Share this page
rufe mata bakin wanda hakan yasa hankalin Meenah dawowa jikinta, cikin murgud'a baki take kallon Aysah tace; “Kinga ki bari ko,ba Ammi ta shiga tsakanin muba ina ruwanki da bakina kawai zaki zo ki rufemin?!” Aysah tace tana kokarin bud'e wardrop, “Gani nayi kinga miji harda sakin baki shi yasa nazo na rufe miki dan gudun kar sauro ya shiga.” “Ahh abinda yafi miji na gani ba mijin ba,Allah kina shigar min hanci da kudundine karki bari na fatoki dan ni girmanki baya bani tsoro kawai dan dai kar Ammi ta sake min fad'ane amma da kinga abinda zan miki.” Meenah ta fad'a tana harar Aysah, wajan mirror ta k'arasa dan dama powder take shafawa shine tajiyo dirar motoci taje ta leka, “Oh dai ni kinga tafiya ta sai kiyi da aljanu bani ba.” Aysah ta fad'a tare da turo mata bayan ta,jinjina kai Meenah tayi wallahi dama ta dad'e tana tara Aysah dan haka sai tayi fad'a da ita zataji dad'i, A parlor ya tarar da yareema Ngari sai faman murmushi yake mai da ka ganshi kasan yana cikin nishad'in ganin d'an uwan nashi, junan su suka rungume cikin tsantsar kauna a haka Ammi ta fito ganin su tayi manne da juna kafin tayi wani abun su Affy da Aysah sun rungume su baki d'ayan su hud'un ta saki lallausan murmushi wanda ya baiyanar da fararan hakoranta. K'arasawa tayi wajan tare da cewa; “Toh asamu guri a zauna mana wannan murna haka kamar an dad'e ba'a had'u ba.” Zama suka yi su duka suna dariya, kasan cewar idan yazo gidan nishad'i yake ji shi yasa ma har mantawa yake da cewar shid'in sarki ne,jiki yake warewa ayita hira dashi.Suna ta hira amma ko gilmawar Meenah babu,Ammi ce ta kula da hakan lokacin k'arfe 1:30pm anata kawo lunch ana ajiyewa ta kalli Affy tare da tambayar ta; “Affy ina Bitti..?!” Sai da kirjin Maimartaba Aliyu hydar ya buga jin sunan da Ammi ta fad'a, ya manta da sunan kwata-kwata nan da nan ya bi bakin Affy da kallo danjin abinda zata fad'a, wayar yareemah Ngari ce a hannunta tana kallon wani game tace. “Ammi tana d'aki d'azu da na duba bacci takeyi.” “Oya toh maza jeki kice nace tazo ina nemanta.” Da gudu Affy tayi upstairs tana kiran Meenah harta shiga cikin bedroom d'in, tashinta tayi tana yatsina ta bud'e idanuwa ganin Affy marainiyar wayon ta yasa tace, “Dalla kekuma meye na tashina ina bacci,yasin zan mareki.” Affy tayi saurin jan baya tare da cewa, “Toh ba Ammi ce ke kiranki ba.” Sakkowa tayi tabiyo ta da gudu suka fito parlon Affy ta cewa, "Ammi! Ammi!! Wayyo kinga wai saita dokini ko."tafad’a cikin hausarta da bata fita, Ganin wanda ke cikin parlon yasa Meenah saurin dakatawa tana hura hanci, Ammi ce tayi mata magana da cewa, “Zonan Aminatu.” A kusa da ita ta zauna tana turo baki tare da hararar inda Affy ke zaune Ammi tace, “Bitti baki ji zuwan yayanku bane shine kikak'i zuwa ki gaida shi?!” “Ina bacci nefa Ammi shine waccan marar kunyar taje tana duka na.” “Kai kai kai ni d'in ce na dukeki aunty Meenah? Ammi wallahi ban doketa ba cewa kawai nayi tazo injiki.” Affy ta fad'a jin Meenah zata yi mata sharri,Ammi ce ta harareta tare da cewa, “Ai gashi yanzu kin karyata ta,maza ki bata hakuri ai yanzu auntyn kuce gabaki d'ayan ku.” Kamar Affy zatayi kuka ganin ga mari ga tsinka jaka,a hankali tace. “Sorry aunty Meenah.” Shafa hancinta tayi sannan Meenah aka kad'a kai alamar an hakura,mik'ewa Maimartaba Aliyu hydar yayi zuwa bathroom dan yin alwala,yana