Share this page
sallama ba tana kashe wayar tana kokarin kiran mijin nata sai ga yayya gumsu ta shigo d'akin ta kalli Ammi tare da cewa. “Baba ya aiko da mota wai duk muje baki d'aya,har baah Ngari a tafi dashi.” Kirjin Ammi ya buga hankalinta ya tashi ta fara tunanin abinda ke faruwa, mik'ewa tayi gaba d'ayan su suka shiga mota suka tafi ga murnar baah Ngari ya samu sauki ga kuma fargabar kiran da aka yi musu na sassafe wanda basu san kona menene ba har suka shiga cikin shehuri babu wanda ya gano kiran da ake yi musu.. *KATSINA STATE* *KURFI LG* Tun ranar da baba maigadi da haj salamatu suka tafi kurfi take xaune agidan yayar sa akauyen na Kurfi kasancewar shi Baba mai gadi bashida aure matar sa ta rasu shekarun baya kuma Allah be bashi arzikin yaya ba harta rasu.. A can wata unguwa yayar Baba mai gadi take xaune da mijin ta amma yakanyi tashi xuwa gari gari yayanta kuwa duk manya ne kowannensu yayi aure Toh anan haj salamatu ta sauka kan Allah yasa ta gano gidan tsohon mijin nata da yayanta domin ta rokesu gafara ko Allah xesa su yafe mata.. Zaune suke itada inna hab’i yayar Baba maigadi akan wata jemammiyar taburma suna tsince shinkafa y’ar gwamnati kallo d’aya xakaiwa haj salamatu kagane yanxun duniya bata damawa da ita gaba d’aya ta fice a hayyacinta ko kadan baxaka iya kawowa itan bace.. Bushe shinkafar inna habi tai tana kakkabe xaninta da alama ta gama, “Tsiyata da hinkafar hausa akwai aikin gyara dubi heda nakusan b’ata awa biyu fa ina gyarenta..” Dan murmushi haj salamatu dake gyaren wake agefe tai kafin tace, “Haka take kam in baka gyara taba kuwa da kyau kaita tauna b’untu..” Sallamar Baba maigadi ce ta tsaidasu daga maganar da suke,shigowa yai hannunsa d’auke da fatanya dayan hannun kuwa leda ce baka d’auke da salak dasu tumatir agefe ya ajiye yana goge gumin dake gangarowa a fuskar sa, “Sannu Danjuma..Neman halal da wuya bari akawo maka ruwa”cewar inna hab’i Jinjina kai yayi kafin yaja kujerar dake gefe ya xauna yana duban haj salamatu, “Hajia Alhmdlh an gano gidan iyalin na ki..” Dafe kirji haj salamatu tai kafin ta mike tsaye dadi duk ya isheta ta jima a haka kafin ta nemi waje ta xauna kusada inna habi data ajiyewa Baba maigadi ruwan randa a kofi,dauka yai yasha sosai seda yai hamdalah sannan yasake dubansu, “Wallahi yaya ashe gidan Malam Bashiru na unguwar kuka take nufi..” “Kayya bade surikin hurera ba..”cewar inna habi “Shi de wallahi dattijon Malamin nan mahaifin su muhammadu harith mai jan sallah ba” “Toh Alhamdulillahi komai yaxo cikin sauk’i” “Wallahi kuwa se sanda kika kimtsa se a rakaki ko hajia?!”cewar danjuma dake kallon haj salamatu Mayafinta haj salamatu ta janyo cikeda zumudi tace, “Yanzu ma se muje baba don abinda yakawoni kenan” Baki inna habi ta rik’e kafin tace, “Kayya salamatu yanxun titin unguwar kuka baxata shigu ba kibari de xuwa gobe idan Allah yakymu se mu rakaki don ance hanyar su Fulani ke tare matafiya suna kwace masu kayayyakin su..” Badon taso ba haj salamatu tace, “To shikenan inna da yau da gobe duk dayane Allah yakymu goben lapia” “Amiin”cewar inna habi da Danjuma Sun jima suna tattauna yadda xasu bullowa tafiyar goben har aka kira sallar la’asar sukayi abinci yadahu sukaci cikin kwanciyar hankali..... *WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```Edited