Modu ganin layla har suka fara soyayya harma yau ya aureta dan da ban kaita k'asar waje karatuba ba yadda za'ayi layla ta samu wayewar da ta samu har mutum irin wannan ya ganta yace yana sonta ba, dan haka nazo idan kuma rashin kunya zaka yimin bismillah d'an halak kafasa...!”
Shiru Muhammad hadee yayi ganin yadda take faman d'aga murya,inna ce tayi magana cikin b'acin rai tace,
“Bake ce sanadi ba wallahi,dan tunda Allah yayi laylatu itace Matar Muhammad toh ko tana kauyan kayayau sai Allah ya kaishi can ya aurota, dan haka kidena cewa haka idan masu ilimi suka ji kina cewa haka toh zaki zubarwa da 'yarki mutunci musamman idan suka gano cewar ke d'in mahaifiyartace.”
“Mtwww sakarci kawai.”cewar ummah had’e da watsa hannu baya alamar tofin ala tsine.
Ta fad'a tare da komawa ciki inda sauran suke,nan inna ta dinga bawa Muhammad hadee hakuri sannan ya fita zuwa harabar gidan ita kuma inna ta koma ciki tana yiwa al'amarin addu'a.
Shirye shiryen wushe wushe ake tayi wanda xa’a gudanar a k’aton wurin taro da akayishi na musanman domin bukukuwan cikin shehurin bakin yareemah babagana yak’i rufuwa sekace gonar auduga Allah Allah yake agama taro a dank’amai amaryar sa Modu kuwa gaba d’aya hankalinsa atashe yake ganin k’iri k’iri sarki Aliyu hydar yacire Ammi yajingineta amatsayin mahaifiyarsa sam daka ganshi kasan baya cikin hayyacinsa,
Shiga ta alfarmar rantsattsiyar laffaya akaiwa amaren biyu billy da layla aunty yaruwaiya itace ke nad’a masu shar suka fito da kyansu amarya billy shigar lace tai blue color aka nad’a mata laffaya peach itakuma layla maroon ne se laffayarta gold color beela’s touch itace tai masu makeup abinde se wanda yagani kawai,
K’arfe takwas aka fara gudanar da wushe wushen angwaye Modu da yareemah Babagana shiga sukai cikin dakakkiyar shadda golden datasha aiki brown sun matso kyansu yan uwa da abokan arxiki kuwa shigar dangasho sukai da mandil layla a d’arare take komai samshi hankalin Modu ma ba akanta yakeba su Basma sune k’irjin biki ankasa zaune se hidima ake,har aka gama duk wata al’adar da ake a taron aka watse bayan anci ansha anwatsa dollar anraba savouniers,
Sashena musanman anan aka ware bak’in layla su ummah se gwalli ake ita game ‘ya ita ko layla sam tak’i yarda ma sukeb’e da umman domin yanzu wata wutar haushinta takeji tana k’ara ruruwa a zuciarta na martabarta data rabata da ita yanxu tasan batada wata sauran k’ima ko mutunci a idon Modun,
Modu naganin taro ya watse yasaci jiki yatafi sashen sarki Aliyu Hydar don yaci _*Alwashin_* seya daidaita tsakani Aliyun dasu Ammi....
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_*
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
_Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wani masoyi makarancin son rai ko zab’in iyaye?!ina sonku kuna raina akoda yaushe....!
*61*
*D*a sallama Modu yashiga babban parlorn sarki Aliyu Hydar,xaune ya iske sarki Aliyu Hydar kansa asama da alama tunani yake d’an gyaran murya Modu yai se a sannan sarki Aliyu Hydar yadawo daga duniyar tunanin da yake nannauyar ajiyar zuciya yasauke ahankali ya amsa sallamar Modu tareda gyara xaman kishingid’ewar dayai.
Samun guri Modu yai yaxauna daga kujerar nesa dashi,
“Ranka yadad’e yai k’arko my guy,yerwa nayinka fiye da tunanin mutum”
D’an Murmushin k’arfin hali sarki Aliyu hydar yai cikeda nutsuwa yace,
“Godia nake guy,yaya hidima?!”
