Share this page
ahankali “Toh Allah yamaki albarka babe...thou de nasha raki wayyo aunty furera kizo kitemakeni”ya fada yana kwaikwayon muryarta, Saurin rufe masa baki tai tana daria ahankali hankalinsu kwance shafa kanta yai ahankali yace, “Jeki had’a mun ruwa nai wanka xanje gidan yayarki(kiara)” “Okay oud”sannan tamik’e tashiga band’akin Bayan yayo wankan ita tatemaka mashi ya shirya sannan yatafi gidan kiara sosai yanzu kam layla tasamu nutsuwa komi Modu yana masu da kiara baya nuna banbanci yana iyakar kokarinsa ganin kowacce yabata hakkinta dake kansa to haka sudinma suna iyakar k’ok’arin su wajen faranta masa... Da sallamarsa yashiga gidan kiara tana xaune cikin mini skirt da half vest kanta ba dankwali tayi parking d’insa da sauri tarungumeshi tana bashi butterfly kiss a cheeks d’insa, “Hun pie”yace da ita yana xaunar da ita akan laps d’insa... “Handsome bae” “Baby bout that...uhm audio you promised or you ain’t gonna...” Saurin katseta yai ta hanyar sa hannunsa a lips dinta, “Why won’t I precious one?!here you go..”ya k’arashe maganar tareda d’akko wayarsa ya kunna audion Na salafiyya Aka pharmacist myriam dayake magana akan, “My dear daughters of Adam you are all beautiful: *Rejoice you are the queens of islamThe Queens of jannah!* You are The servants of Allah your creator and not servants of dunya! *You are covered with hijab like diamonds and pearls in it's shell!* You travel only with bodyguards that are your mahram so that no man can have access to you that easy or molest you because you are precious like the queens and princesses! Your prophet is the best man that ever existed!!! Your mothers are Ayesha and khadeeja and Maryam and asiya that were such a great women that they left their prints in every heart and history with their hearts and minds not with their looks and body these women that changed the world! You are not the color of your nails or the color of your lipstick or no! You are worth more than that you are a heart and a soul and a mind that think! *You are miss eternal jannah not miss temporary fake fading dunya!* Oh my sisters how beautiful you are when you walk in the streets covered preserved like Queens that men respect you and lower their gaze on you!! They see you as a "red warning botton " instead of "available green botton"!!! A man have to ask your hand from your bodyguards"mahrams" and make you his wife to be able to touch you and see you and have you just like an expensive diamond what an honor Allah gave you my sisters!!! Smile my sisters you are muslimahs a free women as Allah say:" so they will be known (as free women) and not be molested(by perverts)" Quran Surat al ahzab Sau biyu audio din yana karewa kiara na dawo dashi baya tana sakeji ahankali bayan ya k’are ta Kalli Modu, “Babe whos this Ayesha?!” “Ayesha she’s the wife of our beloved prophet muhammad SAW,actually my name was derived from his...” “Sounds cool..what of Maryam?!” “Myram s Mary the mother of prophet isa that’s uhm Jesus” Kad’a kai kiara tai tareda sa hannu tana shafa beards d’insa, “Babe I really really want to knw more abt prophetic histories I want to learn something new like that of prophetic Moh sunnas you said a day before yesterday...” “Okay hon right away”cewar Modu sannan yad’akko