dasu wani katafaran apartment wanda ba sosai ake shigarshi ba.sun sha mamaki lokacin da suka tarar da kowa na gidan a ciki har dana nesa ashe tun daran baba mai murabus ya tura musu text messages kan cewar su zo yana son ganinsu.can gefen mijin nasu Ammi ta hango hajja yakolo wadda tayi k'asa da kanta daka ganta kasan bata da gaskiya,sai hajja gajiram dake kusa da ita sai faman kuka take yi. Ammi ta k'arasa itama ta zauna sai faman tunanin abinda ya tarasu takeyi, da sauri yareemah Ngari yayi gurin mahaifinshi wanda ke kishingid'e hannunshi dafe da k'irjinshi ya k'arasa tare da durkusawa fuskarshi fal murmushi cikin sassanyar muryar shi yace.
“Baba barka da safiya Allah ya kara maka lapia Ameen?!”
Da sauri maimartaba ya mik'e zaune ido waje yake kallon d'an nashi dai-dai lokacin sarki Aliyu hydar da Meenah suka shigo suma suna kallon ikon Allah, mai martaba shehu bulama ya riko yareemah Ngari hawaye fal a cikin kwayar idanunshi yace.
“Alhamdulillah..Alhamdulillah..Alhamdulillah.”
Yana fad'ar haka ya tashi zaune yayi sujudu-shukur yana kuka wanda ya kasa b'oyuwa sai da ya fito fili kowa na gurin jikinshi yayi bala'in yin sanyi,shima yareemah Ngari yayi kamar yadda yaga mahaifinshi yayi,be d'ago ba har sai da yaji mahaifin nashi ya d'ago sannan shima ya d'ago suka rungume juna cikin tsananin kewa maimartaba sheshu Bulama yace.
“Hak'ik'a duk wanda yace Allah ya kuma rik'eshi a duk abinda yake yi yasan cewar yana ganin shi toh lashakka ba zai tab'a tab'ewa ba,sannan ba zai tab'a wulak'anta a duniya ba,
“Yau gashi ban mutu ba Allah ya nuna min lokacin da zan kumajin muryar yarona bayan tsawon lokaci da aka d'auka wajan cutar min dashi Allah kaine Allah,Allah ka d'auki rayuwarmu muna masu jin tsoranka da yi maka biyayya a duk abinda ka umarce mu Alhamdulillah.”
Ya fad'a tare da janye jikinshi daga na yareemah Ngari,cikin farin ciki sarki Aliyu hydar ya k'arasa wajanshi da sauri suka rungumi junansu Ammi dake gefe sai faman share hawaye take da k'asan hijab d'inta yareemah babagana shima ya mik'e ya k'arasa wajan su duk suka rungumi juna cikin tsananin jin dad'i da farin ciki.
Sun dad'e a haka ganin basu da niyar sakin juna ne ya yasa shehu Bulama yin murmushi yace musu.
“Toh ya isa haka ku bari muyi abinda ya taramu idan aka gama sai kuyi duk abinda zakuyi.”
Suna murmushi suka saki juna sai sukaji hajja gajiram ta k'ara b'arkewa da kuka tamkar wadda aka daka ta d'ago jajayan idanunta duk suka bita da kallo amma banda shehu Bulama shi taron ma ya fara bud'ewa da addu'a cike da rashin damuwa dajin kukan da takeyi duk da cewar kukan na hanawa aji maganar tashi sosai kasan cewar bashi da murya ta dakushe sabida kukan daya sha a daran jiya.bayan an shafa addu'a ne ya sake gyara zama still hajja gajirim ta kuma k'ara volume d'in muryarta shehu bulama ya girgiza kai cikin takaici amma beyi magana ba ganin haka yasa yareemah babagana kallonta cikin takaici sabida duk gurin ita ake kallo bama sauraran mahaifin nasu ake yi ba yace.
“Mami wai ya haka ne?baba fa magana yake yi amma kink'i yin shiru haba mana.”
Hajja gajiram tayi mai banza baba maimartaba ya kalkeshi yace,
“Karka kuma yi mata magana ka barta duk abinda take yi ta sani.”
