in anjima xan dawo”
“Aliyu ai yanzu zamu wuce kowa yatafi semu har ‘yan yola ‘daxu da safe sukabi jirgi suka tafi yaruwaiya ma bata jima da tafiya ba”
“To shikenan bari nabari ku gama”
“Affy kuje wajen auntyn taku ku mata sallama kafin kusake xuwa”cewar Ammi
“Meenah tashi muje wajen aunty Basma”cewar Aysaa
“Ni babu inda xanje kuje ku dawo inanan”Meenah tabata amsa had’e da yatsina fuskarta,
“Baa Hydar kaji wai baxata ba”inji Aysaa
“‘Kuje kawai”
cewar sarki Aliyu Hydar don shikam yagaji da magana,fita sukai suka ‘kyaleta itakuma Ammi tahau sama ‘karasa ha’da kayansu parlorn yaxama daga shi se ita,
Ganin daga shi se ita yasa Meenah hanxarin tashi xata gudu ya mik’e da sauri ya damk’o hannunta yadawo da ita kujerar dayake ganin tanata wutsil wutsil zata tashi yasa ya d’orata akan cinyarsa yana binta da kallo,
“Innalillahi wa’inna ilahirr raji’un”Meenah tace hakan tana gwalalo manyan idanuwanta had’e dasa tafukan hannayenta duka biyun ta toshe bakinta dasu jinta a cinyar k’ato,
Daria taso tabashi yagimtse ta had’e da had’e ransa cikin cunkushewar murya yace,
“Wakike cunowa baki d’azu uhm?!”
“Dan Allah ka saukeni katotuwa dani,beside babu kyau dan Allah ka kyaleni nifa ba ‘yar is...”
Bata k’arasa ba sarki Aliyu Hydar yasa bakinsa cikin nata yahanata k’arasa maganar deep and passionate sumba me ratsa jiki yashiga yi mata gaba d’aya jikinta ya mutu se hawaye da take,
Meya tuno oho ya tureta gefe dukkansu suka shiga maida numfashi Allah yaso ba wanda yagansu haka jiki sanyaye Meenah ta mik’e tahau sama da gudu bata ko k’ara had’a ido dashi ba ganin yadda take had’a stairs harda hardewa yasashi murmushi ahankli yakwantar da kansa a kujera had’e da kamo lips d’insa na k’asa yana tsosa......
Su Affy basu jimaba suka dawo lokacin Ammin tagama had’a masu kayansu har ankai mota kasancewar tun dare sukai sallama da mai martaba mai murabus,
Kan Meenah a ‘k’asa har suka shiga mota tak’i tahada ido da sarki Aliyu Hydar shiko abin daria yake bashi ashe akwai abinda yake kashe bakin Meenah troublemaker,har suka ja mota sarki Aliyu baibar parking lodge d’inba harseda aka rufe tangamemen gate ‘din palace d’in...
<><><><><>
“Yayya yakike ganin za’ai yanzu kenan?”Cewar hajja yakolo.
