maimurabus ta bashi hakuri kafin wa'adin iddar ta ya kare yasa ya maida ita.
A b'angaran Aliyu hydar kuwa bini-bini ya kira Modu shi kuma sai ja masa rai yakeyi hakan take yanzu ma sai faman waya yakeyi mai amma sai da ta kusa tsinkewa sannan ya d'aga yana mai dariya yace,
“Guy wai meyasa sai faman takura min kakeyi ne ehyi?!”
“Mtww duk kayi ka gama yanzu ina ita Meenahn take ina son inji muryarta please Yaya Muhammad.”
Wata mahaukaciyar dariya Modu yayi wadda tunda yake be tab'a bud'e ta haka ba jin Aliyu hydar har da ce mai Yaya,yanajin shi yayin da shima d'in yake zaune a bedroom yana murmushi shi kanshi daya fad'a sai da yaji banbarakwai amma ba yadda zaiyi dole ya lallab'a har ya samu ya had'ashi da Meenah sabida ya kira wayarta akashe ya kira gid'ad'o yace baya tare da ita ya nemi aunty yaruwaiya tace mishi tana gurin baba shida Mai Alooma tana had'a musu abinci hakan yasa dole ya kira Modu tunda ance suna tare da ita da layla da kiara da sauran wasu kawayanta abokai da yan uwa.
“Guy idan bazaka had'a muba sai na ajiye phone d'in kaji?!”
“Idan ka ajiye anjima idan naga ana shirin kawo maka ita sai nace bakajin dad'i kace a bari sai gobe you know me zan iya tsab wallahi ka lallab'ani....”
“Ok ai ni dama yanzu nasan baka sona guy but kayi daga yaune zamu had'e kuma sai na rama.”
Dariya Modu yayi yana hangen Meenah dake zaune tana shan fresh milk sannan yace,
“Mr arrogant kasan dai yanzu baka da wani time na yin ramuwa sabida kullum kana fada amarcin ma ba barinka za'ayi ka more ba da anji kayi kwana biyu baka zuwa za'a fara yi maka fassara kala-kala.”
Ya k'arasa fad'a yana dariya, kin kula sarki Aliyu hydar yayi sannan Modu ya kira Meenah gefe ya bata wayar sannan ya matsa ya koma wajan matan shi domin sun had'e kai sosai suna kuma bashi kulawa ba kamar kiara da batajin kunyar kowa ko gaban waye idan ta ganshi sai ta sakar mai peck shine dai ake bari dajin kunya dan wani sa'in ji yake kamar ya nutse.
“Yah?!”
Cewar Meenah bayan ta kara wayar jikin kunnanta,yana jin muryarta ya sauke wani marayan numfashi sannan shima tace mata,
“You.”
“Me! To fa What?!l
“Ina son kizo side d'ina ina son ganinki now kuma karki gayawa kowa kinji ni ko?!”
Kamar yana ganinta ta zaro idanuwa tare da dafe kirji sannan tace,
“Nazo fa kace?!”
“Eh kuma yanzu.”
"Tab wallahi ni bazan iya zuwa ba gaskiya amma kai kazo mana.”
“Ke!ni d'in kike cewa nazo bayan nine mijin ke kuma matar ko kin manta?!”
Ta kuma ware idanuwa cikin sarkewar murya tace,
“Toh bari na gayawa Ammi.”
Jin abinda ta ce ne yasa shi saurin cewa,
“No barshima kawai na fasa ya hidima?!”
Taji ya fad'a cikin basarwa,a hankali tace,
“An gama komai sai zuwa dare za'ayi wushe wushe Dinner sai a...”
Tayi shiru ta kasa k'arasawa sabida kunya,shine da kanshi ya k'arasa mata abinda take son fad'a tayi shiru yace,
“Sai a kawo ki ko?!”
Wani shirun ta kuma yi shi kuma yayi dariya tare da cewa,
“Bye-bye sai an kawokin yau sai na zane ki tunda ina miki magana kina min shiru.”
Kit taji ya katse tabi screen d'in da kallo,turo baki tayi sannan ta k'arasa inda Modu yake ta mik'a mai wayar shi ita kuma ta koma inda ta tashi ta zauna,nan aka cigaba da hira ana wasa da dariya har Yaya gumsu tazo taja Meenah dan zuwa a sake kamsasata da gyarata.
