Share this page
yi waya da ita tace tana shehuri, Allah yasa dai ba bacci yayi ba dan a kan hanya nake wucewa zanyi...” Kallonta security d'in yayi fuskar nan tashi a had'e kamar bazai bariba sai kuma yaga ai tunda ta wuto get yasan da gaske take gashi babbar macece wadda idan ka ganta kasan lallai daga babban gida ta fito,cikin girmamawa ya matsa mata ta wuce ciki wanda hakan ya kuma sanya jikinta yin rawa tamkar ana girgizata. Tafiya take a hankali tana faman waigowa bayanta har ta k'arasa ciki, parlorn babu kowa sai k'arar naurar sanyayya d'aki ga wani uban kamshi da yake standard ta fara rarraba idanuwa,sannu a hankali tana tafiya harta k'arasa kusa da bedroom d'inshi,ido d'aya ta kanne tana leken ciki zaune ta hangeshi saman sallaya yana lazimi dan idar da sallarshi kenan kasan cewar yanzu kam alhamdulillah yana iya yin wasu abubuwan da kanshi ba tare da an temaka mishi ba.hannu ta zura ta ciro kullin abinda boka ya basu ta kalleshi sannan ta cije lips tare da sakin wani kayataccen murmushi ta fara warwarewa cikin sauri. “Innalillahi wa'innailaihir raji'un Umm..umm..Umma!” Hajja yakolo taji an fad'a cikin d'aga murya,da sauri ta waigo tare da sakin abinda ke hannunta idanuwanta sunyo waje alamun rashin gaskiya maganar da akayi yasa yareemah Ngari saurin fitowa be kai ga k'arasa fitowa daga d'akin ba Aysa tace, “Baah wait.!” Cak ya tsaya cike da mamaki, nan da nan gid'ad'o ya zaro waya tare da matsawa ya kira Ammi tana d'agawa Aysa ta karb'e wayar jikinta na rawa tace, “Hello Ammi gashi nan za'a k'arasa kashe baah....” Kasa k'arasawa tayi saboda kukan daya kwace mata, cikin tashin hankali Ammi tace, “What.?! Aysa kuna ina? waye yake kokarin kasheshi? sannan duk ina security's d'in gida?!” Kashe wayar Aysa tayi dan tafison suzo su gani bawai su tsaya tambayarta ba. Ai kuwa kafin kace mene tuni ta sanarwa da maimartaba mai murabus lokacin shi kuma yana tare yarremah babagana yana ta kwantar mai da hankali,yana jin haka suka mik'e duk a parking lot suka had'u dan haka dasu Ammi su yayya gamsu suka tafi a motar maimartaba maimurabu irin zungura-zunguran motocin nan masu tsadar gaske suka nufi dambu road. Suna zuwa gate man ya wangale musu gate lokacin duk masu tsaron gidan suna cikin side d'in yareemah Ngari sun hana hajja yakolo motsawa sai faman rantse-rantse take musu amma sam basu kulata ba,shigowar su Ammi ne yasa k'irjin hajja yakolo kuma bugawa a take ta hau kuka yayin da Maimartaba ya tsaya yana kallonta cike da mamaki jikinshi har rawa yake yi yasa hannu d'aya ya dafe saitin zuciyarshi. Aunty yaruwaiya da jikinta har rawa yake cikeda masifa tace, “Dama ance rana dubu ta b'arawo ce,guda d'aya dal ta me kaya ce yau gashi Allah ya tona muku asiri a idon duniya, wallah baba ba ita kad'ai keyi ba harda Mami duk bakin su d'aya.” Shi kam maimartaba sam kasa magana yayi gashi yana son nuna fushinsa amma ya kasa yin hakan sai dai yadda yakejin zafin a zuciyar shi har gara ace a fili yake nunawa yadda kowa zai gani yasan halin da yake ciki,cikin sark'akk'iyar muyar wadda ta shak'e yace. “Ya haka?me kike yiwa kuka yakolo?!” Sai a lokacin hajja yakolo ta d'ago kai ta kalleshi tunawa tayi da cewar hajja gajiram ta shaida mata cewar ta samai na cikin abinci yaci tayi saurin mik'ewa tare da k'arasawa kusa dashi cikin kukan kissa take cewa, “Yauwa gara da Allah ya kawoka,yanzu ni yarannan zasu kallah suce wai nazo zan kashe yaron nan daga zuwa dubiya?!” Da mamaki hajjagana ta kalleshi jin abinda zaice sai taga ya kamo hannuwan yakolo cikin lallashi yana cewa. “Kiyi hakuri yara ne wata kira ko gamo sukayi sukaga kamar wani zai kasheshi ya b'ace shine suka ce kece,yi hakuri kinji.” Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar hajja yakolo yayin da hajjagana ta kallesu zuciyar ta na zafi sabida ganin ga gask'iya k'iri-k'iri amma an taketa nan fa yayya gamsu ta fara bala'in nata aunty yaruwaiya na taya ta,kallon k'ofar bedroom d'in Ammi tayi taga yareemah Ngari tsaye cak ya kasa gaba ya kasa baya tabi gurin da kallo cikin zafin zuciya wadda takeson dannewa dan karsu fahimci halin da takeci tace, “Karka fito ka bari ina zuwa.” Juyawa tayi ta fita duk suka bita da kallo apartment d'inta ta shiga tana share hawaye da mayafin jikinta harta k'arasa wajan dustbin ta d'akko tsintsiya da parker ta wuce ta d'akko moper sannan ta shiga bedroom d'inta ta d'akko zam-zam da ganyen magaryar da ake mai magani da ita ta d'ebo,kitchen ta kuma biyawa ta d'ibi kanwa ta zuba cikin kofi tare da zuba ruwa tayi hanyar apartment din baah Ngari dasu. Tana zuwa bata kula kowa ba har su yayya gamsu da suke masifa bata kula suba ta fara share bakin k'ofar sannan ya yayyarfa ruwan kanwa a wajan sai da ta bi ko'ina na gurin da ruwan kanwa sannan ta k'arasa gurin yareemah Ngari tare da kamo hannunshi suka fito,fatanta koma me tazo dashi ya k'are mata a kanta tunda ai ba zuwa gidan suke ba bare ta tabbar da cewa lallai dubiya tazo. “Ya kamata dai mu koma ni banga amfanin zuwa nan ba sam.” Cewar maimartaba yana k'ok'arin juyawa ya fita, babu wanda ya tanka bare yajuya su tafi sai hajja yakolo da har lokacin jikinta be dena rawa ba,ganin har ya shiga mota amma basu fitoba yasa shi tura security guda d'aya yace yaje ya kirasu idan ba haka ba zasu tafi, koda yaje tarar dasu yayi duk sun zauna suna mayar da yadda suka ganta ya rissina bayan yayi sallama ba tare da ya kallesu ba yace. “Ma'am Maimartaba yana jiranku.” Kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, “Kace mai mun dawo gaba d'aya.” Ya kuma russunawa sannan yafita,koda ya sanar da maimartaba be nuna damuwa ba saidai hamkalinshi ya tashi amma bazaka gane hakan ba sai a cikin ranshi drive yaja suka bar gidan hajja yakolo kuwa kirjinta banda bugawa babu abinda yake yi har suka isa gida kowa ya wuce apartment d'inshi. Sam hajja yakolo k'in bari tayi su had'u da hajja gajiram sabida batama san abinda zata ce mata ba,da k'anwarta ta buga mata waya cewar gata nan zatazo sutafi sai tace mata kawai ta wuce gida ita tagama abinda zatayi ta tafi wani gurin a haka suka rabu shi kuwa sarki Aliyu hydar sam bema san abinda ke faruwa ba suna ciki shida Meenah sai wasan b'uya suke yi dan sam Meenah tak'i bari su k'ara had'a idanu. Cikin dare ko'ina tsit kakeji a cikin shehuri musamman idan ka fito wajan lokacin ne Hajja gajiram ta fito hannunta d'auke da maganin da boka ya bata wanda ta sanya shi cikin buta,sanye take cikin doguwar riga mai d'an girma ta yafa wani zani a kanta a haka ta sulale tayi apartment d'in Maimartaba sarki Aliyu hydar ... A hankali ta dinga tafiya har ta shiga ciki duk