Share this page
iya jure typing ba ciki harda hidindimun makaranta na yau da kullum_ _Da wannan nake kira da babbar murya ga masoya wannan littafi da su k’ara hak’uri da nana hafsatu Insha Allah duk sanda nasamu time xan turo_ _Nagode Allah yasaka da khairan_ _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: 2018, 3:30:07 PM: Nana_Hafsaat💕: *```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE*``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 *```A STUNNING LOVE STORY*``` *```NA*``` ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 *```Home of expert and perfect writers*``` ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR*``` *```Edited by*``` _ya hajja ceh_ ```nanahafsat.wordpress.com``` _wannan shafin nakine uwar d’akina my mentor *Ummi_Aisha* ubangiji Allah ya k’ara maki d’imbin basira da kwarin ido..Rabbi yabar zumunci ya k’ara tsare ki ya d’aukaka ki aduk inda kika shiga a rayuwa_ *69* *SHEHURI* *B*illy na fitowa zata shiga motar da sarki Aliyu hydar ya bada umarnin a kaita gidan su kawai taji an shak'ota ta baya wanda shak'ar tasa ta sakin k'ara da faduwa k'asa tana dafe keyarta mamaki ya kusa kasheta ganin idanuwan hajja gajiram akanta sunyi jawur tamkar zakin da ya kwana hudu be samu nama ba,a razane billy ta mik'e jikinta na rawa hankalinta a mugun tashe ta fara neman hanyar guduwa,shak'ota hajja gajiram tayi tare da yarfa mata wani lafiyayyan mari mai matuk'ar zafi wanda yasa billy gushewar hankali na 'yan dak'ik'an lokaci,cikin tsananin b'acin rai ta fara magana, “Lallai Bilkisu da kin bari kin fita daga gidan nan da zaki gane cewar shine babban kuskuranki a duniya,kin cutar min da d'ah kina niyar guduwa saboda ke bakida hankali? Toh idan kinga kinbar cikin masarautar nan ki tabbatar yareemah babagana ya tashi lafiya kalau idan ba haka ba kema sai na miki abinda ya faru akan shi wuce muje.” Sum-sum-sum billy tabi hanyar da hajja gajiram ke nuna mata,wani mugun tsoran ta takeji bata kaunar taga wani abun ya had'ota da ita saboda ta gano cewar kanta kawai ta sani sai 'ya'yanta uwa uba bata tsoran kowa hatta mijinta.Hanyar asibitin dake cikin masarautar sukayi da alama wajan yareemah babagana zata kaita,nan da nan jikin billy ya fara rawa hankalinta yayi matukar tashi dan tasan duk abinda ya sameshi itace sila idan ya mutu ya zatayi? “Na shiga uku..!” Ta furta a fili ba tare da tasan kalmar ta fito wajeba,muryar hajja gajiram ce ta tabbatar mata da cewar a fili tayi maganar dan yadda taji ta bata amsa cikin kakkausar murya tace, “Ai baki shiga uku ba sai sanda kikaga kema kina cikin yanayin da yake, wallahi ina tausaya miki a duk lokacin da likita ya fito ya sanar min cewar yareemah babagana ya rasu wallahi kinji na rantse?kema sai kin bishi idan yaso sai nima a kasheni...” Fitowar likita ne yasa hajja gajiram yin shiru cikin tashin hankali take tambayar shi,kallonta likitan yayi kafin cikin girmamawa yace, “Rankishi dad'e muna son ganin bilkisu a ciki saboda ya damu hakan yasa muka kasa gano menene ya samu cikin nashi da yake ta faman rik'ewa amma yaki bamu had'in kai shi kawai bilkisu yake son gani,muna da tabbacin idan aka kawo bilkisun zamu samu mu gano matsalar har ya bamu had'in kai,so yanzu a kirata idan kuma tayi nisa muna son a yi duk yadda za'ai muganta a wannan lokacin.” Wata muguwar harara hajja gajiram ta sakarwa billy wadda ke