godiya take zabgawa nan yasa driver d'inshi yace ya kaita gidan su,ko apartment d'insu bata kallaba bare asa ran zata shiga...
*ADAMAWA YOLA*
Meenah ce xaune gabanta babban bowl ne dake cike da kayan marmari wato fruits hannunta kuwa d’auke yake da plate d’an karami cikinsa kuwa ba komai bane fyace ruwan markad’adden tumatir (blended tomato)da madara olden burger data had’asu xata goge fuskarta da auduga(cotton wool)Sosai tayi fresh kamar katsage jikinta jini yafito don laushi,jikinta se kyallin haske yake sosai natural colour d’inta yasake haskawa,tayi b’ul b’ul da ita y’ar ramarnan duk tatafi don sosai yanxun jikinta yake murmurewa...
Gid’ad’o ne yaxauna akusada ita akujerar datake me cin mutum uku dubarta yake yana faman yatsina fuska,
“Lapia kike goga tumatir a face naki?”
“Gid’ad’o kenan me kakeso nasa?!”
“No I just asked ai..Nagade tumatir amfaninshi ai a abinci ne ko?! Nd your scrubbing it on your face”
“Kai gid’ado Kai kam matarka tashiga uku da tambaya to tumatir amfaninsa base a abinci ba kawai kana jina??”
“Uhm”kawai yace badon ya yardaba..
“Wannan tumatir da madarar daka ga ina hadawa xan goge face d’ina dashi amfani da gyaren dayake a face din mutum yafi amfanin mai creme ko lotion me tsada saboda yana cire dabbara dabbara na fuska (patches)yana cire pimples kuraje,yana cire gishirin hanci da spots kai abubuwa da dama de ga gyara face dayake tai kyau tai fresh tai smooth kaman na baby..”
“Dagaske?! Aiko xan gayawa my zee”
Y’ar daria Meenah tai,
“Allah sarki zee jia kwa taxo takarba dangashou bakanan tacemun xataje bornun itama..To komade menene kace mata idan ta saka ba’a magana harse ya bushe for life 15mins seta wanke da ruwa me d’an dumi tagoge face din da towel ko wani abu tsaftacacce..”
“Okay xanfada mata..”
“To ya school yau bakaje ba?!”
“Kai ai Apti tana rola ni nayi shawara da Baffa ai hostel kawai xan koma saboda kullum sena makara...”
“Eh gaskia yamafi kam..”
Gyada kai gidado yai hade da mikewa daga xaunen dayake hannuwansa xube cikin aljihun wandon sa haryakai kofa yadawo ba makawa Meenah kawai taji sakin rankwashi akanta gashi badamar tai magana taruga tagama shafawa..jaddada kai tayi alamar bashi yad’auka ,a dari yafice yana mata daria ..
Da dare Meenah na hakimce a parlorn aunty yafendo wayarta tahau ruri ganin aunty maijiddah ce wato mahaifiyar ta yasa tai hanxarin dauka ta kara a kunne,
“Kixo yanzu Ina nemanki..”
“Toh yayya..”cewar Meenah sannan tai hanxarin ficewa xuwa sashen yayyan gabanta kuwa se dukan uku uku yake na Allah yasa ba wani lefin tai ba..
Tana shiga ta taradda Aunty yafendo anan k’arasa wa tai daga gefansu ta xauna bayan ta kwashi gaisuwa aunty yafendo ce tafara magana,
“Amiinatu..”
Dago kanta Meenan tai jin sunan da aunty yafendon takira ta dashi ahankali ta amsa,
“Na’am aunty..”
“Magana zamuyi dake muhimmiya wadda xaki ajiye hankalin ki waje d’aya ki sauraremu kina jina?!”
“Eh!aunty..”
Sosai aunty yafendon tashiga jan kunnen Meenah kan rayuwar gidan aure tana dasa aya aunty maijiddah ta dauka sosai itama tai mata nasiha me shiga jiki Meenah se kuka take abun tausayi ita kanta aunty yafendon sedatai hawaye itade aunty maijiddah batai kukan bade amma daka ganta kasan dakiya ce kawai..
