Share this page
sekace ba musulmaba nanfa turawa maxa sukahau mata tafi,wani jemammen bature daga cikin y'an tafin yatashi yanupi wajen Laylan hannunsa rik'e da kwalbar wine,rinannun jajayen hak'oransa yadashe kamar gonar auduga yarik'o k'ugunta hakan yayi dede lokacin da idanuwan Modu indimi suka sauka akan layla da baturen daya kamo k'ugunta,rintse idanuwansa yai yabud'e ko mafarki yake sud'inne de idanuwansa suka tabbatar masa,cije k'asan lips d'insa yai duk tunanin nasa betab'a xaton shaid'anancin Layla da duniyancinta sunkai haka ba seyau daya gani da idanuwansa don dagaya masa akaima baxe tab'a yadda ba kad'a kansa yai alamar jinjinawa lamarin na Layla,gefe d'aya kuma sanyi yaji aransa na rashin ganin Basma dayai,atlast zuciyarsa xata wanke xargin dayake akanta,Kiara ce ta tab'oshi don nuna masa abincin da aka kawo a dede lokacin daya d'aga cup xeyi sipping champagne idanuwansa suka sake sauka akan Basma... Besan lokacin daya furta; "What the fuck...." ahankli yakebin Basman da kallo yayinda gefanta wani matashine d'an indiya hannunsu sark'e da juna sun nupi kusada su Layla suka xauna a teburi mecin mutum 4 kansa ne yafara masa nauyi na abubuwan daya gani,gaba d'aya ilahirin jikinsa rawa yake,ko kad'an yakasa tab'a abincin da aka kawo,da Kiara ta tambayeshi cayai kansa ke ciwo ta tausaya masa k'warai ganin har idanuwansa sunyi jajir dasu, itadinma bata wani ci abincin sosai ba suka tashi suka fita ta k'ofar baya bayan yabiya waiter kud'in shi beko yadda yak'ara kai kansa saitin su Laylan ba... Team#SRKZB?"lovers😘 Wannan page d'in nakune my WORD PRESS FOLLOWERS😘thank y'll for the amazing comments,likes and love😘❤I totally heart y'll😍❤ Sak'onki ya iso gareni Aysha😘ubangiji Allah yabar so da k'auna..Nagode k'warai💯💞 WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com _18_ Wannan shafin nakune Ammunah and Nusy from MU SHAA KARATU grp😘❤da duk ma members na cikin grp d'in..nagaisheku kyauta😘❤ ...... Modu indimi nasauke Kiara a gidansu yaja motar da k'arfi yai apartment d'in ma'aruf yana parking motar ya kife kansa akan sitiyarin fara tariyo abubuwan dasuka faru d'axu yafarayi yajima yana recalling abubuwan har seda ma'aruf yai knocking glass d'in k'ofar motar hangensa dayai tundaxu yadawo beji shigowarsa cikin gidan ba yasashi dubawa yaga ko lapia??button Modu yadanna yabud'e glass d'in k'ofar ma'aruf ya lek'o da kansa taciki yana masa magana; "Aboki lapiar ka kuwa kusan k'arin awa d'aya kaifa acikin motar nan kome kake oho thought ko rik'ewa motar tayi don tasaba haka ina fatan lapia de ko?!" "A.. Aboki la...lapiya yanzu dama xanshigo"Modu yabashi amsa muryarsa na d'an karkarwa "Okay muje ciko to"ma'aruf yace hakan asanyaye yanabin fuskarsa da kallo Fitowa Modun yai daga cikin motar ya k'ulle tareda bawa ma'aruf muk'ullin ahankali yace; "Thank you.." "Aboki meyake faruwa ne??kalli idanuwanka yadda sukai ja dan Allah menene yake damunka"cewar ma'aruf daya k'arasa xancen yanabin idanuwan Modun da suka kad'a sukai jajir da kallo.. "Nothing fa,kawai allergy ne kasan m allergic to butter cream cake shine kuma naci bada saninaba..." Tab'e baki kawai