Allahu inna”layla tafad’a bakinta na rawa tasake cewa
“Toh inna niyanxu awane yanayi nake shin laifuffukan dana aikata abaya anya inna allah xe yafemun kuwa?!”
“Kayya laylatu kidena dawo da hannun agogo baya hak’ik’a Allah me gafara ne tabbas zina tana daga cikin manyan laifuffuka wanda dukkan shariun da Allah
taa’la ya saukar sun hadu akan haramcin zina,
Al kur’ani mai girma da Sunnar Annabi saw,da dukkan Malamai sun hadu akan haramcin zina Kofofin zina guda biyar ne
_kallo zuwaga Abinda Allah ya haramta,Shigar batsa,Kalaman batsa,kebancewa da matar da ba muharrama ba,Shaawa Mai karfi babu aure Allah taala yace:”kada ku kusanci xina Manzon Allah saw yace :Mai zina ba zaiyi zina ba,yayin da yake xina har sai an cire masa imani.
Abdulllah Dan Mas’ud Ra yace :Duk Al’ummar da take zina,ta jawo wa kanta fushin Allah,da sun halaka.Musulunci yayi umarni da tsare
abubuwa biyar,sune : Addini,Dukiya,Rayuka, Hankali,Mutunci,
Nasaba,amma zina ita kadai tana rusha adannan duka,Hukuncin mazinaci, mai aure kisa ta hanyar jifa,mara aure bulala
dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku,shedu guda hudu,Mutun yayi
ikirari da kansa,samun mace da ciki babu aure,ko shubha.Bisa sharudda da aka sanyawa kowanne
Tabbas laylatu abinda kika aikata abaya babban laifine domin Zina wata babbar musifa ce da
bala’i da dukkan sharri,da take ruguza al’umma,take wargaza iyali,take tarwatsa gari,take rushe
mutunci,take jawo karayar tattalin arziki,da fatara,da tsiya,da annoba,a cikin rayuwar dai dai ku,da gidaje,da unguwanni, da
gururuwa,da kasashe,da duniya baki daya,
Zina itace cikakkiyar fitsara,acikin zina ake samun dukkan sharri kamar :
Raunin Addini,Raunin Akida,Karancin Imani,Rashin kunya,Rashin kishi,Rashin mutunci rashin kwarjini,Rashin hasken fuska,Duhun zuciya,Rashin kima,Rashin Nagarta,Rashin Nutsuwa,Rashin Amana,Fushin Allah,cikawa babu imani,da Azabar Allah,
Wannan shine kad’an daga cikin illolin zina laylatu amma Alhamdulillah ked’in yanxu bakya cikin masu aikatawa Allah ya tsare mu da zuriyar mu,da
dukkan al’ummar musulmi daga afkawa zina,wadanda suke yi Allah ya shirye su mukuma Allah ya k’ara tsaremu da kariyarsa”
Innah na kaiwa nan tai shiru tana sauraron kukan layla ahankali layla tad’ago tadubi innah da idanuwanta da suka koma jawur kamar gaushin wuta cikin murya kuka tace,
“Yanxu inna se Allah ya kamani da laifukan baya ko?!”
“Kidena fad’in haka laylatu karki k’ara fada kisani shifa Allah me saukine kuma yana saukakawa bayinsa adukkan lamura”
Innah nagama fad’in haka ta mik’e had’e da kiran furera dake k’arasa gyara gidan laylan sallama sukaiwa layla domin aranar xasu juya katsina kauyen kurfi sosai layla tayi kuka takawo alherin da Modu yace tabasu tabasu tarakasu har gate sannnan tadawo parlornta taxauna tasaka disk d’in wa’axin malam ja’afar tana sauraro dayake magana akan:
“YANA DAGA CIKIN ILLOLIN DA ZINA TAKE
HAIFARWA TUN ANAN DUNIYA....
