Share this page
yace bata kulashi hasalima dai data ganshi zata ruga gida da gudu.” Hawayen ne suka zubuwa mahaifin billy ya sanya k'asan rigarshi tare da share k’wallar da suka zubo, gabaki d'ayan su suka zuba mai idanuwa mahaifin billy yace musu. “Allah sarki da’ace tuntuni naji wannan bayanin babu abinda zai hanani yin saurin bawa maimartaba sarki Bulama auran 'yata ga d'anshi ba sai dai yanzu kashh! Bilkisu na cikin wani hali wanda mu kanmu bamu san make faruwa da itaba,amma hak’uri zan baku kuyi hak’uri abawa sarkima hak’uri domin anyiwa bilkisu fyad'e hakan yayi sanadiyar daya sa bata k’aunar kowane namiji hatta yayunta har yau bata zama kusa dasu, ni kaina bata dad'e da fara kulani ba...” Ya k'arasa fad'a yana hawaye,cikin tsananin tausayi babban cikin su yace, “Allah sarki koma waye Allah bazai barshi ba domin ya cuci yarinyar duk da cewar bamu ganta ba, amma munsan tana da hankali kuma abar tausayi ce,yanzu zamu je mu sanar da maimartaba inyaso duk abinda yace sai mu sanar dakai.” Sallama suka yiwa mahaifin bilkisu suna kuma lallab'a zuciyar shi domin sun san duk wanda aka yiwa wannan abun toh lallai bazai tab'a mantawa ba kuma kullum zai kasance cikin damuwa. Bayan sun koma suka shaidawa sarki maimurabus duk abinda mahaifin bilkisu ya shaida musu, “Allah sarki yanzu mutane basu da imani, sai ayi ta b'ata musu tarbiya ana lalata musu rayuwa ko mantawa suke da mutuwa oho, ni kam nasan duk iya abuna babagana yaji abinda ke faruwa da yarinyar nan toh bazai aureta ba duk da shima ba wani hankalin kirki gareshi ba.” Sarki maimurabus ya fad'a cike da jimami baya k’aunar fyad'e kuma duk wani wanda aka kama toh yana hukunta shi sosai, wani bafade dake kusa dashi ya kalla tare da cewa, “Balmu jeka kira min yareemah babagana,idan baya apartment d'insa saika k'arasa ka sanar da mahaifiyar shi cewar idan ya shigo ta turo min shi...” Da sauri bafadan da aka kira da Balmu yayi k'asa tare da yin gaisuwa sannan ya fita daga sitting room d'in da gudu dan cikawa sarki umarnin daya bashi.Cikin sa'a yana zuwa ya ganshi ya fito cikin shirin shi na english wears yana k’ok’arin gyara hannun rigar shi bafadan ya k'arasa dad'an sauri cikin girmamawa da k'askantar da kai yace; “Allah ya temaki jarumi yareemah ka dad'e kayi k'arko mahaifinka yana son ganinka yace nazo na shaida maka.” Wata uwar harara yareemah babagana yayiwa bafadan tare dabi ta gefenshi ya wuce,kome ya tuna kuma sai ya tsaya cak ba tare da ta juyoba, “Gani nan.” Haka kawai ya fad'a tare da juyawa ya koma cikin d'akin,sumar kanshi da take a gyare ita ya koma ya hargitsa tayi wani yarbatsai sannan yayi wani shegen murmushi ya fito tare da nufar apartment d'in baban nasu. Ko sallama yareemah babagana beyi ba a haka yana wani bud'awa ya tsattsalake mutanan wajan ya shige har wajan mahaifinsu baban ne da sauri yace, “Wa'alaikumus salam...!” Duka aka kalli maimartaba dan babu wanda yaji sanda babagana yayi sallama,amma shiru kowa yayi dan kar mutum yayi magana yanzu yaji saukar ruwan rashin kunya dan haka kowa ya kuma maida kai k'asa ganin ya bar shi kikam yasa mai martaba sallamar kowa yabar wad'anda ya aika da kuma shi babaganan,kallan shi yayi tare da cewa, “Toh babagana zauna mana kaji abinda yasa na kiraka.” “Nah a hakan