ma'aruf yayi saboda yasan bahaka aininhin xancen yakeba shiga cikin apartment d'in sukai atare,ma'aruf yahaye kan kujera yaciga da kallon shirin 'greys anatomy'da ake a tv shikuma Modu yahau stairs yashige d'aki a bakin gado yaxauna yafara tunani da xancen filin daya saba shi kad'ai; "Kona kira Layla nace nagansu da Basma a clubbing yau?! Kai a'a kuma idan nafad'i haka xasu gano akwai wata a k'asa... God damn it niyanxu yaxanyi?!" Yafad'i hakan yana sakin siririn tsaki Ganin xancen nasa bana k'are bane yasanyashi tashi yashiga band'aki wanka yayi had'e da d'auro alwala yafito pajamas yaxura yahaye kan gado wayarsa yad'akko yai dialing number yareemah Aliyu Hydar ringing d'aya biyu ya d'auka; "Hello....The charming prince yakake?!"cewar modu indimi "Lapia Lou oga at the top"yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa... "Waneni wannan aise ku manya manya..." Daria kawai yareemah Aliyu Hydar yai bebashi amsa ba. "To ya gidah da kowa?! Yaya jikin baa Ngari??" "Alhamdulillah..."yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa a tak'aice "To Masha Allah.. When are you coming back ne?!"cewar modun "Idk guy.. Ina jiran baba haryanxu de.." "Yeah correct..To Allah yasa muji alkhairi" "Amiin.. Ya kagama compiling project d'innaka?!" Sosai kai modu yai yana tunanin k'aryar daxe masa can yace; "Bank'arasaba de bibliography kawai nake correcting wajen in-text referencing d'innan.." "Oh okay..." "Yup amma nakusa k'arasawa..." "Congrats..."yareemah Aliyu Hydar yabashi amsa "Ina Basma?! Nasan kananan kana mata wulaqancin daka saba" "Sure.."cewar Aliyun "To Allah yabaka lapia guy..Barin k'yaleka haka nasan ka matsu nakashe" "You are sick.."cewar Aliyun Daria Modu indimi yai san ransa sannan yace; "Okay good night mr arrogant..." "Ok night.."cewar Aliyun.... Modu indimi nakatse wayar yajefar da ita agefe kwanciya yai kansa asama yana tunanin mafita harde bacci b'arawo yasa ceshi... WASHEGARI; Da sassafe modu indimi yatashi daga bacci yafad'a band'aki yayo wanka kayansa yaxura yafeshe jikinsa da turaruka yanupi dinning area inda ma'aruf ke having breakfast jan kujera yai yaxauna bayan yabashi hannu sun gaysa, "Aboki se ina haka?! Wannan sammako haka ko yau xaka koma ne??"Ma'aruf yace hakan yana sipping black tea d'insa "No zanje school ne gurin project supervisor d'ina amma xandawo da rana kamar yadda kace d'in inaso na had'u da Arfat" "Oh baka gama ba haryanxu?!Allah yatemaka to,karde kajima kasa yarinyar mutane jiranka" "Nagama fa.Zanyi submitting ne kuma inason ganin supervisor d'in nawa shysa,nd Insha Allah da wuri zandawo" "To Allah yasa..." "Ameen"Modun yace Had'e da jawo plate yashiga serving kansa da roasted egg,French sandwich se coffee yana gamaci yaiwa ma'aruf sallama yatafi Cambridge university makarantarsu..... _19_ Wannan shafin nakine ~Kherdejerh😘❤ and the entire members of RANO ONLINE NOVELS nagaisheku gaisuwa mai yawa😍❤ ......... Bornu_Maiduguri_ Shehuri(Masarautar sarkin Bornu) "yanxu yayya kina ganin hakan shine mafita?!"cewar yakolo dake maganar tana kallon gajiram jiran amsar daxatace "Hakan shine mafita yakolo,saboda Idan muka