wayarsa yashiga bud’o tarihin annabi SAW yana bata sosai take ganewa fuskarta d’auke da Murmushi... *SHEHURI* “Yakolo Ina cikin tashin hankali fa” “Yayya wai menene yake faruwa sam nakasa gane Kan wannan matsaloli?” “Kibari kawai yakolo bankadaddiyar yarinyar nan shegiya data samu gidan jin dadi andakkota daga halin rashi tashiga samu wai har itace xataki amincewa da babagana?” “Banganeba yayya” “Da hausa fa nake magana yakolo,Toh na karkare maki xance de matar babagana ce taki amincewa ya kusanceta” Salati da sallallami yakolo tashiga rafkawa tana tafa hannuwa rantsuwa ta kwaso ta dire kafin tace, “Kinsan Allah yayya ba haka aka bar suba nifa dama xaman hajjagana a shehurinnan har aka k’are biki ba yadda dashi naiba xuwatai tai barbade barbadenta da bunne bunne ta tsibbance Kan bilkisun don karta yadda auratayya tashiga tsakaninsu da babaganan Kinga ai xa’a asamu shigar ciki don daga ganin shegiyar tana bak’in cikin kisamu jika, “Daga B’angaren babaganan don Kinga koba jima koba dad’e dole dannasa xe gaji mulkin bornu” “Wannan haka yake yakolo sam tunani na bezo nanba lalle hajjagana dani take nikwa xan nuna mata bokana yafi nata lalle batasanni bane banida imani ga duk tahalikin daya shiga gonata inbatai wasaba yadda tashigo gidannan tasameni haka xata fita tabarni aciki koya kikace yakolo??” “Kwarai kuwa yayya,ked’in nande kece babu nabi yinki a shehurinnan” “Godia nake tawajena ki aika ayomun iso da jakadiya mangu taxo yanzu base anjima ba” Da sauri yakolo ta kad’a kanta alamar to sannan tafice don kiran mangu makirar jakadiyar dake temaka masu wajen yin kulalliya a masarautar... Zaune bilkisu take gabanta abinci ne kala-kala masu rai da lafiya tana ci hankalinta kwance, babagana ne ya fito daga bedroom d'inshi ya bita da kallo cike da so ga uwa uba tsananin buk'atarta dake taso mishi a duk lokacin da ya kalleta. Itama tana ganinshi tayi saurin mik'ewa tsaye tana binshi da kallo na kurrilla kamar yadda take yi duk lokacin da ta ganshi. “Hey!ya aka yine?!” Da sauri billy ta girgiza mai kai alamar ba komai mirandar hannunshi ya ajiye sannan ya juya ya shiga cikin wani sitting room.Billy kam ganin mirinda yasa taje ta d'auka dan best drink d'inta kenan,komawa tayi wajan dining taci gaba dacin abincinta tana shan lemon harta gama sai dai wata irin kasalace ta addabii jikinta ta mik'e da kyar ta nufi bedroom d'inta tana layi tamkar wata 'yar maye. Babagana dake labe ya saki wani kayataccan murmushi yana lasar lips d'inshi sannan yabi bayanta.A yashe yaganta a tsakiyar d'akin idanuwanta a lumshe ya k'arasa inda take ya d'auketa yayi kan bed da ita sai faman bud'e ido take tana kallanshi dishi-dishi. Hajja yakolo na fita ta k'irawowa hajja gajiram jakadiya,tana zuwa hajja gajiram tace, “Jakadiya ina son kije gurin boka akan maganar hajjagana,ina son a d'auke hankalinta a cikin shehurin nan domin abubuwanta sun fara yawa,so nake yi goben nan kije kina jina?!” “Toh rankishi dad'e kamar yadda kika ce za'ayi Allah yaja zamaninki ki dad'e ki k'arko.” Da haka jakadiya ta tafi tana tunanin yadda za'ayi ta yanki dajinnan zuwa wajan boka tunda ta had'u da aljana kuluwa tace itace ajalinta,gashi bazata iya cewa bazata ba nan ma hajja gajiram tayi mata ila ita kam ta shiga uku..... #UZURI🤦🏽‍♀🙈 _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` Ina kike eshart TSAFE?!to ki matso kusa ga page d’inki sukutum ke kad’ai domin jin dad’inki.... *65* *B*abagana kuwa tunda ya samu billy tasha Mirinda nan ya d'auketa yayi kan gado da ita, kallonta yayi da idanuwan shi da suka yi wani iri ya kai bakin shi cikin nata billy tayi saurin amsar sakwan nan da nan lamari ya canza salo sam ta fita daga hayyacinta kai daka ganta kasan bayin kanta bane.Da haka babagana ya samu ya sauke nauyin da ya dad'e yana mak'alemai a cikin jini da tsokarshi, kallonta ya kuma yi tare da rungometa cikin jikin shi yana jin wani azababban sonta na k'ara gudana a cikin zuciyar shi. Allah sarki ita kam bacci tayi sai faman kallonta yake sosai yaga ta kuma yi mai kyau dama billy akwai kyau domin chocolate ce tana da round face mai d'auke da siririn hanci da idanuwa madaidaita gashi akwai gashin gira wanda shi ya k'arawa fuskarta kyau da annuri,kitson kanta ya kalla wanda yake d'as dashi sai kyalli yake yayi mata peck sannan yaja bargo ya rufesu. Jakadiya Mangu kuwa washe gari rasa yadda zata yi tayi,bayan ta fita ne ta biya ta gidan 'yarta ta bata ajiyar kud'ad'anta da gwalagwalai wanda ta samu kyauta a wajan su hajja gajiram saboda aikin da take musu.Fita tayi bayan ta tari mai keke napep ta hau ta sanar dashi inda zai kaita dan sam ba ta hanyar da ta saba bi zata bi ba kasan cewar tasan zata had'u da aljana kuluwa. Sai da jakadiya tayi nisa acikin kauyan ta fara dosar dajin da zata samu bokan kawai taga wata tsohuwar almajira tana yi mata wani irin kallo.Kin kulata jakadiya tayi sai da tayi nisa kawai taji k'afarta ta dama ta rik'e tayi-tayi amma Ina tak'i takuwa nan ta fara waiwaye ko zataga wani ya temaka mata amma ina babu kowa ko tsohowar bata gani ba nan ta fara kurma ihu amma tsit jakadiya tayi ta ihu akawo mata d'auki amma babu kowa sai ta rushe da kuka dan ji tayi k'afar na mata wani zugi tamkar a cire mata. Har kusan magriba jakadiya na zaune a gurin ta kasa tashi gashi babu kowa sai tsintsaye da kwari dan wasu ma sai cizonta suke yi ga kishir ruwa da yunwa duk sun addabeta kamar ta mutu, ana kiran magriba taji tamkar ana janta jakadiya ta rintsa ido sai kurma ihu take,bata tashi bud'e idoba sai ganinta tayi a cikin shehuri nan da nan ta kuma shiga cikin rud'ani a gurin ta saki fitsari. Masu zirga-zirga a cikin gidan ne suka ganta suka yi kanta da sauri suna tambayarta ko lafiya. “Ku kaini d'aki...!” Haka kurum jakadiya ta iya fad'a ta fad'i k'asa sumammiya,tattagarta suka yi suka kaita cikin d'akinta,a nan wata baiwa taje ta sanarwa da hajja gajiram kasan cewar tace idan anganta a kiramata ita amma koda aka gaya mata halinda aka ganta tab'e baki tayi cike da rashin damuwa daga nan ta yasar da zancen. Babagana kuwa sai wajan la'asar suka farka motsinta ne ma yasa shi farkawa yana kallonta.Tana ganin halin da take ciki kawai ta fashe da kuka tare da kudinninewa a cikin bargon,janyota yayi tayi saurin fisge jikinta ya kuma matseta ganin ta kasa kwace kanta yasa ta kyaleshi sai dai taki bud'e fuska sai uban kuka da take mai cikin murya k'asa yake magana. “My billy dan Allah kiyi hakuri ki fuskanceni wallahi ina sonki sonki zai iya illatani please ki gafarce ni kinji?!” Cikin kuka murya a dashe itama tace mai. “No!bana sonka ni bana