“Wannan seku mutumina”
Y’ar daria sarki Aliyu hydar yai,
“Guy kaima kabiyo sahu ai”
“Kaide bari kawai”
Shiru sukayi dukkansu na d’an wani lokaci Modu nata tunanin tayaya xe sako maganar Ammi ahankali yace,
“Da fatan kaje kun sasanta da Ammi”
“Ance maka nayi fad’a da itane??”
“No,yaxa’ai kai fad’a da ita kawaide yadda kake ignoring d’inta hakan be kamata ba”
“Plss let me be Modu,idan Kasan abinda kazo fad’a kenan to xantashi nabar maka wajen”
Shiru Modu yai kawai dan it’s being ages da sarki Aliyu hydar yaki rashi da Modu har ya manta shiru Modu yai cikin sigar jan hankali yafara magana,
“Wata rana wani sahabin manzo SAW yaje wajen manzon Allah sai yace dashi yarasulullahi wayafi cancanta dana kyautatawa sai annabi SAW yace dashi mahaifiyarka sai mu’awiya d’an haidata yasake cewa dashi sai kuma wa?!sai manzo yace mahaifiyarka sai mu’awiya ya k’ara cewa sai kuma wa?! Sai manzo SAW yace mahaifiyar ka,sai mu’awiya ya k’ara cewa sannan kuma wa?! Sai manzo SAW yace mahaifinka,
“Kaga guy wannan Hadiths d’in yana mana nuni da muhinmmancin uwa kaga seda yakira uwa sau uku kafin yakira uba,Guy kada kabari wasu can suk’ara yin galaba akanka su shiga tsakaninka da mahaifiyarka kada kazo kanayin nadama domin idan kace xaka bijirewa Ammi to wallahi Allah baxe barka ba irin wahalar datasha wurin d’aukar cikinka guy kayi tunani akai”
Dan siririn tsuka sarki Aliyu Hydar yaja tareda kauda kansa gefe daga kallon Modu murmushin dayafi kuka ciwo Modu yai ahankali yace,
“Guy kada kabari Ammi taxubar da hawaye akanka domin yadda kake mata xe iya sanyata hawaye kuma hawayen iyaye musibane guy,kaje kanemi gafarar Ammi kasanyata daria guy please i beg of you baxan mantaba if you can recall a islamiyar mu then akwai wani hadiths da akai mana shi shima wani mutumine yazo wajen manzo SAW seyace dashi ni naxo natafi yak’i tare dakai amma nabar iyayena sunata kukan rashina atare dasu sai manzo SAW yace koma wajen iyayenka kasanyasu dariya kamar yadda kasasu kuka domin kukan iyaye yanasa al’arshin Allah ya raurawa,
“Kaga kenan idan har iyayenka nafushi dakai to Allah ta Allah yana fushi dakai which means rayuwar ka ta tagayyara kenan idan har ba neman afuwarsu kai suka yafe maka ba,this is so not you kadawo guy d’inka da mukasanka dashi me son iyayensa musanman mahaifiyarsa wanda ke son yan uwansa yakeson masu sonsu yake kuma kyauta ta masu kaji?”
Shiru sarki Aliyu hydar yai beyi magana ba yade sunkuyar da kansa k’asa,
“Naga kamar kana tunanin duk abinda nafad’a k’arya nake to bari nasaka maka wa’azin wani mufti kilan inkaji daga bakinsa kayi gaggawar xuwa wajensu domin rok’ar yafiyarsu” Modu yafadi haka had’e da d’akko wayarsa yasa wani audio nawani malami dake magana akan,
“MAI SAB’AWA IYAYANSA TO YAYI KUKA DA KANSA”
Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika alakarsa da iyayansa.Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda yasa agaba ya duba alakarsa da iyayansa,Duk wanda yaga baya jin dadin rayuwar sa to ya bincika yadda yake zaune da iyayansa
duk wanda yaga mak’iya sun rinjaya a kansa ya tintibi zaman sa da Iyayansa.Sabawa iyaye yana jawo dukkan matsala a rayuwa kamar,
_Sa iyaye kuka,saboda bakin ciki
_Yiwa iyaye tsawa,ko hantara ko tsaki ko gunguni,
_Kosawa da iyaye da gajiya da su ko tsanarsu
_Daurewa iyaye fuska ko sha musu kunu
_Yiwa iyaye kallon raini da hadarin kaji
_Yiwa iyaye tsiwa,da daga murya akan su
_Kushe iyaye,da daukar su gidadawa.
