fara addabar shi zuciyar shi na ayyana mai abubuwa da yawa sai dai tsoran yin ya rinjaye shi cikin muryarta ta shagwab'a wadda ta zama jikinta tace mai,
“Ya hydar dan Allah kazo muje ku gaisa da...”
Bata k'arasa ba kawai ya janyota jikinshi ya matseta kam a cikin kirjinshi tamkar zai maidata cikin shi,wani mugun tsorone ya ziyarci zuciyar Meenah hankalinta ya tashi a hankali taji yana bin jikinta da fuskarshi yana shak'ar kamshin jikinta mutsu mutsu ta fara yi na kwatar kai amma ta kasa sai ma jin tsinin hancinshi da iskar bakinshi taji a saitin tsakiyar kirjinta hanuwan shi kuma yana jujuyata dasu duk tabi ta firgice har wani fitsari-fitsari ta faraji murya na rawa ta fara magana,
“Ya hydardan Allah kayi hakuri wallahi bazan sake zuwa inda kake ba yanzun ma tilastani aka yi please na tuba kayi hakuri...”
Tana can tana neman afuwa sai jinsu tayi a k'asa timm!Still yana rungume da ita sai faman yamutsata yake yi,ganin ihunta yayi yawa ne yasa shi lalubo bakinta ya zura nashi ciki tsit kakeji hakan ya hana Meenah magana tana faman lumshe idanuwa wani yanayi na daban yana k'ara shigarta tanajin Aliyu hydar d'in har cikin jini da tsokarta abinda bata tab'aji ba sai yanzu.
Tsawon 2minutes yana abu d'aya ganin yana neman wuce gona da iri ne yasa Meenah ta cizar mai lips na k'asan ba shiri sarki Aliyu hydar ya saketa Meenah ta mik'e da sauri tare da barin apartment d'in da gudu lakacin Basmah ta fito daga apartment d'in hajja yakolo hakan yasa basu had'u ba.
***
Washe gari d'aurin aure wajan k'arfe goma da rabi akaje aka d'aura na yareemah babagana da bilkisu sai da aka shafa fatiha sannan babagana ya kuma tabbatar da cewar billy ta zama tashi hankalin shi ya kwanta farin cikin shi ya dad'u,ana gamawa wasu aka tafi kano dan d'aura auran Modu da layla kasancewar duk yan uwan mahaifin nata a kano suke da xama ciki harda waliyyin daxe d’aura duk da cewar shi Modun baya nan yana wajan Kiara amma duk da haka baza’a fasa zuwa a d'aura da layla ba.
Gidan Maman ta aka sauka ta gama tattara mutane dama duk da tasan laylan ta gujeta amma bata gayawa kowaba tace dai amaryar taje gurin 'yan uwanta ne yi musu sallaama,nan ma d'in wakilan layla suka shaida auran b'angaran Modu harda Mai Alooma akaje dan shine wakilin shi,ana gana d'aurin aure suka juya da nufin cewar za'a kai amarya anjima zuwa shehuri...
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO_*👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
*58*
*G*aba d’aya Basma su hajja gajiram sun susutata kancewar wai bak’ak’en aljanu ne a kusurwoyin gidan nata sune ke hanata samun ciki ta haihu sam ta ajiye wani batun tunani agefe kullum cikin bankawa gidan tsubbun hayak’i take kusurwa da kusurwa har d’akin baccinsu sannu ahankali sihirin yafara cin sarki Aliyu Hydar kwata kwata baya tunanin mahaifiyarsa hajjagana da yan uwansa ciki harda matarsa Meenah..
Kullum mai martaba mai murabus cikinyi masa fad’an yaje ya ziyarci Ammi da yan uwansa yake amma sam sarki Aliyu Hydar yak’i shikansa abun yanad’an damunsa watarana amma gangar jikinsa tak’i yarda yai hakan..
B’angaren Modu kuwa kullum cikin xulumin aurensa da layla yake sam yakasa tsaida hankalinsa waje d’aya shi yanzu gaba d’aya jinsa yake duniyar tamasa xafi bawanda aka tsana seshi sarki Aliyu Hydar yayi yayi su xauna suyi magana yaji matslar sa fafur Modu yak’i yauma dakyar yasamu yakirashi xuwa fada bayan k’afa tad’auke,
“Guy!bantab’a xaton akwai abinda xe dame kaba kakasa sanar dani waini kake b’oyewa abinda ke damun zuciyarka why ban isa kafad’amin bane ko kuma ban cancantaba?!”
