Share this page
aka fidda rai da sake ganin ta , Cikin masu zuwan har da yayun su maza da matayen su da wasu daga cikin 'ya'yan su , sai kuma dangin su na wajen uwa da na uba duk gasu nan dai gayya guda , Nan take labarin auren ya sake bazuwa a tsakanin su , jin cewa har da na 'yar Rahima mace da Hamza ɗan Aminatu, da za'a musu haɗin gida, nan take suka yi sabon zama na musamman , inda suka sake ninka gudummawar su da zasu tafi da shi da daman turaren wuta ne da turaren jiki na ruwa ( Humra ) har ma da na wanka da mayukan jiki da na gashi , ( kulaccan da karkar ) suka ɗau nawin yiwa Rahima ƙarama gudummawar sa ,a matsayin su na dangin uwa sai suka sake ninkawa da wani haɗin turaren wutar da humran , su kulaccan da karkar makamancin wanda yake ajiye duk suka haɗa acikin manyan mazubai suka rufe , Sannan suka sake ƙarawa da kayan ƙamsasa girki da daɗaɗa shi irin nasu na can , haɗi da ingantattun ganyayyaki haɗin shayi ( tea ) da suke ƙara lafiya da kuzari tare da sanya nishaɗi, shima roba-roba suka keɓence shi . Bayan haka matar baban wan su da ake ƙira Hajje khalsum ta ƙira Amnee tana sake tambayar ko akwai kuma wani abunda suke so a taho musu da shi daga nan N'Djamena ? Nan Amnee tayi amfani da wannan damar take sanar da ita buƙatar ta na son a haɗo mata kaya gyaran jiki tare da magagungunan mata ,irin nasu masu ɗauke da sunadaran da suke ƙamsasa kowanne saƙo na jikin duk wata matar da take amfani da shi , bayan sun mata gyara ciki da bai . Amnee ta cigaba da cewa a faɗa mata adadin kuɗin da zai isa a kawo kayan gyaran kashi uku , kafin ta gama bayani Hajje Khalsum ta katse ta , tana sanar da ita cewa ai wannan ta kawo cuta inda ake da tushen maganin ta , domin kuwa ƙanwar ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya , ƙwararriya ce ta wannan fanni na gyaran mata ciki da waje , domin kuwa faɗin ƙasar su ansa da ingantattun magungunan ta , babban shago ne da ita anan babban birnin N'Djamena da taƙe sayar da irin waɗannan magungunan da kayan , har kuma ƙasa-da-ƙasa ake ɗaukar ta tana zuwa gyaran jikin , tare da haɗawa mata ingantattun magunguna dan haka kada ta damu , nan da kwanaki biyar inshaAllah zasu taho tare da ita . Zuciyar Khaalty Rahima ta daɗa cika da ƙaunar 'yar uwar ta , domin ko bata faɗa ba tasan cewa dan Yakaka ne Amnee ta ƙira Mai gyara , da daman tuntuni take son tayi wani yunƙuri akai , amma kunya da kara suka hana ta ganin cewa duk wasu ragamar bikin na hannun Amnee , sai kuwa ga shi zata sa a gyara mata Yakaka , Duk abunda ake na zafafa shirye-shirye , Yakaka ta maida kan ta mai zaman ɗaki , daga kuma ta samu sarari sai ta shige banɗaki taci kukan ta , tsoro da damuwa sun hana ta walwala , tuƙuru tsoron rayuwar da zata riska nan gaba kaɗan take , Daga Amnee har Khaalty Rahima ba wacce ta bata sarari bare ta ji damuwar ta saboda sun riga sun san ko damuwar ta mecece ?dan haka suka kyale ta suna sabgogin su , Ganin bata yin wani shiri , ko alamun gayyatar ƙawaye koda na mutunci ne yasa suka fara lallashin ta kan cewa " yakamata ita ma ta gayyaci mutane , ranar auren ta rana ce mai ɗimbin tarihi wacce yakamata mutanen da duk tayi ko da zaman mutunci da su ne su shaida wannan ranar , Yakaka tace " ita fa bata da ƙawaye , ƙawarta