tsaye jikinta sai kyarma yake yi,cikin takaici ta kalli likitan tare da cewa, “Ai gata nan likita,wannan ce bilkisun ita ce ke neman rayuwar shi muguwa azzaluma kawai...” Dr imran najin haka ya juya yana kallon bilkisu dake ta faman zubar da hawaye,a hankali ya furta. “Madam muje ciki ko?!” Yana gaba tana bayanshi kirjinta na bugawa tamkar zai tsage,suna shiga taga yareemah babagana a kwance rik'e da cikinsa yana ganinta ya mik'amata hannunshi alamun tazo gurinshi billy ta kalli likitan cikin tsananin tsoro dr imran ya d'aga Kai alamar taje,a hankali ta k'arasa gurinshi babagana yayi saurin rikota tare da matseta cikin jikinshi murya a wahale yake magana, “Please my billy dan Allah karki gudu ki barni ina sonki ina matukar kaunarki idan kika gujeni zan iya rasa rayuwata,ki yafemin duk abinda nayi miki son zuciya ne da rud'un shaitan dan Allah...” Shiru tayi jikinta nata faman rawa har dr imran ya kallesu cikin tausatawa duk da besan abinda ke tsakaninsu ba ya dai fahimci cewar ita bilkisu bata son shi shi kuma yareemah yana sonta so mai tsanani.tana zaune ya damk'i hannunta tamkar wani zai kwaceta a haka aka fara dubashi ita dai billy kad'an ne ya hanata sakin fitsari dan tsananin tsoro da tunanin abinda yasa taji anacewa matar shice ita. Sai da aka gama treatment d'inshi sannan dr imran ya kallesu yana dariya dan abun yanzu dariya yake bashi yace, “Sir ya kakejin cikin naka yanzu?!” “Normal dr ni tun zuwan matata gurin naji banajin komai yanzu ma gida zamu wuce.” Cewar yareemah babagana yana yi idanunshi cikin na billy wadda ketafaman kallon wani kwalin magani,dariya dr imran ya kumayi kafin ya k'arasa kan wani table yayi rubuce-rubuce jikin wani file sannan ya dawo yana cewa, “Okk zaku iya tafiya dama rad'ad'in naushin cikinne yasa kayi ta rik'ewa but maganin da kasha yanzu zai temaka maka sosai Allah ya k'ara lafiya ya tsare gaba.” “Amin..!” Yareemah babagana ya fad'a wanda har lokacin yana manne da jikin billy itako sam bata kallonshi wani tsanar shima taji saboda rik'etan da yakeyi, fatanta a yanzu kawai taje gida ta sanarwa da babanta cewar saceta yayi ya kuma yi mata fyade har yake ikirarin cewar ita matarshi ce. Mak'ale da juna suka fito cikin sauri hajja gajiram tayi gurinsu, kwace hannun babagana tayi daga na bilkisu ta juya tana zabga mata harara ta rikoshi tana shafar fuskarshi cikin kulawa, d'ayan hannun yasa ya kamo billy tare da sanyata cikin kafad'ar shi ya kalli hajja gajiram data bud'e baki yace, “Please Mami wannan itace zuciyata,janyeta daga gareni tamkar kin ciremin raina ne so please ki kyaleta...” Mamaki da tashin hankali suka dirarwa hajja gajiram tana k’ok’arin yin magana saigasu hajja yakolo da sarki maimurabus sun k'araso wajan,kallon hajja gajiram hajja yakolo tayi fuskarta cike da alamun tambayar ta yadda akayi har ta taho nan batare da tasani ba bayan tasan suna tare acan wajan jakadiya mangu.Ganin sarki maimurabus nayiwa babagana magana yasa hajja yakolo janyo hajja gajiram tana tambayarta abinda ya faru cikin takaici ta fara gaya mata. “Yoo banda sarkin gida yaje ya sanar min ai da tuni yarinyar can ta kashemin babagana,ina fitowa daga d'akin da aka kwantar da jakadiya basai muka had'u da sarkin gida ba,nan yake gayamin cewar ai matar yareemah babagana ta yimai aika-aika gatacen ma shegen sarkin nan yace a kaita gida,ina zuwa kuwa naga zata shiga