Share this page
evening, munzo ka bamu kud'in lik'i Ammi ta hanamu.” Cewar su Affy suna turo baki alamar shagwab'a cikin b'acin rai yareemah Aliyu hydar ya harare su, “Sai aka ce ku biyo ni bedroom d'ina?!” Aysa ta girgiza kai alamar a'a sannan suka fara k'ok'arin sauka daga kan gadon,sai da suka kusan fita daga d'akin sannan yace musu, “Ku bari idan na fito zan baku, ko kuma kuje wajan Modu kuce nace ya baku.” Da gudu suka dawo tare da rungume shi suna yi mai godiya,yareemah Aliyu hydar kuwa ya k’ank’ame pillow kamar zai maida shi ciki saboda shi a halayyar shi ko su baya son su dinga ganinshi a yadda suka ganshi yanzu sai yaga kamar be dace ba.Suna fita da murna wajan Modu suka wuce wanda dawowar shi kenan daga karb'o kayan yareemah Aliyu hydar na aure daga wajan wanda aka bawa order kawo su,yana fitowa daga mota suka gaya mai ya basu 10k saboda ita kenan cikin wallet d'inshi suka ce mai, “Thank you Yaya Modu Allah ya kaimu naka kaima muyi murna.” "Amin sisters." Ya fad'a tare da wucewa yana murmushi su dama basu da raina abu ko yaya aka basu zasu yi godiya su cancana shi yadda zai ishesu, amma falmata da ta tambaya aka bata 10k rainawa tayi wai babu abinda zasu yi mata sai da yareemah babagana ya bata 15k ta had'a 25k sannan tace maneji kawai zata yi ta karb'a ta wuce gida yacika mak’il da yan uwa da abokan arziki Ayiya ma dake aure a lagos taxo da ‘yan ‘ya’yanta,suma ‘yay’an hajja yakolo dake karatu a cyprus su fannah da rukymamah sun d’au hutu sunzo, _______ Dama Modu ya hau net duk ya sanar da d'aurin auran yareemah Aliyu hydar Mai Alooma ma duk yasa an sanar a kafafan yad'a labarai daddyn Basmah ma yasa an sanar hakan yasa ko'ina ka gitta zancen auran akeyi manya da yara talakawa da masu kud'i. Ana'i gobe d'aurin aure wanda sai an fara zuwa Kano anyi na Basma da safe sannan a dawo atafi yola ad’aura na Meenah, Modu ya kalli yareemah Aliyu hydar cikin sauke ajiyar zuciya yace, “Guy! Hotels biyar na kama fa,kuma yanzu ma naji maimartaba yana cewa sai an k'ara wasu saboda sauran sarakunan da zasu zo,I think fa harda queen Elizabeth kasan fa mutuniyar shice sosai.” Yatsina fuska kawai yareemah Aliyu hydar yayi shi duk ba wannan ne damuwar shiba irin wasan dokin (hawa)da aka shirya za'ayi bayan an kawo amare gashi duk abokan shi na gurin yana jin kunyar aga Meenah ace matar shice,ya dafe goshi Modu na kallan shi yayi mai wani irin kallo tare da cewa, “Meye kuma? Kai fa na Lura tunda bikin nan ya k’arato kake ta wani fad'in rai na daban yanzu kuma muna hira ka wani yi shiru bayan duk anayin komai ne dominka.” Cikin sanyin murya da kwantar da kai yareemah Aliyu hydar ya kalli Modu tare dayin k'asa da murya, “Wai dan Allah ba yadda za'ayi a yi cancelling event d'in wannan hawan dokin da za'ayi? Please guy nifa bana son shi dama dai babu wannan babyn da zan yadda amma idan friends d'ina suka ganta ai sai sumin dariya co's shes too young.” Modu ya zaro idanuwa yana kallon yareemah Aliyu hydar da mamaki a fuskarshi, “Ba ruwa na ah,ba tsarina bane dan nasan duk abinda zan shirya maka ba yadda zaka yi ba bare na burgeka.Wannan shirin su baba ne da Baffa Mai Alooma Ghaji,dan haka kai ne ya cancanta kaje kace musu baka so a sokeshi...” Kafad'a yareemah Aliyu hydar ya d'aga alamar ko ajikin shi,d'auke maganar yayi ta hanyar cewa, “Guy!Dan Allah idan munje d'aurin auran nan kar kabari friends