***
Babagana kuwa tunda yaje gidan su billy be samu fuskar ganinta ba yasan ta tonamai asiri yayi kukan yayi magiyar akan subarshi ya ganta amma ita kanta billyn taki yadda har yau da aketa shagalin biki kowa yana murna amma shi ko fitowa beyi daga apartment d'inshi ba. Ammi ce taga sam tunda tazo bata sashi a idanunshi ba shida matarshi dan haka yanzu ta nufi apartment d'in nashi da nufin bashi hakuri ko wani abun suka yi mishi basu sani ba haka ta dinga wuce mutane ana mika mata gaisuwa tare da fatan sanya alkairi a cikin taron bikin har ta karasa cikin apartment d'in dogarawan shi suka gaida ita sannan ta tambayesu ko yana nan suka ce mata eh dan haka ta shiga tare da sallama.
Tsit cikin parlon hakan yasa ta kuma yin sallama tana kallon yanayin gurin karaf ta hangeshi kwance k'asan carpet yayi ruf da ciki yana sauke numfashi da kyar,da sauri ta k'arasa kusa dashi tana salati ta riko hannunshi mai rik'e da tabar wiwi wadda duk gata nan ansha an yar da k'asan wajan kwali biyu Ammi cikin tashin hankali tace,
“Subhanallahi yareemah mezan gani haka?ina matarka bilkisu har kake wannan abun...?!”
Yana jin abinda ta fad'a ya rushe da kuka tare da sake makalo hannunta cikin nashi,ganin haka yasa tayi saurin ciro wayarta ta kira maimurabus yace gashi nan zuwa,sake kallon shi tayi cikin tausayawa duk da batasan matsalar shiba tace,
“Ina bilkisu babagana..?!”
Ya mik'e zaune da kyar tamkar wanda yayi jinya yace mata,
“Ammi billy na ta gudu ta gujeni,Ammi dama ace kece kika haifeni ba Mami ba nayi nadamar kasan cewa tsatsonta wallahi da ace 'ya'ya na tsinewa iyayansu ko da tuni na tsinewa Ma....”
Ammi tayi saurin rufe mai baki tana rintsa idanuwa dai-dai lokacin maimartaba ya karasaso cikin parlorn,abin da ya ganine a zube a d'akin ya k'ara d'aga mai hankali sannan ya kalli babagana cikin takaici yace,
“Yanzu wannan kayan da kasha sune suka sanyaka jin relief? Tur da wannan d'abi'ar taka na sani ko a gaban Allah za iya tsayawa akan tabbatar da cewar na baka tarbiya da ilimin addini dana zamani sai dai kai din bakayi amfani da suba yau da ace kaikad'aine d'ana na tabbatar da yanzu idan ban mutu da bakin cikin kaba toh ina kwance bana moruwa sabida bakin cikinka,amma yanzu Alhamdulillahi inada masu sharemin hawayena kai kuma Allah ya shiryeka gashi son mace yana neman haukataka.”
Ammi ta kalli babagana sannan ta kalli mijin nata cikin sanyin murya da kwantar da kai ta ce,
“A'a rankashi dad'e kayi hakuri ka gafarta mai sannan ka zauna muji matsakar shi na sani kaid'in mai saurin afuwane.”
Kujera ya janyo ya zauna tare da kallon Ammi yace,
“Nasan ke baki son me yake faruwa ba amma ni nasani kuma macace ta maida shi haka shine yazo yana shan kayan maye sabida hauka.”
Anan ya sanar mata da abinda ya sani yareemah babagana ya kalleshi cikin bugun zuciya yace,
“Baba na kayi hakuri ka yafemin,hakika kamar yadda kace da bakada 'ya'ya da yanzu na nakasa ka toh hakama da bakada Ammi da tuni sauran matan sun nakasaka domin su Mami ba mata bane na gari duk da cewar akwai mahaifiyata a ciki amma hakan bazai hana na yabi Ammi ba,wayyo Allah na ina ma ace ta tsatsonta na fito da yanzu nima ina cikin 'ya'yan da zakayi alfahari dasu,
“Kayi hakuri baba ka gafarce ni sannan kayi min exchange d'in uwa domin Mami ba uwar da mutum zai nuna bace yana kuri tana alfahari da nagartarta ba,Mami ta cuceni ta cuceka baba sannan cutarwarta duk akan Ammi ne please baba ka gafarta min ka yafemin don gaf nake da rasa rayuwata tunda har na rasa billy..”
