bedroom d'in wanda yasa tayi saurin jan baya tana faman dafe k'irjinta zuciyar ta tamkar zata fito dan tsananin tashin hankali tayi saurin jingina jikinta da bango saboda numfashinta neman dena aiki yake yi. Tana jiyo yarinyar na ihu tana bashi hakuri amma yak'i sakinta har dukanta tajiyo yanayi.
"Nashiga uku ni gajiram wannan wane irin bala'i ne yau take gani? Babagana ya wulakantata,yaci zarafinta tana can tana fafutukar neman mai mulki shi yana nan yana b'ata yaran mutane cikin takaici ta fad'a cikin d'akin tana tafa hannuwanta idanuwan ta sai zubar hawaye suke.
A hankali babagana ya d'ago yana kallonta bayan ya rufe jikinshi da blanket kallon yarinyar dake kwance tamkar matacciya hajja gajiram tayi taga bata da niyar suturce jikinta sai ta matsa kusa da ita da niyar d'auketa da mari nan taga idanuwanta a kafe bata ko k’iftawa hankalin hajja gajiram ya k’ara tashi ta kalli babagana dake k’ok’arin janyo pajamas d'insa zai sa tace;
“Dan ubanka ka kashe musu yarinya,sannan ka tsaya kana kallo na ‘yar gidan uban wacece ka d'akko musu eh?”
Ta tambaye shi bayan ta k'arasa ta rufe jikin yarinyar gorar ruwan eva ta hango sai a lokacin tayi tunanin shafawa yarinyar ruwa,da sauri tayi abinda zuciyarta ke gaya mata aikuwa cikin sa'a yarinyar ta farfad'o tana ta ihu tana cewa;
“Yareemah dan Allah karka b'atamin rayuwata,karka rabani da *Martabata* dan...dan...dan ahhh.”
Yarinyar ta saki wata razananniyar k’ara wadda tasa hajja gajiram juyawa da gudu zata bar d'akin taji babagana ya dakawa yarinyar tsawa hakan yasa ta tsayawa.mik'ewa yarinyar tayi tana janyo kayanta ta sanya rigar duk ta yage saboda kokawar da sukayi tana gama sanyawa tayi yunk’urin mik'ewa ta kasa sai ta kuma sakin wani kukan gashi ta kasa kallon hajja gajiram sai itace tayi k’arfin halin cewa yarinyar;
“Ke dallah rufemin baki sakarai kawai uban waye yace ki biyo shi ai da saninki kika zo ya lalataki shine dan munafinci kin ganni zaki dinga yiwa mutane kuka,tunda kika b'atamin yaro dan ba halinshi bane kema sai kinci ubanki yau d'innan sanar dani ya akai kika shigo cikin gidan nan har cikin d'akin nan?!”
Hajja gajiram tayi maganar tana kafeta da idanuwa ranta a b'ace,shi kuwa yana gama sanya takalmi da kaya beyi wani tunanin yin wanka ba yasan ya kai yabar gidan ko takan su bebiba.cikin kuka yarinyar tacewa hajja gajiram;
“Suna na Bilkisu sheriff bunu mai agogo mu y’an unguwar bulunkutu y’an nono ne ana kirana da billy ni d'aya ce 'ya mace a gurin iyayena mun samu tarbiya da ilimi both boko da Arabia wata rana na dawo daga gidan yaya na akan hanyata ta komawa gida shine naga ana bina da mota sai nayi saurin tsayawa dan naji tsoro saboda motar bata k’ananan mutane bace gashi babu mutane a layin sai mai motar yafito ya karaso inda nake tsaye jikina har rawa yake saboda ban saba tsayawa a waje ba,kallon da naga yanamin ne yasa na k'ara tsurewa na shiga cikin tashin hankali bud'ar bakin shi sai cewa yayi min;
“am in need of you baby."