da cewar akwai dogarawa amma basu hanata shiga ba tunda suna ganin itama uwace a gurin shi, tana shiga ta fara lek'awa parlor sai ta hangeshi kwance kan three seater tayi murmushi sannan ta koma baya sam bata san ba bacci ya keyi ba dan gaba d'aya zuciyarshi babu dad'i saboda sosai yaga tsoran shi cikin kwayar idon Meenah ya rasa meyake mishi dad'i ya mik'e da kyar ya fara zagaye d'akin kamin ya wuce bathroom wanka yayi tare da alwala ya shimfid'a pray-mat ya hau ya fara sallah,ita kuma hajja gajiram tana waje tayi sib'itir tana aikin da boka yasa ta tana k’ok’arin binne maganin da dubura yana sallah yaji ana magana a waje tun yanaji kad'an-kad'an har dai yajiyo sosai yayi saurin sallamewa ya fito wajan dai-dai lokacin yareemah babagana shima ya shigo dan yaga shigowarta sannan kuma side guda maimartaba sarki Aliyu hydar ya bashi anan cikin nashi kan cewar kafin billy ta dawo,da sauri ya shige d'aki jikin shi na rawa idanunshi ya fara kankancewa kafin yaji ya sulale a k'asan gurin ya fad'i murya k'asa-k'asa yake furta, “Mami! Mami!! Mami...!!!” Shima maimataba sarki Aliyu hydar yana ganinta ya fara waige-waigen ko zaiga mutane ganin babu kowa yasa shi furta kalmar “innalillahi'wa'inna'ilaihir raji'un” Daa k'arfi hakan yasa hajja gajiram yin wurgi da layar hannunta tana zaro ido ganin sarki Aliyu hydar a tsaye a kanta ya juya mata baya. Rigarta ta raruma ta sanya a bai-bai tsabar k'id'ima ta fara niyar guduwa maimartaba maimurabus ya shigo apartment d'in ganin zata gudu yasa shi saurin rikota,kamar wasu yara haka suka dinga ja in ja Allah ya temaki shehu Bulama ya rik'eta kam kafin ya fara k'ok'arin janta suka koma nashi apartment d'in har yajata ciki tana turjewa tare da furta kalmar hakuri karya tonamata asiri ta tuba tabi Allah ta bishi amma fur saida ya sadata da d'akinshi ya wuce can kurya cikin wani kyakyawan akwati ya bud'e tare da janyo wata zungureriyar takobi sai faman shek'i taki yi ya koma kusa da ita sai faman runtuma mai ihu take yi ya sanya mata cikin hannunta tare da kwanciya a k'asa yace. “Kasheni ki huta da duk abubuwan da zasu dinga sanyaki aikata shirka.” “Wallahi baba tana kashe ka nima zan kasheta sannan in kashe kaina damani k'arashe ne sannan naga duk abinda ya faru akan idona na gani.” Dirim dim!!! Suka jiyo muryar yareemah babagana a bakin kofa yana hawaye idanunshi sunyi jawur tamkar garwashi dama shine ya kirawo mahaifin nasu yaje ya gani,shi kuwa sarki Aliyu hydar da sauri ya koma ciki,d'akin Meenah yaje ya bubbuga taji shi cikin wani irin murya hakan yasa taje ta bud'e tana bud'ewa ya fisgota seda ya rarumi labbanta yashiga sumbata na wasu yan dakikai nutsuwa tashige shi sannan yajata suka fita suka bi bayan babagana anan suka had'u duk suna cikin tashin hankali.... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```Edited by```: ```Ya hajja ce``` ```nanahafsat.wordpress.com``` *75* “*N*ayi dana sanin kasancewata daga cikin tsatson ki Mami domin ked’in abar kyama ce”cewar Yareemah Babagana dake matsar hawaye Yana magana ne yana karasawa cikin parlorn ya yinda su sarki Aliyu Hydar ke biye dashi a baya gimbiya Meenah kuwa faman mutsitstsikar idanuwa ta shiga yi don tabbatar da mafarki take... Jikin hajja Gajiram in banda rawa ba abinda yake, “Tur da samun u...”be k’arasaba mai