ma yayi dan sauri nake akwai inda zanje yanzu,so ina jinka.” Yareemah babagana ya fad'a yana share hanci da bayan d'an yatsanshi guda d'aya,wani murmushin takaici baban nashi yayi sannan ya sake gyara murya yace, “Toh ai na d'auka kayi hankali lokacin da kazo min da zancen zaka yi aure hakan yasa yau na aika gidan su yarinyar dan na samo maka auranta, mma ka bari duk lokacin da kayi hankali kuma kake da lokacina sai na yi maka bayani.” Ai yareemah babagana yanajin ance billy be san lokacin daya gurfana gaban baban nashi ba, mutsumutsu ya fara yi yana k’ok’arin kamo hannun maimartaba mai murabus amma yayi saurin janyewa tare da kauda kai; “Baba dan Allah kayi hak’uri please wallahi nayi hankali kuma yanzun ma wajanta nake son naje ko baza ta fitoba naga kofar gidan su shi yasa na fad'i waccan maganar amma dan Allah baba m sorry.” Shiru maimartaba yayi ba tare da yayiwa yareemah babagana magana ba, ganin haka yasa babagana mikewa tare da k'ara hautsina kanshi ya kalli maimartaba cikin takaici yace, “Shikenan baba tunda na riga na fita hakkin ku na sanar daku cewar ina son aure kuma bilkisu nake so kunk'i yi min ko?Toh wallahi Allah duk abinda ya biyo baya kune sila....!” Ya fad'a tare da juyawa zai bar gurin maimartaba ya kirashi cikin taushin murya. “Ni kake cewa duk abinda ya biyo baya mune sila? Toh kaje amma idan ka tashi yin abun sai ka cire sunana aji dan ni ban haifi 'ya'yan dazasu wulak’anta ni ba, Allah ya shirya ku baki d'aya.” Saka kai yayi yabar gurin yanata k’unk’uni su kuma mutanan suka ci gaba da tausar maimartaba yana murmushin yak'e yana cewa ai ba damuwa dan ya san babagana ya gama tsinka shi,duk gidan 'ya'yan hajjagana kawai zai iya yiwa magana a matsayin shi na mahaifinsu suyi shi cikin mutunci da biyayya amma sauran sai addu'a kawai. Da haka suka ci gaba da tattauna matsalar da ake samu wajan yiwa yara fyad'e baga manyan ba harda yara jarirai da tsofaffin mata wanda sai dai a iya cewa Allah wadarai,kwana biyu dayin maganar babagana shima mai martaba sarki mai murabus ya nemi Modu,tunda yadawo shehuri yake fargaba yana tsoran abinda zaije yazo idan ya fad'i *_SON RANSHI_* a gurin maimartaba, fatan shi guda d'aya kar a hanashi auran Kiara domin itace burin rayuwar shi. Tunda Modu yadawo be nemi sarki Aliyu Hydar ba kullum yana d’akinsa bayan yadawo daga strolling yana kishingid’e maimartaba maimurabus yasa aka kira shi, gabanshi na tsananin fad'uwa ya shiga bayan ya gaida kowa na gurin kamar kullum idan maimartaba zai yi magana da 'ya'yan shi ko 'yan uwanshi sai ya kori kowa banda aminan shi mutum uku haka yauma sai daya sallami mutane ya kalli Modu cikin jin dad'i yace; “Mommodu kai muke sauraro domin lokacin dana d'ibar maka har ka k'ara wani akai, da fatan kaje kun gama dai-daitawa da ita yarinyar, sannan a ina take ya kuma sunanta dan inason a cikin shekarar nan kaima ace kana tare da iyalinka....” Wani uban gumi ne ya dinga tsatsowa daga goshin Modu indimi ba tare da yasan hakan na faruwa ba,shikam ya shiga uku me zai ce da baba game da kiara ta yadda va zai samu matsala ba, shin ta ina zai fara bayani sama ko k’asa tsakiya ko gefe. “Kai tunanin me kakeyi haka Mommodu?!” Modu yaji muryar wani daga gefen shi hakan yasa shi kai hannu yana goge zufar da