Share this page
ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of expert and perfect writers) nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakine DEEJAH WAZEERI marubuciyar DR HAJAR💉😘❤... _22/23_ Yareemah Aliyu Hydar na kishingid'e kan sofar d'akinsa wayarsa tafara ringing 'My everything' shine sunan dayai appearing akan screen d'in wayarsa da sauri ya gyara xamansa ganin Ammi ce ke kiransa saurin swiping yai yad'auka cikeda girmawawa kamar tana ganinsa yace; "Nda wattu Ammi,eh ina nan.. A'a tun d'axu natashi Ammi .. To shikenan ganinan yanxu xan taho insha Allah ..." Yana katse kiran yai hanxarin sauya kayan jikinsa xuwa k'ananan kaya samfarin polo designer dama yayi wankansa turaruka ya bulbula ya nupi fada dan gaisheda mai martaba tun kafin ya k'arasa d'aya daga cikin dakaran sarki yasanar mishi mai martaba bayanan tun safiya yafice cikeda fargaba Aliyu yareemah Hydar yaja motarsa yatafi gidan Ammin yana danna hancin motarsa cikin makeken parking space d'in gidan Ammin idanuwansa sukai masa toxali da 'Royce 'Royce'motar mai martaba. Ga kuma shamakinsa agefen motar ya mak'e atsaye kamar gunki jiki a sanyaye yareemah Aliyu Hydar ya rufe motar kotakan dogaran dake gaisheshi bebiba yai hanyar sashen Ammi gabansa se dukan uku uku yake a sanyaye yai sallama yashiga babban parlorn Ammin xaune yahango mai martaban akan kujera mecin mutum uku ita kuma Ammin nadaga k'asa agafensa gefan Ammin shima yaxauna bayan ya kwashi gaisuwa agurinsu mik'ewa Ammin tai xata basu waje Mai martaba yace taxauna a nutse yafara magana; "Aliyu..." Ahankali yareemah Aliyu Hydar yace; "Na'am Baba" "Kabani hankalinka nan babu wasa atattare da abinda xance yanzu ina fatan ka fahimta??" "Eh Baba" "To abisa binciken danayi akan wannan yarinyar dakake nema acan inda kake karatu nagano cewar yarinyar ba y'ar mutunci ba ce saboda haka nariga da nayanke hukunci babu kai babu ..." Shikenan jin Aliyu Hydar yatsaya na y'an wasu mintina gaba d'aya sauran abinda mai martaba yake cewa ba ji yakeba yarasa awacce duniya yake parlorn yaji yana jujjuya mashi ahnakali yasa hannu yadafe kansa dake barazanar fad'owa saboda azababban ciwon daya fara mai,muryar mai martaba ce tadawo dashi daga duniyar kurmayen daya tafi... "Ina fatan kagane..." "Baba...Kayi hak'uri amma..."be k'arasa ba mai martaba ya dakatar dashi a d'an tsawa ce; "Karka soma furta duk wani haryafi dakasan ya danganci wannan yarinyar nade gaya maka... Yanzu Ina son sanin ko akwai wadda kakeso bayan ita??" Ahankali yareemah Aliyu Hydar ya girgiza kansa alamar a'a, mik'ewa mai martaba yai yana kallon Ammin data xubawa sarautar Allah idanu tana binsu da kallo a dak'ile yace ; "Nizan wuce zanturo dr Samuel yak'ara duba jikin Ngari.." "Toh" Ammin tace had'e da mik'ewa tsaye ta rakashi har wajen mota shikwa yareemah Aliyu Hydar takaici goma da shatara ne suka sashi agaba dayayi k'ok'arin mik'ewa tsaye sai jiri yad'ebeshi yaxauna haka Ammi taxo tasameshi ko kallon inda yake bataiba tasakai xata hau sama murya a sanyaye ya furta; "Ammi.." Bata jiyo bakuma ta k'arasa hawa ba tace; "Menene?!" "Ammi dan Allah kiyi hak'uri" "Bani zaka bawa hak'uri ba wanda kake neman bad'awa k'asa a ido yakamata ka nemi yafiyarsa"tana k'arasa fad'ar haka tai hayewarta sama Kamar k'irjinsa yatsage