Share this page
idan mutum ya xabeshi se yafi dacewa fid dunya wal alkhira?!” Cikin murya ahankali Meenah tace “ZAB’IN IYAYE.” Tana gama fad’a Aliyu ya d’agata suka haura stairs din sama sedaya direta akan gado sannan shima yakwanta agefanta bayan ya janyota jikinsa, “Kece ZAB’IN IYAYE na saboda haka kece SON RAI na Meenah duk wata wadda xatazo abayanki take ked’innande kece kuma har yau inaiwa Allah godia danabi zabin iyaye nai biyayya Allah ya bani ke amatsayin matatah I love you so much Meenah Nd I promise to make you the happiest you can be” Gyara mata kwanciya yai akan pillow bayan ya xame jikinsa daga nata peck ya dora mata akanta kafin yace, “To nixan koma sashen Basma kinsan acan nake yau,ki kira kilishi ta shirya miki kayan pls jjrginmu na safe ne..” Kamar baxatai magana ba sekuma tace, “Ya Aliyu dagaske bada sis Basma xamu tafi ba wai?!” “Da ita xamuje mana sede su a London xamu barsu itada layla bayan anyi suna xasu karbi certificate dinsu na bsc a school sekuma masters da xasu fara kekuma lokacin kin haifar mana babyn mu ko?! Amma ni dake Paris xamuje ba London ba saboda haka sunan kiara kawai xamu halarta semu wuce France anyiwa doctors magana saboda xaki xama on meds kafin Allah ya saukeki lapia ko?!” Gyada kai Meenah tai alamar eh,sake sumbatar goshinta yai yamata saida safe annan ya fice yakoma sashen Basma wadda hartai tafiyarta ta kwanta da alama haushi taji girgixa kai kawai yai sannan ya haura sama d’akin nata yana murmushi... *WASHEGARI* A whole private jet ne ya cinye yan tafiya sunan Aisha kiara kasar England wato London,tsawon awanni goma sha biyu ne yakaisu kasar ta England inda motoci suka daga dasu daga airport xuwa wani hotel dake birnin Birmingham kafin da safe suka shirya suka tafi gidan nasu kiara duk su aunty yaruwaiya su Ammi su billy su Falmata dasu Affy duk sunje gimbiya Asmy ce kawai bataje ba kasancewar tana nata laulayin ciki dukda ba babba bane hakan be hana sarki Ngari kasa ya tsare din baxatan ba taso xuwa domin har kuka tai dakyar yashawo kan abarsa ta hak’ura... Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Modu wato yayya khadija inda xa’a dinga kiranta da ihsaan anci ansha an wataya ankuma kashe tsutsar ido Aysaa dama tana kasar tana karatu a Oxford itace tasake xaxxagayawa dasu sukaga garin sosai,kwanansu bakwai suka juya Nigeria bayan Aliyu yakai Affy Florida taga Disney castle dama shi kad’ai ne alkawarin da be cika ba acikin alkawararrukan daya dauka mata.. Se bayan kwana biyu sannan Aliyu da Meenah suka daga xuwa kasar France,. Sosai Meenah take samun kulawa a k'asar France dan nurse guda aka bata take kulawa da ita a gida yayin da shima Aliyu hydar yake bata tashi kulawar ta musamman,kullum suna tare basa tab'a rabuwa duk inda d'aya yasa k'afa yacire toh d'aya ma sai ya d'ora tashi abin nasu gwanin ban sha'awa.satin su uku a France Basmah taje kan dole Aliyu hydar ya rage nanik'ewa Meenah sai dai zuciyar shi na azabtuwa duk da cewar hotel d'aya suke sai dai kowa da room d'in shi. Lokacin da cikin Meenah ya isa haihuwa Basmah bata nan taje shan iska ya rage daga Aliyu sai Meenah tana kwance kanta saman cikin shi yana matsa mata yatsun hannunta tayi saurin zare hannun tare da mik'ewa zaune,Aliyu hydar shima ya tashi yana kallonta sai faman wulkita idanuwa take