Share this page
anyiwa amarya haka,ana gamawa layla tajanyo akwatin da kayan Basman yake Aunty yaruwaiya tashiga shiryata tunda sud’in ba iyawa sukaiba, Dede lokacin su Aunty yafendo suka iso da Meenah daketa raba idanuwa tad’an fad’a kad’an da alama kannata ba k’aramin ciwo yai mataba sashen dasu Ammin suke suka shiga aka gaggaysa sukuma su Basma suna k’asa a d’akin dake parlorn k’asa, Rungume Meenah Ammi tai har cikin b’argon magudanar jininta take sonta kamar yadda takejinsu Affy jin jikinta dad’an zafi yasa Ammin d’ago Meenah tanabinta da kallo, “Bitti(y’ata)bakida lapia ne??” Ahankali Meenah tad’aga kanta alamar eh,Aunty Yafendo ta karb’e zancen, “Wallahi batajin dad’i amma da sauk’i Alhamdulillah” “Wayyo sannu Bitti”cewar Ammi had’e da sake rungumota jikinta itade Meenah se raba ido take, Abinci aka shiga kawowa su Aunty Yafendo dake kukan zucin rabuwa da d’iyarta, “Bitti beri bei(sakko kici abinci y’ata)”cewar Ammin Dan gata abaki Ammi tashiga bawa Meenah abinci itade akunyace takeci tana gamaci tarik’o hannunta tashiga da ita wani d’aki tace ta kwanta ta huta, Cikin k’ank’anin lokaci shehurin yad’auki color da ankon dangasho da mandil mayafi da ake sakawa a wushe wushe su Affy da sauren ‘yanuwa blue and black sukasa ‘yammatan amarya kuma peach and black sukasa,amarya Basma kuwa sanye take cikin Swiss lace black me design d’in gold aunty yaruwaiya tanad’a mata laffaya gold anmata kitson gaba (kela yaske) yasha design da gwal tasha sark’ar gwal har anklet na k’afarta ma na gold ne tayi masifar kyau ansa mata nose stud na hanci da ake mak’alawa wanda bashida b’ular hanci, Ango da friends d’insane suka shigo ciki,yan uwa aka d’auki shewa ana tsokanarsa sanye cikin yadi bak’i yasha aiki gold yamurxa hula da agogo da takalmi sau ciki duk bak’ake sauran friends d’insa kuma gold yadi sukasa sunyi matuk’ar kyau abinde se wanda yagani, Akunyace aliyu hydar ke gayda su Aunty yafendo Meenah dake cikin d’aki a kwance jin muryarsa yasa ta k’ara jan duvet tarufe kanta,mik’ewayai yafita abokan suka bishi abaya mota yashiga yakame a owners corner Basma na d’ayan gefen kambun mulkin mutumin naku sun motsa ko kallonta beyiba shiru kawai tai kanta a k’asa Modu neke driving Layla kuma agaba ta hakimce bawanda yacewa wani k’ala har suka isa wajen kasancewar daga cikin apartment d’in Ammin xuwa tent d’in daxa’ai occasion d’in ba nisa amma dukda haka a motoci aka shisshiga aka tafi, kid’an ganga kuraa ne ketashi a tent d’in Modu na parking yai fitowar sa gudun kar layla taganshi amma ina sedata hangoshi baki wangale cikeda mamakin ganinsa tace, “Oud” Badon yasoba yadashe baki kamar gaske kai kace besan tare suka tahoba yana sosa k’eya, “Babe” Yace hakan yana duban agogonsa kamar gaske,da sauri yace, “M in a haste, will holla you later” Yafad’a had’e da barin wajen da sauri be bari ta sake fad’ar wani abunba jiki sanyaye ta tsaya abakin motar tana jiran fitowarsu Basma.... Cikin motar kuwa ba wanda kewa wani magana ganin haka yasanya Basma janye shirun ta hanyar fad’ar, “Sugar boo...” “Uhm Basma”ya bata amsa kansa a kan wayarsa yana latse latse Maida wayar yai cikin aljihunsa yana dubanta tayi masa kyau sosai a hankali ya kamo hannunta yana murxawa,shiru tai tana amsar sak’onsa, Bece komai ba yaci gaba da murxa hannunta yana duban kunshinta dan bakaramun son nalle ya keba musanman ja seda ya gaji don kansa