9
Wannan shafin nakune y'an HOME OF NOVELS da XOXO'S PALACE❤Allah yabarmu tare...!
..
Kamar baxe d'auka ba saboda nauyayyan baccin dake kansa sekuma yasa hannu ya danna had'e dasawa a handsfree.
"Yo man.."yafad'i hakan cikin sweetest sleepy voice d'insa
"The charming prince,yakake guy?!"modu indimi yabashi amsa
"Lapia Lou..you?!"
"Same here guy,ya nija?!hope Komi lapia?!"
"Qalau guy..."yak'arashe guy d'in yana rufe bakinsa da hammar bacci
"Bacci kake ne guy?!"
"Wallahi bacci nake amma natashi,"
"For real...katashi?"
"A'a a mafarki.. Idan kakira kamun shirmene you knw me yanzu xan katse kiran wallahi.."
"Calm down guy,kasande seda gist nake kiranka ko??anyways go and fresh up seka kirani akwai magana nima badan namakaraba dayau xandawo amma gobe Insha Allah xandawo.."
Seda gaban yareemah Aliyu yafad'i jin maganar da modu yayi,be iya bashi amsa ba sema kashe wayan dayayi,da sauri ya mik'e yafad'a band'aki,bewani jimaba yafuto da bathrobe yana tsane curly gashin jikinsa kasancewar jikin yareeman acike yake da yalwar bak'in gashi kwancacce ,jallabiya kalar xuma yad'akko yasaka bayan yafesheta da turaruka,sallar la'asar yagabatar kasancewar lokacin har yad'an gota yajima yana addu'oi kafin daga bisani yatashi yakoma bakin royal bed d'insa yaxauna tunani yad'anyi cikeda ajiyar xuciya yad'au wayarsa yai dialing number modu indimi yana addu'ar Allah yasa ba abinda yake kawowa a zuciyarsa bane yake shirin faruwa...
Ringing d'aya biyu modu indimi yad'auka yana dariya;
"What a day,yau the charming prince Aliyu SB dakansa ne yakirani??lalle abinda mamaki.."
"Guy.. Guy m not in the mood,fad'i abinda xaka fad'a please".
"Tohh your honor,da farko de munje outing da new babe danayi jia da shekarn jiya.. Guy kaga babe d'in,ashe kunada full Coca Cola shape a Oxford?!guy jiya na more rayuwata kuma guy...."be k'arasaba yareemah Hydar yasaki tsaki cikin fad'a fad'a yake magana;
"Kaine na mamajo,wanda mata suka dama?! Dama shine abinda yasa ka kirani?!"
"Allah de yabaka lapia,mutum har mutum amma bayaso ad'akko masa xancen mata,to nikam yanzu idan banyi xancen mace ba xancen me xanyi?!"
Cikeda takaici yareemah Aliyu Hydar yakatse kiran had'e dajan wani dogon tsaki..ringing wayarsa tak'arayi seda modu indimi yakira sau biyu be d'aga ba ana ukun yad'aga yai shiru yana sauraronsa;
"Arrogant mutum de beyibama wlhy,haba mutum se zuciya ta gaira babu dalili,anyways bawani abu bane,babane (mahaifin yareemah Hydar)yakirani d'axu asking me of your girlfriend ko bushra take kowa oho de namanta sunan,yana neman k'arin bayani akanta..."
"Mekace toh?!"
"Mexance kuwa?! Nace bansan taba,atak'aice ma nace nibanajin kokonada wata budurwa.."
"You are sick"shine kawai abinda yareemah yace
"To ai ba k'arya naiba,nibansanka da wata tsayayyar budurwaba,kullum fuska a murtuke kamar xaki,wacece xata kulaka,beside koda sunmaka magana rashin mutunci kake musu,kwanaki agabana kakusa marin wata yarinya saboda tace kana burgeta ko k'arya nayi?! Ko kuwa islaha course mate d'ina datace tana sonka ba cimata mutunci kayi ba koka manta ma kwanannan kaje kayi reporting aka canxa maka apartment saboda y'anmata suna damunka da love letters?kai k'arya kace wai surutun next door ne suke damunka.. Guy U're full of shit,Insha Allah seka mutu akan wadda xaka kwashi kashinka da hannunka..."
