Share this page
domin ta bata cikon kuɗin da za'a yi harkokin aiki kama daga kuɗin jirgi da Samy Baby ta bata tabbacin ta samu wanda zai mata hanya muddin ta saki kuɗi cikin kwanaki uku ma za ta ɗaga India, da yake kan Sofi ya kunce ilmin zamanin ta tare da wayewar ta sai suka gaza yi mata amfani saboda taƙi basu dama shaiɗan da muƙarraban sa kaɗai ta sau wa ragamar rayuwar ta cikin tsakanin jiya da yau ko ibada ta daina yi kwata-kwata da daman dai ba sosai take tsayar da Sallah ba amma daga jiya zuwa yau ko Sallah ɗaya bata yi ba,  cikar mummunan burin ta kawai take mafarki a bacci ko a farke ita dai burin ta ta ga bayan Yakaka "kaicho Sofi . Haka ta ɗau kuɗi zunzurutu naira Miliyan biyar da dubu dari shida ta bawa aminiyar ta Samy Baby bayan naira Miliyan huɗu da rabi da su kenan kuɗin da ke account ɗin ta da tun a jiya tayi transfer su zuwa account na Samira. Wannan farin kudin kuwa kudin duk wasu gwala-gwalan ta ne tare da wani daya na Momy kori da ta amsa Aro bata mayar mata ba duk ta hada su ta sayar ta dankawa Samira kudin.  "Samira dan Allah ki tabbatar kome ya tafi yadda ya dace kin ga Doctor tafiya zai yi to so nake kafin ya Dawo kome ya kammala sai dai ya dawo ya tarar da gawa kawai . "Kar ki damu ƙawata to meye amfanin ƙawancen mu idan ban miki ba ? Ke ce fa Sofiya ? kar ki damu jibi-jibin nan zan bar ƙasar nan ke dai ki kwantar da hankalin ki bana son yadda duk kika bi kika tada hankalin ki kin ga yadda kika koma kuwa? Kamar wata bazaurar Jaɓa . Ɗauke kai Sofi tayi tana jin zagin walaƙancin da Sofi tayi mata a fakaice . Cikin wayencewa Sami baby ta miƙa hannu ta ɗau wayar Sofi da take ajiye a tsakanin su ba tare da Sofin ta hana ta ba tayi wasu 'yan taɓe-taɓen ta a wayar ta ajiye mata daga nan Sallama suka yi saboda Sofi ta ce bata so Doctor Hamza ya dawo bata gida . Haka kowaccen su ta nufi motar ta Sofi ita ce ta fara barin harabar wajen kafin Samy Baby ma ta tada tata motar ta jaa ta cike da nishaɗi ta kama hanya ' Kome ya tafi mata dai-dai yadda ta tsara yanzu abunda ya rage mata kawai shine ta tattara duk wasu abubuwan da ta mallaka a garin Abuja ta cika motar ta ta bar garin zuwa garin Damaturu inda ta zaɓa domin gina sabuwar rayuwar ta . Ita da Sofi kuma daga ta ƙarasa rufta ta a rami kamar yadda ta shirya a jibi kafin ta bar jahar Abuja sun rabu kenan haihatan ah to aina Sofi ta san za ta kama ta ? Sannan ma cikin shirin ta na ƙarshe da zata yi ta san za ta ingiza Sofi ta aikata abunda zai sa ta iya ƙarasa rayuwar ta a gidan Yari da ba zata samu damar neman ta ba ma dan haka ita ta sha kenan ta kuma rufe shafin Sofiya a rayuwar ta "kayya Samira . Lokacin da Doctor Hamza ya dawo gida ya tarar da Sofi a kitchen tana girki ba ƙaramin daɗi ya ji ba dan haka ya saki jiki da ita ya tsaya a kitchen ɗin suka yi 'yar hira yana ta jaan ta da wasa . Ƙarfe biyu dai-dai ya musu Sallama ita da Yakaka bayan ya haɗa su ya musu 'yar nasihar kan su zauna lafiya kafin dawowar su sannan ya ɗau kuɗi masu kauri ya danƙawa Sofi ko za su buƙaci wani abu sai suyi amfani da shi duk da ya san a store da kitchen akwai kome na daga kayan abinci Dauriya Sosai Yakaka ta nuna lokacin da suka masa rakiya bata yi kuka ba sai Sofi ce ma ke zuba masa shagwaɓa wai za tayi  kewar sa shi kuma gaba ɗaya hankalin sa yana kan Yakaka Ko kaɗan ba son ransa