Bayan sungamai mata fad’an ne hade da jan kunne sukace kuma taje daki yaya gumsu tana jiranta itama xatai magana da ita gaban Meenah se fad’uwa yake sanin yaya gumsun mafadaciya ce tun dama can jininsu bexo d’aya ba don abu kalilan xatai gumsun xata rufeta da fad’a don bata d’aukar nonsense..
Shiga d’akintai bakinta d’auke da sallama xaune ta hango ya gumsun abakin gado tana danna waya ganin Meenan yasa ta ajiye tana murmushi kamar ba ita ba..
“Meeno no..”
“Uhum ya gumsu”sannan ta gaisheta..
“Sannu Meeno su walididi nata kuka sesun biyoni sunxo naki yadda”
“Laa Meyasa?!”
“Wallahi kawai.. k’ara’ina xanyi inci kwalliya ta na gwangwaje a shagalin bikin nan inkwa dasu na taho ai ban isa nai hakan ba..”
“Banji dadi ba”cewar Meenah
“Saxo daga baya May be ko ranar daba event haka”
“Okay allah yakymu”
“Ameen Meenah..magana xamuyi dake kingade ke yanzu ba yarinya bace kamar da,yanxun da aure a kanki kome xakiyi kisani seda amincewar Aliyu wani shirme da sokonci dakike kullum inaso ki ajiye ayau ya kare kafin mukai ki bornu kina jina?!l”
Cikin sauri Meenah tace
“Eh yaya”
“Toh..Yanzu xan danja hankalinki akan yadda ya kamata ki dinga tarairayar Aliyu ta siga davan davan kamar;kissa,jan hankali da kuma ladabi da biyayya kowanne xan daukeshi d’aya bayan d’aya namiki bayani akansa,
“Kisani dukkan xamantakewar rayuwar aure ba xata yiwuba saida kissa,idan akace miki kissa ta kunshi abubuwa da yawa,kissa ta kasu kashi biyu akwai kissa marar kyau akwai kuma kissa me kyau,mara kyau itace ta shirye tuggu da makirci da sihiri xakiga kishiya ta kullawa kishiyarta sharri ko idan ta daidaici tagama girki taje ta tsuga mata gishiri ko yaji ko kananzir ko kuma tai k’ok’arin fitar da ita daga gidan ma gaba d’aya,xakiga mace ta shiga tsakanin d’an mijinta da mijin,
“Ta cikin dabara ko mace tashiga tsakanin mijinta da iyayensa da makamantansu wannan kissa mara kyau sede muce tur da ita.Allah ka ganar da masu irin wannan kissa..
“Amma kissa mai kyau itace kulawa da mai gidah da tarairayarsa kamar Kwai wanda daga ciki akwai,
“Kissar magana,kissar tafiya,kissar kwalliya,kissar abinci,kissar tsafta,kissar kallo mind you ba kallon film ba sarai nasan halinki da gab’unta to kallon miji nake nupi yawwa se kissar shagwaba da kissar kwanciya se kissar kula da jikin mai gidah suma xan d’auki kowanne nai miki bayani akansa Ina fatan kina ganewa?!”
Cikin k’asa da kai Meenah tace,
“Eh ya gumsu”
“ *Kissar magana* idan xakiyi magana da mijinki ki kasance cikin nutsuwa da tauna magana da xaki gaya masa kafin ki fadeta don gudun gaya masa maganar da baxai ji dadinta ba ko bata masa rai,
“Ki dinga magana cikin sigar hankali karki dinga bud’e masa muryarki kala kala wani lokacin ki maketa wani lokacin ki dan budeta wani lokacin ki dinga yi a hankali kamar bakyason magana,wataran kuma idan kinason gaya masa magana mai dadi ko ta soyayya kice saiya baki kunnensa xaki rada masa.Se kissar mu ta gaba,
“ *Kissar tafiya* idan xakiyi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko yana kallonki daga inda yake ki dinga tafiyar da xata dauke masa hankalinki xuwa gareki misali ki dinga tafiya a hankali kamar bakyason taka k’asa wani lokacin ki dinga tafiya kina karairaya kina dan jujjuya jikinki wani lokacin kuma sauri sauri xaki dingayi kina juya maxaunanki idan ta gaba yake kallon ki kisan yadda xaki dan dinga girgiza kirjinki cikin hikima bata sigar da xai gane ba,amma fa meenah mijinki kad’ai xaki dinga yiwa wannan kala kalar tafiyar cux kikaiwa wani xaki dau zunubi ne”
Cigaba da koyamata kissoshi tadingayi kama daga kissar kwalliya da kissar abinci kissar tsafta da kuma kissar kallo ciki harda kissar shagwaba data kwanciya wanda sosai ya gumsun taja kunnen Meenan akan kissar kwanciya ta kar kare mata da yadda xatai kissar kula da jikin mai gidah..