nuna zalamarmu a fili ina tabbatar maki da cewa mai martaba baxe k'ara yarda da muba..." Ajiyar zuciya yakolo tai tana k'wafa,murmushin dayafi kuka ciwo gajiram tai a hankali tace; "Duk yadda kikakai ga k'ololuwar tsana akan shegiyar matarcen mekama da aljanu itada y'ayanta ina tabbatar maki da cewa yadda natsanesu yafi ga tunanin bil adama natsanesu natsani duk wani wanda xeso su nak'i jinin me furta kalmar data shafi sunansu banasansu banason cigabansu kwata kwata saboda haka inason ki kwantar da halinki kibada had'in kannan ninasan aikin boka na sambisa xeyi kamar yadda yace d'in,karki manta bayau yasaba mana aiki ba ko kinmanta??" "A'a yayya banmantaba" "To ki...." Bata k'arasa xancen ba yareemah babagana yaturo k'ofar da k'arfi yashigo yana tafe yana tangad'i kamar ze fad'a akansu cikin muryar maye yasa yatsa yana nuna gajiram mahaifiyarsa yana magana yana layi; "Saboda tsabar renin sence na....nace kibani huge amount of money xaki rubuta wani shir..shirmen check wal.. Wallahi se...sekin ba...bani su ko..kokuma naje nad'uka da kaina ainasan inda kike ajiyesu bayan kema.. Sa..satowa baba ku..kukeyi ko angaya mik... "Bek'arasaba hajia gajiram tamike tsaye ta kama kafad'unsa ta xaunar dashi "Haba yareemah haba sarkin gobe haba maxan fama karka manta fa sarautar bornu takace se yadda kai da ita idan kahau karagar mulki,inde kud'ine karka damu xan k'aramaka kaji??"cewar gajiram data karairaya murya tanawa babagana kirari... "Naji..."cewar babagana daya mik'e yafice yana tangad'in giya Uban tagumi gajiram taxabga,yakolo ce tadawo kusa da ita tana bata baki; "Haba yayya karkice xaki dingasawa kanki damuwa dayawa ,komai ze wuce kamar yadda bokan sambisa yai alk'awari.." "Hakane kuma..."cewar gajiram Sun jima suna tattauna yadda xasu k'ara b'ullowa al'amarin sannan yakolo tai mata sallama takoma sashenta itada kuyangunta dake take mata baya,hajia gajiram nakishin gid'e bayan fitar yakolo 'Ayiya'yarta k'arama kuma auta acikin y'ay'anta baxata wuce shekara goma sha takwas a duniya ba tafito sanye cikin doguwar rigar da akayi shaping d'inta takoma fitted gown kanta yane da mayafi kalar rigar hannunta d'auke da muk'ullin mota da alama fita xatai cikin hanxari hajia gajiram ta mik'e tana binta da kallo cikin kanuri tace; "Ayiya ndararo len3min?!(Ina xakije Ayiya?)" Batare da Ayiya tadubi gajiram batace; "Lakkaro leyin(Wani wuri xani)?"cewar Ayiya "Shi gurin bashida suna?!"gajiram ta tambayeta "Kai yayya nifa gaskia kina b'atamin lokaci must u knw all my whereabouts??ha'a" Batajira cewar gajiram ba tai ficewarta waje k'wafa kawai gajiram tai had'e da komawa tai kwanciyarta .. (k'alubale gareku iyaye mata yakamata ku k'ara sanya ido akan y'ay'ayenku musanmanma y'ay'aye mata sakaci da barin y'arki taita karakaina a yawon zuwa gidan k'awaye da sauransu bai kamataba ki kula sosai ta fannin k'awayen datake mu'amala da su wayar hannunta da sauransu... And to the bourgeoisies(masu kud'i)dake barin y'ay'anku suna driving luxurious motoci akan titi suna yawon bin joints da sunan wayewa wannan 20th century ne.uwargidah dan maman neelam tabawa neelam mota karkice kema