martaba mai murabus yai saurin dakatar dashi,, “Ya isa Babagana ya isa...Mahaifiyar kace be dace ace kana gaya mata irin wa’innan maganganun ba..Kayi hak’uri kaji?!shi Allah...” Kukan Falmata ne ya tsaidashi daga maganar da ya kewa Babagana cikin kuka face face ta k’araso parlorn ta xube agaban shehu Bulama hawaye d’aya na bin d’aya tashiga zayyane abinda yakawota, “Baba kayi mun rai,ka jik’aina Baba” Dubanta Shehu Bulama yai cikin taushasshiyar muryarsa irin ta iyaye nagari yace da ita, “Allah shine ma mallakin rayuka Falmata,domin shid’in mabuwayine gagara misali..” Kad’a kai Falmata tashiga yi.. “Baba na aikata babban lefi wanda bansan da wane idanuwan xan dubi Allah ba ranar gobe kiyama” “Kayya Falmata kisani ce fa Allah gafururrahim ne majik’an bayin sa ne a kowane yanayi..” Shiru tai na yan wasu dak’ik’ik’ai kafin ta ce, “Baba...Baba...Duk tarbiyar da ka ginata akaina na rushe ta ta hanyar..” Shiru tai tasanadiyar kukan data k’ara rushe wa da shi.. Meenah da ke gefan Aliyu se duban yan parlorn take da kallo tasake shigewa jikin Aliyun hannunta cikin nasa kamar wanda xa’a k’wace shi dariya ma taso tabashi ya dake kawai cikin zuciyarsa kuwa inbanda takaici ba abinda ya lullubeshi duba da irin ha’ula’in da Gajiram da ‘ya’yanta suke neman sanyasu aciki.. “To muna sauraron ki..Kilan ma duk cikin set up din Mami ne..” cewar Babagana daya fad’i hakan cikeda takaici hade da sakin wani bahagon tsaki ji yake kamar ya shakosu itada Mamin ya rufe su da duka koya samu sassaucin abinda yakeji a zuciyarsa game da su.. Hannu Shehu Bulama ya d’aga masa sannan ya juya ga Falmata da tai wuri wuri da ita, “To ina sauraron ki Falmata..” “Baba..Hakik’a na aikata mummunan lefi wanda da farko banyi niyyar sanar da kaiba dubada irin tarbiyyar da ka d’orani akanta amma nasa k’afa nai fatali da hakan, “Wanda ba kowa ne ya ja mun ba face Mami..Nayi nayi ta kyaleni nai aure tun shekarun baya tak’i ni kuma baba na matsu matsuwar data kaini ga halaka..Baba kayi hak’uri ta sanadiyar hakan harta kaini ga.. “Rabuwa da mutunci na na rabu da martaba ta baba ciki harda samun ci...” “Cikin shege ko Falmata?!”cewar Babagana hade da rafka mata uwar harara Tashi yai yana huci xe bigeta sarki Aliyu yai saurin dakatar dashi ta hanyar rik’e hannunsa yana girgiza masa Kai, “Kayi hak’uri baa babs kaga ba ishasshiyar lapia ce da ita ba..” Bakin magana Shehu Bulama ya rasa se binsu kawai yake da kallo yarasa ta cewa gabaki d’aya jikinsa ya yi masa sanyi hannunsa yasa agefan zuciyarsa ya dafe wajen saboda baraxanar fad’uwa da wurin yake masa,Hajja Gajiram dake gefe a tsakure se wuri wuri take da idanuwa kamar na mujiya Meenah kuwa binsu kawai take da kallo mamaki karara kwance a akan fuskarta.. Ahankali cikin k’asa da murya hannunsa dafe akan kirjinsa shehu Bulama yace, “Abar wannan muhawara zuwa da safe dubada yanxun dare ne..Dare mahutar bawa yanzu ba lokacin mu bane karmu shiga hurumin ababen da mu d’in ba ma gani..” Kad’a kai Babagana yai yana huci,sarki Aliyu kuwa karasawa yai kusa da shehu bulama ya temaka masa yakaishi d’akinsa Falmata kuwa inbanda hawaye ba abinda take, Komawa apartment d'insu sarki Aliyu hydar yayi jikinshi duk yayi sanyi Meenah na mak'ale dashi ganin ya bi dasu ta guri mai duhu,suna shiga parlor'n Meenah ta fara zame jikinta