Share this page
neman bala...” Dakatar dasu sarki Aliyu Hydar yai yana d’an murmushi ganin fadancin nasu yak’i karewa,cikin sarauta yace, “Ina sarkin fada?!” “Yana waje ranka shi dad’e ko ayo maka iso dashi ne?!Allah ya kara maka lapia?!”cewar jakadiyar tasa.. Jinjina kai sarki Aliyu Hydar yai da sauri ta fice don kiran sarkin fada ba ajima ba jakadiya tadawo ita dashi zubewa sukai a k’asa suka sake sabuwar gaisuwa nan sarki Aliyu Hydar yacewa sarkin fada yatafi da fadawan babagana xe neme su bayan yaji ta bakin uban gidan nasu wato yareemah Babagana.. Kad’a kai sarkin fada yai cikin sauri ya tusa keyar fadawan babaganan uku waje,dukkansu za’ai masu bulala talatin talatin na kai karar da ba huruminsu ba shikuma dayan bafaden dayace a hukunta billy shikuma xa’ai masa bulala sittin da kuma sati d’aya agidan yari bisa ga saurin katse tarar numfashin mai martaba daga furucin daxe yanke lefi na biyu kuma dayace a hukunta billy batare dayai duba da itadin matar uban d’akinsa ba ce hakan yayi nuni da lalle bafaden ba k’aramin lefi yai ba domin ba a yankewa sarki hukuncin daxeyi domin kalmomin da bafaden yai furucin dasu sunyi fatali da kundin tsarin masarautar tun alif shekara ta dubu d’aya da d’ari tara da cassain da bakwai... Bayan fitar su bafaden sarki Aliyu Hydar ya bawa jakadiya izinin fita daga fadar dama sauran dakaran dake tsare lapiar sa fadar takasance daga shi sekuma bilkisu domin shi sarki ne meson sirri bayason ko yaya sirrin cikin gidah yafito wajen masarautar bare kowa yaji.. Cikin muryar sarkin dayasan meyake ya fara magana, “Bilkisu..” Cikin sarkewar murya alamar tsoro tace, “Na’am rankashi dad’e..” “Ko zansan meke faruwa?!shin ina shi maigidan naki yake yanxu?domin ko kadan ban yarda da k’arairakin da suke fada ba” Shiru bilkisu tai tana tunanin ta fada masa k’arya ne kota fad’i gaskia?!yo inma tayi k’aryar ta gudu har gidansu xa’a bita ba ita kad’ai xa’a hukunta ba rankataf din danginta se sun kwashe kashinsu da hannuwansu domin gidan sarauta ba wasa bane gashi rigima ce ta kunnowa kanta da hannunta ba wani ne yasa ta ba.Ta lula sosai cikin shawara da zuciyar ta ta sake tsinkayo muryar sarki Aliyu Hydar, “Bilkisu ina saurarenki..” Wiki wiki tai da idanuwa ta gefan ido tad’an kallo sarki Aliyu Hydar ganin shi da fuskar rahama da alama kuma xeyi saukin kai yasata dan sake rausaya kai cikin muryar tausayi tace, “Ranka shi dad’e ni me lefi ce domin a sanadiya ta ne yake asibiti ynxu..” “Shi wa kenan?!”cewar sarki Aliyu Hydar cikin rashin fahimta.. “Shi...Shi yareemah babaganan” “Ko zansan meyasa tasanadiyarki yake asibiti” “Allah yakara maka lapia ga gafarceni na daga abinda labbana xasu furta saboda hakika yareemah babagana ba mutumin arziki bane” Ware idanuwa sarki Aliyu Hydar yai cikin sauri don sake gasgata abinda tace yace, “Kikace mene??” “Allah ya kara....”saurin katseta yai domin shi bai fiya son irin wannan kirarin fadanci ba, “Ki kirani da sunana pls..” Girgiza kai tai alamar baxata iya ba..cikin murya k’asa k’asa tace, “Ranka yadade hakika yareemah babagana