tafin hannun shi na dama. Zama ya gyara yafi sau uku sannan yayi k'asa da kai yana cewa, “Am dama baba uhmm ita wadda mukayi alkawarin zamuyi auren da ita sunan ta uhmm uhmm Kiara arniya ce wallahi baba...” Maimartaba yayi saurin d'aga mai hannu cikin fuskar shi kuwa baza ka gane abinda ke cikin ta ba, numfashi ya sauke tare da kallon Modu yace, “Narasa gane mike cikin k’wak’walwarku gabaki d’ayanku,idan aka ce kuje ku nemo aure daga me d'akko kara sai mai samo yayi sai wanda kana nunamai gabas yana cewa yamma wallahi banyi tunanin kaima sakarai bane sai yanzu...” Sunkuyar da kai Modu yayi ba tare da ya kuma yin wata maganar ba,shiru yayi na d'an wani lokaci sannan maimartaba yace, "Tashi ka tafi Mommodu zan nemeka amma kar ka sa ran auran wannan yarinyar dan ban yadda da auran ka da ita ba.” Daram k’irjin Modu ya buga jin ance bazai auri Kiara ba,tamkar ya fasa ihu haka yake ji zuciyar shi na wani zafi ranshi na suya be yi magana ba ya fara kokarin tashi,har ya fara tafiya babu wanda yayi mai magana hakan yasa zuciyar Modu yin sanyi ya tabbatar abinda maimartaba ya fad'a babu fashi shi kam ya shiga uku idan aka had'a shi da irin Meenah dan a tsarin rayuwar shi yana son ya auri mace wadda ta cika ko'ina dan baya son wani kame-kame. Har ya kusa barin parlon yaji muryar maimartaba yana kiran shi cikin muryar shi mai cike da dattako yace; “Mommodu yaka nan kaji.” Mudo ya koma ya zauna nesa da shi sannan yace, “Baba gani.” “Yauwa abinda yasa nace ka dawo,na amince zaka aureta domin yin hakan ba haramun bane,sannan idan Allah yasa ta da rahama sai muga ta musulinta amma da sharad'in sai dai kaima zamu had'aka da *ZAB'IN MU* kamar yadda aka yiwa d'an uwanka wannan shine abinda zan sanar maka tashi kaje Allah yayi maka Albarka amin.” Ai sai ga hak’oran Modu a waje cikin sauri yayi k’asa da gwiwa yana sake yin godiya a gurin Maimartaba shi yama riga ya sha'afa akan cewar za'a bashi wata bayan Kiara,ita d'in kawai yake hangowa da cikin farin ciki da zumud'i yabar parlorn sai cikin fada wajan maimartaba Aliyu hydar. Mamaki ne ya kusa k'arasa maimartaba Aliyu hydar da ya zama mutum-mutumi saboda ganin Modu da yayi gashi kuma ga dukkan alamu yana cikin farin ciki da nishad'i,kamar yadda ya saba indai ya shiga fada yakan yi duk abinda yaga kowa nayi idan ya shiga yanzu ma sai da yayi gaisuwa sannan ya k'arasa gurinshi cikin nishad'i yace, “Guy gaskiya an had'aka da takunkumi, dafa da ne da yanzu kana kwance yanzu kuma ga uban rawani ga zama babu motsi gaskiya kana cikin cell da yawa...” '”Yar harara kawai Aliyu hydar ya sakarwa Modu sannan ya kifta masa ido alamar yana son sanin meke faruwa,Modu na gani yayi murmushi tare da shafa kai cikin murya k'asa-k'asa yace mai, “Mr arrogant na Basmah da Meenah,guy akwai labari sai daifa akwai matsala but na ajiye matsalar a side kabari idan ka dawo apartment d'inka zamu had'u dan ni bazan iya wannan k’umk’um d'in ba..” Modu na fad'a ya fita daga cikin fadar yayin da yabar Aliyu hydar cikin sak’e-sak’en zuciya.... #UZURI👏🏼👏🏼👏🏼👏🏼acigabada hak’uri da matar Yusleem abubuwa ne sukaimin yawa... amma naci *Alwashin*insha Allah komai xedawo norms norms rabbi yabar zumunci da k’auna... WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```nanahafsat.wordpress.com``` ```Wannan