Duk surutun nan da modu indimi yake kojinsa yareemah Aliyu Hydar bayayi,shi danna ipad d'insa yakema da alama yayi zurfi a research d'in dayake..Jin shirun yayi yawa ne yasa modu indimi k'ara yin magana;
"Guy kanajina kuwa??"
"Oh no m sorry mekake cewa ne? I was carried away ne dawani Mail dayashigo na oil mogul d'innan na baba.."
"Kan babban bala'ii"shine abinda modu indimi yaketa furtawa..
"Yi hak'uri guy,kaji?!"
"Bakada kirki ko kad'an yanzu yadda kakewa yanmatan haka xakamun?! Yana kiraka ina magana saboda tsabar renin hankali kabar ni naita magana ni kad'ai kamar wani sabon mahaukaci"
"Naji naji, I will amend my mistakes"
"To yanxu yaxa'ai?? Ko kasan har baba yaturo da pj(private jet)yad'aukeni nikuma namakara nace se gobe idan Allah yakymu"
"I have no idea.."shine kawai abinda yace tareda gyara kwanciyar k'asaitar dayai
"To Shikenan Allah yakymu goben nide Allah yasa karka janyomun ace nima nakawo matar aure"
"To meye ai ashirye kake,kaida kakeda y'ammata lots,meye abun damuwa?! Ko hud'u akace kakawo nasan xaka kawosu"
"Whaaat??"
"Ehh wallahi kaida kakema kanka kirari da mata suna binka kamar rak'umi da akala seyadda kai dasu"
"Noo guy.. That aside,wallahi nikam banda wacce ayanzu nakejin xan aura"
"Saboda me??kaban daria ma"yak'arashe xancen yana daria k'asa k'asa
"Guy duk shirmene,had'uwar school ne kawai,dana gama school i assure you namanta dasu da rayuwarsu tundaga gate wallahi, I want a descent wife from a humble family,wa'incan duk tarkacene"
"You are sick.."yareemah Aliyu yak'arashe xancen had'e da sakin tsaki
"Allah i'm serious"
"To shikenan sekayiwa baba wannan bayanin baniba,kagama maganar?!i need some time to think"
Salati modu indimi yayi kamar wanda akayiwa mutuwa,murya asanyaye yace;
"Nagama most arrogant person on earth,Allah ubangiji yacanxa maka wannan halin"
Kafinma yakashe kiran yareemah yarigashi ,yana katse kiran yajefar da wayar akan sofar dake kusada shi,hannu biyu yasa yadafe kansa yalula duniyar tunani... Dak'yar yasake canxa kayan jikinsa xuwa farin yadi kansa ba hula ya nupi fada wajen mai martaba bebar wajen mai martaba ba harse da sukaci abincin dare tare sannan yakoma makwancinsa..
Washegari da safe; goma saura kwata modu indimi ya iso shehurin cikin d'aya daga cikin prado din mai martaba,da sauri fadawa suka iso suka karb'a hand-luggage d'in hannunsa tareda masa iso zuwa fada wurin mai martaba,suna yanayi sosai da yareemah Aliyu Hydar sede shi yanada hasken fata sosai kuma yanada jiki amma ba sosai ba,aji (alhaji)bunami indimi mahaifin modu indimi kawune ga mai martaba wato mahaifin yareemah Hydar kenan,komi tare mai martaba yakeyi masu kasancewar modun da shekara d'aya ya d'ara yareemah Aliyu hydar,tun a aji d'aya na secondary mai martaba yad'auki d'awainiyar modun yakuma d'akkoshi yadawo dashi hannunsa da xama har yanzu da suke karatu a waje,kowannensu shi yaxab'i makarantar dayakeso dakuma program d'in daxe karanta, shigar suit modun yayi k'irar blazer blue color yasha tie black yayi kyau ba k'arya sosai se wani shafa sajensa yake ganin jakadiya tarako wasu y'ammata xasu shiga mota da alama bak'in hajia gajiram ne dan daga sashenta suka fito,yana shafa saje yana kallonsu suma suna kallonsa dan bakad'an ba yatafi dasu,jakadiya nasakasu mota tajuya cikin sassarfa takoma sashen hajia gajiram tana zuwa ta zube ak'asa tana haki..
"Meke tafe dake?!"cewar hajia gajiram tafad'a cikin k'asaita.