yamai dani gonar sa ya satoni daga gidan mu yana aikata masha’a dani,yana zina dani shine yake tamin haddina ya rabani da mar...” “Sshhhhh”sarki Aliyu Hydar yai hanxarin katseta ta hanyar d’aga mata hannu.. Zuba mata idanuwa yai yana binta da kallo sosai cikin zuciyarsa kuwa bansa kalma d’aya ba abinda yake maimaitawa, “Ko batada hankaline?” Yana kallonta yana maimata kalmar ganin yaya mata da mijinta zata dinga kiransa da wanda yaketa mata haddi ya rabata da martabarta bayan sadaki ya biya ya aureta dubban mutane suka shaida haka?!” Sake jinjina kai yayi lalle biri yayi kama da mutum tabbas batada hankali inba tabuwar hankali ba abinda xesa taiwa mijin nata gula aciki dahar hakan xesa akai shi asibiti bayan nan kuma takira mijin nata da suna mazinaci wanda ya rabata da martabarta yaketa mata haddii.. Sake girgiza kai yayi a karo na uku yad’au xancen Bilkisun ya ajiye a matsayin zancen mahaukaciya wadda hankalinta ya gushe.. Tab’e baki yai ganin yana batawa kansa lokaci awajen wadda ba tasan hakanba tunda aganinsa ba tada cikakken hankali a nutse ya dubeta tareda furta, “To malama bilkisu naji xancenki kuma..uhm hakan dayai be kyauta ba saboda haka duk sanda aka sallamo shi daga asibiti xamu sake xama daga nan semuji inda mtsalar take..” Kad’a kai bilkisu tai cikin sauri tace, “Toh Allah ya kara maka lapia ko xan iya tafiya gidanmu duk sanda ake nemana se naxo??” “Ina kenan?!” “Can gidanmu dake unguwar bulunkutu yan nono gidan iyayena..” Ware idanuwa yai hade da sake jaddada kai,lokaci d’aya sarki Aliyu Hydar yaji tausayin bilkisun ya dirar masa azuciya donshi axatonsa haukanne ya motsa tunda gashi har tana xancen tafiya gidansu bayan tasan itadin me aure ce ... “A’a bilkisu..Kibari xakije gidah amma ba yanxu ba idan aka gama shirye shiryen komai da kaina xansa akai ki har gidah a mota ko bakyaso?!” Dashe baki bilkisu tai jin xa’ kaita gidah tagasu abbanta tagaya masu fyade akai mata shiyasa bata dawo daga islamiyya ba tunda tafita... Cikin sauri ta kad’a kai, “Inaso wallahi ..Nagode k’warai..” “Nima Nagode”yace da ita yana murmushi Kiran jakadiya yasa aka masa ahankali yace da ita ta tafi da bilkisu ta karbo mata temakon gaggawa don sabon haukan daya tab’a kwakwalwar ta da axama jakadiyar ta rik’e hannun Bilkisun tana d’an nesa da ita don karta kai mata duka jin an ambaci sabuwar tab’uwa ce Bilkisun,fita sukai xuwa sashen ta bayan sunyi sallama da sarki Aliyu Hydar din.. Sun kuyar da kai yayi yana tunanin ina mafita?! Jin kansa yafara sara masa yasashi xaro wayarsa don kiran Meenah ko jin muryarta xe d’an wartsakar dashi,yana cikin dialing number Modu yai sallama bayan ya kutso kai cikin fadar yana murmushi... Bashi hannu yayi suka tafa, “Mutumina...Kaga sarkin barebari mijin Basma da Meenah yayan Aysaa k’anwar my Affy” Dan murmushi sarki Aliyu Hydar yai bayan ya gyara xaman kasaitar dayai hade da maida wayarsa cikin aljihu... “Guy!lapiar ka kuwa?!” “Da akai yaya??”cewar Modu “Da wannan soki burutsun naka mana” “To ai gaskia ne kaiba sarkin bane,ko kuwa ba mijin Basma da