“Yadda boka na sambisa yace haka xa’ai”
“To shikenan”
“Shehu(mahaifin mai martaba Aliyu Hydar)baya sona baya k’auna ta idan ba tsantsar k’iyayya ba Meyasa xa’aiwa Aliyu sarauta ga mata biyu alokaci d’aya inba gata da soyayya ba”
“Kibari kawai yayya nikaina kwana nai banyi bacci jiya ba na sak’a na ware na sak’a na ware ai hajjagana tagama wankewa tabashi yasha shysa”
“Aikwa zanyi maganinta da danginta rankatakaf setasan dani take had’aka kaf gombole ba wanda besan gidan ubana ba mahaifiyata harta koma ga Allah ubanmu be isa yatsallaka Kara ba fyace tabashi order,
Nixata nunawa asiri Allah natuba mune cikakkun maiduguri wallahi sena salwantar da rayuwar ahalinta kaf kuma shi shehun wallahi baxe gaji jika daga b’angarentaba ballantana wata rana ya mulki bornu wallahi baxe yiwu ba”
“Hakane wallahi Ina goyan bayanki yayya”
“Kibari kawai bade hajjaganar takoma gidantaba xamu fara gudanar da aiki daga yau ammafa kisani tatacciyar k’auna yace mu nunawa Basman”
“Ai ni nafara tuni yayya don jiyama da figigiyar yaruwaiyar nan tarakota wajena bakiga sakin fuskar danai mata ba kuma d’axu ma naturasu rukymamah wajenta”
“Yawwa dakyau hakan xamuyi tayi harmu samu mushiga jikinta sosai mugama da shegiyar kafin a kawo d’ayar jemammiyar nikome yagani ajikinta oho jiki duk k’ashi ba fata kodayake munafukinnan yace shiya had’asu”
“Wallahi fa wai ahaka itace yar dama daman ita dayarma bata gabansa ko yaushe xata tare oho”
“Kema kinsan seta tsumata da kayan tsibbu tukun”
Cewar hajja gajiram fuskarnan tata amurtuke kamar tsohuwar zakanya idanuwanta micimici sun sake shigewa ciki jazir dasu kaida kagani kasan tana cikin ha’ulain rayuwa,
Hakade sukaita aibata hajjagana da ‘yayanta har sarki mai murabus basu cireba suka shiga zaginsu suna kwashe masu albarka suka k’ark’are xancen da yadda xasu dinga janyo Basman ajikinsu suna cusa mata miyagun halaye da tsibbance tsibbance harse su samu su cinma burukansu.....!
#SRKZI?!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 48:31 PM: Nana_Hafsaat👑: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE*
💖?👨👨👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
_*Home of expert and perfect writers_*
DEVOTED TO:
*XARAH BUKHAR*
nanahafsat.wordpress.com
*55*
Wik’i wik’i tai da idanuwa cikin sauri tace,
“Canai right away”
Tana k’arasa fad’a tasakko daga kan kujerar tai gurfane tanabin dishes d’in da kallo da wanne xata farane,
Kisre tad’akko k’wara biyar tasaka akan plate tad’akko wani na miya taxuba miyan k’ubewan aciki,gefe d’aya kuma soup na kayan cikine akan soup plate se snacks da zob’on ginger da yaji kayan k’amshi gefe d’aya kuma flask ne kakkaura cikeda kunun gyad’a,
Duk abinda yake a warmers seda ta zuba masa shide kallon yanda take faman tula masa abinci kawai yakeyi da narkakkun sleepy eyes d’insa,
“Gashi”tafad’a tana cuno baki.
Maida kallonsa yai kan wayarsa yacigabada latsawa yana murmushi ganin yayi banxa da ita yasanyata tashi tad’an dawo nesa dashi kad’an ta d’ora plate d’in akan cinyarta se k’unk’uni take k’asa k’asa,
“Haa bud’e bakin”tace tana kai masa lomar kisre bakinsa.
Ba musu yad’age cute lips d’insa had’e da dan bud’e bakinsa kad’an,cikeda takaici tashiga danna masa lomar bakinsa rik’e hannunta yai yana d’an gutsira ahankali saboda shi azahirin gaskia bayaiwa abinci cin sauri ahankali yakeci loma bayan loma,
Kisre biyu kawai yaci yai mata alama da ya isheshi nuni yai mata da flask d’in kunu taxuba masa tamik’a hannu tana mik’a masa ya had’e da hannun nata yana sipping harya shanye..
Dukta takura matuk’a sotake kawai taji yace tatashi tatafi kamar yasan k’unk’unin datake sake gyara xaman k’asaitansa yai yana duba jaridar yerwa daily trust dake hannunsa ganin kamar yama manta da ita yasanyata yin magana had’e da cuno baki gaba,
“Yaya Aliyu...”
“Uhm”yace yana sake flipping page na jarida,
“Natafi?!..”
“Cinye wannan kisren da kika bari”
“Kai yaya Aliyu,kobah kaibane ka bari?!”
“Don’t let me repeat my self”
“Ya Aliyu aradun...”