d'in amarya suce za'ayi wani pic's dan ni bana so kaji?!” Modu ya kuma zaro idanuwa yana kallon yareemah Aliyu hydar dake yamutsa fuska alamar baya so Modu ya temaka mai,murmushi yayi tare da d'aukar phone d'in yareemah Aliyu hydar ya mik'a mai, “Karb'i oya buga ka sanar mata cewar idan kunzo kartace ayi hotuna kai baka so kaga bama za'ayi mana tayi ba bare muk'i yadda ace munyi wulak’anci....” Tsaki yareemah Aliyu hydar yayi akaro na biyu cikin takaicin Modu mik'ewa yayi yabar mai parlorn ya koma bedroom ya ci gaba da harhad'a abubuwan shi masu amfani a cikin trolley yana kuma tunanin yadda zai tsaya ranar hawan dokunan da Meenah yasan sarai an jamai raini da kuma jin kunya a wajan abokanan shi na kunya dana dangi, *WASHE GARI* Tun da suka yi sallar asuba basu koma ba,gidan ya cika da 'yan uwa da abokan arzuk'i dan hatta Ammi cikin palace d'in ta dawo acewar maimartaba idan an gama biki sai ta koma gidan ta,shiri suka yi tayi Modu kuwa tamkar shine angon dan yafi yin komai da muhimmanci indanta yareemah Aliyu hydar ne kawai ashafa fatiha kowa ya watse amma ina! Ammi ma har walima ta had'a tareda had’add’en wushe wushe wanda za'ayi da daddare idan anyi komai an gama sai a kai amare kokuwa nace amarya Basma, Misalin karfe 8:30am kowa ya shirya za'a tafi airport masu tafiya a mota dama tun jiya suka tafi, su Mai Alooma da maimartaba da sauran manyan iyaye duk sun shirya ango kawai ake kira wanda suna d'aki sai gabza rigima suke yi, “Guy idan zaka saka malun-malun kasa ko mai auran mata d'aya ma yana sawa bare kai da zaka yi biyu a lokaci d'aya, oh kaga big bobo...!” “Bana so ni bazan saba kai tunda kasa shikenan ka wakilce ni” “Ok toh bari na sanar da baffa karma aga mun fita dakai a haka ayimin magana..” Modu ya fad'a yana kokarin kiran Mai Alooma a waya, da sauri yareemah Aliyu hydar ya fizge phone d'in yana yatsina fuska kallon Modu yayi yana hararsa, “Kai kenan sai sonkai k'arar tsiya bana son irin wannan abun.” “Ok naji kai kuma bakayi sai kaji za'a kaika k'arar ko?!” Banza yareemah Aliyu hydar yayi mai hakan nan badan yaso ba ya sanya babbar rigar,ba karamin kyau tayi mai ba,Modu yayi murmushi sannan ya d'auke shi photo ba tare da ya saniba yana cikin gyara ta hakan sai ya bada wani style. “Guy bana so ka goge.” “Nayi gaba sai ka fito.” Cewar Modu yana fita daga cikin room d'in,da sauri shima ya bi bayan shi yana fad'in, “Zaka sani nima wata rana zan maka.” Suna fita aka fara murna,masu yin pics nayi kowa so yake ya rab’i ango har suka isa gurin su maimartaba,gaidasu yareemah Aliyu hydar yayi suna ta sanya mai albarka su Ammi dasu hajja gajirim da hajja yakolo duk suna wajan bak’in ciki kuwa kamar yahudo zuciyoyinsu yafito yak’e kawai suke don kar atafi dasu abaki amma taciki naciki.Bakin Ammi kuwa yak'i rufuwa don farin ciki a haka suka isa gurin motocin da aka tanada zuwa airport harda yareemah Ngari dake kan wheelchair ana turashi yayi kyau cikin shigar sarauta sosai yak’ara jin sauk’i maganace de haryanxu befara ba dakuma doguwar tafiya hakan ne ya janyo tsantsar farin ciki a fuskar yareemah Aliyu hydar hajja gajiram ta had'iyi wani bak’in yawu mai zafi wanda ta kasa bayyana ko na menene.Suna tsaye har suka bar gidan sannan aka koma aka ci gaba da hidima dan yau su aunty yafendo zasu k'araso da Meenah bayan anje and’auro nata auren anjima, Suna zuwa airport jirgi suka shiga