ɗaya Lubna kuma tayi aure , bayan ita bata da wata ƙawa , da suka matsa mata ma kuka ta sa tana cewa " Amnee Mama kun san fa irin rayuwar da muka yi , ina mutane suka mu'amalance mu da mutuntawa bare har su kai mu kusa da su ? Da zamu iya ɗorar da zumunci idan bayan Malama Maryam da Lubna babu wasu mutane ta wajena , sai ta basu tausayi suka bar maganar , amma daga baya sai suka sa ta ƙira Malama Maryam ,bayan sun gaisa ta miƙawa Amnee wayar dan ita kunya take ji ta faɗi ranar auren ta da kanta , ta baki da baki Amnee ta shaida mata sanya ranar bikin 'yar ta kuma ɗalibar ta , Ba ƙaramar murna Malama Maryam tayi ba har ma tayi Alƙawarin halartar bikin , basu bi ta kan Yakaka ba wacce take faman ƙwalan-ƙwalan da ido tana son sake yin wani kukan , suka yi ficewar su daga ɗakin suka bar ta , dumuwar ba zai sa a fasa kome ba , domin na ɗan lokaci ne kuma gata ne babba ake shirin yi mata . Cikin kwanakin nan Falmata sai ta fita walwala , domin ita labarin bikin Yakaka da Yaya dakta yayi awo gaba da kaso kusan talatin na damuwar ta , duk da cewa ba wai ta daina jin damuwa da rashin ji daga Biyamuradi bane , farin-cikin auren Yakaka ne yake saisaita mata damuwar ta . Doctor Hamza kuwa tun ranar da ya isa Abuja ya so sanarwa da Sofiya halin da ake ciki kan lamarin aure da ya taso masa , saboda hakkin ta da yake kan sa ya zama dole ya sanar da ita . Sai dai yadda ta tare shi cike da ɗoki kamar wanda ya shekara rabon sa da ita ba kwana guda ɗaya tal ba , sai ya kashe masa ƙwarin guiwar sanar da ita labarin da yake tafe da shi sanin da yayi ba abun farin-ciki bane a wajen ta, Sai yayi zaune kawai yana bin ta da kallon yadda take ta ririta shi tana tarairayar sa , tayi kwalliyar ta fes-fes cikin riga da siket , ta mammatse manyan kayan da yafi so tare da ita sun firfito ko yaya ta motsa suna rangaji tare da dusashe masa ƙarfin gani suna tayar masa da kwaɗayi . Shi dan ta shi tuni ya haƙura da ya zauna tare da ita ,ita kaɗai saboda a halin zaman su na aure babu ta inda ta kuskuro shi sai ta wajen girki wanda shi kuma hakan bai wani dame shi ba saboda shekarun girma da ya fara shigo masa , a matsayin sa na likita shekara arba'in ya kamata ya fara kiyaye kansa daga ciye-ciye barkatai da sunan jin daɗi . Rashin haihuwar su kaɗai ke ɗan taɓa ransa , kuma yayi-yayi da ita taje asibiti ya haɗa ta da kwararrun likitocin mata su duba ta taƙi , daga baya yayi watsi da ita lokacin da ya fahimci akwai wata matsala tata da take ɓoye masa , koma menene ita ta sani shi dai ya san lafiyar sa rass , domin a farko-farkon shekarun auren su yayi gwaje-gwaje da dama kan rashin haihuwar su domin gano ina matsalar take ? Ta haka suka tabbatar masa da ingancin lafiyar ƙwayayen halittar sa dan haka shi bashi da fargaban kome , Yawan ƙaunar da take gwada masa salo-salo yasa yake ɗaga mata kafa , domin kuwa ta san ta kan sa sosai bai wani cika murɗe mata ba muddin ta raɓu da jikin sa , Domin a yanzu ma kasa sanar da ita labarin ƙarin auren sa yayi , maimakon haka kawai sai ya ɓige da neman samun nutsuwar gangar jikin sa ya shiga shinshinata yana gwada mata soyayya irin wacce ita dai tunda take da shi bai taɓa yi mata makamancin haka ba , zuciyar ta ta ji ta kunburo tana daɗa tunbatsa da ƙaunar