bala’in kamshi akan bakinsa cikin kunnenta yafara mata magana,
“Wane irin perfume kikasa Uhm?!”yace hakan yana sunsunar wuyanta hannunsa d’aya yana yawo dashi cikin ilahirin jikinta..
Gaba d’aya yafara neman birkita mata lissafi don sarki Aliyu Hydar bade iya tarairayar mace ba don salon yadda yake romancing d’insa yafita daban..
“Kinji??....”yafadi kinjin cikin wata iriyar murya datasa Meenah kasa handling kanta
Dakyar tabashi amsa tana k’ok’arin cire hannunsa daga cikin rigarta,
“Khumra ne..”
Sarki Aliyu be samu bakin yin wata maganar ba saboda gaba d’aya Meenan ta rikitashi da fitinannan kamshin turarukhan jikinta..
Sosai yashiga romancing d’inta babu inda baya kissing ajikinta hakama hannunwansa ko’ina yawo yake dasu cikin jikinta lokaci d’aya ya lalubo tattausan labbanta yashiga yi mata deep and passionate French kiss daya saka Meenah kuka gaba d’aya takasa gane kan Aliyun don sosai yake romancing d’inta ciki harda cire mata dankwali yana shafa kitson kanta..
Jin kukan nata yayi yawa yasashi sakinta ya xame jikinsa daga nata yamike yana gyara jallabiyar jikinsa idanuwansa sun kad’a sunyi jajir dasu bebari sun had’a ido ba ya fice da sauri yabar Meenah dake tsiyayar hawaye tana maida rigarta jikinta da duk ya cukurkuda mata ita kwasa tai aguje tai sama tashiga dakinta ta murza key band’aki tafad’a ta sakarwa kanta shower tana wankan tsarki tana hawaye gaba d’aya daren jiya da safiyar yau Aliyu yak’i sarara mata sam batasan fitinar tasa ta xarce kima ba se yanxun da ta tare agidan sa...
<><><>
Da misalin k’arfe uku na rana hajja yakolo ta shrya tsaf cikin laffarya pusher pink taje ta nemi izini wajen mai martaba mai murabus kan xataje gidan kanwarta hajja fatee ta dubota batada lapia mai martaba ya barta itada kanwarta dake aure a unguwar basu da nisa suka fita a motarta kamar gaske..
Gaban hajja yakolo se dukan uku uku yake ta ina xata fara ne?! Sannu a hankali har suka k’arasa gidan hajjagana dake Damboa road..
“Nashiga uku ni batulu”cewar hajja yakolo dake duban gidan na hajjagana
Kanwarta dake driving din ta kalleta kafin tace,
“Kaka batulu ni Ina ganin kawai mu juya ki hak’ura da abun nan dan gaskia its very risky kuma kamata yai ace ita gajiram din itace xatai komi ai ba dole seda ke ba”ta k’arashe xancen tana sakin tsaki..
Harararta yakolo tai tana k’ok’arin dedeta nutsuwarta lokacin da sukai parking a dede k’ofar gate d’in..
“Ina ruwan ki?!”
“A’a babu kam wallahi ina jiranki Allah yabada sa’a sekin fito..”
Yakolo bata tanka mata ba tai ficewarta daga motar tana duban security guards din dake baje a gate d’in,hadixa k’anwar yakolo dake mota ta kece da daria ganin yadda yakolon ke harharde tafiyarta tana bin gefe cikeda tsoro,daria ta sake kecewa da ita kafin tace,
“Allah ya kyauta ya rabani da taya aikin kishiya ki xauna kina bautawa kishiya sekace wadda hankalinta ya gushe”ta k’arasa maganar hade da sakin wani bahagon tsaki cikeda takaici ta kara tsare yakolo da ido tanad’an jiyo maganganun da suke da gatemen din..