motocin ma anan aka barsu kasan cewar da’an d'aura auren za'a dawo ad’auro na Meenah. *KANO* Suna zuwa suka wuce gidan sarkin kano anan aka d’aura auren sunje da sadaki dubu d’ari biyu sarkin kano ma yaxo danasa dubu d’ari uku amatsayin gudunmawa aka had’a aka bada sadakin Basma naira dubu d’ari biyar lakadan daganan aka tafi Royal Tropicana donyin reception sekuma aka d’unguma zuwa gidansu Basma nanfa suka tarar k'ofar gidan su Basma mak'il da al’umma xuwansu su yasa ya kuma cika tamkar sukari ya zube kiyashi sun taru akai tsabar mutane different tribes, Ana gama d'aurin aure Basmah dake cikin d'aki gurin k’awayen ta tayi wani mugun tsalle cike da murna layla ta kalleta tana yatsina fuska cikin takaici ta kalleta, “Ko tsari wallahi,kin fiye rawar kai.” “Naji d'in ki fad'i duk abinda zaki fad'a yau ranar murna ta ce dole nayi rawa yau na zama mallakin my sugar boo...” Duk 'yan d'akin suka saki dariya banda layla dake ganin rawar kan Basmah yayi yawa harda zuwa wajan window tana lek’e cikin sa'a ta hango yareemah Aliyu hydar yana ta murmushi mutane kowa sai kama hannunshi suke ana mai Allah ya sanya alkairi. Basu samu damar shiga cikin gidan ba kasan cewar anata jiran su za'a tafi a d'aura na Meenah,Basmah bata so ba dan sai da tayi ta kiran wayar shi amma ba'a picking kasancewar tana aljihun shi kuma a silent take. Tana ji tana gani suka juya basuyi magana ba kamar ta ce wayyo Allah dan tsananin bak'in ciki. *BORNU(SHEHURI)* Su maimartaba suna komawa ya kalli yareemah Aliyu hydar cikin murya k'asa k'asa yace, “Aliyu maza jeka ka sauya kayan jikinka yanzu muna jiran ka...” Da sauri yareemah Aliyu hydar yabi dakakkiyar farar shaddar jikinshi,babu abinda tayi koda kura babu cikin zuciyar shi yake fad'in, _*Kardai itama wannan yarinyar sabon wanka zan yi mata_* Muryar maimartaba ce ta kuma dukan cikin kunnanshi yana cewa, “Tashi mana Aliyu.!” Yareemah Aliyu hydar ya mik'e cikin sanyin jiki ba kwari a haka ya shiga apartment d'inshi,tsayawa yayi yana kallon kayan yama rasa wanne zai kuma sawa sai tsaki yake ja yana haskilo Meenah yana yamutsa fuska kayan jikin shi ya cire ya shiga bathroom wanka yayi sannan ya fito a nan ya tarar da an fito mai da wanda zai sa,hararar kayan yayi cikin takaici ya k'arasa wajan dressing mirror yana shafa lotions, yana gamawa ya koma wajan kayan lokacin Modu ya shigo rik'e da waya a kunnenshi yana cewa, “Ok baba bari na gaya mai,toh shikenan insha Allahu.” Katse wayan yayi yana kallon yareemah Aliyu hydar dake a tsaye,dariya Modu indimi yayi sannan yace, “Angon Basmah da Meenah,kaga me two wives anyi d'aya sauran d'ayar kayi sauri baba yace kai ake jira mutane nada abubuwan yi.” Yareemah Aliyu hydar ya kauda kai tare da shafa sumar kanshi yana sauke ajiyar zuciya, “Guy me yasa yanzu ma aka kuma fito min da malun malun?!” Modu na d'aga kayan yace, “Maimartaba ne yace su zaka saka after an gama d'aurin auran sai kasa duk wanda ranka yake so harda ma English wear’s duk zaka iya sawa but yanzu kasa wannan kazo muje kai kad'ai ake jira...!” Ba yadda zai yi hakan nan ya sasu shadda ce light brown me d'igo d'igon ash sai maiko take yi d'inkin ya zauna a jikin shi yayi masifar yin kyau ya d'aura hulla zannah bukhr sannan ya bulala turaruka wajan kala takwas Modu ya kuma yi mai one pic,yareemah Aliyu hydar be kula shi ba suka fito zuwa wajan fada inda za'a d'aura