zaune zahiri a gaban ta .
Yau ne Alƙawarin su da likita dan haka bayan sun kammala karin-kumallo , suka shirya cikin jibga-jibgan rigunan sanyin su rufaffu tundaga wuya, crew neck sweatshirt.
Biyamuradi ya maƙalo hannuwan Falmata tare da ɗaukar Mama bisa kafaɗar sa ,
Ƴar tafiyar da bata cika yawa ba , mai cike da nishaɗi saboda 'yar hirar da ta gifta tsakanin su da ta ƙara musu shauƙin jin daɗin kasancewa da juna ,
Suka iso asibitin , babu ɓata lokaci suka haɗu da likita , bayan tambayoyin da yayi mata game da sabon cigaban da take samu kan lafiyar ta ,
Cikin amsoshin da ta bashi da bincike-binciken da ya sake yi , ƙarshe ya shaida musu da cewa dole a kai ga matakin ƙarshe na yin aiki ga idon .
Ba tare da ja ba Biyamuradi Youssouf ya amince , cikin lokaci kaɗan aka shigar da bayanai tare da ɗaura ta akan wasu magunguna daban da zata sha na tsawon sati biyu da za'a mata aikin idon .
Sun baro asibitin zuwa gida , akan hanya Biyamuradi Youssouf ya cigaba da ƙarfafawa Falmata tare da kwaɗaitar da ita samun lafiyar idon ko da kuwa ace bata warke baki ɗaya ba .
Maƙotan su suka tadda daga ƙofar su suna ƙoƙarin kulle na su gidan ,
Cikin mutunci Biyamuradi Youssouf ya matsa kusa suka yi musabaha da Maigidan duba da irin mutuncin da suka yi masa a jiya na riƙe masa Mama ,
Balaraben da matar sa suka sake jajanta masa kan ɓacewar Falmata a jiya ,
Cikin jin daɗi ya sake matso da Falmata jikin sa , yana shaida musu cewa ita ce wannan ,
Nan ya gabatar musu da kan sa , Matar sa da 'yar sa , ƙasar da ya fito da dalilin zuwan sa nan .
Inda shi ma Balaraben ya gabatar masa da kan sa , sunan sa Musa Adnan , matar sa kuma Ramlat , sai Yaran su mata biyu Hind da Zahira , Aiki ne ya kawo su nan , musulmai ne 'yan asalin ƙasar Kuwait .
Da murna tare da ƙauna irin ta musulunci Ramlat ta matsa ga Falmata ta kama hannun ta tare da juya harshe cikin faransanci ta gaishe ta tana tambayar ƙarin lafiyar jikin ta ? ,
Da jin daɗi Falmata ta amsa mata ,tana riƙe hannun Ramlat da ke cikin nata ,
Babu ɓata lokaci Musa Adnan yayi musu tayin ko zasu bi su strong museum? Inda zasu tafi da 'ya'yan su domin shaƙatawa ?
Ɗan Jim Youssouf yayi , cikin son yin nazari ,shi fa bai cika son tsawaita mu'amala da mutanen da bai wani san su sosai ba
sai dai Musa ya katse masa hanzari ta hanyar bugun kafaɗar sa kaɗan , ya juya masa harshe cikin faransanci ,
"Allez, c'est l'un des meilleurs endroits pour emmener des enfants et des familles dans la région de Rochester am sure you'll enjoy the place. ( ka zo mu tafi , yana daga cikin jerin wurare mafiya kyau domin iyali da yara a garin Rochester na tabbatar zaka ji daɗin wajen )
Falmata wacce daman zaman waje ɗaya tsawon satika ya fara gundurar ta , ta ɗan kwanto da kan ta bisa kafaɗar sa ,
"BaBan Mama s'il vous plaît nous devons y aller, ( mu tafi mana ? )
ta furta hakan tana yin ciki da muryar ta ,,
Ganin sa ya kai kan zagayayyar fuskarta da take ƙyallin da ke bayyana shaidar yanayin wajen ya amshi fatar ta ,
Ya mayar da ganin sa ga Musa dake jiran amincewar sa ,
"Okay let's go.