zuciyarsa tafito haka yareemah Aliyu Hydar yakeji saboda tsabar takaici ahankali ya mik'e ya fita waje yanayi yana dafa bango harya k'arasa motarsa yatasheta Allah ne kawai yakaishi gida lapia dan dak'yar yake ganin gabansa,yana zuwa yashiga d'akinsa dakyar yafad'a kan gado wasu zafafan hawaye ne suka shiga reto a fuskarsa kona menene?!oho,dakyar ya iya shiga band'aki yad'auro alwala yad'auki qur'ani yafara karatunsa a zuci yad'an jima yanayi harseda yaji zuciyarsa tadena zafi sannan ya ajiye wayarshi ya d'akko yakira Modu had'e da sawa a handsfree ringing biyu modu yad'auka shima anasa b'angaren gabansane yashiga fad'uwa ganin kiran Aliyun daya shigo wayarsa a hankali yareemah Aliyu Hydar yafad'awa Modu duk yadda sukai da baba yak'are xancen da ; "Yanzu yaxanyi kasan halin shehurin nande yadda yake" "Guy yanxu kasan abinda nakeso kayi?!"cewar Modu indimi "Seka fad'a" "Kaje kabawa baba hak'uri fushin iyaye masifa ne guy,kabashi hak'uri Insha Allah nikuma jibi xanzo mu tattauna yadda za'ai" "Toh"kawai yareemah Aliyu Hydar yace sannan ya katse kiran yana shrya kalaman daxe bawa mai martaba hak'uri dasu.. Da yamma yareemah Aliyu Hydar yashrya cikin manyan kaya yana adduar Allah yasa mahaifin nasa beyi fushi dashi sosai ba bakinsa d'auke da addua yatafi fada wajen mai martaba yana shiga yatarar da mai martaba da waziri futa yai yabasu waje sedaya jira suka gama maganar sannan yashiga ciki nan ya k'ara tabbartar da lalle mahaifin nasa yayi fushi dashi da daane sallamar waxirin xeyi harse sungana dashi tukun amma yanzu seda yajirasu a k'ofar fada nakusan minti 20 tukun sannan aka masa iso yashiga,yana shiga yagayda mai martaba ba lefi ya amsa da d'an sakin fuska nan Aliyu Hydar yai k'asa da murya yashiga bawa mai martaba hak'uri akan abinda yafaru da safe,mai martaba yace masa bakomai shi be rik'e shi azuciya ba kuma gata yai masa bawai dan yasashi awani hali yasa ai binciken ba,atak'aice de tare sukaci abincin dare suka kuma tab'a hira har mai martaban yace yaje xe nemeshi jibi amma bai fad'a mai akan dalilin dayasa yace xe neme shi jibin ba,kwana d'ayan nan haka Aliyu yayita sukuku Allah Allah yake washegari tayi yaji neman me baban yake masa... WASHEGARI; Jirgin safe modu yabiyo ya iso Bornu,yareemah Aliyu Hydar na cikin naxari acikin laptop d'insa Modun yashigo bakinsa d'auke da sallama gaisawa sukai da Aliyun kowa fuskarsa d'auke da farin cikin ganin d'an uwansa haka suka shiga hira har rana tad'an fito sannan suka shiga fada gaisheda mai martaba ya amsa faran faran,yayi farin cikin ganin modu shima har yace masu sudawo anjima tare ze turasu wani waje.,bayan sunkoma d'akin Aliyu ne Aliyu yai tagumi,modu dake gefe yai y'ar dariya ahnkali yafurta; "Guy... What's wrong?!" "Akwai matsala fa..." "Tame fa?!"cewar Modu "Guy gabana fad'uwa yake karfa baba yace zaimun auren dole" Ido Modu ya gwalalo sannan yace; "Kasan me kake fad'a kuwa?" "Yass mana,auren had'i mana deep down abinda zuciyata take rayamun kenan" "Guy bafa akanka aka fara ba karka manta falmata(wacce suke uba d'aya da Aliyun,babbar y'ar gajiram)ma haka akai mata kuma gashinan tana xamanta a Lagos peacefully da mijinta da y'ay'anta ko yaji bata tab'a yiba haka ma fannah itama ba...,"be k'arasa ba yareemah Aliyu Hydar yakatse shi; "Please dan