fitowa ya tafi sallah, Ammi ce ta kalli Meena tare da fad'in, “Bitti eki sallah idan kinyi saikizo ki kaiwa yayanki abinci can dining room d'in baba.” Tsuke fuska tayi alamar ita fa gaskiya bata son zuwa inda yake, ganin hakan ne yasa Ammi yin murmushi tare da dagewa akan cewar ita zata kai dan so take yau su kulla juna saboda shariyar tayi yawa babu me neman wani a cikin su. “Ko bakiji niba bane Bitti?!” Ammi ta tambayeta cikin d'an d'aga murya,a razane Meenah tace, “Naji Ammi amma nida su Aysah ko zamuje kinga fa kayan da yawa?!” “Eh sai kuje da Affy.” Tashi tayi ta wuce room d'insu,bayan tayi sallar ma k’in tashi tayi sai da Ammi ta shigo tayi mata magana sannan ta fita,yana zaune kishingid'e hannunshi rik'e da phone yana ta faman kiran Modu amma yaki picking,sai da suka gama ajiye komai dama ya tambayi Affy tace sauran abu biyu su gama d'akkowa dan haka suna yin shigowa ta k'arshe yace, “Ke zonan.” Ba tare da ya kallesu ba Meenah tayi kokarin fita Affy tace, “Ni?!” Ya girgiza kai tace, “Aunty Meenah dake yake fa.” Zabgawa Affy harara tayi karaf suka had'a idanuwa yace mata, “I said come here...!” Ai tuni sai tsintar Meenah yayi a gaban shi sai faman tura mai baki take tana kunkuni,hannu ya d'agawa Affy alamar tayi tafiyar ta sannan ya maida kallon shi gurin Meenah wanda ke ta faman cizon kasan lips d'inta. A hankali ya mik'e tare da komawa kan kujera ya zauna, itama Meenah mik'ewa tayi tana binshi da kallo cike da takaicin shi. Kishingid’awa yai akan kujera mecin mutum uku yaxaro wayarsa yashiga dannawa ganin kamar yama manta da ita a tsaye yasanyata furta kalmar, “Latsi”ahankali tana wani yatsina fuska “Me kikace?!common Matso nan dak’ik’iya kawai” Yafurta yana nuna kusa dashi,girgiza kai tayi tasoma hawaye saboda tasan abinda yake shirin yi inmade yaci xalin gashinta kokuma ya shiga kissing d’inta wanda tad’au hakan ta ajiye amatsayin iskanci ashe d’an iskane tananan tana shirya ranar zata fito ta fad’awa Ammi cewar yaya Aliyu Hydar d’an iskane... “Baxaki matso ba sena taso na kwasheki da mari” Matsowa tashiga yi tana hawaye hannuwanta d’aure akan tulun gashinta dayasha shuku,se ynxu ya lura ashema ba d’ankwali akanta bayan uban warning din daya buga mata kwanaki akan lalle taxauna kullum kanta d’aure da d’ankwali ko hula,jikinta rawa yafarayi ganin irin kallon dayake watsa mata, Ganin tana b’ata masa lokaci yasanyashi tashi xe fincikota tai saurin dakatar dashi, “Dan Allah kayi hak’uri karka tab’ani wallahi bakyau” Sakin baki yayi wai yaushe yarinyar nan zatai hankaline?!gashi har zata shiga ss2 amma batasan menene aure ba siririn tsaki yasaki had’e da murtuke fuska taku d’aya biyu yai ya cafkota yaxaunar da ita a kusa dashi, Sleepy eyes d’insa yaxuba mata yana mata wani shegen kallo na ido cikin ido kasa kallonsa tai ta sadda kanta k’asa tana wasa da pattern d’in rigarta ajiyar zuciya yasauke kome yatuna oho ahankali cikin daddad’ar muryarsa yace, “Zubamun Abincin and feed me” Yana k’arasa fad’a ya lumshe idanuwansa kallonsa tai tana cuno baki k’atoto dashi zata bashi abinci abaki, “Latsi” Cewar Meenah had’e da tab’e baki “Kikace me?!”cewar Sarki Aliyu Hydar yana ware idanuwa...! ..... *ina kuke masoya makaranta littafin SON RAI KO ZAB’IN IYAYE?! Ina baku hak’uri da babbar murya narashin posting davanayi kwana biyu hakan yafaru ne sanadiyar clearing da chats dina sukai nayi typing har read more uku amma Wlhy nanemeshi narasa wayar tayi clearing chats dina tatass shiyasa seda nasakeyin wani tukun #Nagaisheku Nagaisheku Nagaisheku gaisuwa mai d’imbin fatan alkhairi💋❤....!