“Hajiya Ina xuwa daga Ina kuma?!”cewar wani security dake nufar yakolon ganin tana tunkarar gate xata shiga
Hannunsa yakolo ta kalla zungureriyar bindiga ce Ak 47 a hannunsa yana pointing d’inta da ita yawu yakolo ta hadiye murya na rawa tace,
“Uhm uhm abinnan wannan me gidan ce ta turo ni”
“To Hajia me gidan ai bata nan in fact ba kowa ma a gidannan”
Dedeta muryarta yakolo tai,
“Eh ai na sani biki akeyi acan shehuri shine tace nazo nan wajen yareemah Ngari na duba mata jikinsa kafin tadawo gobe”
Shiru security din yai yana duban yakolo daga sama har k’asa kallo d’aya xakai mata kasan agidan masu hannu da shuni take sam batai kama da masu bara ballantana maula ba,jin yayi shiru yasanya yakolo sake cewar,
“Idan kuma baka yadda ba shikenan bari nakoma na sanar da yayyan..”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace,
“‘No it’s okay kije amma kada ki dad’e plss”
Gyada kai tai sannan ta wuce ciki da sauri tana shiga dama garin maganin yana hannunta tafara barbadashi har cikin gidan ja tai ta tsaya rasa hanyar sashen Ngari tai don bata sani ba gashi karta koma securities din su ganota wata baiwa tagani tafito daga wani b’angare hannunta dauke da foodflask na abinci da sauri ta nupeta tana murmushi,
“Sannu Bitti(‘yata)
“Yawwa mama Nda dubdo?!”
“Dubdo silewa..Yareemah Ngari na ciki kuwa?!”
“Eh yana ciki shida dr dinsa ne ma yanzu yagama cin abinci”
“Okay bari yagama yayya ce ta aiko ni”
Jin an ambaci hajjagana yasanya baiwar fad’ad’a murmushinta,
“Allah sarki mama ki shigo ciki ki xauna to”
“Toh nagode bitti”cewar yakolo
“Idan dr din yagama xan sanar dake mama”
“Toh”
Wani matsikaicin parlor ta kaita bayan ta cika gabanta da kayan marmari lokaci xuwa lokaci yakolo ke duba agogan hannunta ganin biyar saura kwata yasanya ta sakin tsaki..
Wayar tace tafara kukan agaji ganin sunan hadixa akan screen din yasanya ta saurin d’auka ta sa a kunnenta,
“Na’am hadixa..Kintafi kuma?!bangane ba,okay xaki dawo...To bansani ba de wai yana tare da likitan sa dukde yadda ake ciki xakiji bayan nagama..Uhm I will call you,toh sekin dawo”
Tsaki ta saki bayan ta ajiye wayar kallon agogo tai dake daure a tsakiyar hannunta ganin yadda lokacin yake ta tafiya yaushe har xata samu tai abinda xatai..
*SHEHURI*
*Z*aune mai martaba mai murabus yake gabansa cike da abinci yama rasa wanda xeci gajiram ta turo k’ofar parlorn tashigo tasha kwalliya Kai kace xaben wanda yafi kowa kwalliya xata...
“Ranka yadad’e..”cewar gajiram cikin sigar jan hankali
Kallonta shehu Bulama yai yana sake runtse idanuwansa na kode mafarki yake ne,
“Ba mafarki kake ba ranka yadad’e..Nice dai gajiram dinka mahaifiyar babagana”
Y’ar daria shehu Bulama yai yana dubanta
Matsawa tai kusa dashi ta karbi serving spoon din hannunshi tashiga serving mashi abincin a plate..
“Haa bud’e bakin”ta fad’i hakan tana kai masa lomar bakinsa
“Bis...”Be k’arasa gajiram tai hanxarin cusa masa abincin
Ganin xe sake wata basmalar bayan ya hadiye abincin yasanya gajiram sake danna masa wata lomar hade dasa hannunta tana shafa y’ar furfurar dake sajensa,tuni ta sha’afar dashi daga neman tsari hartaci galaba akansa ta faki ido ta tsiyaya garin maganin acikin black tea dinsa ta kai masa bakinsa nanma bata bari yayi bismillah ba harya shanye
Seda ta tabbatar ta gama komi ta b’angaren sa sannan tatashi tafita bayan sun dan taba hira sashen ta takoma tana shirya yadda xata binne layar anjima batare da an gano taba..
Tana xaune a parlor tana kar kad’a kafafuwa falmata y’arta tashigo idanuwanta kwance shab’e shab’e da hawaye tashi tsaye gajiram tai hannuwanta dafe akan kirjinta,
“Falmata..”
“Mami”cewar falmata dake goge hawayen dake tsiyaya a face d’inta
“Zo nan falmata kigayamun meke faruwa fada kukai da wata?tun jia bakya gidan nan falmata ina ki kaje?!sanar dani damuwar ki”
Fadawa falmata tai jikin gajiram tana kuka sedatai me isarta sannan tai shiru tana sauke zuciya,shafa kanta gajiram tashiga yi,
“Ko xan san meke faruwa falmata??”