Billy ta kuma sakin kuka tare da toshe bakinta tana faman girgiza kai,hajja gajiram dake tsaye jikinta sai karkarwa yake ji take tamkar ta shak'e billy dan tsananin takaici,bata k’aunar taji ana cewa babagana yayi wani abun Allah tsine sai dai ya zata yi tunda ita kanta ba tsoranta yake yiba,muryar billy ta katse mata zancen zucinta inda ta cigaba da cewa;
“Inajin ya fad'i haka na fara jada baya cikin sa'a kuwa na kwasa aguje ban tsaya ba sai a tsakiyar d'akin Maman mu,nan tayi ta faman tambaya ta akan abinda nakewa gudun ban b'oye mata komai ba tace min daga yau ko naga mota na bina na dinga guduwa karna tsaya nace mata tom.tun ranar ban sake ganinshi ba sai yau da asuba na shirya zan tafi tahafiz banji motsin shiba kawai sai ganin shi nayi rik'e da hijjab d'ina kafin nayi yinkurin guduwa ya toshe min bakina inda ban sake sanin komai ba sai a cikin d'akin nan....”
Bilkisu ta k’arasa maganar cikin kuka mai ban tausayi amma dan rashin imani irin na hajja gajiram sai taja wani uban tsaki tare da nuna billy da yatsa tana cewa;
“Ki shiga hankalinki,kisan abinda zaki dinga fad'a wannan maganar taki duk kamekame ce domin babu abinda na yadda dashi a ciki yanzu zan baki kud'i masu yawa wanda zaki yi amfani dasu ki rufe wannan shegen bakin naki idan kika kuskura kika sanar da wani cewar ga wanda yayi miki wannan abun baza ku sake kwana d'aya a cikin duniyar nan ba dake da iyayanki kina jina ko?!”
Cikin bak’in ciki da zafin zuciya billy ta d'aga kai alamar toh tana share hawayanta,da haka hajja gajiram ta mik'e tsaye tana cewa;
“Ki shiga bathroom kiyi wanka kizo ina jiranki a parlor.”
Tana kaiwa nan tabar d'akin waya ta d'auka tana neman jakadiya,tana d'agawa tayi mata bayani tare da cewa;
“Ina son yanzu kije gurin boka na sambisa kice ina son yanzu a d'auke hankalin yarinyar ta kasa fad'ar wanda yayi raping d'inta.”
Jakadiya ta rissina har k’asa kamar tana gabanta tace;
“An gama rankishi dad'e..”
Billy na fitowa kanta a k'asa hajja gajiram ta mik'e tayi gaba billy na biye da ita tana tafiya tamkar 'yar kaciya har suka shiga apartment d'in hajja gajiram,kud’in ta d'akko masu yawan gaske ta damk’awa billy dake sharar hawaye sannan ta kalle ta cikin kask’anci tace;.
“Kiyi gida karki k'ara koda mafarkin gidan nan bare kiyi tunanin shi kinajina...?!”
Tayi maganar a fusace billy ta d'aga kai tana hawaye cikin muryar kuka tace;
“Toh..!”
Da k’yar ta fito daga cikin shehurin ta samu me napep lokacin tasha bak'ar wahala saboda akwai nisa kafin ka fito daga cikin palace d'in tana shiga cikin gida komai ya tsaya mata cak ta kasa tuna waye yayi mata wannan abun haka har su abban ta da 'yan uwanta suka gane abinda ke faruwa da ita akai akai tafad'a tayi shiru duka,lallami duk tayi shiru sai kuka da take yi.......