* *_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER; MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` *```57```* *```shehuri```* *S*ai wajan k'arfe 10:00pm sannan maimartaba Aliyu hydar ya samu damar komawa apartment d'in shi,wanka ya fara yi sannan ya sanya kaya marasa nauyi,parlor ya koma yana jiran zuwan Modu dan yanzu suka gama waya yace mai gashi nan zuwa. Zaman jiran Modu yayi tayi bunu-bunu Basmah ta leko ta gani ko sunyi sun gama amma sai taga Aliyu hydar kad'ai a zaune yana duba wani d'an k'aramin littafi na addu'o'i *Fortress of the Muslim*, tana k'ok'arin fitowa taje wajan shi sai kuma taji muryar Modu a cikin parlorn ya shigo yana cewa, “Kan bala’in can, aure me gyara mutane, kai dama haka ka zama?Toh wallahi an gama dakai guy domin rawanin nan da ake sargafa ma b'oye maka komai yake yi kai zuki Masha Allah...” Modu ya fad'a yana k'arewa Aliyu hydar kallo domin gani yayi kyawunshi ya karu ga wata irin kamala data k'ara baibaye shi.Sarki Aliyu hydar ya shafa hab'arshi yana sakin wani kayataccen murmushi,zama ya gyara yana kallon Modu yace, “Kaga guy nifa ba surutu nace kayi min ba so nake ka gaya min ina ka tafi kayi min yaji...?!” “Guy naje neman aure ne kuma na samu.” “For real?!” “Eh mana dama ai na gaya maka bazan kuma ne manka ba sai na samo auran Kiara, toh baba ya yadda kuma insha Allahu soon zaku sha biki.” A mamakin ce sarki Aliyu hydar ya kalli Modu jin abinda ya fad'a, kallon shi yayi cikin sonjin k'arin baya ni Modu yayi dariya yana cewa, “Kayi mamaki ko? Toh ai ba abin mamaki bane domin Basmah da Kiara ba d'aya bane,ita Kiara dama a haka aka haifeta cikin addininsu,sab'anin Basmah da koyi takeyi da d'abi'unsu shi yasa kasamu matsala wajan neman auranta a wajan baba,ni kuma bayan soyayyar Kiara akwai jahadi tare da d'inbin lada mai yawa agurin Allah idan har ta musulinta sanadiyar auran mu.” Jin-jina kai kawai sarki Aliyu hydar yayi dan ba k'aramin mamaki yayi ba ta yadda maimartaba maimurabus ya amince da batun Kiara,sun dad'e suna hira har wajan 1:00am sannan Mudo yayi mai sallama ya tafi sai dai har suka gama hirar be gayawa Aliyu hydar cewa shima za'a had'ashi da wata ba dan ya tabbatar idan ya fad'a sai yayi mai dariya. Kwana biyu tsakanin maganar babagana da mahaifinsu yana jiran ya karajin an kirashi amma shiru,ganin baza'a kara nemanshi bane yasa shi yau ya shirya cikin wani tsadaddan yadi mai matukar kyau ya sanya direct ya wuce gidan su billy,cikin sa'a kuwa yana zuwa ya tarar da mahaifinta zai fita. Da sauri babagana cikin ladabin da baima san yana dashi ba ya fito daga mota ya k'arasa wajan shi tare da yi mai sallama, gaisawa suka yi cikin mutunci sannan babagana yace, “Baba dama magana nake so muyi.” “Toh toh shikenan mu k'arasa daga zaure ina tunanin hakan yayi aiko?!” “Eh baba yayi.” K'arasawa suka yi cikun zauran gidan sannan babagana ya kuma gaida mahaifin bilkisu har k'asa kafin ya fara magana; “Baba dama nine wanda yake son auran bilkisu, dan Allah baba ka amince min inasonta nayi alkawarin rik'e maka ita da gaskiya da rikon amana, zan iya auranta a yadda take baba sannan zan nema mata magani aduk