Shiru Modu yai bai tanka masa ba yajima ahaka sannan yasaki ajiyar zuciya ahankali yace,
“Layla...”
“What about her??”cewar sarki Aliyu Hydar,
“Guy bana sonta bana sonta,ni I was thinking ma kokai kasamu baba kagaya masa cux i was kinda confused how on earth baba yasan da maganar layla”
“Have i ever lied to you?!”cewar sarki Aliyu Hydar ahankali
Girgiza kansa Modu yai,
“Then why should I start now?!Guy wallahi kaji rantsuwar musulmi kosau d’aya bantab’a magana da baba akan abinda yashafi aurenka da layla ba,koka manta baban yad’auka ma bakinmu d’aya”
“M sorry,abunne yad’auremun kai tayaya baba yasani?!”
“Guy mantawa kai lokacin aurena nima bahaka yatura harcan London ba akai bincike akan Basma?!”
Kad’a kansa kawai Modu yai alamar Eh,
“To Guy yarinyar nan tana bala’in sonka tunda har xatai tattaki taxo har nan yerwa domin baka hak’uri ai wallahi ba k’aramin sonka takeba wallahi da safe dana ganta bayan nasakko daga sama ita kuma tana rakub’e ajikin kujera senaga kamar ba itaba saboda gaba d’aya ta canxa kamanni kamar ba wannan had’addiyar babe d’in dakake mutuwar so bace,
Lalle so yana azabtar daku kaida ita yadda kasan an canxa maku kamanni”yak’arashe xancen yana dariya ahankali..
D’an murmushi Modu yai domin baxe iya dariya ba saboda yadda yakejin ransa na sosuwa d’an hira suka tab’a dukkowa ransa ba dad’i sannan Modu yamik’e yafita bayan sarki Aliyu hydar ya rokeshi daya tsaya ya saurari layla yaji abinda taxo dashi..
Yana tafiya yaji taku a bayansa layla ce se sauri take tana kiran sunansa tsayawa yai yajingina da gate d’in balcony yaharde hannuwansa yana binta da kallo sanye take cikin doguwar rigar atamfa gaba d’aya ta xabge ta rame se k’aton mayafi dako shiga beyi da kayan ba tayafashi sam mutum xe kwaso rantsuwa yadire kancewar ba layla fashionista bace tada,
Har k’asa ta tsugunna tana gaisheshi sosai abin yaso yabashi daria ya gimtse ya amsata ciki ciki,
“Muhammad dan Allah ka tsaya ka saurareni katsaya kaji abinda naxo dashi wallahi duk abinda xan fada maka babu k’arya acikinsa”
Shiru Modu yai yana saurarenta batare daya amsa mataba ya shiga cikin balcony yaja kujera yaxauna binsa tai itama ta tsakure agefe,
Ahankali tafara magana,
“Kamar yadda kasani sunana layla bashir dikko asalinmu yan garin katsina ne a kauyen kurfi mahaifina shine d’an asalin garin katsina mahaifiyata kuwa takaru ce y’ar makkah amma ance usul d’insu yan kano ne domin acan aka haifeta,mu uku ne awajen iyayenmu kawai saboda duk haihuwar da mahaifiyar mu take rasuwa suke,
“Muhammad harith shine farkon d’a awajen iyayenmu se mabiyinsa muhammad hadee seni auta domin nikad’aice mace acikinmu duk wani gata iyayenmu suna nuna mana musanman ma ni dayake nikadaice ‘ya mace,
“Mahaifinmu ya kasance me k’aramin k’arfi dukda de a yadda yaya muhammad yake bamu labari yace abbanmu da ya kasance acikin halin samu kafin yadawo yaxama cikin rashin domin karayar arxiki tasameshi ne tun lokacin yaya muhammad Harith ne kawai d’ansu aduniya,
“Mahaifiyata hajia salamatu takasance irin uwar nan masu son abun duniya domin akan idanuwanmu take cakular colar rigar mahaifinmu kan lalle idole seya mata abinda takeso sam akan kudi idanuwanta sun rufe bata ganin kan kowa da gashi”
Shiru layla tai tana goge hawayen dake kwance shab’e shab’e akan fuskarta datai firit saboda rama,ahankali murya a taushashe Modu yace,
“M sorry..”
