me wahalar karyuwa, Amma Insha Allah komi xexo da sauk'i musanman yanxu da muka gano ainihin abinda akai amfani dashi,ina fatan kungane??" Cewar mufti yaseer ibn na'Allah...
Ammi sandarewa tai axaune takasa magana se yareemah Aliyu Hydar ne ya iya k'ok'arin bashi amsa a sanyaye;
"eh mungane mufti..."
"To Masha Allahu wannan addu'oi na ganyan magarya dana baku su xasu duk'ufa kwita masa kuma kunawa kanku,sannan ku rik'e addua tabbas addu'a itace makarin mumini daga miyagun aljanu dama mutane masharranta,ungo wannan littafin rik'e"yak'arashe maganar yana mik'awa Aliyu Hydar wani d'an littafi k'arami na larabci...
Mik'ewa yareemah Aliyu Hydar yayi yakarb'o littafin,
"Wannan littafin azkhar ne Akwai addu'oi aciki wanda xaku dinga tofa masa a ruwansa yanasha tunda shi baxe iyaba,sannan kuma kudingayi dukda nasan kunayi d'in amma yaxama dole ku sake xage damtse kunayinsu addu'oine na neman tsari wanda xaku dingayi da asubah koda safe se na maraice sekuma wanda xakuyi da daddare idan zaku kwanta komi yananan arubuce da larabci da kuma turanci ina fatan kagane??"
"Eh mufti nagane Allah yasaka da alkhairi.."
"Ameen Ameen,hajia kicigaba da hak'uri kamar yadda duk tsawon shekarun nan kikai hak'urin kike nemawa d'anki kariya yaxama dole yanzu ma kisake k'aimi wajen neman lapiarsa hajia,kinji?!"
mufti yak'arashe xancen yanakallon Ammi dake kad'a kai na jimantawa murya asanyaye Ammin tace;
"Nagane mufti Allah yasaka da alkhairi insha Allah xamuyi komai kamar yadda kace..."
"Yawwa hajia,sannan kusamo pure zam_zam kudinga tofa mashi addu'ar aciki ana d'an bashi yana sha ana kuma goga masa ajikinsa,yana iya shan ruwa ko?!"
"Eh ana bashi kad'an ba sosai ba shima sau biyu zuwa uku ake bashi arana kuma sesunyi diluting magungunansa aciki tukun"Ammi tace hakan tana kallon Aliyu Hydar dake flipping pages na littafin da mufti yabayar
"Toh to shikenan dukde yadda xa'ai abashi yadinga sha d'in saboda hajia ba k'aramin abu akaiwa prince Ngari ba har yau jifansa ake,kinsan duk sihirin daxa'ai amfani da jini da ruwa yafi saurin kamuwa ga bil adama,kamar yadda nafad'a maki abune akai da jinin da aka shashi(kaciya)tun wancan lokacin kenan aka kuma sakashi aruwa hajia,ruwa kuma ba k'arami ba wala Allah irin babban tekunnan aka jefashi ciki Allahu a'alam koma menene dayardar rabbi muda Allah muka dogara insha Allah komai yaxo k'arshe don't loose hope shine kawai"
Kad'a kai kawai Ammin tai,shima Hydar besamu bakin magana ba saboda yadda maganganun muftin nayadda akaiwa baa Ngari sihiri ne suka shiga masa reto ak'wak'alwa,haka de muftin yacigaba da gaya masu yadda xasu rik'e kansu da addu'oi na tsari da yawon karatun alqur'ani saboda shi gidah daba'a karatun alqur'ani kamar kango ne(uncompleted building)sannan daga k'arshe yashiga yi masu wa'azi da k'arfafa masu gwiwa akan kome nene yasamu bawa to muqaddari ne daga rabbil_izzati,yajima yana masu wa'azi me tsuma jiki sannan yamasu sallama yatafi...