_Kauda kai,idan iyaye suna magana .
_Fifita mata akan iyaye
_Fifita Abokai akan iyaye
_Jawowa iyaye matsaloli da rigingimu
_Gulmar iyaye
_Zagin iyaye ko jawo musu zagi
_Damun iyaye da kade kade da wake wake
_Rashin shawara da iyaye
_Kauracewa iyaye
_Tsagalgalewa iyaye da rashin kunya
_Iyaye su dinka tsoran dan su
_Kin amfani da sunan iyaye
_Dukan iyaye da gajiya da su
_Fatan mutuwar su
_Yi musu gori dan kayi wani abu.
_Boyewa iyaye samu ko wadata,
_yiwa iyaye karya da Karyata iyaye
_Yiwa iyaye sata,
_YI musu gori
_ Yin musu dasu ,
_Rashin yi musu addua
_ Barin iyaye cikin kunci da wahala.”
Audio d’in na k’arewa Modu yakashe wayar ahankali yai ajiyar zuciya tareda fad’in,
“Allah kasa mu gama da iyayanmu lafiya,kayi musu rahma kamar yadda suka yi mana tarbiyya tun muna yara Ameen,ni xan wuce Guy Allahu ya warware duk abinda akai maka domin ba k’aramin cutar ka akaiba believe you me akwai abinda aka maka kuma koba jima koba dad’e sarkin sarauta gagara misali xe karya koma menene ya bayyana abinda ke b’oye”
Yana gama fad’a ya mik’e yai fitar sa batare da jiran cewar sarki Aliyu hydar ba,Modu nafita sarki Aliyu Hydar yad’ago kansa daga sunkuyen dayai ahankali yashare hawayen dake tsiyaya a idanunsa sannan ya maida kansa sama yacigaba da tunanin dayake.
<><><>
Washegari da safe jirginsu kiara matar Modu ya iso yerwa motoci atawaga sukaje d’akkasu ‘yan rakiyar tata bawasu masu yawa bane k’awayentane su bakwai se aunties d’inta su uku daga dangin mahaifinta,
Liyafa sosai aka had’a masu su kansu seda sukasha jinin jikinsu suka kuma rena kansu don basuyi xaton haka dangin Modun suke da had’uwa ba,cima kala kala aka cika masu akan makeken dining table din sashen da aka saukesu sunci sunsha sun kuma gyatse domin duk irin cimarsu aka tanadar masu,
Kamar ko yaushe aunty yaruwaiya itace ta shirya Amarya kiara cikin kayan al’adar wushe wushe tayi kyau babu k’arya domin komai black and gold akai mata abinka da farar mace alkyabbar mata dukda ba fara bace kalar turawa amma se kayan suka k’ara haskata tayi kyau.
Duk wata al’ada da ake seda akai mata sosai abun ya k’ara burgesu itada yan uwanta da k’awayenta domin sosai ake haba haba dasu an karbesu hannu dubu bama biyu ba kid’an ganga kuraa kuwa family d’inta suka dage suna cashewa sekace sun iya sosai akaci daria aka kuma yi kulu washrabu ga savouniers kala kala abinde se wanda yagani kawai.
Washegari yakama ranar lahadi kenan da safe akai bud’ar kan amaren uku wato bilkisu da kuma kiara se layla hak’ik’a sun sami abin arziki dayawa daga dangin maxajen nasu kama daga turamen xannuwa da turaruka na ruwa dana turarawa ciki harda awawwarayen gwal kyauta daga mahaifiyar Modu tafiyayyu tundaga indimi zuwa shehurin abinde se kallo.
K’arfe biyu na rana aka fara shirye shiryen kai amaren gidajen nasu Amarya bilksu matar babagana ita aka fara kaiwa domin ita a shehurin xata xauna tank’amemen gidah na bene daga d’ayan sashen akaiwa babaganan da matar tasa babu abinda babu acikin gidan tabbas naira tayi kuka.