yi tana cizon lips ya janyota jikinshi Meenah tayi saurin zarewa yace, “Ajlaal ya haka?!” Cikin turo mai baki tare da rik'e bayanta tana yarfa hannu tace, “Bayana ne zai fad'o Yaya na shiga uku.” Yana jin haka hankalin shi ya tashi da sauri ya d'auki wayan shi ya kira nurse dama tana cikin hotel d'in dan haka basu jima ba sai gata tayi ma Meenah tambayoyin yadda takeji ta gaya mata nurse d'in tace suje hospital,d'aukar ta yayi domin ba wani nauyi ne da itaba sai dai cikin ne daya d'an k'ara mata suka shiga mota sai asibiti suna zuwa akayi scanning doctor yace haihuwa tazo Meenah najin haka ta fashe da kuka tare da ruko Aliyu hydar wanda jikinshi yayi sanyi ganin yadda take kuka tace. “Yaya ka yafemin kasan ance idan mutum zai haihu k'afarshi d'aya a duniya d'aya a lahira take,ni dai na yafe maka kace masu aunty Yafeendo su yafe min dasu Ammi da...” Yareemah Aliyu hydar yayi saurin toshe mata baki yana girgiza mata kai zuciyar shi na bugawa yasa tattausan hannunshi yana share mata hawayen dake zirarowa a fuskarta yace. “Ya isa haka Ajlal duk wannan abun ba zaisa ace mutum ya mutu ba, idan kika duba layla ta haihu gata nan da d'anta Bilkisu ma biyu ta haifa kuma duk suna nan da rai, ga Aisha (kiara) ma ta haihu lafiya kema insha Allahu Ajlal lafiya kalau zaki haihu kinji kiyi ta addu'a kina innalillahi wa’inna ilahirr rajiun kinji?!” Shiru kawai tayi mai ba tare da tace komai ba dan hankalinta a mugun tashe yake,nurses ne suka zo suka janye gadon Aliyu hydar ya bisu suna zuwa labour room aka dakatar dashi suka shiga da ita tana ta kiran sunan shi ya tsaya a bakin k'ofar hankalinshi a tashe yanajin tamkar ya rushe da kuka. Yana tsaye a reception sai faman addu'a yake mata sai ga kiran Basmah, da kyar ya zaro wayar daga aljihunshi ya kara akunne yaji Basmah na tambayar suna ina. “Hospital..” Haka kawai ya iya ce mata cikin tashin hankali tace, “Aminatu ce zata haihu?!” “Eh.” Ya sake fad'a daga haka ya ajiye wayan Basmah najin haka itama ta taho bayan ta bugawa layla waya ta gaya mata. Basmah na shiga dai-dai lokacin aka fitowa da Aliyu hydar baby d'inshi a cikin shawol nurse ta mik'e mai tana fad'in, “Congratulations sir.” Kan na k'asa yayi saurin d'agowa yana bin hannun nurse d'in da kallo baki bud'e ya kasa karb'a sai Basmah ce ta k'araso da sauri ta k'arb'i boy d'in, kallon nurse d'in yayi yana kallon k'ofar d'akin da Meenah ke ciki kamar ta gano abinda yake son tambaya tayi murmushi tace, "Don't worry sir your wife is fine and she says to give you this..” Karbar farar paper hannunta yai yana dubawa”Thanks nd by the way I hate you ..”shine sakon da Meenah ta rubuto a bashi.. Sai a lokacin Aliyu hydar yayi murmushi dan ya gano ma’anar sakon Meenah ya juya yana kallon jaririn dake hannun Basmah yana cewa,. “Tell her I love her beyond her wildest expectations..” Jin ya amsa yasa nurse d'in juyawa ta koma room d'in tana dariya da murnar an gane sakonta. Sai da aka gyara Meenah sannan aka basu damar shiga bayan an maida ita wani gadon... Hak’ik’a Allah ya zubawa yaron Meenah kyau sede ace tubarkAllah kawai domin har kyauta asibitin suka basu kancewar anjima ba’a haifi kyakkyawan jinjiri irin sa ba,sosai yake yanayi da Aliyu Hydar sede sumar kan sa ta Meenah ce hade da yanayin manyan idanunsa duk na Meenan ne, Yareemah Aliyu