mota na dawo da shegiya,shine shi kuma yake neman nuna min ta fini a gurinshi harda cemin wai zuciyar shice ita...” Ta k'arasa maganar cikin b'acin rai,ita kam hajja yakolo rasa abin cewa tayi dan tsananin mamaki tabbas ada sunayin nasara akan duk wani abu da suke kullawa amma yanzu komai warwarewa yake duk kuwa da iya uban kud'in da suke kashewa akan duk wani aiki da za'ayi musu.wani mugun tsoro ne ya fara shigarta dan tana tsoran kar asirinsu ya tono tasan abun bazai kare da jin dad'i ba gashi tana son mijinta dan sarki maimurabus namijine tamkar da dubu. Suna tsaye suka ga maimartaba yaja hannun babagana wanda ganin mahaifinshi be sa ya saki hannun bilkisu ba,tare suka wuce apartment d'inshi sannan suma hajja gajiram suka bishi suna tattauna yadda zasu bullowa alamarin. *_ADAMAWA YOLA_* Zaune suke suna hira suyi dariya suyi jimami kawai Meenah 'yan son girman suka zo mata ta kalli gid'ad'o tace, “Gid'ad'o kasan dai yanzu ni ba sa'ar wasanka bace bako?!” Kallonta yayi cikin tsananin mamaki ya fuskanci tunda tazo garin take nuna mishi wani girma da fifiko dan kawai anyi mata aure,shafa keya yayi yana kallonta kafin yace, “Eh amma nima yanzu idan akayi min aure babu abinda bazan iya ba ciki kuwa harda zamantakewar aure..” Da sauri Meenah ta zaro idanuwa tana kallonshi jin abinda yace,kai ta kad'a tana kallon gefe a hankali takai bakinta saitin kunnan shi tace, “Gid'ad'o dama kai d'an iskane?!” A kufule cikin jin haushinta yace, “A'a nafi karfin iska d'an guguwa ne ni kinji ko?!” “Uhmmm!” Cewar Meenah jin abin ya girmeta ko yaushe gid'ad'o ya zama d'an iska bata saniba?daga yin tambaya shine zai bata wannan amsar dan ya rainata,da badan karya k'ara narko mata wata babbar kalmar ba data kuma gaya mai wata sai dai taga shi dinma kyar yake ba kamar daba. “Meenata zo kiji muyi wani secret.” Cewar aunty yaruwaiya data shigo yanzu kasance war sunsake dawowa ganin Meenan,mik'ewa Meenah tayi tana dungurin gid'ad'o lokacin da taje zata wuce ta gefenshi,yayi kwafa snannan ya d'auki remote control ya fara canza channel.Meenah na zuwa wajan aunty yaruwaiya ta kama hannunta tare da shiga cikin bedroom d'in da take,zama suka yi sannan aunty yaruwaiya tace, “Meenah kinga dai ni ba sa'arki bace ba kuma k'awarki bace ba kuma kanwarki bace ni auntynki ce amma na ajiye komai ina koya miki surruka da dabaru na zama da miji wallahi idan kikayi wasarara sai dai kiji ance baah hydar zai k'ara aure ke kuma sai dai abarki da aure akanki keba mai aureba ke kuma ba budurwa ba kin zama huto dake da babu duk d'aya, “Kinga yanzu dole ki koyi yadda zaki damki mijinki ya zamana babu ta yadda zai ga abin kushewa a jikinki,kisan yadda zaki iya jan hankalinshi ya zamto koda yana cikin fada a zaune tunaninki bazai gushe a cikin zuciyar shi ba,yanzu naji ance jibi zaki koma da kin koma za'ayi biki ki tare saiki dage karki tsaya jin kunya mijinki ne d'an uwanki kuma yayanki kin ganeko?!” Ajiyar zuciya Meenah ta sauke cikin turo baki tace, “Aunty yaruwaiya jibi fa naji kina cewa?ni wallahi ban gaji da nan ba shi kenan daga zuwana za'a wani ce na koma sai kace ba'a sona...?!” Tayi maganar tana turo baki cikin shagwab'a wadda ta zama jikinta, kallonta aunty yaruwaiya tayi cike da so da shakuwa tace, “Eh kinsan dai halin Baffa yace shi bega zaman da kikeyi anan ba gara ayi bikin ki tare yasan yayi miki aure." “Kaji kajifa