_YOLA (JIMETA)_
*K*wance yake akan makeken gadan su baki d'aya ya takura ya k'agara yaji ance su koma gida,yana son ganin yareemah Ngari domin yanzu yana yawaita mafarkin shi cewar gashi ya warke yana magana yana iya tashi zaune ayita hira duk sanda yayi mafarkin nan ranar jinshi yake cikin nishad'i wayar shi ya janyo yana son jin muryar Basma sannan ya sanar mata cewar su biyu zai aura koya zata ji idan ya sanar mata da wannan maganar oho...;
Ringing biyu tayi Basma ta d'auka cikin so da shauk'in ganin kiran kasan cewar yanzu shima yana yawan kiranta sab'anin da sai dai ta kira shi,tana karawa ta saki ajiyar zuciya har yana jiyowa ya tambaye ta cewa;
“Ya?!”
“M fine my boo kawai inajin dad'i ne idan naga ka kirani,nasan yanzu ina da muhimmanci a cikin ranka ko?!”
Ta tambaye shi tana gyara zamanta kasan cewar tana cikin hall d'in da suka gama lecture.Shafa saman sumar shi yayi ba tare da yace mata komai ba,cikin daddad'ar muryar shi yace mata;
“Basma we need to discuss something and it’s serious please ki bani aran hankalinki nd bana son kiyi min mummunar fahimta domin komai na iya faruwa kinajina?!”
Duk da taji fad'uwar gaba hakan be hanata daurewa tace mai;
“Ok my boo inajinka,kuma zan fahimceka insha Allahu.”
“Ok kinsan anje gidanku an nemar min auranki kuma nasan kece kika nuna da saninki aka aika har yasa aka bani ba wani jayayya.so i want to you to know.... Am.. Am, Basma you know I love you ba yadda zanyi yanzu haka ku biyu zan aura keda wata cousin d'in.....”
Bata bari ya k'arasa ba cikin tashin hankali wanda besan tana dashi ba yaji tana cewa;
"And so what?!yareemah ni zaka wulak’anta? Ka yaudareni dama tun ba yanzu ba nasan baka k’aunata amma babu damuwa ni na hak’ura na bar mata kaje ka aure ta yareemah I.. I.. I.. h.."
Ta kasa k'arasawa kawai ta kashe wayar,sosai yaji tausayinta fiye da yadda yak’i tsammani toh ya zai yi gabaki d'aya sai hankalin shi ya koma ga yadda zai yi ya koma school dan yaga Basma ya nuna mata cewar ita *SAN RAN* shi ce Meenah kuma*ZAB'IN IYAYE* ce domin sune suke son had'a su.
“Oh god darn it...!”
Yareemah Aliyu hydar ya fad'a yana dukan pillow duk duniyar tayi mai zafi ya mik'e tsaye dan neman Modu ya sanar dashi cewar gobe zasu koma ya gaji da zaman yola...
Yana fita ya hangeshi shida Meenah da gid’ad’o a zaune sai b'abbaka dariya yake kai da kagani kasan labarin dariya suke bashi,kamar ya juya haka yaji amma sai ya fasa ya doshi gurin cikin takunshi na k'asaita wanda zai iya tabbatar maka da cewar lallai prince ne ba tare da an sanar dakai ba.yana zuwa suka had'a idanuwa da Modu dake rik'e da ciki saboda dariya yayi saurin d'auke kanshi cikin basarwa ya kuma damk'ar tulun gashin dake kan Meenah.
“Wayyo Allah nashiga uku aunty yafendo zai cire min gashin kaina..!”
Meenah ta fad'a tana ihu Modu ya mik'e da sauri dan k’watar ta yareemah Aliyu hydar yayi saurin d'aga mishi hannu tare da cewa;
“K’yaleni guy yarinyar nan sai na koya mata hankali kafin mubar gidan nan,ba tada kunya at-all ta rainani tamkar ta tab'a ganin hak’orana a waje”
Kuka kawai take harda su majina yareemah Aliyu hydar yace;
“Zaki kuma kallo na daga yau?!”