sekin bawa y'arki mota taje duk inda taga dama hakan daga k'arshe shike janyo nadama da danasani alokacin da kuma babu wata hanyar da xa'abi iyaye ku farga ku kula da y'ay'ayenku domin kiwone Allah ubangiji SWA yabaku kuma dole yatambayeku abisa abinda yabaku kiyo,bance duka aka taru aka xama d'aya ba,aka sari abinda ke faruwa awannen k'arnin kenan,gashinan rashin tarbiyya yana dad'a k'aruwa shikuma aure yana k'aranci,da anyi tambaya yan unguwa xasu soke xance saboda yar gidan wance bataji,shaye shaye take,da yawon banxa ko kuwa yar lez ce..Which s true...Dan Allah mu kula da y'ay'anmu musanman mata dama harkokinsu nayau da kullum...!) ...... University of Oxford(United Kingdom) "Babe jia kin birgeni fa,haka nakeso kidinga enjoying life d'inki"Layla taceda basma hakan "Da nayi me?"tabata amsa tana k'arasa drying kanta da hand dryer "Da kika dumurmushi kud'in Harrison mana" "Oh.. Kema aikin dumamusa naki Peter yake kowa?shegiya mak'aryaciya hardasu cewa da saurayinki acan ashe k'aryane" Daria Layla ta bushe da ita sedatai me isarta sannan tace; "To ke aganinki waye saurayin?! Oud de besan wannan wajen ba tunda shi ba'anan yakeba,kuma yama xa'ai mufita da wannan outfit d'in tare dashi?haba nace miki da saurayina ne kawai dan kije,gashi kuma kinsamu lucky day harda sabon iPhone 7 gaskia ba'indiyannan ya mutu akanki dagaske sonki yake da aure k'awata" Tsaki Basma tasaki tareda kashe socket d'in dryer hannunta ta d'ora d'ankwali akanta sannan tawani sha kunu tana kallon Layla dake jiran dabata amsa a tak'aice ta furta; "Sede ya mutu wallahi,jikina da ruhina mallakar Aliyu ne seyanda yai dashi" Tak'arashe xancen tareda shigewarta band'aki bata jira cewar Laylan ba,itama Laylan tsakin tasaki tana mitarta ita kad'ai; "Seki jirashi ai banxa yanacan ya mance da ke da rayuwarki kinanan kina ihu bayan hari ga inda xaki dandali arziki ana kaiki kinak'i.." Mtcew tak'ara sakin tsaki akaro na uku had'e da jawo wayarta tashiga daddannawa rai b'ace ....... Caribbean Mart..... "Yi haku'ri Arfat nak'ara five minutes late" Cewar Modu indimi dakebin wata matashiyar budurwa da kallo looking so modesty yar kyakkyawa bak'a tayi lullub'i da mayafi kalar kaftan d'in jikinta da alama itace Arfatun ahnakali tace; "Apology is accepted"cewar Arfat Gyara xama modu yai bayan sungaysa yashiga fad'a mata abinda yasa yace tatemaka masa da sunayen matan ajinsu,yak'arashe zancen da; "Inaso kifad'amin abinda kika sani akansu,I want nothing but to the truth plss" Nande itama Arfat d'in tafad'i duk abinda tasani akansu Laylan tak'arashe xancen da; "Even though ba wata mu'amala ce ke shiga tsakaninmu ba psychologically de is lyk Laylan itake influencing ra'ayin Basman,nasan duka basaji gaskia at all Amma laylan tafi Basman saboda maxa kala kala take tarawa abakin block na apartment d'insu wannan shine abinda nasani tsakanina da Allah.." Godia sosai Modu indimi yaiwa Arfat yakuma gamsu sosai da abinda tafad'a don from her decent looks ansan bazataiwa wani k'azafi ba,ma'aruf suka kira yadawo don dama waje yabasu abinci me rai da lapia modun yasa aka kawo masu sukaci suka k'oshi sannan suka sauke