by```: ```Ya hajja ce``` ```nanahafsat.wordpress.com``` *77* *S*hiru Shehu Bulama yai yana jinjina kai hade da ajiyar zuciya ya jima a haka kafin ya maida dubansa ga Ayiya dake gefan yakolo cikin sark’ak’iyar murya a tausashe yace, “Ayiya hanxarta kikai ta xuwa asibiti kafin ku k’arasa xan kira dr na b’angaren optometrist(ido)ya duba idanun..” “Toh baba”cewar Ayiya.. Mikewa Aysaa tai ta temaka Ayiya suka tafi da yakolon xuwa asibiti.. Da azama yareemah babagana yayi saurin fita ya cafko hajja gajiram wadda ke faman k’ok’arin fita harabar masarautar hannuwanta ya kamo hawaye nabin kuncinsa ya fara kokarin janta zuwa wani d'aki anan cikin apartment d'in amma ta kafe guri d'aya.da kyar yasa iya karfinshi yajata tana dukanshi tana yakushin hannunshi tare da harb'in shi da kafarta amma haka ya daure duk da cewar yanajin zafi ya shigar da ita tare da janyo k'ofar ya rufe sai faman dura zagi take yi tare da bankad'a asirinsu. A gurin ya zauna yana kuka yayin da can parlor kuma kowa yashiga yin jimami mai martaba maimurabus yace ayi addu'a kowa ya koma harkar gabanshi.Modu ne ya daga hannu alamar zai fad'i wani abun sai faman sosa keya yake yi Shehu Bulama yace, “Toh Modu muna jinka kai muke jira.” “Dama baba tun jiya muka zo akan maganar kiara, domin ta shaida mana cewar tana son ta musulinta,jiya munzo muka samu jakadiya kolo hakan yasa bamu zo mun sanar dakai ba nace ta bari sai yau.” Babu wanda beji dad'i ba a cikin ranshi yayin da Shehu Bulama yayi murmushi yana girgiza kai yace. “Lallai sai yau na kuma tabbatar da cewar har yanzu kud'in yara ne,shi Aliyu be iya gudanar da harkokin cikin fada duk ina lura dashi sai soyayya daya saka a gaba.kai kuma Modu daka ga baka samu damar gani naba ai da saika bata kalmatush-shahada,irin wannan Ai ba'a jira ace sai wani yazo ko sai yana nan, “Alhamdulillah dama abinda muke son jikenan yanzu kaje ka yi duk abinda ya dace bawai dole sai ka kawota nan ba zamu zo da kanmu muyi mata murna.” Cike da murna yayi wa baban godiya sannan sukayi addu'a kowa ya fara yin inda zai tafi.kusa da sarki Aliyu hydar ya matsa wanda da alama so yake ya tafi da Meenah ita kuma taga su Ammi ko kallon inda yake batayi ba dan karta bishi, Modu ya rab'a yace. “Guy kana ruwa wallahi tunda har baba ya gano matsalarka king of love...” Aliyu hydar ya yatsina fuska cikin rashin damuwa yace. “Eh naji kaga ba ta yadda za'ayi kenan a dinga rabani da matata,kuma naji dad'i tunda sun gane cewar *ZAB'IN IYAYE* ya sanya ni zama hakan ai da ba haka nake ba.” Modu ya kyalkyale da dariya yace. “Hope dai kayi kokarin aje kaya dan gashi ni har zan riga ka ajewa..?!” “Ok abinda ka aike ne yi kenan dama?toh ban sani ba ka samin ido fa da yawa.” “Sorry guy bari naje gida wallahi jina nake a sama, da my kiara ta tsarkaka zamuyi aiki watakila mu dace itama ta samu nata rabon yau...!” Ya fad'a tare da juyawa ya tafi yana dariya,yayin da Aliyu hydar shima yayi smiling tare da girgiza kai yana mamakin Modu da har gaya mai yake cewar zai yi aiki yanzu. <<<>>>> Cikin wata d’ayan nan abubuwa da dama sun faru kamar zuwan mahaifiyar Layla wato haj salamatu inda sukazo da y’ar rakiyarta inna hab’i dakyar da temakon bakin Modu Layla ta yafewa mahaifiyarta ta inda haj salamatun ta sheda mata wani satin xata auri Baba Maigadi wato Danjuma.. Sosai