daga nashi yayi saurin kankame ta jikinshi yana faman rintsa ido. Bedroom d'in shi yajata suka tafi suna shiga ya kulle ta hanyar sanya security ba tare da ya bari ta fahimci hakan ba ya jata zuwa bed d'in shi ya kwantar da ita tare da kwanciya a kusa da ita Meenah dake cikin blanket sai faman rarraba idanuwa take jira kawai take taji ta inda zai fara, bata gama tunani ba taji hannunshi cikin k'irjinta yana rage zafi,ita kuwa jikinta ne ya hau rawa ga uban d'in bin tambayoyin da take son yi mai na game da zuwan su apartment d'in babah da abinda taji suna ta magana amma sam ya kanainaye ta hanata tabuka komai. Meenah bata sake ko motsi ba taji yana sauke wani uban numfashi kafin ya matseta a jikinshi tamkar zai maida ita cikin shi. Murya k'asa-k'asa ya manna tattausan lips d'inshi cikin kunnanta yace, “Kinyi bacci ne?!” Meenah ta zaro ido tamkar yana ganinta tayi kamar bata ji ba,sake tambayar ta yayi ta kuma kudundinewa tana rintsa ido yace. “Au baza ki gaya min ba toh ina jin haushi na kikeji dan banje gaba d'aya bako?!” Girgiza mai kai tayi alamar a'a yayi murmushi ya sake shafarta yana kokarin juyo da ita,gani yayi idanunta gam yayi murmushi tare da zura bakin shi cikin nata yana tsotsa a hankali,ya dad'e har sai da yaja ra'ayinta itama ta fara taya shi ba tare da tasani ba har sai da ya tabbatar da itama taje limit d'in da yaje sannan ya rabu da ita ya sake cewa. “Muje muyi wanka nasan kema yanzu dole kina bukatar yinshi.” Da kyar ta samu damar yin magana tana rufe ido tace. “Zanyi amma ni dai ba tare zamu yi.” “Why..!?” Ya tambaya yana sake makalota zuwa jikin shi,tayi shiru dan bata san abinda zata ce mai ba kawai dai tasan baza ta iya yin wanka tare da shi ba salon iskanci kawai. Tashi yayi a hankali ta saci kallonshi har ya shiga bathroom, ya d'an jima a ciki sannan ya fito duk a tunaninta wankan yayi tayi saurin rintsa ido tamkar me bacci,ba zato bare tsammani kawai taji ya zare blanket d'in ya sureta suka nufi bathroom d'in tun tana zallewa har ta hakura sai da suka gama sannan suka fito sai turo mai baki take yi, kofa ta nufa da niyar fita tajita lock tayi saurin juyowa sai taga sam ba ita yake kallo ba har ya gama shiryawa sannan ne ya kalli inda take tare da sakar mata murmushi yana kashe mata ido d'aya. “Dan Allah ka bud'e min kaya zan d'akko.” K'arasawa yayi inda take jikinta d'aure da towel ya finciko shi gaba d'aya sai gashi a hannunshi ya bita da kallo, ai kuwa tayi saurin yin k'asa yayi dariya ya k'arasa tare da d'aukarta ya kaita kan bed,blanket ya janyo ya lullub'a mata sannan yakai bakin shi kan goshinta sannan yace a hankali. “Sleep Meenah please.” Juyawa yayi ya koma bathroom dan d'auro alwala yayin da ya bar Meenah kwance cikin d'in bin mamaki da al'ajabi ganin shifa ba damuwa zai yi ba tunda bashine zai kwanta a haka ba, da sauri ta sakko ta bud'e gurin kayanshi tana hango underwears d'in shi ta d'auki sabuwar vest fara kal ta bud'e ta sanya sannan ta hango trunk tayi saurin d'auka ta sanya sim-sim ta koma ta kwanta,tana jin shi ya fito ya tada tun tana ganinshi har bacci yayi gaba da ita hankalinta kwance. Ab'angaran su Hajja Gajiram kuwa lokacin da su Aliyu hydar suka wuce basu kulasu ba ya sanya Falmata sakin wani kukan, rarrafawa tayi kusa da yareemah babagana tana kuka harda