nace haka zuciyata take rayamun xaka fara wannan dogon bayanin?!" "No m serous,duk abinda iyaye suka shiga ciki yafi albarka beside kai kace ba son Basman nan kakeba.." "Yaushe nafad'a?!"cewar Aliyu "The charming kasande baxanyi k'arya ba yadda kake bawa yarinyar nan tough time kowa yasan baka sonta" "That was then... Atleast kobana sonta ina jinta har cikin raina kuma kaima kasani bantab'a jin haka akan wata mace ba" "Kai abarde maganr tunda baba de yace bakai ba..."be k'arasaba Aliyu ya wurga mai pillow a baki yanabinsa da harara Nan Modu yashiga tsokanarsa harde Aliyu yatashi yakoma parlor yabar masa d'akin,gurin k'arfe 2 na rana suka nupi fada danyiwa mai martaba Barka da rana ,bayan sungayshe shine ya umarcesu dasu xauna suci abinci bayan sunci abincinne mai martaba yai gyaran murya yafara magana; "Toh Alhamdulillah kafin nafara fad'ar koma menene ina rok'an Allah dayai maku albarka.. Yasa ku kammala karatunku lapia kufito da sakamako mekyau..." "Ameen baba"suka fad'a atare kowannesu da abinda yake sak'awa acikin zuciyarsa "Toh kamar yadda nace maku akwai inda xan turaku wannan wuri ba k'oina bane fyace gidan kawu Alooma Ghaji dake Yola_Jimeta,banason koda wasa naji ance kayi mis behaving.."yafad'i hakan yana nuna Aliyu Hydar sannan yacigaba da fad'ar; "Kunsan de kawu ne agurina kukuma kakane agareku saboda haka kuje da nutsuwarku kamar yadda kowa yasan ku nutsattsu ne,banda sakarci kuna jina...?!" "Eh"suka furta a sanyaye "Toh kai Aliyu wannan ce tambaya ta k'arshe da xan maka bayan wannan yarinyar akwai wadda kakeso?!" "A'a baba"Aliyu Hydar yafad'a asanyaye "Toh Masha Allahu sakamakon binciken danai nagano waccan yarinyar ba y'ar kirki bace naxauna nayanke shawarar had'aka aure da y'ar kawu Alooma kuma munrigada munyi magana dashi yaji dad'i k'warai dagaske yakuma yi na'am da wannan batu,kuma wani abin dad'inma yarinyar k'arama ce ko zance bata somayiba balle manema subud'e mata idanuwa,Ina fatan kana jina??" Yareemah Aliyu Hydar nantake yanemi bakin magana yarasa jiki ba kuxari yad'aga kai alamar eh... "Toh Allah yamaku albarka,sannan kaima Modu nabaka lokaci k'alilan ka nemo mata y'ar mutunci da dattako inba hakaba kaima kasan sauran" "Toh.. Toh Insha Allahu Baba zan nemo da izinin Allah..." "Toh Allah yamaku albarka,idan kunshrya se jirgina yakayku kuyi kwana biyu kuma kai Aliyu katabbatar kunsa santa kanku da ita kajiko?" "E"kawai Aliyu Hydar yace muryarsa araunace "Toh zaku iya tafiya...Allah yakyku lapia yadawo daku lapia kuyi k'ok'arin kintsawa da wuri kutafi naga alamar garin dad'an hazo" "Toh"sukace atare sannan suka sake duk'awa sukai masa sallama suka fice Harsuka shrya suka hau jirgi suka d'aga zuwa garin yola yareemah Aliyu yak'i cewa komai maganar duniyar nan Modu yamasa yak'i amsashi har suka isa airport mota taxo tatafi dasu cikin garin modu befasa yiwa Aliyu magana ba shikuma kamar robot haka yaxama ko kallon gefensa yak'iyi kansa a k'asa da alama naxari yake mintina k'alilan ne suka kaisu jimeta GRA babban signboard ne agefan wani layi me d'auke da gate bak'aramin tsaruwa layin yaiba boldly ajikin signboard d'in anrubuta 'MAI ALOOMA GHAJI LINK' se asannan yareemah Aliyu Hydar yad'ago kansa yabi signboard d'in da kallo jin alamar rage gudun motar da drivern yayi.... Da sauri