Share this page
ta xarta yai mulki,kaide d'innan kaine ka cancanta domin kaikafi cancanta daka mulki sarautar borno" "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..."shine kalmar da yareemah Aliyu Hydarketa maimaitawa a fili,zuciyarsa kuwa kamar xata faso don b'acin rai "Se kuma me?"cewar Ammi "Se maganar aure dayamin"yareemah Aliyu Hydar yace hakan muryarsa na rawa idonsa ya kad'a kai jawur "To Alhamdulillah tunda yamaka magana dama nima inason jin tabakinka akan wannan batu,yaya kukai dashi?!" "Ammi nace mashi akwai Wadda nakeso amma bamu gama dedetawa ba" "Wacece ita?!a'ina take?!yar gidan waye?!"duk lokaci d'aya Ammi tamai wannan tambayr "Ammi itama student ce a c'an Oxford tana karantar international economic relations ...Yar gidan commissioner of finance ce na kano state..." K'arasa maganar Aliyu Hydar yai tareda yin shiru yana jiran me Ammi xatace Ajiyar zuciya Ammi tasauke,tad'an jima kafin tayi magana da alama tunani take,sannan tace; "To yakukayi da baban naku wane hukunci yad'auka?!" "Ammi cayai xa muyi magana ,amma kafin nan yace modu indimi yasanta?! Nace mashi a'a saboda shi modu a Cambridge yake kuma made bagama dedetawa mukai ba da ita..." "To ba abinda xance sede nace Allah yaxab'i abinda yafi alkhairi,sannan Hydar duk abinda mahaifinka ya xartar ma'ana kowane hukunci yad'auka akanka,kad'au hakan amatsayin xab'i mafificin alkhairi,kada kabi SON RANKA_ZAB'IN IYAYE shine ZAB'I_ nagari Hydar ,kaita addua Allah yazab'i abinda yafi alkhairi kaji?!" "Ehh Ammi Insha Allah .." "To Allah yamaka albarka Hydar.." "Ameen Ammi godia nake..!" Yareemah Aliyu da Amminsa sun jima suna hira ,dan k'ararrawar d'akin yareemah Ngari ce ma takatse masu hirar da suke, k'ararrawar amfaninta yana nuna cewar yareemah Ngari yatashi daga bacci kokuma yana buk'atar wani abun.da sauri yareemah Aliyu yamik'e yanupi apartment d'in tilon d'an uwan nasa dasuke uwa d'aya uba d'aya.....! WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: 2017, 8:06:21 PM: _Hafsat👑: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of expert and perfect writers) nanahafsat.wordpress.com _4_ Yareemah Aliyu_Hydar natashi daga bacci ya fad'a band'aki yin wanka yad'au lokaci aciki kafin yafuto d'aure da bathrobe dakuma k'aramin towel yana tsane gashin kansa daya kwanta luf kamar gashin jariri,closet d'insa yabud'e yaciro shadda sky blue fesheta yadingayi da turare kamar ruwa sannan yashafa mai dasauran dangin su roll on, bayan yasaka kayan ne yakawo hularsa xanna bukhar dark blue yad'ora akai,safa yasaka sannan yakawo batozzi covered shoe dark blue yasaka bak'aramin kyau yayiba,chapette yagoga akan pink lips d'insa sannan yafice daga d'akin se bulala k'amshi yake ga kyau dayayi kamar wanda xashi gasar xab'en kyau.. Yana futa straight fada yatafi wajen mai martaba,bayan sun gaisane mai martaba yasa aka kawowa Aliyu abinci yaci sannan yad'anyi gyaren murya yafara magana; "Aliyu..." Dumm gaban Aliyu Hydar ya buga jin sunan da babansa yakirashi dashi a iya saninsa da Hydar mahaifin nasa yake kiranshi