Shiru gurin yayi sai kukanta da yake tashi yayin da hajja yakolo tayi tsomu-tsomu da ita jikinta sai rawa yake yi Ammi na kallonta sai dai kawai ta girgiza kai Shehu Bulama ya fara da cewa,
“Alalhak'ik'a dole ne na fara godewa Allah subahanahu wata'ala daya bani ikon yin numfashi a doran k'asa,ya bani lafiyar yin aure abisa sunnar ma'aiki sallawa'alaihi wasallam,ya kuma albarkace ni da yara masu yawa masu albarka Alhamdulillahi a kullum ina gode mishi,
“A cikin daddad'ar rai da rayuwar da ya bani dama ya sanar damu cewar akwai kaddara a duk jikin bayi masu rayuwa a doran k'asa, nasani Allah ya jarabce ni da mata da 'ya'ya wad'anda nasan suna d'aya daga cikin kaddarata kuma na karb'eta banyi fushi kojin haushi ba amma kaf cikin ilahirin iyalina babu wanda bansan halinshi ba sai dai duk abinda kayi zan maka nasiha bazan nuna maka cewar nasani ba idan kaji falillahil hamdu idan bakaji ba bani na fad'a ba fad'ar Allah ce yau gashi asiri ya tonu kowa ya fito da halinshi na fili dana b'oye.”
Tari ne ya sark'eshi ya fara yi ba k'akk'autawa da sauri Ammi taje ta zuba mai ruwa ta bashi yasha sannan yayi shiru sai da ya lafa kowa nayi mai sannu sannan ya cigaba da cewa,
“Yau gashi tun tsawan shekaru da wad'annan bayin Allah suka d'auka akan rayuwar abokiyar zamansu da ba ita ta kawo kanta ba,kamar yadda na auro su har gaban iyayansu haka itama na aureta.sannan kamar yadda'ya'yansu suke nawa haka itama nata nawane halal malak amma sai suka sanya mata idanuwa daga ita har yaranta basa san ci gabansu tun suna k'anana har kawo jiya da idanuwana dana yaronsu ya gane musu mummunan abu wanda bazan iya sanar daku ba sai dai bana fatan hakan ya sake faruwa koda kuwa a mafarki.”
Shigowar Modu ne yasa kowa kallon kofar ya shiga yana sunkiyar da kai domin shi bashi da labarin meeting d'in sai yanzu da sarki Aliyu hydar yayi mai text message sannan yaga na baban ma wanda yayi mishi da dare, ya samu guri ya zauna sannan baba maimurabus ya ciga ba da yin magana,
“Yau gashi hakuri da tawakkali yasa komai ya warware cikin hukuncin Allah,sai dai Allah ya jarabce ni da d'a/'ya wanda aka samo min shi ta hanyar da be dace ba. Sannan Allah ya jarrabi d'ana da soyayyar wata baiwar shi wadda itama hakkinta ne Allah ya biya mata yau gashi yana cikin halin takura da nadama
“Duk cikin tuggun wad'annan bayin Allah suka jazawa baiwar Allah har suka ja mijinta ya rabu da ita alhalin suna son junansu amma su basu ga hakan ba,shin wai me suke nema na kasa ganewa?!”
“Baba Allah ya k'ara maka hakuri ya kuma k'ara maka tawakkul muma ya bamu irin hakurinku.”
Suka jiyo muryar Modu wanda yayi k'arfin halin yin magana duk da cewar besan silar maganar ba. Baba maimartaba ya d'ago yana kallonshi yace,
“Amin ya rabbi kullum fatana Allah yayi muku albarka.”
“Amin baba.”
Duk suka fad'a Aliyu hydar dake zaune sai satar kallon Meenah yake yi ita kuma da sun had'a ido zata turo mai baki cike da shagwab'a duk abinda suke yi Ammi na kallonsu gaba d'aya ta rasa gane waye wawan a cikin su dan tsabar wauta sai yi suke yi tamkar ba sarki ba soyayya ce fal a cikin idanunshi da gangar jikinshi ta d'auke kai tare da tab'e baki cikin ranta tace.
“Allah yasa ma suna jin abinda ake fad'a.”
Falmata ta mik'e ta k'arasa gurin mahaifinsu cikin kuka ta durkusa tana neman gafararsa yace,
“Ai ni falmata ban rik'e kowa ba nawa da wanda ba nawa ba fatana muyi sa'a Allah ya yafe mana duk kurakuran mu,sai dai bansan yadda zaki yi rayuwa da wannan cikin dake jikin ki ba gashi kuna final year.”