Murya na rawa Layla tacigaba,
“Mahaifiyata tasa mahaifina agaba seda yasaida duk wata yar kadararsa muka koma kano da xama,tamaida mahaifina kamar wani sauna komi tace shi yakeyi bashida ikon tsallaka karan data ajiye kwatsam baxan mantaba ranar wata laraba da safe k’anwar mahaifiyata taxo suka shiga d’aki bansan me suka tattauna akaiba har suka gama k’anwar tata tatafi,
“A daren ranar ummanmu ta sakawa mahaifinmu banbamin masifa kan lalle idole itama seya biya mata kudin jirgi taje makkah tagano danginta hak’uri yadinga bata kan babu yadda xeyi ne da yanada hali babu shakku seya biya mata,
“Wallahi Muhammad ina cikin baccina ummanmu tatasheni washegarin ranar da sassafe naxata ma ko makara nai a makaranta saboda akwai jarabawar jssce daxa muyi a lokacin umartata tai danai sauri na kintsa nafuto nasameta awaje bankawo komaiba na shirya nafito kallo d’aya naiwa abbanmu dake hawaye a gefan rijiya bansan meke faruwa ba nafita da sauri don tuntubar umma ina fita tai hanxarin cusa k’eya ta cikin mota taxi mukai gaba,
“Tambayar duniya naiwa ummana tak’i amsamun musanman yadda hankalina yatashi saboda aranar xamu fara rubuta jarabawar junior waec lokacin inada shekaru goma sha shidda a duniya muhammad to cut the story short mahaifiyata wadda takawoni duniya wai itace xata kaini ga halaka,
“Muhammad ummana itace takaini wajen da akaravani da virginity dina muhammad ummana itace dakanta takaini wajen da d’an shekaru sittin aduniya yarabani da martabata muhammad ummana itace takaini inda aka fara sanina a mace ba a gidan aure naba,
“Ina kuka ina kiran sunan mahaifiyata dataxo ta ceceni amma sam ummah batai ko yunkurin hakanba naci kuka nakai kukana ga Allah saboda ko a islamiya malaminnu yana yawon ja mana kunne kan mukai martabar mu gidan aurenmu domin shine mutuncin kowacce ya mace,
“Atak’aice muhammad ummana kudi tanema dani domin bayan yagama lalatamun rayuwata kudi himili guda cikin jakar ghana must go yabawa ummana dashi taimana vissa dakomi muka tafi makkah can wani gari wai riyard acan ummana tamaidani abun samun kudinta gaba d’aya tabudamun idanuwa manyan mutane dasu nake harka dagani har ita abinda muka dingayi kenan sosai ummana taxama me kudi tana kano to jiddah harya kasance ma tana debo mata ana harka dasu tana biyansu,
“A makkah nagama secondary school d’ina alokacin muka koma kano daxama tanfatsetsen gida umma tasiya mana a nasarawa gra,su muhammad Harith sunyi sunyi sujawoni nakoma wajensu fafur nak’i domin idanuwana sun bud’e ummah tayi yunkurin jan yayyuna suka nuna mata basacin haram sun fara mata wa’azin shiryuwa tafafutukesu suka bar gidan bakinsu d’auke da adduar Allah yasa mugane gaskia,
“To a unguwar muka had’u dasu Basma matar Aliyu Hydar ummah tanuna masu cewar rabuwatai da mahaifinmu kan kishiya data shiga tsakani zumunci me karko muka kulla dasu harde aka kaimu Oxford muke karatu tare kusan nice nasaka Basma acikin miyagun halaye though Basma bata taba bawa wani d’a namjji kantaba itade tafi harkar romancing kawai Banda romancing bata komi”
Shiru tai tana sakin kuka me tsuma zuciya,kallonta kawai Modu yake beyi yunkurin hanata ba sunjima ahaka tana kuka shikuma yana tunani harde tagoge hawayen tacigaba daga inda ta tsaya,
“Shekarar farkon karatunmu na had’u da wani saurayi sunanshi imraan shi hutu yaxo kawai England ba karatu ba nan muka k’ulla dashi haryakaini wajen iyayensa kancewar yatsaidani amatsayin wacce xe aura bansan me sukace masa ba yadakkoni yadawo dani gidah tundaga ranar imraan yafita harkata baya d’aukar calls d’ina naci kuka kamar xan mutu domin har kwanciya nai a asibiti,
“Saboda alokacin naso nayi aure muhammad musanman idan nashiga social media naga ana maganar aure ana posting couples senaji ina sha’awar inama nice wlhy muhammad babu ranar daxato takoma ga ubangijinta banyi kukaba saboda nikaina nasan nab’ata rayuwata muhammad,
“Ko kasan tun first year d’in karatuna ummana tadena biyamun school fees yaxanyi muhammad?!wallahi dole ce tasa nake exposing jikina don nai attracting maxa nasamu kudin daxan biya dana apartment din damuke ciki saboda nariga nayi nisa akaratun bare ince xan fasa idan nace xanfasama kudin daxan biya nadawo ma wani aikinne muhammd..