“‘Mami...”sekuma tai shiru,
“Na’am falmata”
“Mami promise me baxaki fadawa baaba komi nadaga abinda xance dake ba”
“Nayi alk’awari falmata”
Cikin kuka falmata tace,
“Mami ci...Ciki ne dani”
Neman jintaa da ganinta gajiram tai ta rasa na yan wasu dakikai kafin ta kwaso ashar ta dire akan falmata,cikin huci ta hankadeta gefe tana karkade jikinta kamar taga abun kyama cikin xaro idanuwa hade da tashin hankali bayan ta waske ta da mari har biyu tace,
“Fad’amun ba se anjima ba uban waye nace dan gidan uban waye ya miki ciki??da har xaki bud’e baki ki cemun ciki ne da ke wallahi anyi haihuwar asara nayi dana sanin haihuwar ki bankad’addiya y’ar iska kawai”
Shiru falmata tai tana share hawayen fuskarta cikeda takaici gajiram ta sake sharara mata mari,
“Xaki gayamun dan gidan uban waye ya maki cikin ko sena hallaka ki yanxun?!”
“Mami...Mami Amadi ne fa”
Sam Mami ta ma mance da wani me suna Amadi a duniya don kidimewa cikin kifkiftta idanuwa tace,
“Wanene Amadi sanar dani shin d’an gidan uban wanene a yerwa?!”
Cikin ja baya da karkarwar jiki falmata tace,
“Mami Amadi de..Amadi..Amadi dogaren baa babs(babagana)”
Me yakwan gajiram tai salati ashar ta lalaiyo ta sake durawa falmata cikin takaici da masifa tace,
“Anmake barikin naki be kaiki ko’ina ba se mutuncin ki daya ragu don uban ki ki samo cikin dan masu farcen susa mana wanda dole ne xa’ace ya aure ki asirin ki a rufe shine xaki je don tsinantaka da shegiyar jaraba irin taki ki kwaso cikin Amadi,Amadi fa Amadi kaxamun dogarin babagana da ba kullum yake wanka ba bare wanki yaron da kullum cikin samamun wari yake aamma don tsabar kwashewar albarka shine xaki kwaso cikin sa banxa gantalalliya Amadin da ba’asan asalinsa ba”Ta k’arashe xancen hade da sakin tsakin takaici
“Mami..”cewar falmata dake riko kafafun gajiram tana kuka
“Mami ki temakeni kikai ni asibiti Mami mutuwa Xanyi”
Tsaki Mami ta saki,kafin ta janye kafafunta daga hannuwan falmata dake rik’e dasu,
“Koma menene ke kika janyo wa kanki dan uban ki lokacin da mahaifiinku yace kowa yaxabi makaranta yakaishi bacakikai bakya so ba ke anan xaki da kika fara anan din kika dena,kika saka yawo agaba dayake kunnen kashi ne dake ai ga irin tanan abinda ya biyo baya,
“Kuma a hakan kike so na kwashe ki na kaiki asibiti xancen cikin yafito kowa yasani?!tukun nama ina shi Amadin?!”
Cikin kuka falmataa tace,
“Mami yace shi ba cikin sa bane wai sharri nai masa”
Wayar Mami ce tafara kara lokacin anfara kiraye kirayen sallar magrib ganin yakolo ce yasa tai hanxarin dauka ta kara a kunne,
“Hello..Yakolo,na’am!kai haba har yanzu?!kassh to se yaushe kenan?!okay can anjima kenan?to shikenan tawan sekin dawo,nima nagama dayan saura na anjima,to sekin dawo wani mummunan alkaba’in yasake faruwa kede bari abinda babagana yai shi akaiwa falmata ita harda rabon shege aciki wallahi..Kede bari sekin dawo kawai abun ba’a cewa komai”
Katse wayar tai ta mike bayan ta makawa falmata harara sannan ta wuce sama fuu kamar xata tashi
sake fashewa da kuka gimbiya falmata tai tanayi tana surutai ita kad’ai kamar xaucacciya...
<><><>
Da k’yar jakadiya Mangu ta mike tana d’an d’ingisa k’afa don yau kam taci alwashin ko gunduwa gunduwa su gajiram xasuyi da namanta hakan baxe hanata fayyacewa hajjagana kullun kutingwilar da sukai mata abaya ba kai haryanxun ma da bata tare da su tareda neman yafiyarta na abubuwan da aka had’a baki aka k’ulla da ita..