Meenah tayi shiru tana hawaye bata ce komai ba ya kuma jan gashin yadda zataji zafi tayi magana amma taurin kai irin na Meenah ya hana tayin magana,ganin haka ne yasa yareemah Aliyu hydar janta zuwa apartment d'insu su Bulama da gid'ad'o sai hakuri suke bashi amma kallo d'aya yayi musu suka ruga da gudu apartment d'in aunty yafendo dan su gaya mata. Modu kuwa anan ya ci gaba da zama saboda karya bisu abin ya zama rigima Allah kad'ai yasan abinda zai mata kasan cewar Meenah ta bashi labarin tsakuwar data watsa mai harda ce mai yareemah Aliyu hydar yayi kuka dan k'arya.
*s*una shiga ya tura keyarta cikin parlorn sannan ya bita da kallon babu wasa sai faman zara idanuwa take tana soshe-soshe tare da turo baki tana kus-kus dashi alamar gunguni take mai abinda yafi tsana cikin rayuwar shi dan yafison ka fito fili kayi magana koda bazaka ce komai ba.
“Kneel down Meenah kona b'allaki a gurin nan.”
Share hawaye tayi batace mai komai ba sannan tak'i yin abinda ya sanyata, k'arasawa yayi inda take tsaye tayi saurin b’oye fuskarta da hannunta da suka sha maroon d'in lalle suka yi mata kyau yayi kamar zai mareta cikin sauri tace mai;
"Wallahi da na cewa Baffa eh zan aureka amma yanzu zanje nace mishi na fasa saboda kasheni kake nemanyi,ni dama sai da nace bakai nake so ba Yaya Modu nake so amma Baffan nan yace wani kai,toh wallahi sai na fasa dan ma kasamu na amsa.”
Sakin baki yayi cikin tsananin mamaki da takaicin maganar ta yace mata;
"Shut up!Ni zaki cewa dan na samu kince zaki aure ni? Ok go ahead jeki fad'awa Baffan tunda baki da kunya fitsararriya sai na gyara miki zaman kwakwalwarki get the out stupid girl...!”
Da gudu tabar parlorn tana maijin haushin shi sai dai kafin taje apartment d'in aunty yafendo sun had'u itama ta taho,kallon su tayi kamar ba itace tagama kuka ba yanzu idanuwan fayau bako d'igwan hawaye aunty yafendo ta tambayeta;
“Meenah meya had'aki da Yaya Aliyu?!”
Ta kalli bayanta tare da maido da kallon gurin aunty yafendo tace;
“Ba shine d'azu ya kayar dani ba shine na watsa mai tsakuwar dana d'iba kawai yanzu muna hira da Yaya Modu yazo yajani ya kaini parlorn su,har da cewa wai zai gyara min zaman k'wak'walwata sai kace wata mahaukaciya.”
Tayi maganar cike da yarinta aunty yafendo ta kalleta tare da kad'a kai tana cewa;
“Ikon Allah! Kukuma irin taku salon soyayyar kenan?!”
“Nifa ba shi nake so ba Yaya Modu nake so dan ma ya samu nace wa Baffa eh na yadda zan aure shi shine yake cin zalina.”
Meenah ta fad'a tana kallon hannun gid'ad'o dake rik'e da wata 'yar ball tana tunanin yadda zata fizge ta ruga da ita. Cikin sa'a kuwa tayi wuf ta ansa tare da kwasawa a guje tamkar iska zata kayar da ita aunty yafendo ta bita da kallo tare da girgiza kai tana fad'in.
“Allah ya shirya min ku amin.”
Da haka ta wuce gurin aunty Maijidda kasancewar dama tana da niyar zuwa sai kuma akazo aka sanar mata cewar yareemah Aliyu hydar ya shak'i Meenah.....