Laylan ta lura maman nata yanxun ta canxa halinta duk wani kyale kyale nada datake yanxun batada wannan budurwar zuciyar uwa uba ga ibadah data sanya agaba ta dukufa cikin rokar ubangiji kan laifukan ta na baya domin shid’in gafurur raheemu ne kwanansu biyu suka koma katsina... B’angaren Hajja Gajiram abun kam ba sauki haukan ta kullum gaba yakeyi k’arshe de a wani daki aka sakata kamar cage haka yake ta taga ake xura mata abinci don duka takeyi sosai haukan nata bana wasa bane ga leukemia cancer da ta kamu da ita tana stage one.. Haj yakolo kuwa duk wani ko’kari anyi mata anma fafur ido yak’i budewa ga ciwon mutuwar barin jiki wato paralysis data samu special optometrist all the way from India aka d’akko yaita gwaje gwajensa su bloodtest,ultrasound,Ctscan,MRI da echocardiogram sun nuna komai na idanunan normal ne amma yayi relating da abun da Amaurosis Fugax wanda xa’a iya kiran ciwon da temporary loss of vision ko episodic blindness tuni yakolon tad’au hakan a matsayin kaddara da kuma mugun halin dasu ka aikata abaya Allah yakamata ya saukar mata da aya akan idanun,majina malale akan hancinta hawaye kwance shab’e shab’e akan face d’inta tadinga kuka tana rokar yafiyar su hajjagana su yafe mata tuni suka yafe mata ganin yanxun itan abar tausayi ce kuma ba komai abunda ta shuka ta girbe abinta... Acikin watanne kuma Shehu Bulama da Yareemah Ngari Bulama suka tafi k’asar Germany domin General Checkup Sosai Yareemah Ngari yasake kyan gani ga wani kyakyawan gemu(beards) daya tara a fuskarsa wanda yai mugun amsar kyakkyawar fuskarsa kanwar Modu data kare karatu a cyprus bana Shehu Bulama ya nema masa aurenta zankadediyar yarinya kyakkyawa son kowa Kin wanda ya rasa me suna Asma’u wadda ake kirada Asmy tuni ta karb’i xancen da hannu dubu ta kuma yadda,aka tsaida ranar aure sati d’aya bayan dawowar su daga Germany... B’angaren su sarki Aliyu Hydar kuwa abun ba sauki gaba d’aya soyayyar Meenah ta yiwa sarkin muguwar damk’a gaba d’aya ya xauce mutuniyar taku kuwa tuni ta karo wulakanci iyayi da yanga abun kam ba sauki kamar kullum Meenah na xaune a garden din apartment dinsu tana kallon animation na Barbie Mariposa Sarki Aliyu Hydar yaxo yasa meta yana wani narke mata ajiki tasan abunda yake bukata sarai ta ganoshi tashare shi ta cigaba da kallon ta a laptop. Sa hannunsa yai yaxare dankwalinta yashiga shafa tulun gashin ta, “Ajlaal” “Mene kuma Ajlaal?!tace hakan tana ware idanuwa “Plss Ajlaal ko kadanne” Ta gane me yake nufi ta basar dashi tahanyar jefo wata maganar, “Not until kafadi menene Ajlaal?!” Cikin shafar lips d’inta da hannunsa hade da pecking d’inta yace, “Suna ne kawai na larabci yana nufin beautiful stubborn,young princess” Dan murmushi kawai Meenah tai tana dubansa kafin ta mike xaune daga kwanciyar datai, “Why me..?i mean I’m not pretty like other girls dakai dating..” “What...no of course you are..Ajlaal you are so beautiful inside and out my meenah” “Kai ya Aliyu but ni ramammiya ce” “So what Ajlaal”yafadi hakan yana hade bakinsa da nata Sun jima ahaka kafin yasaketa yana maida numfashi ahankali cikin xura hannu cikin rigarta tareda sa bakinsa dede kunnanta yashiga magana cikin sexy voice stil hannunsa yana karakaina cikin rigarta duk yahana ta nutsuwa, “So what Ajlaal?Beauty comes in all different