Yareemah Aliyu Hydar sunjima su na k'ara tattaunawa da Ammi harde yai photocopying littafin a photocopy machine dake study d'insu Affy,yaiwa kowa copy d'ai d'ai sannan yanupi masallacin dake cikin gidan don gabatar da sallar zuhr kasancewar lokacinta yayi,yajima yana addu'oi a masallacin sannan yatashi yanupi sashen baa Ngari don ganin ya ya jikinsa?!dakuma farayi masa addu'oin kariyar da mufti yabayar....
16
........
Oxford university England;
"Babe yaude kinga oud d'ina kinji yadda yake k'amshi ko?!"
Layla kecewa basma haka tareda k'arasa cire d'ayan takalmin k'afarta don da alama basu dad'e da dawowa ba,Basma dake gefen gado tana faman dannawa bakinta kaxar kfc(Kentucky fried chicken)tai hanxarin had'iyewa tareda korawa da sanyayyar milkshake na vanilla sannan tace;
"Naga Muhammad d'inki,he's handsome and kind.., so very funny gaskia akwaishi da zolaya you guys made my day Nagode"tak'arasa fad'ar maganar tareda sake yagar cinyar kaxar dake hannunta...
"Glad you liked it"Layla tace hakan tareda yin Murmushi,..
"No I loved it... Thank you,yaushe rabon danaci kfc me dad'in wannan guess tun sugar boo d'ina yananan"
"Ai oud akwai son kayan dad'i kigafa mukace yabarshi amma dole sedaya siyo mana,ai akwaishi dakashe kud'i konawane,dan Allah kizo muje clubbing anjima ma plss...?!"
Ido Basma tagwalalo tace;
"Wa??rufamin asiri nagaji gaskia..."
"Pretty please,haba babe yaude kawai ,haba mana a Maryland hills and clubbing ne kuma vvip lounge xamu xauna"cewar Layla dake faman shagwab'e fuska dukdan tayadda..
"Fine...."Basma tafadi hakan tareda sakin tsaki...
"Yayy osheey,welkm abode babe"Layla tak'arashe maganar tareda hugging Basma
"Cikani babe karki karyani kiwa my prince asara..."
Basma taceda Laylan haka tareda mik'ewa daga kan gadon,itama Laylan mik'ewa tai had'e da d'aukar bathrobe tai hanyar bandaki tana dariya tana magana;
"Yanacan kilama anyi masa aure"
Da sauri Basma tabiyota da pillow zata doka mata
Aguje Layla tashige band'aki tana dariya...
"Screw you babe bakinki yasari d'anyan bushasshen kashi" Basma tace hakan tana hararar band'akin sekace Laylan tana ganinta
.......
"Hello kiara"
Cewar modu indimi dake video call da kiara sabuwar baturiyar budurwar dayai,kwance yake akan waata kujera doguwa agefan swimming pool dake apartment d'in abokin nasa...
"Hi handsome"kiara tabashi amsa tana biting lips d'inta
"Babe i missed you..."cewar modu kamar gaske
"Oh no you don't..."
Mik'ewa modu yai daga kwance yana kallon kiara tacikin wayar,sanye take cikin bikini outfits,cikin in ina kamar gaske yace;
"Why.. Why honey?!"
"Cuz i saw you with another gal..."
"Whatt? No no
Where and how?!"modu yace da ita
"At the casinos"
"Ohh that..just forget about that moment sweethrt you knw i love you past my mind beyond my soul..."
"Awwn i love you too"
" I wanna take you out,how about a night clubbing?!
"Yass that will do...."
Cigaba da rarashinta yai harta hak'ura sannan yake cemata k'arfe 10 nadare xexo yad'auketa suje clubbing d'in yana ajiye wayar yakoma kan kujerar ya kwanta yana tsaki,kome yatuno oho sekuma yasake d'aukar wayarsa yai dialing wata number had'e dasakawa a handsfree;
"Hello aboki kana inane?!"cewar modun
"Guy ina school amma yanxu xan dawo,anything?!"