1-RUSHEWAR TATTALIN ARZIKI: annabi (saw)
ya bayyana acikin hadisi cewa dukkan
society da suka ta‘allaQa da aikata al-fasha
Allah madaukaki yana dankwafar dasu ta
fiskan tattalin arziki dss,
2-GUSHEWAR KUNYA: annabi (saw) yace da
imani da kunya dan-juma ne da dan-jummai,
muddin 1 ya tafe to 1n ma baya zama,
3-YA‘DUWAR ANNOBA / CUTUTTKA: annabi
(saw) yace zina bazata bayyana ba (kowa
yana aikatawa ba shuwagabanni da
mabiya ) face sai Allah me girma da daukaka
ya sauQar wada mutane annoba / cututtuka,
Dan-uwa ka dubi yanda HIV/ AIDS yake
kashe mutanenmu, Allah ya kyauta,
4-MUDDIN KAYI SAI WANI YAYIWA NAKA:
annabi (saw) yace ita zina BASHI ce, inkayi
sai an maka,
Duk wanda yayi zina da “yar-wani ko uwar-
wani ko yayar-wani, to shakka babu sai anyi
da nashi akwan atashi
Allah sarki hakan ya faru a yankin mu
Wani mutum ya kasance me tsanani wa
yarsa (mace) kasancewar ta girma ya hanata
fita koda makaranta ne, kullun haka---
Rannan saiga “ya“ da ciki,
Karshe yasa mata wuQa awuya kota fa‘da
wanda yayi mata ko ya yanka ta,
Qarshe tace - ina wannan Qawarta me zuwa
yau-da kullum akace ‘ei‘ tace ba mace bace
namiji ne,
Kaga illan zina kenan
5-GUSHEWAR MUTUNCI/KIMA ACIKIN JAMA‘A:
ka kula duk wanda yake zina to Allah saiya
cire masa kima da kwarjini acikin jama‘a
zakaga bashi da kima acikin mutane.
6-MUTUWA BA IMANI: annabi yace duk me
aikata zina al-fahsha to Allah ze zare imani
daga gareshi Qarshe ya mutu ba imani
Annabi yace duk wanda yayi zina da matan
aure- to Allah ze kwashe dukkan aiyukansa
na al-khairi yabawa mijinta
Aranar tashin al-Qiyama kuma Allah ze masa
azabar rabin wannan al-ummah ita matar
ma haka.
Innalillahi wa‘inna ilaihir-raju‘un !!
Annabi yace babu laifi da Allah yafi kyama
sama da mutum ya saka AL-AURANSHI A CKIN
FARJIN HARAM !!
Dan-uwa na ka sani aduniya dayan shirka
wa Allah da kisan kai babu laifi dayafi Qirma
sama da zina !!
Allah ka mana katangar Qarfe da aikata zina”
Layla’ na k’arasa jin k’arshen wa’azin tafashe da kuka ahankali taketa maimata,
“Nashiga uku ummah ta lalatamun rayuwata Allah kaiwa ummah abinda....”
“Ssssh”
Modu yakatseta da alama yajima awurin yana sauraronta da sauri tad’ago kai tadubeshi sekuma ta mayar da kanta k’asa tanaci gaba da kukanta...
#Alhamdulillah dole nai godia da babbar murya agareku masoya nana hafsatu hakika banda bakin godia agareku kusani alkalami yayi kadan wurin zayyano sunayenku Nagode k’warai wurin nuna damuwarmu akaina hakika adduoinku sun karbu idanuwana sun warke rak’as k’as ubangiji Allah yabar zumunci da k’auna,kusani akullum kuna cikin zuciyar matar yusleem har abadan da’iman...!”
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
*63*
*K*allonshi tayi tagan shi yayi fresh fuskarshi tayi fayau sai dai idanuwan shi da suke mata wani irin kallo wanda baya rasa nasaba da kallaman da yaji tana fad'a,jikin shi ya janyota nan da nan kirjin layla ya fara bugawa dan ita yanzu sam bata son taji ya rab'eta duk sai taji ta tsangwami kanta cikin sanyin murya taji yana magana,
“Layla idan rai ya b'aci hankali ake sawa ya nemo shi,yanzu wad'annan kalaman da kike fad'a koni ban cancancesu ba bare uwa mahaifiyarki wanda tayi d'awainiyarki,tana sonki hakan yasa tayi miki wannan abun wanda take ganin kamar shine dai-dai kedai yanzu tunda kin gane gaskiya kici gaba da istigfari itama ki dinga yi mata ko Allah zai sa ta gane gaskiya kin gane ko?!”
Layla da tayi lamo ajikin shi ta d'aga kai alamar taji sai dai har lokacin zuciyar ta batayi sanyi ba kasan cewar tasan oud d'in nata baya sonta yanzu arniya tafita k'ima a wajan shi,tasan ita kawai cikon gida ce a gurin shi.Modu ya janye ta daga jikin shi yana duba agogon dake kafe a katafaran parlon sannan ya kalleta yana kokarin tashi tsaye yace,
“Zan fita zuwa wajan Aliyu hydar idan kina da sako wajan kawarki queen Basmah ki kawo sai na kai mata.”