inda yake baba amincewarka nake so, domin mahaifina yace sai kun yadda tukunna” Kafin Abban billy yayi magana sai ga su billy da kanwarta zasu fita, tsayawa billy tayi kurum tana kallan yareemah babagana ko kiftawa bata yi, gaban shine ya fad'i a tunanin shi ko tona mai asiri zata yi dan shi besan hajja gajirim tasa an gusar da hankalinta akan shi ba. Saurin sunkuyar da kai yayi k'asa yayin da kirjinshi ke bugawa tsoran shi d'aya karta fallasa abunda yayi mata gashi yanxu an kara zazzaga mishi wutar kaunarta,lallai billy the magnificent domin har wani sauk'in ta yak'e ji cikin magudanar jinin shi. Abba ne ya kalleta tare da yin murmushi yana shafa kanta yace, “Bilkisu ko kin sanshi kike ta faman kallonshi keda ko had'a idanu da namiji bakya yi?!” Bata yi magana ba tana ta kallon yareemah babagana,ganin haka yasa abba cewa, “Zainab ina zakuje?!” Ya tambayi k’aramar wadda suke tare da bilkisun,ledar hannunta ta nuna mai tana cewa, “Abba Umma ce tace muje mu kaiwa yakaka kubewa ce.” Kai kurum ya jin-jina sannan yace, “Toh bilkisu zo ku tafi aikenku kuyi sauri Ku dawo duk wanda ya kiraku karkuje Ku tafi.” Fita suka yi amma duk da haka billy bata dena waigen yareemah babagana ba,ganin sun kule yasa shi sauke wata katuwar ajiyar zuciya sannan suka ci gaba da magana. Abban billy yace, “Toh yareemah naji bayaninka amma ka bari zanje can fadar dan muyi magana nida mahaifinnaka insha Allah komai zaizo da sauk'i” Jin haka yasa babagana zura hannu cikin aljijun wandon shi ya zaro kud'i wanda bemason adadinsu ba ya mikawa abban billy sai godiya yake abinda be tab'a yi ba kyauta da godiya,nan abban billy yace a'a bazai karbi ko kwandala ba amma yareemah babagana ya ajiye mishi ya fita da Sauri yana jin farin ciki.Ba yadda mahaifin billy yayi hakan nan ya d'auki kudin yaje yana bawa matar shi labarin yadda aka yi,itama addu'a tayi tare da cewa idan da alkairi Allah ya had'a idan babu Allah ya had'a kowa da rabansa. Sati d'aya wani lokaci Basmah ta shirya cikin shiga ta alfarma,lokacin sarki Aliyu hydar na fada ita kuma ta aika aiyi mata iso wajan maimartaba mai murabus cewar zata zo tana san magana dashi, bayan an sanar mai yace toh yana sauraran zuwan nata,cikin ladabi ta shiga sitting room d'in nashi yana kishin gid'e jikin wani tum-tum babu kowa sai shi ta samu waje ta zauna kanta a k'asa jin sunan da yakirata dashi tace, “Sannu baba barka da rana anyini lafiya?!” “Lafiya lau Maryamu ince dai lafiya lau kuke ko babu wata matsala ko?!” “Lafiya lau baba dama akan Muhammad ne wato Modu,baba akwai wata friend d'ina da suka dad'e tare dan tunkafin musan shida maimartaba 'yan uwane suke tare, toh kuma baba ta riga ta fad'a a gida tana da wanda take so wato shi sai yanzu kuma katsam ya fara nuna mata cewar shi yanzu kamar dai so yake su rabu kuma sunfi 3years suna tare shine nace to bari zan gaya maka inyaso sai aji inda matsalar take.” Mamaki ya kama maimartaba maimurabus zama yayi sosai yana kallon Basmah yace, “Ya sunan yarinyar?!” Basmah cikin zakuwa tace, “Sunanta layla baba.” “Ashsha ashsha kenan dai idan na fahimta ya yaudareta kenan ko? Dan ni yazo ya sanar min da cewa yana son auran wata yarinya sunanta Kiara amma ba muslma bace, yanzu haka ma na tura mutum biyu sun had'u da can kawunsu na yola Mai Alooma Ghaji dan suyi bincike daga nan sai a fara shirya-shiryan aure Ashe yana