shafinma nakine my yahajja,har kullum baxan gaji da sadaukar maki da page ba domin ked’in tadabance azuciar nana hafsatu```💋❤ *59* *S*hirya shiryan biki aka soma yi both sites hajja gajiram ma tana yi dan taga take-taken babagana nason tona musu asiri a wajan mijin su,hakik'a anyi b'arnar dukiya sosai maimartaba da Mai Alooma har da sarki Aliyu hydar sunyi namijin k'ok'ari domin Modu har hawayen dad'i yayi dan hanashi yin komai suka yi hatta d'inkunan da zasu saka yi musu aka yi d'aurin aure kawai suke jira. Shima yareemah babagana hidimar shi kawai yake yi,komai ya samu bilkisu duk tsadar abu haka zai siya yace na bilkisu ne.sarki Aliyu hydar kuwa tsaf ya shafe babun mahaifiyar shi da 'yan uwan shi kwata-kwata baya tuna su yanzu duk abinda su hajja gajiram suka ce mai shi yake yi hatta maimarbata mahaifinshi yanzu baya mai biyayya kamar yadda yake wa hajja gajiram da hajja yakolo domin yadda ake dirka mai asiri yayi over hakan yasa suka ci galabar shi. Tsaf su Ammi suka shiryo suka dawo palace dan yin hidimar biki,Aysah ce kawai babu tana school. Apartment d'in da take sauka idan ta zo nan suka yada zango kasan cewar sauran sati d'aya kuma za'a fara event gobe shi yasa suka taho. Aunty yaruwaiya ce ta janyo Meenah suka kule cikin wani d'aki babu wanda ya sani,kallon Meenah aunty yarwaiya tayi tare da cewa; “Aunty Meenah kin shirya zaki yi abinda na ce miki?idan har zaki yi aunty Meenah yau a yanzu nake so ki fara bana son ki bani kunya da mamaki so nakeyi ki nunawa duniya cewar kema 'ya ce kuma matar sarki mai biyayya da sanin darajar mutane sannan kuma *ZAB'IN IYAYE* ba abun wasa bane please Meenah kice zaki yi...” Wiki-wiki Meenah tayi da idanuwa domin tun da aunty yaruwaiya ke mata wannan hud'ubar take jinjina irin iskancin da ake son koya mata,duk da cewar yanzu tana s.s 3 kanta ya k'ara wayewa iliminta ya kuma bunk'asa sannan ta fara sanin meye aure da yadda ake yin shi amma bata yardarwa zuciyarta cewar zata iya yin abinda yaruwaiya take cewa tayi ba,duk da cewar itama yanzu takan yi missing d'in fad'an su da sarki Aliyu hydar sai dai batajin zata iya yin abunda take nuna mata. “Aunty Meenah kinyi shiru ko kema baki son mu tsamo Aliyu hydar daga halaka,sannan bakya son ladan da Allah ke bawa mace idan tayi wa mijinta da 'yan uwansa biyayya?!” Cikin kid'ima Meenah tace bakin ta na rawa, “Aunty yaruwaiya ina so amma gaskiya ni bazan iya ba kuma mugunta yake min indai ya ganni.” Tayi maganar tana turo biki wanda ya riga ya zama jinin jikinta,cikin takaici aunty yaruwaiya ta mik'e tana cewa, “Wai ke dallah can sai yaushe zaki hankali kisan meye dai-dai da rashin dai-dai? Ke kanki taya aka sameki inda ba aure da tattab'a juna tsakanin miji da mata ba?Ko kin d'auka kina zaune a gida kiyi abinci ki gyara gida kiyi sallah shine kawai aure da musulinci?Toh bari ni zan nuna miki abu na farko da nake son ki fara yi kuma idan baki ba wallahi wallahi zaki ga abinda zan miki wawuya kawai.” Figar hannun Meenah aunty yaruwaiya tayi ranta duk a b'ace,ita kuwa Meenah banda turo baki ba abinda take yi a haka suka k'arasa kitchen, fridge ta b'ud'e ta d'akko kankana da dabino b'arewa tayi sannan ta cire kwallan dabinon gabaki d'aya ta had'a tayi blending d'in