu damar yin magana cikin rawar baki had'a da inina tana kallon maimartaba tace;
“Rankashi dad'e wa...wa...wane d'an namu a ciki?!”
Batare da yakawo komai cikin ranshi ba yace;.
“Yareemah Aliyu hydar mana, shine zai yi aure kuma su biyu zai aura sai dai d'aya ce zata tare k’aramar kuma sai ta kammala secondary school insha Allah.”
“Yareemah Aliyu hydar kuma? Ahayyeee nanaye lallai sai yanzu na gane nufinka,dama tuncan nasan baka k’aunar yareemah babagana idan ba haka ba ai shi yakamata ayiwa tunda ya girmewa Aliyu nesa ba kusa ba toh wallahi da sake dan wannan nuna banbanci ne”
Hajja gajiram ke ta faman jaraba ta inda take shiga ba tanan take fita ba,bin ta kawai maimartaba yake da idanuwa ba tare da yayi magana ba,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru tana hucci tamkar wadda tayi uban gudu. Hajja yakolo ce ta tab'e baki dama ita sai taga hajja gajiram tayi abu tukunna take yi saboda karta rasa me goyan bayanta dan haka yanzuma tana yin shiru ta karb'e zancen;
“Haka ne kam wallahi yayya dama an dad'e ana 'yar wariya a gidan nan,toh wallahi a dinga yi ana duba gaba dan in yau anyi abu anji dad'i toh na gobe baxai yiba garama a duba kodai a had'a su auran ko koma shi Aliyu yayi hak’uri ayina babagana tunda shine magajinka indai da gaskiya da kuma adalci...”
“Ke ma dai kya fad'a mai.”
Cewar hajja gajiram tana karkad'a k’afarta sai faman huci take dama abinka dame jiki tabarakallah Masha Allah. Sai da ya gama jin ta bakin su sannan ya kallesu cikin salo na manyantaka ya fara magana;
“A duk cikin tsarina bana yanke hukunci koda a cikin yaranane sai na bawa kowa hakk'insa ke gajiram idan kinyi k’arya yanzu a gurin mahaliccinmu ba'ayi sau nawa ina kiranki keda babagana akan maganar yayi aure? Sau nawa nake ce miki idan beyi ba da kaina zan zab'a mishi mata dake da shi kuka nuna min ku bayanzu ba,shi cewa yayi min ma dakyar idan zai yi auran saboda bashi da burin ajiye mata,amma wai yanzu ke zaki min maganar cewa sai an jira babagana yayi aure sannan Aliyu hydar zai yi saboda ni banda iko akan ku ko?!”
Suka yi tsit kamar ruwa ya cinye su yayi murmushin takaici tare da ci gaba da magana;
“Amman da yake ba kuda adalci ni zaku cewa na fiye san kai,toh ku gaya min ta wanne fanni nake muku rashin adalcin?!”
“Oho dai ai kowa ma yasa ni...!”
Hajja gajiram ta kuma fad'a,ganin suna neman tayar mai da hawan jini ne yasa shi cewa;
“Toh dai na fita hak’k’inku na sanar muku,zai yi aure acikin watan nan kafin ya dawo daga k'arasa clearing d'in project d'inshi nake so akai kaya ayi duk wasu abubuwan da za'ayi,daya dawo sai d'aurin aure.koda baku tambayi wad'anda zai auraba dan karkuce ba'a sanar muku ba to ba kuwa bane wadda ta kasan ce *SON RAN* shi a kano iyayenta suke,sai kuma ta biyun da takasan ce *ZAB'IN IYAYE* wato Aminatu 'yar gidan Baffan su wato kawu Mai Alooma Ghaji,karku ce ban gaya muku ba ku tashi kuje ina buk’atar hutu.....”
Ganin ya dafe k'irji yasa hajja yakolo saurin mik'ewa tabar parlorn da sauri sannan hajja gajiram ta zabga wani mugun tsaki ta mik'e itama tabar parlorn tana maganganu had’e da lailayo ashar ta d’urawa hajjagana da zuri’arta kaf a zuciyarta,
girgiza kai kurum maimartaba yayi tare da yi musu fatan shiriya nan da nan ya fara tari wanda dai-dai lokacin Hajjagana (Ammin su hydar) ta bugo mai waya.Da kyar ya iya d'agawa duk da haka yana yin tarin tanajin shi ta dinga mai sannu yana amsawa da kyar kafin wasu 'yan mintina tarin ya lafa mai Ammi tace;
“Sannu ka d'an sha ruwa mana.”