Bayan ankai bilksu aka zarce da layla da kuma Kiara gidajen su dake unguwar damboa road wanda mai martaba mai murabu ya bashi kyauta don farin ciki seda Modu yai kuka ta bayan gidan Ammi gidajen suke gidaje ne manya maka maka guda biyu kowanne da gate d’insa na layla gate d’inta nata baya ita kuma kiara nata gate d’in tagaba yake unguwa d’aya suke amma hakan da akai seya xamto kowanne layinsa daban wani baxe tab’a had’uwa da d’an uwan saba domin fasalin kowanne da inda yake kalla,
Ankashe dollar domin su kansu family d’in kiara sunyi mamakin gidan ace k’erarran gidah haka akuma nigeria sekace a Washington DC abinde se san barka kawai,kowacce da akwatunan ra’aki da kususuram aka kaita kamar yadda al’adar take.
Se dare sannan kowanne y’an uwansa suka tafi bayan inna taiwa layla wa’azi me ratsa jiki tareda sake jan kunnanta kan rayuwar gidan miji,seda Modu ya mula yasha iska sannan yatafi gidajen nasa gidan kiara yafara zuwa tukun ya ajiye mata irin cimarta sannan ya wuce gidan Layla hannunsa d’auke da ledoji se bulbula k’amshin oud yake bakinsa d’auke da sallama yahaura sama yatura d’akin dayake tsammanin natane ciki yahangota akan katotan Italian royal bed kanta asunkuye sanye take cikin alkyabba kalar sararin samaniya....
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_*
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
Wannan shafin nakine *Ummu Abrar*,ked’in tadabance azuciyar xoxo,Rabbi yabar zumunci Ameen..!
*62*
K’arasawa cikin d’akin Modu yai bakinsa d’auke da sallama cikin sanyayyar muryarsa ahankali layla ta amsa,gefan inda take yaxauna yana d’an duban wristwatch d’in hannunsa ahankali yace,
“Kinci abinci?!”
Kad’a kai tayi alamar eh gaba d’aya jikinta rawa yake taso tabashi daria yabasar yai murmushi kawai k’asa yasauka yadudduba harya gano kitchen komi anjerashi yadda yadace plate yad’akko da serving spoon da cup yad’auraye yakoma saman tananan inda yabarta bubbud’e ledojin yashigayi yaciro chicken wings d’in da akai masu recipes na musanman gefe d’aya kuma French flat bread ne da sauce d’insa zuxxuba mata yai yatura gabanta had’e da tsiyaya mata fresh milk ya ajiye mata with care yace,
“Dauka kici”
Batai musu ba don balain tsoronsa takeji dannawa cikinta tashiga yi harseda yaga taci sosai sannan yace tabarshi haka ya nannad’e sauran yasa a mini freedge d’in dake gefen d’akin cikeda nutsuwa yace,
“Tohm layla kamar yadda kika sani ku biyu na aura abokiyar xaman ki da ita aka fara d’aura mun aure ma’ana ita nafara aura kafin ke yaxama dole kibata girmanta kuma itama dole tabaki naki,
“Kowacce xanmata kwana bibbiuu kamar yadda na tsara kuma Insha Allahu xanyi ko’kari na kwatanta adalci atsakaninku,don haka idan kinada magana toh seki fada saboda xankoma d’ayan gidana yanxu”
Kad’a kanta tai ahankali tace,
“A’a”
“To shikenan ki tashi kirage kayan jikinki Kiyi alwala seki kwanta kinji??”
“Toh”
“Yawwa toh mukwana lapia”
Yana k’arasa fad’a ya fice daga d’akin ya kulle entrance door na gidan ma rufe ta yai da extra key d’in sannan ya jaddadawa mai gadin kan ya kula masa da gidan sosai...
Gidan kiara ya koma kwance yasameta hannunta d’auke da iPad dinta tana Skype da mamanta seda yabari suka gama sannan yabata light peck a lips d’inta,
“Babe”
“Uhm hun”
D’aukanta yai yad’orata a laps d’insa yana shafa bayanta kunnenta yad’an cija tasaki k’ara murmushi yai yad’auketa se band’aki wanka sukayo shikuma yayo alwala ya hau kan sallaya yana sallar nafila se binsa take da kallo ganin yadda yake sallar bayan yagama yadawo kusada ita ya janyota romancing d’inta yafarayi ahankali haryai addu’ar saduwa da iyali sannan yashiga babban aiki ya maida kiara babbar macace cikin k’ank’anin lokaci,
Kowannensu yashiga bak’on yanayi dagashi har ita abinka da ba sabunba kafin safiya kiara taraina kuranta shide Modu se sanya mata albarka yake cikin harshen turanci,
Kodah safiya tai shiya k’ara kintsa gidan ya d’auke bedsheet d’in yasa a washing machine yacanxa wani se nannan yake da kiara abinci ma da aka kawo daga shehuri shiyai feeding d’inta sannan yatafi gidan layla gaba d’aya takasa had’a ido dashi shi daria ma take bashi be wani jima ba yakoma gidan kiara lokacin yan uwanta har sunxo xasuyi mata sallama alheri sosai ya masu sannan mota tajasu se airport sukabar kiara hawaye kwance shab’e shab’e kan fuskarta dakyar Modu yashawo kanta tai shiru....