Arfat a campus library bayan Modu indimi yacikata da alheri,gida suka nupa bayan yayi sallar magrib ne modun yasake fita wurin wani abokinsa dake final year d'insa shima a Oxford d'in dayake expert ne na b'angaren mata,Modu naxuwa yasake tambayarsa akan halin su Basman,shima same abinda Arfat tace haka yafad'a..Godia Modu yaiwa abokin nasa sannan yakoma gidah a daren yakira mai martaba kasancewar lokacin yammacine a Nigeria,ringing biyu mai martaba yad'auka nan Modu yake gayamasa yagama binciken daya sashi a nutse mai martaba ya furta; "Nagode k'warai Modu,Allah yamaka albarka.Da sassafe xan aiko da flight amma ba a bornu xaku sauka ba kaje gidana na Abuja nima xanzo akwai meeting da xamuyi da shugaban k'asa da sauran sarakuna,bayan mungama Insha Allah xamu tattauna acan dakai .."Cewar mai martaba daya k'arashe xancen cikin dattako da sanin yakamata... "To baba Allah yakymu goben,ahuta lapia" Sallama sukai da mai martaban ahankali Modu yajanyo pillow ya kwanta yana tunanin yadda xata kaya goben..... Team#SRKZI?lovers😘 Ina kike sis Nobeey?😘nagaisheki sis Nobeey crush d'in Modu indimi😜 WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com _20_ This page is urs SEEMBY LUFF😘❤I love you beyond words😍Allah ya k'ara basira acigaba da suburbud'o mana SAHR_KHULAYD💯 ..... WASHEGARI; Federal capital territory(Abuja)..... Ganges street maitama Abuja. Modu indimi ne kwance idanuwansa a lumshe da misalin k'arfe takwas na dare da alama bai dad'e da isowa daga tafiyar dayaiba gefensa d'an k'aramin trolly ne bak'i wanda xe iyacin kaya kala biyu kawai,kwance yake akan royal kujerun dake parlorn side table d'in dake gefan 3 sitter kujerar dayake take away ne me d'auke da tambarin tulip bistro se lemon don simon na kwali da ruwan gorar nestle wayarshi ce tafara ringing jin sautin taken 'ganga kuraa' yaganar dashi mai martaba ne don shi kad'ai yasanyawa ringing d'in saboda yadinga fayyace kiransa akodayaushe akuma ko'ina yake. Hanxarin d'auka yai yana mik'ewa daga kwancen dayake; "Assalamu alykm... Na'am baba! Eh ina cikin gidan yanzu haka,eh bandad'e da shigowa ba... To to Shikenan baba bakomai seka k'araso Allah yadawo dakai lapia,nabarka lapia.''katse wayar yai ya ajiye gefe tareda komawa yasake kwanciya a kan kujerar dayake Ko'ina na cikin parlorn agayre yake tatas,don kullum akwai ma'aikatan dake gyarashi saboda mai martaba anan yake sauka idan yaje Abujan,makaken parlor ne me d'auke da kujerun Royal har set biyu kowanne da kalarsa,haka curtains d'in parlorn kalar kujerun ne,makekiyar tv ce had'e da set d'in kallo a jikin bango,gefe guda kuma dinning table ne mecin mutane 6 shima k'irar Royal... Modu indimi har bacci yafara d'aukarsa yajiyo karakainan shamakin mai martaba yana isar da isowarsa kafin ya mik'e yatashi har mai martaba yashigo cikin parlorn,da sauri modu ya mik'e yana rufe bakinsa saboda hammar dayai shamakin mai martaba ne yafice yabasu waje shikuma modu ya durk'usa yana gayda mai martaban amsawa mai martaban yai tareda fad'in; "Jeka samu hutu Modu Idan Allah ya ara mana ran ganin gobe cikin k'oshin lapia xamu tattauna da safe da izininsa Insha