auren, Gabaki d'aya sai yaji kunya ganin yadda ake ta nan nan dashi kowa so yake ya ganshi,private jet yashiga shida friends d’insa sauran mutane kuma suka shiga sauran jiragen da akai hiring suka d’aga garin yola dan d’aura auren meenah suna zuwa aka fara gudanar da d’aurin auren mahaifin Modu indimi shine ‘waliyyi’ se aka d’akko sadawu (sadaki) bayan angama tambaye tambayen ‘sigga’ ne aka d’akko dinar saboda shine yake amatsayin sadaki ayaren kanuri bayan angama tambayoyin ‘sigga’ ne(the act of asking and acceptance between the family of the bride and groom and their witnesses), Da misalin k’arfe 2:00 dede aka d’aura auren yareemah Aliyu Hydar shehu bulama Goni da amaryar sa Aminatu Mai Alooma Ghaji akan sadaki sisin gwal guda d’ari biyu kwatankwacin kud’in sadakin Basma. Sannan aka d’unguma aka shiga cikin gidan don gaisawa da mutan gidan su aunty yafendo da sauran yan Uwa da suka zazzo gefe guda kuma had’addiyar liyafa Mai Alooma Ghaji yatanadar masu da cima kala kala a garden dake cikin gidan, Cikin gidah kuwa tun lokacin da aka d’aura auren Meenah ce kwance a d’akinta se rawar sanyi take bakinta yana kad’uwa aunty yafendo ce tashigo d’auke da kayan meenan da aka kawo daga gurin ‘hudayya’ se alkyabba datai mugun amsar kayan cikin sauri tak’arasa gefan gadon had’e da d’an bubbuga gefan gadon, “Meenah tashi and’aura ki kintsa yanzu xamu wuce yerwa da yardar Allah” Jin shirun yayi yawane yasata yaye bargon had’e dasa hannu xata tasheta taji jikin rau yad’au zafi kamar gaushin wuta,cikin tashin hankali ta ajiye kayan hannunta agefe tad’ago meenah had’e da tallafota jikinta murya araunane tace, “Meenah meya same ki dama bakida lapia?!” Meenah tai shiru takasa magana saboda azabar ciwon da kanta da gab’ob’in jikinta sukeyi mata,cikin tashin hankali murya narawa aunty yafendo tace, “Gayamin ina.. ina..inane yake maki ciwo ajikinki?!” Kasa magana meenah tai se ambaliyar hawaye dake kwance shab’e shab’e a fuskarta ahankali tad’ago hannunta dak’yar tanuna kanta dake mata ciwo kamar xe fad’o don axaba, #SRKZI?! Ina kuke masoya makaranta littafin *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE?!* nagaisheku gaisuwa mai d’imbin fatan alkhairi.....! WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!* 💖?👨‍👩‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (_*MISS XOXO_*) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (_*Home of expert and perfect writers_*) *Devoted to* cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*) *Tukwicine agareku*: *Billyn Abdul*(Tawan) & my beloved sis(ya *Hajja ce*) *particular thanks goes to my two adorable daughters*: *Bitti Feedhom & dota Billy S Fari* _46:47_ nanahafsat.wordpress.com ____________ *A*hankali Basma tatako taxauna akujerar dayake kasancewar yana zaune ne akan kujera mecin mutane uku(3 sitters)se faman murmushi take shiko Kansa a k’asa yana latsa wayar hannunsa cikin Muryar jan hankali tace, “Sannu da zuwa sugar boo,yasu baba da kowa?!” “Alhamdulillah,duk suna gaidake” Yak’arashe maganar had’e da d’an d’agowa ya kalleta sanye take cikin cod-lace cream color anyi mashi kwalliya da stones maroon seta saka komai maroon harta agogon fatar dake daure a hannunta maroon ne, Tayi makeup amma ba irin heavy d’in nanba sosai ya amshi kalar fatarta ruwan wankan tarwad’a,bata cika tsayiba amma baxaka sata a jerin gajeruba,tanada d’an