sa , gefe guda kuma wani irin tsantsar farin-ciki take ciki , "yau Doctor ne yake nuna mata zallar so tare da kalamai masu tausasa zuciyar masoyi ? Babu shakka masu iya magana suna cewa daɗewa a mabauta ma ƴanci ce ." Shi kuwa a ɓangaren sa zuwa washegari ya tabbatar dai ba zai fa iya sanar da ita ba , sai ya kuɗurce zai tura ta can Maiduguri da wuri , su da suka rakito auren sa san yadda zasu yi su sanar da ita domin shi Allah ya sani ba zai iya ƙarawa kansa damuwar haukar da sofiya zata iya yi ba akan ta shi damuwar da yake ciki , gara tayi haukar ta acan idan yaso ma ta huce akan ita Yakaka , shi duk wannan ba damuwar sa bace tsuntsun da ya jaa ruwa . Saɓanin yadda ya zaci damuwar sa zata zama ƙanƙanuwa sai lamarin ya zarce tunanin sa domin tunda aka yi batun auren su kullum tsaffin laifukan ta daɗa sabunta kan su suke a zuciyar sa , baki ɗaya sai ya susuce kamar farkon lamarin . Ya zama ko office ya tafi baya wani taɓuka aikin kirki , har waɗanda ke tare da shi suka fara fahimta , Suleiman Amininsa shine ya fara farga da yawan damuwar da yake ciki ya kuma matsa masa da tambaya ? a farko Doctor Hamza ba shi da niyyar sanar da Suleiman da kan sa , sai ko bayan auren , sai dai yadda ya matsa masa da tambaya yana nuna damuwar sa a fili ya sa shi sanar da shi cewa "aure zai ƙara da ƴar Innar sa da aka ba shi , " Wani sasakai Doctor suleiman yayi yana kallon Hamza , kafin ya wani kwashe da dariya , sai da yayi dariyar ta ishe shi , Doctor Hamza bai ce masa ƙala ba illa ma rubuce-rubucen sa da ya shiga yi , yana jin yadda ransa ke ɓaci da dariyar walaƙanci da suleiman ya sanya shi a gaba yana yi . " Ka ce dai alƙadarin Safiya ya karye , zaka yi wani yunƙuri dan ganin ka fara tara naka zuri'ar , lamari yayi kyau haka ake son Namiji to amma nayi mamaki ina kuma kan yi ko yaya zaka yi da mata biyu ? Da wutsiyar ido Doctor hamza ya dube shi , ba tare da ya bar abunda yake yi ba yace , " Su masu mata biyun me suke yi da na su ? Wata dariyar Doctor Suleiman ya sake kwashewa da ita kafin ya ɗora da cewa , " wataƙila jera su suke suna ado da su a gidajen su , ya ɗora da cewa watanni nawa aka sa lokacin bikin ? Banda abunka abokina to menene abun damuwa ? Ai hurhuɗu ya kamata ma mu ajiye , domin ko nima ba domin tafiyar nan da na ɗan yi ba da yanzu batun auren mu yayi nisa da Aminah ta , wataƙila ma sai dai mu haɗa ayi rana ɗaya tunda kuwa ita ma ƴar Maidugurin ce , wata nawa aka sa ? Muryar Doctor Hamza can ƙasa yace , " kwanaki goma kachal suka rage har da yau da muke ciki , Tsumu Doctor Suleiman yayi yana kallon sa wannan karon kamar bai yadda da abunda yace ba , ganin haka yasa Doctor Hamza cigaba da cewa , " tare za'a haɗa da na ƙanwata Rahima , saboda ayi a huta , tarewar kuma sai yadda hali ya min wataƙila ta kai watanni huɗu a maidugurin ko ma fiye da haka kasan dai kome daki-daki ake yin sa . Da fara'a sosai a fuskar sa Doctor Suleiman ya shiga taya shi murna yana taya sa shi da fatan alheri cikin raha ya ɗora da tsokanar sa , " kace ciwon so kake ciki mana tare da kewa , shiyasa duk ka wani zama haka , babu shakka wannan ƙanwar tamu mai sa'a ce , to sabon shiri kenan zamu fara dan angwanci ya same mu da rana tsaka ba tare da mun shirya ba , amma duk da