Meenah bane ko k’arya nai kaiba yayan Aysa da Affy bane??” Tab’e baki sarki Aliyu Hydar yai kafin yace, “Allah yabaka lapia...” “Amin tare da kai...Nace meya faru ne naga matar baa babs tafita yanzu da alama yasha yayi tatul ya batasha kashi halan cux nasan halin mutumina” “Naah!ba haka bane guy nikama tuno min wallahi,Kai Allah kabawa wannan baiwa taka lapia” Ware ido Modu yai cikin sauri yace, “Batada lapia ne?!ina..Ina shi mijin nata??” “Wallahi guy kabari Ina tsoron duniyar nan ka kwanta lapia da mutum kutashi bashida lapia..” Tsaki Modu yasaki cikin takaici yace, “Dan Allah kabani amsar tambayata” “Guy yarinyar nan tasami matsalar tabin hankali,nan fadawan baa babs suka kawo kararta ta dakeshi aciki yanzu haka yana asibiti” “To amma ni kalau naganta fa har gaisawa mukai” “Believe it or not yarinyar nan tanada matsala har facatai wai baa babs dan iskane wai yarabata da virginity d’inta kajifa?!imagine mijinta da yabiya sadaki inba haukaba meya kawo wannan?hardasu xata tafi gidansu” “Cab Allah yabata lapia gaskia batada lapia kam” “Amin..nace jakadiya tafara bata duk wani temako daya dace” “Ka kyauta sosai to ya wife dinka?!” “Kalau take,yaya naka?!”cewar sarki Aliyu Hydar sannan yai kicin kicin da face d’insa don karma yasako xancen Basma.. “Wallahi Alhamdulillah yanzu ma daga gidan layla nake nakai kiara” “Okay” “Yeah..laylan tana bata tarihin annabawa” “Yayi kyau..Allah yasa ta musulunta de” “Amin ya rabbi..munata addu’ar hakan batada aiki fa sejin wa’zin su mufti isma’il menk su khalid yasin kasan guy satin baya nadawo daga aiken baba kenan nashiga gidan kawai naji k’ira’an sudeis yana tashi ashe itace tasaka tanaji, “Na tambayeta meyasa takeji?!l kasan me tacemun?!”Girgiza kai sarki Aliyu yai alamar a’a “Seta cemin wai tanajin peace of mind duk sanda takejin karatun” “Wow..Allah ya dawo da ita addinin gaskia” “Amin ya mujeeb..Nikam Guy yakamata kadawo da Basma pls” “Kaima kasan hanyar garin nasu ai” “Maida wuk’ar bada fada nazo ba,ganinai abinda yadace kenan..” “To sannu baba..” “Yawwa kunyi magana dashi kuwa?!” “Mun fara magana dashi yace naje xe nemeni,Allah yasa ma yace na kyaleta gaba d’aya..” “To ba Amiin ba,saboda tagama maka amfani dole kace haka mana tunda ga baby Meenah xata tare” “Kaine jarababbe ai..Ni wannan ba damuna yaiba Malam beside Meenah yarinyace ba abinda xata iya ragemun” “Allahu Akbar ina tausayawa ranar daxa ka tsugunna akasa kana rokonta wallahi kabi ahankali..” Tab’e baki sarki Aliyu yai batare da ya bashi amsa ba cikin rashin damuwar bashi amsar dayai Modu yasake cigaba da magana, “Kana wani cewa Baby ce ai reno xa’a baka wallahi ka kiyayi bakinka kayi masa linzami kasani ita mace bata kad’an komai kankantarta..” Tsaki sarki Aliyu Hydar yai domin maganganun Modu sun isheshi tuni kambun mutumin naku suka motsa cikin takaici da isa yace, “Bakada inda xaka jene?! Ina bukatar a kyaleni ni kad’ai” “Arrogant kawai..Allah deya canxa maka wannan halin rabbi yasa Meenah ta gasa ka” Modu na k’arasa magana ya mike yana murmushi da alama soyake ya tsokano