can ya yaudari yarinyar mutane,Shikenan Maryamu tashi kije zan yi magana dashi Mudon dan naji daga inda matsalar take.” A hankali Basmah ta tashi tana yiwa maimartaba maimurabus godiya sannan tayi mai sallama ta fita,tana fita ta kira layla akan cewar tayi addu'a ta kwantar da hankalinta.Shi kuwa maimartaba maimurabus waya ya d'auka ya kira Mudo, ba b'ata lokaci sai gashi fuskar nan wasai cike da farin ciki ya kalleshi bayan ya zauna baban yace, “Mommodu wacece kuma layla....?!” Daram zuciyar Modu ta harba da k'arfi cikin razani ya kalli baban yana kwalalo idanuwa,baba na ganin haka ya gazgata maganar Basmah dan haka ya gyara zama danjin ta bakin Modu wanda keta faman soshe-soshe. “Ina jinka kayi shiru.” Cikin rashin gaskiya Modu yace, “Baba ex girlfriend d'inta ce ita.” Murmushi ne ya kwacewa maimartaba cikin murmushin ya maimata Kalmar a fili, “Ex girlfriend Mommodu?Saboda ka samu Kiara shine zaka barta ko kuma dai wani abun tayi maka?!” “Wallahi baba d'abi'unta ne basu yi min ba,akan idona na ganta da wani arne suna rawa agaban mutane kuma.” “Shine dalilin da yasa ka dena sonta?!” “Eh baba."” Murmushi Maimartaba yayi sannan yace, “Toh idan banda abinka ai da sai kayi k’ok’arin tsamota daga inda take k’ok’arin fad'awa, tunda dai da kana sonta toh yanzu ma ka daure ka cika ladanka itama ka aureta dan kar a barta ta shiga wani halin, kaga barinta da zakayi bamusan kuma abinda zata fad'a ba kayi jahadi ka dad'a da ita kaga kanada d'inbin lada a gurin Allah,kaga dai itama Basmah tunda aka aureta dawa ka tab'a ganinta? Babu sai dai mijinta toh kaima kayi jahadi zanyi bincike akanta idan har an dace toh inason ta zama wadda itace *ZAB'IN MU* da muka yi maka tunda kaima an baka *SON RANKA* ko ba haka ba Mommodu?!” Tunda maimartaba ya fara magana komai na d'aukar magana dake jikin Modu sai da ya tsaya dan haka beji karshen maganar ba sai jikin shi dake faman rawa tamkar wanda shocking ya Kama. “Tashi ka tafi Allah yayi muku albarka,insha Allah bikin bazai wuce one month ba za'a had'aku da kai da babagana dan shima munyi magana da mahaifin yarinyar.” Tashi yayi yabar gurin ko ganin gaban shi bayayi har ya bigi falmata be kulaba sai jin tsakinta yaji, apartment d'in su na Aliyu hydar ada nan ne yake a matsayin inda Modu ke zaune dan haka can ya nufa zuciyar shi na zafi yana tunanin yadda aka yi har baban yasan tsakanin shi da layla. Bayan 'yan binciken London sun dawo ne aka kuma tafi gidan su layla, itakam an samu matsala dan iyayanta basu yadda ba sunce bazasu had'a yarsu kishi da wadda ba musulma ba, ganin yadda laylan ke kuka harda su suma yasa suka amince ba yadda zasu yi a gurin itama aka biya kud'in nagani inaso aka tsaida biki one month dukan su. Hajja gajirim kuwa hauka takusa yi jin cewar an samowa yareemah babagana auran bilksu, tsine tsine ta dinga yi harda wad'anda sukaje nemo auran babu wanda besha zagi ba, shi kuwa yareemah babagana yana wajan parking lot taje ta shak'i wuyan shi wai wallahi sai yace ya fasa ya rasa wadda zai aura sai 'yar matsiyata wadda ta gama gararanba a titi, ya kalleta yana kecewa da wata shegiyar dariya yace, “Mami lokacin da zaki auri baba shi yace yana sonki ko kuma kece kika ce kina so dan ni sai naga kamar baki son meye so ba?!” “Ubanka nace ubanka babagana ni kake gayawa haka,shegen yaro kawai ban sani ba.” “Toh sakar min rigata, kuma