sannan yakamo hannunta suka fito daga ciki, Da taken ganga kuraa suka shiga wajen taron bayan su kuwa dangine dake taka rawar ganga kuraan abinde se wanda ya gani,duk wata al’ada da ake ta kalawa seda akai musu su tulur duk anyi anci ansha anraba souvenirs Basma dad’i kamar me kusan duk events din dasukai a kano Be kamo ko k’afar wannan akyau ba, Anjima sosai ana raya al’adar sannan aka watse fuskar kowa d’auke da murna bandasu hajja gajiram ‘ya'yan fata, Abun da ya bawa mutane mamaki shine ana kammala wushe wushen aka yi shelar za'a nad'awa yareemah Aliyu hydar sarauta, shi kanshi yareemah Aliyu hydar d'in sai da k'irjin shi ya buga dan tsananin rud'ani da tashin hankali, sanarwa aka yi akan cewar washe gari za'ayi nad'in da yardar Allah. Nan da nan zuciyar hajja gajiram ta fara bugawa, kanta tayi saurin dafewa saboda yadda take jin shi tamkar zai fad'o k’asa dan ciwo....... #SRKZI?! *WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER WRITER:MISS XOXO*👌🏼 [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE* 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 _*Home of expert and perfect writers_* DEVOTED TO: *XARAH BUKHAR* TUKWICI: *TAWAN(Billyn Abdul)&MY YA HAJJA CE* PARTICULAR THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DOTAS: *BITTI FEEDHOM&DOTA BILLY S FARI* nanahafsat.wordpress.com This chappy is all urs tawan *billyn abdul* Barka da kammala rubuta littafin *karayar arziki* lapia,Allah ya barki da Abdul d’inki👌🏼 *53* *K*wanci tashi ba wuya awajen Allah bayan komawarsu Ammi damboa road dasati d’aya aka sanya Meenah a makarantar su Aysaa da Affy ana mata jarabawa taci aka sanyata a ss1 wato babban ajin sakandire na d’aya, Sosai take maida hankali akowanne subject,tafi Affy da aji d’aya ita Affy a jss3 take ita kuma Aysa tana zangon aji na k’arshe wato ss3, Meenah akwai maida hankali a aji ga ko’kari shysa kowa yake sonta matslar ta d’aya tanada mugun surutu da rashin ji duk wani list of noise makers tofa sunanta ne na farko duk lokacin break seka hango ta da k’awayen ta a school compound ansasu kneel down koda Affy tayi mata magana catake ta kyaleta itafa Allah yayanka mata baki dontai magana wlhy baxatai shiru ba meye amfaninsa Ammi tayi fad’an tayi harta gaji don Meenah trouble maker ce ta k’arshe ta maida Ammin kamar kakarta, Bayan sundawo daga school islamia suke xuwa da malami yake koya masu acikin gidan suda masu aikin gidan da daddare kuma lesson teacher ne yake xuwa ya masu extra lesson to anan d’inma se lesson teacher d’in yayi dak’yar sannan take xama ayi mata inba haka ba seta gagaresu don kusan kullum seta saka Affy kuka taita tsokanarta saboda taga tanada saurin kuka ita tana sharbar kuka ita kuma tana babbaka daria kullum haka sukeyi, <> Ranar asabar d’in farkon watan junairu mai martaba mai murabus wato mahaifin sarki Aliyu Hydar ya tafi k’asar waje donyi masa dialysis d’in k’odarsa wadda takamu da ciwon lopus Ahmad d’an Mai Alooma Ghaji shine yai masa jagorancin zuwa k’asar ta Germany a asibitin st josef dake Wiesbaden, Gidah yaxama sesu hajja gajiram da yakolo se tsula tsiyarsu suke suna tata rashin mutunci don mai martaba Aliyu Hydar kotakansu bayabi saboda Ammi taja masa kunne yabasu girmansu kome nene xasu yi babu ruwan sa idone nashi,hakan dayayi masune yasanyasu yin yadda sukeso a shehurin kullum cikin ‘yanta bayi da sauya wasu suke barin amintattun