jiki amma ba sakwafkwaf ba,tanada kyanta dede misali ‘yar gayuce ta ajin k’arshe hakan yasa bak’aramar classy ce ita d’inba,komai nata dede gwargwado baxa’a sata alayin munana ba bakuma xa’asata ana kyawawava gatanande tsaka tsaki ce tubarkAllah... “Nagode sosai ina amsawa” Tafad’a kanta a k’asa tana wasa da zoben dake hannunta na tsakiya yatsunta d’auke da maroon nalle se wani dunk’ufar dakai take kamar yadda Ammanta tace kada tadinga k’ura mai ido k’uri wannan alamar rashin kunya ne, Hakan ba k’aramin burge yareemah Aliyu Hydar yayiba saboda da dane seta kusa cinyeshi d’anye saboda tsabar yadda take maidashi tv bata gajiya da kallon kyakkyawar fuskarsa mai cike da hasken kamala bata d’agoba ta nuna layla dake gefe shi bema lura da itan ba ganin yadda ta takure agefe guda kamar wadda tazo rok’on gafara, “And she’s Layla my bestie and also a sister from another momma” “Layla” Yafad’a atak’aice tare da d’an d’agowa yadubeta kasa kallonsa Layla tayi saboda wani kwarjini dataga ya mata ahankali tace, “Na’am! Ina yini?!” “Lapia lou” Yabata amsa atak’aice, “Ba ba..ri akawo maka ruwa” Tafad’a da sauri sannan tamik’e tafita cikin sassarfa bata jimaba tashigo tare dawasu yara d’auke da warmers na abinci se drinks da wani plate da akai folding da foil paper,sumsum Layla tafi ce bayan sungama kawo komai don bata zata haka Aliyun Basman yakeba sedata ganshi tarena ajinta, “Babe sakko kaci abincin” Cewar Basma dake faman loda masa grilled chicken akan fried rice dataji had’i da French salad rik’e baki yareemah Aliyu yai yana kallon abincin ganin yadda take lodashi kamar mutum goma ne xasuci d’an murmushi yai kafin yace, “m fasting” “No wasa kake right?! Yaxa’ai kai matafiyi kace azumi kake?!” Tace hakan tana d’an harararsa da wasa murmushi kawai yayi ahankali yasakko badon yanaso yaciba sedan karya gwaleta kawai don azahirin gaskia shiba ma’abocin abinci bane,caccakunar abincin yashiga yi yana yafitar loma yana kaiwa bakinsa kad’an yaci yabarshi yasha ruwan gorar dake gefe,Basma dake gefansa kuwa ji take kamar anmata bushara sewani murmushi take cikin jin dad’i wai yau itace ke xaune da yareemah Aliyu Hydar agidan su yakumaci abincin gidansu da niyyar neman aurenta Lalle addua bata fad’uwa k’asa banxa kamo sunansa da tadingayi a addu’oi tana kaiwa Allah kukanta daya mallaka matashi gashi yabata kuwa har fiye da tunaninta cikin tunane tunanen datake yine tajiyo muryar Aliyu, “What r you smilling for??” “Nothing much sugar boo” Murmushi kawai yai sannan yashiga fad’a mata abinda yakawoshi nan Basma tak’ara tabbatarwa tabbas itace son ran Aliyu Hydar tunda haryazo lallab’ata don kawai ta ambaci cewar yaudararta xeyi ta k’ara tabbatarwa da ba k’aramin so yake mataba tunda haryana ambatar ba gudu ba ja da baya, Yak’arashe xancen da, “May be gobe ko jibi ma xamu koma can school nida cousin d’ina danace miki shima yana England” “Okay Allah sarki, Allah ya kayku lapia nima Maybe next week xamu koma” “Ok great!so... Bansan yakuke al’adun bikin kuba I dunno ko zaki buk’aci wani abun yanxu kafin bikin” “No bakomai sugar boo,for now dasu baba xa’ai wannan maganar maganar events kuma nikam inason irin bukukuwan ku” Murmushi Aliyu Hydar yayi Kafin yace, “For real?” “Wallahi inason wushu wushu d’innan” Daria yashiga yi,Basma tai rau rau da idanuwa kamar xatai kuka, “Not fair sugar boo” “Sorry! Wushe wushe ake