colors,shapes and sizes” Dan murmushi Meenah tai tana k’ok’arin cire hannunsa cikin rigarta dakyar ta iya cewa, “Nace..Nace..Nace ni ramammiya ce” “Oohh Ajlaal,then I will fatten you up..Taso kinji” “Nayi maka mene?!” Shafa keyarsa yai yana kallonta bayan ya mike tsaye, “Zo kiji magana za muyi” Mak’e kafada Meenah tai, “Uhm uhm nak’i wayon kobah nagaji ba sau bi...” Bata k’arasa ba Aliyu ya dagata yai cikin gidah da ita xatai magana ya rufe bakinta da nasa be diretaba se kan royal bed dinsu... Seda sarki Aliyu Hydar yasamu nutsuwa sannan ya kyale Meenah cikeda furucin Allah yai mata albarka wankan tsarki sukayo Meenah na xaune akan dressing Mirror tana tsane kanta da towel tai hanxarin duban Aliyu dake k’ok’arin sanya alkyabba ajikinsa, “Ya Aliyu.” “Uhm..Mrs Aliyu” “Ya Aliyu inason nacigaba da karatu na..” Dan Shiru yai yana naxarinta yadda tai naarai narai da idanuwa xatai kuka, “Ya kikeso ayi kenan..?” “Ko school dinsu Aysaa”bata k’arasaba ya furta, “What?!”yafadi da karfi da alama besan ma yayi hakan ba “Plss” “Wasa kike amma ko?!”yace hkn tareda hanxarin dawowa kusa da ita “M serious ya Aliyu.. I really really need to further my education career..” “Ajlaal kefa matar aure ce ba budurwa ba yaza’ai na barki kitafi har Oxford ki karatu while ni ina nan bornu hakan yadace?!” “But ya Aliyuu” “Sssssh Ajlaal no but’s”Aliyu yai shushing d’inta hade da janyo ta jikinsa yaashiga comporting dinta, “Akwai online schools Ajlaal,I think Affy ma nan xatai cux tafiya rawan kai” Daria Meenah tai tana k’ok’arin goge hawayen fuskarta, “Xan fara duba maki mekyau semu fara preparation ko?!tukunna ma wane course xaki tunda science kikai?” “Biopsy..” “What?!Biopsy de wanda suke discovering cancer?!” “Eh...”cewar Meenah hannunta d’aya kan cyboc d’insa taana shafawa “Well Allah yasanya albarka Ajlaal Biopsy issa unique course bakowane yasan dashi ba ga yawon cancer dake ta karuwa a duniya Allah de ya karemu” “Amin ya Aliyu” Hannu sarki Aliyu yasa yana k’ok’arin xame towel din Meenah tai hanxarin dakatar dashi tana binsu da kallon Yaya haka?! “I want you all the time you have turned me into a sex addict” Rufe idanuwa Meenah tai tana daria kafin tace, “Kai ya Aliyu so it’s my fault?!” “Eh Ajlaal duk lefin kine,with your soft skin and sexy legs and with those cute little...,” Be k’arasaba Meenah ta tureshi da k’arfin tsiya tai bandaki da gudu tana dariya girgiza kai kawai sarki Aliyu yai sannan yafice ixuwa fada fuskarsa d’auke da kyakkyawan murmushi... Tafiya sannu-sannu kwana nesa sedah duk aka gama ruguntsumin shehuri da nacin bugo waya da Shehu Bulama yakewa Aliyu tundaga Germany sannan Aliyu yatura aka dawo da Basmah,lokacin ta d'an zazzage akan muguwar k'ibar nan da tayi a baya sannan tayi laushi domin duk wannan rawar kan ta denayi ta zama silent ta dawo sashenta wannan aka gyara ba zaka tab'a gane cewar wai matar gidan ta jima bata cikin shi ba. Kwananta biyu da dawowa amma bata sanya Aliyu hydar a cikin idanunta ba gashi zuciyar ta sai k'ara axabtar da ita takeyi akan soyayyar shi. Fitowa tayi parlor'n ta cikin shiga ta alfarma domin duk an kuma zuba mata wasu kayan dai-dai window'n da yake kallon harabar gurin shak'atawar apartment d'in ta hangoshi kishin gid'e akan carpet yayin da Meenah ke jikinshi yana karanta wani d'an littafi. Zuciyar