inde yakirashi da Aliyu to maganar daxeyi takai k'ololuwa a muhimmanci.. "Na'am baba" Aliyu Hydar ya amsa kiran da mahaifin nasa yai masa muryarsa har rawa take.. "shekararka nawa yanxu?!" Seda gaban yareemah Aliyu yafad'i kafin yace; "Baaba watan gobe xancika talatin" "Masha Allahu ,To Aliyu magana nakeso muyi dakai ta hankali,sannan abubuwa biyu ne sukasa nace kataho daga makaranta Ina fatan kanajina?!" Cikeda azama yareemah Aliyu ya kad'a kansa tareda fad'in; "Inaji baba" "To Masha Allahu,wato abinda yasa nace kazo abu nafarko de akan maganar murabus danake shirin yine zuwa wani lokaci k'alilan wanda tattaunawar damukai da waziri kenan jia,wanda kaima kasan shekara da shekaru Ina fama da ciwon 'lupus'( lupus is a chronic inflammatory disease that occurs when ur bodys immune system attack your own tissues and organs) sannan abu nabiyu kuma Aliyu inaso kafito da matar aure dan agaskia baxan bari ma ka koma can makaranta ba fyace ansa ranar aurenka tunda karatun naka yazo k'arshe 'modu indimi yafad'amin hakan yace project ma kuke correcting ko?!" Tunda mai martaba yafara magana gaban yareemah Aliyu Hydar ke fad'uwa,ga wani gumi dake kwarara ajikinsa dukkoda sanyin na urar air conditioner dake turare d'akin... Maganar Mai martaba ce ta tadawo da Aliyu Hydar daga duniyar tunanin daya lula.. "Ko ba haka bane Aliyu?!" Mai martaba yace hakan yana tari ahankali tare da d'an dukan k'irjinsa "Ha... Hakane baba gyara mukeyi ana i jibi xantaho muke maganar dashi..." "To hakan yayi Allah yabaku sa'a Ina fatan kayi na'am da duk abinda nace?!" "Ehh baba" "To da akwai yarinyar da kuka dedeta ko kuwa?!" Dumm gaban yareemah Aliyu yak'ara sarawa akaro na biyu,shide yasan duk matan dake mutuwa akansa ba sonsu yakeba sannan basma dayake d'an tausayawa suke magana itama ba wani kwanta masa tai araiba... "Kayi shiru Aliyu,ko bakada tsayayyiya?!" Mai martaba yace da Aliyu Hydar haka ganin shirun nasa Yayi yawa... "Baba gaskia bamu gama dedetawa da Ita ba.." "Anan yerwa fato(maiduguri) take?!" "A'a baba acan take itama tana second year d'inta amma yar kano ce"yak'arashe xancen yana susar k'eya "Modu indimi ya santa?!" Cewar Mai martaba "A'a baba aidayake modu shi a Cambridge yake yanade yawan zuwa school d'in tamu amma bansan koyasantaba dan bamu gama dedetawa ba" "Too shikenan jeka xamuyi magana" Rissinawa Aliyu Hydar yasakeyi yafara magana a hankali; "To baba nagode Allah ya k'ara maka lapia da nisan kwana" "Ameen Aliyu" "Baba inaso naje wajen Ammi mugaysa" "To shikenan sarkin tuk'i seya kaika ko?!" "Da baba ni nakeso nayi driving dayake nad'an jima banyiba" "To hakanma yayi,seka dawo..idan kaga sarkin dawakin tsakar gidah ka turo minshi" "To Ameen baba,nabarka lapia.,xanturo shi yanxu..Yak'ara rissinawa sannan yafice ___Yareemah Aliyu Hydar nafita parking lodge ya hango sarkin dawakin tsakar gidah bashi sak'on mai martaba yai sannan yakarb'i key d'in benz new model yahau yasa key yafigeta se titi, be xame ko'ina ba se damboa road yana zuwa makeken gidan Amminsa guard men suka bud'e mashi tangamemen gate d'in ganin ko waye aciki gakuma tambarin h_r_h sb ajiki amatsayin number motar... Yana gama parking motar affy da aysa suka fito aguje ganin sa da sukai ta cctv d'in cikin parlorn da suke xaune.. "Baa Hydar"affy da aysa suka k'walla masa kira had'e da xuwa subashi huge mammoth hug har seda yakusa fad'uwa ......! WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE??•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakune yan HASKE WRITERS ASSOCIATION 💡 (Allah ya k'aro maku hasken ido da d'imbin basira,Allah yabarmu tare💞) 6 Shiga yai apartment d'in baa Ngari bakinsa d'auke da sallama,babban parlor ne k'ato komi naciki samfarin royal ne harta console dake mak'ale ajikin bango,tatas ko'ina yake kamar b'angaren me lapia,kansa tsaye ya wuce hanyar d'akin yayan nasa dogarai ne gudah uku dasuka sha nad'i da d'inkin babbar riga irin na dogarai kalar masarautar wato kore da ja( green and red),matsawa gefe sukai suka bashi hanya yashiga cikin d'akin bayan sun kwashi gaisuwa.Kwance yahango yayan nasa me kula dashi yana gyara mashi kwanciya da matashin kai(pillow),kamarsu d'aya sak da Hydar,sede shi bekai hydar fad'in jiki ba dayake majinyaci ne, Amma haryaso yad'ara Hydar din a hasken fata da kuma yalwar gashin kai da tsinin hanci... Abinde sede afurta kalmar tubarkAllah...! Alama Hydar yaiwa me kula da Ngari da hannu,shin yakoma bacci ko kokuwa idanuwansa biyu?! "Ya farka..." Shine abinda yace da Hydar ahankali sannan ya k'araso yagaisheshi tareda ficewa daga d'akin yajanyo masu k'ofar... Cikin sauri yareemah Aliyu Hydar yak'arasa gaban Royal bed d'in da yareemah Ngari(usman)Ke kwance,sanye yake cikin k'ananan kaya yan kanti rigar fara me layi layin blue, se blue d'in jeans dake jikinsa,hular kansa tasanyi tad'an zame kad'an yalwataccen gashin kansa yakwanta sidif kamar jariri, kaikace lafiyayyane a yadda yake..da sauri Aliyu Hydar yajanyo hular yagyara masa tareda janyo duvet yak'ara rufe masa jikinsa,duk abinda yake ,d'an uwan nasa sebinsa yake da kallo kaida kagani kasan yayi murna da ganinsa ba kad'an ba.. "Nda dubdo baa Ngari?!ya k'arfin jiki" Tattausan murmushi yareemah Ngari yaiwa yareemah Hydar, "Allah yak'ara maka lapia baaa Ngari Allah yakawo k'arshen wannan wahalar,Allah yasa kaffarane" Murmushi yareemah Ngari yasake yi akaro na biyu had'e da lumshe idanuwansa biyu ahankali sannan yabud'e ,alamar Ameen Nagode.. Hawayene suka soma gangarowa daga idanuwan yareemah Aliyu Hydar da sauri yamaidasu gudun kada d'an uwan nasa yagani, ahankali yasa hannuwansa yana massaging k'afafuwan yareemah Ngari, addua yake ahankali yana tofa masa a ilahirin jikin nasa, tausayin d'an uwan nasa yasake kamashi ganin ga mutum har mutum amma ba bakin magana zeji amma baxe iya mayarwaba, sannan babu dama yamotsa jikinsa kamar me paralysis gaba d'aya jikin nasa ashanye yake, sannan baya iyaci baya sha sede ta drip ake saka masa me protein, wannan wacce irin rayuwace,meyai haka ake cutardashi?!Sallamar doctor d'in yareemah Ngari ce ta tsaidashi daga dogon tunanin da zancen zucin