su,tacewa tayi sannan ta zuba peak milk da sugar d'an kad'an, cikin wani kyakyawan glass jug transparent ta zuba sannan ta kalli Meenah dake tsaye tana kallonta tace, “Ki d'auka yanzu kije ki kaimai yana can corridor ko Matar shi Basmah karkiji tsora idan kin ganta ki wuce gurin shi wannan abun dana gaya miki rannan shi zaki gwada yau,wallahi Meenah idan baki yi ba ina kallonki kin dai son banida mutunci gara ma kiyi kuma karkiji tsoron shi kinji ko?Oya d'auki kije 'yar albarka...” Hararar tray d'in Meenah tayi kafin ta d'auka tana kunkuni kasancewar tasan halin aunty yarwaiya hakan yasa ba tayi mata gaddama da musu ba tabi ta baya inda ba mutane sosai. Meenah na hango shi taji k’irjin ta ya buga da karfi abinda bata tab'aji ba kome hakan ke nufi, a hankali ta k'arasa har inda yake bakinta d'auke da sallama kanta a k'asa tana kallon tray d'in hannunta, jin sallama ne yasa shi d'agowa a hankali cak ya tsaida idanunshi akan fuskar Meenah,da sauri ta kalli bayanta dan ganin ko aunty yaruwaiya na kallonta ganin ba kowa yasa ta k'arasawa inda yake fuskarta a shagwab'e ta dire mai tray d'in a gaban shi.juyawa tayi tana kallon k'ofa nan tayi ido hud'u da aunty yaruwaiya tana kara zare mata ido tayi saurin juyawa a fili ta furta Kalmar, “Wayyo Allah na shiga uku..” Kallonta ya kuma yi a yatsine tamkar be santa ba ta kalleshi itama kamar gaske tace, “Habba rankashidad'e har zuwa aka yi aka ce ma munzo amma ko kaje sai ka zauna anan kai kad'ai, anyway ni gani nazo harda drink na kawo maka saboda ka rage kad'aici..” Tayi maganar tana tsiyaya mai a k'aramin cup mai matukar kyau wanda mahad'in jug d'in ne,sai data zuba sannan ta mik'a mai yabi hannun da kallo wanda yasha jan lalle harya fara zama kalar maroon a yatsun hannun, ganin yak'i karb'a yasa ta waigawa still aunty yaruwaiya na kallonta sai ta kuma matsawa kusa dashi wanda har tana tab'a kafarshi daya mik'ar da ita. “Haba rankashidad'e wai kurma ka zama ne yau naji baka magana? Ni dai zuwa nayi in tayaka hira amma naga kamar baka so.” Ta fad'a kamar wata babba,can taji yayi magana kamar baya so, “Ke!Waye ya turo ki nan gurin?!” Saurin kallon shi tayi ganin kamar ya harbo jirginsu tayi saurin juyawa bataga kowa ba hakan yasa ta kuma kura mai ido wanda shima ita yake kallo, matsawa tayi har suna gogar kafad'an juna wannan karan da gaske take yi bawai teaching d'in aunty yarwaiya bane dai-dai kunnan shi ta rad'a mai, “No body kawai nazo ne, toh ai nima matarka ce kuma aunty yaruwaiya tace zan iya tab'aka harma lada za'a rubuta min.” Bakinta yabi da kallo wanda yasha pink d'in janbaki yayi kyau gashi sai motsashi take yi,hannun shi yasa ya damk'i gashin kanta sannan ya matso da fuskarta sitin tashi har hancinsu na gogar na juna sannan ya sake maimaita mata kalmar d'azu, “Waye ya aiko ki nake tambaya?!trouble maker kawai” Meenah ta saki k'ara a hankali tana rintsa idanuwa saboda zafi ya kuma ja mata cikin axaba ta zura hannunta ta sakalo wuyan shi tare da saurin fad'awa kirjinshi tana mai karar zafi,ta baya Basmah ta biyo nan idanunta suka yi mata mugun gani kasan cewar idan ta baya ka taho zaka zata mouth to mouth kiss suke yi,wata irin kara ta kurma tare da rufe idanuwanta da hannunta, aunty yaruwaiya na gani ta tuntsire da dariya