Modu yadubeshi a hanxarce yafurta; Team#SKRZI?!Lovers😘❤ WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👨‍👩‍👧 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfect writers) nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakune marubutan k'warai;XEE YABOUR & SADIYA ABDULLAHI SHEHU(STYLISH BCH) _26/27_ Shiru yayi still saboda ko yaya yayi yunk'urin yin magana to za'a gane irin fushin shi, da sauri tamkar Modu yasan abinda yake cikin ranshi yayi saurin kallon aunty yafendo yana murmushi yace; "Aunty yafendo karki damu ba shi tayi niyar watsawa ba, matsala aka samu." Modu ya fad'a yana k'ok'arin rik'o hannun yareemah Aliyu hydar dake faman kallon k'asa baya ko k'iftawa dan tsananin takaici da haushin daya cika mai zuciya. Cikin nuna b'acin rai aunty yafendo tace; "A'a cewa nayi waye yayi mai wannan d'anyan wulakancin a cikin su?!" "Aunty yafendo Meenah ce ta watsa mai tazo zata watsama gid'ad'o." Wani yaro d'an k'arami da be wuce six years ba ya fad'a yana nuna inda Meenan ke tsaye tamkar gunki, ita kanta bata son hakan zai faru ba amma a cikin zuciyar ta tasan cewar tsautsayi ne kawai ya gifta. K'ok'arin gaida ita Modu yayi tayi saurin dakatar dashi; "ina zuwa Muhammad bari na cicci k'aniyar yarinyar nan tukunna sai mu gaisa." Aunty yafendo ta fad'a cikin damuwa na abunda Meenah tayi wa yareemah Aliyu hydar. "Zo nan Amina.."Aunty yafendo ta kira sunanta bayan ta sanya mata ido kasan cewar tasan bak'aramin aikinta bane ta arce ... Meenah ta turo baki tare da tsuke fuskarta bakin ta sai faman motsi yake alamar tana k'unk'uni,a hankali kuma ta fara tafiya harta k'arasa gurin aunty yafendo. Kunnenta d'aya aunty yafendo ta rik'e da d'an karfi Meenah ta saki wani k'ara tana bubbuga k'afa wanda hakan yasa yareemah Aliyu hydar d'agowa a hankali ya kalleta fuskar shi ba yabo ba fallasa, saurin kawar da kanshi yayi daga kan Meenah tare da jan tsaki cikin zuciyar shi dan ya d'auka babba ce tayi mai haka. Maganar da aunty yafendo ke yiwa Meenah ita ta dawo da hankalin yareemah Aliyu hydar wanda ya kalli Modu indimi alamar su tafi yayi mai dan yagaji da zama da k'azantar dake jikin shi. "Sakarai kawai gashi nan garin shashancin ki kin b'atawa yayan ki jiki, maza tsuguna ki bashi hak'uri kafin ranki yayi mugun b'aci." Aunty yafendo ta fad'a tana tsare Meenah da ido. Wadda ake yiwa maganar da alama bata da niyar yin abinda ake sata dan yanayinta ya nuna gashi sai faman d'an bubbuga k'afafuwa take tana tutturo baki fuskar ta kamar tayi kuka cikin k'unk'uni tace; "Nafa ce bashi zan yiwa ba aunty amma sai cewa kike na bashi hak'uri ni wallahi Allah ni gid'ad'o nazo watsawa accidentally yafad'a kanshi." Da sauri Modu ya kalli aunty yafendo cikin murmushi yace mata; "Aunty rabu da ita kinsan abinka da yaro bari muje ya cire kayan kawai." Modu yana fad'in haka yaja hannun yareemah Aliyu hydar suka koma apartment d'in da aka ware musu,ita kuma aunty Yafendo taja kunnen meena tai cikin sashenta da ita,sukuma sauran yaran sukabar wajen cikeda jin dad'in ba meena saboda kullum ojoro take musu idan suna wasa...Tun a hanya yareemah Aliyu hydar ya finciki hannun shi daga na Modu ya k'arasa ciki ranshi a b'ace, yana k'ok'arin cire rigar yaji Modu na cewa; "Guy yarinyar nan akwai taurin kai wallahi." Yareemah Aliyu