dayake; "Wa'alaika Assalamu warahmatulAllahi wabarakatuh...." Yareemah Hydar ya amsa ahankali.. Hannu Doctorn yabashi suka gaysa sannan yawuce wajen yareemah Ngari, gwaje gwajensa yai sannan yaciro drip yasaka mashi had'e da sake gyara mashi kwanciya, ganin bacci yafara d'aukan yareemah Ngari yasa yareemah Hydar fita yana jiran doctor yagama mashi allurar yafito..Doctorn yana fitowa yasake bawa yareemah Aliyu Hydar hannu suka gaysa.. "Yaushe kashigo gari?!" Doctorn yace da yareemah Hydar hka "Jiya nazo dr mele(idris) ya issue d'in baa Ngari i hope jikin nasa yana sauk'i?!" Nannauyar ajiyar zuciya dr mele(idris) yasawke,sannan yace.; "Tohh abinne se a slow yareemah, but trust me Wlhy muna iya bakin k'ok'arinmu Kasan shi irin wannan ciwon bana asibiti bane kad'ai kawaide mu muna k'ok'arine tahanyar gwajin jikinsa da blood,stool nd urine test (jini,kashi da fitsari)sekuma drip da muke saka masa da magunguna damuke diluting dasuke keeping d'inshi healthy and energetic, sekuma d'an abubuwan daba'a rasaba, amma se andage sosai da addua ,akan duniya da dukiya daxa'a tafi abarsu ake neman kashe ran da Allah ya halitta... Kai Allah kashiga tsakanin nagari da mugu Ameen" Dr mele yak'arasa maganar yana jinjina kai Iska me zafi yareemah Aliyu Hydar ya fusgar daga bakinsa,ya jima yana haka kafin yace; "Dan Allah dr mele(idris)nasan kuna trying possible best d'inku akan baa Ngari,amma dan Allah asake kula da lapiarsa sosai, idanma yadda ake biyankune yai kad'an nixan ninka maku kud'in nayi alk'awari..."yareemah Hydar yace hakan muryarsa cikeda tausayawa "Worry not yareemah,nidaku we are family,anxama yan uwa, sanin kankane nine family doctor d'inku for over 30years tunkafin a haifeka kenan,so badan kud'i nake muku aiki ba,nikaina ina fatan samun sauk'in yareemah usman ina Kuma tayashi da addua Allah yatashi kafad'unsa Ameen.Saboda haka kakka damu duk wani k'ok'ari munayinsa,muna kan yinsa,da yardar Allah komi ze dawo normal" "Allah yasa dr...Allah yasa Ameen"yareemah Aliyu Hydar yace hakan yaname goge zafafan hawayen dake ambaliya a fuskarsa "To nixan wuce yareemah, anjima kad'an dr fallomi zezo yasaka mai drip d'in dare sekuma sauran meds" "Okay dr,Allah yasaka da alkhairi" "Ameen ya rabbi yareemah," Sallama dr mele yaiwa yareemah Aliyu Hydar,ahankali yareemah yatura k'ofar d'akin yareemah Ngari hangoshi yai yana baccinsa peacefully se mekula dashi dake gefe a zaune, me kula dashi yana ganin yareemah yai sauri ze fito, ahankali yareemah yamai alamar daya xauna sannan ya kullo masu k'ofar yafito Kai tsaye yai hanyar sashen Amminsu.... Ringing wayarshi tafarayi 'Basma Oxford'sunan dayai appearing kenan a screen d'in wayar tasa,kamar baxe d'auka ba sekuma yad'aga fuskarnan a murtuke ransa inyai dubu a b'ace yake yarinyar tafara takurawa rayuwarsa gashi shikuma bayason a takura masa.. "Boo boo." Basma takirashi da haka, "Basma..."shine kawai abin da yace "Baby Bakada lapia ne?!" "Da akai ya ya kuma??"yace a kafule "your voice sounds...."bata k'arasaba yai saurin katseta ganinsu Aysa dasuke