Shiru tai sanin yahanata irin rantsuwar,d’an murmushin yak’e tayi,
“Ya aliyu wallahi ban iyacin kisre ba tun agidah”
Banxa ya mata yacigaba da karanta jaridar sa takalli miyar kub’ewan da kallo d’aya xakai mata kagane akwai yaji aciki,gashi batason yaji ko kad’an idanuwanta sunyi rau rau xasu kawo hawaye daria taso tabashi ya gimtse,
Gutsiren kisren tai tad’an cakuli miya kad’an ahankali tace,
“Ya Aliyu”
“Yass,uncultured!”
“Shikenan”
Tak’arashe maganar had’e da kai lomar kisren bakinta bashiri tafuto dashi tana shushin yaji kafin tai wani abu mai martaba Aliyu Hydar yahad’e bakunansu waje d’aya seda yatabbata yatsotse yajin tass sannan yasaketa yakoma inda yake yana wani had’e fuska don yasan halinta yanxu seta tafi wajen Ammi aikwa be gama xancen zucinba tafice tana kuka hawaye kwance shab’e shab’e akan fuskarta,saurin bin bayanta yai kafin ta k’ulla masa wani sharrin wajen Ammi...
Tana fita ta k’ara sakin wani kukan me sauti don Ammi taji aikwa tajin cikin kid’emiwa Ammin ta mik’e ta rungumota tana rarrashinta,
“Menene Bitti me akai miki eh??”
Jan majina Meenah tai had’e dasa hannu tagoge ambaliyar hawayen dake sharara daga idanuwanta tabbas yau xata fad’awa Ammi cewar yaya Aliyu Hydar d’an iskane me tsotse bakinta sekace alawa,ta bud’e baki kenan xata fara xayyanewa Ammi bayani sarki Aliyu Hydar yashiga parlorn cuno baki gaba tai xatai magana cikin sauri yarigata,
“Ammi...wai ashe.. batacin kisre..”yak’arashe maganar yana sunkuyar dakai had’e dasa hannu yana sosa k’eya.
D’auke kanta Ammi tai daga kallonsa don sarai tagano rashin gaskiya a idanun sarki aliyu hydar girgiza kai meenah tai tana cuno baki,
“Kobah shiba ne yasa...”
Bata k’arasa ba sarki Aliyu Hydar yasake karb’e xancen,
“Ammi tabbas nayi kuskure bansan batacin kisre ba nai forcing d’inta m sorry”yafad’a cikin sauri,
Sake girgiza kai Meenah tai alamar xancen bahaka yakeba,
“Ammi wallahi ba...”
“Shikenan Bitti koma meye Kiyi hak’uri kinji”tak’arashe maganr tanadan bubbuga mata baya alamar ban hak’uri.
Kamar iska fuuu haka Meenah tahau sama da sauri tana sharb’ar wani sabon kukan,girgiza kai kawai Ammi tai musanman yadda taga reactions d’in sarki Aliyu Hydar tasan tabbas ba haka xancen yakeba amma komade meyai mata matarsa ce baxata shiga huruminsu ba,bagarar da xancen tai tahanyar d’akko wani xancen harde Aliyun yasaki jiki sukaita hirarsu da Ammin...
Kodah Meenah takoma sama haka tadinga rusgar kuka kamar wadda aka aikowa da sak’on mutuwa tanayi tana tsayawa tanaci gaba Aysah dake d’akin tana kallo a system tasaki tsaki musanman yadda kukan Meenan ke hanata jin muryar film d’in datake kallo,
A kafule tace,
“Wai meye hakane eh?! Haba tun d’axu kike kuka natambayeki natambayeki kinyi shunning d’ina kinga inhar baxaki dena kukannanba wlhy sena sauk’a k’asa nahad’aki da Ammi ko baa Hydar”
Rage sautin kukanta tai tashiga rerawa ahankali cikin muryar kuka tace,
“Aysah,kobah yaya Aliyu bane ashe d’an iskane...”
Shiru tai tacigaba da kukanta.
Ware idanuwa Aysah tai tana jaddada kalmar da aka danganta d’an uwan nata da ita cikeda muryar mamaki tace,
“Meyayi kike kiransa da wannan sunan haka!!”