“Hope kingane?!”
“Nagane ya gumsu”cewar Meenah datai wiki wiki da idanuwa wai yau ya gumsu ce take hira da ita hirar ma ta manya duk kunya ta davaibayetaa
“Yawwa to se dan karin jan hankali daxan miki wanda idan kika dumfafi yinsa tabbas xaki xamo shalele awurin mijinki yaxamto ba wacce yakeso da gani se ke hanyoyin jan hankalin sune,
“Kula da duk wani abu da mijinki yafi so,ki kula sosai da duk wani abun da bayaso ki lura da abinda yake damunsa da hanyar da xaki kula da iyayensa da danginsa da yadda xaki xauna lafiya da kishiyarki babu ruwanki da wani kishi na banxa da wofi wanda xe kaiki ga hypertension,kishi dole ne ba ace karki ba amma akwai irin kishin da akeyi bana yanxu da yaxama na hauka ba,kede babu ruwanki don baki taso kinga anayi a gidan ku ba ga aunty nan da yayya kamar ya da kanwa haka suke abun sha’awa ba’a taba jin kansu ba ina fatan kina ganewa?!”
Kad’a kai Meenah tai tana wasa da yatsun hannunta cikeda nutsuwa ya gumsu ta cigaba da yi wa Meenah jan hankali akan rayuwar gidan miji ta k’ark’are da,
“Abu na k’arshe shine ladabi da biyayya,babbar magana kenan domin duk abubuwan dana fada abaya idan ba ladabi da biyayya yaxama na banxa don duk iya tafiyar ki ko iya farinki idan bakya yiwa miji biyayya meye amfaninsa?!Misali kinyi kwalliyar jan hankali kinyi masa kalar girkin dayake so jira kike ya dawo yaga kwalliya,
“Yaci abincin da kika tanadar masa amma yashigo ba sannu da xuwa ba karbar kayan hannunsa saidai ki bishi ki dire masa abincin da kika yi masa tana iya yiwuwa ma alokacin ki fara masa k’arar kishiya ko kudi da makamantansu toh tell me tayaya zaiga kyan kwalliyar sannan kuma yaji dadin abincin?!,
“Ko kiga wasu matan miji na magana suna yi suna fada sosai fad’i in fada bai dace ba sam kamata yai idan mai gidah yana fadansa kiyi masa shiru idan yagama sai ki bashi hak’uri idan kuma ke aka batawa baxaki iya bada hak’urin ba tunda ranki yakai kololuwa a baci to kiyi shiru kawai kuma ko menene yace kiyi masa koda kuwa ran naki a bace yake don kansa shima xe sakko ku shrya,
“Wasu kuma matan xaki ga suna yawan korafi akan maxajen su don abinda ba abin fada ba sai su rufe su da fada wasu ma kawai xakiga sun fice daga harkar matan kwata kwata inkinga sun kusancesu to sede idan rabo ya tsinke yawanci kuma xakiga akan maganar da mukai d’axu ne akan rashin gamsuwa damu da maxajen mu ba sayi xakiga mace har mace,
“Kamar ita tai kanta don kyau sai kiga sun had’a kishi da wadda bata kaitan ba harma xata xamto itace mai fada aji gurin mijin xakiga yana Allah Allah girki ya xagayo kanta don yafi gamsuwa da ita xakiga wasu matan suna yawan tambaya to meyasa wata macen ake gamsuwa da ita wata ba’ayi?!,
“Ba komai bane yake kawo haka kisani sai kowa da irin ni’imar da Allah yai masa misali kowanne jinsin halitta akwai maza akwai mata kuma both ana samun farare da bak’ake dogaye da gajeru mai kib’a da siriri ke kowanne abu dake jinsin bil adama xaki ga nawani yafi nawani to haka ma ni’ima take ajikin mata da maxan wata macen tanada ni’ima sosai bata buk’atar kari wata kuma tsaka tsaki ce wata ma bata da ita se d’an abunda ba’a rasa ba,