"Yawwa pls kamar kace akwai wata budurwar cousin d'inka dake karantar international economic relations dake second year ko?!"
"Eh ya akai??"
"Dan Allah details nake so na matan ajin akwai wani abu danakeso nai figuring out ne"
"Budurwa kayi tamaka k'arya"cewar abokin modun yana daria
Daria shima modun yai sannan yace;
"Get me the details first,koma meye kaji daga baya plsss kaga jibi xankoma"
"Alright then..."cewar abokin
Godia modun yai tareda kashe wayar ya ajiye shikad'ai kamar zaucacce shi kad'ai yafara mgn yace ;
"Allah yasa abinda nake tunani bashi bane...Could this ruise actually turn into something real?!kai impossible"yak'arashe xancen had'e da mik'ewa tsaye ya koma cikin apartment d'in abokin nasa......
Team#SRKZI?!lovers😘😍
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••
💜?👪
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
Ina kike QURRATUL AYN?! To ki matso kusa ga page d'inki sukutum ke kad'ai Tawan😘❤
_13_
Happiest bday momma Lurv(momma KAUSAR M HASSAN)I love and adore you😘😘Allah yakawo healthy babies Amiin...!
......
Oxford university England;Modu indimi yana isa England wani apartment d'in abokinsa dake Oxford yawuce sedayai wanka ya huta sannan yafita d'an night outing daya saba koxeyi sababbin babes,aikwa yasamu ya gwangwaje outing d'insa da new babe d'insa black American mesuna 'kiara'...
Washegari da safe Modu indimi yatashi daga bacci kenan wayarsa tafara ringing 'coca_cola shape' sunan da yai appearing akan screen d'in wayar tasa,kamar baxe d'aga ba sekuma yad'aga had'e da sawa a speaker cikin kasalalliyar murya yafara magana;
"Sweethrt..."yafad'i hakan tareda sake gyara pillown dake gefansa ya kwanta yana lumshe ido
"Oud..."tabashi amsa cikin sigar jan hankali
Dashe hak'ora modu yai Kamar tana ganinsa;
"Mekikace sweethrt Waye oud d'in?!"
"Kai mana..."
"Meyasa naxama oud?! Oud ba perfume bane??"
"Of course habibee, your scent is divine,shiysa nake ce maka oud"
Aifa gaba d'aya yarinyar tatafi da modu, da sauri ya mik'e yana kallon kansa a mudubi had'e dasaka hannunsa yana wani shafa gashin kansa,cikeda jin dad'i yace;
"Awww thank you sugar.. I feel loved"
"Kana ina yanxu oud?!"
"Gimme like 20-30 minutes ,m coming to meet you"
"Awwwn how sweet?? A'ina xamu had'u?!"
"Duk inda kikace my lady"
"Okay how about sabon casino and bites da aka bude wajen Elizabeth Taylor street?"
"Anything for you sweethrt,sena.." Be k'asara ba ta katse shi
"Guess what oud??"
"What?!"modu yabata amsa
"M coming with my sis along,babbar k'awatace nd also my course mate,she's dying to meet you"
Sake gyara tsayuwarsa modu yai agaban mudubi,yana smiling jin ance wata tamutu ason ganinsa,se wani blushing yake yana shafa sajensa,muryartace takatse masa faman shafe shafen sajen dayake,nan yatuno be babata amsa ba da sauri yace;
"Oh really, I can't wait.., my regards to her kafin mu hadu"
"Okay oud.. C yah"
"Aha sweethrt..!"k'it yakatse wayar tareda hanzarin shiga bathroom don yin wanka...
....
"Babe yace he can't wait to c you... Guess he's super excited too"
Tsaki basma tai tana gyara kwanciyarta.
"Haba basma Kidena haka wallahi ,yanxu ke ba abin kunya bane nakirasu mama nace akan saurayi yatafi yabarki kinwatsar da studies dinki da duk wani walwalarki?! You need to cheer up,abinda yasa nace xamuje tare saboda kidena wannan xaman kad'aicin dakike da ware kanki daga cikin mutane abu yana damunki,mutane rahma ne basma,yaude kad'ai inaso kidawo yadda kike da muje outing plss kinji??"