Hydar yad’au son duniya ya dorawa babyn har d’an haushi mutuniyar taku takeji don gab’anci,jirgi biyu yan uwa da abokanan arziki sukai zuwa kasar France don halartar sunan baby boy, Ranar suna yaro yaci sunan Mai Alooma Ghaji wato baby Alooma Aliyu Hydar SB domin bai manta halaccin da baffan nasa yai masa a duniya ba shine yai ruwa yai tsaki akan auren sa kuma ta tsatsonsa ne ya hadu da abokiyar rayuwar sa wato Meenah wadda takasance zabin iyayensa abun alfaharinsa,Sultan shine sunan da xa’a dinga kiran babyn dashi anci ansha an wataya an kuma aje record don duk wata kafar yada labarai ta media xancen sunan baby sultan akeyi don harta sarki Ngari Shehu sedaya halarta shida gimbiya Asmy wanda ke kunshe da nata cikin.. Baby sultan yanashan dawainiya awajen mahaifinsa da kuma Basma wadda takejinsa har magudanar jinin ta don kusan kullum yana wajenta se xesha mama tukun sannan take maidashi wajen Meenan... Se bayan sati biyu cif sannan Basma takoma England cike da kewar baby Sultan,Aunty yaruwaiya itace ke xaune da Meenan har se Meenan tacika kwanaki arbain sannan xata koma Sosai take yi mata duk wata kulawa da ya kamata abawa mai jego ga gyara na musanman da ake mata ciki harda gyaren jiki kamar wata sabuwar amarya daka rabeta xakaji kaima ka kamu da kamshin.. Yareemah Aliyu Hydar kuwa hak’uri kawai yakeyi domin yana azabtuwa rashin kusantar Meenah daya rabeta xe rage xafi aunty yaruwaiya xata fitittikeshi dolensa ya fice yana gunguni shiya fara jin haushintama Allah Allah yake kwanakin su kare ta tattara tatafi tabarsu,don takaici ma London yatafi wajen Modu nan yai weekend d’insa ranar litinin da safe suna having breakfast Aliyu se tsaki yakeja ba kakkautawa takaici ya ishi Modu kamar ya tashi yarufeshi da duka a kafule ya dubeshi yana harararsa, “Kaga pls niba tsaka ba ne,ka cikawa mutane kunne da tsakinka na gaira babu dalilii”Mtcew shima yaja tsakin cikeda takaici, “Guy aunty yaruwaiya is getting on my nerves ta hanani na..”sekuma yai shiru yana girgixa kai kawai Tuntsirewa da daria Modu yai hardasu rik’e ciki yana magana yana cigaba da dariar, “Tayimun dede tunda kaidin mutumin banxa ne” Cikeda takaici Aliyu yai murmushin gefan baki, “How I wished Meenah bata wani jinin bik’i kai kaga yanda takara kyau kuwa sam bana controlling kaina idan Ina tare da ita,Ita kuma annoying aunty yaruwaiya nan dede da minti d’aya bata barinmu idanunta k’yar akaina wallahi ko kunya bataji haba ni banmasan meyasa akace itace xata xauna da mu ba wallahi,duk ga tsofaffi nan amma arasa wanda xa’a bari se ita”cewar Aliyu Hydar cikeda takaici, Daga kafada Modu yai alamar ko ajikinsa dinnan hade da daukar cup din tea d’insa yashiga sipping hankalinsa kwance seda yashanye tea d’insa tsaf sannan yadubi Aliyu Hydar dake faman karkada kafafunsa kaida kaganshi kasan yana cikin damuwa, “Allah sarki aunty yaruwaiya guy baruwan aunty aciki wallahi believe you me tsabar nacin abun kasa aranka kawai,banda kai da abunka ma ai gata ake maka m sure gyaren da ake mata don kai akeyi mutumina karuwar kace kuma ma ai ba ita kadaice matar kaba akwai uwargidah Basma kuma tana garin nan..” Shiru Aliyu Hydar yai kawai batare da yabashi amsa ba jin shirun yayi yawa ne yasanya Modu mikewa tsaye yana kallon agogonsa sekuma ya saki murmushi cikeda tsokana yadan