Layla ta saci kallonshi nan da nan suka had'a idanuwa dashi tayi saurin sauk'e nata,kai ta girgiza kafin ta bud'e baki da kyar a hankali tace mai,
“Ka gaida ita kawai...”
Modu ya juya yana murmushi tare da cewa,
“Ok zata ji..”
Bin shi tayi da kallo har ya b'ace mata sannan ta sauke ajiyar zuciya bedroom ta koma ta kwanta zuciyarta cike da tunanin yadda rayuwarta zata yi a gidan yadda taga oud na wani shareta yana d'auke kai tasan zata sha wulakanci da wannan tu nanin bacci ya d'auke ta mai cike da mafarkai kala daban daban...
_*Shehuri_*
Misalin k'arfe 10:30pm aunty yaruwaiya ta kamo hannun Meenah,ta k'ofar kitchen suka bi ta yadda babu wanda zai gansu sai dai Ammi dama tana fakwansu yanzu ma sai da ta biyo bayan su ba tare da ta yadda sun ganta ba nan aunty yaruwaiya ta bare iborn ta sawa Meemah a baki tace,
“Yauwa tawan idan kinje kina d'ora lips d'inki akan nashi ki zura mishi ita kin gane ai,kina d'an yi mai fari da idanuwa sai kin tabbatar da sakwanki ya isa gareshi sannan zaki cire bakin ki hope m clear?!”
Meenah ta sosa hab'arta kafin ta kalli aunty yaruwaiya tace,
“Kince dai shima kinyi mai magana ko aunty?!”
“Eh mana nayi mai ba kina gani d'azu na fito daga fada ba ai zancen naje nayi mai.”
Jin haka yasa Meenah jin dad'i sannan ta juya ta tafi hanyar da tasan zata samu sarki Aliyu hydar ba tare da ta samu 'yan tsurku ba,Meenah na zuwa ta hange shi zaune yana duba wata jarida kafar shi d'aya kan d'aya gefen shi coffee machine ne da cupcakes ta juya bayanta taga babu kowa sannan ta k'arasa cikin bedroom d'in, yana jin motsi amma be ko kalli gurin ba dan yasan babu me zuwa sai Basmah kuma ita yanzu suka yi waya tace tana wajan hajja yakolo yasan sai ta dad'e sannan zata shigo amma yanzu ya d'auka dawowa tayi d'aukar wani abun.
Shirun da yaji ba'a k'araso ciki sosai ba yasan yashi kallon k'ofa karaf suka had'a idanuwa da Meenah ta sakar mai murmushin ta mai matukar kyau,da tsananin mamaki yake kallonta shi yanzu ma besan yadda zai yi da ita ba ya kuma kallonta tundaga sama har k'asa. Sanye take cikin wata had'ad'iyar laffaya mai matukar kyau sai dai sam bata yi mata kyauba kasan cewar Meenah ba k'iba sai tayi kamar zanata akayi sannu a hankali yaga tana warwareta ya zaro idanuwa bayan ya had'e rai bata damuba dan dama aunty yaruwaiya tace zai yi hakan,sai da ta cire nad'in lafayan tas ta tsaya daga ita sai wani arnan mini skirt dark blue da wata arniyar vest white ta k'arasa kusa dashi tana wata tafiya yayin da bakinta ke motsi alamar tana shan alawan.
Aliyu hydar kuwa tsabar tsananin mamaki kasa rufe baki yayi sai binta da kallo yake,cikin shagala ya ajiye jaridar yana kallon Meenah ta zauna a gefen shi tare da kashe mai ido d'aya tana lumshe wa,a wahale zuciyar shi na bugawa yace,
“Meenah...!”
“Yes honey.”
Tayi maganar tamkar wata karuwa tana sake matsawa jikinshi,tabbas yarinyar nan ta waye da yawa wai nan ma ko secondary school bata kammala ba Ina ga ta tafi higher level sai abin da yafi haka kenan,haka sarki Aliyu hydar yayi ta ayyanawa kafin yaji yatsunta a cikin kunnansa tana juya su a ciki shi kuma sai faman lumshe idanuwa yake can ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya da karfi.