wallahi tallahi Mami idan kika ja aka hanani auran my billy sai na tona muku asiri duk abinda kukeyi tundaga kan baa Ngari har zuwa kan abubuwan da kukewa Basmah akan Aliyu hydar sai na fad'a kuma kinsan makomar a gurin baba,ga saki ga zaman gidan yari” Sakin shi tayi da sauri tana kallonshi tare da waigawa ko zataga wani,ganin babu kowa yasa ta kalleshi cikin takaici tace, “Wallahi da haihuwarka k'ara b'arinka,duk dan kai nake wannan wahalar amma dai-dai da rana d'aya baka tab'a faranta min raina ba banza kawai” Tana kaiwa nan ta juya cikin tashin hankali,bin bayanta yayi da dariya harda buga kafa yana cewa, “Haka kurum inason yarinya har sonta yana neman halakani sannan ki wani ce ba itaba,ai nasan bokan naku wallahi naje naci ubansa sai naga wa zaku Kama.” Rigar jikinshi ya kalla nan yaga duk tayi wani iri dan haka ya koma side dinshi ya sake kaya yafita shan iskah hankali kwance.... Cikin sauri Hajja gajiram ta k’arasa sashen hajja yakolo ko xama bataiba tafara xayyanewa hajja yakolo duk abinda ake ciki da yadda suka kaya da babagana tak’arashe xancen had’e da xabga uban tagumi... Ajiyar zuciya hajja yakolo tasauke, “Yayya inaga lokacin da xa’a bawa Basma hayak’innan tafarayi yaxo” “Ko?!” “Allah yayya abinda xa’ai kenan kinga seyanda kikai dashi tunda shi babagana yafara fand’arewa gwara mukama dahir inyaso ko takansa se abi afara soke duk wasu abubuwan dasuke neman kawo mana cikas ciki harda hajjagana” “Wannan abu yayi yakolo tabbas bankawo wannan hayak’inba seyanxu dakika tunamin dashi yananan a ma’ajiya me kyau xan d’akko shi to tayaya xaki gayamata kafin ta harvo jirginmu?!” “Wannan duk me sauk’ine yayyya kede kifata kawai aikinmu yaci amma danta wannan sakaryar kima dena damun kanki domin shashasha ce ta ajin k’arshe nagaya miki fa gaba d’aya bata tunani inde akan abinda yashafi kayan matane komai d’urmawa cikinta take shegiya Allah yasa tasha abinda xe karta” Tak’arashe xancen tana daria,dariar itama hajja gajiram tasa se b’abb’akata suke ba k’akk’autawa dakyar suka tsagaita sannan suka shiga shrya yadda xasu kamo bakin xaran don cinma manufarsu akan sarki Aliyu Hydar.... *```DAMBOA ROAD```* Zaune suke dukkansu kowa da d’an aikin dayake tab’awa anata hidimar shirya kayan Aysaa a akwatuna xata tafi k’asar England don yin karatun bachelorette degree akan international law.. Gefe d’aya kuma Meenah ce hakimce akan sofa sewani faman yatsina fuska take tana shan kunun mard’om wanda da alama tilasta mata akai seta shashi,Aunty yaruwaiya dake gefe tad’anyi murmushi, “Oh ni ruk’ayya kinga idan bakyasha bani na kwankwad’e shi tass” Ta k’arasa magana tana mik’awa Meenah hannu alamar tabata,hararar wasa Ammi tajefa mata, “Uhm uhm yaruwaiya karki xama babbar kwabo mana,kyaleni da ita dole setashanye kununnan” “Kai yakaka ki kyaleta mana”Cewar yaruwaiya.. “A’a wallahi ita kenan baxata saba da abin al’adar taba?!Haba aibaxe yiwuba” Cuno baki Meenah tai tana wani yatsina fuska kamar xatai kuka tace, “Kobah nasha dayawa ba Allah Ammi nikam ya isheni haka” Ammi bata tankaba sesu Aysaa dake daria k’asa k’asa kallo d’aya aunt yaruwaiya tai masu sukai tsit.. “Yanzu ajinki nawane Aminatu?!”Aunt yaruwaiya ta tambayi Meenah “Ss2 nake Aunty”cewar Meenah “Art ko science?” “Science nakeyi” “Okay to allah yatemaka” “Amin”cewar Meenah “Yakaka itama makarantar su Aysan xata tafi