bayin da suka dad’e shekara da shekaru suna aiki a masarautar suna xaune tsakani da Allah to duk irinsu su gajiram ke korarwa suna yada magana suna habaice habaice shide mai martaba Aliyu Hydar kanzil baya ce masu saboda shi dama mutum ne wanda inba mugun sabo kukaiba tofa xaka d’auka kurmane don baya magana se jefi jefi shima seta kama tukun,duk wa’enda suka kora seya kirasu yabasu kud’i me tsoka yace suje suja jari haka yaketayi shiyasa mutan bornu ke k’aunar mulkinsa kullum shehurin acike yake da bil’adama kutare da makafi haka mai martaba Aliyu Hydar xebasu hannu su gaysa sam bashida k’yama ko hantara a mulkinsa abinde se wanda yagani kawai, <><><><> *shehuri* “Guy baba yace fa yananan akan bakansa nakasa gane maka count me out idan har baba yayanke hukunci” Mai martaba Aliyu Hydar yacewa Modu hakan xaune yake akan kujerar mulkinsa a makekiyar fadar dake shehurin suka d’aine aciki gefan damansa a k’asa kuma Modu ne kansa a k’asa da alama yatafi duniyar naxari ajiyar zuciya yasauke, “Your honor nifa bawai bansamu wacce nakeso na aura bane no nasamu kawaide bana jin baba xe yadda da wadda nakawo” Murmushi mai martaba Aliyu Hydar yayi kafin yace, “To fa kaikuma naka salon kenan?! To batada hali mekyau ne ko yaya?!” “No she’s descent kawaide...” Sekuma yai shiru, “Uhum kawaide me?!”cewar sarki Aliyu Hydar “Kiara sunanta Black American ce y’ar Florida” “What?!...” Maimartaba Aliyu hydar ya fad'a cikin tsananin mamaki yana bin Modu indimi da kallo wanda kanshi ke k'asa yana wasa da yatsun hannuwan shi kai da ka ganshi kasan yana cikin damuwa. “Eh!nace maka sunanta Kiara ya kake neman garani ne bayan kaji abinda nace.” Jinjina kai Maimartaba Aliyu hydar yayi domin sosai ya jinjina maganar Modu wai Kiara yasan ma baba kwata-kwata bazai yadda da wannan maganar ba, kallon shi ya sake yi yana sauke numfashi yace, “Guy ya kamata ka canza idan ba haka ba kaima gab kake da fad'awa inda na fad'a wato kaima a had'aka da *_ZAB'IN IYAYE_*, gara ka fito da Coca Cola shape kafin a nemo maka ramammiya me taurinkai kaima....”yak’arashe maganar yana yar dariya ahankali, “God forbid wallahi saika ce kai your honor.” Shareshi Maimartaba Aliyu hydar yayi dan shi kwata-kwata ma mantawa yake da wata matar shi Meenah ko waya suke da Ammi baya tambayar ta kusanma suna school suke yin wayar.Modu ne ya kuma gyara zama kasancewar duk ya damu ya takura gashi sarki maimurabus yace mai daya dawo one week ya bashi yazo ya fad'a mishi *_SON RANSHI_* idan ba haka ba toh za'a zab'ar mai a dangi tunda suna nan da yawa. “Your honor, please gimme some advice wallahi kaina ya k’ulle ya zan tunkari baba da maganata da Kiara?!” "”Uhmm ba ruwana cikin wannan maganar.” Maimartaba Aliyu hydar ya fad'a ba tare da ya kuma kallon Modu ba dan kar ya bashi ma tausayi,da mamaki Modu ya kalleshi mik'ewa yayi tsaye cikin jin takaicin shi yace, “Okay haka xaka ce ma?! Ba komai nima wata rana zaka nemeni ni zan wuce sai wata rana...!” Modu yana kaiwa nan yabar cikin fadar da kallo Maimartaba Aliyu hydar ya bishi yana mai dariya daga cikin rawanin shi, bayan ya fita ne sauran masu jira a k’ofar fadar suka koma aka ci gaba da gudanar da fadanci baki d'ayan su babu wanda be haifi Aliyu hydar ba amma duk suna girmamashi tare da bashi goyan baya wanda sosai yake jin dad'i. <><><><><> “A'ah yayyah wannan yarinyar baza tayi wahalar zurmawa ba, yanzu