cewa” “Ohh,inason shi wallahi” “Dun worry za’ai maki ai traditional abune da ake agidansu bride but tunda keba yar yerwa bace xamuyi idan ankaiki maid” “Wow i just can’t wait” Hirarsu suka shiga yi yajima agidan har wajen 3 sannan ya mata sallama yatafi bayan yabata wata jaka ta calvein Klein d’auke da designers turaruka har parking lodge ta rakashi driver yajashi xuwa airport daganan flight yad’aga dashi se bornu, _*Bornu(damboa road)_* Mai martaba ne xaune shida hajia hajjagana mahaifiyarsu Aliyu Hydar hannunta d’auke da notepad dakuma pen da alama abubuwa take jotting aciki, “Kinga de Alhamdulillahi sun wuce stage d’in Ra’aski ko?next abinda yanzu xa’aje dashi shine kayan gawo, se kuma kworo ko tunda al’adane yasa” Mai martaba yace hakan yanabin Ammin da kallo cikeda so da tataciyar k’auna,d’ago Kai Ammin tai tana dubansa murmushi tasaki kafin tace, “Kai Abu uthamn ‘kworo’ai anwuce stage d’in tunda ita Aminatun ta yarda ko?!” “Hakane kuma to yanzu se sarte(sa ranar aure)ko?!” “Eh da sadawu(dowry)ba” “Tabbas,to yanzu abinda yarage shine ra’aski (gawo)se sarte da sadawu” “Eh” Ammin tace atak’aice sannan tai jotting a notepad, “To ita kuma d’ayar yarinyar dake kano kawu Mai Alooma yace yananan tafe xasuje shida kawu bunu suji yadda suke gudanar da hidimar bukukuwansu cikin week d’innan xa’ai komai agama shi Aliyun nace dasu ko gobe ma xasu iya tafiya” “To Allah yasanya alkhairi Ameen” cigaba da tattauna yadda abin xe kasance sukai shida Ammin gwanin ban sha’awa,sun d’au lokaci suna tattauna yadda komai xe wakana har cikin dare kasancewar anan xe kwana kwanakin dayake d’iba masu yajuyo kanta, _*washegari_* Cikin sauri Modu yake k’arasa shirinsa yadubi Aliyu dake wani gyare gyaren jikinsa kamar d’awisu dogon tsaki yaja kafin yace, “Haba london fa ba Abuja bane 12hrs ba kusa bane se wani banxan gyare gyare kake inkasa hak’urima baxaka jimaba xaka dawo musha biki” “You are sick..” Aliyu Hydar yace hakan tareda jan trolley d’insa yai gaba ko takan Modu bebiba dake faman ja masa tsuka a karo na ba adadi had’e da zabga masa harara, Gurin maimartaba suka wuce ya sanya musu albarka sannan yasa driver ya kaisu airport suka lula k'asar London cike da nishad'i, Mai Alooma Ghaji suna zuwa suka wuce kano,an tattauna komai cikin jin dad'i da nishad'i sannan aka bar shi akan cewar za'a bada kud'i sai Basma ta had'a kayan lefanta da kanta sai events d'in da zasu yi acan masarauta idan an kaisu amman duk suyi nasu abubuwan,basu jima ba suka koma shehuri nan suna shaidawa maimartaba yayi farin ciki sosai sannan ya bugawa Ammi itama ya sanar mata,sosai taji dad'i sannan ta fara shirin had'a lefan Aminatu kasancewar Mai Alooma yace baya bukatar komai amma maimartaba yana son ace tun yanzu Aliyu hydar ya fara kamanta adalci a tsakaninsu, A cikin sati d'aya aka sanya rana 2months, yareemah Aliyu hydar yana can aka sanar mai ta waya, yayi murna sosai tare da yin addu'ar samun kwanciyar hankali idan yayi auran, Hajja gajiram kam gabaki d'aya ta damu,tayi iya yinta dan ganin sun zauna da babagana amma abun ya citura yak'i kullum da abin da zai ce mata yana yi,yauma kamar kullum tayi shiru tana tunanin yadda za'ayi a warware auran nan na yareemah Aliyu hydar amma abun yaci tura sam yak'i ya tsaya suyi magana da hajja gajiram d'in,ganin tana neman takura mai ma yasa ya dena dawowa gidan sai wajan 12:00am