Ya k'arasa maganar cikin fashewa da wani irin kuka Ammi tayi ta lallashinsa yayin da maimartaba yayi shiru yana son ya gano inda maganar babaganan ta nufa inda yace anfi cutar da hajjagana yana son gano shin tayaya kuma akan mene sai dai baya son tambayar shi dan karya gaya mai abinda zai k'ara d'aga mai hankali, suna nan zaune Ammi na tayi mai nasiha su hajja gajiram da yakolo suka shigo fuskarnan tasu a had'e ba kamarta hajja gajiram cikin isa da tak'amar cewar d'anta ne tace,
“Mezan gani haka banda tsabar cin mutunci ina gidan yarona bashida lafiya a kasa sanar min sai kishin-kishin danaji?ashe kuna nan ku kuma?!”
“Mami ya haka?!”
“Ban sani sabida banida kima a wajanka shine ka kasa aikamin cewar bakajin dad'i sai su zaka aika mawa...?!”
Babagana ya kalleta cikin takaici sannan ya kalli mahaifinnashi yace,
“Ka gani ko baba?wallahi na tabbatar da ace Ammi zataje tagansu a lokacin da baah Ngari na kwance ta gansu a kusa dashi godiya zatayi musu koda kuwa da nufin cutarwa sukaje,amma yanzu ni dubi bani nakira Ammi ba jitayi bata ganniba yasa tazo amma ita da take ikirarin cewar ta haifeni bata zoba tun lokacin da muka samu rabuwar kai tsakanina da matata sai yanzu dataji labarin kuna nan.”
Da mamaki hajja gajiram ta kalleshi shima itan yake kallo sannan tace,
“Ni kake gayawa haka yareemah?!”
Shiru yayi mata maimartaba ya mik'e tsaye tare da cewa,
“Allah ya baka lafiya ya kuma shiryaka duniya da lahira, ke kuma tashi kije kinbar mutane baki a can..”
Daga haka suka zagaye su suka fita,shima babagana bedroom ya wuce yana wani layi tamkar hajijiya zata kayardashi yayin da aka bar hajja yakolo da ita cikin tsananin mamaki kafin suma su juya su fita zuciyar hajja gajiram cikin tsananin damuwa da takaici tare da d'aura aniyar wannan karon da kanta zataje gurin boka dan ayi mata maganin hajjagana.
***
Bayan sallar isha aka shiga shirya amarya Meenah Cikin wani tsadadden uban su lace ne ajikinta Black me torches golden,komi na jikanta gold ne har anklet(sarkar kafa)na k’afarta da bular hancinta duk gold abu tasa,sarkar wuyanta ma abun kallo ce me kwandalelen kambun gold a tsakiya,har kanta seda aka mata kwalliya da gold yayi d’as akan kela yasken(kitson gaba)kanta ga had’addiyar Arabian laffayarta da aunty yaruwaiya tashiga nad’a mata abinde se wanda yagani kawai...
Mamza beauty ce itace taiwa Meenah kwalliya da kawayenta gaba d’aya photographers su mai gaskiya da Georgeokoro se snapping Meenah suke wanda se murmushi take abunta kamar yadda aunty yaruwaiya tace tadingayi...
Dangosho ne pusher pink and black kawayen Amarya sukai se mandil mayafi kamar yadda al’adar take,yan uwa kuwa blue dangasho sukasa kowanne da kela yaske..
Taf shehuri tacika da manyan mutane da abokan arziki kai dama yan gayyar sodi dake san ganin kwakwaf,yadda kasan rana haka masarautar Ke tashi koina da dal da dal d’in fitulu ne...