“Kinga..,ko bashi bane kullum kullum inyazo seya dinga tsotsan bakina kamar sweet kuma yauma bakiga yadda yamunba kawai dan...”,
Cikeda takaici da mamaki bata k’arasaba Aysah takatseta,
“Ssshhh,Haba Aunt Meenah haba karma kifada awani wajen sesu maki dariya”
Tashi Aysan tai tadawo kusada Meenah tadafata cikin muryar lallami tace,
“Duk abinda yamaki shine auratayyar ba haramunne aunt meenah..”
Katseta Meenah tai tana wurga mata kallon mamaki,
“Bakisan cewa idan kana bari namiji natab’a maka hannu ko jikiba ciki kake ka haihu?!”tafad’a da iyakar gaskiyarta.
Y’ar dariya Aysah tai tana girgiza kai,had’e da jajanta yarinta irinta Meenah,
“Konima sanda ina k’arama Ammi tafad’amun haka aunt Meenah,trust me duk zancene iyaye ke fad’a saboda mudinga kaffa kaffa da wanda xamuyi mu’amala awaje wanda ba muharrim d’in muba”
Jaddada kai Meenah tai badon ta yadda ba,
“Latsi”tafurta a gatsile.
“Tohm shikenan yanxu Aunt Meenah tun yaushe baa Hydar yafara maki haka?!”
“Yadad’e tun sanda sukaxo shida ya Modu yake faman tab’ani yana kamamun gashina yawwa namanta ban fad’a maki ba mugu ne kuma..”tak’arashe xancen had’e da jan majina.
Y’ar dariya Aysa tasakeyi,
“Aunt Meenah to da’ace hakanne da yanxu aikinyi cikin kin haihu ko?!”
Banxa Meenah tai mata tana cuno mata baki gaba,tab’e baki Aysah tai takoma tacigaba da kallonta,canta mik’e tasauka k’asa gurin su Ammi suka shiga hira da yan uwanta banda meenah da Ammi tayi tayi tasakko tak’i har sarki Aliyu Hydar yagama xamansa yatafi Meenah bata k’ara sakkowaba...
*England*
“Aboki kasamu yarinyar nan kawai kagayamata abinda yasa kake shunning d’inta amma wani rashin d’aukar wayarta duk bashi bane”
Ma’aruf yace hakan yana duban Modu dake sakin tsaki lokaci xuwa lokaci.
“Ko?!”cewar Modu kansa a sama.
“Allah aboki wannan shine best solution,call her kasamu waje peaceful kagayamata abinda yasa kake ignoring d’inta”
“Huh”cewar Modu
“Trust me wannan shine”
“Toh i will try”cewar Modu...
*
*Peter Mart and Bites*
Zaune Modu yake yana dialing wayarsa sanye yake cikin suite coffee datai mugun amsan k’irarsa.
Lokaci lokaci yakan kalli kewayan Mart d’in ko xe hangota ganin babu alamarta yasanyashi mik’ewa yana gyara collar rigarsa cikin sauri tak’araso sanye cikin fitted riga da wando da suka d’ameta d’am suna bayyana surar jikinta.
Siririn tsaki Modu yasaki yana istigfari a zuciyarsa yarasa Layla wacce irin yarinyace me kunnen k’ashi sam batasan meye kunya ba.
“Oud”
Tafad’a tana k’ok’arin rungumarsa saurin ja baya yayi yana girgiza mata hannu alamar karta soma.
“Layla..”yafad’a atak’aice bayan yaja kujera yaxauna
“Longest time oud,I love and miss you thou de kanata ignoring calls d’ina dunno why?!”
D’an Murmushi yai yana shafa kwantaccen sajensa yajima kafin yad’ago ya dubeta tayi rau da idanuwa sosai yahango tulin soyayyar sa a idanuwanta,
“M sorry dear”yafad’a a tak’aice,
Menu yad’an duba yana flipping pages d’in,
“Mexa kici??”
“Duk abinda xakaci oud”
Kad’a kansa yai sannan yai ticking coffee nd buttercream sandwich ya mik’awa waiter d’in ya karb’a yatafi yakawo masu.
Tura mata wani d’an k’aramin plate yai gabanta d’auke da sweets guda biyu d’aya a bud’e d’aya anannad’e cikin ledarta.