majina ta fara k'ok'arin riko mishi kafa yayi saurin matsawa tare da zabga mata wata uwar harara murya a dashi yace mata yana nunata da yatsa. “Karki sake ki tab'ani domin ba wai wani abu kikai na daban ba, nima d'in da kike gani na bawai tsira nayi daga tarkon da kika fad'a ba. Falmata kinsan 'yan mata nawa na b'ata?duk da cewar cikin su duk da yardar su ba zan iya k'irgasu ba,mutum d'aya ce a duniyar nan nayi raping d'inta kuma itace wadda sanadin hakan yasa nayi kuka da hawaye na na fad'a tarkon wutar azababbiyar kaunarta yanzu haka ta guje ni zuciyata zafi takeyi saboda rashin sanyata a idanuna da banyi ba, wallahi nayi nadamar abubuwan dana aikata a baya,tunani na ne yake gaya min cewar kud'i suna maganin komai sai gashi na kasa siyan soyayyar bilkisu dasu,ina sonta sannan nasan idan bata dawo gareni ba kaunarta itace silar barina duniya, “Kakaf cikin 'ya'yanki mami babu wanda bashi da tabo,babu wanda be kona zuciyar mahaifinmu ba amma Ammi fa?duk irin abubuwan da kuke kulla mata da yake zuciyarta a tsarkake take gashi nan kullum ita da 'ya'yanta sai bunk'asa suke mu kuma daga wannan bala'in sai wancan yau ina cikin bakin cikin rayuwa Mami idanuwana sun..." Ya kasa k'arasawa saboda sark'ewa da maganar tayi yayi saurin juyawa yabar musu gurin hawaye na bin kuncin shi zuciyar shi na zafi tamkar zata tarwatse. Hajja gajiram ta fashe da kuka yayin da Falmata nta bita da kallo tana dafe da ciki wanda take jin tamkar ta luma mai wuka ko abinda ke ciki zai mutu dan bata fatan fitowar shi duniya, basu tashi daga gurin ba nan suka ci gaba da zama Hajja gajiram najin tamkar idan ta fita kowa zai san halin da aka ganta a ciki. *DAMBOA ROAD* Se juyi yareemah Ngari yake a kan gadon baccinsa idanuwansa arufe yaketa furta kalmar, “Innalillahi wa’inna ilahirr raji’un..Ammi su Mami xasu kashe ni Ammi da wuk’a xasu yanka ni..” Firgigit yatashi yana maimaita salati yayinda k’ararrawar dake dauke adakin Ammi tashiga kara hakan yana nuni da something s wrong a sashen Ngari da sauri Ammi dake sallar nafila akan sallaya ta sallame dama ta idar da axama ta mike tai hanyar sashen Ngarin yaruwaiya na biye da ita abaya ko dankwali babu akanta kowannensu fuskarsa d’auke da damuwa gani suke wani abun ne yasake faruwa dashi dubada irin alkaba’in d’aya faru daxun.. Shigar su dakin Ngarin yayi dede da mikewar Ngari daga kan gadon yana ganin Ammin ya mike ya nufe ta fuskarsa duk ruwan hawaye ne da sauri ya rungumeta tsam kamar wadda xa’a kwace masa ita cikin muryarsa daddad’a yace, “Ammi....” Rufe idanuwa Ammi tai ta bud’e baki hangame ta dube shi tana murmushi kafin tace, “Alhamdulillahi..Allah kaine abun godia” Tana k’arasa fada ta fuskanci gabas tai sujudish shukru wato sujjadar godia ga Allah.. “Ngari..”cewar Aunty yaruwaiya cikeda dadi tasake cewa, “You can talk again...Alhamdulillah what a blessing!”tafad’a tana hawaye Murmushi kawai yayi mata kafin ya sake rungumo Ammi kowannensu yana hawaye ahankali Ngari yasa Ke cewa, “But Ammi nayi mafarki mara kyau..” “Akan menene Ngari?!”cewar Ammi fuskarta cike da damuwa... Girgiza kai yayi kafin yace, “It was about my past..Ance ba kyau mutum ya fad’i mafarkin dayai mara kyau..Kede kawai kicigaba da mun addu’a” “Insha Allah Ngari Allah xe cigaba da kareka mugun nufin su yakoma kansu” Hannun