nuposhi da sauri suna k'walla mashi kira "I'm kinda busy basma, will holla you idan ina free.."k'it yakatse wayar dede lokacin da auta affy ta mak'alk'aleshi tana tambayarsa; "Baa Hydar ,dan Allah bani mugaysa" "Ohh no.."yareemah Aliyu Hydar yafad'a k'asan mak'oshi, "Abokin nawa zanbaki ku gaysa?!" Ware ido affy tai tana rufe hancinta alamar kunya..suka hau daria k'asa k'asa itada Aysa seda sukai me isarsu sannan affy tace; "Kai baa Hydar,ta mace ce fa,we heard her voice tundaga balcony"tace hakan cikin hausarta dabata fita dede.. Da gudu ta antaya tana fad'in; "Barima nafad'awa Ammi" "Affy.. Affy .. Ke affy"haka yareemah Hydar yadinga k'wallawa affy kira Amma ina tuni tashige part d'in Ammin nasu, Bin bayanta sukai shida aysaah amma ina suna shiga affy tana k'arasa gayawa Ammin komi,se haki take tana k'arasa fad'in; "Se yacewa ta mace cen cikin wayan nasa wai he's kinda busy wai he'll holla her idan yana free"cikeda hausarta dabata fita Kamar bango yatsage yafad'a haka yareemah Aliyu Hydar yaji,se asannan yatuno handsfree yasaka,cikeda takaici yake jifan autar tasu da harara,tuni ta afko b'aran b'aramar datai bashiri sum sum tamik'e tai d'aki awayonce,itama aysah dake bayan yareemah Aliyu Hydar d'in bin stairs tai tahau ta arce saman,kan lefin yadawo kanta,jiki ba k'wari a kunyace yaxagayo yaxauna a k'asan kujerar da Ammi take yana susar k'eya....! • Nagode sosai ga masoyana wanda suka kirani da wanda sukaimun text message dama wanda basu samu damaba,Allah yabar zumunci naji sauk'i sosai Alhamdulillah...Allah yabarmu tare,#Nagode k'warai,Ina kuma mik'o sak'on gaisuwata ga duk masoyan littafin son rai ko zab'in iyaye😘❤nagaisheku nagaisheku nagaisheku gaisuwa mai k'ima😍😊 WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com 8 Ina kike dota feedhom?! To ki matso kusa ga page d'inki sukutum ke kad'ai😘❤...Allah yabar so da k'auna💞 Saurin tsayar da kukan nata Ammin tai jin yareemah Aliyu Hydar nakiran sunanta,don da' alama batasan ma ta luluk'a tunani haka ba,ajiyar zuciya tasauke tareda cigaba daga inda ta tsaya; "Jikina ya mutu lik'is Hydar, hankalina ya tashi ba kad'an ba dana tuno xanbar Ngari,nande nasake danne zuciya ta nake tambayar mahaifinku shin agurin wa ngarin xe xauna?.. Amsar daya bani haryau tanamun yawo a k'wak'walwata,sunayen wanda ya ambata sunraxanani ba kad'an ba ganin yadda suka saka yaron agaba sun tsaneshi tun haihuwarsa tun yana xanin goyo sukeson suga bayansa, dande Allah yayi shid'in mai tsawon rai ne..." To suwaye haka?! Yareemah Hydar keta maimaitawa cikin zuciyarsa cikeda fargaba da tashin hankali..muryar Amminsa ce takatse mashi tunanin dayatafi nande yak'ara kid'emewa dan baitab'a kawowa kodah wasa ba sune, dan a'iya saninsa kaf shekarunnan amsarde d'ayace da Ammi take bashi idan yatambayeta abinda yasa bata shehurin(masarautar d'in shehun borno) babu Komi Hydar nice nace banasan xaman masarautar shine kawai amsar da Ammin ke bashi duk sanda yatambayeta... "Hajiya gajiram sherrif da hajia yakolo(kishiyoyin ta) sune sukai abinda haryau Ngari ke kan