“D’auki kisha”
Yafad’a yana tsare ta da ido,
Cikin sauri layla takad’a kai had’e da saurin mik’a hannu tad’au alawar wacce ke cikin ledarta ba bud’addiyar ba,d’an murmushi yai ahankali yace,
“Meyasa kikai choosing wannan??”
“Oud itace a killace ai wannan kwa bamusan tunyaushe take abud’e ba kalli fa duk wasu abubuwa acukwikwiye ajikinta”tak’arashe maganar tana masa nuni da bud’addiyar alawar cikeda k’yama...
“To ita kuma wannan da kika bari waxe sha uhm?!”
“Bawanda xesha oud,kokai baxan bari kasha ba saboda bamusan meyasa take a bud’eba iska da virus duk sungama hawa jikinta gwarade wannan da ba bud’addan ba”
“Ko?”yace da ita yana sake dubanta jin yadda tadage tana kwararo masa jawabi bil haqqi da gaskia.
“Allah oud”
Jinjina kai yayi had’e da sauke nannauyar ajiyar zuciya cikeda nutsuwa yace,
“Kinsan meyasa nake avoiding d’inki layla?!”
Cikeda tashin hankali layla tagirgixa kanta alamar a’a.
“Layla kinga yadda kika d’auki sweet d’innan dake cikin leda saboda yafi killatuwa?!”
“E oud”tabashi amsa cikin tashin hankali.
“Good”yace ahankali sannan yacigaba,
“Sak haka rayuwarki take layla,nayi maki hakane saboda na gwada hankalinki layla,don’t you knw duk abinda akafi killaceshi yafi value a rayuwa,
Meyasa kikasan har darajar alawar dake cikin ledar ta tafi wadda ke bud’e inganci?! Layla kaman yadda kika xab’i alawar cikin leda kikabar bud’addiyar haka duk wani me hankali xe xab’i budurwar dake killace jikinta a matsayinta na ya mace ya aura,
Kinga yadda bud’addiyar alawar nan take a bud’e bawanda xesha harse ansayata a leda an killace baxan boye makiba layla idan badena wannan shigar kikaiba wallahi kinji namaki rantsuwar musulmi babu wani d’an kirkin daxe aureki layla,unless kincanxa halin ki,kinada structures mekyau meyasa baxaki killace jikin kiba harse kinyi aure,tell me meyasa kike exposing jikinki Layla?!”
Shiru layla tai sam tanemi bakin magana tarasa,
“Uhm layla tell me why?!”
Kuka tasaki ahankali me tsuma zuciya,
“Layla....Kiyi tunani layla,kefa hausa Fulani ce y’ar manyan mutane me halin dattako,kina biyewa turawa kina bud’e jikinki,duk wani runs shirmene layla,yanxu Ina Basma uhm?! Kiyi tunani layla kicanxa halin ki pls kidena duk wani shirme kidawo ki rungumi tarbiyya r da aka ginaki akanta agidanku,
Wanda m hundred percent sure kaf gidanku bawanda yasan kina rashin ji a sch,beside idan Allah yad’au ranki ahaka baki repenting ba mexa kije kice masa uhm”
Shiru layla tai se jan kukanta take tana rerashi ahankali,kallon agogansa Modu yai tareda sakin siririn tsaki lokacin dayai xasu had’u da ma’aruf harya soma gotawa mik’ewa yai yana gyara button d’in hannun rigar sa cikin muryar lallashi yace,
“Kidena kuka pls,kije kiyi tunani akai shawara nake baki saboda ni nad’aukeki amatsayin k’anwata ta jini sam banason yadda kike exposing jikinki a titi abun yana hurting d’ina layla and Kiyi hak’uri idan abunda nace yayi hurting d’inki m so sorry, nd nixan wuce yanzu saboda akwai inda xamuje nida aboki na yanzu,lokacin da mukai dashi harya gota ma”
Itade ko d’ago kanta bataiba kanta a k’asa tana kuka had’e da sharb’ar majina,jinjina kai kawai yai had’e da d’aga kafad’unsa sama yai gaba abinsa yafita daga Mart d’in yabar layla kai sunkuye ajikin tebur tana rera kuka me tsuma zuciyar duk wanda ya saurara zuciyarta cunkushe da kalaman Modu,sake sakin wani kukan tai mai sauti wanda harseda mutanen dake wajen suka juya suna kallonta itakuwa kukan datake yanxun bewuce kalaman Modu na k’arshe ba wanda tabbas tasan itada Modu kilan har abadah baxasu sake had’uwaba bare xancen soyayyar su,kukanta tacigaba da ja fuskarta kwance shab’e shab’e da hawaye me cikeda kaico na irin *kaxamar rayuwar* data sanya kanta aciki...