sonka banason wannan abun kaima bana son ganinka...!” Rufe ido yayi sannan ya kuma matseta a jikinshi tana ta faman fizge-fizge sai da suka dad'e a haka sannan ya sassauta mata rikon da yayi mata. Mik'ewa yayi ya shiga bathroom d'inta ya had'a mata ruwan wanka, dawowa yayi nan inda ya barta yazo ya d'auketa har bargwan dan yasan idan yayi magana bazata kula shiba yaje ya sanya ta cikin ruwan ya fita zuciyar shi washar,haushin shi d'aya da take cewa bata sonshi bare son ganinshi. Sai da akayi kwana biyu sannan jakadiya ta samu sauk'i wanda har ta k'araci ciwonta hajja gajiram da hajja yakolo basu ko tura sunce sunayi mata sannu ba sai ma jiranta suke tazo ta gaya musu yadda suka yi da boka na sambisa.Yau tana tashi apartment d'in hajja gajiram ta nufa tana zuwa tayi gaisuwa lokacin babagana na zaune a parlorn ya tasa ta a gaba akan sai ankai billy k'asar waje dan dubo masa lafiyarta. “Rankishi dad'e ki dad'e ki k'arko a cikin shehurin nan da fatan an tashi lafiya?!” Ko kullata hajja gajiram batayi ba sai ma magana da ta cigaba dayiwa babagana, “Nace maka kayi hakuri komai ya lafa min sannan sai akaita ni wallahi dad'ina dakai rashin hakuri.” “Okk nine banida hak’uri ko?Toh wallahi sai naje na gayawa baba sannan na sanar mai da duk kullin da kuke mai inyaso sai a gane mara hakuri a cikin mu.” Da sauri ya mik'e hajja gajiram ta rud'e cikin tashin hankali wanda batasan ta furta ba tace mai, “Eh mana rashin hakuri nace maka maganinta ba na asibiti bane nice nan nasa aka kawar da hankalinta akan ka dama duk wani namiji dan karta tonamaka asiri akan abinda ka aikata mata sannan ka b'ata sunanka a wajan mutane..” Wani mugun kallo ya watsa mata tamkar wata kanwarshi kafin ya daki tumtum din dake wajan k'afarshi sai faman wani nishi yake tamkar wani doki. “Kika ce mene?!” Shiru hajja gajiram tayi kirjinta na bugawa dan saida ta kammala fad'a sannan ta gane aika-aikar da tayi wajan tona asirinta, “Wallahi mami kin cuceni kin sani cikin mugun yanayi wanda takai ta kawo bana samun karbuwa a wajan matata sai na gusar da hankalinta shin wannan shine son da kike cewa kina yi min?Na rantse da Allah kafin nan da k'arfe d'aya idan baki sa an karya sihirin nan ba toh kuma yau d'innan naku zai tonu billahillazi kuwa....!” Yana kaiwa nan yafita daga parlon har yana take hannun jakadiya da takallmin k'afar shi covered shoe.Nan da nan ta rintsa idanu saboda azaba tana yarfe hannun wanda yake mata zugi, hajja gajiram ta d'auki waya ta kira hajja yakolo ba jimawa sai gata tana zuwa ta shaida mata duk abinda ya faru dama hajja yakolo bata san cewar babagana yayi raping d'in bilkisu ba sai yanzu. “Toh yanzu yayya meye abin yi?!” Kirjin jakadiya na bugawa tana tsoran kar ace ita zataje gurin bokan tayi ta maza cikin dauriya tace, “Ai rankushi dad'e kur'anin Allah yanzu kauyan nan baya shiguwa saboda aljanu sunyi yawa.”nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar musu, amma ko a k'afar ta kalminsun suka ce mata sai ta koma yau ko su gayawa sarki cewar itace tayiwa baa Ngari asiri,cike da tashin hankali haka jakadiya ta tafi bayan sun bata kud'in mota. *_Back to Dambo road_* Alhamdulillah Meenah kam ta maida hankali akan karatunta dan ganin ta samu kyakkyawan sakamako sai dai ta gefe d'aya soyayyar sarki Aliyu hydar ta