Ammi ya d’auka ya d’ora akan bakinsa yana hawaye,cikin rawar murya yace, “Ammi ki tashe ni daga mafarkin dana keyi Ammi..Dagaske ni ne nake magana bayan kusan shekaru talatin bana yi?!” Girgiza kai Ammi tai hawayen dadi se kwaranyo wa yake a fuskarta, “Ngari ba mafarki kake yi ba kai d’inne kake magana Allah yakawo k’arshen komi kasan dama duk runtsi to fa akwai dadi a gaba” Kad’a kai yayi yana murmushi kafin ya dubi aunty yaruwaiya dake hawaye dan murmushi yai cikin sanyayyar muryarsa yace, “Aunty yaruwaiya kela yasken(kitson gaba)ki yayi kyau” Dan dukan wasa takai masa tana goge hawayen dake kwance akan fuskarta,hannuwanta tasa tana taba gashin kanta, “Dankari yo aini banma san ba dankwali akai na ba oh ni rukayyah da wannan uban daren..” Daria suka saki dukkan ninsu sannan daga bisani tai musu sallama tafice da sauri don tsarkake kanta Ammi ta jima awajen Ngari har asubah tatemaka mashi yai alwala ya tsarkake jikinsa da ruwan adduoin ganyen magaryar da ake mashi bayan yayi azkhar na subhi, Seda Ngari yace taje ta huta dakyar tafice ta ta koma sashenta sosai yanxun takeji kamar and’au ke mata wani gundumeman dutse azuciyarta don dadi..ya jima yana addu’oin kariya kafin daga bisani yakoma ya kwanta don sam beyi wani baccin kirki ba.. Wajan misalin k'arfe 6:30am Aliyu hydar ya d'auki wayan shi,layin Ammi ya shiga nema ta dad'e tana ringing dan har sai da ta kusa tsinkewa sannan yaji ta d'aga tare da yin sallama kai daga jin muryarta kasan tana cikin farin ciki. cike da ladabi kamar yana gabanta ya gaishe da ita sannan yace. “Ammi yanzu zan shigo nasan anjima bazan samu ganinki ba.” Ammi tayi murmushi muryarta a sake fiye da yadda ya saba jinta yaji tace mai, “Toh rankashi dad'e ai ni na koma gida tun jiya yanzu haka inada babban albishir da zanyi maka amma sai ka fara bani tukwaici tukunna.” Murmushi sarki Aliyu hydar yayi tare da k'ara manna jikinshi dana Meenah yace. “Ammi ai duk duniya banga abinda zan d'aga nace zan baki shi ba a matsayin tukwaici sai dai nace Allah ya kara kauna tsakaninki da babana.” Ammi tayi dariya mai sauti sannan tace, “Amma hydar wai tukunna ma ina 'yata take.” Ido suka had'a da Meenah wadda ke faman kad'a mai kai alamar karya ce suna tare yayi murmushi tare da shafa gashin kanta yace, "Ammi gata nan in bata ku gaisa..?!” Ya tambaya yana kashewa Meenah ido d'aya tayi kicin-kicin da fuska dan baza ta iya yin magana ba gani zata yi kamar Ammi zata gano abinda suka yi,cikin sa'a kuwa taji Ammi tace. “A'a kabarta har sai lokacin da zata d'auki waya ta kirani kamar yadda kayi.” Tayi maganar tana dariya shima yayi murmushi sannan yace, “Toh Ammi albishir d'in da za'a gaya min fa?!” Ammi ta kuma murmusawa tare da cewa, “Baah ya warke yanzu da bakinshi ras zan baka shi ku gaisa amma sai anjima dan sai ya fara yiwa babanku tukunna.” “ What? Ammi Alhamdulillahi bari na taho ni yanzu, ash sorry Ammi babah yana cikin damuwa ina jin ma yanzu haka k'ila a had'a meeting na gaggawa anan cikin shehuri.” Sarki Aliyu hydar ya fad'a cikin tashin hankali Ammi tace, “What's wrong hydar?!” Kasa fad'a yayi domin maganar babbace baxai iya gaya mata ba dan haka yace, “Sorry Ammi but...but bazan iya fad'a ba da bakina.” “Ok tohm Allah ya kyauta bari na kirashi naji.” Bata ko bari sunyi

Chapter 29 of 35