bugi gefan inda Aliyu yake xaune, “Toh Guy barinje gidah wajen Aisha mu gwangwaji amarci later on naje wajen my layla itama mu kashe arna abinde se sam barka kawai mutumi na” Tsaki Aliyu Hydar ya saki sannan ya mike yai tafiyar sa don sosai Modun ya kular dashi nan yabar Modu tsaye yana kwasar daria yasan ko banxa ya kular dashi.... Seda aunty yaruwaiya tai kwanaki hamsin cif sannan takoma Bornu,ranar Aliyu don dadi har zuba ruwa yai akan marbles yasha,a daren nan Meenah ta gane kuranta don bai mata adadi ba se gaf da subhi ya kyaleta shima baby sultan ne yaceci mamansa da kukan yunwar abashi mama, Watan baby sultan uku su Aliyu suka dawo Bornu banda Basma da bata kammala hada masters d’inta ba Meenah an sake xama y’ar gayu ga iya kwalliya da kissa,satinsu uku suna xaga dangi ciki hardasu ziyarar Hajja gajiram da aka maida ita gombole gidan iyayenta donsu kula da ita,yakolo kuwa ba gani ga kuma paralysis amma Alhamdulillah takan godewa rabbi ahalin da take don tana samun kulawa dede gwargwado wajen mijin nata dakuma su Ammi don sam basa kyamatarta kome yi mata suke tunda batashi take yiba, A daddafe Aliyu ya k’arasa yin wata d’aya a Bornu daganan suka tattara suka koma Abuja unguwar wuse 2 ademola adetokunbo kusada Rock view hotel dan datsetsan duplex ginin macce d’aya nanne gidan da Meenan xata xauna while wani gidan benan a unguwar maitama ganges street nanne ya ajiye amatsayin na Basma wadda xata tare idan ta kammala masters d’inta tadawo, Satinsu d’aya agarin Aliyu yaiwa Meenah da Affy registration na Baze university domin shehu Bulama ne ya bukaci hakan kancewar duk wani Online school dasu Meenan xasu yi shirmene gwara suyi makaranta sosai Petrochemical engineering shine course din da Affy xatai Ita kuma Meenah tasamu Medicine,successfully suke karatunsu babu wata matsala, <><><><> “Ya Aliyu ka kyaleni pls”cewar Meenah dake turo masa baki gaba Xaune suke akan kujera mecin mutum biyu Rabin jikin Meenan a kan Aliyu yake se yamutsa ta yake son ransa yana wani lumshe ido cikin wata irin murya yace, “Pls kibari na kara kinga gobe xan tafi Bornu” Bata ce masa komai ba tade saki jikinta kawai nan yagane ta amince aikwa awajen komai ya kwana kukan sultan ne yasanya aliyu kyaleta tabashi mama sannan suka tsarkaka jikinsu ya jasu sallah uku nayi ya saukesu itada Affy a sch wadda tadawo gidan itama saboda school daki d’aya Aliyun ya gyare mata take xaune aciki, <><><><><> Months later, Sosai garin bornu suke alfahari da mulkin sarki Uthman Ngari,mutum ne shi me gaskiya da son gaskiya baya wasa da duk wani hakkin wanda yake k'ark'ashin shi hakan ya k'ara kwantar da hankalin maimurabus. Sarki Uthman Ngari yana zaune a cikin fada ya gama solving wani case na mata da miji aka aiko mai cewar uwar gida na asibiti, duk da cewar zuciyar shi na son zuwa wajan nata sai dai yak'i tashi saboda kunya yana daga zaunan ya dinga yi mata addu'a da fatan Allah ya sauketa lafiya aikuwa ko mintuna 30 ba'ayi ba aka sake zuwa aka ce mishi ta haihu ta samu baby boy itama a nan ne ya tashi aka rakashi zuwa asibitin dan gano lafiyar su. Anyi murna sosai musamman Ammi tayi farin cikin ganin tsatson Ngari dan basu rab'a zaton zai tashi ba bare har yayi aure tayi murna har ta kasa boyewa sai da mutane suka gano, anyi suna yaro yaci sunan Muhammad cewar