fa kusan kullum tana sashena wajan su fannah kuma tana dad'ewa bata koma can apartment d'inta ba..” Hajja yakolo ta fad'a tana kad'a k'afafuwanta hannunta rik'e da tufa sai faman jujjuyata take yi, wani d'an k'aramin k’ulli hajja gajirim ta d'akko tare da mik'awa hajja yakolo tana fad'in, “Yauwa idan tazo yau ki bata wannan magani kice tasa shi a k'asan gado setin inda yake kwana kice mata na mallakane seyanda tai dashi bama ze kuma tunanin yanada wata matar bayan itaba,kinga idan muka samu aka warware wancan auran sai itama muyi nata aikin amman kafin nan kina bata zumar nan kuwa ta hana d'aukar ciki?!” Hajja gajiram ta fad'a tana kallan hajja yakolo numfashi yakolo ta sauke tana fad'in, “Yayyah kenan tun yaushe ai kwananta d'aya da zuwa gidan nan na fara bata bayan nace mata na k'arin ni'imane kuma abin dad'in ma a gabana take sha dan na tabbatar, shashashar har da cemin ma zata bada kud'i a karo mata wata.” Sosai hajja gajiram taji dad'i sannan ta sake jajjadawa hajja yakolo kan cewar ta tabbatar wannan d'in ma tayi yadda aka umarce ta,daga nan hirar su suka ci gaba dayi har wani lokaci.Shigowar babagana ne ya katse musu hirar ya shigo idanuwan shi jawur a tsaye ya tsaya kyam akan hajja gajiram yayi kamar zai yi ball da ita,hajja gajiram ta had'iyi wani zazzafan yawu ita kwata-kwatama ta manta da alk’awarin da tayi mai na cewar zata sa aje abinciko mata gidan su Bilkisu sai yanzu da ta kuma ganin shi dan dama babagana sai yafi sati ba tare da ya nemi inda take ba sai in matsalar shice sannan zai nemeta har inda take. “Mami haka mukai dake?!” Babagana ya fad'a cikin zafin rai, miyau hajja gajiram ta had'iya akaro na biyu tana kallonshi, hannuwan shi ta kamo amma da sauri ya fisge ji yake yi tamkar ya bugeta tsabar takaici cikin sanyin murya tace mai. “Kaga kayi hakuri ina sane da wannan zancen so nake na gama da wannan matsalar wadda itama duk akan ka nakeyi sannan sai na ko......” “Enough Mami ni ce miki nayi na damu da waccan matsalar ne? Wannan itace damuwata itace matsalata mami billy zan aura ita nake so infact Mami billy itace numfashina ya kamata ki ajiye duk wani aiki kiyi min nawa idan ba haka ba kuwa wallahi sai na gayawa baba duk abinda kuke yi..” Daram-dam kirjin hajja gajiram dana hajja yakolo ya buga, da kallo suka bishi dan sun san yasan duk wani kulla-kullan su cikin sanyin murya da nuna kaskantar da kai hajja yakolo tace, “Yi hakuri yareemah kasan yayyah na kaunarka, yanzu ma zancen da mukeyi duk k'aruwar kace wannan d'inma zata yi maka shi kamar yadda kake so kai dai ka k'ara hakuri.” “Au Allah ko?!” Ya fad'a yana kallon hajja yakolo tayi saurin yin kasa da idanuwa dan karma ya gaya mata bakar magana, tafiya ya farayi yana cewa, “Ok shikenan na bada nan da one week wallahi ayi min abinda nake so idan ba haka ba komai zai iya faruwa ciki harda rasani da zakuyi..” Sakan shi yayi ya fita cikin izza da fad'in rai kamar wani arne, sukuma suka bishi da kallo baki a bud'e hajja gajiram ta kali hajja yakolo cikin yanayin damuwa ba tare da kowa yayi maganaba. Sumsum hajja yakolo ta mik’e bayan tad’an bawa hajja gajiram baki tana tafe tana waige harta k’arasa site dinsu Basma kasancewar tasan sarki Aliyu Hydar na fada kanta tsaye tashiga ciki ba fargaba, Basma tasakko daga sama da sauri jin door bell dama kuma tasan da xuwanta bayan sungaysa ne tamik’e xata d’akko mata ruwa da