"Allah yaja da ran uwar d'akina sarauniya uwargidah sarautar mata,ked'innan de kece babu sauyi wajen mai martaba,uwar gimbiya falmata yayar gimbiya ayiya,kaga mahaifiyar yareemah babagana sarkin gobe,Allah yaja da ranki uwar d'akina ki dad'e kiyi k'arko."
Murmushin jin dad'i hajia gajiram tai irin nasu na sarauta da alama taji dad'in wannan kirari da jakadiyar ke mata
D'aga kai tayi alamar tafad'i abinda yakawota nande jakadiya takaikaice tafara magana;
"Naje rakasu yaya jainaba da Amsa(hafsa) ne senaga motar mai martaba tashigo canake kayane aka d'akko senaga bahaka ba,Allah ya k'ara miki lapia,idanuwana sesuka ganemini modu d'an gidan kawu bunami na indimi,can nahangeshi shida fadawa sun mai iso cikin fada wajen mai martaba..."tanakaiwa nan tai shiru kanta a k'asa
Hajia gajiram tad'au lokaci sosai kafin tai magana,da alama wani naxarin take,lokaci d'aya ta d'ago jajayen idanuwanta da suka kad'a suka sakeyin jajir k'anana dasu aciki Kamar na mujiya tasaukesu akan jakadiyar datai tsiri tsiri da ido kamar tsohuwar kura,rannan a murtuke murya adashe cikin kanuri tace mata;
"Jekimun iso da yayya(hajia yakolo,kishiyarta)"
"To uwar d'akina nabarki lapia"da sauri hartana cin tuntub'e ta fita...
Part d'in amaryar tashiga wato hajia yokolo tana kishingid'e k'afafuwanta akan tum tum jakadiyarta na matsa matasu,cikin sauri jakadiyar hajia gajiram takwashi gaisuwa tareda fad'in abunda yakawota,gyad'a kai kawai hajia yakolo tayi,kamar me ciwon magana cikin harshen kanuri tace;
"Yo dai k'erma lukin...(to ganinan fitowa yanxu....)
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••
💜?👪
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan shafin nakune;
Humayra b (MELODY)da VESMERH er lele😘❤
10
Bayan modu indimi yashiga fada yad'ebi gaisuwa wajen mai martaba sun d'an tab'a hira,mai martaba yace dashi yaje yahuta tukun da safe xe nemeshi,d'akin dake kusa dana yareemah Aliyu Hydar aka gyarawa modu indimi kasancewar nanne dama d'akinsa,modu indimi yana fita daga fada ya nupi sashen hajia gajiram. Saboda abune dayaxama wajibi inde kaje masarautar tofa bayan ka kwashi gaisuwa wajen mai martaba to dole ka kwashi wata gaisuwar wajen matansa,yana zuwa sashenta jakadiya ta masa iso yashiga ya gaisheta murmushi fad'ade a fuskarta ta amsa kaida kagani kasan akwai wata a k'asa,shi kanshi modun yayi mamaki k'warai matuk'a bayan sungaysa ne ya nupi wajen hajia yokolo itama amsawan tai da fara'a;
"Banyi wushe(lapia qalau babana)ya ya makaranta an k'are kenan?!"
"Alhamdulillah Aunty.A'a nazo... Naxo ganin gidah ne kawai"yatsinci kanshi dabata amsa haka
"To Allah yabada sa'a"
"Amiin aunty nagode"yak'arashe xancen tareda mik'ewa tsaye
Sallama yamataa sannan yafice waje yanupi apartment d'insu wato b'angaren su yareemah Aliyu Hydar,d'akin yareemah Aliyu Hydar yafara nufa tareda yin knocking kusan sau biyar kafin yareeman yace;
"Yasss"
Ahankali modun yabud'e k'ofan yashiga,kwance yahango yareeman kansa asama yana kallon p.o.p da alama tunani yake jin sallamar modun ne yadawo da aliyun daga tunanin daya tafi,amsawa yai had'e da gyara xaman dayai..
"The charming prince..."modu indimi yafad'i haka yana me bin fuskar yareemah Aliyun da kallo had'e da bashi hannu su gaysa.
"Guy..yanzu kaxo?!"
"Noo nad'an jimafa though ba sosai ba"
"Oh okay.."
"Meke faruwane guy?! Fuskarka duk ya fad'a kayi looking so pale,lokaci d'aya kaman wani wanda kai wata kana cuta,haba mana daga maganar aure,idan nine kaima wallahi mata hud'u xan aura rana d'aya"yak'arashe xancen yana dafa kafad'ar Aliyun
Murmushi Aliyu Hydar Yayi sannan yace;
"You are sick..."