sarki Ngari albarkacin mai sunan yana kuma fatan yayiwa addinin musulunci hidima,su Meenah ana exam sai pic's ta gani tana tajin haushi akayi taro lafiya aka gama lafiya. Bayan suna da wata d'aya aka yi bikin Falmata kasan cewar ta samu wani mijin hamshak'in d'an kasuwa ne yace yaji ya gani zaiyi shahada zai aureta sai dai matan shi biyu itace ta uku,haka ta hakura domin tana masifar son yin auran. Su Meenah tamkar bata ajiye Sultan ba aikuwa Aliyu hydar yaji haushin raye-rayen da tayi dan haka yace bikin Aysah tana exam za'a sa ta dinga mai magiya yace haka ya tsara, cikin ikon Allah kuma itama Basmah Allah ya azurtata da nata rabon wata biyu kenan aka dinga murna tare da fatan Allah ya sauketa Lafiya. Lokacin Billy da waziri kuma yareemah babagana duk wanda ya gansu bazai ce sunyi zaman doya da manja ba dan soyayya suke zubawa tamkar zasu cinye junansu, ga yaransu tabarakallah son kowa kin wanda ya rasa babagana baya kallon ko wace mace da gashi idan ba matar shi ba hak'ik'a billy ta ciro tuta har yanzu ba'a dena karb'ar mata hakkinta ba a gurinshi domin soyayyar da Allah ya d'ora mishi ta isheshi dan Billy na wanashi sosai. *BONUS CHAPTER* (for my dearest one..Asmy b Aliyu I love you so much) Tsaye Aliyu da Meenah suke a kitchen agaban gas cooker tana nuna masa yadda xe talge tuwo gaba d’aya yayi dumu dumu da kayan sa duk ruwon tuwon ya faffallatsal masa a dakakken yadin jikinsa se gumi yake,daria Meenah tashiga yi tana nuna tuwon y’ar harararta yai, “Meya faru Ajlaal?!” “Kobah kai bane ya Aliyu kalla fa tuwon yayi ruwa se andaure da gari” “What?!”yafadi hakan yana duban tuwon Kashe gas cookern yayi hade da rungumo waist d’inta cikin kunnenta yashiga yi mata “Kyale shirmen tuwon nan pls zo kiji wata magana maman baby” “Ina xanzo gani a kusa dakai..” “Noh a d’aki kinji baby..” “Nah naki wayon” “You don’t understand I love you I love you more than life itself more than anything on this world I think bout you all the time you have turned me into a sex addic...” Be k’arasaba Meenah ta hade bakinsa da nata,shi kansa yayi mamaki yadda tashiga sarrafashi sedata gaji sannan ta kyaleshi akwai dama abinda yakeso kenan ya dauketa be ajiyeta ko’ina ba se kan gado,seda yasamu nutsuwa sannan ya kyaleta suka shiga maida numfashi, Cikin shafa kwantaccen gemunsa Meenah tace dashi, “Ya Aliyu dan Allah karka rabu dani I love you so much...” Sssh yai saurin katseta yana shafa bayanta, “Naci ALWASHIN komai runtsi Meenah baxan taba rabuwa dakeba domin kedin ZABIN IYAYE na ce ina SON ki har cikin RAI na...” “Ya Aliyu ka kuwa san ka iya TATTALIN MACE?!wallahi ko a novels albarka I so much love you yayanah” Dan hararta yai, “Ta Ina naxama yayanki ne pls?!dan Allah kidena cemun wani ya Aliyu kinji baby” “Allah kai yayah na ne..” “Nine yayan naki muna kan gado d’aya muna shagalinmu kikirani da yayanki?!nide kawai atemaka acanxamun suna pls” “To shikenan seka xab’a cikin wanda xanyi listing;Mon Amour,mon Cherie,babe,sweetat,hayatee,habeebee,life partner,soul mate,honey boo boo,hero,angel,roseberry and finally miftahul qalb..” “Miftahul qalb..saboda na kulle soyayyar duk wani tahaliki daga zuciyar ki naxama ke kinxama ni..” “Zan rayu dakai miftahul qalb zan mutu dakai abadan da ni da kai xamu xauna..” “I love your eyes Ajlaal..”yafadi hakan