fara tasiri a cikin zuciyarta,lecture d'in aunty jaruwaiya ya shigeta sosai tanajin Aliyu hydar har cikin zuciyarta sai dai tsoranta d'aya tana ganin kamar yayi mata girma, kusan kullum idan suna da interval zata zauna ta dinga tsara romantic text messages tana mai sending har yanzu da ya kasan ce suna sauran kwara biyu su kammala final exams dinsu. Yauma zaune take a study room tana duba text book d'inta na geography ta dukufa sai kallo take tana d'an jotting kafarta duk biyun a saman table yayin da ta jingina jikin kujera sam bataji motsi ba bare taji shigowar mutum ba sai ji tayi an kamo tulun gashinta daga bayanta tayi saurin rik'ewa tana rufe ido tare da furta, “Ashhh!” Kafin a hankali ta ware idanuwa karaf tayi ido hudu da sarki Aliyu hydar sanye cikin kayan shi na sarakai,da sauri ta fara kokarin fisgar gashinta dan wani kunyar shi taji amma yak'i saki sai ma k'ara matsewa da yayi cikin hannunshi. “Dan Allah ya aliyu kasakemun gashina it hurts...” “Baxan saki ba,ke meyasa kunnen kashine dake ne mena ce maki akan barin gashinki ba d’ankwali?!uhhm” Shiru meenah tai tana cuno masa baki gaba, “Xaki dena pouting ko sena landing maki slap?!” Dena cuno bakin tai still tana runtse idanuwa saboda yadda ya damki tulin gashin nata.. Sakin gashin yai yana wurga mata harara cikin isa yace, “Trouble maker kawai..” “Definitely arrogant” itama tafad’a ahankali da alama batasan maganar tafito fili ba Ware idanuwa yai yana binta da kallo, “Kikace mene?” “Kobah canai kaina yana ciwo ba”tafad’a muryarta har tana d’an rawa.. “Liar”yace hakan had’e da tab’e baki.. Hannu yasa yad’auki littafin dake gabanta na modern physics, “Tell me...mekika fahimta aciki?!” “Everything...” “Okay fine”sarki Aliyu Hydar yace da ita haka tareda jan kujerar dake kusada ita yaxauna had’e da d’ora k’afafuwansa a kan nata cikin isa yace, “Menene theory of entrainment shin menene sukace human beings suyi?!” “Theory of entrainment..”ta maimata kalmar tana d’aga kanta sama alamar tunani... Binta yake cike da kallon kurilla tundaga yan yatsun k’afafunta har zuwa fuskarta... “Uhm,if you get it right kinada babban kyauta inkuma baki amsa ba nanma kinada punishment cuz kince kinsan everything..” Wik’i wik’i tai da idanuwa tana dubansa cikin in’ina tace, “Theories are like conce...”bata k’arasaba ya tsaida ta, “Ba theory nace kimin defining ba kawai get to the point dak’ik’iya kawai” “Theory of...”sekuma tai shiru tana cuno baki “Uhum Ina jinki” “Ya aliyu wallahi bansaniba dan Allah kayi hak’uri kada ka kamamun gashina plss”tak’arashe maganar tareda saurin sa hannu ta damk’e gashin nata... D’aga kafad’unsa yai tareda mik’ewa daga zaunen dayake yatashi tsaye ya rankwafa har setin fuskarta suna iya jiyo numfashin juna.. “Dan...” Bata k’arasaba ya had’e lips d’insu yashiga kissing d’inta sam tak’i bashi had’in kai ganin haka yasashi zare bakinsa cikin kasalalliyar murya yafara mata magana hannunsa d’aya akan labbanta yana xagayesu.. “Kiss me back Ameenah...”yaja Naaa d’in cikin wata irin siga me ratsa magudanr jinin duk wanda ya saurara, “Ya aliyu plss..” “Sssh”yakatse ta ta hanyar kad’amata kai kunnenta yad’an cixa, “Plsss I beg of you kinji Ameenah” Hakan dayake ba k’aramin sanya meenah wani iri yake ba barin yadda yake kiran sunanta yawani jashi