“Don haka Ameenatu kisani kamar masu bukatar karin jini da ake cewa ga abubuwan daya kamata suci haka ma matan masu neman k’arin ni’ima ajikin su akwai abinda yakamata suci domin ance idan kanada kyau to kadad’a da wanka,sai dai wasu matan suna amfani da magunguna barkatai wanda wasu ma basusan komeye ba sudai suci susha buk’atar su ta biya kawai shikenan,
“Wanda xakiga yin hakan xakiga yana haifar da cututtuka barkatai ga mata,shawara ta dake Aminatu karki xamto cikin irin wa’innan matan masu bankawa cikinsu kowane magani suka ji ance yanayi aa sam karki soma kowaye yakawo ko yaxo maki dashi karki soma amfani dashi kinji de na gargadeki domin hakan yana haifar da toshewar mahaifa,hana haihuwa ko canxawa yaro kamanni kamar wata k’awata sumayya matar ma’aruf wallahi abinda yafaru da ita kenan,
“Tahaifo yaro marar cikar halitta abun tausayi saboda ita komai cusawa take ta bankashi a baki duk bamu sani ba se bayan da xata haihu a asibiti dr tace har cancer magungunan suke sawa dakyar aka mata cs don kasa haihuwan tayi abu nabiyu ga kaikayin gaba wato infection,
“Da kurajen gaba plus ciwon ciki ke da abubuwa da dama de kede ki lazimci shan fruits kamar yadda kikaga ana saki sha anan su kankana gwanda,ayaba,guava,lemo,tumatir,rake,aya,kwakwa,dafaffiyar gyada xuma,nono,madara,madaran shanu gurji cukwi,zogale da ruman da inibi se tuffa da kuma xaitun kina ganewa kuwa?!”
Nodding kanta kawai Meenah tai gaba d’aya jikinta yayi sanyi se yanzu tasan tabbas aure aka mata batare da ya gumsu tadamu da damuwar da Meenah tashiga ba tacigaba da maganar ta,
“Se abu na k’arshe naga dare yayi wato addua kirik’e addua Aminatu wallahi addua makarin mumini ce ke duk wanda ya lazimci addua wallahi baxe taba tabewa ba azkhr dinnan kidinga yawaita yinsu nataho maki ma da wasu littafin du’as din suma ki rik’esu gidanki kullum yaxamto cikin karatun qur’ani musanman suratul baqra domin duk gidan da ba’ayinta ance kamar kango yake,
“Ki yawaita yin addu’oi na neman tsari ga korar shaid’an ya kuntata masu ya karyasu ke dama mutane ma sharranta masu nufarku da sharri addu’a tana jawo yardar allah ta’ala,suna gusar da bakin ciki da bacin rai a zuciya,suna janyowa zuciya farin ciki da nishadi,suna karfafa zuciya da jiki,suna jawo arziki suna kara imani da tawakkul da sabr ke sunasa komai na mutum ya daidata ya samu peace of mind ki kama allah Aminatu kirike addua da qur’ani Insha Allah rabbi xaki bani labari,anan xan tsaya seki fad’i tambayoyin ki karkiji kunyata Ameenatu ko tsoro saki jikinki ki fad’amun abinda baki gane ba.”
Shiru Meenah tai tana k’as k’as da yatsun hannunta kunya dukta isheta jin shirun yayi yawa ne yasa ya gumsu sake tambayrta,
“Uhum Meenah ina jinki”
“Ba..Babu komai ya gumsu duk nagode JazakillAhu khairan”
“Ameen..To shikenan dukde abunda baki gane ba ko kikeda karin bayani akai seki kirani awaya yawwa nasanki dama ke sarkin kamshi ce amma ki kara xage damtse khumras dinnan na wanka dana wanki da jiki dana moping duk fa kidage wajen amfani dasu kingade garin kamshi xa’a kaiki dangin kamshi ki sake kaimi da sauran turarukhan jiki dana tsugunno dana kaya dana gidah du kolakcas dinnan duka kiyi amfani dasu,
“Idan sun kare kiyi waya ayo miki wasu koki had’a da kanki irin kamshin da kikeso aikin iya ko?!”