Sai a lokacin kowa ya gano wadda aka ce ta samo d'a/'ya ta kuma rushewa da kuka dama hajja gajiram bata yi shiru ba har lokacin tamkar ma bata cikin hayyacinta dan yadda takeyi tana faman harare-harare tana sosa cikin kunnanta tare da yarfe hannu,baba maimurabus yace.
“Ni yanzu ban san yadda za'ayi ba sai dai ki ajiye jarabawar domin fitarki da wannan abu shine tonuwar asirina na uku baya ga na mahaifiyarki dana d'an uwanki dan ma shi Allah yayi mai lud'ufi ya samu ya aureta harda rabo a tsakanin su, sai dai ta gujeshi alokacin da shi d'in yake tsananin buk'atarta.”
“Kaza...kaza..Kazan...ub....can! K'arya ne wallahi Allah ni za'a yaudara dan kaza...kazan uw... Can?toh wallahi kunyi karya domin sai hajjagana tabar gidan nan,sai Aliyu yabar kujerarshi yabi duniya yayinda Ngari zai k'arasa barzahu,wallahi tallahi sai 'ya'yanta sun shiga duniya dagani sai 'ya'yana mune zamu zauna a cikin shehurin nan,
“Sannan nace bana son bilkisu kai babagana shegen taurin kaine dakai tamkar d'an gidan fir'auna nace maka bana son bilkin nan amma ka nace tun sanda na kamaka akanta shine yanzu dan ubanka harda yi mata ciki ko? itama yakolo da muke aikin tare so nake mu kammala komai itama na koma kanta hahahaha ho ni shegiya..!”
Suka ji hajja gajiram na fad'a idanuwanta sunyi jajawur gashi sunyi manya tamkar zasu fito waja yayin da hajja yakolo ta zaro idanuwa tana kallon hajja gajiram cikin tsananin mamakin jin kalamanta.
“Alhamdulillah kayk'ayi koma kan mashek'iya Allah ya mayar muku da abinku Allah ya k'ara.”
Yaya gumsu ta fad'a cikin tab'e baki tana hararar su, baba maimurabus ya dafe kai tare da dafe k'irji jin irin surutan da hajja gajiram keyi da sauri yareemah Ngari da Modu suka k'arasa wajan shi suna k'ok'arin gyara mai zaman sukuma sauran yaran sai kuka suke yi dana gajiram d'in dana yakolo sai Affy yayin da Meenah ta mak'ale jikin aunty yaruwaiya jikinta sai tsuma yake ganin tamkar hajja gajiram ta samu tab'in hankali.
“Kayya gumsu kiyi shiru dan Allah..”cewar Ammi,
Sake gyaran murya shehu Bulama yai xe cigaba da magana kenan hajja Gajiram tasa ki wata bahaguwar kara sekace bijimin sa tanayi tana shusshura k’afafuwa,
Ammi da Ayiya ne sukai kanta don ganin tana k’ok’arin yage kayan jikinta cikin suratai tafara magana tana bubbuge hannayensu daga jikinta,
“Jakadiya Mangu Allah ya isa tsakani na dake Jakadiya mangu kilan kece kika hak’o asirin da mukai akan Ngari dake rijiyar kauyen damboa...”
Dafe kai Ammi tai tana k’ok’arin rufe bakin Gajiram dake surutai,wani tsalle Gajiram tai tatashi akan k’afafunta duk kowa na parlorn ya bita da kallo cikin soshe soshe da cixgar gashin kai tashiga reto maganganu,
“Mune muka raba hajjagana daga gidan nan munso fitar da ita gaba d’aya to bokan ta yafi namu”
Tsaki aunty yaruwaiya ta saki kafin tace,
“Wallahi yayya da Allah ta dogara wahidin Ahadin domin shi din mabuwayine gagara misali”
Daria Gajiram ta saki cikin rawa tacigaba da magana tana sosar kai kamar me kwarkwata,
“Mune muka nakastar da yareemah Ngari tun lokacin shayinsa mukai amfani da jinin don cinma manufarmu akansa,mune muka sanyawa shehu Bulama ciwo domin ya mutu babagana ya gajeshi a mulki sede kassh hakan be yiwu ba domin shegen d’an na hajjagana da mukaso yaxama dan iskan daya gagari iyayensa shine yanxun akan karagar mulkin bornu”
Daria Gajiram tasake kwashewa da ita itade yakolo dake gefe jikinta se bari yake ganin bilhaqqi da gaskia gajiram din taxama me tab’un hankali tatas sihirin da suka aikata se xayyano su take,
“Ni Gajiram nida Yakolo da temakon amintacciyar jakadiya ta wato Mangu mune nan muka shiga tsakanin Aliyu da matar sa wato Basma itama da yake idonta ya rufe ta aikata duk abinda mukace gashi yanxun tayi biyu babu babu haihuwa ta sanadiyar toshe mata mahaifa da mukai da kuma rabuwar igiyar aurenta da Aliyu..
