Share this page
ganta cikin mamaki ta tambayeta, “Bilkisu lafiyar ki kuwa ina zaki haka...?!” Bata juyo ba ta shiga toilet tana cewa, “Umma kashi nakeji wallahi.” Shiga tayi sai da ta dad'e sannan ta fito rik'e da baya kafin ta zauna ta sake komawa Umma tace, “Ina kuma zaki koma bilkisu?!” “Wayyo Umma fitsari wallahi kashin ma yak'i yi kuma inajin shi.” Bata dad'e ba ta sake fitowa tana k'ok'arin sake zama ta kuma cewa fitsari Umma na ganin haka ta fara kokarin kiran abba a waya yana d'auka tace, “Malam sai ka dawo gida domin ga bilkisu nan ta fara nak'uda.” Ai abba yana jin haka ya taho gida a hanya ya bugawa yareemah babagana aikuwa a tare suka dira motocin su a kofar gidan domin dama shima yareeman yana hanyar zuwa gidan. Umma kuwa ta d'an harhad'o duk kayan da tasan za'a buk'ata dan haka abba na shiga lokacin abun yayiwa Billy tsamari ya kamota bayan an sanya mata hijjab, a motar yareemah babagana ya sata suka tafi shida Ummi abban kuma suka tsaya k'arasa d'aukan abin buk'ata sannan suka bi bayansu. Cikin ikon Allah suna zuwa aka wuce da ita labour room,drip kawai aka sanya mata da wasu allurai a ciki (inducing)kafin wani lokacin billy ta haifo kyakyawar 'yarta, wani nishin akaji tana yi nan fa aka kuma dukufa shima ba jimawa sai ga baby ta biyu, sunsha mamaki dan duk sanda sukaje scanning cewa akeyi d'aya ne ashe Allah ya boye abinsa. Sai da tasha d'inki daga nan wani wahalallan bacci yayi awan gaba da ita, lokacin da aka kawowa yareemah babagana yaran ya gansu ya tuna cewar nashi ne halak malak sai kawai ya saki kuka baji ba gani abba ya buga aka sanarwa da shehu bulama kafin wani lokaci sai ga Ammi,Allah sarki Ammi inuwar giginya ce kowa yana shigarta yasha inuwa mai dad'i. Shiga yayi cikin d'akin hutun da aka kaita, bacci takeyi hankali kwance fuskarta tayi fayau yareemah babagana ya rik'o hannunta yana hawaye yasan da idanunta biyu sai ta mazge shi sabida ta tsaneshi bata son ganinshi, a hankali ya tashi ya kwanta a jikinta ba tare da ya sakar mata nauyinshi ba.ya dad'e a haka kafin ya zauna kusa da ita kaunarta da soyayyar na k'ara bin sassan jikinshi anan su Ammi suka shigo suka tarar dashi. Sai bayan sallar magrib sannan billy ta farka idanta tar akan yara guda biyu dake hannun kanwar Umman ta wato yakumbo Dije murya k'asa-k'asa tace, “Yakumbo nah.” Yakumbo ta mik'e da sauri da yaran a hannunta ta k'ara bakinta bud'e tace. “Sannu 'yarnan sannu kinji Allah ya saukeki lafiya mun gode mishi.” “Yakumbo kuma biyu na haifa a cikina?!” “Eh kuwa bilkisu gasu ma kuwa yaran sak mahaifinsu farin ne kawai naki.” Nan da nan billy ta saki kuka haka ta dinga yi ba k'ak'autawa sai da tayi mai isarta lokacin su Ammi sun dawo aka samu ta basu nono suna sha tanajin wani kaunar yaran tana shigarta,bayan sallan isha'i suna zaune a d'akin yareemah babagana ya shigo be kalleta ba ya kalli Ammi yace, “Ammi ku d'akko yaran mu tafi gida.” Ai billy najin haka tayi saurin rungume guda d'aya a jikinta tana kokarin kwatar d'ayan a hannun Ummi yareemah babagana yai saurin rigata ansa yace, “Meye naki a ciki? Da bakinki kika ce bakya so kin tsanesu dakin haihu za'a kaisu gurin mahaifinsu, toh yanzu kin haihu zan tafi da yarana na samu me