“Eh ya gumsu”
“To shikenan allah ya miki albarka kije ki kwanta da safe kamun mu tafi xan kara miki wani dan jan kunnen,Allah ya tashemu lapia kije nasan aunty na jiranki”
Mikewa Meenah tai hade da sake yiwa ya gumsu godia sannan tafice suka koma sa shensu itada aunty yafendo bayan sunyiwa aunty maijiddah sai da safe,dakyar Meenah tai bacci ta jima tana juyi akan gado banda hud’ubobin su ya gumsu ba abinda ke mata yawo akai wasu siraran hawaye ne suka xubo mata tuno karashen kalmomin da aunty maijiddah ta fada mata d’axu na xata sake sabuwar rayuwa ne yanzu domin aljannarta tana k’arkashin kafar sarki Aliyu_Hydar...
*washegari*
*D*a safe bayan ya gumsu ta kara yiwa Meenah fada aunty yafendo ta kara mata gyaren jiki ba abinda ke tashi ajikinta se kamshi data gilma xaka gane taxo wajen kamshin is divine
Yan uwa duk sunxo domin shagalin biki xa’ai,Baffa yaso yahana fafur su ya gumsu su kaki kancewar suma sesun gyagije abune na lokaci d’aya,da xa’ai fulanis day domin yiwa aunty yafendo kara tunda itace marikiyar Meenan kuma ba fulata nace a yolan amma Ammi wato hajjagana ta roki alfarmar ayi a bornu domin zugarta nadayawa kuma yawanci kawayen Meenan a bornun suke,
Da zuhri suka isa yola bayan an huta ne meenah da kawayenta suka fara shirye shryen tafiya bridal tea party wanda xa’ayi a harabar garden na gidan harta aysa dake Oxford xeda taxo don halartar shagalin bikin,mamza makeover itace aka dakko tun daga abuja don yiwa Amarya kwalliyar biki har a kare,photographers kuwa su georgeokoroweddings ne da Maigaskiya photography,steivein reinz da kuma bighstudio abunde se wanda yagani kawai duk wata kafa ta social Media bikin ake watsawa tun kafin a fara abunka da bikin who is who tuni ivs su keta yawo a net..
Karfe bakwai da rabi aka fara taron bridal tea party Meenah da friends d’inta ne kawai sukaje se maxan ajinsu da kuma gidado da ya kafa ya tsare miss pinkin sa,sosai Meenah tai kyau cikin floral cave party dress dinta baby blue me torches pink,friends nata su bestie dinta Astuto_Nina,Miss pinki,xarah nee,Nabeelah da sauran friends nata duk sunyi kyau cikin baby pink floral dress dinsu abinde se wanda yagani kawai an gwangwaje ansha rawa ansha savouniers kafin shagalin bikin gobe wato fulanis day..
#Hrh shehun bornu
#gimbiya Aminatu Ghaji Bulama
_Su rano maman affan kuwa ba’a samu damar halarta ba saboda ba’a bata kati ba se instagram tashiga taga video din a northern hibiscus wanda akai tagging da#bridal tea party of Ameenah Ghaji Bulama aka Mrs Aliyu Hydar_(his royal highness emir of bornu state)
_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_*
[4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```nanahafsat.wordpress.com```
```Edited by```:
```Ya hajja ce```
_*wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wani kanuri/barebari dake fad’in k’asar nan..Musanman yan yerwa fato..Nagaisheku Nagaishe ku dangin k’amshi gaisuwa mai d’imbin fatan alkhairai_
*71*
*B*ilkisu na zuwa unguwarsu taga baki d'aya yanayin unguwar ya canza daga yadda tasanta,a k'ofar wani had'add'an gida mai matukar kyau jikin shi duk tiles nan taga driver d'in ya tsaya tare da fitowa da sauri ya b'ud'e mata murfin kofar yana cewa,
“Rankishi dad'e gamu munxo Allah ya k'ara miki lafiya.”