hydar yayi mai banza dan maganar ma k'ona mishi rai take yi bare idan ya kalli jikin shi ji yake tamkar zai yi kuka, Modu ya sake tuntsirewa da dariya yana zaune a 1sitter harda buga k'afa dan mugunta ya sake kallon hydar yace; "Guy yarinyar nan akwai taurin kai, ji yadda aunty yafendo ke fama da ita akan ta baka hak'uri amma tak'i. Ni nayi observing d'in yarinyar akan abin da yasa tak'i cewa kayi hakuri d'in." Modu ya kuma tuntsurewa da dariya yana nuna yareemah Aliyu hydar da yatsan shi, sai da yayi dariyar sa me isarsa kafin yace; "Yadda na lura kawai dan ba kai tayi niyar zubawa ba so tana ganin baka hak'uri bashi da wani amfani gashi sai faman cin na shanu kake." Modu yak'arashe zancen had'e da sake fad'awa kan kujerar yana dariya sannan yasake cewa; "Allah yasa dai ba da ita za'a hada kuba,dan gaskiya yarinyar nan daga ganinta trouble maker ce kaikuma gaka arrogant prince wanda be..." Be k'arasa magana ba yareemah Aliyu hydar ya d'ago tare da zabga mai wata uwar harara, cikin b'acin rai da takaici yace; "enough Modu please let me be...Wannan ai maganar banza ce kake gaya min, me zanyi da wannan babyn da ko su Affy da Aysa sun girmeta?!kalleta fa ai wallahi baby sitter xan xama wannan yar shilar ai renonta zanyi Allah ma yakiyaye...!" Yareemah Aliyu hydar yaja tsaki tare da shigewa bathroom d'in cikin parlorn yana me jin haushin maganar Modu.Modu na nan zaune hannun shi rik'e da wata magazine yana dubawa, motsin fitowar hydar ne yasa shi kallon inda yake yana faman gumtse dariyar shi dan indai ya ganshi sai ya tuna abinda yafaru.K'arasawa gurin da trolley's d'insu take yareemah Aliyu hydar yayi tare da jan guda d'aya wadda daga gani Kasan tashi ce ya shiga bedroom ba tare da yayi ma Modu magana ba. Sai da ya shirya tsaf sannan ya fito yana faman d'aure fuska dan kar Modu ya kuma yi mai maganar. "Guy!ya kamata fa muje mu gaida aunty yafendo kasan bamu gaisa ba k'anwar mu tayi maka wannan aika-aikar, kuma nace mata zamu dawo." Modu ya fad'a yana satar kallon yareemah Aliyu hydar dake gyara k'asan wandon jikin shi, cikin nuna rashin kulawa yace; "Ba inda zani ai munje kuma ta ganmu hakan ma ya isa." Yareemah Aliyu hydar ya fad'a haka Modu yayi saurin kallon shi cikin rashin jin dad'in maganar Aliyun, mik'ewa tsaye yayi tare da zura hannu cikin aljihun shi ya zaro wayar shi tare da cewa; "Bari na kira baba sai nace kace baza muje gaida aunty yafendo ba tunda ta ganka." Modu ya fad'a tare da yin dailing numbern mai martaba ya kuma sata a handsfree dan Aliyu ya san da gaske yake fad'a zai yi. "Mtsce"yareemah Aliyu hydar yaja tsaki tare da mik'ewa lokacin da yaji wayar ta shiga ya kalli Modu cikin yatsina fuska yace; "Muje ni dad'i na dakai sharri da rashin gane wasa nake maka." Daidai nan suka ji muryar Mai Martaba a cikin wayar yana sallama; "Wa'alaikums salam baba, Eh!, mun sauka lafiya, Eh!, baba komai normal Alhamdulillah yanzu ma aunty yafendo zamuje mu gaisar munje gurin aunty Maijidda mun gaida ita, Eh Abba yace mu bari gobe shi sai mu had'u lokacin mun huta, toh!, baba sai anjima." Modu ya fad'a tare da tsinke kiran yana maida wayar cikin aljihun shi. Duk maganar da suka yi yareemah Aliyu hydar yaji sai dai yaji dad'i da Modu be fad'i abun da yace zai fad'a ba dan yasan zai iya, "guy muje