A dabaran ce Meenah ta sanya mouth d'inta cikin nashi tare da tura mai sweet d'in bakin shi gabaki d'aya ya rud'e ya fara yamutsa ta yama manta da cewar ba Basmah bace Meenah ce,ita kuwa duk da tana cikin tashin hankali sai tayi shiru ta kasa yin magana bare ta hanashi sai dai kana iya hango bugun zuciyarta saboda tsananin tsoro.
Tafiya tayi tafiya sam sarki Aliyu hydar ya fita hayyacin shi domin wannan karan Meenah na bashi gudun mawa yana gaf ta shiga babbar fadar da ba'irin wanda ya saba shiga kullum bace kawai suka ji muryar Basmah bayan ta gansu tayi saurin juya musu baya, da gudu kuma tayi waje bedroom d'inta tayi tana kuka wani zazzafan kishi na addabar mata zuciya.
Shikam gogan da kyar ya iya zame jikin shi a gun Meenah amma abin mamaki sai ta sake narke mai ta hanashi tashi kwata-kwata tana mai wani d'an kuka k'asa-k'asa, rasa yadda zai yi sarki Aliyu hydar yayi ga tunanin Basmah ga Meenah itama ta narke mai uwa uba ya kasa yin magana.Da kyar ya samu ya saita zuciyar shi yana kokarin tashi Meenah ta kuma makale mai ita kanta ji take bazata iya barin shi ya fita ba,ganin haka yasa shi rungumeta ba dad'ewa tayi bacci sai da yaga baccin yayi nisa wajan karfe 1:30am sannan ya zame jikin shi ya nufi room d'in Basmah.
K'ok'arin shiga yake sai yajiyo muryarta tana kuka tana nagana daga ji waya take dan haka ya tsaya yana jin abinda take cewa,
“Wallahi umma duk ina yin abinda kuka ce amma wallahi tunda yarinyar nan tazo gidan nan sai ya dinga kiranta d'akin shi bansan meyasa ba wallahi amma duk magungunan da kuka bani ina samai kuma ina turare gidan..”
Daga can cikin wayar hajja yakolo ce ke cewa,
“Rabu dashi kedai ba kina yin yadda muka ce ba?Toh kisha kurumin ki itama zamuyi maganinta ai ke kin fara ganin alfanun maganin ko?!”
Basmah ta share hawayan dake bin kuncinta tace,
“Eh Mama har fa na k'arkashin gadon da na samai wallahi yana nan amma kullum cewa kuke zai kara so na amma sai dai inganshi da wannan figaggiyar yarinyar da babu abinda zata nuna min.”
“Sha kurumin gimbiya abinda ma gobe zasu bar gidan ki dena damuwa zamu san abin yi kinji ko?!”
Kafin tayi magana ta ganshi a tsaye akanta fuskarshi babu yabo ba fallasa baza ka tab'a gane yaji maganganun ko bejiba yadda yayi sai dai tsarguwa da kuma rashin gaskiya tasa asirinka ya tonu,Basmah jiki ya fara rawa tayi saurin katse kiran tana kallonshi harya k'arasa inda take shima ya zauna.
“Basma keda waye haka cikin dare?!”
Kasa cewa komai tayi banda kirjinta dake dukan tara-tara jikinta na rawa hawaye na bin kuncinta jiyayi kanshi na sarawa ya fara kifta idanuwa yana dafewa kafin wani lokaci idanuwan shi sunyi jawur, da sauri ya mik'e directly ya wuce d'akinshi Meenah na kwance na bacci yayi saurin lekawa nan yaga wasu jikejike da wasu layu rakwacam a karkashi tamkar wani d'akin d'an bori.Kanshi ya dafe saboda tsananin sara mai da yake yi ya fara furta kallamar da ya dad'e bejita a bakinshi ba.
“Lahaulawalakuwata illabillahil aliyulazim, innalillahi wa'inna'ilaihir rajiun how comes?!”
Da sauri ya kalli saman gadon yaga Meenah na bacci hankali kwance yayi saurin mik'ewa tare da d'aukarta a hannu yayi waje shaf ya manta da matsayin shi na sarki yayi hanyar apartment d'in da yake tsammanin su Ammi na can.