seta kejin duk dunia babu wanda ya iya fad’in sunanta kamar sarki Aliyu Hydar d’in... “Please”yasake fad’a yana d’aga hannuwansa alamun rok’o Me Meenah ta tuno oho ta sak’ala hannuwanta ta xagayo wuyansa tashiga maida masa da martanin sumbar dayake mata sund’au lokaci suna maimata abu d’aya sannan Aliyu yafara wuce gona yasa hannunsa cikin rigar Meenah hakan yayi dede da shigowar Affy basuji xuwanta ba sai maganar ta sukaji akansu, “Baa Hydar” sekuma tai saurin juyawa xata fita ganin yanayinsu da sauri sarki Aliyu Hydar ya tsayar da ita Meenah kuwa kunya kamar kasa ta tsage tafad’a ciki haka taji cikin sauri tashiga gyara button din rigarta da kuma gashin kanta da ya hargitsa mata shi,cikin b’acin rai sarki Aliyu Hydar yashiga saukewa Affy banbamin masifa ganin ta katse masa jin dadi, “Ke kidahumar ina ce?! Ko kuwa kwakwalwar kifi ce da ke?da kina musulma baxaki sallama ba haka kawai xaki fad’owa mutane ba neman excuse ba komai shashasha kawai” Shiru Affy tai se hawaye sharr don tunda take yayan nata be tab’a mata kodah tsawa ba balle harta kaida fad’a irin haka se surfa mata ruwan masifa yake kamar wanda xe tashi ya doddoketa, “Badake nake magana ba ina magana kina wani faman kuka kamar wadda na daka?!” Cikin kuka,hawaye se zuba yake kamar ruwan famfo tace, “Wallahi Allah sau uku ina sallama bawanda ya amsa shine na... nace barin duba ko bakwa ciki”ta k’arashe xancen muryarta se rawa take, Shiru sarki Aliyu Hydar yai ganin laipin sane,dubar Meenah yai yaganta se tsiri tsiri take da idanuwa suna had’a ido ta sadda kanta k’asa d’an murmushi yai kafin yadubi affy, “M sorry little sis,kinji favourite sis?!” D’aga kanta tai alamar toh,tashi yai yaxo har kusa da ita ya rungumeta, “My little sis,our baby of the house kakki fushi da baa Hydar d’inki mana kinji?!next time duk sanda xaki shiga waje kibari abaki dama tukun kinji?!” “Toh baa Hydar,amma Ammi ce tace naxo na kirawo kufa wai kai kaje kasameta a parlorn ta sekuma wai aunty Meenah taje lesson teacher dinta ta chemistry taxo..” Ware idanuwa sarki Aliyu Hydar yai kafin yace, “For real?!” “Allah kuwa” “To gamu nan zuwa yanzu xakiga wayana akan coach kid’auka ki transferring amount d’in daxe isheki shopping aikinsan code dinko?!” Cikeda murna Affy tad’aga Kai, “Eh Eh baa Hydar...yay thank you thank you Allah ya saka da khairan”tana gama fad’a ta fece da gudu Girgiza kai sarki Aliyu Hydar yai tareda yin hamdalah azuciyarsa sanin badon wannan wayon dayai yamata kyauta ba to da babu abinda xe hana ta xayyanewa Ammin abinda tagani... Komawa yai kusada Meenah ya janyota jikinsa cikin kaskantar da murya tareda kashe mata ido d’aya yace, “A’ina ma muka tsaya?!” Ai Meenah bata bari ya rufe bakiba tai wuf tamik’e dama hanyar neman guduwa take,yunk’urawa yai daniyar kamota tai hanxarin fita da gudu tana masa gwalo girgiza kai kawai yai sannan yabi bayanta yanupi parlorn Ammi inda tace yasameta kafin ya k’arasa ya tsaya a corridor ya gyaggyara rigarsa da rawaninsa da suka ya mutse harya sa hannu xe bud’e k’ofar parlorn yashiga sekuma yai hanyar console mudubi dake gefen corridor aikwa ido hudu yai da bakinsa dayai dumu dumu da pink jambaki cikin hanxari yacusa hannunsa a aljihu yaxaro handkerchief d’insa ya shiga gogewa yana gogewa yana murmushi seda ya tabbatar