“Wannan xuwan da mukai da Basma lokacin bikinta alokacin naje kurfi saboda nasami labarin mahaifina da yayyuna sun koma can,dan abba har yayi aure ya auro wata y’ar dattijuwa y’ar kankiya baxawara ce yaya muhammd ma yayi aurensa carpenter ne shi a k’auyen shikuma yaya muhammd hadee yasamu scholarship a umar yar’adua university dake katsina,
“Tun lokacin nanemi gafarar mahaifina da yan uwana,bayan nakomane naketa kiranka domin nabaka labarina muhammad tabbas nasan nima inada nawa kamason lefin,ciki harda irin shigar danakeyi wanda bata kyautuwa kuma tunsanda mukai magana dakai last wallahi bansake banxar shiga ba kuma bansake having affair dawani d’a namiji ba natuba natuba muhammad kaima ina rokonka daka yafemun muhammad saboda nasan sam ni bakai samun nasarar abokiyar zamantakewar aure ba,
“Kodah akazo neman aurena da yan uwanka sukazo ummah itace tafito tace wai bata yadda ahad’a yarta da arniya ba sedanai kuka nadau waya nakira su yaya awaya sukazo da kannen abba sannan aka yadda aka nemi auren,
“Ummah ta lalatamun rayuwa tabbas nasan banda wani ragowar mutunci yanxu saboda haka abinda yakawoni wurinka shine tabbas idan har akai aurena dakai lalle na zalinceka na ha’inceka domin ni wata k’azantace atattare dakai banason ‘yayanka su xamto cikin kaxamar rayuwa irin tawa”
Jinjina kai tayi had’e da jan majina saboda kukan datake harya haddasa mata mura ahankali tai ajiyar zuciya sannan tacigaba,
“Wannan shine tak’aitaccen tarihina muhammad,abu nabiyu kuma niba y’ar kowankowa bace yar talakace wannan shine almuhim dayasa naxo wajenka don nashaida maka cewar ni najanye maganar aurena dakai xankoma kurfi wajen yan uwana naxauna har Allah yakawomun miji irina talaka”
Tana k’arasa fad’a tamik’e tsaye harta soma tafiya tajuyo tadubeshi sekace mutum mutumi sam yanemi bakin magana ya rasa cikeda muryar tausayi tace,
“Nabarka lapia muhammad se wata rana Allah ya k’addara saduwarmu”
Tana k’arasa maganar tai wucewarta ta tafice daga masarautar don dama abinda yakawota kenan shiru Modu yai sam yarasa ahalin dayake ciki fari ne ko bak’i?sake gyara xamansa yai ya lula duniyar tunanin ina mafita?!...
_*```Damboa Road```_*
“Haba yayya yanzu ke shikenan seki xauna aita rabaki da ‘yayanki anrabaki da gidan mijin ki andawo d’anki an maidashi nakasasshe shikuma wanda yarage ana neman rabaki dashi gaba d’aya anma rabaki dashi din.
“Ni gaskia nagaji ai ca’akaima rama cuta ga macuci ibadah ne,mumafa a yerwannan muke ki bani dama nima na mayar masu asirinsu kansu kink’i haba haba dan Allah hak’urinki yayi yawa wannan bayi bane”
Yaruwaiya ce ketaiwa Ammi banbamin mita itade Ammi kanta a k’asa tayi shiru ahankali tad’ago kanta tasauke idanuwanta akan yaruwaiya cikeda murya irinta mutanen dasu Kasan abinda suke tace,
“Haba yaruwaiya idan hankali yab’ata ai hankali ne ke nemoshi,dansu sun b’ata mumeyasa xamuyi kisani shifa Allah baya bacci yananan amadakata koba jima koba dad’e kowannensu xe girbi abinda yashuka...”