Badon basma taso ba ta mik'e tashiga band'aki cikin sauri layla tak'arasa shiryawa,shiga tai cikin k'ananun kaya riga da wando purple and black se covered shoe datasa black tayi kyau ba lefi,ba mayafi bare d'ankwali hula pcap tasaka purple sak yartsana haka tafito kamar yar budurwar baturiya kasancewar fara ce ita,se xagaye d'akin take tana kiran sunan basma;
"Basma ki sauri plss,haba oud yanacan yana jiranmu ba dad'i tsaida mutum"
Basma dake gefen closet tana shryawa daria tai sannan tacigaba da gyara mad'aurin doguwar rigar data saka tace;
"Ganinan Juliet shima Romeo d'in naki nasan kila ko k'arasawa wajen beyiba"
Itade Layla bata bata amsaba tade cika tayi fam saura kad'an ta fashe don haushi saboda ko kad'an batasan tab'atawa oud d'in nata rai,cikin sauri basma tak'arasa shryawa had'e da d'aura wani d'an yalolan mayafi akanta sannan suka fice xuwa inda xasu had'u da oud d'in nata...
Suna zuwa 'casino and bites'Layla tanunawa basma 'modu indimi'da hannu yana xaune cikin d'aya daga cikin kujerun alfarmar da aka tanadar vvip suites modun yakama masu,xaune yake sanye cikin k'ananun kaya yayi bala'in kyau kwarjinin sarauta sosai shimfede yabayyana a ilahirin jikinsa da fuskarsa waya yake dannawa shysa bema lura dasu ba,tunda layla tanunawa basma 'modu'gabanta yake fad'uwa sosai take ganin kamar tasanshi amma tarasa a'ina jiki ba k'wari suka k'arasa inda yake suka zauna,gaysawa sukai gaba d'ayansu ,nan layla tagayra xama tafara introducing d'in basma wajen modun;
"Basma this is oud,my very own habiby... He's from Cambridge university and a final year student....!"tak'arashe xancen tana murmushi
Murmushi basman tai ahankali tace;
"Nice to meet you oud.."
"And she's basma,a sister from another momma,my very own best friend and also a course mate,room mates ...blah blah blah to cut it shot she's my other half"Layla tak'arasa maganar tana bin modun da kallo
"Basma..."yananata sunan ahankali
Harya d'an fara naxari axuciyarsa sekuma ya basar,kallon basman yayi for some seconds sannan yace;
"Nice to meet you basma,sunana Muhammad amma anakirana da modu ba oud ba kamar yadda sweethrt tace"
Daria sukai gaba d'ayansu,sannan waiter yakawo menu na abinci,abinci me rai da lapia modun yace akawo musu da dessert sunaci yanajansu da hira kasancewar shi faran faran yake da kowa ga zolaya da ban dariya,harde basma tasaki jiki tasa baki ana hirar tare da ita...
14
my profound and sincere gratitude goes to my beloved friend(pharmacist MYRIAM😘)this chappy is urs❤
.....
Bornu(Maiduguri)
SHEHURI(masarautar sarkin bornu)
saurin k'arasa goga turaren oudul haramein yai atafin hannunsa tareda rufe k'ofar closet d'in nasa,sanye yake cikin k'ananun kaya da suka amshi kyakkyawar k'irar jikinsa,jar rigace tad'an kamashi kad'an kana iya gano 9packs d'insa,me gajeran hannu,se rubutun handsome prince bak'i dake rubuce boldly ajikin rigar,bak'in jeans yasaka se covered shoe bak'i shima,hular kansa pcap(person cap)ce ja kalar rigar amma ta kamfanin polo,yayi kyau ba k'arya abinde seda a furta kalmar tubarkAllah dan kyawun da yareemah Aliyu Hydar yayi hannu baxe rubuta ba, da hanxari yafito daga apartment d'insa ya nupi fada wajen mai martaba,bayan sungaysa ne mai martaba yai gyaran murya yafara magana;
"Aliyu....!"