Sai a lokacin ya juya ya d'auki cup tare da tsiyayar zam-zam dake gefansa yayi basmalah yasha,
“Na gode matar kwarai,Allah yayi miki albarka.”
Maimartaba ya fad'a bayan yasha ruwan zam zam d’in cikin jin dad'i Ammi tayi murmushi tare da cewa;
“Amin nagode Abu Hydar.”
Suka d'an tab'a hira duk akan yadda tsarin bikin zai kasance kafin su ajiye wayar kowa na farin ciki da yadda hirar ta kasance musu.
_*KANO_*
Flight yabi ya sauka a Malam Aminu Kano International airport, already dama daddyn Basma ya riga ya tura mai da driver dan haka suna sauka driver yayi wa yareemah Aliyu hydar waya suka had'u ya d'akko shi,basu tsaya a ko'ina ba sai a unguwar sultan road dake nassarawa GRA a kantameman compound d'in gidan su princess Basma Lol.
Idanta kyar akan motar ta window har ya zuro kafafuwan shi ya fito,tana ganin shi taji wata zazzafar k’aunar shi ta kuma cakar mata zuciya,
“Hmmm yama za ayi na iya rabuwa da sugar boo?haba this can't be happening”
Ta fad'a a fili tana murmushi,Yayan ta ne Usama yayi mai jagoranci zuwa cikin sitting room d'in da aka k'ara gyara shi sai kamshi yake tamkar company d’in yin turaruka,yareema Aliyu hydar kenan sai wani taku yake tamkar yana jin kyankyami ya k'arasa ya zauna bayan sun gaisa da Usama wanda zasu yi kai d'aya a shekaru dashi Usama na fita wayar Aliyu hydar ta fara neman agaji yana ganin kiran yayi wani murmushi irin na gefen bakin nan sannan ya d'aga tare da karawa a kunne yace;
“Guy ya?!”
Modu ya d'anyi tsaki kad'an cikeda takaici yace;
“Wai kana inane tun d'azu nake neman ka?!”
Murmushi yareemah Aliyu hydar yayi wanda har Modu na iya jiyowa sannan cikin isa yace mai;
“Kano!”
“What?...!"
Dai-dai lokacin Basma da layla suka shigo cikin sitting room d'in yana jin shigowarsu amma yak'i juyawa harsai da suka k'araso idanuwan su ya had'a dana juna ta sakar mai murmushi tana bin kayan jikin shi da kallo don bak’aramin tafiya yai da gangar jikinta da zuciyarta ba sosai yamata kyau,
Sanye yake cikin d’inkin riga Bauchi style(buhari style)riga da wando na dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya tasha aiki dark color se hular zanna bukhr datai mugun amsan kayan dakuma gashin kansa daya kwanta luff Kai abinde sede afurta kalmar tubarkAllah kawai don d’an sarkin bornu yayi kyau babu k’arya gakuma uban k’amshin dayake tashi daga jikinsa...
“M serious guy,kaje kasamu Mami tarakaka bulabulin ngarnam d’in ko Allah zesa adace”
K’it yakashe kiran yana daria ahankali don sosai yake jiyo k’arar sautin tsakin Modu yasan yanacan yakusa fashewa don haushi,
Team#SRKZB?!
Y,ALIYU(BASMA AUR MEENAH?!)🤷🏾♀
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE*
💖?👨👨👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
_*Home of expert and perfect writers_*
DEVOTED TO:
*XARAH BUKHAR*
TUKWICI:
*TAWAN(Billyn Abdul)&MY YA HAJJA CE*
PARTICULAR THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DOTAS:
*BITTI FEEDHOM&DOTA BILLY S FARI*
nanahafsat.wordpress.com
*48/49*
K*wance yake daga shi sai boxers da vest yana ta bacci kawai yaji ihuu kamar a cikin mafarki da sauri ya mik'e zaune yana neman jallabiyar shi amma bata nan can ya hangota jikin hanger arataye yayi saurin rungumar pillow yana kallonsu ranshi a b'ace,gadon suka hau tare da cewa;
“Yaya Aliyu good
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 35