Caraf yaruwaiya ta amshe xancen cikeda mita tace,
“Kina nupin yanzu Shikenan semu tsaya muna xuba idanu ana rabaki da ‘yayan naki kekuma baxaki iya komai akaiba?! Haba yayya ina matarsace gatanan ko takanta bayabi wannan ai cutace kuma sannan kice ayi shiru abar xancen??”
“To yaruwaiya mekikeso nayi bayan addu’oin damukeyi?!kinsande baxanyi shirka ba kamar yadda suke ko kuwa?!”
“To amma yayya...”Bata k’arasaba Ammi ta d’aga mata hannu alamar tai shiru,
“Nabarsu damai duka yaruwaiya,kisani komai nisan dare gari xe waye wallahi Allah xe bayyana me gaskia domin shid’in mabuwayine gagara misali ina fatan kin fahimta?!”
Kad’a kanta yaruwaiya tai ahankali tace,
“Nagane yayya to Allah yawarware koma menene ya sake mana katangar k’arfe da duk wani mai nufar mu da mugun abu”
“Ameen”Ammi tace ahankali akuma nutse.
jinjina kai kawai yaruwaiyan keyi tarasa wani irin hali Ammin kedashi sam bata rama abinda kishiyoyinta ke mata ko cikin yan uwa ita halinta dabanne shiyasa take ganin bud’i arayuwarta ta ko’ina,
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_*👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
*60*
_*```London Gazette Avenue```_*
Biki aketa gwangwajewa agarin na london ango Modu sanye yake cikin ubansu blazer bak’a datai mugun amsar kyakkyawar k’irarsa itama amarya Kiara ba abarta abaya ba sanye take cikin bridal cave dress ja me design d’in bak’i ba k’aramin kyau tayi ba,abokanan ango su ma’aruf suma suit suka sassanya bak’ake da tie ja sukuma k’awayen amarya suka gwangwaje da tasu shigar mini party dress kalar baby red abinde se wanda yagani ba k’aramin kyau sukai ba a tangamemen compound d’in gidansu kiara ake gudanar da taron,ango Modu bunami indimi yakasa rufe bakinsa don farin ciki wani nishad’i yakeji se dashe hak’oransa talatin da biyu yake yau shine gashi ga kiara amatsayin mata da miji itama kiaran ba’abarta abaya ba wai itace yau amatsayin matar Modu saurayin datake muradin son rayuwa dashi duk duniya..
White wedding se dinner da beach party suke kad’ai ne bukukuwan da suka rage a bikin nasu Modu da amarya Kiara,hak’ik’a iyayenta ba k’aramin rashin jin dad’i sukaiba sanin yadda kiaran Ke mutuwar son Modun sunsan koba jima koba dad’e dole xatai switching religion gasu su rik’akkun yan catholic church ne suna bak’in cikin ‘yar tasu ta tsame kanta daga cikinsu,
Ana cikin hidimar shagali mai martaba mai murabus yakira Modu awaya yajadda masa lalle idole yahau jirgi yadawo yerwa domin agudanr da shagalin bikin Laylan itama babu yadda Modu ya iya haka yasa Kiara agaba yana kalallameta da magana harde yashawo kanta ta yarda takuma amince dashi d’in kan xata biyoshi bayan ankammala nasu events d’in,
_*KATSINA STATE(KURFI)_*
Layla baiwar Allah tana xaune agaban murhu tana iza xaman itatuwa jira take tuwon ya isa talge ta talgeshi gaba d’aya taxama abar tausayi lalle base mutum ya mutu yake canxa kama ba gaba d’aya layla tacanxa kuma ta jeme dukta lalace rayuwar datai abaya tabbas itace take girbeta yanzu gefan kod’add’an zanin dake jikinta tasa tana share hawaye har inna matar babansu taxo ta sameta ahaka,murmushi innan tai don sam Laylan batada masaniyar an d’aura aurenta da Modu domin rabonta dashi tunsanda taje yerwa bashi hak’uri gyaran murya innan tai ahankali tace,
“Laylatu tashi kije kiyo wanka kishiga d’aki na ajiye maki kaya bisa katifa kid’auka ki sanya kinji ko?!”