_*Shehuri_*
Babagana kuwa kwanan bak’in ciki yai sam billy tahana shi kanta magiyar duniya yayi tak’i ko bari yaxo kusa da ita dayayi yunk’urin hakan xata fasa masa ihu sekace zaucacciya saboda tsabar yasa abun arai har kuka yayi don ganin yadda bilkisun ke fasa masa ihu kamar taga dodo atak’aice de a k’asan floor ya kwana abinda be tab’a yiba tunda uwarsa ta haifeshi kodah safiya taima duk zuciyarsa ba dad’i haka ya dinga zaxxagewa mutane kwandon masifa ciki harda hajja gajiram falmata kanwarsa kuwa rabon mari tasamu don sharara mata mari yai kawai don ta tambayeshi meyasa ransa yake a b’ace,
<><><>
Zaune Meenah da Ammi suke Ammi na had’a wani khumra cikin kwalbarsa Meenah kuma a sunkuye take tana gyara farcenta da nail set jefi jefi suke d’an tab’a hira da Ammi,
“Meenah,Meenah,Meenah”aunty yaruwaiya ce ke dokawa Meenah kira daga sama,
“Na’am aunty ganinan”Meenah ta amsa tanad’an d’aga muryarta yarda aunty yaruwaiyan xatajiyota
Mik’ewa tai tana karkad’e doguwar rigar dake jikinta samfarin morocco design Ammi ce tad’an dubeta cikeda dattako tace,
“Bitti kingama had’a kayan naki ko?!”
“Eh Ammi nagama shoes d’inane kawai ban mayar ba”
“Okay yawwa suma ki kintsa komai saboda gobe idan Allah ya kaymu da safe xamu koma gidah”
“Toh Ammi”cewar Meenah sannan ta haura sama wajen aunty yaruwaiya,
D’akin da aunty yaruwaiya ke ciki ta tura da sallamarta aunty yaruwaiya naganinta tamik’e daga xaunen da take ta nupota tana tafa hannuwa cikin sauri take fad’in,
“Isauri isauri kid’an gyaggyara gurin Aliyu xakije yanxu”
Ido Meenah ta gwalalo scene d’in rannan tatuno tuni tafara girgiza kai tanaja da baya tace,
“Uhm uhm Aunty baxan iyaba plss dan Allah”
Tsaki aunty yaruwaiya taja cikeda takaici tasake sakin wani tsakin sannan tace,
“Kinsan halina de sarai tunmuna sheda juna nidake kiyi abinda nace Meenah,kinsande badon wani abun nake saki ba donki janyo manashi yadawo ne kinade gani ga mahaifiyarsa nan ko kallo bata ishesa ba muma yan uwansa kina kallo magana bata had’amu ciki hardake matarsa wanda daba haka yakeba,inba xakiba toh Seki xauna ai mutaru bak’in ciki duk ya kashemu”
“Toh aunty ni tsoro nakeji kobashi bane..,”
Bata k’arasa ba aunty yaruwaiya ta katseta,
“Toh seki xauna ai mutaru mu jambare ba wan ba k’anin kina ji kina gani wannan bulunbotin xata kwace miki miji sakarya kawai”
Me Meenah ta tuno oho cikin sauri tace,
“Aunty xanje naji xanje”
Cikin sauri yaruwaiya taja kunnenta tashiga rad’a mata abinda xata masa ta k’ark’are da,
“Kuma kiyakice wannan kunyar ki ajiye aside nagaya miki duk wani shunning d’inki daxeyi karki yadda ki tabbatar kinsashi kasala hope m clear?!”