Cikin motar da Musa ke jaa da kansa suka kama hanya , akan hanya hira ta sarƙe a tsakanin su , inda Musa yake sanar da Youssouf aikin sa na cruise-ship worker da yake yi ƙarƙashin company jiragen ruwa na ƙasar amurka , ya cigaba da sanar da shi irin tarin ƙasashe da garuruwa gami da tsibiran da ya ziyarta wanda aikin sa ne ya bashi damar haka .
Falmata da Ramlat ma suna ƴar hirar da bata cika tsawo ba saboda rashin nunan yaren faransancin a bakunan su duk biyun , yayin da ita kuma Falmata bata jin Turanci bata jin larabci yaruka biyu da Ramlat ta fi iyawa .
Basu yi tafiya mai nisa ba suka iso bakin katafaren Museum ɗin , Musa shi ya yanka musu tikitin shiga ciki .
Da sanya kafar su wajen ya ɗau hankalin Youssouf da yau ya taɓa zuwa , ƙwarai tsarin gine-ginen wajen suke da ban sha'awa ,
Mama kuwa tsalle ta fara yi ganin manya-manyan liluna da kayan wasanni irin na yara masu ɗaukar hankalin yaro har ma da babba .
Da gudu ta saki hannun Falmata ta bi bayan su Hind da suka riga suka yi gaban kan su zuwa wajen kayan wasanni ,
Falmata tana ƙoƙarin riƙo ta , ta zille mata , hankalinta tashe ta shiga ƙiran sunan ta bata so ta gusa daga kusa da ita kar ta ɓata ,
Youssouf ya kamo hannuwanta , yana fuskantar ta , yace mata
'ki rabu da itta Fatima , kayan wassan yara ne dayawa a wajen su ta gani ta tafi wurin tare suke da sauran yara,
"kar ta ɓata ko kuma ta ji ciwo Baban Mama da dai...
"shitt
yace yana ɗora mata yatsa akan bakin ta ,
"baza ta ɓata ba , zo mu tafii inda take ,
Yana riƙe da hannun ta suka nufi ciki , inda da ƙyar suka lalubo yaran da suka nutse cikin kayan wasanni ,
Mama sai ihu take me yasa aka zaƙulo ta daga cikin shirgin da ta shige ?
Musa shi yayi musu jagora zuwa shashi daban-daban na kayan tarihin wasannin yara tun na tala-taini , tare da tsoffin cartoons,
Suna tafe har suka ɓullo gaban gidan sasemet street ,
Ɗan murmushi Youssouf yayi yana ɗage girar sa , kafin su haɗa baki shi da Mama wajen cewa,
"Sasemet street ?
Dariya Musa da Ramlat suke yi ganin yadda Mama take tsallen Murna , tare da ihun ƙiran sunan toys ɗin da take gani na sasemate street a waya ko Laptop ɗin baban ta da koyaushe shine cartoon ɗin kallon ta , Wanda shima kuma favorite children's show ɗin sa ne tun yana yaro hakan ya sa ya koyawa Mama ma kallon sasemate street.
"Elmo , Grover, Abby, cadabby , cookie-monster, Big bird ..
Ta ƙarasa jera ƙiran sunayen su tana rufe bakin ta da hannuwan ta biyu , da gudu ta taka zuwa wajen ƴar ƙofar gidan Elmo ,
Tana matsa ƙararrawar ding dong ditch , ga zaton ta Elmo zai leƙo ya buɗe mata ƙofa ,
Kara ƙunne tayi a jikin ƙofa cikin 'yar muryar ta take ƙiran " Elmo , Elmo ouvre la porte ( Elmo open the door )
Dariyar da wajen ya ɗauka tare da hasken camerorin da suke ɗaukar ta hoto shi ya ankarar da Youssouf yawan mutanen da suka tsaya kallon shirmen da Mama ke yi cikin Burgewa ,
Dariya yayi ya taka wajen ta yana ƙiran sunan ta ,
Ɗaukar ta yayi ,
"Mama Elmo il dort maintenant ne le dérange pas okay ?) , elmo yana bacci kar ki tayar da shi kin ji ko ?
Gyaɗa kai tayi tana waiwayen ƙofar , daga step ɗin suka tsaya Musa ya ɗauke su hoto a camerar sa , Youssouf ya kamo Falmata suka tsaya a wajen Musa ya sake yi musu wasu hotuna ,
Haka suka cigaba da yawatawa a strong museum , tsawon lokaci kafin su yada zango a wajen wasan pinball , nan wasan ya koma na manya tsakanin Youssouf da Musa , an tuno ƙuruciya , cike da nishaɗi da dariya suka dunga buga wasan pinball , kafin daga bisani su koma kan wasan retro arcada .