"M serious wallahi,y'ammata gasunan birjik a family d'innan ga y'ammatan family d'in uncle mai idris katakarmabe dake t'chad,gana uncle Goni Mele dake nan nan bulunkutu..."
Siririn tsaki Aliyu Hydar yaja had'e da mik'ewa tsaye da sauri modu indimi ya rik'o hannunsa yadawo dashi yana daria k'asa k'asa;
"Shikenan my mouth pim.. Anbar xancen .Yawwa d'axu xanshiga fada wajen baba nahango jakadiyar Aunty gajiram taraka wasu babes sunshiga mota,kagansu guy?!full option ga skin d'insu so gloomy kuma suna kama da aunty gajiram sosai,dan Allah ko kasan su?!"
"No I don't"shine kawai abinda yareemah Aliyu yace
"Please guy..."
"Kaima bakasan suba bare ni"
"To ni xanyi k'ok'arin sanin su waye,cuz babes d'innan akwai structures,though wadda tai laffayan tafi kyau"
"Okay fine...,ya kukai da baba?!"cewar Aliyu Hydar
"Nothing much,yace de anjima ze neme ni,koya ake ciki de i will let you know"
"Good"
Mik'ewa modu indimi yai had'e da d'aukar jakar system d'insa bin d'akin yai da kallo kamar me neman wani abu,sannan ya dubi Hydar daya sake maida kansa kan p'o'p kai kace tv ne a jiki tsabar yadda yamaida hankalinsa can yana tunani
"Guy nikam ina babagana?! Banganshiba tun shigowata"
"bansaniba wlhy,rabona de dashi tun jiya"yabashi amsa still kansa a p'o'p
"Okay... Tohm later barinje nai wanka nad'an samu nap"
"Alright "
Murmushin takaici modu indimi yai had'e da girgixa kansa tareda jajantawa irin na halin ko'inkula da yareemah Aliyu Hydar kedashi,abu meyakwan yayi baya se k'ara gaba yake,fita yai had'e da rufe masa k'ofar sannan yashiga nasa d'akin..
WASHEGARI;
Da safe bayan modu indimi yai wanka fada ya nufa a bakin k'ofar shiga sukai kicib'is da yareemah Aliyu Hydar yafito shikuma xe shiga,murmushi modu indimi yai masa gaisawa sukai sannan yace;
"Tun asubah amma kake nanko?? Thought you were still lying on bed kamar baby..."
Daria kawai Aliyu Hydar yayi bebashi amsa ba,shima modun dariar yayi sannan yashiga cikin fada,gaisawa modun sukai da mai martaba sannan mai martaba yafara magana;
"Nasan zakai mamaki k'warai matuka na abinda yasa nace kazo ko?!"
"E..Eh baba"modu yabashi amsa kansa a k'asa.
"To bawani abun bane illa wani temako dana keso kayimun ina fatan zaka bani had'in kai?"
Murya atsorace modu yace;
"Insha Allah baba"
"To modu wannan magana da zamuyi dakai tsakaninmu ne ni da kai sekuma Allah daya haliccemu.."
"To baba Insha Allah"
"Modu,shekara da shekaru kunsan ina fama da ciwon lupus,wanda haryaci k'arfina dole se anmun dashen k'oda wanda kafinnan dole ne se anyiwa wajen remedy sosai,shine likitana yace indena stressing kaina yakamata nasauka daga kan karagar mulki.. Ina fatan kasan inda maganata ta dosa?!"
"A'a baabaa"modu indimi yafad'i haka muryarshi a sanyaye
"To modu xanyi murabus ne daga karagar mulki kuma babu wanda ya cancanta anad'awa wannan rawani fyace Aliyu... Kuma kaga babu inda aka tab'a sarki babu Iyali ko??"
"Eh baabaa"
"To wannan shine abinda yasa nakiraka modu,bakomai bane fyace inaso ka bincikomin Wacece yarinyar da Aliyu yake nema acan,shin y'ar mutunci da dattako ce ko kuwa? Ina fatan ka fahimta??"
"K'warai baba nagane"
"To yacemin acan makarantar tasu take,harnake tambayar sa shin kasanta?yace a'a don basu gama dedetawa ba tukun,amma nasande baxaka rasa wata hanyar daxasan wacece itan ba ko?!"