ita sam tama manta da cewar Basmah zata iya zuwa wajan amma hakan sai ya Kara mata jin dad'i domin tasan yau ta tunawa Basmah cewar akwai wata Matar fa bayan ita. A razane suka saki juna nan Meenah taga Basmah tayi katuwa da ita ga uban kumatu da tayi sam bata ganeta ba ta kalli Aliyu hydar cikin b'ata fuska dan har lokacin kanta be dena zafiba tace, “Ya Aliyu wannan wacece?!” Ta bayanta taji Basma tace, “Uwarki ce ke bakida kunya zaki zo nan gurin har kina bashi baki yana tsotsa? Toh na rantse da Allah...” Bata k'arasa ba Meenah ta mik'e tare da kama shamilallan kugunta tana girgiza shi tace, “Wallahi ba dai uwata ba dan gobema zata zo sai dai ni ki zageni haka kawai,toh...toh mai ai Yaya nane kuma uhmm...uhmm mij....mijina ne kuma.” “Amina...?!” Basmah ta furta dan duk basu san juna ba tunda Basma ba zuwa gidan Ammi take ba sai dai kullum tana wajan su hajja gajiram dan gani take sonfi kaunarta akan Ammin. “Yes thats ma name. Meenah ta bata amsa tana murgud'a baki,kallon Meenah sarki Aliyu hydar yayi cikin b'acin rai yace, “Ke!Matar tawa kikewa wannan farin da ido?!” Da sauri itama Meenah ta kalleshi tana turo baki tace, “Toh..toh ai dai nima matarka ce ehe.” Zaune ya tashi ganin haka yasa Meenah kwasa da gudu tana kiran Ammi har ta shiga kofa da aunty yaruwaiya taci karo nan da nan tayi saurin fad'awa jikinta tana sauke nishin wahala hannunta dafe a kirjinta,cikin jin dad'i aunty yaruwaiya tace, “Kin min daidai tawan duk da banajin abinda kuke cewa amma aikinki yayi kyau zoki wuce sauran na gobe tawan ki denajin tsoro ko shakka kinji ko?!” Meenah jin an yabeta yasa ta bud'e hakora tana dariya sai wani farin ciki take yi sannan suka shiga cikin sauran dangi aka ci gaba da yin komai tare. Basmah kuwa ganin Meena tabar wajan yasa ta kallon sarki Aliyu hydar tare da juyawa da sauri tana matsar hawaye, shima mik'ewa yayi kamar an tsikare shi yana kokarin shiga kofar parlor yaga Modu ya tare hanyar da zai shiga fuskar shi a had'e yana mai wani kallo,kasan cewar babu bafadai a wajan yasa babu wanda ya hana Modu yin hakan, Kallon sarki Aliyu hydar yayi tare da nuna takaicin shi afili yace, “Kabani kunya uwa uba kuma mamaki,tun kana ciki suke d'awainiya dakai har ka girma kayi wayo suka yi maka aure sannan baba ya sauka daga kan mulkinsa ya baka duk dan ganin da suke maka mai hankali kuma adali ashe nan gaba zaka nuna musu iyakar su,wallahi nasha mamaki sannan kuma kabi a hankali domin alhakinsu a kanka bala'ine a gurinka, idan kaga dama kaje ka gaida mahaifiyarka idan baka ga dama ba kabi matarka ciki. Modu na fad'a ya bashi hanya,ga mamakinsa gani yayi ya shiga ko kallanshi beyi ba,girgiza kai Modu yayi tare da cewa, “Allah ya kubtar dakai domin an saka a halaka mr arrogant.” Shima juyawa yayi yafita be sake bi ta kanshi ba, washegari 'yan yola suka zo harda aunty Maijidda da aunty yafendo dasu yakaka su gidado dasu bulama,murna wajan Meenah ba'a magana aunty yafendo sai kara mannata a jikinta take yi ganin yadda 'yarta ta kuma wayewa da Kara yin kyau sai dai ba kiba har yanzu cikin ranta take cewa,”kila sai ta haihu zata yi kibar.”Amma a fili bakinta kin rufuwa yayi saboda ganin Meenah ta kuma yin fresh.. Shirye-shirye aka ci gaba dayi Amarya layla batason abinda ake