Sake fashewa tai da daria,Babagana dake gefe kawai girgiza kansa yake yana hawaye hakama sauron yayan nata gaulayen kuwa se tabe tab’e suke ya xungorota da k’afa ita kuma ta cuno baki tana janye kafar tasa Aunty yaruwaiya dake kallon su take taiwa gumsu sign da ido girgiza kai kawai sukai suka cigaba da jin xancen sabuwar tabi wato gajiram..
“Ni Gajiram nida yakolo mune nan kwananan lokacin tarewar figaggiyar yarinyar can wato Meenah muka tafi har kauyen gombole muka hadu da sabon boka yabamu aiki Kan idan har muka aikata tofa komai namu xe dedeta idan har kuma aka samu akasin haka to yana tabbatar mana da cewar reverse s d case,,heheh akan iyalan hajjagana kaf mukai aikin dama shehu Bulama domin cinma burinmu wanda muka dade muna muradi,
“Yakolo akace ta binne abu a karkashin inda Ngari yake kwana da kuma farfajiyar gidan hajjagana ni gajiram..”sekuma ta fashe da daria tana nuna kanta dayan hannun kuma tana sosa duburarta dashi,
Ta jima tana soshe kafin tacigaba,
“Ni Gajiram ni bokan nan yabawa aiki yasa nadena sallah da duk wani aikin ibadah nabawa shehu Bulama maganin acikin abinci batare da yayi basmala ba kamar yadda boka ya umarta yanzu ...Yanzu...Yanxu abu na ukun xan aikata xan binne laya da duburata batare da wani yaganni ba kuma ba kaya ajikina xanyi a farfajiyar sashen Aliyu..”
Tana gama magana ta arce waje da gudu tana ihun,
“Karku bari tsinannun sugani aradun Allah se zuriyar hajjagana kakaf ta wulakanta..”
Binta abaya su Ammi sukai domin sitirce mata jikinta don duk ta cire kayanta ta xubar a bakin kofa xigidir haihuwar uwarta da alama de kwakwalwarta ta tab’u,Parlorn yakoma daga shehu Bulama se su Affy da hajja yakolo dake faman mitsitsika idanuwa da tafukan hannayenta girgiza kai kawai shehu Bulama yai hade da ajiyar zuciya yajima kafin ya dubi yakolo ya soma magana,
“Ina fatan kinji duk abinda Abokiyar xamanki take cewa shin duk abinda tafad’a ki fadamin wannene be koma kan tata xuriyar ba?! Ba cin fuska ba duk abinda tafad’a yafaru akan yayanta kinsani nasani kowa yasa ni,to ked’in wacce ribar kika samu inbanda koma baya tur da hali irin naku Allah ya shirye ku shine magana ta kawai..”
Ya k’arasa magana yana jinjina kai,kuka yakolo ta soma tana girgiza kai,
“Toh dan Allah ku kunna fitilar parlorn kada ku azabtar dani wallahi tilastani tai..”
“Me..?!”cewar shehu Bulamaa hade da sakin siririn tsaki ahankali,
“Wallahi bana ganin komai ranka ya dade”
“Karki kawo xancen sakarci anan yakolo domin mudin ba’ababen wasanki bane..”
“Na rantse da Allah..wallahi Allah bana gani”cewar yakolo hade da fashewa da kuka..
#idan zaka gina ramin mugunta to gina shi ga jere,domin KOMAI NISAN DARE GARI XE WAYE...