Kowa ya hallarci taron duk koda card admits one,Fulani night din da akai a damboa road shima yahadu over amma wushe wushen yafi haduwa saboda anfi bashi muhimmanci tunda abin al’dane da yaxama dole ayi shi...
Motoci a tawaga sune suka fara tafiya harabar da xa’ai event din daya sha kwalliya cikin gold and black abinde se sam barka Banda kamshin aroma na abincin kanuri su dangin kisre da brabusko kai harda kunun mard’om shima ba’a barshi a baya ba gefe d’aya kuma local dishes ne na hausa se international dishes wanda suma aka dakkosu na musanman don manyan da suka halarta..
Taro ne daya kun shi governors wives diplomats,ministers,matayen sarakuna da kuma manyan malamai da attajirai da ma yan kasuwa ciki harda abokanan arziki da ba’a barsu abaya ba..
Se bayan kowa yashiga mc tai announcing shigowar Amarya Meenah wadda tashigo da friends nata dakebin taken gangaa kura kowanensu yasha kitson gaba abinde se sam barka kawai...
Su astuto_Nina best frnd sune agaba gefen amarya kuma miss pinki ce ta bayanta kuwa Nabeelah ce da dota billy s fari su Humayrah da summaya da rukynamango se watsa hannuwa ake anabin wajar ganga kuraa..
Bayanta kuwa yan uwa ne su aunty yaruwaiya da su aysah da sauran step sisters na sarki aliyu Hydar ,can k’arshe kuwa su Yaya gumsu ne da gidado dayai burning face shima yana bin tawagar amaryar sanye suke wasunsu cikin dangashe,jene klabe da kuguna karibe..
Tuni aka fara xubawa makadan gangaa kura yirne,waje kuwa jin kida yana tashi yasa aka fara sakin al’adar durum kageye,su kaka deeja kuwa se bada ngaya ka ajiye suke(turare wuta)...
Meenah na dosar tsakiyar fili aka canxa waka xuwa na shuwas wato dangin aunty maijiddah mahaifiyarta wakokin khamal yaqub/mansur ne ke ta tashi dana Amina rawaram..
Meenah na xama aka fara gudanar da al’ada saboda sarki Aliyu Hydar baxe samu damar halarta ba komi anmata shi itade se k’ark’aro murmushi kawai take,
Anci ansha ankuma gyatse can na hango yan home of novels suna lafta loma idanuwa hudu mukai da rano dake saye kisre tana dannawa a nursing bag din affan girgiza kai kawai nai don tasaba,mama arfat ce a gefanta d’auke da arfatu a cinya tanata dannawa cikinta kunun mard’om..gefanta kuwa my billyn abdul ce banda lodawa cikinta fried rice ba abinda take..
Dariata na gimtse ganin mom Heena da maryam umar suna yagar cowleg Dankari na fada a fili can na hango su aysha hamxa anata snapping plate din abinci tana uploading a Instagram nashiga uku nace ganin yan haske writers sunata lafta loma sis Ummy na kalla tamun sign da karna kwafsa musu taci *alwashin* xata ce masu sunyi zarin abinci😹
Can gefen Hall kuwa rano Online novels ne da ya hajja ce novels keta lomar abinci,excellent writers members ma can na hangosu su nafee anker da didi se danna snacks suke a jaka..
Gefe d’aya kuwa QURRATUL ayn ce da miss Hafsy Ke yatsuna face wai adole kar arenasu..
Murmushi kawai nai karaf muka had’a ido da aunty sis dake d’auke da khaleel da sultan agefanta barinta kuwa momma shakur ce dasu feedo sodangi,Nuceey,Asy khaleel,Melody da vasma kawata..
K’arshen Hall kuwa su members din duniyar makaranta ne da musha karatu grp Nuceey da Anmunah nagani suna dagamun hannu da sauri Anmunah tataso miss xoxo ya labarin alwashi shiru?! Y’ar daria nayi kafin nace haba anmunah a bikin ma baxaki hak’ura ba to tace kuyi hakuri yananan tafe....