mana." Modu ya fad'a yana kallon shi, tare suka fito har zuwa sashen Aunty yafendo Suna gab da shiga cikin parlorn kenan bayan Modu indimi ya shiga shi kuma yareemah Aliyu hydar ya tsaya cire takalmin shi kasan cewar covered shoe ne,yana d'agowa hakan yayi daidai da Meenah wadda Bulama ya biyo da gudu tafito dan tsira kawai jikake garam!ta fad'a jikin shi. A rud'e Meenah ta juya tana mamakin jinta jikin mutum, idanuwa suka had'a wanda na yareemah Aliyu hydar sunyi jawur, Modu ne daya ji shiru bega ya shigo ba yasashi lek'awa kawai yaga abin da ke faruwa. "Hey watch it...You are very very stupid..!" Yareemah Aliyu hydar ya fad'a bayan yaja gashin kanta da hannun shi tamkar zai ciro shi saboda irin rik'on da yayi mata. "Wayyo Allah na shiga uku zai kashe ni...!!" Meenah ta fad'a cikin ihu tana faman bubbuga k'afa tana rintse idanuwa saboda yadda take jin wani zugi a kanta har zuwa brain d'inta. Da sauri Modu ya k'arasa gurin yana kokarin k'watar ta amma ya kasa saboda yareemah Aliyu hydar yayi mata wani riko na b'acin rai wanda idan ba'ayi a hankali ba zai iya tsige mata shi baki d'aya. Bulama sai hakuri yake bashi shida gid'ad'o amma tamkar zugashi suke dan yareemah Aliyu hydar bashi da niyar sakin ta, dama haushi biyu ne ya had'u na d'azu dana yanzu da tayi mai. Modu ya rasa yadda zai yi hydar ya saki yarinyar, kallon Meenah Modu yayi cikin lallashi da tausayin ta dan yadda take zubar da hawaye yawu na dalala ga majina yace; "K'anwata just say sorry to him,call him yaya Aliyu Hydar." K'in fad'a tayi sai faman ihu take yi tana faman buga k'afa, ihun ne yasa aunty yafendo fitowa da sauri daga balcony d'ankwalin ta a hannu. Idanu ta zaro ganin abin da yake faruwa cikin ranta tace; "Ashe haka yareemah Aliyu hydar yake da rik'o" Abu kamar wasa taga hydar ya rik'e gashin Meenah tamkar ya damk'i sanda tayi saurin k'arasawa gurin tana ma yareemah Aliyu hydar magana.; "Ayya Aliyu hydar kayi hakuri ai na yi mata fad'a sosai wallahi." Aunty yafendo ta fad'a cikin rawar murya. "Aunty yafendo itace ta k'ara zuwa ta bige shi yanzu da zai shiga parlor." Bulama ya fad'a cikin gasgata maganar shi. "Kai lailahaillallahu..! Ni wuro me wannan rana take nufi?! Yareemah Aliyu hydar dan Allah kayi hakuri wallahi kwata kwata Meenah batajin magana gashegen tsokano fad'a da k'iriniya" K'in sakin mata gashin yayi sai ma cikin parlorn ya jata a haka, Modu ne yayi wa Meenah magana cikin tsawa; "Won't you apologies to him?!okay fine naga alamar taurin kai gare ki bari na barki dashi." ya fad'a tare da komawa ya zauna akan kujera da aka kewaye k'aton parlorn dasu. "Am sorry dan Allah wallahi bazan k'ara ba." Meenah ta fad'a cikin shashek'ar kuka ganin babu inda taurin kanta zai kaita sai wahala. Jin ta furta kalmar hakuri da bakinta yasa yareemah Aliyu hydar ture ta fuskar nan tashi a had'e ya k'arasa kusa da Modu ya zauna cikin nuna isa da k'asaita. Modu ya juya mai baya lokacin aunty yafendo ta k'araso tare da zama Modu ya gaisheta sannan shima yareemah Aliyu hydar ya gaida ita da k'yar kanshi na kallon center table d'in parlorn. "Kayi hak'uri kaji hydar Meenah bata ji ga tsokano fad'a ta kuma ce baza ta bada hakuri ba, ya wajan su Hajjagana da jikin yareemah Ngari duk lafiya ko?" Kallonta yayi ganin shi take kallo yasa shi