sauri hajja yakolo ta tsaida ita, “Basshi Bitti nasha ruwa yanxu nagode sauri nake” Ba musu Basma tadawo kanta k’asa wai ita kunyar uwar miji, Kunce gefan laffayarta yakolo tai taciro wasu k’ananan ledoji farare guda biyu ta mik’a mata d’aya, “Ungo wannan wanda namiki bayani nace xankawo maki d’innanne xakisa a wajen kwanansa gefan inda kikasan yana kwanciya na mallakane xakibani labari ki adanashi a kyakkyawan wuri karkibari yagani koya sani” Da sauri Basma ta karb’a tana murmushi had’e da jinjina kai jin an ambaci mallaka don akwaita da d’an banxan kishi inde akan Aliyu Hydar ne, “Nagode ummah Allah yasaka da alkhairi Allah yakara lapia da nisan kwana” “Kayya bar godia bitti babu komai wlhy aibabu godia tsakaninmu,se wannan karb’i ki rik’e da kyau” Ta mik’a mata ragowar d’ayar ledar dake hannunta d’auke da wasu abubuwa kamar tinya hannun Basma har rawa yake saboda xumud’i, “Wannan shi ake cewa sa kishiya k’wafa” Kad’a kai Basma tai gaba d’aya ta nutsu sotake taji nasa aikin, “Kinga wannan hum goran tula akece dashi ammafa me lak’anin ningi hatsabibi kenan” Murna Basma hardasu rungume yakolo don dad’i, “Ummah nagode k’warai Allah yasaka da alkhairi hak’ika ke uwa ce tagari Allah yabar k’auna” “Amiin bitti zanmiki text din yadda xaki komi” Cewar yakolo se dashe hak’ora take kamar gaske amma k’asan zuciyarta kuwa inbanda la’antarta ba abinda take bata jimaba ta mik’e tafice ita kuma Basma tahau sama don fara gudanar da tsibbun farko sannan tadawo tafara bunkawa cikinta goron tular se yauk’i yake kaida kagani kasan ansaka wani abin aciki amma shashashar ko lura batayi haka taketa dannawa cikinta, <><> Anayin hutun third term break Meenah tatafi yola hutu kamar yadda Ammi ta tsara ita dasu Affy dasu kai mata rakiya rashin ji se abinda ya k’aru ammafa tad’an k’ara gayu kad’an ba laipi, B’angaren uwar gidah sarautar mata Basma kuwa abin ya girmama kullum cikin d’irka mata magunguna su yakolo suke kullum de xancen d’aya ne daga mallaka sena ni’ima, kullum acikin bunkawa cikinta take yau goron tula gobe saiwar burgu jibi suce gasaya kuma kowanne da aikinsa amma kosau d’aya abun baya kama Hydar se ita Basman dake hawa kamar farashi sosai tayi k’iba amma kosau d’aya bata tab’a fashin wata ba, Gata dayawan buk’ata harijace shikwa Sarki Aliyu Hydar bahaka yakeba donma wani lokacin yana tausaya mata don sam shi abun baya gabansa ita kuwa Basma bata gajiya sekace engine haka take, Yauma kamar kullum tana xaune ta bubbunkawa cikinta magunguna se matse matsen kafafuwa take gashi sarki Aliyu Hydar yana fada se yarfe hannuwa take jin abun bana k’are bane yasa taja laffayarta ta nad’a tanupi sashen hajja yakolo kuyanginta biyu na biye da ita dak’yar take amsa gaisuwar da ake mata don amatse take jinta sam yau abin ba sauk’i....! __ _*Uzuri uzuri uzuri masoya makaranta wannan littafi ak’ara hak’uri da nana hafsatu de#AnaMugunTare_* _*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO👌🏼_* [4/22, 4:53 PM] My Xoxo: *SON RAI KO ZAB’IN IYAYE* 💖?