Allah.." "To Allah yakymu baba Nagode Allah yatashemu lapia.. Ahuta lapia nabarka lapia"yak'arashe xancen had'e da d'an rissinawa sannan ya mik'e yasauka k'asa wani d'aki da aka tanadar masu gefan corridor duk sanda sukazo Abujan anan suke sauka. ...Da safe da misalin k'arfe 10 da rabi na safiya Modu yatashi daga bacci bayan komawar dayai daga sallar subhi,cikin sauri yai hanxarin shiga band'aki wanka yayi had'e da d'auro alwala yajima yana shafe shafen kayan k'amshinsa don abune daya xama wajib d'insu shida yareemah Aliyu Hydar ta b'angaren k'amshi sede ayi hamdalah kawai don har yareemah Aliyu Hydar yafi Modu son turaruka da kuma tuttulasu ajikinsa kamar ruwa..yajima yana aikin shafa wancen goga wancan kamar wanda xashi gasar xab'en wanda yafi kowa k'amshi,yana gamawa yaxura kayansa wannan karon wanka shadda yai dark blue anmata aikin light blue 'zanna bukhr'hula ya d'ora light bak'aramin kyau yayiba sosai,safa yasaka bak'a had'e da xura takalminsa samfarin vassace,shi kansa tsayawa yai yana kallon kansa a mudubi kunsan modun naku da d'an rawar kai,yakashe selfies harda mirror selfie sannan yad'akko sallaya ya shimfida yagabatar da sallar walha kamar yadda ya sabayi kullum addu'oinsa yai yashafa had'e da ninke sallayar ya mayar kan drawer cikin hanxari yafito yahau sama gurin Mai martaba don rabonsa dashi tunda asubah da suka gabatar da sallah,yana hawa ya hango mai martaban sanye cikin kayan sarakai kalar d'orawa yayi kyau sosai sede afurta kalmar tubarkAllah kawai,gaisawa suka k'arayi sannan mai Martaba yai gyaren murya cikin nutsuwa yafara magana; "To Modu abinda yasa nace kazo Abuja mu tattauna yakashi kashi biyu,d'aya saboda taron da zamuyine ajiyan amma almuhim abinda yasa nazo Abuja saboda mu tattauna ne donta taro xan iya turo waziri ya wakilceni ina fatan ka fahimta?!" "K'warai baba nagane.." "To Masha Allahu.."abinda Mai martaba yace kenan atak'aice.. Gyara xaman gurfanensa yai yashiga fad'awa mai martaba komai akan binciken dayai ba'abinda ya b'oye masa,yak'arashe da; "Kuma bayan ganinsu danai da idanuwana da temakon k'arin bayani da k'anwar abokina tai wallahi baba har wani abokina nasake bugar cikinsa don kauda zargi to amma dukde abinda suke fad'amin guda d'ayane kamar yadda nace da farko baba"Modu indimi yak'arasa xancen had'e da saukar da kansa k'asa Ran mai martaba idan yayi dubu yab'aci,gashi da manyan idanuwana tubarkAllah sesuka sake fitowa saboda tsabar b'acin rai,mik'ewa yai tsaye yana magana cikeda b'acin rai; "Zancen banza zancen wofi,dama irin yarinyar dayake kulawa kenan shysa yace min basu gama daidaitawa ba?!" "Kayi hak'uri baba nide inada tabbacin cewa wallahi besan haka halayyarta takeba kuma kamar yadda nace d'in ance k'awar tatace take cusa mata wa'innan miyagun halayen" "Duk naji naji magana d'ayace baxe aureta ba tunda ba y'ar mutunci bace Allah xe bashi wadda tafita ko yanada wacce yakeso bayan ita?.." Kad'a kai kawai Modu yai alamar a'a k'asan xuciyarsa kuwa cike take da dana sanin fad'ar dayai ganin yadda mai martaban yai saurin yanke hukunci lokaci d'aya betab'a kawowa haka abin xe xama ba... "To niyanxu xankoma