Kan yareemah Aliyu Hydar a k'asa ya furta;
"Na'am baba"
"Karkaga haryanxu ban baka damar komawa makaranta ba,ina fatan kasan dalilin dayasa??"
"Eh baba.."
"To Masha Allahu,daxarar Nagama aiwatar da bincike akai xanbaka damar ka koma kaji ko??"
"To baba... Allah yasa agama lapia"
"Ameen ya rabbi,kana buk'atar wani abunne?! yanxu ma'ajiya yafita se ai hanzarin kiransa..."Mai martaba yafad'i haka yanabin d'an nasa cikeda kallon tatacciyar k'auna
"A'a baba kawai inaso naje naduba jikin baa Ngari ne"
"To too hakan yayi,Allah yabashi lapia,Allah yatashi kafad'unsa,dukda haka xan had'aka da ma'ajiya wannan ni nai niyya,ka gaishesu sosai Insha Allahu nima xanje asatinnan akwai abinda nake jira ne.."
"To babaa Allah yakymu Nagode k'warai"
"Zaka iya tafiya..."
"Nabarka lapia"yareemah Aliyu Hydar yace hakan had'e da d'an rissinawa sannan yamik'e yafice
Yana driving yana tunanin kalmar binciken da mai martaba yace,cikeda tunani barkatai ya k'arasa gidan Ammin nasa,bak'ar Lexus itama tadanno kanta xata fito,jan birki yai yatsaya ganin su Affy ne,da sauri suma suka fito suna rigerigen gaisheshi;
"Baa Hydar nda rufto(good afternoon)suka fad'a atare
"Kilewa selai cutest little Affy nd adorable Aysa... Ina zakuje haka ba Ammi?!"
"Wushe wushe d'in falmata yar k'awar Ammi ake,ita kuma Ammi tana tare da mufti(malam/sheik) d'in baa Ngari"Aysah tabashi amsa
"Okay,sekun dawo karku dad'e hope m clear?!"
"Ehh..."suka bashi amsa atare .
"Yawwa baa Hydar shawangena(nayi kyau)?!"cewar Affy dake faman murmushi tana jiran amsar daxe ce..
"You luk amazing Affy...."
Sallama sukai mashi suka tafi shikuma yaja motarsa yak'arasa parking ,kai tsaye apartment d'in baa Ngari yashiga bacci ngarin yake hakan yasanya Hydar komawa sashen Ammin nasu,yana xuwa yatarar da ita da 'mufti yaseer ibn na'Allah'wanda ke temakawa k'warai matuk'a wajen d'ora iyalan Ammin bisaga kariya da temako na addu'oi ganin iyalan Ammin akatange suke anyi musu sukuwa da sihiri kala kala..,, Gaishesu yayi dukkansu sannan yamik'e ganin magana suke,Ammince ta dakatar dashi daga mik'ewar dayai;
"Maxa Hydar ga notepad da pen can nasu Affy d'an d'akko kamun jotting wannan addu'oin da mufti xe bayar kaji?!"
"To Ammi.."yak'arasa fad'a tareda d'akko littafin da biron.....
Gyaran murya mufti yaseer ibn na'Allah yayi yafara fad'in abinda Hydar xe rubuta,cikeda nutsuwa Hydar yafara rubuta abinda muftin yake cewa cikin rubutunsa had'add'e atsare kaikace machine ne yake rubutawa saboda yadda rubutun yake d'aukar idanuwan duk wanda yakalleshi;
Yadda ake war-ware sihiri -
_A samu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai (idan an samu busassu sunfi), sai a nik'a a zuba cikin ruwan.
_Sai a karanta suratul fatiha a cikin sa, kuma a dinga yi numfashi yana shiga cikin ruwan.