shi haryakai bakin k’ofa yajiyo yana masa dariya yana magana, “Kaifa gaba d’aya rayuwar ka abar atausaya mata ce kai kullum axaune kake akan kujerar nan gata dukba dadi gakanan gakanan kamar mutum mutumi bakada ikon wataya wa seda motsin fadawanka abu nabiyu ga takunkumin abun bakin kanan sekace wanda yai lefi ake mai horar magana kai i pity ur life abu na uku ga uban kaya shurum an lafta maka sekace wani doki kai kai kai abubuwa de gasunan ur life...” Be k’arasaba sarki Aliyu cikin takaici yad’au tumtum ya jefa masa yana sakin tsaki,gwalo Modu ya masa yafice yana dariya ganin ya kular dashi kamar yadda shima ya gasa masa bak’a daxun... Bayan fitar Modu sarki Aliyu Hydar yaja tsuka ba adadi sam yagaji shima da wannan sarautar sosai yake son rayuwar sa ta baya yaje inda yakeso yadawo sanda yaga dama amma yanzu ko balcony ya leka se duniya taji ta sani.. *WASHE GARI* _DAMBOA ROAD_ Aminatu Mai Alooma Ghaji shine sunan da xakaji kawai yana tashi a loudspeaker a harabar makarantar tasu Meenah don yau suka xana jarabawar su ta k’arshe ta kammala makarantar secondary,duk wasu manya manyan kyaututtuka ita aka bawa don murna har kuka Meenah tai... Sosai Malamai suke yabonta kan kwazonta juniors dintama sun yabeta kwarai matuka don sam batada mugunta itace headgirl amma bata taba duka kocin zarafin na kasan taba akwai tade da son girma shiyasa suke girmamata.. Duk yan uwa dake jihar Bornu sun ziyarci graduation dinsu Meenah sarki Aliyu Hydar ne kawai be samu xuwa ba don da sassafe flight d’insa yad’aga xuwa garin na gombe amma don takaicin rashin halartar taron har kusan kuka yai musanman yadda Modu yadinga tsokanarsa yana nuna masa videon ta Skype uwa uba yadda Meenah taci kwalliya tai kyau kamar wata uwar mata.. Bayan taro ya watse aka koma gidan na Ammi musanman Ammin ta hadawa Meenan liyafa ta y’ar k’aramar walima anci ansha Meenah har kuka tai don surprise Ammin tai mata batason da ita ba sosai yan uwa suka bata kyaututtuka masu daukar hotuna da videos seyi sukeyi suma taro be watse ba se gaf da kusan la’asar tukun sannan kowa ya watse bayan yatake cikinsa da cima kala kala ga kuma kayan rabo da suma ba’a barsu abaya ba.. Se bayan hudu sannan su Meenah sukai shirin tafiya yola itada yan rakiyarta su aunty yaruwaiya da Affy Ammi har hawayen tafiyar bittinta tai sekace wadda tatafi kenan har abadah itama Meenan tadanyi hawaye na rabuwa da Ammin domin Ammin macace me halin dattako da sanin yakamata sam bata d’auki meenan amatsayin suruka ba tad’auketa kamar yadda tadauki su Affy.. Har airport Ammin tarakasu Meenan sannan suka shiga d’aya daga cikin private jet din shehurin suka d’aga garin na Adamawa yola... *Kano* Zaune take a gefan bakin gadonta gaba d’aya ta xabge ta rame kamar ba itace tai shararriyar kiba shekarun baya ba,dukta fige ta lalace ta kwanjame ta jeme idanuwanta sun sake shigewa loko seta sake muni..Rik’e hannunta yake d’auke da qur’ani tana karatun suratul mu’uminun, Sallama mahaifiyar tatai tashigo d’akin hannunta d’auke da plate da abinci aciki amsa sallamar Basma