sick bed d'insa,amma Allah yafisu,dan so sukai su rabashi da duniya dayake Allah mabuwayine gagara misali seya nuna masu k'arfin addua yafi sihiri,kuma Insha Allahu yadda na haifi yarannan lapia haka xe wartsake yadawo yadda yake da,da yardar rabbi..." Kamar gunki haka yareemah Aliyu Hydar yaxama,se hawaye dake ambaliya a kyakkyawar fuskarsa,so yake yai magana amma yakasa. Narkekiyar jijiya ce tafuto tundaga cikin kansa zuwa gaban goshinsa inde hakan tafaru tofa antab'o _Aliyu_hydar_mazan fama_. Ammi na hankalce dashi ganin haka yasanyata kallon agogon dake d'aure a hannunta na hagu k'arfe 3 saura kwata agogon ya nuna.. "Tashi Hydar katafi gidah,nasan mahaifinka yanacan yana xuba idon ganinka" "Ammi nina dawo nan kenan"amsar da Hydar yabawa Ammi kenan had'e da gyara xaman k'asaitan dayai a k'asa... "Zaka tashi ko sena sab'a maka?!kadawo kenan?! Ina kadawo?! Kuma bari kaji koda wasa karna kuskura wallahi kaji rantsuwar musulmi ko yaya naji ance ka canxawa sauran iyayen naka akan maganar dakaji yanzu xakasha mamakin abinda xan maka,kanuna komai ba komai bane,tun kafin ahaifeka hakan tafaru kuma insha Allahu yadda yakejin sauki ahankali komai xedawo normal,kaide abinda nakeso dakai shine kacigaba da taya d'an uwanka addu'a kaima kuma kadingayin naneman tsari daga miyagun mutane dama aljanu..kana jina??" "Ehh Ammi inaji..." "To tashi katafi.." "Ammi da so nake na kwana anan,saboda akwai abinda xamu tattauna da dr fallomi" "Kunyi da baban naku xaka kwana ne?!" "A'a amma de yanxu nakeson kiransa awaya nafad'a masa" "A'a karka somayi,dr fallomi kuma ba guduwa xeyi daga garinba.Duk sanda kadawo kwayi maganar,tashi yamma tanayi" (Dayake Ammin irin iyayennanne masu tsayin daka agidansu,akwai tarbiyyar y'ay'anta da d'orasu akan mizanin gaskiya.. Bata basu k'ofar daxasu raina nagaba dasu kwata kwata,kuma ko yaya bataso y'ay'an nata su k'etare maganar mahaifin nasu ko nagaba dasu) "To Ammi natashi"yace hakan tareda mik'ewa tsaye Kitchen Ammin tashiga shikuma yana tsaye,basket tafito dashi arufe d'auke da warmers na abinci da flask, yar aiki tabawa tace tasawa yareeman acikin mota... "To Ammi nabarki lapia...."yace hakan had'e da d'an rissinawa "To Hydar kagayda mahaifin naku seka sake dawowa,sannan kayi istikhara akan wannan maganar Allah yaxab'a maka mafificin alkhairi kaji?!"Ammi tafad'i hakan with care "To Ammi Insha Allah,Nagode kwarai" Kamar karta basshi yatafi haka taji,tanason d'an nata yaxauna agurinta musanman dayake kishiyoyin nata bamasu halin k'warai bane amma yata iya?! Dole tabarshi yatafi kamar yadda sukai yarjejeniya da mai martaban tun shekaran baya kan inde xatabar shehurin(masarautar)to yaxama dole tadawo da yareemah Aliyu Hydar gurinsa tun lokacin Aliyu hydar d'in yanada shekara 7 aduniya,hakan kuwa yakasance,Ita tana damboa road d'aya daga cikin gidan sarkin shikuma Aliyu Hydar yana tare da mahaifin nasa a masarautar, tuno yarjejeniyar dasukai a wancan lokacin yasanya Ammin hawaye lokaci d'aya tasa hannu tana goge shi ganin Aliyu Hydar d'in na mata sallama xeshiga