Wani d'aki ya nufa yana bud'ewa yaga aunty yaruwaiya ta rafka wani uban tagumi kai da ka gani kasan tana cikin tashin hankali,tunanin shine ya bashi ko da Ita Basmah tai waya sai kuma ya had'e rai cikin b'acin rai yace,
“Aunty wa kike jira ko waya kika yi?!”
Ai tana jin muryar shi ta mik'e tana hamdallah musamman da taga ya taho da Meenah,cikin murna aunty yaruwaiya tace,
“Yo ga tanan yarinya tayi tafiyar ta daga cemin kana kiranta.”
K'arasawa yayi kan gado ya kwantar da ita sannan ya kalli aunty yaruwaiya yace,
“Ni k'arya take min ina Ammi take?!”
Zaro ido aunty yaruwaiya tayi tana kallon sarki Aliyu hydar jin yana neman Ammi da sauri kuma ta kamo hannunshi suka fita, wani d'aki ta kaishi lokacin karfe 2:00 na dare suka hangi Ammi zaune akan sallaya tana jan carbi bayan ta farka uban tagumi,cikin sanyin murya taji murya kamar ta Aliyu hydar sai dai tayi tunanin gizaune kamar yadda ta sabaji kullum amma sai taji ya kuma kiranta kamar a zahiri tayi saurin juyowa ganin shi yasa tayi saurin mik'ewa tsaye.
Kasa hak’uri yai da sauri ya nupeta ya rungumeta yana hawaye wani tarin soyayyar mahaifiyar tashice takara shiga zuciyarshi gefe d’aya Ammin kuwa wani tausayin d’an natane yasake mamayeta ahankali tasa hannu tana goge masa hawayen,
“Ammi”yafurta ahankali yana sake rungume Ammin kamar wanda xa’a kwace masa ita,
“Na’am Aliyu..”tabashi amsa tana k’ok’arin maida hawayen dayake neman zubo mata,
“Ammi dan Allah dan annabi kiyafemun kinji Ammina I deserved to be punish rayuwata is miserable Ammi kimun duk abinda kikaga yadace saboda ni...”
“Sssh”...Ammi ta katseshi tana girgiza kai cikeda nutsuwa tace,
“Mekaimun Aliyu?!bakamun komai ba Aliyu karma kasake fad’in haka kaje kasamu bacci Aliyu kaji?!”
Kad’a kai kawai yai yanasake kankame Ammin sun jima ahaka seda Ammi tace yatafi haka sannan yakoma apartment d’insa jikinsa duk ba dad’i cikin zuciyarsa kuwa sake sake yake na hukuncin daxe d’auka akan Basma kotakanta bebiba yawuce apartment d’insa nada lokacin yana saurayi acan yaraba dare yana shawara da zuciyarsa,
_*WASHEGARI_*
Da sassafe sarki Aliyu hydar yakoma sashen sa ko kallon Basma bayayi jikinta se rawa yake nasanin kashinta ya bushe,wankan sa yai yashirya tareda temakon shamakinsa fada yawuce akadan taba fadanci sannan yanupi sashen baba wato mai martaba mai murabus zubewa yai a k’asa yana neman gafarar baba amsar da Ammi tabashi shi baba yabashi kancewar shi baiyi masa komai ba Allah yayafesu gaba d’aya..
Ita kanta Meenah tayi mamakin yadda sarki aliyu hydar yake haba haba dasu aunty yaruwaiya kuwa tsabar dadi ruwa taxuba a k’asa tasha,har Damboa Road sarki aliyu hydar yaraka su Ammi nan yahad’u da Modu har gidajen Modun yashiga yagysa da matan Modun sannan yadawo gidah cike da kewar Amminsa da ‘yan uwansa ciki harda matarsa Meenah da yanzun yake jin wani bak’on lamari akanta..
Tunda yadawo ya wuce part d’insa sauran aikin fada kuwa waziri yadora akai yadda yabar Basma da safe yanxunma haka yaganta ko wanka bataiba fuskarnan a murtuke yakalleta kallo d’aya tai masa ta saukar da kanta k’asa don yadda yake yanxun bashida maraba da Aliyun sa na da cikin isa yace,
“Ke...”
Cikin kuka Basma tad’ago idanunta ta sake dubansa da sauri ta sadda kanta k’asa ganin idanunnashi a tsuke ya kalleta yana jin wani tsanarta yace,
“Kin bani mamaki domin a yadda kike sona banyi tunanin za'a had'a baki dake wajan ganin an rusa min rayuwa ba.Basma da ace iyayena basu da ilimi da tawakkali da yanzu kinja min sun tsinemin sai Allah ya kareni toh na gode dama idan baka da hakkin mutum Allah baya zalintar ka ina son ki sani Basmah ni dake har abada ki had'a kayanki ki koma kano na sauwak'e miki.”