yana kissing kan idonta sannan yacigaba da magana in a romantic way, “I love the way you laugh,I love your smile I love your lips”yace hakan hannunsa na yawo kan jajayen labbanta, Murmushi Meenah tai da alama tana jin dadin sakon dayake aikamata ahankali ya xura bakinsa cikin nata yashiga bata deep and passionate sumba me ratsa jiki sun dau lokaci ahaka kafin ya xare bakinsa cikin nata, “I love that you are not afraid to eat in front of me i love your glooming skin,i love your hair Meenah,gashinki shine abu na biyu danake matukar so a jikin ki,i love you so much Meenah ina sonki Ina sonki nayi dana sanin rashin fada maki da wuri tun a yola i regret not telling you sooner..” “You are going to make me cry”cewar Meenah cikin muryar kuka,gaba d’aya maganganun Aliyu se yawo suke mata akai,kafin kace mene ta fashe da kuka,ta rasa wani irin masifar so Aliyun nata yake mata.. Girgixa kai Aliyu yashiga yi yasake janyota jikinsa yasa harshen sa yashiga share mata hawayen, “No please don’t cry..” Door bell na gidan sukaji yana kara da sauri Meenah tashiga lalubar rigarta tana k’ok’arin sawa,Aliyu ya fusge rigar yana sake nanukar ta,cikin dan daga murya Meenah tace, “Miftahul qalb su Affy ne da sultan pls ka kyaleni na tafi kaji..” “No not until kince kina sona..”yace hakan yana langabar dakai.. Gwalale idanuwa Meenah tai tana duban Aliyu,shafa saman kirjinta yai yana dan murmushin gefan baki.. “Meye abun kunya Ajlaal?kalle mu akan gado necked,touching and kissing ai abun kunya ya kare tunda har muka aje sultan..”yace hakan yana kashe mata ido d’aya.. Cikin rufe idanuwa tace, “ I love you my ALI JAN XAKI,ALIKO HYDAR MAZAN FAMA GADANGA K’USAR YAK’I” “I love you most Ajlaal,what a STUNNING LOVE STORY..Allah yabarmu tare har k’arshen rayuwar mu..” Da wannan suka rufe xancen da sumba me ratsa jiki harta kaiga sun shiga babban aiki.. Sum sum ni nana Hafsatu naja legidiz Benz dina na rufo masu k’ofar dakin domin na fara shiga hurumin da banawa ba.. TAMMAT BI HAMDULILLAH. ...... _Love is patient love is kind it does not envy it does not boast its not proud it does not dishonor others,it is not self seeking,it is not easily angered it keeps no record of wrongs,Love does not delight in evil but rejoice with the truth,it always protects,always trusts,always hopes,always perseveres#MEENALIYU2018_ _Anan ni Nana Hafsatu nakawo k’arashen littafina me suna a sama😊kunsan shid’an Adam ajizine tara yake be cika goma ba duk wanda nabatawa rai farawar littafinnan zuwa k’arshensa ina neman yafiyarsa,ina fatan dan fadakarwar dake ciki Allah yasa mu amfana da ita,kurakuren ciki rabbi yayafemun.._ _First of all I wanted to thank each and everyone of you reading this,thank you for reading my story,thanks for the calls,messages and comments I wholeheartedly appreciate it..kusani har kullum kuna ran Nana Hafsaatu,da baxakar ku nake rawa my fans..Fatana Allah yabar mu tare.MISS XOXO na yinku beyond words😊Rabbi yabar zumunci.._ .. _Wannan littafi kacokan naki ne sadaukarwa ne agareki my cutest ZARAH BUKHAR,Rabbi yabar mu tare har abadan da’iman Allah yasaukeki lapia yakawo mana healthy babyn mu me yawan albarka..I love you lots😍❤_ ... _To my mentor my hero the very best sis I gat😍❤my sweetest sis UMMI AISHA I’ love and adore you beyond words,more and more