Cikin rawar murya layla tace,
“Inna barin k’arasa tuwon nan na kwashe senayi wankan”
“A’a basshi jeki kiyo wankan kede”
“Toh”
Kawai Laylan tace sannan ta mik’e tashiga d’akki tad’akko sabulun kore irin d’an yanka d’innan had’e da sosan buhu tashiga bayi shaf shaf tai wankan tafito tashiga d’akinta dake d’auke da shamilalliyar katifa dukta yayyage ta shafa manta,
Hodar tony montana tad’an shafa sama sama sannan tashiga d’akin inna turus taja ta tsaya saboda ganin had’addan French lace datai dayasha d’inkin Senegalese cikeda axama tafuto ta tsaya bakin madanfami inda inna keta kwasar tuwonta tana narkashi cikin wata kula dukta faffashe,
“Inna ina kayan daxan saka?!”
“Kidiba d’akina yana bisa kan gado”Inna tafad’a cikin katsinanci,
“Inna wannan kayan Kina nufin suxan saka?!”layla ta tambayi Inna baki bud’e
“Eh sune”tabata amsa tana cigaba da kwashe tuwonta da mara,
“Inna ina..ina..ha’a..meyasa xan saka wancen kayan bafa nawa bane,inna kigane ni yanzu banason ‘kyale kyalen nan wallahi,niyanxu duniya ta koyan hankali nagane gaskia don Allah inna ki hanxarin sanar dani kayan wanene yanzu base anjima ba na mayar masu dashi”layla tafad’a cikin kid’imewa
“Laylatu kije kisaka kayannan koma menene xakiji abakin mahaihinki”
“Shikenan inna xansaka”
shine kawai abinda layla tace sannan tashiga d’akin inna tasanya kayan tsayawa tai tanabin ilahirin jikinta da kallo ba k’aramin kyau taga tayi ba riga da xani akaiwa lace din kalar sararin samaniya dayasha ado da baby pink duwatsu,
Vaseline tagoga abakinta sannan tadanyi d’aurinta mekyau,taburma tad’akko tadawo tashimfid’a atsakar gidah hannunta d’auke da littafin 40rabbana tana karantawa jefi jefi sukan tab’a hira da inna dake karkada miyar kukarta se warin daddawa ne ke tashi,
“Inna tun tashina yau banga abba ba ko lapia?!”
“Lahia lou laylatu tun sahe suka tahi kano”
“To Allah yasa lapia de”
“Lahia lou insha Allahu”
Da wannan suka shiga wata hirar k’arar ihun ilham y’ar yaya muhammad hadee ce ta tsaidasu daga hirar da suke da gudu yarinyar tad’ane cinyar layla hancinta dumu dumu da majina,
“Ilham kedawa?!”
Cewar layla dake karkad’e tulin k’asar dake cure agashin yarinyar daba xatafi shekaru 3 ba aduniya,
“Da amma”
Ilham na rufe bakinta fureran tashigo dashe baki layla tai domin ba k’aramin sonta takeba don kullum setacewa yaya muhammad hadee yayi sa’ar mata,
“Aunty furerata ina yini?!”cewar layla
“Lahia lou layla ya gidah?!”
“Lou lou aunt”
“Inna ina yini?!”
“Lahia lou hurerah kun iso?!”
“Eh mun iso inna,layla kanki da kitso ko babu?!”
Aunty furera ta dubi layla tana tambayar ta,
“Akwai aunty furera amma yau satin shi biyu duk ya tsufa mekika gani?!”
“A'ah ba komai tashi zaki na kuma yi miki wani yanzun nan.”
Aunty huraira ta fad'a tana d'akko wani tsohon crate d'in lemon kwalba ta ajiye shi a bayan layla tana cire mata d'ankwalin da ta d'aura tare da furta,
“Wash Allah na.”
Layla tayi saurin cewa,
“Aunty furera kina wash Allah kuma kina k'ok'arin k'arawa kanki wata wahalar?!dan Allah ki barshi tunda ina garin gobe sai kiyi min.”