Kuka ta kuma sawa jikinta na rawa ta mik'e ta k'arasa jikinshi,janyeta yayi yana mata wani wulakantaccan kallo cikin takaici yace,
“Kin sani cikin shakku Basmah kinsa tun iyaye da kakanni babu wani sarki daya tab'a yin saki saini nasan zan samu challenges da yawa daga gurin manya amma Basmah ba zan iya rayuwa dake ba nasan nan gaba zaki iya kashe ni tunda har aka iya had'a baki dake wajan ganin an rabani da duk 'yan uwana na gode da irin sakamakwanki gareni *SON RAI* ne ya jamin auranki.”
Yana kaiwa nan yabar d'akin bedroom d'inshi ya shiga wani bak'in ciki yake ji a ranshi kafin ya janyo wata jotter ya fara rubutu hannunshi na rawa kamar mara gaskiya,nan nad'ewa yayi sannan ya koma d'akinta nan inda ya barta anan ya tarar da ita,ko kallanta beyi ba ya ajiye mata akan gado ya bar d'akin da sauri ganin zata biyo shi.
Da sauri Basma tabi bayansa tashiga d’akin idanuwanta ne suka kai kan farar takardar dake ajiye akan gado gabanta ne yashiga dukan tara tara tuni hajijiya tafara d’ibarta dakyar da daddafa drawer tak’arasa kan gadon hannu narawa tadau takardar tashiga bud’ewa hawayene suka shiga wanke mata fuska tunkafin ta k’arasa bud’ewa tana gama budeta tashiga bin rubutun da kallo:
_*Ni Aliyu Hydar na saki matata Basma Basheer Mai_Kano saki....._*
Bata k’arasa ba tai wulli da takardar had’e da sakin wata razananniyar k’ara xaman yan bori tai a k’asan gadon dab’as tashiga buga kanta ajikin katakon gadon tana shusshura k’afafuwa kamar sabuwar tab’uwa fuskarta kuwa hawaye ne kwance shab’e shab’e suna sharara se jan kukanta take me cikeda tarin *NADAMA*
#Ni Mrs yusleem nace I cannot keep taking panadol for this couple undetected headache ooo yau Basma gobe Meenah jibi Modu gata hajja gajiram da y’ar koranta yakolo na jefar da alkalamina akasa ina xan iya caraf ya hajja tacafe da sauri na juya na kalleta ya hajja ya haka?! Watsa hannu baya tai kan ta kwarankwatsa labari be k’are ba....🤣🤣
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO😍❤
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
*64*
Kuka Basma tashigayi ba k’akk’autawa se rera shi take ta d’au lokaci tanayin kukan kafin daga bisani tatashi jikinta duk ba k’arfi ta zura doguwar rigar dake rataye ajikin hanger dudduba d’akuna tashiga yi neman sarki Aliyu hydar bata ganshiba a parlorn k’asa ta hangoshi axaune hannuwansa dafe a kan kuncinansa kansa a k’asa ya sunkuyar,
Gabanta na fad’uwa ta k’arasa sauka kallo d’aya ya mata ya maida kansa k’asa ad’arare taje gabansa ta tsugunna murya narawa tace,
“Aliyu dan .....”bata k’arasa ba ya dakatar da ita da sauri,
“Karki sake kikawomin zancen wofi don narigada nayanke hukunci kuma baxan janye ba don haka kigaggawar komawa inda kika fito kuma kada kisaki naji ance kinje wajen wani nawa akan wannan batu inba haka ba duk abinda yabiyo baya ke kika janyo”
Yana k’arasa fad’a ya mike yabar mata parlorn..
Ta jima a tsugunne inda yabarta tashiga sak’awa tana warewa lokaci zuwa lokaci takan goge hawayen dake sharara a idanunta dakyar tamik’e takoma d’akinta medium size akwatinta tajanyo tashiga had’a kayanta tanayi tana rera kukan Ina mafita?!