Team#BASMAH AUR MEENAH?🤷🏾♀
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*
💖?👨👩👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(_*Home of expert and perfect writers_*)
_*Devoted to_*
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_*:
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_42/43_
Wannan shafin nakine Aneesa Abubkhar Rimi _*ANEELURV_*
nanahafsat.wordpress.com
____________
*H*aka meenah tacigaba da kukanta tanayi tana gungunin itade tafuson yaya Modu sau dubu akansa haka kuma sunfi shak’uwa tanayi tana zumb’uro baki had’e da jan majinar axabar ciwon kanta dayaja mata shi harya haddasa mata mura,
Seda yareemah Aliyu Hydar yai dariyarsa mai isarsa sannan yasha kunu kamar bashiba yafara taku cikeda k’asaita yadawo har kusa da ita sunajin numfashin juna yadda jikinta ke rawa abin yaso yabashi dariya sekuma yaci magani yana k’are mata kallo hakan yayi dede da sakkowar aunty yafendo daga sama bata lura dasuba kasancewar stairs d’in kallon dama yake sukuma k’ofar dasuke daskare a tsaye hagu take kalla kiranta tashiga yi don taduba d’akinta batanan takuma san cewar batada lapia a yadda meenah ta shirga mata k’arya,
“Meeno nah,ke meenah kina Ina ina kika shiga kikabar famfon sink se zuba yake shi kad’ai?!”
Muryar meenah narawa tace,
“Aunty ga... Gani nan kobah yaya a....”
Xata fara kwararo magana Aliyu Hydar yai hanxarin sa hannunsa ya toshe mata baki hakan yayi dede dashigowar aunty yafendo parlorn komawa gefe Aliyu yai yana soshe soshen k’eya kallo d’aya meenah tai masa sekuma tai hanzarin maida dubanta ga aunty yafendo wacce ke k’ok’arin ficewa daga parlorn da saurin ta da alamun kunyar ganin data yi masu atare,zuciyarta cikeda murnar kilan meenah da Aliyun sunfara dedeta kansu...
Jin yakuma kama gashinta da k’arfi ne yasata sakin k’aramar k’ara,k’afafunta suka d’auki rawa tanamai runtse ido don azaba,cije lips d’insa yai yakuma sake damk’ar gashinta cikeda fad’a yace,
“I repeat meyasa bakya saka d’ankwali?!”
Tuni ta soma hawayen axaba sai k’aramin tsalle takeyi amma bai saki gashinba daky’ar tadafe kanta cikin muryar kuka ta amsa,
“Ni bana sonshi ne saboda aradun Allah..”
Bata k’arasaba yasa hannu ya buge mata bakin bayan yasaki gashin,
“Idan kika sakemin rantsuwa da aradun Allah sena b’allaki sannan kibud’e kunne kiji rules d’in daxansa maki dak’ik’iya kawai,hope m clear??”
Ta bud’e idanu tana kallonsa sekuma tai saurin sadda kanta k’asa tana mai runtse idanuwanta cikeda ciwon dakanta kemata,murya a hankali tace,
“Toh”
Jinjina kai yayi had’e da fad’in,
“Okay fine”
Mik’ewa yai yaxauna akan kujera mai uku had’e da zaro wayarsa yashiga dannawa yakwashi mintina k’alilan yana danne dannensa awaya itakam idanuwanta sun kawo ruwa ta k’agara yabarta tatafi cikin zuciyarta kuwa banda,
“Arrogant,mugu,azzalumi Allah ya isarmin..”
Sukad’ai take maimaitawa harde ta tsinkayo muryarsa yana fad’in,
“Kodah wasa,kodah wasa naji ko aka gayamin kinbawa wani labarin duk abinda yafaru yanzu sena yanke miki wannan gashin naki na dodo kamar na rapunzel kina jina?!”