grease to your elbow,you’ve been with me since the very beginning and you are still with me till the end without you i will be fish food😊And I know you that I know you know it😅I love you so much sistoo me😍❤May you be forever blessed Allah yasa ki gama service dnki a sa’a our very own otondo😊💃🏿_ ... _To my YA HAJJA CE my hero my biggest supporter Wannan littafi TUKWICI NE agareki I just want to thank you from my cheesy romantic heart for supporting SON RAI KO ZABIN IYAYE for recommending it to others most importantly for believing in me😊and supporting me to finish this story,badan ke ba wallahi I would not have beeen able to keep writing like this,Thank you so much kedin tadabance a xuciyata,Allah yaraya mana ihsan yabarku tareda uncle😊👌🏾_ .... _Tawan tawan,My BILLYN ABDUL mi fren mi love mi best❤Wannan littafi TUKWICI ne kema agareki😊a har kullum alkalami baxe iya rubuta dimbin godia ta agare ki ba kalmomi sunyi kadan wurin kwararo kalaman matsayin ki awajena,Rabbi yabar mu tare matar abdul,Allah ya Kara dankon soyayya tsakaninki da Abdul😊Ina sonki Kina raina akoda yaushe.._ ..... _SPECIAL THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DAUGHTERS;BITTI FEEDHOM AND DOTA BILLY S FARI😊I LOVE YOU SO MUCH AND I ADMIRE ALL THAT YOU EMBODY,MAY GOD CONTINUE TO BLESS YOU GUYS..YOU AREE ALWAYS IN MY ❤_ .... _MATAR NASIR BABAR AFFAN KAWAR MISS HAFSY..AND MY BELOVED MISS HAFSY LIKE A JEWEL TRUE LOVE IS RARE TO FIND BECUX M LUCKY TO HAVE YOU GUYS..ALLAH YABAR MU TARE.._ ... _TAWAN,MY LOVELY MRS NGARI USMAN SHEHU BULAMA MY ASMY KEDIN TADABANCE AWAJENA NO ONE WILL EVER TAKE YOUR PLACE I LOVE YOU🧡🧡_ .... _MY SEC MOMMA FEEDOH AND MY SADEEYA KHALEEL ME ZOBO DA MY ANKATUWA I LOVE YOU SO MUCH IF I COULD DESCRIBE LOVE IN ONE WORD I WILL CALL IT YOU GUYS 😊🧡🧡_ ... _MY MOM SHAKUR AND DEAREST SEEMBY LUFF AND MY NUCEEY LOVE😍🧡THANKS FOR SUPPORTING ME THROUGHOUT,I LOVE YOU SO MUCH😘💙_ .... _AUNTY MAIJIDDAH MUSA,GAISUWAR BAN GIRMA GAREKI AUNTYN TWINS😍❤OUR VERY OWN MAMMA💙YADDA KIKE BAMU SHAWARWARI AKAN LITTATTAFAN MU ALLAH YABAKI LADAN YASAKA MAKI DA MAFIFICIN ALKHAIRINSA ILYSM💙_ .... _AND TO MY CO WRITERS ONLINE AND PUBLISHED WRITERS ALLAH YA KARA MAKU BASIRA DA KWARIN IDO,YADDA KUKE FADAKARWA A YANAR GIZO ALLAH YASAKA MAKU DA MAFIFICIN ALKHAIRINSA😊_ ..... _INA KUKE YAN HOME OF NOVELS DA XOXOS PALACE KAI DAMA DUK GRPS DIN DANAKE CIKI TO KU MATSO KUSA,NI NANA HAFSATU BANDA BAKIN GODIAA GAREKU FATANA YADDA KUKE BIBIYAR LITATTAFAI NA ALLAH YABIYA MAKU WISHES DNKU😊_ .... _INA YAN WORDPRESS?!THANK YOU SO MUCH FOR THE COMMENTS LOVE AND CARE❤I LOVE YOU GUYS BEYOND YOUR WILDEST EXPECTATIONS🧡🧡_ .... AND LAST BUT NOT THE LEAST YAN KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSO. HOME OF EXPERTS AND PERFECT WRITERS..RABBI YABAR MU TARE DA BAXAR KU NAKE RAWA; _PHERTY,UMMI AISHA,KHALEESAT HYDAR,YA HAJJA,MAMAN KHADEEJA,BILLY GALADANCI,SAFIYA HUGUMA,NUCEEY LOVE,AFRA BHAI,NANA DISO,AYUSHER,ASMY B ALIYU,AISHA DAN SABO,FEEDHOM,FAXY FASHION..SANNUNKU HASKAKKUN MARUBUTA👌🏾👌🏾MORE GREASE TO UR ELBOWS😊❤_ ........ ALHAMDULILLAH...SEKUN JINI A SABON LITTAFI NA ME ZUWA NAN GABA😊...TAKU NANA HAFSATU MOMMODU HADEE MISS XOXO😍👌🏾... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏾_* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da

Chapter 34 of 35