Bornu base gobe ba,kai kagama project d'inne mutafi tare?!" "A'a baba ban k'arasaba tukun" "To Allah yatemaka" "Ameen baba" Sallama Mai Martaba sukai da Modu yahau pj d'insa yakoma Bornu,shikuma Modu se washegari xe hau jirgin safe yakoma school, da daddare a dunes mall yai having supper sannan yakoma gidah,wanka kawai yai yasa kayan baccinsa lokaci lokaci yake sakin tsaki kwata kwata hankalinsa baya kan Laliga ball da ake tsakanin RealMadrid da sociedad dake nunawa a tv daga k'arshe ma mik'ewa yai tsaye yana faman xagaye parlorn yana magana shi kad'ai; "What if Aliyu yagano nine wanda na gudanar da binciken?! Oh ya Allah! Kawankeni acikin wannan ruguntsumi me wuyar sha'ani dake shirin faruwa..."haka Modu yaita sumbatu shi kad'ai kamar zaucacce yanayi yana tsaki harde bacci b'arawo yasaceshi,atak'aice de akan kujerar dayake mitar akai ya kwana.... ©HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of expert and prefect writers) SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?! 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ®NANA HAFSAT (MISS XOXO) nanahafsat.wordpress.com 21 This page is urs FADEELA LAMIDO,writer of bugun zuciya😘😍❤ ....... Bornu(Maiduguri) Shehuri(masarautar sarkin Bornu) Kodah mai martaba yakoma haka yawuni sukuku ba walwala atattare dashi,duk wani k'ara da y'an k'orafe k'orafe da aka kawo masa waziri yad'ora akai yace yayi,daga k'arshe ma ya tattarra yakoma sashensa saboda bayasan a takura masa wunin ranar shehurin de duk gatanan gatananne ba dad'i narashin walwalar sarki,kodah yareemah Aliyu Hydar yaje gaisheshi ma bawani sakar masa fuska yaiba shikansa yareeman jikinsa yayi sanyi rashin ganin fara'ar mahaifin nasa saboda be tab'a ganinsa ahaka ba,sukansu gajiram da yakolo sunsha jinin jikinsu ganin sarkin ahaka saboda a'iya shekarun mulkinsa baxaka tab'a kawo rana d'aya ace fuskar sarki ta canxa ba, saboda shi mutum ne adali me sanin yakamata kuma faran_faran dashi kullum fuskarsa cikin annuri take da dattako kamar ba sarki ba bashida girman kai ko d'aure fuska sam bahaka yake ba shiysa har award aka bashi a London na sarkin dayafi kowa a nahiyar Afrika,yadda Mai martaba yaga rana haka yaga dare idanuwansa basu runtsa ba,dayayi juyi akan gadon alfarmasa ba abinda yake tunanowa se maganganun da modu yagayamasa akan Basma,daga k'arshe ma mik'ewa yai yashiga band'aki yayo alwala yafara sallar nafilfili... WASHEGARI; Da sassafe mai martaba yashrya ko takan fada bebiba,balle yatsya cin abinci,sarkin tuk'ine yajashi se damboa road gidan hajjagana mahaifiyar yareemah Aliyu Hydar suna zuwa aka bud'e masa gate b'angaren yareemah Ngari yafara shiga bacci yake amma Alhamdulillah yad'an fara murmurewa bakamar daba ficewa yai daga b'angaren bayan yawa Ngarin adduar samun lapia,sashen hajjagana ya nupa bayan jakadiyarta tayi hanxarin fad'a mata gafa mai martaba nan,yana danna kai cikin parlorn k'amshin turaren wutar ambar yadaki hancinsa lumshe idanuwa yai har cikin zuciyarsa yaji dad'in k'amshin bakuma yau yasaba jin gidan hajjaganar cikin wannan k'amshin ba nantake wani yanki na b'acin ransa ya ragu,cikin hanxari ma'aikatan