Sandarta ta dago tafara dogarawa da ita sannu a hankali harta k’arasa sashen na hajjagana dake cikin shehurin tana xuwa tayi neman iso aka bata izini tana shiga ta tarar da hajjagana da kuma aunty yaruwaiya a parlor se murmushi suke da alama tad’in da suke ya masu dad’i...
Mangu na karasawa ta xube a kasan carpet din dake baje a harabar parlorn cikin hawaye face face a fuskarta hajjagana da yaruwaiya suka dubi juna kana suka maida dubansu kanta cikeda isa yaruwaiya tace,
“Salon makircin ku da asirinku be bar muba shine kika biyo ta har sashenta shin da wanne kikaxo!! Narantse miki da Allah idan da bokayen maiduguri kikaxo dasu akanki nan wajen yau sekin sauke su yanzu”
Xata k’ara magana Ammi tadaga mata hannu alamar tai shiru cikeda dattako da kima irinta mutanen kirki Ammi tace,
“Shin da me kikazo Mangu?!”
Share hawayen fuskarta Mangu tai don sosai yanxun tayi nadama nadaga abubuwan data aikata don kusan kullum cikin mafarkai take marassa dadi wanda idan ka auna suna nuni ne da abubuwan da ta aikata a baya marassa kyau cikin kuka tace,
“Na cancanci ko wane irin mummunan hukunci da xa’a yankemun hakika ni Mangu bada wani abun naxo ba fyace tarin dimbin laipuka dana aikata wanda naxo na fayyace su na kuma roki gafara idan da halin afuwa..”
Tsaki aunty yaruwaiya tai ji take kamar ta tashi ta rufe jemammiyar shegiyar da duka gashi Ammi ta hanata magana wannan shine adakeka ahana ka kuka...
Cikin k’asa da kai hawaye na kwarara Mangu ta soma magana....
*Kankiya LG*
Dak’yar mahaifiyar layla ta mike bayan ta idar da sallah tana bubbuga kwankwasonta saboda azabar ciwon dayake mata,Shafa addu’ar tai sannan ta nannade dankwalinta ta daura shi akanta ta rame ta xuge ta lalace ainun kamar ba ita ba y’ar dattijuwa mai farcen susa,kallo d’aya xakai mata kasan tayi nadama kwarai matuka don sam yanxun sallah bata wuce ta hakama karatun qur’ani kullum cikin yinsa take ga yawan Kai kukanta ga mai sama daya yafe mata dimbin laipikan data aikata saboda shi din mabuwayine gagara misali..
Farfajiyar gidan ta fita tsit ba kowa yau tun asubah bataji duriyar kartin banxan ba jinjina kai tayi har xata koma cikin gidan sekuma tai saurin xura takalmanta ta fita tana d’an had’awa da gudu megadin dake tsare gidan ne ya tsaida ta yana kallonta,
“Ina xuwa hajiya?!”
“Baba mai gadi kaimun rai ka ji kaina katemakeni ka kyaleni na tafi dan Allah yadda katemakeni na kubuta kaima Allah ya temakeka kaji?!dan Allah ka tausayamun baba”
Shiru yai yana de kallonta amma bece komai ba ganin beyi magana ba yasata sake kwararo masa roko duk dan ya kyaleta ta kubuta,
“Dan Allah baba kaji?!”
“Hajia idan na kyaleki kika kubuta mexance da iyayen gidan nawa??”
Shiru haj. Salamatu tai sanin batada tacewa don gaskia ya fad’a har ta hak’ura xata koma ciki yakirata,
“Zo hajia”
Be rufe baki ba ta dawo jikinta se bari yake,
“A wane gari kike?!”
“Baba ni yar kano ce amma inada iyali a katsina a kauyen kurfi”
“Kurfi?!”ya maimata sunan..
“E kurfi baba..”
“Allah mai iko nima dan kurfin ne..Kuma Ina tunanin yanxun na biki kawai mu kubuta tare saboda idan kika barni anan suka dawo suka ga na kyaleki kin kubuta tofa ba makawa sunan baba me gadi murugayi domin kashe ni xasuyi”
“To baba muje mana ko?!”cewar haj salamatu dake kallon kudu da arewa kar wani yataho..