"Eh baabaa Insha Allah zan fara gudanar da bincike da zarar nakoma"
"To Masha Allahu,naji dad'i kwarai dagaske,idan kagama shirinka xuwa gobe ko jibi seka koma saboda banason ad'au lokaci..."
"To baba"
"Kaima idan da akwai wadda kuka dedeta sekai magana"
"To baba amma bamu gama dedetawaba tukun"
"To Allah ya xab'i abinda yafi alkhairi,kaima kayi k'ok'ari ku dedeta kaji ko?"
"To baba"
Modu indimi yace hakan tareda lulawa duniyar tunanin karfa shima ai masa irin na Aliyu Hydar,duk xancen dame martaba yakeyi hankalinsa baya jikinsa k'arshen xancen kawai yaji;
"Zaka iya tafiya"shine kawai abinda modun yaji,
Rissinawa yayi yaiwa mai martaba sallama sannan yafito dede k'ofar fada yaci karo da jakadiya mangu(hadixa) jakadiyar hajia gajiram se raba ido take a tsorace,duk'awa tai tana gaisheshi ko takan gaisuwar data kemai bebiba yarab'a tagefanta ya wuce saboda yadda yakejin ransa,yana wucewa tasauke nannauyar ajiyar zuciya ganin bai gano komai ba,a d'ari taja lomatsatstsun k'afafuwanta tai sashen hajia gajiram.
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••
💜?👪
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Wannan babin nakine *_Aunty maijiddah😘❤Allah ya k'ara raya mana y'an biyu cikin tafarkin islama yakymu aurensu musha biki.!
11
Jakadiya mangu(hadixa)na xuwa wajen hajia gajiram ta zub'e a k'asa tana raba idanuwa bayan ta kwashi gaisuwa,wata baiwa dake gefan hajia gajiram ce tafara magana;
"Sarauniya ta amshi gaisuwarki jakadiya mangu,shin meke tafe dake wannan karan?!"
Jakadiya mangu tak'ara kaikace baki tana magana irin tasu wanda suka shahara a harkar munafurci;
"Allah yasake ja da ran uwar d'akina tadad'e tayi k'arko,kamar yadda jiya idanuwana suka gane mini modu bunami na indimi ban runtsa ba haryau danai asubanci zuwa fada.."shiru tai tana jiran amsar daxa'a bata
Firgigit hajia gajiram tai tareda mik'ewa daga kwanciyar k'asaitar datai Lalle jakadiya taxo da labari kenan,sallamar sauran bayin dake babban parlorn tai had'e da maida dubanta ga jakadiya mangu datai k'asa dakai tana jiran amsarta,dogon ajiyar zuciya gajiram tai sannan tafara magana;
"Kiyi hanxarin sanar dani meke tafe dake,shin meke faruwa?! Namiki alk'awarin kud'i me tsoka,had'e da tufafi na alfarma ko kuwa ki fad'i duk abinda kikeso ni gajiram namiki alk'awarin cika maki burin ko menene kike buk'ata"
"Nazo da labari marar dad'i wanda tun sanda najishi jikina bebar tsuma ba,uwar d'akina ina fatan abinda bakina da labb'ana xasu furta yanxu babu tsattsauran hukuncin daxe biyo baya agareni?"tak'arashe maganar cikeda firgici
Murmushi hajia gajiram tai wanda har seda wawakeken bakinta yadashe gutsatstsarun hak'oranta suka bayyana awaje.A k'arafafe tafara magana;
"Karki damu jakadiya mangu,kada ki manta ked'in ta wajen muce,tun kafin musan yadda zamuyi k'ullun kutingwilar barin hajjagana(mahaifiyar Aliyu Hydar)daga shehurin nan muke tare dake,kuma hardake acikin mutanen da suke cikin abu mafi soyuwa awajena da baxan tab'a manta alkairin da sukaimin ba domin kinbada babbar gudanmawa wajen sake dunk'ufar da rayuwar yareemah Ngari,tabbas ked'in wani haske ce arayuwarmu mangu,domin badan keba da bamusan taimakon da ko waye boka na sambisa ba da har bak'in asirinsa tareda aljanunsa xedinga bibiyar ahalin Hajjagana ba,tabbas tun kafin ki fad'i koma menene mangu dagayau na y'antaki kuma nak'ara miki matsayi kece babbar jakadiyar shehurin nan"