haka ma ɗan yi wasu tsare-tsare a gurguje me da me za'a yi na biki ? Kallo mai kama da harara Doctor Hamza ya masa , kafin yace " Dan Allah zan roƙe ka Alfarma Suleiman, kar ka ƙara min damuwa , duk garin nan bayan kai ba wanda na faɗawa zancen nan , ko ita sofiya bata san da zancen ba dan haka ka ma bar maganar wani biki zancen ya tsaya kawai a tsakanin mu , bayan kai da daman zaka je bikin Rahima babu wanda zan gayyata . Da wani irin yanayi Suleiman ya dube shi kafin yace " ko meyasa ? " kawai ra'ayina ne , mu ba yara bane da za'a yi wani raye-rayen biki ina ma muka ga lokutan ɓatawa ?. Gƴaɗa kai Suleiman yayi cike da shakku yace " to shikenan tunda kace haka Allah ya kyauta . " Amin nagode abokina , Doctor Hamza ya amsa masa , domin ya sauƙaƙa yanayin rashin daɗi da ya hango a tare da Suleiman sai yace , " ina aka kwana kan batun lamarin ita Aminar taka ? ko idan muka je Maidugurin za'a yi wani motsi mai ƙarfi ne ? kasan fa kun jima da yarinyar nan ya ci ace anyi auren nan . Cike da zaƙuwar jin an masa susa inda ke mar ƙaiƙayi Doctor Suleiman yace ," bari kawai abokina wannan yarinyar ko yau aka kawota gidana ta walashe ni , gyara zancen nan ka ma , saboda ai ni na jima ina son ta ba wai mun jima a tare ba , domin kuwa ai ita har yau bata wani bani dama ba , ni kaɗai ke fama , Ya dubi fuskar Doctor hamza da yayi kasaƙe cike da takaicin yadda ya zauna gotai-gotai da shi 'yar yarinya ƙanƙanuwa na masa yawo da hankali wajen shekaru uku , sai kace ƴa gwal ? Doctor Suleiman ya katse zancen da Doctor Hamza yake son ɗorawa ta hanyar cigaba da cewa , " kar ka ga laifina Abokina , Amina ta cancani da kowanne ɗa Namiji yayi sha'awar ajiye mace mai nagartartun halaye da Addini haɗi da nutsuwa irin ta , wallahi ko kai da kan ka idan na baka labarin irin rayuwar da yarinyar take yi mai cike da tsantsanin kiyaye kan ta duk kuwa da cewa inda take rayuwa ƙazamtatce ne , halayyanta na ƙwarai nake kwaɗayi ba kome ba , saboda na sha gwada ta ba sau ɗaya ba , na kuma sa mutane wasu daban ma sun gwada ta amma ko sau ɗaya ban taɓa kamata da wani laifi saɓanin zahirin ta da take bayyane kullum cikin kamala da nutsuwa ba . a yadda kake ƙyamatar halayen wasu matan nasan zaka yi mamakin nagartar da ita take da shi , kuma zaka bada goyan baya ɗari bisa ɗari akan na auro ta , musamman idan ka ji irin hali na tausayawa da suka riski kan su a ciki ita da ƴar uwar ta , Cike da gajiya da yadda ya zauna yana yabon wata wacce har yau shi da kan sa bata bashi darajar da za ta saurare shi ba , bare kuma su abokan sa Doctor Hamza yace " to Allah ya tabbatar da Alheri abokina . Kamar yadda suka yi alƙawari ana saura kwanaki biyar ɗaurin Aure Mutanen N'Djamena suka iso ,sun tasamma mutane ishirin da ɗoriya , domin sun kusan cika falon Prof da anan suka fara ssuƙa , bayan an gaisa murnar sake ganin juna ta kachame a tsakanin su har da 'yan koke-koke , banda yaren su na larabaccin Chad babu abunda ke tashi a wajen , Zainab , Hafsa da suka iso tun jiya , har Rahima haɗi da Yakaka da Falmata , a tsakanin su duk babu wani mai jin yaren har sosai , dan haka sai suka tsaya kallon su fuskokin su ɗauke da murmushi , Bayan sun ɗan nutsu sun sha ruwa da lemu , sai Matan suka shiga ciki inda za'a musu