_*Acigaba da hak’uri da y’ar mutan yerwa abubuwa ne sukai min yawa musanman yanxu danake shirin komawa makaranta,#ina miko gaisuwa ta mai d’imbin fatan alkhairai agareku_*
_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_
24/01/2018, 10:25:42 PM: Nana_Hafsaat👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 14:01 PM: Nana_Hafsaat👑: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE*
💖?👨👨👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
_*Home of expert and perfect writers_*
DEVOTED TO:
*XARAH BUKHAR*
nanahafsat.wordpress.com
*54*
*K*ishingid'e ta sameta tare da kuyanginta, da kyar Basma ta k'arasa wajanta wanda hajja yakolo na ganinta tayi saurin mik'ewa tana bawa kuyangin nata umarnin fita,kallon Basma tayi cikin tsananin mamaki ganin yadda ta shigo rik'e da ciki kuma a sunkuye.
“Bitty lafiyarki kuwa, ya naga kin shigo a duk'e?!”
Wani irin nishi Basma keyi tana matse cikinta tare da kamo hannun hajja yakolo ta matse a cikin nata, ita kam yakolo tayi kololowa wajan shiga tashin hankali da damuwa, bata son wani abun ya faru a ce a d'akinta ne dan haka cikin lallami ta kamo Basma jikinta suka mik'e tana fad'in,
“Sannu Basma taso muje gurin yayya Allah yasa dai ba wani abun bane ke damunki.”
Da kyar suka k'arasa apartment d'in hajja gajiram,zaunar da Basma hajja yakolo tayi a kan kujerun dake zagaye a cikin parlorn sannan ita kuma ta shiga cikin d'ayan parlon wanda hajja gajiram ke hutawa a cikin shi.Jiki na rawa ta k'arasa wajanta itama tana ganin ta shiga tayi saurin gyara zama tana kallonta ganin yanayin ta yasa tajin cewar akwai magana.
Sai da hajja gajiram ta sallami kowa na cikin parlon sannan ta maida hankalinta gurin hajja yakolo,
“Lafiya dai ko na ganki a hargitse?”
“Yayya ba kalau ba yanzu ma tare muke da wannan yarinyar Basma ban san make damunta ba amma gata nan munzu tare da ita tana parlon k'asa..”
Yatsina fuska tayi domin ita a yanzu tafi kowa shiga cikin tashin hankali saboda babagana ya uzzara mata ya hanata kwanciyar hankali akan wata billy kullum billy billy, da kyar ta mik'e suka fita a kwance suka tarar da Basma k'asan carpet har ta fara kuka tana ta murd'e-murd'an ciki.
Wajanta suka matsa hajja yakolo ta d'agota amma Basma ta koma k'asa cikin lallami yakolo tace,
“Bitty d'ago ki mana bayani ai ba kuka zaki zauna kina yi mana ba tunda mu bamu san abinda ke damunki ba...”
Yarfa hannuwa tayi tare da nunawa hajja yakolo setin mararta,murmushi hajja gajiram tayi domin ta gano inda matsalar take dan haka cikin takaici tayi magana,
“Idan banda abinki Basma ai banan zaki tahoba ina shi Aliyu hydar d'in,shine kawai zai iya magance miki wannan matsalar taki kinji ko?!”