bane yayi nisa da ita a dai-dai wannan lokacin sai dai dan ba yadda zai yi aikin sa aikin ceton rai ne dan haka bashi da zaɓi na lokacin da zai yi tafiya a bakin aiki inda za shi ma ceton rai zai tafi dan haka tilas ne tafiyar sa. Haka suka yi Sallama cike da alhini ya jaa motar sa da zai tafi da ita zuwa gidan Doctor Suleiman wanda shi ne zai kai shi airport ya koma da motar tasa gidan shi . Yakaka ita ta bada hanya Sofi ta fara wucewa cikin gidan suna shiga Sofi ta rufe ƙofar ta murɗa ɗan makulli ,  ta ƙasan ido Yakaka ta dube ta Kallon nan da take tsoro shi ta hango a idanun Sofi idan ba gizo idanun ta ke mata ba ma ta ga kamar tana mata wani guntun murmushi. Zuciyar ta ta doka da ƙarfi sum-sum ta wuce ɗakin ta ta bar Sofi a wajen . Kitchen ta shiga a gur-guje tayi girki ta zuba a kula ta bar sauran a tukunya sannan ta jidi ruwan gora da juice ɗin da take ɗan sha ta kai fridge na ɗakin ta ta sa ta dawo ta ɗau abincin tazo fitowa daga kitchen ɗin ta ga Sofi ta tare hanya har yanzu dai wannan kallon ne a idanun ta sannan bata janye murmushin mugunta da take mata ba . Muƙut Yakaka ta haɗiye yawun tsoro . "Mai ciki girki aka yi ne ? Sofi ta tambaye ta fuskar ta a yanayin da bai yi dai-dai da kalmomin da ta furta ba. "Eh nayi girki ne Anty Sofi , naki ma yana tukunya daman yanzu zan zuba miki ' "Bari na kai nawa ɗaki . Sai da Sofi ta mula sannan ta ɗan matsa da kyar Yakaka ta wuce tana shiga ɗaki ta murza ɗan makulli tana jin nutsuwa na safko mata daga nan bata sake fita daga ɗakin ba har dare komen ta a ciki take yi tsakanin banɗaki da tsakar ɗakin Sai wayar ta take yi da Falmata da kuma Lubna da su duka biyun suke cikin watan haihuwar su . Washegari Kamar yadda tayi a jiya haka yau ma tayi girkin ta ta kai ɗaki ta rufe tsawon yinin bata bari sun haɗu da Sofi ba duk kuwa da cewa ta ji motsin ta daga falo . Sau biyu ta samu damar yin waya da Doctor hamza wanda ya shaida mata cewa a gobe zai dawo idan Allah ya yarda dan haka ta ƙarasa yinin ranar cikin nishaɗi da jin daɗin dawowar sa duk da cewa tsakanin jiyan da yau laulayi sosai ya taso ta gaba gadan-gadan kawai dauriya take yi . A washegari da safe Bayan tayi wanka taso fita ta haɗa abin karyawa amma jin yadda Sofi ta ƙure muryar tv tana jin kiɗa ya bata tabbacin tana falon ita kuma cikin kwanakin nan kamar Allah ya ƙara mata tsoron Sofi ne wani irin matsanancin tsoron ta take ji ta yadda ko haɗuwa bata so su yi dan haka ta fasa fita tayi zaman ta kawai a ɗakin da daman ba jin cin abincin sosai take ba yau ta tashi da matsanancin ciwon kai ne . Can kamar hantsi haka tana ɗan taɓa bacci ta ji wayar ta ta ɗau kiɗa , da kyar ta miƙa hannu ta ɗau wayar ganin ƙiran daga masoyin ta ne yasa tayi azamar ɗagawa . Cike da ƙauna da kulawa suka gaisa kafin Doctor Hamza ya shiga rarrashin ta a ƙarshe ya shaida mata cewa dawowar sa a yau ba zata yiwu ba sai nan da kwanaki biyu watau ranar juma'a Wannan karon bata ɗaure ba sai da ta sanya masa kuka da kyar ya iya shawo kan ta tayi shiru da alƙawarin zai dunga ƙiran ta akai-akai duk dai idan ya samu dama . Ba dan sun so ba suka yi sallama saboda  jiran sa da ake yi., duk da cewa ya so yayi magana da Sofi ma domin ya sanar da ita ɗaga dawowar ta shi amma sau uku yana gwada ƙiran ta yana nuna masa cewa tana  amfani/waya da layin nata dan haka ya haƙura ya