shayar dasu bani d'ayar.” Ta fad'a tana kokarin kwace ta hannunta, kuka ta farayi tana buge mai hannu cikin tashin hankali da kuka tace, “Wallahi karya ne ni bance haka ba kabar min yarana wallahi baxan baka ba ai ba wani ya haifar min suba nawane...” Mutanan d'akin suka fara musu dariya ganin yadda take kuka ne yasa shi mik'a mata d'ayar babyn tayi saurin karb'a tana sauke ajiyar zuciya dama can haushin shine ya shafi cikin. Kwananta biyu a asibiti aka sallamesu, babagana yayi matukar yin k'ok'ari daga 'ya'yan nashi zuwa uwar harma da iyayanta ta,sai dai da kyar maimartaba mai murabus ya taushi zuciyar shi aka sanyawa d'aya sunan hajja gajiram wato hasanar usainar kuma sunan Ammi aikuwa tayi murna da farin ciki,sannan da ita akayi komai bata kyamar talaka mutane har mamakinta sukeyi yadda suka ga ta zage sai abubuwa take taya su.Anyi suna lafiya su Meenah, Basmah,layla, Aisha (kiara) duk sunje suma anyi suna dasu hakan ya k'arawa babagana kaunar Ammi duk wani abun suna kuma sai da Ammi ta d'auka akaje aka turawa hajja Gajiram cikin kejin da take, wani taci wani ta b'arar wani ta yagalgalashi haka ta dinga yi calander hotunan yaran kuma ta cire d'ankwalinta ta goya wai tayi yara Allah ya kawo sauki. Ranar wata weekend Aliyu Hydar da Meenah sunje asibiti awo daga nan suka biya gidan yareemah Ngari dake wani sashe a shehurin xaune suka samu Ngarin da matarsa Asmy a garden dinsu suna xaune kayan marmari a gabansu hankalinsu kwance sunyi mugun dacewa,zaune yareemah Ngarin yake yayi xaman k’asaita ita kuma Amarya Asmy tayi pillow da cinyarsa hannunsa kan gashinta yana shafawa suka jiyo sallamar su Aliyun akansu da sauri Asmy ta mike xata tashi Ngari ya rik’e ta, “Babe Ina xaki?!” “Mon Amour I need to cover my head,scarf dina yana ciki” “Oh..”cewar Ngari sannan yai pecking dinta a kumatu ahankali kamar me rada cikin kunnenta yace, “I love you...come back soon” Kashe masa ido d’aya tai sannan ta mike tashiga ciki,karasawa su Aliyu sukai dake faman shasshshafa keya murmushi Ngari yai bayan ya buga masa jarida akai, “Da magana abakin ka bruh” “Baa Ngari bakomi wallahi kawaide Ina admiring kinda love dnku ne Allah yabar ku tare” “Oh Yayi kyau..”cewar Ngari don bai cika magana ba Ahankali Meenah dake gefe tace, “Barka da rana baa,munsa meku lapia?!” “Lapia lou sisturh,Mungodewa Allah ya k’arfin jiki?!” Cikin jin kunya Meenah tai shiru kawai hade da sake sunkuyar da kanta k’asa mintina kadan Asmy tadawo bayanta wata baiwa ce dake dauke da trays da drinks da snacks akai ajiyewa tai agabansu sannan ta koma gefe ta xauna, “Sannunku da xuwa,Barka da yamma ranka ya dad’e maman baby hope babyn mu yananan lapia?” Amsawa Aliyu yai itade Meenah murmushi kawai tai kanta akasa don duk sanda aka ambaci ciki kunyace take lullubeta..Sund’an taba hira tare daga bisani Asmy taja hannun Meenah suka koma cikin gidah suka bar yan uwan junan tare nan suka shiga hirar zumunci cike da kaunar juna abinde se sam barka kawai.. Kodah suka koma gidah sashen Basma ya wuce yaga yadda take tukun sannan ya wuce fada a k’ofar fada ya tarar da Modu xe shiga ciki nan suka gaysa sannan suka k’arasa shiga ciki suka baje akan kujeru kasancewar ba kowa a fadar yamma