_Sai a karanta Ayatul Kursiyyu (aya ta 255 na cikin suratul Baqara).
_Sai a karanta Suratul A'araf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.
_Sai a karanta Suratul Yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan aya ta 82.
_Suratul Kafirun kafa daya
_Falaki da Nasi kafa uku- uku.
_Sai a karanta wannan addu'ar;
"Allahumma rabban-nas az'hibil ba'as ashfi wa antash-shafi la shifa'a illa shifa'uk shifa'un la yugadiru sakaman" k'afa uku.
_Sannan za'a iya k'arawa da wannan addu'ar"Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyka wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika" k'afa uku
Insha Allahu ta'ala idan aka karanta masa wad'annan, kuma ya dinga sha sau 2 a rana safiya da yamma, a kuma dinga masa wanka dashi a waje mai tsarki, ko kuma a samu tawul a jik'a da ruwan a dinga goga masa a jikin sa, Insha Allah nan da sati guda kowani irin sihiri ne Allah SWA se sauq'aqa masa... Sannan base shi kad'ai ba kuma zaku dingayi saboda ita Wannan addu'ar basai an maka/miki sihiri ba, mutum zai iya yi domin tsima jikin sa daga sharrin masharranta.
"Ina fatan kungane?!"cewar mufti yaseer ibn na'Allah...
"Ehh mufti mungane jazakAllahu bi kair,Hydar ka rubuta komai??"Ammi tafadi hakan tana kallon Hydar
"Eh duk na rubuta Ammi., Mungode mufti..."
"Yawwa to Masha Allah,se Abu nabiyu....."mufti yaseer yafad'i hakan yana gyara xaman dayaiii
Zuba mashi idanuwana Ammi da yareemah Aliyu Hydar sukayi suna jiran abinda xai fad'a.......
Ina kike ya hajjata tawa ni kad'ai banda billy matar abdul?😍❤Ina mik'o gaisuwata agareki ya hajjata❤❤gaisuwa mai kima😍❤
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👑
[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••
💜?👪
(A STUNNING LOVE STORY)
NA
©NANA HAFSAT
(MISS XOXO)
®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡
(Home of experts and perfects writers)
nanahafsat.wordpress.com
17
Modu indimi nashiga cikin gidan band'aki yawuce yayo wanka had'e da d'auro alwala ganin sallar magrib tagabato,tsane jikinsa yai had'e dashafa mai da turaruka na ruwa dana maik'o,shigar k'ananan kaya yayi wanda suka k'ara fito da kyawun da Allah yayi masa yana cikin taje kansa k'ararrawar gidan tayi k'ara,lek'awa yai ta window ya hango 'ma'aruf',abokin nasa wanda yake xaune a apartment d'insa,cikin sauri yak'arasa taje kan nasa sannan yasauka k'asa had'e da murxa key yabud'e masa k'ofar,shigowa ma'aruf yai cikin gidan da sallamarsa had'e da rataya jakarsa a handler,hannu yaba modu sukai shaking sanann yasunkuya yashiga zare mad'aurin igiyar takalminsa yana magana da modun;
"Aboki kajini shiru ko? Nida nace ganinan yanxu yanxu"cewar ma'aruf
"Eh Aboki Allah yasade kasamo details d'in..."
"Yeah nasamu wurin Arfat kamar yadda kace,da up head ma xata fad'amin sunayensu saboda wai su 8 ne in number nace a'a tade bani in written xefi maka ko?!"yak'arashe xancen yana mik'a masa wata yar takarda d'auke da sunaye ajikinta
"Eh yafi,thank you so much aboki..."
Ma'aruf yai murmushi wanda kyakkyawan dimples d'insa irin na yareemah Aliyu Hydar suka lotsa,ahankali yace;
"Da alama wannan de koma wacece da ita za'ai tunda kabaro y'ammatan Cambridge kataho Oxford"
"Baxade kaji mutuwar sarki abakina ba,kokafi fbi(federal bureau investigation)son jin k'wak'af"yak'arashe xancen had'e da mik'ewa yai hanyar stairs,
"Aboki menene abin dinner ko order xamuyi?!"cewar ma'aruf
"Namaka ordering fav dish d'inka,ni ba'anan Xanyi having dinner ba.."