sannan. Kallan jakadiya hajja gajiram tayi tana fad'in, “Jakadiya ina son ganin auran nan be tabbata ba har sai lokacin da babagana yayi ya zama sarki sannan shi ma yayi.” Jakadiya dake gurfane gaban hajja gajiram tayi k'as da kai sannan tace, “Allah yayi miki tsawan kwana ki dad'e kiyi k'arko,boka ya tabbatar min da cewar idan na kuma zuwa mai da zancen nan toh hak'ika wani zai...zai...zai mutu a cikin ku,koke ko shi yareemah babagana.”tak’arashe zancen cikeda rud’ani had’e da saurin dafe kuncinanta duka biyu gudun karta sha mari irin na kwanakin baya, Wani huci hajja gajiram ta dinga yi tamkar wata zakanya tana watsawa jakadiya wani mugun kallo,cikin takaici da bakin ciki ta furzar da isakar bakinta tana fad'in, “Jakadiya kiyi hattarar yi min zancen mutuwa, idan ba haka ba ke zaki rigani tafiya kafin ni mtwww.” Hajja gajiram taja tsaki,cikin ladabi da kaskantar da kai jakadiya ta dinga bawa hajja gajiram hak’uri tare da nuna mata cewar fad'ar boka na sambisa ne kuma ya tabbatar mata da hakan, “Tashi ki tafi sai na nemeki.” Jakadiya ta mik'e cikin rawar jiki sannan tayi hanyar fita da sauri har tana yin tuntub'e., Ana‘i sauran sati biyu biki lokacin Aliyu hydar da Modu indimi sun kammala duk wani abunda zasu yi acan London sun tattaro sun dawo gida Nigeria, shirye-shirye ake ta ko wanne b'angare Ammi ta had'a kayan lefe na gani na fad'a ankai can yola akwati talatin da bawaa na bride aunties na gurin uba abun gwanin ban sha'awa komai yaji a lefan customized ne lokacin da aka kai kayan Meenah na gani wani farin ciki kamar zata yi hauka murna kuwa ranar tayiwa su gid'ado alkawaruruka da yawa,data leka ta gano lodin kayan nan sai tayi sufa ta koma tayi tsalle tana juyi tana nishad'i bawai auran takewa murna ba kayan da kuma ganin komai yanzu ana yi dominta ga shi sai lallabata akeyi kamar d'anyan kwai shine ke sata murna ganin gold sark’oki da bangles kala kala wai duk suma natane,komai anmata shi kamar yadda ake a al’adar kanuri abinde se wanda yagani don alk’alami baxe iya rubutawa ba, In return suma dangin amarya Meenah suka basu kayayyaki kala kala dasu dangin khumrah da sauran kaya a casket abinde se wanda yagani ga special abinci anyi kala kala na kanuri da fulbe, _*Nida my ya hajja muna gefe muna kwasar abincinmu tatas muka lashe kwano no shame dan ni harda ihsan naiwa take away lol_* Su hajja gajiram se cizon yatsa suke suna kwashewa dangin hajjagana rankatakaf albarka ganin irin kayan da aka lafta wai duk dan mutum d’aya, B’angaren Basma ma abin se wanda yagani lefe yayi kyau beyond words duk wani kafar social media inka lek’a seka ganshi layla ma idonta yarufe sosai takeson tai aure yanzu sede babu mijin auren, *S*hirye shiryen biki ake from both site abinde se sam barka,Basma nata gwalli xata shiga gidan sugar boo ita kuwa meenah tata murnar rankataf akan kayan lefen da aka shirgo akace duk natane akansu take murna kullum da safe kafin tai komi seta fara duba lapiar kayanta kafinta kwantama seta bisu d’aya bayan d’aya ta irgesu tsaf..... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE* 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 _*Home of expert and perfect writers_* DEVOTED TO: *XARAH BUKHAR* TUKWICI: *TAWAN(Billyn Abdul)&MY YA HAJJA CE* PARTICULAR THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DOTAS: *BITTI FEEDHOM&DOTA BILLY S FARI*

Chapter 12 of 35