Baffa ni wallahi ban shirya komawa ba kawai a kaini wannan gundumemiyar matar tashi ta dinga zazzaro min idanuwa wallahi bana sonta saboda ta fiye sa idanuwa.” “Toh ya zakiyi Meenah tunda zaman tare ya had'aku?ni dai fatana karki wani tsaya yin banzan kishi na hauka,kiyi kishinki mai aji sannan ki kwato zuciyar mijinki ya zamto kece a cikin zuciyar shi kin gane ko?!” “Eh..” Kawai Meenah ta fad'a amma iya kufula ta kufula dan batason komawa saboda ko gidajen kawayanta bataje bare a kaiga na yayunta amma Baffa yace ta koma shawarwari masu muhimmanci aunty yaruwaiya ta bawa Meenah wanda idan har tayi amfani dashi zataji dad'i zakuma mata amfani aduk inda ta samu rayuwarta. A cikin kwanakin da suka ragewa Meenah aunty yafendo ta fara tsumata gaba d'aya sun tasata a gaba aunty Maijidda nayi aunty yafendo nayi aunty yaruwaiya nayi gabaki d'aya Meenah ta sauya ta k'ara haske fatarta sai faman walwali da shek'i takeyi,jikin yayi luwai-luwai ita kanta Meenah jin dad'in tab'a fatarta takeyi dan tsabar taushin da ta kuma yi ga kamshin da ya kame jikinta ko bata saka kayaba haka zakaji jikinta nata tashin kamshi. Ana’i gobe Meenah zata koma duk suna zaune a katafaran parlorn Mai Alooma Ghaji kamar wasa Meenah ta tashi tare da cewa, “Excuse me.” Fita tayi tayi hanyar apartment d'in aunty yafendo dan d'akko wayarta tana son kiran su Ammi,tana yin kwana kawai taji anyi sama da ita ta bayanta nan da nan ta fara ihu tana shure-shuren sauketa amma ina saida aka danganata da cikin d'aki sannan taji an matseta ana shinshinar wuyanta,kyarma jikinta ya farayi hawaye kuwa tuni suka cika mata kunci yayinda kirjinta ya tsananta bugawa tamkar zuciyarta zata fito.A hankali kuma taji an sakala hannu cikin saman kirjinta an d'ora da alama sonjin yadda yake bugawa za'aji ita kam ta rintsa idanuwa jira kawai takeyi taji meza'ayi mata. “My sweet wife.” Taji muryar sarki Aliyu hydar sassanya mai dad'i ta daki dodan kunnanta Meenah tayi saurin juyowa cikin tsananin mamaki take kallonshi shi kuma ya rungumeta yana sake zura hannunshi cikin rigarta saurin turewa tayi tana turo mai baki cikin shagwab'a tace mishi. “Kai!Ya Aliyu ni wallahi kabani tsoro na d'auka walakiri ne yadda naji ana neman d'aukar raina..” “Uhmm My Meenah walakirifa kikace..” “Toh ai kaine ka bani tsoro ni banma san na fad'a ba yaushe kaxo ya Aliyu?!” “Yanzu kuma bazan tafiba sai dake domin ina son ganinki a kusa dani,ace sarki guda amma ba shida mata.” “Nifa sai nan da 3weeks zan koma dan wallahi ban gaji da nan ba.” Murmushi yayi wanda ya k'ara kawata fuskarshi sannan ya d'ago kanta yana kallonta yace, “Kiji tausayina mana Meenah kinsan dai yanzu ke d'aya gareni,a da bana damuwa wai dan banida mata but yanzu ina son ganinki a kusa dani,inajin wani farin ciki a zuciya ta duk lokacin da nake tare da ke,hakika da nabi *SON RAI* na da yanzu ina cikin damuwa amma yanzu har cikin zuciyata ina alfahari da *ZAB'IN IYAYE* na Meenah kice zaki bini ayi bikinmu kizo ki tare a gidanki dan yana can naga baba yasa an cigaba da gyara miki shi please...!” Kallon shi kawai take cikin mamakin jin yace mata wai ita kad'ai gareshi ko ya manta da yana da Basma matarshi ta farko?batayi auneba kawai taji ya d'auketa cak ya wuce da ita cikin bedroom apartment d'in da suka sauka shida Modu,kwantar da ita yayi sannan shima yabita ya kwanta a jikinta bayan ya cire