tura mata saƙo kafin ya kashe wayar sa . Sofi da take baccin asara ƙiran waya ne ya tada ta lokacin da ta ɗau wayar wasu numbers ta gani haka irin na ƙasar waje idan idanun ta sun gani dai-dai ma numbers ɗin na ƙasar india ne dan haka cike da ɗoki ta ɗaga kiran Kamar yadda ta zata ne Samira ce take ƙiran ta daga ƙasar india kamar yadda numbers ɗin suka shaida mata kafin ma ta ji daga bakin Samy Baby . Bata jira sun gaisa ba a ƙagauce ta fara tambayar "Samira kada dai har kin isa india ? Nan Samy Baby tace mata ai ma tana karnataka har kuma ta gana da Boka yanzu haka ma da take jin hayaniya a cikin jirgin ƙasa take kan hanyar ta na komawa masauƙin ta ta kasa haƙura dai dole ta ƙira ta fara mata albishir Boka yace nan da awa biyu zai kammala aikin ta . Wani irin ihun jin daɗi Sofi tayi tana jin kamar an mata bishara da gidan Aljanna. za ta sake yin magana ɗif Samy Baby ta kashe wayar ta . Tana wani murmushin mugunta ta buɗe gidan sim ta zare sim card ɗin ta gutsittsira shi da haƙorin ta ta watsar a gefen hanya ajiye wayar tayi a gefe kafin ta ɗaura seatbelt a hankali ta daga glass na motar kafin ta tayar da motar da bala'in gudu ta cilla ta a titi . Yadda take gudu a titi ba'a ce Mace ce ke jaan motar ba har dai tayi nisa da ainashin garin Abuja tana tuƙi tana bin waƙar da take tashi ta sifukun motar ran ta fes a dai-dai lokacin ji take duniya ta mata daɗin da bata taɓa jin makamancin sa ba ta samu duniya abunda ya rage kawai sai ta miƙe ƙafa domin cin ta . Kafin kamar walƙiya ta ga ɓullowar wasu motoci biyu da gudu da suka yanko daga cikin daji suka yi banga-banga akan titi da yasa ta cikin matsanancin tashin hankalin da ya maye gurbin nishaɗin da take ji ta taka birki ƙuuuuuuu da ba domin Allah ya kiyaye ba da babu abunda zai hana motar tayi ƙundumbala da ita . Samy Baby bata tabbatar yau ita ce rana mafi muni a tarihi rayuwar ta ba sai lokacin da ta fahimci hannun ko su waye ta faɗa' Masu yin garkuwa da mutane ne kidnappers  da take jin labarin su wai-wai sune yau take ganin su a gaban ta kamar a mafarki . Kwakwalwar ta taƙi samun kwanciyar hankalin yin tunani ɗaya kamar yadda idanun ta suka ƙafe ƙaf daga samun damar zubar hawaye duk wasu kalmomi kuma suka ɓace suka shafe daga bakin ta har zuwa lokacin da suka ɗora mata bakin bindiga suka tasa ƙeyarta bayan sun kwashe kome da yake cikin motar suka nausa da ita cikin daji . *** Sofi ji tayi farin-cikin da take ciki ya mata yawan da bata jin za ta iya jurar sa bata ɗan wataya ba dan haka ta ɗau wayar ta da sai lokacin ta lura da saƙon Doctor Hamza . Wani tsallen jin daɗi ta sake yi jin cewa ba zai dawo ba ma a yau sai nan da wasu ƙarin kwanaki wanda hakan duk alamun nasara ne a gurin ta domin kuwa dama ce ta sake samuwa a gare ta . Kiɗa ta kunna a wayar kafin ta buɗe wata 'yar karamar loka da take jikin gadon ta ta fara zaro kwalabe da sauran kayan mayen ta ' Sai da ta tara su jibgi a gaban ta sannan ta shiga ɗaga su ɗaya bayan ɗaya tana tuttulawa a cikin ta tayi ha'in tana jin ta tamkar tafi kowa farin-ciki a duniya tana tangaɗi ta shiga juya jikin ta tana rawa . Daga can ɗakin Yakaka da ta ji shiru babu alamun motsin sofi a falon sai ta lallaɓa ta fito kai tsaye ta tafi kitchen saboda yunwa da ta fara sasuƙar ta har jiri-jiri take ji . Cikin awa guda ta gama irin girkin da take jin