tayi,Modu ne ya kece da daria yana faman shafa gemunsa tsaki Aliyu Hydar yai yana harararsa,cikin takaici da isa yace, “Kaga Malam idan bawani almuhim abune yakawoka ba katashi kabani waje plss” “Guy meyai zafi wani abune natuno ne daya faru a yola da muka je” “Yola kukaje kenan?!” “Nah tun yolan da mukaje dakai,kalmomin shekaru ukun nan still suna mun yawo akai abun har yau daria yake bani..” “Wane abune plss guy don’t ruin my mood abeg” “Katuno sanda kace idan ka auri Meenah baby sitting xakai don raino xa’a baka?!shine nake tunowa kuma yanzun yadda kai dying akan sonta dama na fada maka ai kaki yadda yanxu wa gari ya waya?!”Modu ya k’arasa fada yana sake kecewa da dariya.. Dogon tsaki Aliyu Hydar yaja lokaci d’aya kuma kyakkyawan murmushi ya fad’ad’a a fuskarsa cikin wata irin murya yace, “so ne yasani fadar haka believe it or not” “Kobah so ba” “Kai kasanni ai,kuma kasan yadda nake idan inason abu...Meenah means the world to me,to cut the long narration bantab’a son mace kamar yadda nakeson Meenah ba I love her so much I can sacrifice anything for her love..” “I hope tasani ko?!” “No sena samu time tukun she knws I loved her amma batasan son da nake mata yaxarce wanda take tunani ba” “Then warra you waiting for?!tell her mana kamar ba namiji ba” “No sena gama da abunda nasa agaba tukun” “Kai guy banajin baaba xe yadda da abinda kake shirin yi” “Seka hanashi ai..” “Nason is not easy but you just have to calm your self d...” Be k’arasa ba Aliyu yai saurin katseshi, “Kai I can’t aswr i can’t i I i i I just can’t guy bana samun time din kaina dana family dina for example Meenah yanzu tana bukatar kulawa agareni..” “Somehow true..” “Bawani somehow gaskia ne kaji” “To Allah yaxaba abinda yafi alkhairi” “Insha Allah rabbi alkhairinne ma..” “When xaka samu baban yacemun ze koma germany ko” “Yeah!kafin yatafi de zansameshi May be gobe ma idan Allah yakymu” “To Allah yakymu goben lapia” “Ameeeen” Da wannan suka shiga wata hirar daban sunayi suna tafawa.. _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏾_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```Edited by```: ```Ya hajja ce``` ```nanahafsat.wordpress.com``` *78* Wani mugun kallo mai cike da tsantsar tsana billy tabi yareemah babagana dashi, k'o'karin fita yaga tana yi daga cikin d'akin yayi saurin rik'ota tare da matseta ta baya a jikinshi yana shafar cikinta wanda yayi tudu ta sa hannunta ta ture nashi daga kan cikinta cikin masifa wadda be san tana da ita ba yaji tace, “Malam ka cika ni bana son wannan salon iskancin.” Tana matsen a jikin shi ya hura wata iska daga bakinshi zuwa kunnanta nan da nan kafafuwan billy suka fara rawa ya kuma hura mata iskar cikin kunne jikinta yayi sanyi ya sanyan hannun shi yana shafar wuyanta zuwa saman kirjinta, nan da nan sakon nashi ya fara shiga cikin kwakwalwarta ta fara lumshe ido tana sauke wani irin nishi ya fara murna kawai yaji tayi saurin kwace jikinta ta juyo tana hararar shi ya shafa kanshi idanunshi sun wani shanye cikin masifa ta kuma cewa. “Me ya kawoka gidan nan? Ina son dan Allah idan kai ba maye bane kafin ka fita ka bani takardar saki na domin bana son ka na tsaneka...!” “Kiyi hakuri my billy bazan iya