komai tsaf sannan ya wani canxa yanayin fuskarsa don karma Ammi ta gano komai cikin isa da kamala irinta sarakai yaturo k’ofar parlorn yashiga bakinsa d’auke daa sallama... _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` _*RAMA RAMA MY RAMA LURV..Kina Ina?!To ki matso kusa tawan tamu ‘yan Real Madrid wannan shafin nakine ke ked’ai domin jin dad’inki.._ *67* *C*ikin sauri aka tafi da yareemah Babagana asibitin cikin masarautar temakon gaggawa likitoci suka fara yi masa cikin k’ank’anin lokaci akai masa scanning acikin ana jiran aga sakamakon daxe fito... Duk wannan abubuwan da ake hajja gajiram batada masaniya akai domin suna kan jakadiya mangu itada yakolo se surfa mata kwandunan masifa suke akai kan lalle tana sane take wannan abubuwan domin kwaso rantsuwa sukai suka dire kan cewar babu wata aljana kuluwa da har xata gutsire mata k’afa tana sane akai mata hakan don kar burinsu ya cika, itade jakadiya mangu se ambaliyar hawaye take tana rantse rantse ga azabar ciwon rashin k’afa ga wata masifar datake nemon kunno mata ganin iyayen d’akin nata sunki yarda da ita don yakolo tsabar takaici har shararawa jakadiya mangu mari tai.... Cikin fada kuwa zaune mai martaba sarki Aliyu Hydar yake a karagar kujerar mulkinsa se fadanci ake yayi masifar kyau cikin shigar kayan sarauta kalar k’asa alkyabbar jikinsa kuwa bak’ace datasha adon gwal,d’aurin rawanin sama abun kallo ne,kallo d’aya xakai masa kai saurin maida kanka k’asa domin mai martaba sarki Aliiyu Hydar bade kwarjini ba da hasken kamala..... Ana cikin fadanci jakadiyar sarki taxo neman iso kan ga fadawan yareemah Babagana nan suna neman sarki yabasu iso domin isar da k’ara akan matar yareemah Babagana nanfa fada ta hautsine kowa yana tofa albarkacin bakinsa kan tsaurin ido na dakaran yareemah Babaganan.. Cikin takaici sarki Aliyu Hydar yai gyaran murya tareda sallamar kowa dake fadar sannan yabawa jakadiya izinin shigowa da fadawan yareemah babaganan bayan su kuwa bilkisu ce se raba idanuwa take musanman da tasan sanadin bahagon naushin dataiwa babagana ne aciki yasanya akai gaggawar garzayawa dashi asibiti ita kuma aka taso k’eyarta xuwa fadar.. Shiru sarki Aliyu Hydar yai har yagama jin k’arar da fadawan na babagana suka kawo sannan ya gyaran murya xeyi magana ya bud’e baki kenan xe fad’i abinda xe ce wani d’an shisshigi daga cikin fadawan na babagana ya karaf kamar ance yai magana, “Saboda haka munaso sarki mai adalci da karamci da yayi gaggawar hukunta wannan mata ta yareemah domin ta..” Be k’arasaba fadawan sarki Aliyu Hydar dake gefansa sukayo caa xasu kaimai duka sarki Aliyu Hydar yai hanxarin d’aga masu hannu alamar karsu soma,cikeda girmamawa suka fasa suka xube a k’asa suka shiga bashi hak’uri. “Ayi hak’uri mai martaba Allah yaja da ran sarki Aliyu Hydar d’an shehu bulama,Allah yakarawa sarki lapia da nisan kwana” Gyada kai sarki Aliyu Hydar yai alamar ya hak’ura nan fadawan babagana suma sukace baxa’a barsu abaya ba suka ingixa kan bafaden dayai katob’ara agaban sarki bashiri sukai gurfane suna fadanci don kar ta’asar dayai suma ta shafesu, “Gaishe ka sarki Aliyu Hydar,gyara kintsi da kyau,gaishe ka dangin sarauta dangin kima da dattako,ayiwa dan talakawa hak’uri dangin matsiya ta dangin abun kunya dangin shisshigi da

Chapter 21 of 35