sha'awar ci ta kwashe ta kai ɗakin ta ba tare da ta rufe ƙofar ba sai kawai ta faɗa banɗaki tayi wanka ta ɗauro alwala saboda azahar ta gabato. Tun tana wanka take jin ana ta ƙiran wayar ta har sau uku dai-dai da fitowar ta wayar ta sake ɗaukar kiɗa da sauri ta ƙarasa ta ɗaga ta lokacin da ta ga sunan mai ƙiran Falmata ce . "Hello Falmata na kina lafiya ko ? Ko haihuwar ce ? Ko kin haihun ne ? Ta jero mata tambayoyin ba tare da ta ajiye numfashi ba saboda koyaushe cikin bin haihuwar Falmatan take a rai musamman da yake ita ta taɓa haihuwa ta ɗana ta ji yadda haihuwar ke da zafi duk sai take jin tausayin ƙanwar ta kullum cikin addu'ar sauƙa lafiya take mata musamman da cikin na Falmata ya kusan shige kwanakin haihuwar sa da hakan sabon abu ne a haihuwar fari . "Hello Falmata kina jina kuwa ? Ta sake furta hakan cikin damuwa Dariyar da Falmata ta cika mata kunne da ita yasa ita ma ta murmusa tana sauƙe ajiyar zuciya ta ce "meye abun dariyar kina jina ina miki magana wallahi duk kin ɗaga min hankali ganin yadda kike ta ƙirana ina wanka na zo kuma na ɗaga kin yi shiru. "Yakaka bani nake ta ƙiran ki ba wallahi ni yanzu nan na ƙira ina ƙira kuma kika ɗauka . Ɗan jimm Yakaka tayi "to waye yake ƙirana ? Ta tambayi kan ta , sai bata wani damu ba kawai ta zauna a bakin gado suka shiga hirar su ita da Falmata . Sun ɗau tsawon lokaci suna hirar da take sanya su duka biyun a farin-ciki tare da sake ƙaunar juna ' Kafin kamar daga sama Yakaka ta ji an damƙi kafaɗar ta da yasa ta matuƙar tsorata ta saki wayar ta ta faɗi . Jikin ta yana rawa ta miƙe tsaye tana kallon Sofi wacce take tsaye kiƙam hannun ta ɗaya a ɓoye a bayan ta. An-anty Sofi in-ina wuni. Wata irin shashashar dariya Sofi ta saki da hatta Falmata da bata kai ga katse wayar ba ta ji ta . Zuciyar ta ta fara sauya bugu daga lokacin da ta fara saurarar duk wasu zantukan da Sofi take yi cikin maye murya sama-sama . "Kin yi zaton na kyale ki ko ? A tunanin kin shaa da ni kenan ? Ƙaramar kwakwalwar ki ta baki tunanin kin yi nasara ?  Ni Safiya na bari ki rayu da Mijina ki haihu ? "Wacce irin cusashiyar ƙwakwalwa ce da ke ? Ta kifi ? Kin taɓa ganin an yi haka ? Ba zai yiwu ba , ba zai faru ba ba zai taɓa faruwa ba ki zo ki gina rayuwar ki a kan tawa Hamza nawa ne ni Kadai. "Dole na rusa rayuwar ki a duk lokacin da na so , dole ki mutu Yakaka tunda kin ƙi fita a rayuwa ta to zaki Mutu zaku mutu tare da ke da abunda ke maƙale a cikin ki . Wuƙar da take ɓoye a ɗaya hannun ta ita ta zaro wata kakkaifar wuƙa ce sabuwa fil da alama ita ce mafi girma a cikin jerun set ɗin wuƙaƙen ta . Lokacin da Yakaka ta ɗora idanun ta akan wuƙar ta kuma ji abunda Sofi take cewa jikin ta gaba ɗaya sai ya saki kamar an zare mata lakka wani yanayin da ta kasa tantancewa da shi ya shiga bin gaɓɓan jikin ta idanun ta kuma suka kafe akan wuƙar a hankali ta ji kunnuwan ta na toshewa . "Amma kafin na kashe ki zan so na miki ƙarin bayani kan dalilin mutuwar ki zan faɗa miki irin faɗi tashin da na dunga yi dan na auri Mijina da irin son da nake masa , da nasan ke kan ki za ki iya min uzuri akan kashe ki da zan yi . "Tun ranar farko da na gan shi na kamu da son sa , haka na dunga faɗi tashi alhalin ina korar masoyana har nayi nasarar da aka min tsafin da yasa ya fara kulani a matsayin budurwar sa . "Kar kiyi zaton ke ce rai ta