mota,addua tai masa na sauka daga k'arfe lapia dakuma na tsari sannan suka shafa don k'aida ne kullum in yaxo sesunyi haka,har seda yatashi mota yafara tafiya tana d'aga masa hannu shima yana d'aga mata harya fice daga gidan sannan takoma cikin gidan xuciyarta duk babu dad'i lalubo istigfari tayi tafarayi sannan tahaura sama tana kiran sunan su Affy da Aysaah... Cikeda tashin hankali kala kala yareemah Hydar ya isa shehurin lapia,se sak'e Sak'e yake a zuciyarsa nayadda xe b'ullowa al'amuran musanman maganar da sukai da baba na zancen aure da kuma rik'e masarautar,yajima azaune a parking lodge Kansa kife akan steering motar yana sauke zuciya.Sannan yafito yarufe motar yabawa sarkin mota muk'ullin yawuce part d'insu ko takan dogaran dake mai kirari bebiba,basu suka dena xabga mai kirarin; "Allah yaja da ran yareemah Aliyu Hydar maxan fama gadan ga k'usar yak'i..gaisheka yareemah Hydar d'an sarki jikan sarki d'an sarauniya hajjagana,k'anin yareemah Ngari yayan auta gimbiya afiyatu, seka gaji sarautar bornu da yardar Allah..."haka sukai tayi har seda suka gaji dan kansu sannan sukai shiru suna maida numfashi.. Yana shiga b'angarensa ya fad'a kan gado ganin yadda kansa yafara rinjayarsa saboda axabar ciwo,idanuwansa yafara lumshewa alamar bacci yazo kenan,cikin bacci yaji alamar wayarsa na ringing 'Modu indimi'shine sunan dayai appearing akan screen d'in wayar...! WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakune ;k'anwata rano biologist tareda dota billy s fari,Maman arfat,tareda mommyn heenah..! _7_ Se faman soshe soshen k'eya yake,yana kallon Ammi ta gefen ido,gyara zaman reading glasses d'inta tayi dake fuskarta tai kamar batasan yana parlorn ba tacigaba da karanta jaridar 'yerwa daily press' dake hannunta,hannunsa yaxare daga susar k'eyar dayake ahankali kuma a nutse yace; "Baraanem Ammi..!" tareda saka hannuwansa duka biyu yana massaging k'afafuwan Ammin dayake tana daga daman kujera shikuma yana daga k'asan ta azaune agefe.. "Baranem Hydar..." Ammi tabashi amsa had'e da xare reading glasses d'in idonta.. Ganin bata mashi xancen gulman basma da affy takai mata ba yasa shima ya bagarar da xancen yashiga fad'a mata yadda sukai da dr mele akan ciwon yareemah Ngari,itama Ammin basar da xancen affyn tai tashiga bashi amsar tambayoyin dayake mata dukda talura ba'a sake yakeba gani yake xata d'akko xancen basman... "Ammi dan Allah dan yarasoolullAhi menene asalin ciwon baa Ngari?! Ammi please i beg of you karkice baxaki gayamin ba kinji Amminmu"yareemah Aliyu Hydar yace da Ammin hakan tareda saka hannuwansa biyu alamar rok'o Shiru Ammi tai nawani d'an Lokaci kafin tace; "Meyasa kamun wannan tambayar Hydar?! Have I not warned you..." bata k'arasaba yai saurin saukar da kansa k'asan k'afafuwanta danshin zafafan hawayen dayake suka sauka akan k'afafuwanta,shiru tai bata k'arasa xancen ba had'e da sauke ajiyar zuciya,tabbas abunda xesaka yareemah Aliyu Hydar kuka ba k'aramin abubane.. "Please Ammi dan Allah na rok'eki.."shine kalaman da Hydar keta maimaitawa.. "Hydar,ciwon