Kad’a kai kawai baba mai gadi yai hade da nade kasan wandonsa ya kwasa aguje a baya haj salamatu ta bishi hade da tattare kasan jemammen xaninta itama tana tafiya a tattale kamar y’ar kaciya don ta wahala ahannun barayin ba kadan ba don kowannensu ya kwaso sha’awarsa akanta yake gyagije ta harse yasamu nutsuwa....
Basu suka dena sharara gudu ba har seda sukaje babban titi suka samu mota suka haye da kwandasta (conductor)keta kwala kiran,
“Kurfi kurfi na kurfi su haye mu cale...”
_*Nima xoxo nace to ina katsinawan dikko?!d’akin kara kunya gareku bade tsoro ba...Na gaisheku katsinawa ina kuke?!To Nana Hafsatu na mik’o gaisuwarta musanman yan kankiya local government_
_Ina kuke yan kurfi?!to ga munan muda su haj.Salamatu da baba mai gadi..._
#Assalamu Alaykum
Beautiful people acigaba da hak’uri da Miss xo abubuwa ne sukai yawa wanda dole typing din yaxamto ba kullum nakeyi ba se an d’an d’auki lokaci,Ayi hak’uri de munkusa k’arasa shi Insha Allah
#Nagode kwarai Allah yabar zumunci...💕😻😍❤
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼_*
[4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```Edited by```:
```Ya hajja ce```
```nanahafsat.wordpress.com```
*74*
*S*ake gurfane Mangu tai cikeda nutsuwa tafara magana kanta a k’asa,
“Hak'ik'a rankishi dad'e manzon Allah (SAW)yayi gaskiya da yace mai hakuri yana tare da nasara hakurinki yayiwa wad'anda basu dashi mugun ciwo ne domin har kullum dai kece a saman su duk kuwa ta inda aka bullo miki.Nikam naga ishara koda na sanar miki yanzu nasan an cuceki a baya sai dai nasan ked'in mai afuwace dan Allah rankishi dad'e ki gafarce ni,wallahi duk wani tuggun da ake shirya miki tun daga kanki har zuwa 'ya'yanki rashin lafiyar yareemah Ngari wallahi duk sihiri ne wanda ni suke aikawa wajan k'arb'o musu shi.”
Jakadiya Mangu ta rushe musu da kuka Ammi ta bita da kallo cikin tsananin mamaki,cikin masifa aunty yaruwaiya tace,
“Suk'e turaki ki k'arb'o su suwa ye?!”
Hawaye basu bar zubowa daga fuskar jakadiya Mangu ba jikinta sai b'ari yake tace musu.
“Su...su...su abokan zaman nata wallahi su Kansu a had'e yake duk tare suke yin komai sai dai a baya komai sukayi boka yana basu sa'a sab'anin yanzu da duk abinda suka b’ullo miki da shi rankishi dad'e baya faruwa a kanki sai ya koma kansu musamman ma ita wadda take sawa ayin wato hajja..hajja mahaifiyar yareemah babagana,sam bata kaunar taga kin cigaba dake da 'ya'yanki da duk wani wanda ya rab'eki dan Allah rankishi dad'e kiyi min afuwa kinga nima tsautsayin daya afka min duk ta sanadiyar zuwa k'arb'o abinda za'a cutar daku ne,
“Wallahi Allah hajiya hatta rashin samun haihuwar matar maimartaba na yanzu wato maryamu da batayi ba duk makircin sune da suka dinga d'orata akai na cewar zata mallaki mijinta zai sota kamar babu wata d'iya mace a duniya ita kuma da yake yarinya ce sai ta yadda har suka illatata amma wallahi rankishi dad'e itama ba laifinta bane duk makircin sune akwai abubuwa da dama rankishi dad'e wanda ake ta shirya muku wani ma bakina bazai iya fad'ar shiba sai dai nace kiyi hakuri ki gafarta min gashi ban karu dasu da komai ba sai asarar sashen jikina da nayi.”
Jikin aunty yaruwaiya har kyarma yake yi saboda tsabar kid'ima bakinta sai motsi yake da alama rashin mutunci take son yiwa jakadiya amma idon Ammi ya hanata dan tasan da ta fara zata katseta, duk gurin babu wanda be shiga cikin tashin hankali ba dajin wannan bayani na jakadiya sab'anin Ammi da take ta sakin murmushi wanda duk cikinsu babu wanda ya gane kona meye.kallon jakadiya Mungu Ammi tayi cikin jin dad'i da nuna kamar babu abinda taji tace mata.