saurin amsawa; "Lafiya lau Aunty duk suna gaida ku, shima jikin nashi yanzu Alhamdulillah muna ganin canji da temakwan addu'a." Yareemah Aliyu hydar ya fad'a, sun d'an jima a sashen nata kasan cewar tafi aunty Maijidda hira, abin da aka kawo musu ma basu tab'a ba haka suka fita suka koma apartment d'in da aka basu Modu har lokacin haushin yareemah Aliyu hydar yake.Suna shiga yareemah Aliyu hydar yaga Modu sai faman tsuke fuska yake sai shima yaja bakin shi yayi shiru, kan sofa ya hau tare da janyo wayar shi yana tunanin ko ya kira Basma su gaisa? Tsaki yasaki irin na karta raina shi dan shi ko mace yake so baya k'aunar raini, amma kuma haka nan yaji yana son jin muryar ta ya saci kallon inda Modu yake wanda ke zaune yana video call da kiara coca cola shape cikin kwanciyar hankali, mik'ewa Aliyu Hydar yayi yashiga bedroom ya kwanta akan gado tare da dailing number d'in Basma. Ringing d'aya tamkar jira take dama yaji ta d'aga cikin ranshi yayi tsaki jin ko d'an ajin nan bata ja mai ba. "Hello baby boo i love and missed you" Basma ta fad'a cikin salo najan hankali tamkar tana gaban shi, lumshe idanu yayi yana shafar dogon hancin shi me kamar biro tare da kai hannu yana wasa da kyakyawan gashin daya kewaye mai baki cikin muryar shi mai dad'i yace mata; "Uhmm are you sure??" "Haba boo boo you knw right fa,when r you coming back boo boo? I badly missed your handsome face." Basma ta fad'a cikin nuna tayi rashinshi sosai tana son ganin shi a kusa da ita tana kallon shi zuciyar ta na mata dad'i. "Zan dawo very soon, ya karatunki hope kina yi baki tsayawa wasa?!" Yareemah Aliyu hydar ya fad'a still idanunsa a rufe yayi kwanciyar rigingine. Sun dad'e suna waya wadda basu tab'a yi ba wadda ita kanta Basman tayi mamakin yadda yau yasake yana hira da ita, cire wayar a kunne yayi had'e da bud'e idanuwansa yana bud'ewa yaga Modu tsaye a kanshi wanda da alama ya dad'e a tsaye yana jinshi. "Mr arrogant...!dama kana dad'ewa a waya? Ko dan kaga munzo neman auranka shine kake son bamu kunya? Anyways it's time for prayer kayi alwala muje masjid." Modu na fad'in haka ya shige toilet ba tare daya juyo ba bare yaji amsar da za'a bashi duk da yasan ba me yiyuwa bane ya kulashin ba inda sabo yasaba shiysa yake kiransa wani lokacin da 'Arrogant prince'... WASHEGARI; Team#SRKZI?!lovers😘 Nagaisheku masoya makaranta littafin SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?! Nagaisheku cikin trailer trailer rubuta sunayenku abune da alk'alami baxe iya yiba...kusani cewa kuna cikin ran Nana Hafsatu akoda yaushe😘❤ WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!•• 💜?👪 (A STUNNING LOVE STORY) NA ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 (Home of experts and perfects writers) nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakine ke kad'ai yaya HAJJA CE,tareda y'an grp d'inki HAJJA CE NOVELS GRP _24/25_ "Guy dan Allah kasaki ranka ayi komai agama shi lapia pls i beg of you kaji?!" Nodding kansa kawai yareemah Aliyu Hydar yayi batare daya bashi amsa ba,a hankali drivern ke jan motar har cikin k'aton katafaran mansion d'in na Mai Alooma Ghaji,kai daka gani sekayi tunanin ko gidan shugaban k'asa ne saboda yadda ya tsaru ga fitulu ta ko'ina tamkar a turai.Tun daga gate xaka gane cewar lallai

Chapter 6 of 35