farko da na kashe a kan Hamza ke ce ta uku na farkon jariri ne lokacin da aka bani tabbacin idan har ba'a yi mummunan aikin da aka raba tsakanin jaririya da uwar ta ba to babu shakka uwar jaririyar ita ce matar da Hamza zai aura ba ni ba idan kuwa har aka raba tsakanin su za'a kaɗa uwar wani waje mai nisan gaske ni kuma cikin shekarar Hamza zai aureni hakan ne kuma ya kasance . "Na sha wahala kafin na samu wani ɓangare na daga zuciyar Hamza wanda a ƙarshe sai da aka min aikin da aka kashe wani Mijin da zuciyar sa ta mutu a ƙauna matar sa a can ƙasar india bayan duk na sha wannan wahalar ina zaman daɗi da Mijina za ki ratso rayuwar mu ? "Ya kike tunanin ba za ki zama ta uku ba a cikin jerin Mutanen da za su mutu ba ? Dole ki Mutu dole ki zama mutum ta farko da zan kashe da hannu na akan Hamza . Wasu kauraran hawaye ne suka zubo mata kafin ta cigaba da cewa "kin ga laifi na ne ? Ki duba yadda na lalata jikina saboda kawai na burge Hamza na lalata Mahaifata saboda kawai muyi rayuwar hutu da Hamza bana son ko 'ya'yan cikina su ratsa tsakanin mu . Juyowa tayi ta wani irin fisgo Yakaka da daman tuni alhinin Mutuwa ya safko mata bata da wani sauran ƙarfi . Ta gwara kan ta da bango kafin tayi majaujawa da ita a tsakiyar ɗakin ta yasar da ita da wani azabar ciwo ya sarƙe Yakaka yasa ta saki ihun da ya daki dodon kunne Falmata wacce duk take jin abunda Sofi ke cewa.. Ita ma ihun ta saka da ya amsa sashin ta gaba ɗaya da ƙarfi ta miƙe tsaye lokacin da take sakin wayar hannun ta ta faɗi ƙasa tunanin ta yana tabbatar mata da cewa Sofi ta kashe mata Yakaka a yau . Da gudu Hajja da wasu bayun ta biyu suka shigo waɗan da ihun ta ya je har kunnen su Hajja tana shigowa ta gan ta a durƙushe tana murƙususun ciwo tare da ihun ƙiran sunan Allah da na Yakaka cewa take "Yakaka na ta mutu Sofi ta kashe Yakaka dan Allah ku kaini Nigeria . Hajja wacce kallo ɗaya ta yiwa Falmata ta ga alamun haihuwa a tare da ita ita kuma cewa take "To Alhamdulillah abun yau yazo kenan fatan mu Allah ya raba lafiya sannu Uwarɗakina sannu kin ji daure kowacce Mace da haka ta zama uwa daina iface-ifacen nan ikon Allah ke kuma taki naƙudar da ƙiran sunan 'yar uwar ki ta zo miki o wannan ƙauna ta ku ta girmama . Kafin mintoci goma sha biyar labari ya je wa Hajiya Umma kan cewa Falmata na naƙuda nan take ita da kan ta ta taso zuwa sashin . Ƙarƙashin Umarnin Sarki aka fita da ita zuwa asibiti da kawo lokacin Falmata ta daina surutai saboda ganin idon Hajiya Umma sai dai ruwan hawaye da suka ƙi daina zuba mata a zahiri ciwon da take ji a cikin ranta na rashin 'yar uwar ta yafi ciwon da take ji a sassan jikin ta na buɗuwar ƙasusuwan ta sakamakon abunda yake cikin ta da ya shiryawa fitowa duniya a yau . *** Ciwon da ya turnuƙe Yakaka daga ƙasa ya riƙe mata mara shi yasa ta kasa yin wani yunƙuri na kwatar kanta har lokacin da Sofi ta ƙaraso inda ta jefar da ita tana mata wannan kallon da salon murmushin da zuwa yanzu ta san manufar ta ta kuma gane dalilin da yasa take jin matsanancin tsoron Sofi ashe dan ta ita ce ajalin ta Ɗaga wukar Sofi tayi da iyakar ƙarfin ta ganin  haka ya sa Yakaka kare fuskar ta da tafukan ta biyu tana maimaita kalmar shahada a cikin ran ta kamar yadda take jin kome da ya shafi duniya yana shafewa daga ƙwaƙwalwar ta lahira na maye gurbin sa . duhun da yake da alaƙa da