sakinki ba iya wuya muna tare fata na ki dawo gare ni dan Allah wallahi tun abinda ya faru tsakanin mu na rasa nutsuwata soyayyarki ta sauya ni karki bari kuma ki gujemin domin idan kika yi min haka ban san yadda zanyi ba, a yanzu haka my Billy rayuwa ta tana hannun Allah tana hannunki sai yadda kika yi da ita, kyautata mata ko kuntata mata.” Kuka ta sanya a gurin shi kuma ya k'arasa gurinta, da sauri ta mik'e tana d'aga mai hannu alamar karya ta6a ta ya tsaya cak cike da tausayin ta yana ji tana yi kukan har cikin brain d'in shi.ya d'auki tsawon lokaci kamin ya tashi ya tafi bayan ya ajiye mata uban kud'i wanda ko shi besan ko nawa bane yayi masu abba sallama ya fita. A b'angaran su yareemah Ngari kuwa shirye-shiryen bikin shi ake tayi sannan sarki Aliyu hydar da kanshi yasa aka yo irin zanen gidan da za'a cancarawa yayan nashi tun daga India.. Cikin one month an kammala gini kasan cewar akwai kud'in a k'asa, cikin sati biyu aka fara gudanar da shagalin biki anan cikin shehuri kasan cewar itama Ammi an gyara mata apartment d'in kusa da mijinta shehu Bulama kasan cewar SB yace ta dawo kenan baza ta sake komawa damboa road ba tunda an riga an warware duk wani kulli daya haddasa barinta cikin shehurin yanzu hankalin kowa a kwance yake ba kamar su Meenah dan sarki Aliyu hydar da kyar yake iya fita fada dan ya raini Meenah da soyayyar shi salo-salo kuma yanzu ta zama kwararriya ga lecture din aunty yaruwaiya da suke b'ata kud'i a waya tana gaya mata hanyoyin mallakar miji ba boka ba malam dan haka yasha k'in fita hudubar juma sai gab da za'a tayar da sallah tukunna zai tafi ba kunya dan yama fara wani tunani kuma yana nan yana son aiwatar dashi jira yake ayi bikin Ngari. Alhamdulillah anyi komai na bikin yareemah Usman (Ngari)Shehu Bulama Goni da zankadediyar amaryar tasa Asmau(Asmy)Bunami Indimi Goni cikin jin dad'i da kwanciyar hankali lokacin layla tana watan haihuwarta ita kuma Kiara ta harbu sai dai ba'a tab'a ganewa kasan cewarta doguwa sai cikin yake bin jikinta,Basmah kuma da kyar da addu'a da rokan da Meenah ke mai akan shariyar daya kewa Basman ta samu Aliyu hydar ya karkato kanta dan yanzu ta riga ta b'arar da duk kusan rabin soyayyar da yake mata sannan kishi suke yi mai zafin gaske dan Meenah tana da tsananin kishi ko ranar da zai koma side d'in basmah sai yayi lallami sosai kafin ta barshi duk da shima ba a son ranshi yake barinta ba. Anyi bikin yareemah Ngari da kwanaki biyu layla ta santalo baby boy d'inta murna a wajan abokiyar zamanta wato kiara har kuka tayi dan har tafi Modu murna. Layla tasha matukar wahala wajan haihuwar dan kwananta d'aya tana nakuda mai zafin gaske har ta fara barin wasiya duk a tunaninta mutuwa zata yi. “Mommodu ina za'a kai layla ne? Kasan dai ba gidanka za'a maida ita ba.” Kallon layla Modu yayi sai yaga ta fashe da kuka, cikin ranta kuwa tunani take yi, “Shin ina za'a kaita, gidan babanta ko gidan da Ummanta take aure?!” “Queen meye na kukan kuma?!” Modu ya tambaye ta bayan Ammi tace kowa ya fita ya basu guri dan itama tun daran jiya tana asibitin, layla ta kalleshi cikin jan ido wanda yasha kuka tace. “Oud yazan yi?ina zaku kaini, bana son naje gida duk na takura musu duk da cewar