gidan sukahau gaisheshi d'aya bayan d'aya,lokacin Affy da Aysa sunata shararar baccinsu saboda safiya ce ainun danko takwas batayiba... Zaune Ammin take akan dinning table tana jera abinci sanye take cikin laffaya multi color se tashin k'amshin khumra take,lokaci d'aya tajiyo suka had'a ido murmushi tasakarwa uban y'ay'an nata had'e da xuwa ta tarbeshi cikin girmamawa tagaisheshi bayan sungaysa ne Ammin takawo masa warmers cikeda varieties na abinci da flask na shayi da finjal(cup d'in tea)gaban shi ahankali tashiga serving d'inshi da dadd'adan abincinta kakkauran tea tahad'a masa dayasha kayan k'amshi gefe d'aya kuma funkaso ne da miyan yakuwa da yaji naman kasuwa d'ayan plate d'in kuma soyayyar doyace da k'wai se sauce na hanta d'ayan plate d'inkuma farfesun kaji ne da snacks hannu Ammin tawanko tashiga bawa mai martaba abincin abakinsa bashiri yabud'e baki tashiga zura masa abincin se lumshe idanuwa yake jin dad'in abincin tatass mai martaba ya lode abincin nan se snacks kad'an daya rage,sosai Ammin talura mai martaban nacikin damuwa dukkoda wai ahakanma taragu hira tashiga bashi harde tasamu yarage damuwar sosai har yake bata labarin taron da sukai a Abuja da sauran sarakuna... Bayan nanne kuma yagyara xama yafad'awa Ammin komi na binciken dayai akan Basma amma bece mata Modu indimi ne yai binciken ba,k'warai matuka Ammi ta gamsu da hukuncin da Mai martaba yayanke takuma ji dad'in yadda Mai martaban yad'au abin da muhimmanci harshi dakansa yasa agudanar da bincike,ya k'ark'are mata zancen da ko Aliyun bai nunawa yadda binciken yakasance ba seyanzu.. Cikeda k'arfafa masa gwiwa Ammin tace; "Hakan yayi gaskia kuma aiba se yadda yakeso xa'ayiba duk hukuncin daka xartar shine daidai" Nannauyar ajiyar zuciya Mai martaba yasauke a hankali yace; "Kinsan hukuncin dana yanke yanzu a xuciyata?!" "A'a"cewar Ammin a tak'aice.. "Ni ina ganin kawai zan had'a auren Aliyu da y'ar gidan kawu Alooma dake yola ko yaya kika gani?!" Murmushi fad'ade a fuskar Ammi tace; "Wannan hukunci yayi bak'aramin dad'i najiba kuwa ubangiji Allah yasa matarsa ce" "Kina ganin babu matsala ko?"cewar mai martaba "A'a ko d'aya wallahi hakan yayi daidai tuwona maina kenan aiba son ransa xa'a biba duk zab'in daka zartar shi za'abi saboda sab'in iyaye ai shine mafificin alkhairi" Murmushi mai martaba yai cikeda jin dad'in kalamanta yace; "Kira shi sakaran yazo yanxu ba se anjima ba" "Toh"Ammin tace had'e da mik'ewa tai hanxarin d'akko wayarta tashiga dialing number yareemah Aliyu Hydar.... Team#SRKZI?!lovers😘 ... Kai Kai Kai Nagode mentor da wannan gundumemiyar kyauta da kikaimin na sadaukar da littafinki me d'imbin fad'akarwa agareni😘I love and adore you💯you are just a perfect person your heart is huge and you care so deeply for everyone you let into your life with such gentle kindness. I am in love with absolutely everything you are and do. You are a gift of person that I am lucky enough to call my own💃❤Allah yabarmu tare har abadah😍💯❤ Allah ya k'ara maki basira acigaba da suburbud'o mana; ALWASHI(LABARIN HAFSAT) WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO

Chapter 5 of 35