Ngari nasani,mahaifinka yasani kaima kasani da kowama daya damu damu yasan cewar ba ciwon asibiti bane,kabar xancen Hydar ,Allah baya bacci,Kuma Insha Allah Komi xedawo yadda yake before,da yardar Allah" "Ammi..."sekuma yai shiru kawai bakinsa se rawa yake. Ammi na lura dashi don inde Hydar yakasa magana tofa ran maxa yab'aci,xuciyar xakin ta motsa.. "Hydar kalleni nan"Ammi tace da Hydar Da sauri yad'ago kansa yana kallon Ammin da rinannun idanuwansa dasuka koma jawur kamar garwashin wuta, "Banason sakarci,daga magana shikenan xaka fara wannan zuciyar taka,ina kai doctor yajawa kunne akan kadena frustrating lokaci d'aya?!koka nutsu yanxunnan ko nafasa fad'ar abinda xance" D'aga kansa yai sama alamar yadena, ahankali Ammi tafara magana Kamar batason yi... "It was a long,long,longest time ago.Tun kafin ahaifeka,lokacin Ngari yanada shekara uku da wata takwas a duniya baxan mantaba lokacin muna shehurin(palace d'in sarkin borno)mahaifinku yace xanrakashi tafiya xuwa k'asar ingila halartar wani taro dayake tafiyar taxagayo kaina,dama idan wannan karon yaje da yaya mahaifiyarsu babagana to wani zuwan nice xanrakashi sekuma zuwan mamansu fannah lokacin ba'awani jima da aurenta ba...A lokacin nahad'a mana kayanmu nida Ngari a akwati natanadi duk abinda xamu buk'ata natafiya kasancewar mahaifinku yace dashi xamu tafi...." shiru Ammi tai bata k'arasaba tasa gefen mandil d'inta tana share hawayen dake tsiyaya a idonta,sedatai shiru nad'an wani lokaci kafin tacigaba ,tanayi tanabin fuskar Aliyu Hydar dakallo dake goge nasa hawayen a hankali sannan tacigaba; "Washegari tatas nagama had'a mana komi na tafiya daxamu buk'ata,sega mahaifinku yashigo a hargitse alokacin harnake tambayrsa lafiya?!Shamakinsa yake cemin sarki yana buk'atar hutawa tukun,Shikenan nabarshi ya huta,yayi bacci me tsawo wanda nikaina nake mamakin ko bashida lapia ne?! To bayan tashinsa yake cemin major stress ne kawai bayan haka babu komi,yake sanar dani washegari ne tafiyarmu,inata murna nace barin kwantarda Ngari da wuri tunda jirgin da safe xe d'aga,nan mahaifinku yake cemin wai A'a bada Ngari xamu tafiba,nace meyasa?! Wai sunyi shawara da waziri xa'a shasu(kaciya)tareda babagana dakuma y'ay'an wazirin,banji dad'iba saboda nafuso natafi dashi hankalina xefi kwanciya tunda tafiyar wata d'aya zamuyi,na nunawa mahaifinku cewar tunda de su sauran daxa'a shasu sunfishi shekaru abarshi mana shi idan muka dawo se'ayi,mahaifinku yace a'a yariga da yaxarce hukunci kuma dole haka xa'ayi.Haka nakyaleshi ganin kamar ba'a hayyacinsa yakeba,nikaina nayi mamakin ganin yadda alokaci d'aya yayanke hukunci bayan har vissa da komi anyiwa ngarin" tana gama fad'in haka tai shiru tareda d'aga kanta sama alamar tunani lokaci xuwa lokaci take sauke ajiyar zuciya.... D'ago rinannun idanuwansa Aliyu Hydar yayi yana kallon Ammin tasa dakanta ke d'age a sama ganin yadda hawaye ke gangarowa a fuskarta yasashi maida kansa k'asa,murya a raunane ya furta; "Ammi.....!" WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com

Chapter 2 of 35