“A'ah layla yanzun zan miki ba wani gajiya nayi ba kawai sabone da idan zan yi abu sai nace wash Allah.”
Murmushi kawai layla tayi tana kara karkad'e kasar kan ilham sannan aunty huraira ta fara tsefe mata kanta sunayi suna hira nan da nan aka gama,ko tashi basu yi ba nan suka ci gaba kawai dayin kitson, kafin wani lokaci kasan cewar tana da saurin hannu har an kammala duk da cewar kananune tayi mata shi mai kyau kan ya fito sharr dashi.
Ana kammalawa su Abba na shigowa,sannu da zuwa suka yi mai sannan ya kalli layla ganin yadda tayi kyau sannan ya maida kanshi wajan Inna yace,
“Ince dai baku sanar mata ba ko?!”
“A'ah bamu hid’imata komai ba kamar yadda kace.”
Inna ta fad'a sannan Abba ya kalli layla wadda kirjinta ke bugawa zuciyarta na zullumi jin yadda ake ta yi mata yawo da hankali, Abba yace,
“Laylatu daga d'aurin auranki muke kuma yanzu zaku tafi filin jirgi keda su Yaya Muhammad hadee da inna da kuma hajiya Nana k'awar mahaifiyarki dan kaiki gidan mijin ki tunda sun riga sunce yau suke son akaiki.”
Dafe kirji layla tayi cikin tsananin tashin hankali, kuka ta fara yi tana tunanin wa kuma aka aura mata dan shirun da tayi bawai bata son Modu bane a'ah kawai ba yadda zata yi ne amma yanzu wa aka aura mata shine bata sani ba.
“Tashi layla kije ku kintsa da anyi sallar magriba zaku tafi dan jirgin k'arfe 7:00pm zaku bi..!”
Abba ya fad'a yana kallonta share hawayenta tayi tare da k’ulewa cikin d'aki tana kuma yin wani kukan aunty huraira tabi bayanta,lallashinta tayi amma layla ta kasa yin shiru cikin sheshshek’q tace,
“Aunty furera waye mijina? Shin abba besan akwai wanda nake so ba ya bani wani? Nashiga uku ni layla na rasa oud.”
Ita dai aunty hurairai batayi magana ta sai lallashi kawai dan abba yace ayi shiru kar a gaya mata mijinta har sai taje ta ganshi,ana yin sallar magriba bayan anci tuwo ita kam layla bataci ba aka shirya tare da gyara layla aka shiga makota duk akayi musu sallama suma sunata al'ajabin yadda akayi auran.Layla tasha kuka lokacin da zasu rabu da sauran 'yan uwanta, Yaya Muhammad hadee ne ya rik'e hannunta sai da ya kaita har cikin mota sannan duk wad'anda za'ayi tafiyar dasu suka shiga inna ma tashiga sannan mota ta tashi aka wuce airport.
Suna zuwa airport ba jimawa suka shiga shirgi sai yerwa,suna zuwa jirginsu na sauka nasu Modu ma ya sauka,motar da aka kawo musu ita suka shiga suna ganin wasu rantsatsun motoci tsala-tsala sudai basu tsaya ba suka shiga tasu sannan aka wuce dasu shehuri layla na ganin haka hankalinta ya rabu tana son yin tambaya amma babu fuska har suka shiga ciki.
Kyakkyawar tarba suka samu daga wajan family d'in Modu cikin murna da jin dad'i Basmah ta wuce dasu apartment d'inta, duk babu wanda beyi mamakin ganin mahaifiyar layla a gidan ba ita da wasu aminanta guda uku Muhammad hadee kam jiyayi tamkar ina ma ace bezo ba wannan wane irin abun kunya ne mahaifiyar su ke jamusu sukam sun shiga uku.
Inna ya janyo gefe cikin takaici yace,
“Inna wannan wane irin abune haka da umma keyi?Yanzu wayace dan Allah dan annabi uwar yarinya tazo bafa ita kad'ai bace aka auro na kuma tabbatar babu wacce zata zo gara ma k'ila iyayan arniyar su zo amma itafa? Mukenan ko a ina sai an b'arar mana da mutunci?!”
Kafin inna tayi magana suka jiyo muryar umma a bayan su tana cewa,
“Hadee ni kake cewa ina b'arar muku da mutunci?a tunanina nice sanadiyar da yasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 35