Jinta tayi wani gingirin ganin yadda yake tayi mata sannan yana nuna mata gidan a matsayin wanda zata shiga,sake kallon driven tayi sannan cikin tsoro tace,
“Dan Allah malam ina ne nan ka kawo ni?!”
“Ranshi shi dad'e ai cewa akayi na kawoki gidan mahaifanki toh kuma gashi munzo Allah ya temakeki.”
Ya fad'a cikin gazgata mata abinda ya fad'a,sake kallon gidan tayi sannan ta girgiza kai alamar bata yadda ba ganin tak'i fitowa yasan kuma ba haka takeyi ba yasa shi k'arasawa cikin zauran gidan ya kwad'a sallama,Ummi ce kanwarta ta fito dan ganin wanene tana ganinshi da kayan sarauta ta durkusa har k'asa tana gaidashi ya amsa tare da cewa.
“Yauwa 'yan mata kinga ga yayarki bilkisu tak'i fitowa daga cikin mota ko zaki je idan ta ganki k'ila ta fito?!”
Ai da sauri Ummi tayi waje murfin motar a bud'e yake nan billy ta ganta tayi saurin fitowa da sauri suka rungumi juna cikin murna kafin Ummi taja hannunta suka shiga babu wanda yayi magana a cikin su dan tsabar murna sai da suka shiga cikin gidan.
“Umma ki fito ga Yaya Bilki tazo.”
Cewar Ummi cikin d'aga murya suka k'arasa cikin parlor suka zauna yayin da bilkisu keta faman kallon yanayin gidan tana mamakin yadda rana d'aya Allah kan sauya al'amura bata gama mamaki ba Umman su ta shigo parlon tana murmushi tace,
“Ke dai bilkisu bakya son zama duka-duka yaufa kwanaki uku kenan da kuka zo gidan nan amma yauma har kin kuma fitowa.”
Sakkowa billy tayi daga kan kujera ta fad'a jikin Ummanta tana kuka nan da nan hankalinta ya tashi ta kalli inda Ummi take tace,
“Tashi kije ki d'akko mata ruwa da abinci.”
Ummi ta tashi jiki a sanyaye yayinda billy ta maida hankalinta wajan mahaifiyarta cikin kuka take cewa,
“Umma ya cuceni ya b'atamin rayuwar da kuka dad'e kuna kula min da ita wallahi Umma ba laifina bane saceni yayi ya tafi dani masarautarsu ya aikata zina dani Umma ya b'ata rayuwata dama ace na mutu kar naga rayuwata ta gaba dan nasan sai tafi haka muni da wulakanta...!l
Sai faman surutai takeyi daga gani hankalinta ne ya dawo dan haka Umma ta barta sai da tayi kukan sosai har ya haddasa mata da ciwon kai sannan Umma tace,
“Kiyi shiru Bilkisu kiyiwa Allah godiya daya dawo miki da tunaninki bayan kin kwashi tsawon shekaru sannan kiyi min bayanin shin waye kike maganar yayi miki duk wad'annan abubuwan...?!”
“Umma waye kuka bashi aurena?!”
Tayi maganar hawaye na sake zubowa Umma ta rungumeta cikin sanyi jiki da tunani kala-kala tace mata.
“Bilkisu abin labarine mai tsowo a yanzu haka ked'in matar yareemah babagana ce ke..”
“Na shiga uku lallai sai yanzu na kara tabbatar da cewar wannan mutumin azzalumini macuci da besan hakkin d'an Adam ba,wallahi Umma shine ya cuceni ya b'ata min rayuwa bayan mahaifiyar shi ta goya mai baya shine ya lallabo kuka bashi aurena bayan kunsan ina cikin halin kunci da bakin ciki....?!”
“Innalillahi wa'inna'ilaihir rajiun yanzu bilkisu kinason kicemin yareemah babagana shine yayi miki wannan aika-aikar?Lallai na yadda ba'a gane mutum a fuska sai an yi mu'amula dashi da zuciyar shi,amma yaron nan ya cika macuci a haka kamili kamar zai bauta mana ashe ashe sakayyar Allah ce ta fara riskarshi tun a nan duniya..”