NB
Ansamu akasin suna nacanxa *Ayiya* dotan Gajiram zuwa *Falmata* bayan falmata tanada aure..Agafarce NI,zanci gaba da rubuta Falmatan kawai savoda karku xama confuse...Thank y’ll👌🏼👏🏼
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼
[4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE```
💖?👨👨👧👦
_*```A STUNNING LOVE STORY```_*
*```NA```*
©```NANA HAFSAT
(MISS XOXO```)
®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡
_*```Home of expert and perfect writers```_*
```DEVOTED TO```:
*```XARAH BUKHAR```*
```Edited by```:
```Ya hajja ce```
```nanahafsat.wordpress.com```
*79*
*S*ai da layla ta d'an huta a asibiti sannan likita ya sallamesu,shehuri aka wuce da ita ana zuwa Modu yasa aka kaiwa maimartaba maimurabus jaririn dan ya ganshi ya kuma saka mai albarka.
K’aton d'aki aka warewa layla ta shiga ta zauna 'yan barka sai zuwa suke Aisha (kiara) kuwa ta kasa ta tsare tana rik'e da jariri da kyar take iya bawa mutane su ganshi dan hatta layla bata bawa shi wani sa'in ma sai Ammi ta lek'o tace abashi nono tukunna akeyin tunanin bashi,duk sun barwa Modu yin komai shine zuwa ya d'akko kayansu daya dawo za'a ce ya manta kaza ya kuma komawa bawan Allah babu gaddama bare girman kai haka zai sake komawa yayi musu abinda suka ce ba tare daya saka wani ko wata ba.
Sai dare tukunna Aliyu hydar ya koma apartment d'inshi wanda yake gari guda,a parlour'n shi ya zauna bayan ya gama duk abinda zai yi sannan ya d'auki waya ya kira matan nashi cewar suzo, kowacce ta fara murna an kira ta ba kamar Meenah da take tunanin bazai iya yin wani abun bane yasa ya kirata duk kuwa da cewar yau zai koma wajan Basmah,
A k'ofar shiga parlour'n shi duk suka had'u suka tsaya kalon-kalo a tsakaninsu,Basmah ce ta daure tayi mata magana tana kakalo murmushi tace,
“Ina yin Amina...?”
Aikuwa Meenah ta yatsina fuska da kyar da kai zuciya nesa tace,
"Yini lapia amma kuma kamar dare ne ko?!.”
Daga haka tayi saurin shigewa ciki tana faman cuno baki yana zaune yana facing kofar ya saci kallonsu sai kuma ya d'auke kai dan karma ya fara kallon wata a cikin su d'aya tace yak'i kallonta dan haka ya maze yana ci gaba da karanta news paper d'inshi,da sauri Meenah ta k'arasa jikinshi ta zauna kan kafarshi tana watsa mai wani sassanyan kallo yayi murmushi kad'an tare da ajiye jaridar yace,
“Ajlal karki karya ni fa yanzu kinyi nauyi da yawa.”
Bakinta ta kuma turowa ya kalleshi tamkar ya cijeshi amma ya maze sabida ganin Basmah ya d'an d'auke Meenah daga cinyar shi ya zaunar da ita kusa dashi ta fara zumburar baki shi dai be kulata yayi gyaran murya yana kallonsu yace,
“Ku shirya muje gurin Ammi layla ta haihu.”
Meenah ta zaro idanuwa cikin mamaki tare da ce,
“Nan aka dawoda ita ba gidan su aka kaita ba...?!”
“Toh Ajlal babu kyau ne yin hakan?!”
Sarki Aliyu hydar ya tambaya yana kallonta cikin mamaki, tab'e baki tayi tana jijjiga kai tace,
“Mudai a gidan mu duk wadda tayi haihuwan farko gida ake kaita,amma ita a kawo ta nan dan Allah,uhm'um idan nice kuwa bazan yadda ba tabd'i...”
Dariya yayi sabida ganin har yanzu yarinta na damunta,ita kam Basmah idonta na kan tangamemiyar plasma TV d'in dake kafe a parlour'n tana jinsu amma bazakayi tunanin sauraronsu takeyi ba kasan cewar ta kafa ido tamkar tana son gano wani abun a cikin t.v d'in.
“Ku tashi ko wacce ta d'akko hijjab dare na sake yi.”
Mik'ewa Basmah tayi ta fita ita kuma Meenah ta turo baki cikin shagwab'a da tab'ara ta kalleshi,
“Ni dai gaskiya tsoran fita nakeyi muje ka rakani.”