tai tareda cigaba da karatun datake,ajiye abinci mahaifiyar basman tai agefen bed side drawers sannan taja stood na mudubi taxauna tana duban y’ar tata cikeda damuwa tace, “Maryam...Magana zamuyi” Nannauyar ajiyar zuciya Basma ta sauke hade da rufe alqur’anin ta ajiye a gefe sannan ta sunkuyar da kanta k’asa tana wasa da zoben azurfarta dake yatsan hannunta na tsakiya...Ahankali cikeda ladabi tace, “To ummah..!” _Ina kike Miss pinki?!Miss pinki ta home of novels ina mik’o gaisuwa ta agareki me cikeda d’imbin fatan alkhairai...Har kullum xoxo najin dadin yadda kike bibiyar littattafanta,Rabbi yabar zumunci..._* _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` _Wannan shafinma nakine my Asmy k’awata tawan tawa takaina,kisani ahar kullum wutar sonki k’ara ruruwa take a zuciyar nana hafsatu,Rabbi ya k’ara maki basira da kaifin ido acigaba da suburbudo mana HAFSATUL IKRAM_* *66* **** “Wa’alykm salam..” Ammi ta amsa sallamar tasa xaune take akan doguwar kujera mecin mutum uku hannunta d’auke da remote tana rage volume na tv.. Gefe yaxauna daga k’asanta kansa a k’asa ahankali cikin muryar girmamawa yace, “Ammi barka da rana” “Barkanmu Aliyu..Affy tace maka inason magana dakai ko?!” “Eh Ammi” “Yawwa Aliyu magana nakeson muyi dakai kabani hankalinka nan kana jina?!” “Eh Ammi...” “Wato Aliyu so nake kafad’amin gaskiar al’amarin dake faruwa tsakaninka da matarka Basma,kanata wasa da hankulan jama’a kace taje England ne wajen malaminsu kan abun graduation dinsu segashi da mukasa aka binciko sam babu wani abu dayai kama da haka, “To inason kagayamun gaskiar al’amari shin Menene yashiga tsakaninku kake kwana kwana,kuma wani sabon labari yazo mna kan cewar anga Basma a kano which means tana gidan iyayenta kenan...” Shiru Ammi tai tana d’an girgiza kanta, “Aliyu bansanka da k’arya ba,bansanka da b’oye b’oye ba Aliyu bakada rufa rufa baka b’oyewa iyayenka duk lamuranka hak’ika wannan abu dakayi ya mugun tayarwa mahaifinka hankali yace mun ya tuttunku b’eka akan maganar Basman kak’i, “Kagaya masa kome aciki kanata inda-inda,hakan ba k’aramin d’aga masa hankali yai ba ganin baka b’oye masa abinda yashafe ka,shin Aliyu menene ya had’aka da Basma?kuma wane mataki kad’auka akanta...” Shiru sarki Aliyu Hydar yai shi kansa yasan be kyauta ba na rashin shawartar iyayen nasa... “Kiyi hak’uri Ammi...wato abinda Basma tayimun nayi nayi na yafemata na kasa kuma ban yanke hukunci bane don natozarta maku a’a sam bahaka bane kawaide nayi mata hakanne don tasan duniya makaranta ce ko tayi hankali..” Ajiyar zuciya Ammi tasauke d’an duban Aliyun tai kafin tace, “Shin wane mataki kad’auka akanta har kake neman yafiyarmu,kuma metai maka da har xaka yanke hukunci batare da shawartar nagaba da kaiba?” Gyara xama sarki Aliyu Hydar yai sannan ya shiga gayawa Ammi duk abinda yafaru ya k’ark’are da, “Nikuma lokacin i was out of control shi..shine kawai na rubuta mata takardar saki saboda koda na kyaleta baxata ji dad’in xama dani ba...” Salati Ammi tashiga rafkawa kafin tad’aga hannunta tamai alamar dak’uwa, “Ungo