tsanantar gudun jinin jikin ta da aikin da ya wuce misali da zuciyar ta ke yi ya safko yana mamaye ganin ta ya koma dusu-dusu take iya hango abunda yake faruwa ta tsakanin yatsun hannunta Ba zata iya tantance mafarki ne ko ido biyu ba lokacin da ta ga kamar an ɗaga Sofi anyi cilli da ita gefe . Doctor Hamza take Iya gani ya gifta ya ɗago Sofi da ta faɗi a gefe. Mari ya shiga ba ta a fuskar ta dama da hagu kafin ya ji cewa marin bai gamsar da shi ba ya shiga ƙoƙarin zare belt ɗin dake kunkumin sa da muryar da ba tayi kama da ta shi ba yake cewa "Sofiya ashe haka kike ? Haka kika min Sofiya ? Haka za ki min ?  Kisa kike ?  daman Sofiya kisa kike yi ? . Ta ko'ina yake zuba mata belt ɗin a jikin ta kafin ya fisge ta su ka fice daga ɗakin ya tunkuɗa ta ta bugu da bango jikin ta gaba ɗaya ya farfashe yayi shatin belt . Ragwab ya zauna akan kujera kamar kuma ya zauna akan ƙaya sai ya sake miƙewa gaban ta ya dawo ya tsaya yana kama goshin sa da hannun sa ɗaya muryar sa na karkarwa yace "Sofiya duk abunda na ji kina faɗa da bakin ki gaskiya ne ? Gaskiya ne ? Kin yi kisan kai kina kuma yunƙurin sake yin wani a cikin gidana duk kuma a dalilina ? Fisgota ya sake yi a inda take yashe tana wani wuri-wuri da ido ko ɗigon ƙwalla babu a idanun ta illa wani irin ƙuna da ran ta ke yi ganin kome take kamar a mafarki . Fisge jikin ta tayi muryar ta a hargitse tana sarƙewa bata cikin hayyacin ta tace " Duk abunda ka ji nace na aikata a ta dalilin ka nayi kuma a shirye nake da nayi abunda yafi haka Wallahi ni Sofiya a shirye nake da na kashe kowa akan ka , idan kuma aka nemi raba ni da kai ta ƙarfi zamu Mutu tare ni da kai zan kashe ka na kashe kaina .....' Wani marin ya daɗa bata kafin ya fisgota Yana tunkuɗa ta hanyar barin gidan yake cewa , "Na sake ki Sofiya Ni Hamza na sake ki saki Uku ki fita daga gidana kar ki sake nuna min fuskar ki har abada na tsane ki . Chak! Sofi ta tsaya ta tirje taƙi tafiya lokacin da kalmomin sa ke mata amsa kuwwa a kunnuwan ta suna zama kamar ɗigon ruwan narkakkiyar dalma a kogon kunnen ta . Zata silale ƙasa ya ɗago ta da ƙarfi ya ƙarasa tunkuɗa ta waje ya rufo ƙofa a fuskar ta da har sai da ƙofar ta bugi bakin ta ya fashe . Wani ihu tayi ta shiga buga ƙofar kamar zata ɓalla da yasa makofta fara leƙowa wasu ma daga sama suke buɗe windows suna leƙen ta . Lokacin da ta fahimci ta zama mahaukaciya sai ta tashi da gudu ta nufi bakin titi ta tare taxi . Tana zama ta faɗi inda zai kai ta kafin ta cigaba da Sambatu cewa take " wallahi ban saku ba Hamza ƙarya kake ni da kai mutu ka raba ahaf ai daga aikin karnataka ya fara ci nan da gobe ma zan dawo gidana Kashe Yakaka kuma ban fasa ba wallahi sai na kashe ta wallahi sai ta mutu.. Ƙiiii mai taxi ya ci birki abinda kawai ya iya cewa shine "Hajiya Dan Allah sauƙa na fasa yin Area da kika faɗa . Haka ta sauƙa bayan ta cusa masa zagin rashin tarbiya da turanci shi kuwa ya jaa motar sa da ƙarfi ya buɗa mata ƙura ' Haka ta taka da ƙafa tana tafe tana surutai a dai-dai lokacin ba wanda zai gan ta ba tare da ya mata ganin mashahuriyar Mahaukaciya ba . *** Lokacin da Doctor Hamza ya koma ɗaki inda ya bar Yakaka anan ya tarar da ita yana share guntun hawayen idanun sa ya ɗago ta ya rungume ta tsam a jikin sa yana jin yadda bugun zuciyar ta ke sassarfa da yasan hakan hatsari

Chapter 101 of 103