ina da kud'in da zan iyayin komai amma Inna ta tsufa tana buk'atar hutu baxan samu kulawar da ake saka ran zata yi min ba,Umma kuma ban san yanayin yadda gidan da take aure yanzu yake ba ko akwai inda zan zauna oho...” “Shine kawai yasa ki kuka queen? Please bana son wannan kukan kin san dai idan Aisha (kiara) tazo taga kina wannan kukan wallahi na bani haka zata ce nine.” Dariya tayi sabida tasan gaskiya ya fad'a sannan ya kalleta cike da kulawa yana shafar kanta yace, “Karki damu wannan ba matsala bace, sai akaiki can shehuri gurin Ammi idan yaso gobe zan shirya naje can katsinan idan yaso sai a taho da wani wanda zaku zauna tare yayi miki ko? Ko kuma zaki bari kawai Ammi tayi miki..?!” Zaro ido tayi tana kallonshi yayi dariya yana d'aga mata gira tace, “Wallahi bazan iya yadda ba domin inajinta kamar itace sirikata, so na riga na haramtawa kaina yin hakan..” Yace mata, “Toh shi kenan yanzu ki dena sanya damuwa a ranki gobe zani can gurin su Umman.” “Toh my one and only oud,nagode kwarai Allah yabar mu tare” Yar harararta yai sannan ya mike ya fice sauran mutane suka shigo yan barka... Murmushi Laylan tayi hade da shafa kan babyn dayai kama da ubansa sak kamar yayi kaki ya tofar.. <><><> “Ajlaal..” “Ya Aliyus yus yus..” Dan dariya yai yana kokarin shafa saman k’irjinta tai hanxarin sa hannunta ta ture hannun tana pouting lips.. “Baby why are you avoiding me ne?!two days gaba daya kin hanani jin dumin jikin ki kina gasani wifey adan sassautawa shehun bornu mana” Tab’e baki tai hade da juya masa baya tana kokarin danna wayarta ya kwace yana mata cakulkuli a cikinta daria tashiga yi tana kokarin cire hannayensa, “Ya Aliyu zanci kwai..” Cikin shasshafa jikin Meenan murya kasa kasa yace, “Wanne irin kwai?!”hade da kashe mata ido daya Dukansa tai da throw pillow tana zumburar baki tace, “Negative minded to kwai soyayye nakeso round I mean circle..” “To barin sa a soya maki..”yakarasa maganar hade da saka hannu kan intercom xe kira masu aiki dake kitchen.. Saurin dakatar dashi tai ta hanyar cewa, “Ya Aliyu kai nake so ka soyamun” Gwalalo idanuwa yai yana shafa k’eyarsa cikin sauri yace, “Da wasa kike ko?!ajlaal bantaba abinci ba da kaina” “Common soya kwai baxaka iya ba?!To shikenan”tafadi hakan tana shirin kwabe fuska xatai kuka “No no no pls don’t..Zanyi zan soya” Yana karasa magana yafice yasauka kitchen dinsu yadakko crate din kwai yashiga bin kwan da kallo wayarsa yaxaro yashiga google ya danna ‘how to fry a circle egg’ cikin seconds aka kawo masa recipes din rigar jikinsa yacire ya ajiye a hanger abinka da maxa na aiki a kitchen atakaice seda ya karar da crate daya duk ya konar beyi circle shape dinba cikin gumi dumu dumu dukko da na’urar air conditioner din dake kitchen din hakan be hanashi xufa ba duk ruwan kwan ya faffallatsal masa ajiki Se tsaki yake yana mitar, “Darn it..”over and over again Dakyar yasoya kwan still beyi round ba yai oval shape, Sama yasake haurawa wajen Meenah bakinsa d’auke da adduar Allah yasa ta yarda taci oval din,dakyar yatura kofar dakin plate din hannunsa se rawa yake ya janjo table ya dora mata akai yana sosa keya, “Warris dis ya Aliyu,I don’t like this egg,it’s not round it’s oval I just