kwalliyar dake fuskar shi.Zaro idanuwa Meenah tayi ganin shi tamkar wani balarabe sosai yayi mata matukar kyau idanuwanshi sunyi ciki kai da kagani zaka san akwai abinda suke so,ta maida idanunta kan gashin kanshi wanda yake yar-yar tamkar na indiyawan asali baki sid'ik kafin wani lokacin sarki Aliyu hydar ya zura bakinshi cikin nata yana yawo da harshenshi ita kuma tayi lamo tamkar wadda ruwa ya cinye. “Baby Meenah kinga dai na ajiye duk wani girma da nake dashi nazo gareki please dan Allah karki bani kunya ko ki wulakantani kinji...?!” Yayi maganar cikin sanyin jiki bayan ya cire bakinshi daga nata, jikinta duk yayi sanyi gashi duk ya karya wani kudiri nata tana jin wani abu na yawo a cikin zuciyarta da gangar jikinta ta d'ago suka had'a ido tayi saurin kwar da kai tana murmushi,ganin haka yasa shi jin dad'i tare da ci gaba da jagwalgwalata shaf ya manta da cewar Mai Alooma na jiranshi saboda Meenah ta rik'itashi ya manta da cewar akwai abinda yazo yi zai wuce bornu a ranar. Sun jima a cikin apartment d'in har kusan karfe 4:00pm sannan ya rabu da ita amma tare sukayi sallolinsu ko yunwa basuji ba bare su nemi abinci.sai da ya kammala kimtsawa sannan yayiwa shamakin shi waya cewar yazo yana zuwa ya shiga a parlor ya gansu a zaune duk kunya ta kama sarki Aliyu hydar kafin ya maze yace a gyara mai rawaninshi.Shar suka fito Meenah ta saci kallonshi tamkar bashi bane a gado ji yadda yanzu yayi kamar bashi ba ta tab'e baki zuciyarta fal mamaki,yana lura da ita ya matsa dai-dai sanda zasu fita kusa da kunnanta yace a hankali, “Ki maza ki dawo nasan kema a matse kike dan naga tun lokacin bikin Modu kike da muradina karki damu zanyi gyaran jiki yadda zaki sameni fresh fiye da yadda kike tunani muchh.” Ya k'arasa fad'a tare da sumbatar wuyanta,da sauri ta cisge jikinta sai gudu bata tsaya ba sai a d'akin aunty yafendo dan tasan nan ne kawai bazai iya bintaba.dariya yayi ba tare da yabita ba ya wuce gurin Mai Alooma Ghaji cike da kunya gani yake kamar ya gano abinda yayi,cikin dattaku Mai Alooma ya kalleshi tare da cewa. “Rankashi dad'e gobe insha Allahu suma su Aminatu zasu tafi nafison ayi bikinku tun kafin tazo ta canza ra'ayi wani ya huremata kunne Aminatu har yanzu ba wani ishashen wayo bane da ita idan kuwa tana gidanta tasan dole ita d'in matar wani ce dan haka ka fara shiri ranka shi dad'e...” Babu abinda ke bawa Aliyu hydar kunya irin yaji Mai Alooma yace mai rankashi dad'e duk sai yaji wani gingim kamar kanshi zai fad'o k'asa,sun jima suna tattaunawa sosai Mai Alooma ya babbashi shawarwari masu kyau da amfani kafin ya tashi yaje suka gaggaisa da mutanen gidan dan basu gaisa da kowa ba sai Meenah daga nan suka wuce yana Allah Allah gobe tayi Meenah ta dawo ayi biki ya huta da tunaninta... #Assalamu Alaykum beautiful people...! _A k’ara hak’uri da matar yusleem insha Allahu dana kammala komai xaku jini..Sannan ina mik’o d’imbin gaisuwa ta agareku ahar kullum ina sonku kuna raina ,Rabbi yabar zumunci__*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` _*sweeto..Ina kike sweeto nafee anker?!.Kina Ina?!To ki matso kusa tawan tamu y’ar Real Madrid wannan shafin nakine ke ked’ai domin jin dad’inki.._ *70* *SHEHURI* *S*una zuwa a babban parlorn maimartaba maimurabus suka yada zango still babagana na rik'e da bilkisu tamkar yana tsoran karta gudu zama sukayi dukkan su sannan maimartaba