Da sauri takad’a kanta jikinta se rawa yake,
“Tashi ki fita dak’ik’iya kawai”
Dama abinda takeson ji kenan da sauri ta mik’e xata fita yace,
“Ke”
Tajiyo agajiye tana cuno baki,ya d’an murmusa kad’an kafin yace,
“Ko Modu kada nasake naji something related to this awurinsa if not...”sekuma yai shiru yana cijan lip d’insa na k’asa
Da sauri tafuce hartana tuntub’e gudun kada yasake kiranta jinjina kai kawai yai had’e da sa hannu yashafa curly gashinsa sekuma yamik’e shima yafice,sama yahau don gaida aunty yafendo kwata kwata yak’i sakin jikinsa ganin kunyarta yakeji yasanya itama ko ido bata had’a dashiba a kunyace suka k’arasa gaisawa sannan ya mata sallama yafice,
A balcony yahad’u da Modu yanata zambad’a sauri yana tafe yana gyara karin hularsa murmushi Aliyu Hydar yayi ganin Modu yawuce shi da sauri kamar xe tashi sama bebari sunyi magana ba bayan sungama had’a kayansu sashen Baffa Alooma suka nupa sukayi mashi sallama har parking space ya rakosu shidasu gid’ado da bulama yabisu da adduar Allah ya kiyaye yatsare yakuma saukesu gidah lapia sannan yakoma sashensa don yana ganawa da wasu manyan bak’i,
Ganin Modu bega Meenah suyi sallama bane ya aika gidad’o yakira mashi ita da gudu gid’ad’o yadawo yana haki,
“Kuka take Aminatun,tace baxata zoba”
“For real?ko wata tsokanar tasakeyi?!”cewar Modu yana dariya
“Wallahi bansan mata ba kilan itada aunty ne saboda yau bataje school ba”
“Kai Meenah se addua,to idan tadena kukan kagaysheta kace mu muntafi”
Modu yace hakan had’e da xaro kud’i yabawa gid’ad’on yace su raba shida sauran yaran,sannan sukai masu sallama suka tafi driver yajasu se airport daganan jirgi yad’aga dasu bornu state,
_*Bornu(Damboa Road)_*
Su Aliyu na k’arasawa motoci sukazo a tawaga suka d’aukesu,Aliyu yace su fara biyawa suga jikin baa Ngari tukun kafin su k’arasa shehurin.Suna xuwa suka fara shiga sashen baa Ngari su Ammin suna cikin d’akin harda k’anwarta dake binta itama taxo duba shi,
Jingine Ngarin yake da pillow akan gado sosai ya murmure ba kamar daba yayi kumari ba kad’an ba gaisheda su Ammin sukai sannan suka duba jikin Ngarin murmushi fad’ade a fuskokinsu Aliyun da Modu ganin jikin nasa sosai yayi sauk’i cikeda farin ciki Aliyu yace,
“Ammi akwai improvements ko?Alhamdulillah naga yana iya motsa k’afarsa ma”
Itama murmushin Ammin tai kafin tace,
“Eh sosai Alhamdulillah kagafa yanzu fa ko’ina najikinsa yana motsashi dan jia da sanda ma su Affy suka tasashi agaba haryad’an fara koyan tafiya”
“Alhamdulillah Allah ya k’ara masa lapia”cewar Modu cikeda murna
“Amin Amin Modu”cewar Ammin
Shide yareemah Ngari banda murmushi ba’abinda yake masu tunda ba bakin magana amma kuma Alhamdulillah tunda yana jin mesuke cewa sun jima a d’akin harseda Ngarin yasamu bacci sannan suka koma sashen Ammin sukaci abinci sunfara shirin tafiya ne su Affy suka dawo daga islamia da ake koya masu a cikin gidan da gudu Affy ta d’ane aliyu taname murnar ganinsa,
“Baa Hydar weli weli welcome back”
Murmushi yai yana shafa cheeks d’inta,
“Baby of the family”
“Baa Hydar ashe ashe meenah xaka aura”tak’arasa maganar cikin murna,
Shafa kansa yai ganin duk su Ammin sunxuba musu ido ahankali yace mata,
“Eh”
Sannan yadubi Modu dake rafka surutu da Aysa,
“Guy muje ko nasan baba yana jira”
“A’a haba Aliko Hydara baxaka fad’a mana yadda akaiba”
Cewar k’anwar Ammin dake tambayarsa cikeda son jin yaya aka k’are.kamarsu d’aya da Ammin sede ita bata cika hasken fata ba kamar Ammin,shafa k’eyarsa yai kawai yana duban Modu dayak’i bi takansama ahankali yace,
“Mami komi normal”
“Kai Aliyu haryanxu kananan da wannan Arrogant halin naka to Allah ya kyauta maka aure ne de babu fashi se anyishi”
Murmushi kawai yayi batare dayace komaiba juyawatai tana kallon Ammin kafin tace,
“Yakaka kinji yak’i fad’a ko?!”