inta gama?!” “Oh rufamin asiri yaruwaiya wacce makaranta kuma?yanxuma Allah Allah nake tak’arasa na dank’awa mijinta ita” Ammi tak’arasa fad’a tana jinjina kai,zumburo baki Meenah tai gaba tana bubbuga k’afa, “Ni ni Ammi ba inda xani agurinki xan xauna gaskia” Daria Aunt yaruwaiya tasa ita kuma Ammi tamik’e tai sashen baa Ngari da sauri don baxata iya da shagwabar Meenah ba don yanzu seta sata magana ta gaira babu dalili... ```WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO```👌🏼 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE* 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 _*Home of expert and perfect writers_* DEVOTED TO: *XARAH BUKHAR* nanahafsat.wordpress.com CONGRATULATIONS MY ADORABLE BITTI(FEEDHOM)AND MY BELOVED YA HAJJACE FOR THE SUCCESSFUL COMPLETION OF YOUR EDUCATIVE NOVEL *ABINDA KE B’OYE* THANK YOU SO MUCH FOR THE DEVOTION.I FEEL LOVED,MORE GREASE TO UR ELBOWS,LOVE AND ENDLESS AMOUNTS OF BLESSINGS❤❤❤ *56* *layla* kam da kuka tabar wajan hankalinta a matuk’ar tashe dan alamun da Modu yayi mata sun tabbatar mata da cewar baya sonta yanzu ba kuma zai aureta ba haka yanayin shi suka nuna ita kam ta shiga uku ya zatayi da d'inbin soyayyar da take yi mai ina zata saka duk wata kulawa da tarairaya datake ta faman b'oyeta a cikin zuciyarta. Uban tagumin da tayi ne yasa duk wanda yazo wucewa ta gurin da ta rakube sai ya gane cewar bata cikin tunaninta, kamar daga sama taji phone ringing d'inta tayi saurin zaro ta a tunaninta ko shine ya bugo yace mata da wasa yake sai taga sunan Basmah ya bayyana jikin screen d'in, kwallar ta goge sannan tayi picking tasa a kunne ba tare da tayi magana ba. “yan mata wai ina kika shige ne?!” Taji muryar Basmah na tambayarta,k’ok’arin magana laylan tayi amma ta kasa sai kuka daya k’wace mata mai sosa zuciya,cikin kid'ima da tashin hankali Basmah ke tambayar ta, “Lafiya naji kina kuka, kuna ina?!” “Basmah oud ne oud ne Basmah ya k'aremin tatas saboda ya dena sona ya gama yayi na k’arshe ma cemin yayi ina yawo tsirara...” “What..?!” Basmah ta fad'a cikin tashin hankali ita kuwa layla sai k’ara sakin kukan take yi nan ta sanar mata da duk abinda ya faru cikin mamaki Basmah ta bata hak’uri tare da yi maga alk’awari mai girman gaske daga nan suka kashe wayan kowa da abinda yake sak'awa. Shikwa Modu bayan yakoma wajen ma’aruf sallama kawai yayi masa yahau flight yakoma bornu kasancewar yayanke shawarar gwara yagayawa mai martaba mai murabus wacce yake muradin ya aura domin wata d’ayan daya yanka masa yayi shima kuma mai martaban Alhamdulillah anyi masa dialysis yanxu transplant d’in kawai xa’a masa wanda xe koma bayan watanni takwas... <><><> *Shehuri* *M*aimartaba sarki mai murabus ya aika manyan mutanan shi dan binciko mishi wacece Bilkisu, mutum uku ne suka tafi bayan yareemah babagana ya basu address d'in gidan.Koda suka je baban bilkisu suka nema nan aka shigar dasu cikin gidan duk suka zauna a parlorn matar kasan cewar babu wani guri da za'a iya ajiye bak'i sai nan kuma yaga daga gidan sarauta suke har ma sunyi mai k'arin haske akan cewar sarki maimurabus ne ya turosu. Bayan gaishe-gaishe ne d'aya daga cikin 'yan aiken ya kalli mahaifin billy yana cewa, “Maimartaba maimurabus yana nemarwa d'anshi yareemah babagana auran 'yarka bilkisu,yana neman amincewar ku da kuma na yarinyar domin shi yareemah

Chapter 16 of 35