Da wannan nai saurin barin wajen nakoma table d’inmu nida ya hajjata da asmy lurv da Bitti feedhom dubar ya hajja nai data taune harshe da taunar kashin cinyar kaxa se watsa hannu baya take alamar ciwo..ya hajjata akwai jollof rice kuwa awurin bikin nan?!nodding kanta tai alamar Eh sannan tamun nuni da wajen buffet din dankari nafada azuciyata sannan naduba asmy dake posing ana hoto tawan rakani dan Allah na debo jollof rice kwaso rantsuwa tai ta dire kancewar wallahi baxata ba maxa sunyi yawa ata site din..
Bitti feedhom na kalla tun kafin na fada ta mike itada ihsan suka tafi karbomun abincin...
Gefe d’aya kuwa a wani table shake da manyan mutane aunty maijiddah musa ce hakimce a xaune tsabar karramawa wurinsu akaxo daukar order abincin da xa’a kawo masu..
Anci ansha an gyatse an gyagije ciki harda tulin kayan rabo da kowa yasamu don harda masu doubling don zalama..
Amarya Meenah an sha nasiha daga manya don dama abinda wushe din yake nupi kenan wato ‘Well done da sasanta kanku da kukai har aure ya had’a kunbar stage din Zairo(gauraye)...barka dashigowa beat3
(Besides the entertainment, wushe wushe is to tell the groom and the bride: wushe—meaning ‘well done’. Well done, for daring to get along; well done, for finally graduating from the zairo (bachelorhood) stage of adulthood and well done for becoming a man, a woman—real ones. In what is called beit3,)
Bayan an watse daga taro
cikin sauri aka tafi da Meenah xuwa sashen Ammi aka kara shiryata bayan tayi wani hadin wankan shigar alkyabba akai mata red,tayi bala’in kyau wajen mai martaba mai murabus aka kaita kamar yadda al’adar take yai mata fada sosai sannan aka kaita wajen Ammi daganan ba’a xame ko’ina ba se dankareran apartment din Meenan makekan gidan bene dayaji komai na rayuwa...
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO_*👌🏼
[4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```Edited by```:
```Ya hajja ce```
```nanahafsat.wordpress.com```
*72*
*M*eenah se goge hawayen dake kwararowa a face d’inta take tana jan majina wai yau itace aka kawota gidan mijinta a da tad’auka duk wasa ne se yanxun ta tabbatar aure ba wasa bane,sama sama takejin sallamar dasu aunty yaruwaiya ke mata sannu ahankali har kowa ya watse aka barta daga ita se akwatunan ra’aki da kususuram d’inta na al’ada..
Sarki Aliyu Hydar be samu barin apartment d’insa ba se gaf da shad’aya na dare ya saci jiki ya tafi b’angaren Meenah yana tura k’ofar Parlorn sanyayyan turaren wutar oud yadaki hancinsa lumshe ido yai ya bud’e tuni kasala ta davaibaye masa jiki a hankali yakebin stairs harya haura sama yabude d’akin dayake xaton Meenan na ciki bakinsa d’auke da sallama..
Tsayawa yai yanabin d’ajin da kallo komi purple and black ne k’arasa wa yai kan gadon yajanyo Meenan xuwa jikinsa k’ok’arin k’wacewa take yasake damkota yana sunsunar kamshin jikinta gaba d’aya khamsin khumrorin jikinta da wasu turarukhan dake tashi ajikin Meenan sun haddasawa Aliyun fitina..
Ahankali Meenan tai ta maxa ta b’anbare shi dakyar daga jikinta tana d’an dubansa ta gefan ido sanye yke cikin wata dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya datai mugun amsar jikinsa hannunsa daure da agogan azurfa sumar kansa tasha gyara se wani hasken angonci yake..
Xuba mata idanuwansa yai masu kama dana bacci yana sake narkar mata dasu a hankali cikin wata irin siga yace,
“Kinci abinci??”
“Uhm naci”tabashi amsa still kanta a k’asa don gaba d’aya a tsorace take,
“K’arya kike..”
“Allah naci,kobah yanxu ma cikina ciwo yake ba saboda over loaded”
Tsayawa yai yanabin jambakinta da kallo yadda take motsa bakinta gaba d’aya yakasa rik’e kansa cikin sauri yace,
“Ki..kij..kije ki alwala to”
“Bana sallah..”