Daria kawai Ammin tayi kafin tace,
“Ky’aleshi yaruwaiya(ruqayya)inda sabo yadace ace kinsaba da nunk’ufurcin Aliyu”
“Cab kaikuma Modu fa wacece takan?!”
Aunty yaruwayya tatambayi Modu dake faman tsiri tsiri da idanuwa hakan yabawa Aliyu dake gefe daria mik’ewa Modu yai shima yana dari’ar kafin yace,
“Mami soon xaku ganta”
“Akwai wata yarinya me hankali da nutsuwa wlhy namaka sha’awarta batafi aysah ba”
“Lalle a’ina take mami?!”
“Anannan unguwar bulabulin ngarnam”
“Kan bala’iiincan Mami kirufamin asiri,Guy xomu wuce plss kaji Mami fa”
Gaba d’aya aka saka daria a parlorn jin yadda Modu yarud’e yake magana sallama suka masu sannan suka koma shehurin...
_*shehuri_*
Bayan su yareemah Aliyu Hydar sunkoma fada suka nupa wajen mai martaba suka sheda masa sundawo sund’an tab’a hira sannan yace masu suje su huta yak’ark’are da,
“Nagode maku Allah yasaka maku da alkhairi ya d’aukaki rayuwarku aduk matakin dakuka shiga a duniya kawu alooma yace min komai an gudanar dashi yadda yakamata Nagode maku nagode k’warai matuk’a yanxu abinda yarage shine duk acikin satinnan xa’a gama nema maka auren duka su biyun don ita Meenah ma har dinar na d’aurin auren xa’a bayar shi wannan babu matsala Inafatan kungane?!”
“Eh baba”
“To kuje Allah ya maku albarka seku fara shiri na komawa makaranta ko?”
“To baba Mungode Allah yasaka da alkhairi”suka fad’a atare
Sannan yabasu damar tafiya suka mik’e suka nupi sashen su kowannensu da abinda zuciyarsa ke sak’a masa,
_*YOLA(Mai Alooma Ghaji Residence)_*
“Meenah kukan me kike tun d’axu nayi nayi dake kifad’amin meya faru kink’i ko?to wallahi xan had’aki da Bulama ya lillisamun ke kilan inkika daku kya fad’i menene”
Aunty yafendo ce ke tambayar meenah hankalinta duk yatashi ganin tun safe take kuka kuma tayi tayi da ita tafad’i menene me akai mata amma tak’i saboda tsabar kafiya,
Hawaye kwance shab’e shab’e asaman fuskarta tace,
“Aunty..Nikam haihuwa zanyi,”tak’arashe xancen tana kuka,
Zumbur aunty yafendo tamik’e tana gwalalo idanuwa had’e da dafe k’irji cikin firgici tace,
“Handi inboni,me.. me yafaru meenah?!”Aunty yafendo tak’arashe xancen cikeda d’imaucewa,
“Aunty kobah yaya Aliyu Hydar bane ya murd’e min hannuna shikenan yanxu nayi ciki nasan haihuwa xanyi”
Sanyi aunty yafendo taji har cikin ranta gefe d’aya kuma daria ce ta kusan kufce mata tai saurin danneta ahankali tashiga yiwa meenah bayani dede yadda xata gane dukda tasan ba ganewar takeba saboda yadda hankalin Meenan yatattara yakoma window hango gid’ad’o datai da cima kala kala ta kayan xak’i yabajesu a balcony yana dannawa cikinsa,kallon nasa kuwa datake k’ullalliya take shiryawa nayadda xata rabashi da kayan tahanyar tsokanoshi har Aunty yafendo tagama maganarta meenah batasan me take nupi ba k’arashen xancen kawai taji,
“Kinganeko Aminatun baffa da Aunty da yayya?!”