ya kalli babagana yace, “Ya jikin naka yanzu ina yake maka ciwo?!” “Bako ina baba”. Cewar babagana wanda yaji billy na k'ok'arin kwace jikinta daga nashi duk abinda suke yi maimartaba na kallonsu yayi kamar be gansu ba sai ma cewa yayi, “Toh kozan iya sanin abinda ya faru tsakaninka da matarka har takaiga ga zuwa clinic?!” Wiki-wiki yareemah babagana yayi yanajin tsoran abinda zaije ya dawo,tunda yake be tab'a jin kunya ba irin asirinshi da yake shirin fitowa wajeba.A d'ari-d'ari yake kallon bilkisu cikin kalar tausayi alamar karta tona mai asiri amma ina ta riga ta shiga rud’ani jin kowa yana ce mata matarshi ce dan haka tana son taji yadda akayi ta zama matarshi jiki na rawa tace, “Ranka ya dad'e ina neman alfarma ina kuma son kayi min adalci domin kunnuwana suna jiye min abinda ni nasan ba haka bane,shin ya akai na zama matar wannan azzalumin mara imani da tausayi?ya cuceni ya ci mutuncina dashi da mahaifiyar shi sannan ya maidani gonarshi wajan ban ruwanshi da duk lokacin da yake son yi sai ya nemoni shin tayaya na zama matarshi bayan nasan matsayina be kaiga shigowa cikin zuri'ar nan ba??!” Sosai kan sarki maimurabus ya kulle sam ya kasa gano inda zancen billy yasa gaba hakan yasa shi kallonta tare da cewa, “Bilkisu kinsani a duhu matuka,a yadda nasani ked'in matar d'anace wato yareemah babagana kuma ni da kaina na d'aura auranku.” “Innalillahi wainnailaihir raji'un na shiga uku wannan wace irin muguntace a dakeka sannan a hanaka yin kuka saima d'aureka da za'ayi?, “Ranka ya dad'e wallahi-wallahi tallahi banason shi na tsaneshi duk duniya da za'a harhad'o min duk mak'iyana a bani bindiga ace na kashe mutum d'aya babu shakka da shi zan kashe da hannuna saboda shi d'in azzalumine a cikin zuciyata da gangar jikina dan Allah dan manzon Allah s.a.w ranka ya dad'e kace ya gaggauta sakina saki uku yadda bazanyi tunanin k'ara yin mu'amula dashi ba dan Allah.” Sosai ta d'aureshi sannan mamaki da al'ajabi suka taru sukayi mai dabaibayi a cikin zuciya,babagana kuwa tunda ta fara magana jinshi da ganinshi suka tsaya cak yayinda hajja gajiram da hajja yakolo suka zazzaro idanuwa jikinsu ya hau rawa ba kamar hajja gajiram wadda takejin wani rad'ad'i a cikin ranta dan haka a kufule ta kalli bilkisu cikin takaici tace, “Ke dalla yiwa mutane shiru dan ubanki dan kin samu an tsintoki daga cikin kunci da bakin talauci shine yanzu kin waye zaki yiwa mutane d'ibar albarka?Toh shima ya tsaneki baya sonki ked'in banza ked'in wofi da zaki zauna bakiji kunyar iyayanshi ba ki dinga furta wad'annan kalamin toh...” Bata k'arasa ba taga babagana yayi gurfano wajanta hawaye tamkar bakin famfan da ya lalace yana mata magana hakan yasa hajja gajiram sakin baki galala kamar wadda aka fasawa jitayi yana cewa, “My billy ki fad'i duk abinda zaki fad'a na cancanci fiye da haka amma kidena furta kalaman cewa na rabuda ke nikam har abada bakina da hannuwana bazasu tab'a yin hakan ba,wallahi ina sonki ina kaunarki bilkisu kece rayuwata kidena furta cewa na sakeki domin fad'in hakan sab'one ni dake mutu ka raba har abada.” Gabaki d'aya tsayawa sukayi suna kallanshi tsawan wani lokaci kafin yayi gyaran murya ya fara magana, “Ya isa haka bilkisu ina sonjin meye had'inki da yareemah babagana tun kafin ki zama matarshi.” Kuka takeyi sosai musamman idan taji ance mata matarshi sai taji tamkar zuciyarta zata fito dan