Basmah ta shiga bugu ta samu da kyar tayi baya ta zauna akan kujera tana maida numfashi tamkar wadda tayi gudu, “Na shiga uku ni Basmah ko dai ya manta da na dawo gidan? Shin ko ya goge soyayya ta cikin rayuwarshi har ma ya manta da ni gashi yana kula wannan figigiyar yarinyar?!” Basmah keta faman aiyanawa a cikin zuciyarta kafin hawaye ya fara zubowa daga cikin idanuwanta,karar wayarta yasa ta share hawayenta ta k'arasa inda take ta d'auka sai taga layla ce tayi saurin d'agawa tare da karawa a kunnenta tace. “Hello Maman biyu...” “Na'am amarya zamuce ko kuma uwar gida sarautar gida..?!” Layla ta fad'a cikin wasa yayin da Basmah ta yatsina fuska tare da kawar da zancen ta hanyar cewa. “Wai ke layla bazaki haihu bane?yaushe ne EDD (expected delivery date)d'inki ne?na k'agu naga babyn mufa.” “Uhmm na rasa gane tsakanin keda sister Aisha (kiara) waye yafi k'aguwa da na haihu,ku bakwa hango tashin hankalin haihuwa sai faman jiran mutum ya haihu kuke yi.” Basmah tayi murmushi tare da cewa, “Karki damu haihuwa babu wani tashin hankali a cikinta, kedai kiyita addu'a muma muna taya ki Allah ya saukeki lafiya..” “Amin dai wallahi duk na fiku son naga ma sauke wannan cikin, kuma Allah ya baku masu jin'kai.” “Amin.” Daga nan suka shiga hirar rayuwar duniya sosai suka dad'e suna wayar kafin suyi sallama wannan shine ya d'aukewa Basmah tashin hankalinta akan mijinta sai da tayi sati d'aya cif a gidan sannan ya shiga side d'inta lokacin tana kwance tana karanta wani littafi na addini ya kalleta sau d'aya ya kauda kai. “Ina yini..?!” “Normal.” Kawai yace ba tare da ya sake kallonta ba ya fito parlor ya zauna duk ya rasa me zaiyi mata dan daya kalleta sai ya tuna abinda tayi mai daga karshe tana kokarin fitowa wajan shi taji ya kuma fita da alama sashen Meenah ya kuma komawa.... <<<>>>> “Umma toh ni yanzu ya zanyi?wallahi ni bana son cikin nan dama likitan nan karya yake min gashi nan ya jamin wallahi harshi ban yafe mai ba...” Billy ce kita faman kuka domin lokacin kowa ya gama tabbatar da cewar ciki gareta gashi abban ta yace indai suka yi sanadiyar zubewar cikin toh zasu nemeshi su rasa dan zai bar musu gidan gabaki d'aya tunda basa jin maganar shi. “Kiyi hakuri bilkisu hakika taki kaddarar kenan,ki bari dakin haihu sai a mayar musu da d'an ko 'yar can gurinsu.” “Wallahi Umma yadda na tsani mai cikin haka na tsani abinda yake ciki na, ya Allah ka kawo sanadin da zai sa na rabu da cikin nan ba tare da na haifeshi ba.” Kamar daga sama suka ji ance. “Ba amin ba domin ni ina son mai cikin da kuma abinda yake cikin,haka kuma ina alfahari dasu baki d'ayan su...!” Cike da rud'ani suka kalli k'ofar d'akin, wa zasu gani? babagana ne a tsaye sanye cikin dakakkiyar shadda dark brown wadda d'in kin ya amshi jikin shi sai zubaba kamshin turaruka yake yi.kafin suyi magana abba ya shigo tare da kiran Umma ta fito yace ta rabu dashi domin har yanzu matar shi ce. _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:54 PM] My Xoxo: ```SON RAI KO ZAB’IN IYAYE``` 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*```A STUNNING LOVE STORY```_* *```NA```* ©```NANA HAFSAT (MISS XOXO```) ®```HASKE WRITERS ASSOCIATION```💡 _*```Home of expert and perfect writers```_* ```DEVOTED TO```: *```XARAH BUKHAR```* ```Edited by```: ```Ya hajja ce``` ```nanahafsat.wordpress.com``` _Ina masoyan Asy khaleel?to ku matso kusa shahararriyar marubuciyar taku ta sake xuwa da sabon littafi me cike da dimbin darussa aciki,se ku garxaya wattpad @Asykhaleel domin karanta sabon littafin nata me suna*SAMARIN BANA* kai dama sauran novels d’inta..Kada ku bari a barku a baya,wannan damar ta yan wattpaders ce kawai kafin littafin ya fara yawo a whatsapp.._ *76* *KATSINA STATE* *KURFI...