Kad’a kai Meenah tai alamar eh,
“Yawwa tawajena wuce kije karma kibari Yayya talura da inda xaki”
“Toh”kawai Meenah tace sannan tasauka k’asa tanupi apartment d’in sarki Aliyu hydar hamdalah tai ganin daga shi se shamakinsa yana gyara masa xaman rawaninsa,
Da sauri shamakin yagama gyara masa yafice bayan ya kwashi gaisuwa awajen Meenah kallon tara saura kwata sarki Aliyu hydar yashiga yiwa Meenah wadda tai kamar batasan yana yiba tashiga takun k’asaita harta isa gabansa tsoro fal zuciyarta tadake kawai ta xauna akan cinyarsa yabud’e baki xe magana taita maxa tarufe bakinsa sweet and passionate French deep kiss tashiga bashi hannunta d’aya na shafa quarter million sajensa,gaba d’aya sarki Aliyu hydar yakasa komi sekace mutum mutumi lalle yarinyar nan haka kawai yake maimatawa cikin zuciyarsa seda tai mai isarta sannan tacire bakinta tawani narke idanuwa tana kallonsa cikin zaxxakr muryarta tace,
“Ran sarki yadad’e ashe bamu gaysa ba?!toh Nda rufto(good after noon)”tafad’i hakan tareda sa hannu tana xagaye cute lips d’insa,
Gefan kunnansa taja cikin rad’a tace,
“I just couldn’t get enough of this cutest lips of yours”
Mutuwar xaune sarki Aliyu hydar yayi duk wani rashin mutunci dayai niyyar yi mata yakasa yadda take motsa baki kawai yake kalla beyi wata wata ba yajanyota yashiga bata hot kisses tin tana enjoying harta gaji tashiga tureshi Ina gogan naku yayi nisa bayajin kira bemasan tanayiba yashiga yamutsata son ransa...
Cikin wahalalliyar murya ya k'ira sunanta yana shafar tulin gashin kanta,
“Meenah!”
“Uhmm.”
“Amm waye yake turoki gurina da wad'annan abubuwan?!”
“Ba kowa ni dai kawai ka barni na tafi wallahi duk kasa k'irjina sai ciwo yake min kawai.”
Tayi maganar tana cuno baki kamar zata yi kuka, bin ta kawai yake da ido yadda yaga tana magana kamar an sanya mata battery can taji ya sake matseta cikin jikin shi dai-dai setin kunnanta yace,
“Yanzu kenan kin waye bakya tsoran yin ciki ko tunda har kinsan irin wad'annan abubuwan da suke sanyawa ayiwa mutum ciki?!”
Zaro ido Meenah tayi nan da nan jikinta ya hau yin rawa ta kasa had'a idanuwa da shi yaukam ta shiga uku aunty yaruwayya ta cuceta tunda duk ita ce ta ce tayi hakan wai za'a k'aramata lada acan cikin aljanna.
“Indai kika kuma zuwa inda nake bazaki kuma komawa gurin wad'anda suke aikoki ba sai nayi miki ciki hope m clear?!”
Kasa amsawa tayi dan tsananin firgita da tsoro, janyo fuskarta ya kuma yi yana kallon cikin idanunta yace mata,
“Tashi ki gyara min rawani na yadda kika ganshi idan ba haka ba kuma yanzu kiga k'aryar fitsararki...”
Da rawar jiki Meenah ta mik'e hannunta na karkarwa ta fara gyarawa sam hankalinta baya jikinta hakan yasa batasan warware wa takeyi ba sai da taji ya damk'e hannunta sannan tayi saurin kallonshi a tsorace ganin abinda tayi mai yasa ta b'are mai baki ta saki kuka tana bashi hakuri,
“Dan.. Dan... Dan Allah wallahi ban..ban san haka yayi ba walla....”
Saurin sanya yatsan shi yayi a bakinta,cikin sanyin murya yace mata,
“Get out now..!”
Ai kafin ma ya k'arasa ta fincike hannunta,da gudu tabar gurin tana kuka mai cike da takaici ta kuma sa a ranta duk abinda aunty yaruwaiya zata yi mata bazata k'ara zuwa gurin shi ba.