want it round ya Aliyuuu I’m not hungry anymore” Kamar Aliyu xeyi kuka haka yaji, “Wifey bakici abinci ba fa,kalla I nearly spent 2hours akan soya kwannan pls babe kici kinji?!Babe but you said you were hungry look I made this egg so round the way you liked it” “No ya Aliyu it’s not round it’s oval..Na koshi I will make some coffee kawai” “To mexaki ci nai maki ordering?!” “Uhm wannan Milkshake,pasta,fries,shawarma,bugger,piz...” Shiru tai ganin yadda Aliyu yasaki baki yana kallonta gyara tsayiwarsa yai yana binta da kallon kauna, “Mrs Aliyu are you kidding me?! Kedin dabakya son cin abinci xansiyowa wannan bataliyan kayan?!” “Uhm kobah shi nakeso ba,kuma kuma kuma ai bangama ba” “Toh ina jinki” “Da dominos pizza da tsiren bakin hanyar bulunkutu dinnan na gefan titin nan inda motarmu yataba lalacewa..” Baki bude Aliyu ya gyada kansa ya rike ciki yashiga dariya ba kakkautawa pillow Meenah ta wurga masa da sauri yadena dariyar yadawo kusa da ita yai hanxarin janyota jikinsa yana cusa kansa cikin tulun gashinta dake kamshin strawberry shampoo, “Babe ko bakida lapia ne?!we need to c a doctor kince dama taste dinki ya canxa ko?!” “Uhm but it’s normal I think malaria ne don naduba signs din a google” “But yakamata mudega likitan babe savoda shan meds without the inscription of a doctor is dangerous to health..” “Fine amma ba yau ba” “Your wish is my command my queen..”yakarasa fada hade da bata peck a kumatu sannan yafuce don bayarwa asiyo mata abincin bayan ya tsaya a kasa yashiga dakinsa yacanxa kayansa zuwa shigar sarauta.. Kicib’us sukai da Modu a hanyar fita,harara Modu ya bishi da ita yana wani kallon sa sama da k’asa kafin ya dubi agogon hannunsa yana sake bin Aliyun da kallo tsaki Aliyun yai yana kokarin fita Modu yai bake bake ya hanashi cikin isa Aliyu yai murmushin gefan baki yana kallon Modun shima, “Mr Man Move..” “Ai idan kaga na matsa awajen nan sekaga yamun abinda kake aikatawa kaki fita fada har rana tafito haka kaiwai mutumin banxan inane?!kade bi ahankali guy kafin kaje ka sassauta masu ‘ya kaji wallahi rantsuwan Muslims babu ni a biko” Da hanxari Aliyu yaduba wristwatch din hannunsa seyanxu ya lura ashe yayi mugun kara lokaci akan yadda yasaba fita cikin shafa keyarsa cikeda kunya yace, “Ayimun afuwa..” Tsaki Modu yai yana duban paper hannun Aliyun, “Yau kuma kiran suna xa’ai a fadan kome?!” “Oh this,Alhamdulillah gashi ma temaka badan niba kasiyowa Ajlaal pls” “Mugani batada lapia ne ko me?!”Modu yace hakan tareda karbar takardan hannun Aliyun yashiga dubawa, “What the fuck...Mexan gani meye haka?!thought wallahi takardan magani ne..wannan tulin abincin fa baki xakuyi komi?!” Dan Murmushi Aliyu yai yana Shafa quarter million dinsa, “No Ajlaal ce xataci” “What?! To fa.,”Cewar Modu sekuma murmushinsa ya fadada, “Kode itama ta harbo jirginne?!Kai kai kai someone’s gonna be a dad..” “You are sick,Malaria ne fa shine ya canxa mata taste” Daria Modu yashiga yi seda yai mai isarsa sannan yace, “Kobah malaria ba?!to Allah yabata lapia guy,barin je”yafadi hakan tareda cusa takardan a aljihunsa sannan suka fita tare da Aliyun “But seriously guy yau fa katafka lefi kaga dignitaries din da suke jiranka a fada kuwa