👨‍👨‍👧‍👦 _*A STUNNING LOVE STORY_* *NA* ©NANA HAFSAT (MISS XOXO) ®HASKE WRITERS ASSOCIATION💡 _*Home of expert and perfect writers_* DEVOTED TO: *XARAH BUKHAR* TUKWICI: *TAWAN(Billyn Abdul)&MY YA HAJJA CE* PARTICULAR THANKS GOES TO MY TWO ADORABLE DOTAS: *BITTI FEEDHOM&DOTA BILLY S FARI* nanahafsat.wordpress.com Wannan shafin nakine *ya hajja tah* ina sonki har ruhina Allah yabarki da uncle yaraya mana ihsan yakawo healthy babies thanks for everything #Anatare😘💋❤ *52* *M*urmushi kawai Basma tai had’e da jan hannun layla su xaune akan wasu maroon royal chairs parlorn ya had’u ba k’arya komi maroon and coffee ne a parlorn harta babban console dake mak’ale a gefan wasu tum tum, “Babe gister ni mana fad’amin ya kikaji” Layla tace hakan had’e da d’ad’awa Basma duka a cinya, “babe abin se a slow kibari kawai ba’a magana ammafa nayi enjoying beyond” “Dagaske?!” Cewar layla had’e da wangale bakin mamaki, “Wallahi babe” “Yayi yayi babe allah yakawo ‘ya’ya masu albarka” Cewar layla had’e da bawa Basma hannu su tafa sund’an jima suna hira sannan layla tadubi agogon hannunta dake d’aure a tsintsiyar hannunta na hagu mik’ewa tai tana gyara yalolan mayafin dake jikinta, “Babe bari naje wucewa xamuyi gobe xanje kurfi Monday kuma zanyi resuming school” “Babe tun yanzu?!” Cewar Basma tayi rau rau da idanu xatai kuka, “Lalle daso kike mu rashe arasa wacece amaryar acikinmu?kirufamun kwandon sutura” “Babe kema fa muna saka ran nan gidan Kema zaki xauna” Zabga tagumi layla tai had’e da komawa kan kujera ta xauna murya a sanyaye tace, “Babe oud baya sona yanzu ashe d’an uwan mijin kine nayi nayi yatsaya ma mugaysa yak’i fa fur i don’t know why” “Nima se jiyan naganshi dama kuma sugar boo yacemin yanada cousin a Cambridge bantab’a kawowa shi bane se jiyan, Kiyi hak’uri i knw right bawai da wulak’anci yaki kulakiba kilan saboda hidimar biki ne tunda shine best man” Basma tak’arashe xancen tana patting bayan layla alamar ban hak’uri ahankali layla tasaka gefen mayafinta tana goge hawayen dake sharara a idonta kawar daxancen tai, “Babe kintabbata kingama komi na online schooling d’in?!” “Eh sugar boo duk yayi amma kinji professor yace dole senayi attending grad d’inmu sannan final exam ma kilan wai senazo” “To ai da sauk’i babe nikam namiki murna sosai kintuno Kendall dole se da tai repeating class” “Yeah haka fa to Allah yabamu sa’a” “Ameen Ameen” Suna cikin hira sauran yan uwan Basman da k’awayen ta suka shigo mata sallama don yau xasu koma kano sund’an tab’a hira sannan suka mata sallama xasu tafi sama tahau tasakko da ledoji cikeda kayan kwalliya da atamfofi kowannensu guda d’ai d’ai sunji dad’i sosai tare da nuna mata kayyayakin da Ammi tabasu suma ciki hardasu dangin k’amshi Har k’arshen compound d’in sashenta tarakasu hawaye na tsiyaya daga idonuwanta na rabuwa da ‘yan uwannata da’kyar su aunt yaruwaiya suka samu suka b’anbare Basman daga jikin Layla kowannensu hawaye kwance shab’e shab’e akan fuskokinsu, Ciki suka koma ita dasu aunty yaruwaiya dake faman rarrashinta,su Affy ne suka shigo d’auke da warmers na abinci bayansu kuma akwatunane guda shida dogarai ke shigowa dasu cikin jimami Basma tad’ago tana duban akwatunan lokaci d’aya gabanta ya buga k’wal ubancan tafad’a a zuciyarta ana nufin ace wannan yarinyar ce xata tare akuma sashen ta, Cikin rawar murya tadubi aunty yaruwaiya, “Aunty akwatunan meye?” “Oh wa’innan na al’adane da ango yake yiwa amaryar sa idan ankaita gidansa ake ce masu ra’aki da kususuram biyu sune ra’akin hud’u kuma kususuram” Sanyi Basma taji har cikin q’albinta don axatonta akwatunan kishiryarta ne dukkoda taji ana fad’in kishiyarta ta yarinyace k’arama kuma bayanzun xata tare ba kallonta aunty yaruwaiya tai sosai tahango kishi fal a idanunan Basman