Kuma rushewa tayi da kuka kamar zata mutu haka take ji, babagana ne ya shigo nan da nan ya fara jan tsaki har ya k'arasa inda suke.bin Basma yayi da kallo lokacin ta d'ago kanta nan suka had'a idanuwa,kuma jan wani tsakin yayi dan shima ya gano matsalarta kasan cewar duk yasan sign d'in da duk wace mace zata yi toh sai ya ganota, mtww ya kuma jan wani dogon tsakin dan yasan da ace billy bata durfafi zuciyar shi ba da sai ya cinma manufar Basma sai dai kashh! A yanzu billy ce burinshi ita kawai yake kallo yaji dad'i harma ya samu nutsuwar zuciya dan haka yanzu kawai ya juya yana kallon hajja gajiram tare da buga mata harara tamkar ba mahaifiyar saba yace,
“Mami nagaji har na sanar da baba ta waya nace ina sonta,amma ita bata sona so yace zaisa abinciko idan yadawo in yaso sai ya had'a mu nida wancan yaron (Modu)...”
Kallon mamaki tayi mai cikin razana tace,
“Har abinda ya faru tsakaninka da bilkisu ka sanar mai yareemah?”
“Nop Mami sai yayi min gardama tukunna zan sanar dashi.”
Duk binshi sukayi da kallo,juyawa yayi yabar gidan yana wata irin 'yar iskar tafiya tamkar d'an kaciya,maida kallon su sukayi wajan Basma da ta saki baki tana kallon babagana har tama manta da cewar ga abinda takeji,
“Kinji sauki ko Basma?ai duk wanda yake some-somen mutuwa idan yaga babagana toh sai ya wartsake kema da alama kin denajin abinda kikeji.”
Hajja gajiram tayi maganar tana bin Basma da kallo dan tasan tantirancin yareemah babagana ne silar kawar da feeling d'in da Basma keji,sai a lokacin taji kunya tare da kallon hajja yakolo tace;
“Wallahi Umma wani tsumin ne da na baki labarin za'a aiko min dashi daga kano, toh shine na karamai zuma da peak milk yayi d'an d'umi nasha ya kusan haukata ni”
Yanzun ma bawai denaji tayi ba kawai ya d'an ragune dan taga shed'ancin yareemah babagana babbane wai mahaifinshi yake cewa sai yayi mai gardama sannan zai sanar dashi wani abun.
Sun d'an jima a gurin suna nuna mata hanyoyin da zatabi wajan mallak'e Maimartaba Aliyu hydar sai dai duk babu wata shawara mai tsabta amma haka Basma ta hau tazauna ba tare da tayi tunaniba apartment d'inta ta koma tana ci gaba da aiwatar da aikin dasu hajja gajiram suka bata a cikin bedroom d'in Aliyu hydar.
Maimartaba Aliyu hydar kuwa yana fada anata k'arb'ar korafe-korafen mutane hankalinshi a kwance babu abinda yake damunshi, matsalar shi d'aya yanzu tun ranar da suka yi maganar Kiara be sake ganin Modu ba yau kimanin sati biyu kenan shi kanshi yasan yana K'aunar Modu kamar yadda yake k'aunarshi shima.
*England*
Modu kuwa tunda yaga Maimartaba maimurabus ya matsamai akan zancen aure cewa yayi abashi one month lokacin ya dai-daita da wadda yake so zai gaya musu, ana bashi dama ya koma London gurin Kiara dan ba k'aramin so yake mata ba.Kwanan shi uku acan ko kiran Aliyu hydar ya gani baya d'agawa domin yayi *ALWASHIN* bazai yi mai magana ba har sai ya samu yaddar Kiara cewar zata yadda ta musulinta suyi aure sannan ne zai kula Maimartaba Aliyu hydar har suyi magana.
Lancashire West Yorkshire Mart;
Yauma kamar kullum tun sanda Modu ya dira ak'asar yake faman shawo kan Kiara amma tace mai ita bazata musulunta ba amma zata aure shi tunda tana sonshi,ganin ta kafe akan k'in bin ra'ayin shi yasa ya aminta da cewar zai aureta a haka. Kiara murna kamar zata kasheta domin itama tana sonshi sai dai yafi sonta gashi tana tsoran danginta saboda idan ta musulunta kasheta zasu yi shi ne dalilin da yasa tayiwa Modu gardama.