harda emir din kano sunusi lamido sunusi dana katsina Abdulmuminu kabir usman” Tsaki Aliyu yai yana kokarin gyara rawaninsa,ahankali yace “And so?!kai nakusa aikata plan dina fa wallahi nagaji..” Tuntsirewa Modu yai da daria harda su tangal tangal kamar xe fadi cikeda daria yace, “Gaskia fa ancuceka ga uban takunkumi dan Allah dube ka ka lallafta kaya ajiki sekace wani clown..” Tsaki Aliyu yai kawai yawuce Modu da sauri fadawansa suka kareshi suka shiga dashi fada..Ana cikin gabatar da shiri sarki Aliyu Hydar yai excusing kansa yashiga mini rest room din dake gefan fadar wayarsa ya xaro yashiga daddanawa yadan jima kafin ya mike murmushi fal kan fuskarsa ya koma fada, Meenah na kwance akan coach din dakinta text yashiga wayarta kamar baxata duba ba sekuma ta dakko ta bude tafara karantawa, _Mrs Aliyu you’ve changed my life for the better,I’m inspired to be different when I’m with you,I love your eyes I love your smile I cherish your ways I adore your style wot can I say?! You are one of a kind and 24/7 you are on my mind..Urs Aliyu_ Blushing Meenah tashiga yi tana murmushi hardasu hugging wayar tata tana pecking din screen din replying dinsa itama tashigayi, _As I lie awake in my coach all sort of thought run through my head,like why do I love you as much as I do then I realize it’s because you are you i love you too my king plus don’t forget about my foodies and I also want agwaluma plss_ #Uzuri🙈🙈🙈🙈 _Munkusa k’arasawa saura kad’an plus ina barar addu’oinku pls exams ga project...Nagode kwarai Allah yabar zumunci...Wannan shafin nakune masoyan matar yusleem ni Nana Hafsatu ina miko dimbin gaisuwata agareku tirela tirela#oneLove#😘_ _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```Edited by```: ```Ya hajja ce``` ```nanahafsat.wordpress.com``` *80* *END...* *G*urfane sarki Aliyu hydar yayi a gaban maimartaba maimurabus yayin da gefe guda Ammi ce take dama fura da nono kasan cewar baya son shan wadda akayi blending d'inta,kusa da Aliyun kuma yareemah Ngari ne da yareemah babagana sai Modu a kusa da Ammi duk girman parlor'n amma yaje ya nanik'e mata. Shehu Bulama ya gyara zama yana kallon Aliyu hydar yace, “Ranka ya dad'e kai muke jira ka taramu kayi shiru sai faman kallonmu kakeyi ince dai lafiya ko?!” Kuma gyara zama Aliyu hydar yayi tare da shafa gashin dake zagaye a fuskarshi,sunkuyar da kai yayi yana neman ta inda zai fara dan kowa na gurin shi yake kallo ganin haka yasa shi cewa. “Amm....Dama....Baba abinda yasa nace zanyi magana daku akan maganar kujerar da nake kai ne..” Yayi shiru su kuma suka sake zura mai ido danjin k'arin bayani,shi kuma ya sake sunkuyar da kai sannan yace. “Ina son na sauka daga kai na bawa d'an uwana zaifi kulawa da ita sannan shine yafi cancanta da ita ba niba,ina son na sauka na bawa baah Ngari dan Allah karkuce a'a tunda duk d'aya ne nida shi.” Bak'ara min mamaki kowa yaji ba amma banda Modu kasan cewar tare suka shirya komai,baki bud'e shehu bulama yake kallon Aliyu hydar kafin ya d'ora Modu ya karb'e zancen da cewa. “Haka ne baba wallahi gara ya sauka ya bawa wanda zai iya dan wannan sarkin kawai cukwan kujera ne amma baya komai sai tara mutane yana binsu da eh ko

Chapter 32 of 35