Tana fita cikin rashin sa'a suka had'u da Ammi,ganin tana kuka yasa hankalinta ya tashi tayi saurin rungumota jikinta tana lallashi murya k'asa-k'asa Ammi take tambayar ta abinda aka yi mata,
“Ammi ya hydar ne kawai..kawai dan..dan naje gurin..”
Bata kai k'arshe ba aunty yaruwaiya tayi saurin toshe mata baki wadda k'arasowarta kenan gurin dama tafiya tayi d'akko ruwa.
“Ammi rabu da ita zanje inji abinda aka yi mata yanzu.”
Jan hannun Meenah aunty yaruwaiya tayi ita kuma Ammi ta bisu da kallo mai cike da tuhuma, d'aki suka shiga a bakin gado duk suka zauna Meenah sai turo baki takeyi tana d'an hararar aunty yaruwaiya sanin duk itace ta jamata.
“Ta gurina ya akayi ne meye labari naga kina kuka?!”tak’arashe maganar tana kanne mata ido d’aya
“Uhmm duk fa kekika jamin yayi ta min abubuwa k'arshema fa cewa yayi idan na sake zuwa gurin shi sai...sai...sai fa yace wai bazan koma gurinki ba sai yayi min ciki uhm..uhm.uhmm.”
Meenah ta k'arasa tana kuka cike da gabunta, wata dariya ce ta kwacewa aunty yaruwaiya dan haka ta dinga yi tana dukan cinyar Meenah,da kyar ta samu dariyar ta tsaya sannan ta kalli Meenah tace,
“Meenahtu tawa ni d'aya, wallahi kina burgeni over kawai dai dan ina son ki k'ara wayewa ne amma da zanso ki tsaya a haka nasan sai kin bawa hydar wahala, any ways kema mace ce.,
“Kin gane ko Meenah wannan duk ba wani abu bane Mu da zamu samu ma yayi miki cikin da munji dad'i kuma Insha Allahu da izinin Allah komai zai warware but yanzun ma bata b'aci ba sai dai Ina son ki dinga yawan yi mishi text message zafafa masu shiga rai na soyayya Meenah zaki sha mamaki nan gaba yadda hydar zai mutu akan sonki,duk da yanzu ya rainaki yana ganin kin mai yarinta baki iya komai ba baki san komai ba Ina son ki nuna mai cewar ba'anan take ba kin gane tawan?!”
“Aunty cewa fa kika yi wai yayi min cikin na bani wallahi bana son ciki shine fa ya sanya Maman Afrah kawata ta mutu wayyo ni nashiga uku ni bazan ma sake zuwa gurin shi ba.”
“Haba tawan me yasa kike haka ne kinga gobe zamu tafi gashi babu wani kwakwaran abu daya shiga tsakanin Ku,kuma ai mutuwa riga ce tana wuyan kowa idan banda abinki ko a d'akin ku waye auta amma ai Amman ki bata mutuba so ki dena ambatar mutuwa sai kin haifarwa sarki Aliyu hydar yara masu yawa wad'anda zai yi alfahari dasu.”
“Ni dai gaskiya wallahi...”
“Wallahi me?!”
Aunty yaruwaiya ta tambayeta ganin sai faman cuno baki Meenah take ganin ta had'e rai tace,
“Amma aunty ai shima sai ayi mai magana amma kullum ni sai ayi tamin yana bani wahala.”
“Toh Zan gaya mai sannan kuma zuwa dare zaki koma duk abinda nace kiyi toh kiyi shi kawai,haka ma duk abinda kikaga yayi miki toh ni nasa shi kuma za'a baku lada mai d'in bin yawa.”
Kad'a kai Meenah tayi jin ance shima za'a mai magana daga nan ta mik'e aunty yaruwaiya ta fara gyara ta cikin kayan kamshi masu sanyaya zuciya,tun abin na bawa Meenah haushi har ta fara biyewa aunty yaruwaiya idan ba'ayi wani abu ba zata ce ayi mata ko tayi da kanta..
_*DAMBOA ROAD_*
Zaune layla take da innah da alama nasiha take sake mata sun dad’e suna magana sannan inna ta k’ark’are da,
“Kibi mijin ki sau da k’afa laylatu don kisani aljannarki tana k’afarsa i nayi bari na bari duk abinda be sa dake ba babu ruwanki ciki kinji de nagaya maki”
“Insha
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 35