murmushi kawai tai lalle akwai ruguntsumi agaba kenan in har tunyanzu Basman tafara kishi da meenah.. Sakin jiki Basmah tai sunata hira dasu aunt yaruwaiya atare suka tashi suka rarrakata sashen su Ammi dasu hajja yakolo dake faman da shewa Basma baki suna haba haba da ita kaida kagani kasan akwai k’ulalliya me zuwa, *safiya ta gari* <><><><><> Bayan sarki Aliyu Hydar yagama shirinsa b’angaren Ammin sa ya nupa kasancewar Ammin aranar zata koma gidanta dake damboa road, Yana tafe dogaran dake kula dashi natake masa baya ba k’aramin kyau yayiba sanye cikin kayan sarauta na sarakai nad’in kansa yaxauna d’as abinde se wanda yagani harya k’arasa parlorn Ammi mutane basu dena bajewa a k’asa suna gaidashi ba, Ammin ce kad’ai a parlorn sanye cikin laffaya purple har k’asa ya sunkuya yana gaida Ammin,amsawa tai cikeda fara’a “Yau bakaje fadar ba?!” “Ammi ai baba yace nayi hutun sati d’aya waziri xeci gaba da gudanar da mulki tukun” “Oh to hakan yayi” Kansa a k’asa yana sauraron Ammin duk jinsa yake a takure kamar bashiba, “Nace Aliyu yaumu zamu koma kuma kasan da Aminatu zantafi kamar yadda mahaifin ku yace” “Eh Ammi nasan da xancen” “To abu nabiyu kuma se maganar schooling d’inta yakake ganin za’ai nida nayanke shawarar sanyata a makarantar su Affy to amma bansan kai yaya katsara ba” Cikin sauri yace, “Duk hukuncin dakika d’auka yayi dede Ammi Allah yasaka da alkhairi” “Yawwa,Aliyu na rok’eka kagade matanka biyu sannan meenah ba wajenka xata xauna ba inason dukda haka kadinga kamanta adalci atsakaninsu nasan dede se Allah tunda Aminatu zab’in muce ba son ranka ba amma dukda haka inaso kad’auka duk aurensu kai don son ranka kada kabari kai ya rabu Aliyu.....” “Toh Ammi Insha Allah” “Allah yamaka albarka ya k’ara maka lapia da nisan kwana” Cikeda kunya yace, “Amiin Amin Ammi” _Haka Ammin taxauna cikin hikima take sake lurar dashi yadda xe gudanar da mulkinsa tareda yin adalci a tsakanin al’umarsa sun jima suna tattaunawa kusan sakkowar su Affy daga stairs ne ya dakatar dasu daga maganganun da suke cikeda shagwaba meenah tasakko taxauna kusada Ammi tana cuno baki gaba sanye take cikin doguwar rigar abaya tayane kanta da mayafin abayar sosai tayi kyau,ta gefan ido sarki Aliyu Hydar yai mata kallon k’asa sosai tayi masa kyau barin d’an mitsitsin bakinta data cuno gaba, “Ammi kinga wai baxata tsaya asa mata janbaki ba ko?!” Cewar Aysa hannunta rik’e da jambakin kylie pusher pink murmushi Ammi tai tana bin meenah da kallo data cuno baki gaba ta had’e rai don karma Ammin tace asa mata, “To tunda bataso base a ‘kyaleta ba ko anawa mutum dole?!” Ammi tace hakan had’e da janyo Meenah jikinta ta rungumeta, “Tunda bakyaso su kyalekiko?!” Tashi tai daga jikin Ammin tana yatsina fuska, “Ammi kobah Aysa bace wai ita dole senayi kwalliya nasa jambaki xata nunawa friends d’inta ni kijifa Ammi sekace wadda ake advertising da ita kamar wata barbie doll kuma waima samun zatai bama ta bani nasa ba” Daria sarki Aliyu Hydar yayi ganin yadda Meenan take magana a kwainanance tana watsa hannu baya,juyowatai ita se a lokacinma ta lura dashi sake cuna masa baki tai tana karkad’a k’afa, “Baki gayda yayan naku ba” Cewar Ammi tanabin Meenah da kallo cikeda so da k’auna, “Nda wattu?!” Meenah tace hakan tareda kallon gefe ita a dole fushi take, Be amsaba yakalli Ammi data tsareshi da ido, “Ammi nizan wuce wajen baba

Chapter 14 of 35