* *S*u Inna Hab’i na karya karin kumallo suka fara shirin tafiya unguwar su Malam bashir dikko dake kauyen na Kurfi,su kayan daddawa da kuka ciki harda lalle da tsintsiyar laushi Inna hab’in ta had’awa haj salamatu don suyi tsaraba dashi.. Malam Danjuma na gaba su inna habi na biye dashi a baya suka shiga ketare dajin Allah unguwa xuwa unguwa basu suka isa unguwar kuka ba se shad’aya saura kwata na safe,gidaje ne jere a layin kowanne da inda yake kalla kallo d’aya xakai masu kasan gidajen na marasa shi ne gaba da wata tsohuwar rijiya kadan gidan na Malam bashir yake.. Zafafan hawaye ne suka shiga reto a idanun haj salamatu duba da gidan da uban yayan nata yake rayuwa aciki ko nada da suke ciki sanda take a matsayin matar sa yafi wannan daya ke ciki yanxun.. Se yanxun ta sake tabbatar da cewa wadatar arziki bashi ba ne wadatar zuciya itace,tsaye suka samu dattijon arzikin yana sallah akan dakalin dake k’ofar gidan nasa da alama sallar walhace waya baba mai gadi ya janyo daga aljihun sa data sha nannadewa da kyauro screen din duk ya fashe ya dubi agogo beyi wata wata ba ya maida dubansa kansu haj salamatu dake bin unguwar da kallo, “Haj kushiga daga ciki tunda sallah yake yi nima ynxu xanyi kafin lokacin walhar ya wuce” Haj salamatu bata iya bashi amsa ba saboda ganin wanda yafito daga cikin gidan ba shakka muhammad hadee ne d’anta yaxama babban mutum ya girma don rabonta data sanya ido akansa tun wani xuwa da sukai kano sanye yake cikin jallabiya bak’a kansa ba hula gashin kansa ya kwanta luf abinka da sumar Fulani.. “Toh danjuma”cewar inna habi sannan taja hannun salamatun suka shiga ciki.. Bakinsu d’auke da sallama suka shiga cikin gidan,inna matar Malam bashir ce xaune a farfajiyar tsakar gidan hannunta d’auke da kwano da ludayi tana shan fura..Sallamar ta amsa tana dubansu da kallo Kafin ta maida dubanta ga haj salamatu sosai tagane ko itan wace,da fara’arta ta mike tana shimfida masu taburma kafin tace su xauna bayan ta tura kwanan furar gabansu, “Bismillanku ga hura...”cewar innan Malam bashir, “Alhamdulillah wlhy Mungode”inna habi tabata amsa, Itade hajia salamatu shiru tai kanta a k’asa tana wasa da xaren taburma kallo d’aya xakai mata kasan xancen xuci take, Tallabe haba innan Malam bashir tai kafin ta sauke ajiyar zuciya ahankali tasake duban haj salamatu akaro na biyu, “Haj ya gidah ya bayan rabuwa??” Da sauri haj salamatu ta goge hawayen fuskarta cikin kaskantar da kai murya na rawa dakyar tace, “La..Lapia qalau hajia” Jin shirun yayi yawa ne yasanya inna habi cewar, “Ohh ya kuma zahi nan?!Allah de ya hitar mu lpy..” “Zahi lokacin sa mama,ni wani sa’in ma kinga nan inda nike nan nike jefa matashin kai na kwanta bisa taburma abuna” Y’ar daria inna habin tai kafin tace, “Gaskiar ki y’ar nan ko ni cikin dare nayo wanka sau nawa abinde se du’ai kawai” Y’ar hira suka cigaba da yi itade haj salamatu