Wani irin mummunan fad’uwar gaba aliyu yayi gaba d’aya seya nemi wani farin cikinsa na lokacin yarasa,
“What??”ya furta a dan tsawace da alama kilan be masan yayi ba
“Mensis..”tafad’a ahankali tana dan wasa da zoben hannunta..
"K'arya kikeyi Meenah I knw you fa."
Ya fad'a yana kallon cikin idanta, turo baki tayi kirjinta na bugawa ganin ya kafeta da ido tace,
“Toh wai anayin sallah a haka ne?!”
“Nop amma dai yanzu bada gaske kikeyi ba dan haka ki tashi ina jiranki.”
Kuma jan lafayyarta tayi ta rufe jikinta ya mike zaune sosai tare da cewa,
“Bari in duba ko da gaske kikeyi.”
Ai kuwa suka fara kokawa sabida k'arfin ba d'aya bane tuni ya makureta hararta yayi sannan yace,
“Meenah harkin fara min karya?toh zaki k'arb'i hukunci yanzun nan.”
Mik'ewa tayi cike da jin kunya ganin ya tab'a mata pant,har hard'ewa takeyi da lafayyan jikinta sannan ta shiga toilet ai kuwa tajima a ciki kamar bazata fitoba har ya fara tunanin ya bita sai kuma gata ta fito sai sunkuyar da kai take kai da kagani kasan batada gaskiya.shareta yayi shima ya shiga yayi alwalan sannan ya fito,sallaya ya shinfid'a musu sannan yajasu suka yi sallan Meenah dai duk kunya tayi mata yawa ji take tamkar ba itaba.
“Meenah tawa!”
Ya fad'a tayi mai banza kamar bataji ba,sake murmusawa yayi sannan ya mik'e cike da aji ya fita zuwa parlo,da kallo ta bishi harya fita sannan ta sauke wani uban numfashi tare da d'ora kanta gefen gado tanata tunani shagalin da akayi mutane cacim kamar baza'a rabu ba sai gashi an kawota an ajiye ba tare da an bar mata kowa ba tana ta tunani harya shigo hannuwanshi rik'e da katon tray ya k'arasa har kusa da ita nan da nan ta rufe idanuwa tamkar meyin bacci yana gani yasan karya takeyi yace mata,
“Ma'am tashi inyi feeding naki kinji?!”
Shiru babu amsa ya k'arasa ya zauna tare da janyo ta gaba d'aya jikinsa har sai da yaga ta warware sannan ya barta ya mik'a mata cup d'in fresh milk shima ya d'auki nashi, gaba d'ayan basu wani sha da yawa ba haka ma basu ci komai da ya had'o musu ba sannan Meenah ta haye gado ko kaya bata sauya ba.
“Oya tashi kisanya sleeping dress bana son a kwana da kaya.”
Tana cikin blanket ta zaro idanuwa kamar yana ganinta sannan ta kuma kudundinewa aikuwa ya kyaleta ya fita zuwa nashi bedroom d'in,be jima ba ya fito cikin nashi kayan baccin sai zuba k'amshi yake ya koma d'aki ya rufe tare dayin light off,Meenah najin haka ta kuma kankkamewa jikinta sai kyarma yakeyi sai kuma hawaye sharr domin tausayin kanta takeyi irin labarin da taji na ranar farkon kai amarya.
Kwanciya yayi ba tare da ya kulata ba bare yaje kusa da ita,sai da aka d'auki lokaci mai tsawo taji be kulata ba sannan ta kwantar da hankalinta bacci mai tattare da gajiya ya d'auketa.Shi kuwa saida ya bari dare ya tsala sannan ya fara lalubarta dan ya d'auki alkawarin ko auran dole akayi mishi to bazai bar d'inbin ladan dake cikin daran farkon shi,Meenah na bacci taji hannuwan shi a jikinta nan da nan ta rud'e hankalinta ya tashi cikin dabara da laluma tare da kashe ta da kalaman shi na Allah da annabi sunce da haka ya maida Meenah cikakkiyar mace sai dai tasha kuka kamar nata zai fita karshema korar shi tayi ba arziki ya koma d'akin shi cike da tunaninta.