nan Aliyu nace ungu nan,au yanzu shine kasakar masu y’a bawani bincike babu komai?!katab’a jin ko ganin wanda akace maka yayi saki a shehurin nan tun kaka da kakanni?, “Aliyu xancen nan idan yafito ai dariya xa’ai mana dududu yaushe kai auren ko shekara uku ba’aiba har ka saketa?!katab’a ganin inda aka yanke hukunci babu bincike?kawai kabi son ranka batare da kabi takan iyayen kaba?! Wato kanuna kenan tunda ba zab’in mubace hakan ba wani abun bane ko? To bari kaji nagaya maka tun muna sheda juna dakai Aliyu, “Kaje kayi bikon matarka kakuma bawa mahaifinka hak’uri idan baka saniba Wannan abun dakai zubar da k’imar ka kai a idanun duniya kuma martabar masarautar nan raguwa xatayi” “Ammi kiyi hak’uri Ammi nide gaskia xamana da Basma ya k’are saboda Ammi ni kad’ai nasan abubuwan danaji awayar data keyi” “Nonsense!...To kayi yadda kakeso Aliyu kabi son ranka kayi duk abinda kaga dama kaji tunda kaika haifemu bamu muka haifeka ba” Tuni sarki Aliyu Hydar ya rud’e yafara girgiza kai sega hawaye sharr hak’uri yafara bawa Ammi yana dafe da k’afafunta rawaninsa kuwa har cirewa yai saboda tsabar rud’ewa, “Dan Allah Ammi kiyi hak’uri nid’in banxa wanene ni?!dan Allah kiyi hak’uri Ammi ba abinda nake nufi ba kenan” Hak’uri yadinga bawa Ammi yayi da hausa yayi kanuri duk shi kad’ai kamar zaucacce... “Shikenan Aliyu ya wuce Nide abinda nakeso kaje kabawa mahaifinku hak’uri kakuma sanar dashi abinda yasa kayanke wannan d’anyan hukunci..duk hukuncin daya xab’ar maka sekayi amfani dashi kaji ko?!” Gyad’a kai sarki Aliyu Hydar yai da sauri yace, “Insha Allah Ammi xanyi amfani da duk decision din daya xab’ar mun” “To yawwa hakan yayi se abu na biyu akan bitti ne..” Da sauri sarki Aliyu ya d’ago kansa sekuma ya sunkuyar gabansa se dukan tara tara yake, Batare da Ammi tadamu da yanayin daya shigaba tad’anyi murmushi kafin tace, “Saura kwana biyu tagama jarabawar neco d’inta kana jina?!” Cikeda sauri yace, “Eh Eh Ammi..” “To kaga saboda Allah yarinyar nan shekaru biyu kenan da yan watanni kad’an yarage su cika uku bataje ganin gidah ba tun wani zuwa da sukai lokacin tun Aysaa tananan,saboda Allah kaga kamar ana k’wararta kenan dukdade makaranta takeyi amma kaga ai yarinyace saboda Allah kowa yanason ganin iyayensa ..ko kuwa?!” “Hakane Ammi..yanzu yakikeson ayi?!” “So nake idan baxaka takuraba taje gidah can yola tayi musu d'an hutun kafin ayi biki ta tare a gidanka..Amma fa se idan ba’a shiga hakkinka ba idan har baxaka takura ba bawai canai lallaiba bakuma canai dole ba...” “No Ammi ba komai taje tayi hutun ai tayi ko’kari ma..yaushe xata tafi kenan?”cewar sarki Aliyu Hydar sekace gaske don dakyar yadanne zuciyarsa yafadi haka don gudun bacin ran Ammi amma axahirin gaskia yanxun bayason Aminatu tayi nisa dashi. “Jibi!jibi nakeso Aysa da yaruwaiya suyi mata rakiya sesu yi kwana biyu su dawo” Cikin kid’ima don beyi xaton da wuri haka xata tafiba,batare da yason meyake fad’a ba yace, “Ha’a Ammi kikace kuma jibi xata gama kuma seta tafi a jibin?!” “To ai takwas na safe xuwa goma xasu gama kaga