ba tace komai ba har Muhammad hadee yashigo hannunsa d’auke da leda ciki lemuka ne guda uku na kwalba kusada inna yaxauna bayan ya ajiye ledar agefe cikin sosa keya yad’an saci kallon mahaifiyar tasa, “Ina kwanan ku?!” “Lapia qalau dan nan,ya ya gidah ya aiki?”cewar inna habi “Lapia lou mama”ya bata amsa, Jin hajia salamatu bata ce komai ba yasanya shi tashi ya fita itako hajia salamatun neman bakin bashi amsa gaisuwar tasa tai ta rasa gaba d’aya kaf iyalin nata kunyarsu da tsoran su ne ke cunkushe acikin zuciyar tata. Tuwo miyar kuka na dumame inna ta dumamowa su haj salamatu tace suci,miyar koriya shar da ita se tashin warin daddawa take, Caccakuna haj salamatun tai,ita kuwa inna habi gyara xama tai ta durki tuwonta don kowacce loma seta yabi miyar da alama tai mata dadi ba kadan ba.. K’ofar gidah kuwa koda Malam bashir yagama cin abinci hannu yabawa baba mai gadi suka gaysa,cikin k’asa da kai cikeda girmamawa baba mai gadin yace, “Allah ya gafarta Malam tare muke tahe da bakuwa suna ciki suna jiranka..” “Assha bansaniba ai..Bari muci abinci tukun ko kafin..” “Toh Malam” Abinci aka kawo masu suma de tuwon ne da ruwan pure water sanyayye muhammad hadee ya sayo yakawo musu suna cikin ci Muhammad harith yaxo wajen hannunsa rik’e da ilham ‘yar shi.. Bayan ya gaishe su ne sukace yasa albarka take ya wanke hannu yasa suka shiga ci tare.Cikin gidah ilham tashiga tana kwallawa inna kira, “Inna ta..” Inna na cikin tankade gari ta ajiye kwaryar tana goge hannunta, “Na’am jikalle ta..” Daukarta inna tai ta mata lilo kafin ta dire ta tana haki, “Ji kalle me umman ki take baki haka se nauyi kike karawa TubarkAllah?!” “Masa uhm uhm da nama da madarar gwangwani..” “Dakyau y’ar jikalleta ga kakan ninki can jeki gaishe su” Da gudu ilham ta k’arasa kusa dasu daga gefe tana cin kasan hijabinta tace, “Ina kwananku..” Amsawa sukai dukkansu ciki harda haj salamatu data sake lulawa duniyar tunanin da batai wasarai rai shedan ya rudeta hartai fatali da yayan taba da yanxun wannan yarinyar tasan matsayinta agurinta.. “Da wa kukaxo jikalle?!”cewar inna “Ni da abba ne iya waje tare da su baba..” *Agurguje* Haka su haj salamatu keta xaune har Malam bashir ya shigo fuska a sake ya karbesu hannu dubu bama biyu ba, Tayi mamaki kwarai matuka,nande ta sheda masa abinda yakawota da abinda yasameta hartaxo neman yafiyar su,dan tausayi kowanne cikin iyalin nata seda yai kuka ciki harda ilham davatasan kukan me ake ba abinka da yaro.. Sosai Malam bashir yashiga yi masu nasiha dukkansu bayan komai ya wuce,se asannan haj salamatu ta kara yaba kambamawa da karamci da halin dattako na tsohon mijin nata, Sun jima kwarai a unguwar ta su Malam basheer dan da ca sukai su kwana ma sukace a’a sa sake dawowa tukun,sosai aka shiga hirar yaushe gamo ciki harda furera data garxayo tataho don murna rike da samiru cikeda abinci.. Se yamma likis sannan su haj salamatu suka kama hanyar unguwar su inna habi cike da kewar iyalan nata cikin zuciyarta kuwa ji take kamar an d’auke mata wani gundumeman dutse don jinta take yanxun babu wata damuwa datai ragowa seta neman yafiyar layla wanda yanxun shrye shryen tafiya garin na Bornu take don neman yafiyar Laylan inda halin afuwa... *BORNU* *SHEHURI* Suna shiga cikin shehuri dakaran da suka d'akkosu suka wuce

Chapter 30 of 35