Mahaifiyar Basma kuwa bayan k’afa ta dauke da sassafe sasashen mai martaba mai murabus tai hawaye kwance shab’e shab’e akan fuskarta ta fayyace masa kowacece ita kaidama abinda yakawota wajensa gyaran murya yai bayan yaji abinda ke tafe da ita,
“To Alhamdulillahi naji dadi kwarai da har maryamu tagano lefin tane takuma gyare kurakuren ta,wato axahirin gaskia banida abinda xance anan domin gaskia inason xaman maryamu atare da Aliyu,tunda har tagane komai ni Ina ganin komai ya wuce kuma shi kansa Aliyun na masa fada akan hukuncin daya xartar batare da shawartar muba sede ina ganin jin taba kinsa akan abinda ya yanke yafi tunda wuk’a da nama yana hannunsa..”
Yana gama magana ya tura sarkin gidah yayo masa iso wajen sarki Aliyu Hydar lokacin fitowar sa kenan daga sashensa shida dogaransa cikin sauri ya karasa sashen baban nasa yana shiga yaga mahaifiyar Basma gaysheda mahaifinsa nasa yai sannan ya gaysa mahaifiyar Basma fuskarsa cikeda murmushi kamar ba abinda ya faru..
Mai martaba mai murabus ne ya gyara xama ya fadawa sarki Aliyu Hydar abinda ke tafe da mahaifiyar Basma ya karkare xancen da,
“Kuma tace yarinyar tanata samun masoya masu son su aure ta,Yaya kake gani shin xaka sauwake mata tai aure ne tunda iddarta saura kwanaki nawa kikace ma hajia?!”
Mai martaba yace hakan yana duban mahaifiyar Basma,kanta a k’asa tace,
“Uku rankashi dad’i?!”
“To kaji saura kwana uku shine sukeson suji k’ak’a xaka maidota ne ko kuwa xaka sauwake mata domin tana ta samun wanda sukeso su aureta gashi da sauran igiyoyinka akanta..shine sukeson sanin madafa yanxun tabakinka”
Shiru sarki Aliyu Hydar yai tuno irin haukan son da Basma take masa taki kula kowa seshi,tuni ya lula duniyar tunanin rayuwar su ada shida ita kafin asata a gurbatacciyar hanya rayuwa ce suka yita me tsafta cikin so da shakuwa,muryar me martaba mai murabus ce ta fargar dashi daga tunanin daya tafi,
“Aliyu kayi shiru kai muke saurare saboda yau takeson ta juya kano da kwakkwarar magana guda d’aya”
Shiru Aliyu yai yarasa tacewa tabbas idan yarabu da Basma gaba d’aya beyi mata adalci ba domin babu wanda xe yarda lefin tane caxa’ai don ya auro Meenah ne ita yai waje da ita kuma made ai yana sonta domin ita yafara tsayawa ya fuskanta harya xamto ya aureta taxauna a matsayin matarsa Uwa Uwa son datake masa bai dace ace ya rabu da ita ba barin yanxun dayaji ance wasu suna sonta da aure seyaji gabaki d’aya yad’an ji ba dadi haryake tunanin shin wannan so ne ko kuma shakuwa?!
Abu na k’arshe babu wani sarki a tarihin masarautar da akace ya rabu ko yasaki matar sa saboda haka baxe so ace an fara hakan takan saba beside Meenah yarinyace yanzu take girma take sanin menene auren da yadda xata rik’e shi..beside yawan sakin auren bashida amfani shiyasa gashinan zawarawa sunyi yawa kullum cikin sakin aure ake..
Nannauyar ajiyar zuciya yasa ki a hankali yace,
“Baba nadawo da ita d’akinta na janye magana ta..”
Hamdalah umma da mai martaba mai murabus sukai cikeda jin dadi mai martaba mai murabus yace,
“Alhamdulillahi Allah ya maka albarka Aliyu domin kaidin adalin sarki ne..Naji dadi kwarai Dagaske da jin wannan hukunci naka ubangiji Allah ya maka albarka ya tayaka rikon mulkin nan naji dadi ba kad’an ba domin nikaina zab’in da na keso kenan har cikin zuciyata”
Cikin k’asa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 35