by 3 na rana sesu bi flight su tafi ko?inkuma hakan beyi maka ba to” “No yayi...Allah ya kaisu lapia” “Amin ya rabbi,yaya maganar ziyarar masarautar gomben tananan ko ka fasa?!” “A’a xanje,jibi Insha Allah nima zantafi don har munma yi magana dashi jakadanmu dakecan yacema sunfara gudanar da shirye shiryen yadda taron xe kasance” “To ubangi allah yasa ayi a sa’a Aliyu...Allah yasanya albarka aduk lamuranka sekai mata alheri ko?ka kuma bata abinda xatai guzuri dashi da wanda xatayi tsaraba” “To Ammi Insha Allahu...” Da wannan suka shiga wani xancen Ammin tashiga bashi shawarwari akan mulkin nasa dakuma yadda xe sake xage damtse da kaimi wajen addu’oi ganin yadda ake nufarsa da sihiri kala kala shide sarki aliyu kad’a kansa kawai yake gaba d’aya wannan maganar tatafiyar Meenah beji dad’inta ba saboda sosai yanzu yakejin wani bak’on yanayi akan yarinyar dabeyi tunanin hakan a shekarun baya ba.. Kodah sarki Aliyu Hydar suka gama tattaunawa da Ammi main parlorn yadawo nan yaga Meenah akan sofa hannunta d’auke da textbook na chemistry se jotting pad tanata rubutu da alama lesson teacher din nata tatafi.. D’an gyaran murya yai nan tad’ago tadubeshi sekuma ta maida kanta tacigaba da rubutun da take cikin dakewa yace, “Hey...” “Hi”tabashi amsa still tana rubutu ko kallonsa batai ba Tab’e baki yai cikin I don’t care tune yace, “Kin iya had’a lemon tea?!” “Latsi”tafurta a hankali yadda baxe jiba.. “Miss ghaji m talking to you kin iya kona saka Affy?!” “Na iya”kawai tace a tak’aice “Okay kiyimun like quarter na cup xanje wajen baa Ngari nadawo yanxu” “Ok..ay”tak’arashe had’e da mik’ewa tai hanyar kitchen.. Bin bayanta yai da kallo yanajin wani abu na k’iyasta masa a zuciyarsa dakewa yai yatafi sashen baa Ngari cikin zuciyarsa kuwa se sak’e sak’e yake.. Kodah yaje wajen baa Ngari yadad’e atare da yayan nasa shiya temaka masa ya wanke jikinsa da ganyen magarya sannan ya tattofa mashi azkhar se labari yake bawa Ngarin shide murmushi kawai yake don babu bakin magana ya jima awajen d’an uwan nasa don atare sukai sallar magrib sannan yadawo sashen Ammin don shi shaf yama manta da wani lemon tea dama kawai so yake yai abunda xe sake jin muryarta.. Shigar sa keda wuya Ammi ta sallame daga sallar datake seda ta shafa addua sannan tadubeshi, “Aliyu gwara katafi ko?!kaga dare yanayi naji ance ana gyaren titi a hanyar unguwar taku” “Eh Ammi”kawai yace yana d’an dube duben parlorn koxe hango Meenah.. Kamar kwa Ammi tasan meyake dubawa tace, “Bitti ma tundaxu taxo take cemun katafi ne?! Wai kasata ta had’a maka tea ko?!” Waskewa sarki Aliyu Hydar yai shi adole kar Ammi ta harbo jirginsa, “Oh nama manta shaf..ni Affy nake nema ma akwai abuna awajenta” “Nake jin suna k’aramin parlor suna tilawar hadda don kasan ana isha’i muftin su xezo” “Okay Ayyah,bari naje nakarba sena wuce”yak’arashe maganar had’e da duba wristwatch din hannunsa, Da sallama yashiga parlorn xaune yagansu itada Affy kowanne hannunsa d’auke da qur’ani,Affy naganinsa ta mik’e tai waje don bata mance buhun masifar daya sauke mata d’axu