aikatawa ba tana can wajan 'yan uwanta dan tariga tasan Modu yayi mata nisa mai matukar yawa,shima shiryawa yayi da sauran matasan gidan suka tafi London wajan su Kiara da angama komai zasu dawo sai ayi irinna kanuri a palace tare da sauran amare.Babagana kuwa yafi kowa rawar kai duk da iyayan bilkisun sunce basu san ayi komai kawai a d'aura aure a kaita amma yace sai anyi irinna al'adar su duk da cewar bilkisun bata magana ba kuma ta kulashi sai dai bata tsoranshi kamar yadda take tsoran sauran maza. Har aka gama abubuwa ana gobe d'aurin aure sarki Aliyu hydar beje ya gaida Ammi da Maimartaba mai murabus ba har hakan ya janyo hankalin mutane 'yan bikin suka fara surutu musamman dangin hajja gajiram sunfi kowa sa ido. Da dare bayan anyi sallar isha wajan karfe tara lokacin sarki Aliyu hydar ya koma apartment d'inshi sai aunty yaruwaiya ta janyo Meenah dan so take su karkato da hankalinshi sannan itama Meenah tasan meye miji ya kuma ya dace tayi mai.shirya ta tayi cikin wasu shegun English wears riga da siket kallar pink da yellow tayi masifar yin kyau aunty yaruwaiya ta kalleta tare da furta, “Meenah ta kema macace karkiji tsoran matar shi yauma kinjiko?Sannan idan baki yi abinda na saki ba toh haka zai ta barinki gashi ba kula wasu mazan zaki ba shid'in dai shine mijinki,kinga befi sauran wata uku ba kema akawo ki gidan shi ya kamata tun yanzu kifara sanin abinda ya dace kafin kizo ya wulakantaki.” “Toh aunty yaruwaiya ni dai wallahi kunyar tab'ashi nake yi kuma fa sai yayi ta hararata yana kura min idanuwa.” “Sakarai toh ai hakan da kikaga yanayi miki shima lada ake rubuta miki please Meenah ta yau dai ki daure kice mai kina son shi kinji ko?!” Zaro idanuwa Meenah tayi tana kallon aunty yaruwaiya,hannu tasa akirji tana cewa, “Nashiga uku aunty bazan iya ba ni dai.” “Zaki iya Meenah ta kuma duk abinda kikaga yayi miki karkiji tsoro ko kice masa d'an iska nasan yanzu kinsan ba iskanci bane tunda kuna biology sannan kina zuwa islamiya ga shi kina kallon Indian films so kije kifara neman aljannarki tun yanzu oya jeki kar dare ya kuma yi.” A d'add'are Meenah ta fara tafiya ji take kamar ta gudu amma ba yadda zata yi haka ta shiga apartment d'in Basmah cikin sa'a ta hango sarki Aliyu hydar kwance akan 3sitter yana aiki a cikin laptop wadda ya d'aura akan cikin shi, sallama tayi wadda iyakarta makoshinta dan kuwa beji ba bare yasan shigowa ake yi sai ganinta kawai yayi a gabanshi.Da sauri ya kalleta cikin tsananin mamaki ya kai idanuwan shi kan agogon bangon dake cikin parlorn 9:25pm me ya kawo yarinyar nan yanzu?Aliyu hydar ke ayyanawa cikin ranshi. “Ya hydar ina yini?!” Ta fad'a tana tsaye hannunta d'aya cikin aljihun siket d'in yayin da d'ayan kuma tasa k'aramin yatsanta a baki tana tsotsa,kallonta kawai yake yana jin wani abu akanta amma ya kasa bayyanawa sai ma wani kin san yi mata magana da yakeji, Meenah kuwa ganin yak'i amsawa yasa ta k'arasa kusa dashi ta d'auki laptop d'in daga kan shi ta ajiye akan center table sannan ta dawo ta zauna akan cikin nashi inda ta d'auki laptop d'in ta maye gurbin, jinta akan cikin shi yasa shi rintsa ido yana tsuke baki Meenah kuwa sai raba idanuwa take tana tsoran karya harbata gefe. Kamshin khumran dake jikin ta shine ya

Chapter 17 of 35