Sosai suka nishanɗantu , basu yi aune ba har lokaci yayi ta tafiya, wajen cin abinci suka yada zango,
Kowa ya nemi a kawo masa abunda zai ci , sanin da Youssouf yayi har yau ba kome Falmata da Mama suke iya ci ba dan haka yayi musu order na abunda zasu iya ci .
Daga can wani babban fili da yake a tsaftace suka samu waje gefe , Musa ya jagorance su suka yi sallah .
Hira suka cigaba da yi nan zaune bisa kan dakalin da aka yi su da kayan wasan yara yayin da yaran suka tashi suna cigaba da wasannin su da hawa kan liluna ,
Cikin hirar su Musa ke basu labarin wani tsibiri daya da ya taɓa zuwa a yankin Africa , cikin ƙasar Tanzania , mai suna BAWE a yankin ZANZIBAR,
"Bawe zanzibar yana ɗaya daga cikin tsibirai masu kyaun yanayi da namun ruwa masu ban sha'awa tare da tsirrai masu kyaun gani da taɓa zuciya da na taɓa gani ,
Cewar Musa ,
ya cigaba da cewa ya yawata a ƙasar Tanzania sosai , ya ga manyan namu dawa a cikin dazuzzukan su , wanda duk duniya a yankin ƙasashen Africa kaɗai ake samun irin su ,
Ya ɗora da yi masu bayani kan tsibirin Bawe da ya ƙira da dausayin duniya ,
Har wasu daga cikin hotunan wajen ya nunawa Youssouf daga camerar sa,
Karɓa youssouf yayi yana kallon wuraren da suka yi matuƙar tafiya da hankalinsa , ashe muna da irin waɗannan dausayin masu ban sha'awa a yankin Africa ?
Miƙa masa camerar sa yayi bayan ya gama ganin hotunan ,
ya ɗora ganin sa ga Falmata wacce ba ganin hotunan ta yi ba illa labaran da ta tsinci wasu abubuwan da Musa yake faɗa ,
Amma fuskar ta yalwace take da Kyakkyawan murmushin da ya ƙara mata kyau da haiba ,
"hannun ta ya riƙe yana murza yatsun ta ,
Yace,
" Fatima watarana zamu raya daren mu a Bawe Zanzibar island , kina so ?
Murmushi mai bayyana haƙora tayi , a hankali ta gyaɗa kai
" ina so Baban Mama ,
Shafar kumatun ta yayi ,yana jin yadda ƙaunar ta ke sake mamayar sa , cikin tunanin sa yana hasko yadda zasu yi rayuwa a tsibirin Bawe gefen taku .
Bayan sati biyu
Cikin sati biyun da suka biyo baya Falmata ta cigaba da shan magungunan da aka ɗora ta akai cikin bin ka'idar shan maganin ,
Gefe guda sassanyar ƙauna na gudana sannu kan hankali a tsakanin su mai cike da girmamawa daga ɓangaren Falmata , tausayi da zallar nuna kulawa kuma daga Youssouf ,
Duk wani rashin sakewa da ɗari-ɗarin da take da shi ta rage , ta fara sakewa da shi , har ma tana iya bashi wasu daga cikin labaran da suka shafe ta , iyayen ta, 'yan uwanta da garin su ,
Jin ainahin haƙiƙanin labarin su ya ƙarawa Youssouf zallar tausayin ta , tare da tasowar mikin binnennan laifin sa ga Yakaka ,
Ya haƙiƙancewa kan sa a yanzu Falmata bata da wanda ya fi shi , dan haka ya ɗau alƙawarin kome runtsi zai bata kariya cikin kowanne hali iyakar ƙarfin sa , shi zai zama inuwar hutawar ta bayan gwagwarmayar Rayuwar da suka shiga .
Yau tun da suka tashi sallar asuba basu koma ba , zama suka yi yin addu'a sosai game da aikin da za'a yiwa Falmatan a yau da misalin ƙarfe tara na safe , suna fatan Allah ya sa ayi aikin a sa'a .