ba, Yana ganin Affy ta fice yai hanxarin karasawa kusada Meenah ahankali ya janyota jikinsa hade da karbar alqur’anin hannunta ya ajiye a gefe, Hannunsa yasa a kan gashinta yana shafawa cikin wata iriyar murya yace mata, “Ameenah...!” Kasa bashi amsa tai itade se wasa take da yan yatsunta,hannuwan nata yariko yana bin nallenta da kallo, “Waya miki nalle..uhm?!” Yafadi hakan yana murza yatsun nata.. “Aunty yaruwaiya..” “Dole namata kyauta.. I love it....ur nails looks so take away”yak’arashe xancen hade da sumbatar hannuwan nata.. “Ya Aliyu...ka..karatu Xanyi”tafad’a da sauri ganin yana niyar cusa fuskarsa cikin rigarta.. “Oh about that..”yafada ahankali.. “Eh..” “Okay,Ammi tace jibi xaki tafi yola ko??” Cikin sauri Meenah ta dashe baki, “Eh..Insha Allah” Daria taso tabashi ya gimtse cikin had’e rai yace, “Well nace mata baxaki ba’ai” Kwab’e fuska Meenah tai kamar xatai kuka cikin rawar murya tace, “Ya Aliyu menayi pls?! Inason xuwa wajen aunty da Amma dasu gidad’o pls kakka hanani dan Allah” Daga kafada sarki Aliyu Hydar yai, “Xanbarki kije but under one condition inkuma baki yadda ba to baxakiba” Cikeda sauri tace, “Xanyi Allah...pls inason naje gidah” “Kiss me kokuma xancen yola anfasa”yak’arashe xancen hade da sake janyota yana pouting lips d’insa Shiru Meenah tai tana tunanin tayine kota fasa?!canta daure tana kallon face d’insa sosai taga lalle sarki Aliyu Hydar dinnan ba k’aramin me kyau bane batasan sanda tasa hannu tana shafa quarter million d’insa ba ahankali takoma Kan lips d’insa canta maida gurbin hannunta da lips dinta sund’au lokaci suna abu d’aya dakyar ta iya zare bakin ta daga cikin nasa.. Cikin wata irin murya yace, “ I want more..” Kallonsa tai tana tab’e baki cikin zuciyar ta kuwa mamaki take wai shi baya gajiya da kiss ne haba sekace yan iskan film,tana cikin zancen zuci taji yasake damkota xe maimata tai saurin sa hannu ta riko lips d’insa, “This can’t be happening ya Aliyu...dan Allah yanzu Malam xexo fa” Dan daria sarki Aliyu Hydar yai cikin isa yace, “Okay saboda dole sekinyi wankan tsarki kafin yazo ko?!” Bud’e baki tai tana kallonsa sekuma tamaida kanta k’asa ahankali yasake janyota beyi wata wata ba yacigaba da sumbatar ko’ina ajikinta hannuwansa kuma suna karakaina acikin jikinta seda yagama jagulata sannan yasaketa kunnenta ya murde tad’an saki kara cikin rad’a yace mata, “Yanzu sekiyi wankan me dalili ko?!”yafadi hakan tareda kashe mata ido Itade shiru tai don yaukam sarki Aliyu Hydar yakashe bakin trouble maker mik’ewa yai yana gyara alkyabbar jikinsa har yai hanyar fita sekuma yadawo hade da d’akko wayarsa kirar iPhone X ash color a aljihu ya mik’awa Meenah xare idanuwa tai tana dubansa sekuma tadubi wayar,kamar yasan metake tunani yace, “Ki rik’e it’s urs now,akwai sim aciki xan dinga kiranki inkinje yolan cux baxan samu damar xuwa muyi sallama ba xanyi attending wani grand meeting a masarautar gombe” Girgiza kai Meenah tai tana mika masa wayar, “Ya Aliyu tamun girma wallahi beside its too expensive kar aunty tai fada” Hararta

Chapter 22 of 35