masauƙi , Mazan kuma suka tsaya anan Sashin Prof . A ciki Amnee ta sake gabatar da Yakaka da Falmata , nan aka fara rungumar su ana sumbatar kumatun su da goshi , cike da nuna zallar ƙauna , daga baya kuma aka sake sabuwar gaisuwa har da su Hafsa da mafi yawa sun riga sun san su , su Yakaka ne baƙi . Ba'a kwana ba Hajje Nadiya tare da tawagar ta mata huɗu da ta taho da su domin su taya ta suka buƙaci da su fara aikin da ya kawo su na gyaran Amare . Tun ana saura kwanaki biyu ɗaurin Aure Sofiya ta iso Maiduguri , amma sai ta ƙi ƙarasawa gidan su Doctor Hamza tayi zaman ta a gidan su tare da Mamar ta Hajja kori , da ita ta zuga ta tace tayi zaman ta sai ana gobe ɗaurin auren da Yamma sai su tafi tare , ba dan kome ba kuwa sai dan rashin shirin da yake tsakanin su da Amnee da Khaalty Rahima . Da ko kusa basu so Auren Amnee da yayan su ya sake ƙulluwa ba , kuma duk yadda suka so hana tabbatuwar lamarin fir Prof yaƙi saurarar su , ita kanta zuwan ta wajen sa biyu da zummar yi masa famfo amma bata samun fuska dan haka ta haƙura . Babu abunda yafi ƙara basu haushi irin dawowar Khaalty Rahima da suka fi tsana gidan wannan karon har ma da marayun 'ya'yan ta kamar yadda labari ya iske su Dan haka suka tsara zasu janye jikin su daga sabgar gidan sosai , sai ranar juma'a da Yamma lis , ana tsakiyar yin sakun lallen Amare tukun suka iso , ba su kaɗai bane ƙungiya suka yi da ɗan yawan su domin baki ɗayan ƙannen Prof matan sai yanzu suka zo tare da wasu daga cikin ya'yan su mata , sauran dangi kuwa mafi yawa sai gobe zasu zo . kai tsaye iyayen suka yiwa sashin Prof tsinke ba tare da sun bi ta kan jama'ar sauran Jama'ar Amnee ba mutanen N'Djamena da su Malama Maryam wacce ta iso jiya da Yamma . Suma kuma basu kula su ba , suka cigaba da gudanar da sakun lallen da aka tsara shi cikin irin Al'adun su na mutanen Chad , Kota'ina ƙamshin turaren wuta ne ke tashi da ake zuba shi ta kowacce kusurwa na filin wajen , haka Sofiya tare da wasu daga cikin yaran mata 'yan uwansu suka ratsa taro zuwa ainahin inda amaryar take zaune Abunda ya ɗaure musu kai bai wuce ganin Amaren su biyu ba tare da wacce su sauran basu kai ga sanin ko wacece ba ? ko ita Sofi sai da ta bar yatsine-yatsinen da take yi ta nutsu sosai tukun ta iya shaida Farar balarabiyar da take zaune daga gefen Rahima da aka musu ado iri ɗaya cikin jar lafaya , tundaga kan su har wuya da hannuwa zuwa ƙafafun su adon sarƙoƙi ne masu ruwan gwal irin wanda shuwa arab ke adon bikin su da shi , ( baki ɗayan kayan gudummawa ne daga Hajje Khalsum ) Muƙut ,! Sofiya ta haɗiye busasshen yawun da ya mata saura a baki , kafin ta ɗora da ɗan siririn tsakin da ya bayyana fili . Da ɗan sauri ta matsa kusa da Hafsa zuciyar ta na ƙara ƙarfin bugun da bata san dalili ba , " kamar nasan wannan kuma Bikin biyu ne wai ? Ta ce tana nuno Yakaka a walaƙance , Murmushin yaƙe Hafsa tayi sannan tace " ƙanwar mu ce 'yar Auntien mu Rahima , Da sauri ta sake cewa , " Ok daman wannan yarinyar ita ce ƙanwar taku da aka ce an tsinto su ? Kuma bikin ta itan ma ake yi na gan ta anan kusa da Amarya ko duk shisshigi ne da cusa kai ya bawan gado ? Wata daga cikin ƴar dangin su da ta zo ta jaa hannun Hafsa ɗin tana bata saƙon Amnee na ƙiran ta , ita ta