“Baby sai yaushe?!”
Ya fad'a cikin harshen turanci yana kallon Kiara,hannunshi ta kamo cikin nata tana murzawa a hankali yayin da sukewa juna kallon kurullah kowanne fuska cike da annuri, hannu takai saman fuskar shi ta shafo kwantaccen quarter million d'in dake jiki tace,
“Sai za'ayi biki zanje na gayama family na sannan sai ayi biki irin namu.”
Da sauri Modu ya kalleta girgiza kai yayi tare da Kara matse yatsunta cikin nashi yana cewa,
“No baby irin namu za'ayi kema zakiji dad'in shi.”
Duk maganar suna yinta me cikin harshen turanci batare da damuwa ba Kiara ta yadda domin ita dama ba wani damuwa tayi da sai anyi wani shagali ba, nan suka ci gaba da zancen yadda zasu gabatarwa da iyayan su tare da yin alkawarin babu wanda zai bar wani duk wuya duk tsanani musamman Kiara tafi nanatawa Modu dan tasan a gurinshi ne za'a samu matsala.
<>
Kasan cewar weekend ne hakan yasa Maimartaba sarki Aliyu hydar ya shirya dan zuwa gida gurin Ammi,shiryawa yayi cikin shigar sarakai tagani ta fad'a,rawaninshi aka shigo mai nad'i yayi mai sannan ya fito, da kallo Basma ta bishi dan kullum kara kyau yake yi sai faman murmushi take mai ya karasa a hanhali kusa da ita tare da kafeta da idanunshi dasuke a waje, cikin silent voice d'inshi yace mata;
“Wai meye sirrin ne kike ta wannan hawan kamar ana sanya miki yeast eh?!”
Baki ta turo mai tana bin ilahirin jikinta da kallo,ita kanta tasan tayi kiba sosai har tana neman takura mata tayi saurin kamo hanmuwan shi tare da cewar,
“My sugar boo ni kaina haka na ganni kuma ni bana son k’iba gashi sugar boo ko b'atan wata bantab'a yi ba bare ace ciki ne...”
Maimartaba Aliyu hydar ya zame hannunshi a hankali daga cikin nata sannan ya shafi fuskarta, tana bashi tausayi sosai gashi tana son ta haihu kullum sai ta fad'a mai kamar shine wanda yake badawa amma sai dai yace mata tayi hakuri sannan taci gaba da yin addu'a Allah maji rok'on bayinsa ne,bayi take sosai ba dan datayi sallar zata shafa hannu a fuska ta mik'e tabi lafiyar gado kota wuce apartment d'in su hajja yakoko.
Janye hannun yayi tare da cewa,
“Zanje gida gurin Ammi idan na dawo zan zauna a cikin fada so sai zuwa night insha Allah,kiyi min addu'a kinji?!”
Kai ta d'aga mai sannan suka jera har wajan kofar parlor Basma ta rakashi sai da fadawanshi suka rufamai baya sannan itama ta juya tare da komawa cikin bedroom.
Motoci hud'u aka yi ta maimartaba Aliyu hydar itace a tsakiya sannan mafi kyau da tsada a cikin su, damboa road suka nufa suna zuwa aka wangale musu get shiga suka yi aka yi parking tare da shimfid'a wani dogwan carpet jah tun daga wajan murfin kofar Aliyu hydar har zuwa wajan kofar shiga cikin parlon Ammi na k'asa a tsakiyar an rubuta emir hydar da farin rubutu.
Wani bafadene ya bud'e mai kofar motar yayin da sauran suka k'arasa sukayiwa kofar rumfa kafar shi ya fara zirowa guda d'aya wadda ke sanye cikin cover shoe ash color sannan ya fito da d'aya kafin ya fito da jikinshi baki d'aya, sandar shi aka bashi ya rik'e lokacin ne kuma fadawan suka bud'a mai hanya wannan abun duk anayi ne akan idanun Meenah wadda ke hangensu ta windown daga cikin d'akin su na upstairs,
Baki bud'e take binsu da kallo har suka shige, Aysah ce ta k'arasa inda take tare da sa hannu ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 35