“Toh sai muyiwa Allah godiya daya sa kika gane cewar abinda kuka aikata ba dai-dai bane Alhamdulillahi kuma na yafe miki jakadiya duniya da lahira har dasu d'inma duk na yafe muku,Allah ya ganar dasu suma su gane cewar Allah shine kadiran alaman yasha,duk mulkinka duk matsayinka duk tarin dukiyarka indai har baka sa Allah a cikin lamarinka ba toh ka tab'e tun anan duniya na kuma k'ara yadda da lamarin ubangiji domin dashi na dogara yau gashi ba wani takura muku akayi ba a'a da kankin kanku kuka fallasa abinda kuka b'oye Allah ya shirye mu ya shiryi duk wani musulmi dake fad'in duniyar nan.”
“Amin Ammi.”
Cewar Aysa yayin da Yaya gumsu tayi caraf tace..
“Wallahi basu isaba kanbala'in can!yo ai dama da walakin goro a miya dama sai da nace abincika matan nan amma k'iri-k'iri aka wani ce zato zunubi toh wallahi sai sunyi zaman gidan yari,muza'a wulakanta kema munafuka ba ciwon kafa ba ko ciwon me kikeyi wallahi sai kin k'arbi hukunci tunda kece munafukar,bulalai da xaman gidan kaso shiya kaman ce ku”
“Yi shiru haka gamsu,ni aka yiwa kuma nace na yafe ba shikenan ba,a koda yaushe ana son mutum ya kasan ce mai afuwa da yafiya Allah yana son mai yawan yafiya kuma kuyi hakuri kunji ko banasan ma maganar nan ta fita daga cikin parlorn nan na gaya muku.”
“Ammi wannan ai ba maganar da za'ayiwa shiru bace, naji duk abinda kuke cewa ni kaina ina bayanki yayya gumsu.”
Cewar Modu daya dad'e tsaye a gurin bayan duk ya gamajin komai tun sanda jakadiya take magana,duk gaba d'aya suka juya suna kallon hanyar shigowa parlorn fuskar Modu a had'e zuciyar shi na zafi sai b'allawa jakadiya harara yakeyi wadda tunda ta fara magana har kawo yanzu bata d'ago ta kalli kowa dake cikin parlorn ba.
“K'araso ciki Mommodu.”
Ammi ta fad'a tana kallonshi,kusa da ita ta nuna mai ya k'arasa ya zauna sai faman uban nishi yakeyi tamkar wanda akayi danbe dashi cikin sanyin murya Ammi tace.
“Haba Mommodu!Idan rai ya baci ai bai kamata ace hankali ya gushe ba,meye ribarmu idan muka ce zamu tozarta su?kaga duk mun zama su kenan babu me hankali da tunani a cikin mu.Ina son kuyi hakuri musamman idan kuka yi duba da ganin yadda suka dinga k'ok'arin ganin sun rabamu da Maimartaba amma hakan Allah besa ya kasan ce ba, suka kuma yi k'ok'arin nakasa d'an uwanku toh shi sun samu nasara sai dai tashi kaddarar kenan kuma ya rungumeta, sannan sukayi kokari wajan hana Aliyu ya zama sarkin yanzu amma duk Allah be basu nasara ba kunga sai mu godewa Allah domin yana tare damu kuma yana amsa mana duk wasu addu'o'in mu hakan yasa nace kuma kuyi hakuri ku yafe musu.”
“Amma kuma Ammi ai...”
Ammi tayi saurin katse aunty yaruwaiya ta hanyar d'aga mata hannu sannan ta maida kallonta wajan jakadiya tace,
“Nagode jakadiya zaki iya tafiya Allah kuma ya k'ara sauk'i ya k'arb'i tubanki.”
Cikin tsananin murna jakadiya ta kuma duk'awa tayiwa Ammi godiya sannan ta mik'e tana rarrafawa da sauri Ammi ta danna wata k'ararrawa a gefenta sai ga wata baiwa ta shigo cike da ladabi tayi gaisuwa sannan Ammi tace,
“Temaka mata ki kaita har clinic.”