Yadda kukasan ancewa mangu inta mutu aljanna zata shiga haka tadashe hak'oranta da suka rine saboda tsabar cin goro,ta wangale mici micin idanuwanta had'e da gyara zaman gurfanen datai tafara magana;
"Tabbas banda bakin gode miki uwar d'akina,hakik'a kalmomin bakina dazan mik'o godiata sunyi kad'an,uwar d'akina kisani zan iya salwantar da rayuwata akan inganki keda iyalinki koyaushe cikin farin ciki (Mak'aryacin mutum beyiba*😹kujifa a life worth dying for,Allah karabamu da sharrin masu sharri/miyagun mutane)ke kika y'antani nadawo mutum kika sharemun kukana,uwar d'akina insha Allahu har izuwa ranar da mai duka ze karb'i numfashina baxan tab'a sab'a miki ba bare inbijire miki, nagode k'warai da Wannan kambamawa Allah ubangiji yaja da ran uwar d'akina ki dad'e kiyi kark'o"
shiru tai had'e da ajiyar zuciya tareda kad'a kai irin na jajantawa d'innan sannan tacigaba da magana;
"Da asubanci naje fada ko zan jiyo wani rahotan aikwa kunnuwana sunjiyo muni abinda harna koma ga mai sama baxan mance ba" nande ta fyed'e mata bindi harda wutsiya ma'ana tafada'a mata duk abinda tajiyo nadaga abinda mai martaba da modu indimi suka tattauna d'axu a fada....
Yadda kukasan jirgin sama haka gajiram tamik'e tafice bata zame ko'ina ba se b'angaren yakolo abokiyar asirinta kuma kishiyarta da suka ajiye tsoron Allah waje d'aya suka rungumi shirka(had'a Allah da waninsa)dankwa se abinda boka na sambisa yace dashi suke aiki koda kuwa abun yazarta k'ololuwa a shirka haka suke rungumar kowanne hukunci ya xartar agaresu hannu dubu bama biyu ba.......
12
Wannan shafinma nakine AUNTY MAIJIDDAH M😍Nagaisheki gaisuwa mai d'imbin fatan alkhairi💞may you be forever blessed😘❤
"Guy talk mana tunda kashigo kake shunning d'ina,nasande nine mai laipin right?! To nayi magana yanxu hope komi ya wuce?!"
Yareemah Aliyu Hydar ne yace da modu indimi hakan ganin modun tunda yashiga d'akin aliyun yakecin magani yakuma k'i masa magana se faman tunani yake yana tsaki..
Siririn tsaki modu yak'ara ja had'e da hararar Aliyu Hydar dake gefansa yana danna apple laptop d'insa lokaci lokaci yake d'ago kansa yana kallonsa
"Guy duk ba lefin kabane.., you are full of shiit,dama nasan haka xata faru kuma nasan kasani kawaide baxaka fad'a bane.."modu yabashi amsa yana sake sakin tsaki a karo na ba'a dadi
"Sure?!! Really?"Aliyu Hydar yafad'i hakan yana gwalalo manyan idanuwansa waje tubarkAllah
Nanfa modu yatuno yafara sakin layi bashiri ya canxa akalar maganar musamman daya tuno xancen dasukai da mai martaba sirrine tsakaninsu.(Seni mai rubutawa tareda ku masu karantawa mukada'i mukasan sirrin,kunsan modun naku da d'an banxan surutu yadda kukasan akuce tahaifeshi sekace ba'a gasa masa baki ba inya fara xuba kamar kanya)da sauri har yana in'ina yace;
"Wasa nake guy kawaide kajanyomun nima baba yace...."sekuma yai shiru
"Yace what??"yareemah Aliyu Hydar yafad'i haka tareda rufe laptop d'in dake kan laps d'insa
"Yace na nemo matar aure Kamar kai wai...."