bak'in ciki,sannu a hankali ta samu kukan ya d'an lafa sannan ta kwashe iya abinda ta sani har kawo yau data farka ta ganta tare dashi,sosai maimartaba yayi mamaki sam ya kasa tantance a duniyar da kunnuwanshi suke kafin yayi magana yaji babagana na cewa, “Wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba sai dai idan su Mami ne sukayi mata asiri dan dama sabonsu ne.” “Kai babagana banason sakarci kaji ko,kana da hankali kake gayawa iyayanka haka?toh ka shiga hankalinka,sannan ke bilkisu naji duk abinda kikace kuma na aminta zan nenar miki hakkinki nayi miki wannan alk'awarin amma sai da sharad'in zakuje yanzu clinic a aunaki idan har bakida juna biyu toh a yau zan k'arb'ar miki hakkinki amma idan akwai ciki toh hakika zan jirkinta harsai lokacin da kika haihu insha Allahu..” Wani sabon kukan ta fashe dashi tare da rik'e ciki tana fatan kar Allah yasa tana dashi domin ta tsani me cikin shi kuwa babagana a gurin yayi sujjada ta rokan Allah yasa akwai domin yana sonta yana masifar kaunarta da bukatarta a kusa dashi.muryar sarki maimurabus ce tasa shi ya d'ago sai faman kallon billy yake amna fur tak'i su had'a ido dan jin ranta takeyi tamkar zai fita yace, “Sai dai duk da haka bazamu barki anan ba koda kinada juna biyun har sai lokacin da mukaga ya kamata ki dawo gidan ya dace yanzu bari nasa a kaiki dan a dubaki.” Da haka yasa wasu bayi suka tafi da ita sai dai ya hana babagana binsu sannan yace wa su hajja gajiram suje zai nemesu idan ya yanke hukunci murnar su d'aya da beyi zancensu ba musamman hajja gajiram wadda aka ce ta zage billy harda bata kudin toshiyar baki da haka suka tafi sannan ya kira Dr kafin ma su k'arasa nan suka yi magana dashi sannan ya kashe kiran. Suna zuwa kuwa akasata tayi fitsari ana aunawa aka ga positive idanuwan billy akan shi taga sai faman murmushi yakeyi kirjinta ya hau dukan uku uku da sauri ta mik'e tsaye tare da cewa, “Dr meya faru?Aidai banida shi ko? Dan Allah dr idan kasan akwai please badan niba badan iyayena ba dan Allah ka cire minshi karka bari aji cewar ina tare da cikin wannan azzalumin.” Murmushi ya kuma yi sannan ya zauna yana kallonta yace, “Ranki ya dad'e ki kwantar da hankalinki baki da wani ciki amma me yasa bakison ciki abinda naga kowace suruka ta gidannan tana muradin son taga an aureta ta ajiye tarihi amma ke naga sab'anin hakan...?!” Jin ya shaida mata cewar babu yasa ta sauke wata katuwar ajiyar zuciya ba tare da ta saniba kawai ta saki wani kayataccen murmushi hakika yau zata yaddar da kwallon mangwaro dan ta huta da kuda,da sauri ta mik'e harda yiwa dr godiya ta fita bayin kuma suka bita a baya kamar jeloli.tana tafiya Dr ya kira sarki maimurabus yana d'agawa yace, “Ranshi dad'e anyi yadda kace sannan tana dashi har na tsawan watanni uku gata nan ta taho kuma daga gani tana cikin nishad'i dajin cewar babu.” Cikin jin dad'i maimartaba yace wa dr, “Na gode sannan ina son ya xamo daga ni sai kai ina fatan ka fahimce ni?!” “Insha Allahi rankashi dad'e Allah ya kara girma da lafiya.” “Amin.” Dai-dai nan su billy suka shiga murnarta har ta gaza boyewa ta tsugunna tare da cewa, “Allah ya temakeka munje likita kuma ya tabbatar min da cewa babu.” “Toh bilkisu yanzu zansa a maidake gidan ku kafin na kammala bincike na da kuma shawarar yadda za'ayi na kwato miki hakkinki kinji ko?!” Murna sosai tayi sai faman

Chapter 24 of 35