Shareta yayi ganin lallai rigima take nema tunda tasan ba gurinta yake ba dan idan ita yayiwa haka akan Basmah ranar da rigima zasu kwana,waya ya janyo ya kira Basmah tana d'agawa yace,
“Please ki tahowa da Ajlal aron hijjab dan Allah.”
“Toh.”
Kawai Basmah ta fad'a Meenah kuma ta sake turo baki ita a dole ba haka taso ba,sanye ta dawo cikin nata hijjab d'in hannunta rik'e da wani tazo ta mik'awa Meenah ta k'arb'a tare da cewa,
“Na gode”
Daga haka shima ya mik'e suka jera duk sun sashi a tsakiya hirar su sukewa tsakanin Meenah da shi Basmah kam ko kulawa bata yi sabida sam bata san mezata ce ba a hirar har suka k'arasa apartment d'in Ammi.
Da gudu Meenah tayi ciki tana neman Ammi har cikin bedroom amma babu kowa Basmah kuwa wucewa tayi inda take jiyo magana shi kuma ya tsaya yaga iya gudun ruwan Meenah,yana nan a tsaye kuwa sai gata ta fito da alama bata ganta ba ya kalleta tare da ware mata hannuwan shi alamar ta taho tayi saurin shigewa ya matsa ta yace,
“Ammin bata nan ne?!”
Meenah ta d'aga kai alamar eh yayi murmushi yace,
“Toh ai kece waike 'yar gida ana zuwa kika yi gaba, ita kuma ta shiga can kuma da alama duk suna ciki tunda gashi bata fito ba ita.”
“Ai ita kai ka gaya mata amma ni sai ka barni na tafi nasha wahala.”
“Kai Ajlal babu ruwana ni babu wadda na nunawa inda zataje, yanzu dai kishiga kije kuga baby boy mu koma.”
Zare jikinta tayi daga nashi tayi gaba tana cewa,
“Wai kai duk ka k'agara a wani koma dan zaka je d'akin ta.”
Shigewa tayi shi kuma ya bita da kallo ya lura yanzu ta fiye neman rigima ta babu dalili, juyawa yayi zai koma parlour ya zauna yajiyo muryar Modu a bayan shi,
“Saraki sai Allah kainuwa dashen Allah wai bazaka shiga bane?!”
Aliyu hydar be juyo ba sai da ya k'arasa ya zauna sannan yace,
“Kai guy wai baka tafi gida ba me ka tsaya yi haka a nan?!”
K'arasawa shima Modu yayi ya zauna tare da shafa sumar kanshi ya kalli sarki Aliyu hydar yace,
“Bari kawai guy ina nan sai fama nake da Aisha akan tazo mu tafi amma ta kafe wai anan zata kwana su kuma su yaruwaiya sai zuga ta suke yi so ina cikin damu dan bazan iya kwana ni d'aya a gado ba na saba najini a jikin mace wallahi.”
“Toh sai ka kwana anan kawai cikin su.”
“Kai guy dan bani da kunya...?!”
Cewar Modu yana zaro ido Aliyu hydar yayi murmushi ganin ashe duk iskancin banza yake yi,tashi Modu yayi yaje ya d'akko d'an ya kawo mai, karb'a yayi yana murmushi yayi mai addu'o'i sannan ya kalli Modu yace,
“Guy gaskiya kasha aiki wannan yaron sak kai babu abinda ya bari sannu da k'ok'ari guy.”
Dariya Modu yayi sosai jin irin shak'iyancin da sarki Aliyu hydar keyi mishi, sun jima suna hira kafin Aliyu hydar yace zasu tafi Modu ya shiga yayiwa su Basmah magana suka fito shima ya k'arasa wajan Aisha (kiara) yana lallashi sai da layla tayi magana sannan ta yadda zata bishi zuciyarta cike da kewar boy d'in sannan suka tafi.
Basu samu damar ganin Ammi ba kasan cewar tana wajan mijinta haka duk suka tafi da nufin da safe zasu dawo...
Ranar suna yaro yaci sunan yareemah yareemah Ngari wato usman xa’a dinga kiransa da NAUFAAL kowa yayi mamaki kwarai matuka don ba’ai xaton sunan da Modun xe sanyawa yaron ba kenan,sosai akai shagalin taron sunan a babban katafaren dakin taron dake masarautar anci ansha ankuma rarraba savouniers abinde se wanda yagani kawai..