Jinjina kai kawai tayi gami da jan majina don haryanxu takasa sakin ranta abin yakusa bawa aunty yafendo daria ta gimtse tace,
“Seki kwantar da hankalinki yanxu and cheer up”
“Toh”
Kawai Meenah tace had’e da fecewa aguje tai hanyar balcony hango gidad’o tai yana dannawa cikinsa chocolate na maltesers bata b’ata lokaci ba tararumi ledar gabansa duka ta fece aguje dama gata ba kib’a gudu baya mata wahala,Aunty yafendo dake jikin window tana ganin meke faruwa kanta kawai ta jinjina na irin rashin jin Meenah sakin labulen window tai takama sabgar gabanta bakinta d’auke da addu’ar,
“Allah ya shiryamun ke Aminatu...!”
Nasan har jibi kuna karantawa saboda tsabar yawansa(lol)😊👌🏼
Team#Y.ALIYU HYDAR🤝
BASMA AUR MEENAH!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!*
💖?👨👩👧👦
_*A STUNNING LOVE STORY_*
*NA*
©NANA HAFSAT
(_*MISS XOXO_*)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(_*Home of expert and perfect writers_*)
_*Devoted to_*
cutest momma(_*XARAH BUKHAR_*)
_*Tukwicine agareku_*:
_*Billyn Abdul_*(Tawan) and my beloved sis(ya _*Hajja ce_*)
_*particular thanks goes to my two adorable daughters_* :
_*Bitti Feedhom & dota Billy S Fari_*...
_40/41_
nanahafsat.wordpress.com
____________
_*university of oxford(United Kingdom)_
“*B*abe wai meye hakan tunda kika gama waya kike faman kuka kaman wadda aka fad’a maki sak’on mutuwa,menene pls?”
Layla ce ke tambayar Basma dake faman rera kuka ba k’akk’autawa,cikin kukanta tad’ago tanaiwa lalyla bayani muryarta cunkushe da damuwa,
“Babe,sugar boo ne yakirani yanamun wasu maganganu da k’wak’walwata takasa d’auka”
Bata k’arasaba tasake fashewa da kuka,cikeda tausayinta Layla tace,
“Babe cayai baxe aure kiba or what??”
D’ago jajayen idanuwanta Basma tayi had’e da girgiza mata kai alamar a’a cikin dakushashshiyar murya tace,
“Wai kinji bani kad’ai ze aura ba harda cousin d’insa”tak’arashe zancen had’e da sakewa fashewa dawani sabon kukan,
Ahankali Layla takoma kusada Basma had’e da janyota jikinta tashiga bubbuga mata baya alamar ban hak’uri cikeda k’arfafa mata gwiwa tace,
“Haba babe,worry not nikam I’m hundred percent sure enough kece _son ran_ Aliyu tunda har yafad’a miki haka ai zaki gane cewar itad’in tunda cousin d’insace kilan _zab’in iyayen_ sace right?!”
“I dunno babe”
“To kidena kuka babe we will sort things out kede kidena ma nuna mashi bakison abun kinji?!”
“To”
“Yawwa ko kefa,tashi ki shirya mufita outing”
“Babe bakiji fad’an da Amma tayi mana bane?!”
“Oh about that... To banda abinki waze gayamata?!”
“Babe mude barshi kawai,kinji fa Amma tace honor and
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 35