Anan bilkisu ta bawa su Umma labarin abinda ya faru har kawo yau data ganta tare dashi sannan itama Umma ta sanar mata iya abinda suka sani har yadda akayi auran da kuma yadda shi yareemah babagana ya gyara musu gidan ya zuba musu komai na rayuwar zamani sannan ta sanar da ita yadda sukaga yana tarairayarta kamar zai maida ita cikinsa sannan Umma ta k'arkare da cewar,
“Mu bari abbanku ya dawo yaji sannan kuma mujira hukuncin da sarki zai yanke domin idan kowa ya yarda ni kam bazan yadda ba sai na kwato miki hakkinki..”
Wani sanyi ya ziyarci zuciyar Bilkisu ta kuma kwanciya jikin mahaifiyar tata tana fatan kar Allah ya kuma yin sanadin komawarta gurin babagana bata fatan hakan ta kasance koda kuwa zai mutu.har dare suna tare makota zai zuwa kwasar gaisuwa sukeyi har lokacin da Abba ya dawo shida yayunta nan suma sukaji duk abinda ya faru saidai tunanin Umma dana Abba ya ban-banta domin shi cewa yayi,
“Alhamdulillahi dole mu godewa Allah dan tun anan duniya ya saka miki bilkisu,da ace Allah yayi watsi dake da ko gaskiyar al'amari ya bayyana bilkisu bazamu iya ja da gidan sarauta ba dan da ace munsan gaskiyar tun a baya sai dai muyi Allah ya isa domin zuwa kai k'arar d'an sarki kotu ko police station abun akanmu zai kare dan kila idan shi ba'a d'aureshi ba Mu a kullemu kuma babu me fito damu sai yadda Allah yayi damu,amma kunga sanda abin ya faru sai Allah ya dasawa yaron soyayyarki mai zafin gaske ta yadda ya kasa sukuni har saida yaga ya mallakeki bayan da tuni ya lalata miki rayuwa kuma sannan ya barki da gorin duk wani namijin da zaki aura amma yanzu fa?asirinki a rufe namu arufe amma ni bazan goyi bayan ki kashe auranki ba sannan kuma nayi alkwarin bazan tilasta miki komawa ba dan ba abin hannunshi nakeso ba rufin asirin gidana da mutuncina nake so.”
Bilkisu najin haka ta kuma rushewa da kuka,Umma tace,
“A gaskiya ni banason ta kuma komawa wajan shi domin hatta mahaifiyar shi ba son auran takeyi ba kuma batada imani bare tausayi gara kawai a rabasu Allah ya had'a kowa da rabonsa.”
“Gaskiya kam dan hakan ne zaisa ya gane cewar ba arzikinsa muke so ba.”
Cewar yayanta Bashir wato yana goyan bayan Umman tasu akan ra'ayinta,yayin da Abba yayi murmushi mai ciwo dan yasan shi abinda ya hango su duka basu hangoshi ba dan haka ya mik'e tsaye tare da cewa,
“Zan jira naji hukuncin da mahaifinshi zai zartar duk kuwa da cewar nasan shi besan da wannan abunba.”
Yana kaiwa nan ya fita cikin tsananin mamaki da alajabi sam be tab'a koda hasashen cewar wai babagana ne yayi wa gudan jininshi haka ba sai dai tunawa da yayi cewar ranar dubu ta b'arawo d'aya tal ta me kaya da wannan tunanin ya cigaba da harkokinshi yana son jin sakon kira daga gurin mai martaba maimurabus.
*MEENAH’S WEDDING EVENTS*
Sosai ake shagalin biki sai dai yadda kukasan Modu ne angon dan dashi ake yin komai shi kuma sarki Aliyu hydar maimartaba maimurabus ya hanashi zuwa a cewar shi kar yaje dan kar asamu abin fad'a a cikin al'umma yace yayi zamanshi har a kawota d'akinta hakan yasa duk abubuwan da aka tsara 'yan uwa da abokan arzuk'ane keyin komai.A gurin bikin harda mahaifiyar Basmah domin tazo itama anan ne kuma ta kuma tabbatar da cewar babu wanda yasan rabuwar sarki Aliyu hydar da Basmah ta yadda taji kowa yana tambayarta wai ya karatun Basmah yashe zata dawo sai dai kawai tace musu tana can bata dawo ba da haka ta ja bakinta tayi shiru tana son idan komai ya lafa ta samu maimartaba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 35