Hakika yareemah Ngari yakashe kudi akan takwaran nasa kayan barka ma akwatuna set biyu na loui vitton ya cika da kayan baby hade da shanu guda goma sha biyu dukde na takwaran nasa duk wata cima da akai a sunan shi yayi ya hana kowa ya bayar,kyautar bata tsaya anan ba seda yasake baiwa takwaran nasa fili a unguwar bulabulin Ngarnam dake jihar bornun..
Duk abinda meenah taci a taron sunan sedata amayar gaggawar kiran sarki Aliyu Hydar tayi awaya asukwane ya garxayo ya sunkuceta se asibitin dake masarautar gwajin farko yanuna positive meenah na d’auke da ciki harna tsawon sati goma sha shida wato wata hudu kenan,murna awajen sarki Aliyu Hydar abun harbawa Meenah kunya yai se cuno baki take gaba shikuma ya xauce se sumbatun dadi yake yana sumbatar cikin..
Kiran layikan yan uwa da abokanan arziki ya shiga yi ciki hardasu Ammi ba ko kunya,Meenah ta dallah masa harara tana cuno baki gaba,
“Wai ya Aliyuu meye haka ne?!”
Cikin kissing gefen wuyanta yabata amsa yana gyara mata gashin kanta,
“Da nayi me Ajlaal?!”
“Kobah kai bane kanata kiran mutane kana gaya masu..”
“Toh Ajlaal lefi ne dannayi?! Aidan asan nid’in lafiyayyane ba’ai sangartaccen sarki ba”
“Hum uhm”cewar Meenah hade da ture masa hannu don sam yanxun batason ya rabeta
Bedamuba yasake nanukarta yana sinsinar wuyanta,
“Wifey ashe shiyasa kike avoiding dina bakyason na kusanceki ashe ashe ajiyata ce a nan”yafadi hakan yana nuni da mararta..
“Ni kadena tabani pls”
Dan murmushi Aliyu Hydar yayi wanda har seda kyakkyawar wushiryar sa ta bayyana,
“Toh Ajlaal xan k’ok’arta amma kinsan de baxan dena ba sede na rage ko?!”
Duka takai masa aciki tana dariya sun dan jima aasibitin ana gaya masu yadda xata kula da cikin ta raineshi har izuwa ranar da Allah xe sauketa lapia,daga nan sashen Ammi suka nupa duk yan gidan suna nan aka shiga masu congratulations da gudu Affy ta sakko daga stairs tana tsalle xata rungume Meenah Idanuwan Aliyu sun rufe da sauri ya dakatar da ita yana galla mata harara,
“Ke ke ke..Dakata hakanan se wani gudu kike Kina tsalle idan kika bigemun ita fa tunda yanxun kinsan ba ita kadai bace”
“Allahu Akbar sannu babaa atoh Sannu baba andeji kunya wallahi agaban Ammi kake fadar haka Lalle Aliyu”cewar Aunty yaruwaiya
Se asannan Aliyu ya lura dab’aran batamar dayai sumsum ya fice yana susar keya sukuma yan parlorn suka hau daria,yana fita ya kira Affy awaya seda ta kusa tsinkewa sannan ta dauka,
“Auta zo nan waje ina jiran ki”
Kamar baxata amsa ba sekuma tace Toh,fita wajen tai wajensa yana xaune yana danna waya tadan tsaya nesa dashi tana turo baki agaba,
“Zo nan lil sis kakki fushi da baa Hydar dinki mana kinji autanmu”
Dan murmushi Affy tai sannan takarasa wajensa taxauna akusa dashi,
“Me kikeso nasiya maki yanxu uhm?!”
“Sabon apple laptop”
“Dame kuma?!”
“Se..uhm wannan inaso naje naga Disney castle a Florida”
“Your wish is granted lil sis kita addua Insha Allah xankaiki Florida kije kiga Disney castle..”
Rungumeshi tai tana murna,sannan yamata transfer kudi a account dinta dukdan kartai fushi saboda yasan idan tai fushi to fa kamar da Ammi yake fushin,saboda ko kad’an Ammi batason fushin autar tata!!!
*2 MONTH LATER* (BAYAN WATA BIYU)
Abinci ne a gabanta sai dai sam ta kasa ci saboda yadda taji bayanta ya rik'e mararta na faman tsirawa,tashi tayi da kyar tana dafe ciki zata shiga toilet Ummanta ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 35