hutatce Hafsa daga bada Amsar da take ƙoƙarin harhaɗowa cike da zullumi . Zare hannuwanta tayi daga cikin na Sofiya ta bar ta nan a tsaye , Ji tayi sam ba zata iya tsayuwa a wajen ba tana kallon Yakaka wacce sai ƙirƙiro ƴar fara'a take a tsakanin ƙawayen Rahima da suka zama kamar nata sai zuwa suke ana yin hoto , tare da yi mata fatan Alheri Bata sake bi ta kan kowa ba ta zare jiki ta nufi sashin Amnee inda ta tarar ba yawaitar mutane a falon , mutane basu wuce huɗu ba ƙawayen Amnee , kai tsaye ta nufi ɗakin Amnee da take jiyo muryoyin su daga ciki , Amnee da Khaalty Rahima haɗi da Hajje Khalsum duk shiru suka yi daga tattaunawar da suke suka bita da kallon ganin yadda ta shigo musu ɗaki bagatatan babu neman izni . samun waje tayi ta zauna kafin ta fara gaishe da Amnee , da ƴar fara'a Amnee ta amsa , daga haka shiru tayi tana latse-latsen waya bata da niyyar gaishe da sauran mutanen , dan haka fuskar Amnee ta ɗan sauya daga fara'ar da take tace , " Safiyya baki ga 'yan uwa na bane ? Wannan ƙanwata ce wannan kuma matar wana maza ki gaishe su . Yanayin ta na bayyana rashin jin daɗin yadda Amnee ta disga ta a gaban mutane kamar wacce aka toshewa baki tace " Sannun ku ina wuni ? Fuskar Khaalty Rahima ɗauke da murmushi sosai ta amsa mata har tana ƙarawa da tambayar ta Mamar ta ? Bata bata amsa ba ta mayar da kan ta ga fuskar wayar ta , Sun cigaba da tattauna yadda wasu al'amuran da suka shafi bikin zasu kasance , kafin su tsinkayo muryar Hajja kori da take ƙwalawa Amnee ƙira tundaga ƙofar falo , A kusan tare suka miƙe da sofi wacce ita ma tashin hankalin da ta ji a muryar Mamar ta ya firgita ta , Suka fito falon a tare kichiɓus suka yi da tawagar su Hajja kori tare da sauran ƴan uwan su na kurkusa da suka zo tare , Kamar zata cukumo Amnee haka ta tsaya a gaban ta tana huci , sannan tace " Amina baza ki taɓa sauyawa daga mummunar zuciyar ki mai cike da baƙin-hali ba ke da wannan Annamimiyar ƙanwar taki , da daga dawowar ku ke da ita shine kuka haɗa kai kuka maƙalawa ɗan mu auren Shegiyar ƴar da .... A tsawace Amnee ta katse ta bayan ta matsa baya kaɗan tace , "Hajja kori ki dakata , ya isa kar ki sake ki ce za ki tozartani ko ki tozartamin 'yar uwa ta , wanda kuka yi a da can ma ya isa wannan masifar taku da bala'in a yanzu bazan ɗauke shi ba domin kuwa kunne ya sake ƙaho ya girma . aure kuma tsakanin Yakaka da Hamza babu wanda ya isa ya hana ƙulluwar sa muddin ni na tsugunna na haifi Ɗana nayi ɗawainiyar sa sai ya auri Amina Yakaka , idan kuma a wannan karon ma za ku hana ne to Bismillah sai mu gani . Ƙara matsowa Hajja kori tayi jikinta har tsuma yake tace " tsohuwar kilaki haka kika ce ? Babu shakka dole kice ƙaho ya girma saboda kin gama yawon banzan ki a bariki kin dawo za ki laƙawa.... " Momy kori ki saurara haka nan Dan Allah duk abunda za kiyi kada ki aibata min uwa da mummunan ƙazafi , Muryar Doctor Hamza a kausashe ta ratso falon wanda sauƙar sa kenan a garin ya nufo gida yana faka motar sa bai ko gama tsayawa ba Hafsa ta ƙira shi hankalin ta a tashe tana shaida masa rigimar da ƴan uwan Baa suka zo su nayi musu . Cikin takun sa na nutsuwa ya ƙaraso wajen , yana zuwa ya shiga tsakanin su yana fuskantar Amnee , hannuwan sa duk biyu yasa

Chapter 80 of 103