Baiwar ta kuma rissinawa alamar amsawa sannan ta Kama jakadiya wadda ke ta faman kuka tana godiya a haka suka fita, kamar dama jira sukeyi yayya gamsu da Modu suka fara mita kamar zasu tashi sama ita kuma aunty yaruwaiya abin da ya kona mata rai ne ya hanata cewa komai can kuma tace.
Kai gaskiya wallahi Ammi wai harda yi mata godiya, kota mecece kuma oho.”
Duk Ammi najin su tayi dariya kawai tana kallonsu cikin son bagarar da zancen Ammi tace.
“Wai Mammodu ina matan naka?!”
Sai yanzu ma ya tuna da cewar tare suke sannan ya sosa sajansa tare da furzar da iskar bakinshi yace.
“Wallahi Ammi sabida b'acin raima ni na manta tare muke dasu, sabida muna shigowa naji ana magana sai nace duk su zauna a waje.”
Ammi ta zaro ido cikin mamakin shi tace,
“Waje kuma Mommodu?!”
Yace,
“Eh wallahi Ammi,ah toh ai naga su ba huruminsu bane magana ce ta cikin gida.”
Da sauri Ammi ta mik'e tayi waje tana cewa,
“Subhanallahi surukan nawa zaka bari a waje kai kuma ka shigo ciki dan dai ku yaran nan hankalinku a kaurinku yake..”
Ta k'arasa fad'a tana mai barin cikin parlon, zaune ta tarar da su layla ta mik'ar da kafa sabida sun d'an kumbura yayin da kiara ke mammatsa mata sai hira suke suna dariya da alama basuji haushin barinsu da yayi ba Ammi tayi murmushi cike da jin dad'i sai taji inama ace matan Aliyu hydar suma zasu yi haka lallai da tafi kowa jin dad'i amma kullum tana kan yi musu addu'a Allah ya dai-daita tsakaninsu.
“Kai! kukuma sai kuka biye mishi kuka zauna anan?maxa kutashi ku shiga ciki.”
“Lahh Ammi ai ba komai wallahi idan kuka gama sai mu shigo.”
Cewar layla ita kuma kiara ta mik'e ta k'arasa wajan Ammi tare da rungumeta cikin ladabi tace,
“Good-evening mah.”
Ammi tayi murmushi tare da dafa kanta tace,
“Oya kushiga ciki sai Mu gaisa.”
Komawa kiara tayi wajan layla ta kamo hannunta suka shiga ciki Ammi sai kallonsu take cike da sha'awarsu suna gaba tana bayansu,suna shiga layla ta zauna a k'asan carpet yayin da kiara ta wuce kusa da Modu sai da ta fara kaimai peck a goshi sannan ta zauna kusa dashi ya shafa kai saboda kunyar Ammi tare da basarwa.
Zama sukayi aka ci gaba da tattauna zancen lokacin gid'ad'o ya shigo parlorn kusa da Ammi ya zauna cikin rad'a-rad'a yace.
“Ammi tunda ku bazaku koma gida ba gaskiya ni yau a kusa da baah Ngari zan kwana.”
Kallonshi tayi tana dariya kafin ta riko hannunshi tace,
“A'a ka bari ai gobe zamu koma muma haba kaida za'a bar mana kai a nan.”
“Gaskiya Ammi ni tafiya zanyi anayin sallar isha.”
Ammi tace,
“Toh autah yadda kace haka za'ayi.”
Dariya yayi sannan ya mik'e yana cewa,
“Su Meenah anji lafiyayyan bed harda fad'owa k'asa tim.!”
Aunty yaruwaiya da Yaya gamsu suka tuntsire da dariya dan sun gane su amma Ammi dasu Modu sam basu gane ba.
<<<>>>>>
Gaba d'aya hajja yakolo ta gama fita a hayyacinta domin ganin yareemah Ngari yayi mata wahala mik'ewa tayi da kudirin zuwa duk yadda zata yau sai ta ai watar da,aikin nan tunda gashi har sunyi waya da hajja gajiram ita har tayi guda d'aya amma ita ta kasa yin nata. A hankali ta fita kamar wata mai ciwon jiki ta k'arasa sashen tana zuwa security d'in ya kalleta cikin rashin saninta yace,
“From where?!”
Hajja yakolo taji wani kudum a k'irjinta ciki rawar murya tace,
“Ni..ni..'yar..'yar uwar Ammin shi ce nazo dubashi ne yanzu muka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 35