Kafin ma yak'arasa maganar Aliyu Hydar yafara daria,daria harda rik'e ciki k'walla na gangarowa,laptop dake kan laps d'insa itama fad'owa tai ko ajikinsa haka yacigaba da daria yana nuna modun,shikan shi modun dariar yai sannan yasha kunu yana magana;
"Not fair guy,aika janyo mun rayuwata tana cikin ha'ula'i niyanxu ina naga wata budurwar da har xata kwantamin na aureta?"yak'arashe xancen yana tsaki
Seda Aliyu Hydar yagama dariarsa sannan ya goge k'wallar tareda maida dubansa ga modun daya k'ara tafiya tunani cikeda zolaya yafara tsokanarsa;
"Haba guy daga maganar aure ga y'ammatanan birjik idan ma hud'u akace ka aura ga y'ay'an gidan uncle katakarmabe dake t'chad gana uncle mele dake nan nan bulunku..."
bek'arasaba Modu indimi yajefa mashi trowpillows dake gefan kujera yana hararsa don yasan abinda yafad'a mashi jiya ya mayar masa,daria Aliyu Hydar yai had'e da girgixa kai yace dashi;
"Guy inma xaka nema budurwa kanema before ahad'aka da wata adanginnan kasande yanda shehurinnan yake da son auren zumunci kafin wani ko wata ya lik'a maka daughter d'inshi"Aliyu Hydar ya k'arashe xancen yana yatsina fuska
"Which is true kumafa,kan babban balai dole nasan abinyi. That aside ni wacece bush rat ko wa?!"
"No farm rat"Aliyu yabashi amsa yana tsaki
"No m serious,namance sunan ne who's she?!wacece tai sa'ar sace zuciyar the charming haka?!"
Murmushi Aliyu Hydar yayi kafin yai magana wayar shi tafara ringing yar nacin naku ce take kira 'Basma Oxford' sunan daya fito kenan,modu yakai hannu xe d'auka Aliyu Hydar yad'auke ya aje akan stool har sedata tsinke,modu yai murmushi sannan yace;
"Haba the charming kadena haka plss,ya yarinya xata kiraka kak'i amsawa ohh nagane bakasan naji irin taku salon soyayyar ne ko?!"
Kad'a kai kawai Aliyu Hydar yayi don yagaji da magana har ga Allah befiye son magana sosai ba haka nature d'inshi yake,shikwa modu kamar kanya haka yake zuba kafin Aliyu yace wani abin tuni modu yasako wata tambayar;
"A England take itama?!"
"Uhm"Hydar yabashi amsa
"Same course as yours??"
"Nahh..."
"To wanne?!"
"Ha'a haba guy spare my life pls wannan questions haka?!to cut it short basma sunanta tana karantar international economic relations,second year take..Shikenan"
Da sauri modu yad'au details d'in awaya bebari Aliyu Hydar yagani ba,sannan yace;
"At last kasamu perfect match d'inka yanxu"
"You are sick.."
"No m serious"
"She's just a Frnd more like a Frnd but not my galfrnd gat it?!"
"Wannan banxan turancin de yana nuna budurwar kace,fine!"
"M serious,itade tana sona but nide m trying to.. Kagane?"
"Okay seyaushe kenan?!"
"Guy i don't know,kawaide Ina neman zab'in Allah nagari kuma inason..."sekuma yai shiru
"Kana sonme?!"cewar modu
"I'm just waiting for the right time,banason rushing saboda inason A STUNNING LOVE STORY"Aliyu Hydar yak'arashe xancen yana tsotsan pink lips d'insa na k'asa kamar baby
Daria modu indimi yashiga yiwa Aliyu Hydar had'e da tsokanarsa har tsakiyar dare suna hira, da safe modu yashrya yatafi gaisheda iyayensa dake indimi bashi yadawo ba se dare,washegari da safe yahau jirgi se Oxford university England dan fara gudanar da binciken da mai martaba ya yasashi.....
Team#SRKZI?LOVERS😘❤I heart you all irin totally d'innan😘❤stay tune yanxu labari yafara😊don't be left out...!
Asha karatu lapia nasan har gobe kuna karantawa saboda tsabar yawa😊,Qurratul ayn da Rano gashinan ahutamin gori😎💃
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••
💜?👪
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Happiest bday mentor love🎂I love and adore you💯you are just a perfect person,your heart is huge and you care so deeply for everyone you let into your life with such gentle kindness . I am in love with absolutely everything you are and do.You are a gift of a person that I am lucky enough to call my own..Happiest bday once again sister(UMMI_A'ISHA)
_15_
"Wato hajia ciwon d'anki sihiri ne yamai k'arfi ajiki wanda akai amfani da bak'akaken aljanu tahanyar yimasa bak'in sihiri me k'arfi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 35