Laffaya tanad’a akan rigar dake jikinta kwata kwata lokaci d’aya ta zabge idanuwanta sun sake shigewa ciki kamar wadda ta shekara tana ciwo,harta bud’e k’ofa xata fita tadawo tad’au takardar sakin nata hannu narawa tacusata acikin jakarta sannan tafice daga sashen nata ko kallon b’angaren su yakolo bataiba tashiga mota driver yajata se airport...
Kodah Basma ta isa gidah bata fad’a masu abinda yafaru ba tacede taxo ganin gidah ne kuma xata d’an kwan biyu anan mahaifiyarta kuwa takasa rufe baki se murna take don ita azatonta Basman cike ne da ita dubada yadda tai shahararriyar k’iba ga kuma wani fresh da skin d’inta yai,kashe wayarta Basman tai ta ajiye don yanxun tanada buk’atar nazari akan abubuwan da suke faruwa da ita shin lefin tane ko k’ak’a?!.
Su hajja yakolo kuwa ganin shiru basuga Basma ba yasanya su tambayar jakadiyarta ko lapia?!itade jakadiya amsa d’aya take bawa duk wanda yatambayeta kamar yadda sarki aliyu hydar ya umarceta da tadinga fada Haka take fad’in cewar uwar d’akinnata taje turai saboda kiran gaggawa da malaminsu na makaranta ya mata,
Hajia gajiram kuwa kullum hankalinta atashe yake sam batada sukuni kullum babagana seya sauke mata buhunhunan ruwan masifa akai kan itace tai kulalliya billy bata yarda dashi tak’i bashi hakk’insa ya rame ya jeme kamar ba wanda yai sabon aure ba yanemi kwanciyar hankali ya rasa...
<><><>
*Damboa Road*
Zaune Meenah take itada lesson teacher d’inta littattafaine fal gabanta musanman yanzu da jarabawar kare karatunta ta gabato sam batada wani lokaci na banxa kullum cikin karatu take lessons teachers d’inta kala kala ne kowanne da subject din dayake koya mata sosai take maida hankali musanman dataji Ammi tace xata bata babbar kyauta inta fito da nine credits successfully a waec d’inta...
Zaune suke a study room yanzunma itada hausa lesson teacher d’inta se latsa wayar Ammi take sam tak’i concentrating akan karatun da malamin yake koyarwa don tatsani subject din hausan,Jin tak’i magana yasashi sake gyara murya,
“Madam xanyi reporting d’inki this time around to the prince”
Wani kallo Meenah ta watsa masa kafin daga bisani ta tab’e baki cikin isa tace,
“Excuse me sir... he’s a king not a prince..”
“To Madam ki tsaya kiji last paragraph dinnan dan Allah banason he’s highness yad’au mataki akaina”
“Inaji”kawai tace sannan ta ajiye wayar hannunta tana duban text book din dake study table din da take axaune,
Gyaren murya dattijon malamin yasakeyi sannan yace,
“To daga k’arashe xamu shiga matsayi ko yanayin makwallato..”kafin ya k’arasa Meenah ta katseshi,
“Malam dan yarasulullahi a tsallake page dinnan kalli fa so bulky dukde akan makwallato kobah kwanaki ma kayimun bayaninsa ba kace makwallato wani sashe ne acikin mak’ogwaro akwai wani tantani da yakan ja ya saki kace idan yaja makwallaton xe tsuke idan kuma yasaki xai bud’e don haka makwallaton k’afa ne mai tsukewa ya bud’e gwargwadon motsin tantanin right Malam?!”
Jinjina kai yayi murmushin sa ya fad’ad’a sosai ya k’ara yaba ‘kaimi irinna kaifin basira da kwaxon Meenan cikeda jin dadi yace,
“Correct madam,to next chapter d’inmu xe xama akan ma’anar sauti xanyi maki bayani akan shin menene sauti da kuma yadda ake furucinsa?!”
Gyada kai Meenah tai tanajin yadda yake mata bayani akan ma’anar sauti lokaci xuwa lokaci take jotting important plots na bayanin...
****
*MODU’s*
Sosai Modu yake mamakin yadda yasamu gamsuwa daga layla sam baiyi tunanin hakanba dubada yadda ta b’ata rayuwar ta ada lalle d’an hakkin daka raina...
Gyara mata gashinta daya zubo gaban goshinta yai sannan yabata peck a saman goshinta,
“Babe yanaga kina kunya tane?!”Modu yace da layla tareda kashe mata ido d’aya..
“Oud”tace dashi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 35