"Okay agaida wadda ake mana rowarta idan tayi tsami maji"cewar ma'aruf
Shide modu indimi murmushi kawai yayi bece komaiba yak'arasa hawa stairs tareda shiga d'aki,rufe k'ofar yai gudun karma ma'aruf yabud'oshi,bud'e takardar yai daga ninken datake,'females students of international economic relations department of international studies and foreign language 'shine abinda ke rubuce boldly ajikin takardar,bin sunayen yashiga yi d'aya bayan d'aya har seda akazo kan layla bashir dikko yadad'e yana kallon sunanta sannan yacigabada bin sunayen mutum uku bayan Layla sunan basma ne, arubuce 'Basma Basheer Mai_Kano', kasa cigaba da bin sunayen yai ya jefar da takardar ganin ita kad'aice mesuna basma acikinsu sunayen matane xalla guda 8.Mik'ewa yai tsaye gaba d'aya yanayinsa yacanxa hannu yasa cikin gashin daya gama tajeshi d'axu yashiga hargitsashi zazzafar iska yadinga fezarwa daga bakinsa yashiga xagaye d'akin shikad'ai yafara magana da alama zancen zucin dayakene yafito fili besaniba;
"Nasan Layla batada qualities me kyau,ko bature ma yace tell me your friend and i will tell you who you are,idan har Basma tanada qualities mekyau meyasa xataxo casino and bites da wannan shigar??but may be dan taga outing ne ko?!damn it.."
k'arashe xancen yai yana sakin tsaki,tareda sa hannunsa yanaushi bango,saurin rintse idanuwana yai had'e da rik'e hannun yana murxawa don da alama dukan yashige shi,tsaki yasake saki akaro na ba'adadi yacigaba da maganar dayake;
"To gashi baba yace lalle nanemo qualities d'inta should I lie?! No no no baxanwa baba k'arya ba.. Kuma ai bansan koba haka halinta yakeba bakyau judging abinda mutum bashida masaniya akai... Yakamata na bincika de kuma ma dan naganta a casino hakan baxe nuna tanada bad habit bako?!..To yanzu ni..Be k'arasa maganar dayake shi kad'ai ba ma'aruf yashiga knocking k'ofar yana magana;
"Aboki lapiar ka kuwa?tun daga k'asa nakejin surutunka kai kad'ai sekace wani zaucacce wannan mystery girl d'in naka de tafara tab'a maka tunani da alama"
Bud'e masa k'ofar modu yai yana murmushi,ahnkali kamar bashi ba yace;
"Guy budurwar cousin d'innan naka xata temakeni?!"
"You mean Arfat?"
"Yeah ita plss..Nasan xatace ina takura mata bayan details data bani,This time I want to meet her in person(inaso naganta ido da ido)Akwai maganar danakeso muyi plss aboki.."cewar modu indimi daya k'arasa maganr cikeda tausayawa
Daria ma'aruf ya tuntsure da ita yanabin modu da kallo sedayai me isarsa yace;
"Aboki koma wacece budurwar nan taka tana baka tough time fa haba Aboki nigaskia ba wahalallen namiji bane akan mace haka kawai baxaka wahalar da rayuwata ba,kuma made yanzu kaga dare yafarayi kaji adhan yana kiran sallar magrib baxeyiwu ka had'u da Arfat ba takoma hostel kuma ita bakamar sauran babes d'in campus d'innan bace gaskia,cuz idonta be bud'eba bata fita night outing,so dole sede kayi fixing lokaci da yamma haka saboda da rana ma tana library..."Ma'aruf yak'arashe xancen yana tapping kafad'ar ma'aruf
"Narrative essay d'infa kenan wannan dogon bayani sekace kana presenting Abstract?!zanmaka magana kafin natafi seka had'amu.."modu indimi yafad'i hakan tareda saka takalmansa samfarin sandal kalar kayan daya saka...
"Dade yafi,kadena wahalar da kanka akan mace,kasansu da k'arancin tunani..."ma'aruf yabawa modu amsa,
Shide modu murmushi kawai yayi yafice don zuwa masallaci.. Around 9;45 na dare yana kwance idanuwansa arufe da alama tunanin mafita yake wayarsa tafara ringing 'kiara full option'sunan dayasa mata kenan,saurin mik'ewa yai daga kwanciyar yai don harga Allah shiyama mance da wani clubbing daxasu je hanxarin d'auka yai yasanar mata da gashinan akan hanya katse wayar yai had'e da sake feshe jikinsa da turaruka yasaka pcap d'insa da glasses na lights,motar ma'aruf ya ara yafigeta bexame ko'ina ba se London gazette Avenue unguwarsu Kiara kiranta yai tafito sanye cikin maroon armless riga iya cinya tasaka dogon hills black gashin kanta yasha gyara akwance abayanta bakinta shafe da jambaki maroon tayi kyau ba lefi dashe hak'ora modu yai yana aikamata da sak'on murmushi,da sauri yafice daga motar yatareta gidan gaba yabud'e mata yana murmushi yace;
"Ladies first.."
Shiga kiaran tai tana binsa da kallo dan bak'aramin Kyau yai mataba itama cikin muryata me dad'in sauraro tace;
"Thank you handsome.."
Nodding Kansa kawai yayi batare dayace mata komaiba,love song yakunna masu amotar 'come closer' wak'ar wizkid da drake,juyar da kansa yai b'angarenta yanabinta da kallo had'e dasa hannunsa yarik'o nata hannun cikin nasa ahankli yace;
"U'r looking takeaway honey"
Murmushi Kiara tai sannan tace;
"Awwn and so you handsome....Thank you"
Cigaba da tuk'in yai ahankli hannunsa cikin nata suna maganarsu ta soyaiya 10:00pm dede suka k'arasa joint d'in na Maryland hills and clubbing parking yai suka fito daga ciki hannunsu sark'e dana juna suka shiga ciki yai masu reserving sit a vvip(very very important persons)lodge gurin ba k'aramin tsaruwa yaiba couples ne kowa axaune amma kowa wajensa daban ishasshe daxe iya duk abinda yakeso gefe d'aya kuma disco ne yake tashi ahankali cikeda turawa y'ammata stripers dasuke rausayawa kowani zetaya...
Special menu waiter yakawowa su Modu indimi da Kiara,abinci me tsada da dessert modun yaxab'a yace akawo masu da champagne nagani na fad'a,selfies yafara masu shida ita kafin abincin yaxama ready...
....
"Babe rigar nan tamatseni dayawa karmuga idan sani"cewar basma dakebin matsattsiyar rigar jikinta da kallo dake shirin yagewa Idan tai k'wak'waran numfashi
"Mrs Aliyu dande bakiga yadda kika fito a full option d'inki bane,haba sekace wata sabon shiga bafa yau kika saba night outing haka ba"Layla tace hakan tana kanne mata ido d'aya
Basma tabud'e baki xata sake wata maganar Layla tai hanxarin rik'e hannunta suka shiga cikin Maryland hills and clubbing,sanye suke da matsattsun dogayen riguna dasuke bayyana kusan rabin tsiraicinsu awaje *wa'iyaxubillah,Allah ka k'ara shiryar damu da ahalinmu cikin tafarkin sunnar manzo SAW*,suna shiga basma tamatso kusada Layla cikin rad'a take mata magana;
"Babe ina date d'innaki?!"
"Yanzu xan samo"cewar Layla
Basma tagwalalo ido cikin mamaki,Layla batace mata komai ba ta hau kan disco dance stage tarik'e k'arfe tafara wani girgixa jiki tanabin wak'ar 'work ta Rihanna'
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 35