Sai da gari yayi haske misalin bakwai , Mama ta farka ta fara neman abin karyawa ,
Kamar koyaushe Youssouf shi ya yi musu abun kari da shi da Falmatan sama-sama suka ci saboda rashin nutsuwa tare da Fargaban da suke ciki .
Takwas da rabi na safe ya yi musu a ofishin likita ,
Bayan gaisuwar da suka yi , likitan ya ƙara musu da kalmomin karfafawa ganin kamar suna tare da damuwa ,
A ƙarshe ya yi musu umarnin da su taso ya musu jagora zuwa ɗakin yin aikin inda sauran likitoci suke jiran su ,
Har bakin ƙofar dakin yin aikin da take iyakar sa ya raka ta ,
"kiyi ta addu'a Fatima , nima zan yi ta yi kin ji kou ? Ki roki Allah ya sa ayi aiki bissa sa'a , ki samu lafiya ,
Kai ta gyaɗa ,
Ba tare da ta furta kalma ba ,
Fuskar ta ya riƙo cikin tafukan sa ya Sumbaci goshinta ,
" ki shiga Fatima da Ambaton Allah , Allah shi baki lafiya ,
"Amin
Ta amsa idanun ta na kawo ruwa , haka kawai take jin fargaba gani take tamkar zata iya rasa ran ta a garin neman lafiyar ido ,
Ɗaya daga cikin nurses ɗin da suke cikin ɗakin ta taho ta kama hannun Falmata zuwa ciki ,
Labulen da yake tsakanin su aka yaye , ya zama Youssouf yana iya hango Falmata ta tsakanin gilashin da yayi ƙawayan ga ɗakin da take ciki ,
A shirye ya hangota tsaf, da taimakon nurses ta kwanta akan gadon da yake tsakiyar wasu fitilu masu matsanancin haske ,
Ba ɓata lokaci Manyan likitocin suka matso gaban gadon suka yi ƙawayan yayin da wasu suka shiga jona mata wasu na'urori a kai , wasun su na shirya kayan aiki ,
Aikin da ya ɗauke su tsawon awa guda da mintoci arba'in , da Youssouf ya ji lokacin tamkar tsawon shekara ,
Ɗaki na musamman aka mayar da Falmata bayan an gama yi mata aikin inda zata zauna tsawon awanni arba'in da huɗu kafin a kai ga mataki na gaba ,
Nan suka nemi Youssouf da ya tafi gida zata kasance cikin ƙarƙarshin kulawar su ,
Ya so yayi gardama saboda hankalin sa da yake tashe da son sanin halin da Falmatan ke ciki ,
Sai da Likitan ta ya yi masa bayani mai gamsarwa tare da kwantar masa da hankali ,
Ya sanar da shi allurar da aka mata zata sake ta nan da wasu mintoci , sai dai sun fi son kasancewar ta ita kaɗai , a wannan ɗakin da take zasu cigaba da bata duk wata kulawar da ta dace ,
Hankalin sa bai kwanta ba sai da ya yi masa jagora zuwa bakin ɗakin inda ya hango Falmata a kwance kan gado , an naɗe mata idanun nata da farin ƙyalle , da alama bacci take ,
Sanin da ya yi Mama bata cika lafiya ba ya sa dole ya bar asibitin tare da ita ya nufi gida da zummar dawowa zuwa anjima domin ba zai iya yin har tsawon wasu awanni masu yawa ba tare da ya gan ta ba , ya san halin da take ciki ba ,
Ko da suka dawo gida daga shi har Mama gidan bai musu daɗi ba ,
Mama kaɗai ya soyawa ƙwai tare da kifin gwangwani , ita ma bata wani ci na kirki ba ta ɗauke kai , Alamun ta ƙoshi ,
"Mama ki ci abinci sossai mana ,
Girgiza kai tayi tana ƙwalan-ƙwalan da ido ,
"Papa mu tafi wajen Mama yanzu ,
"zamu tafi idan kin ida cin abincin ki kin ji kou ?
Shiru tayi tana kallon sa ba tare da ta buɗe baki ta karɓi abincin da yake miƙa mata ba ,
Gajiya yayi da riƙe chokalin , ya ajiye gami da miƙewa yana jin yadda zuciyar sa ke cike da kewar ta , baki ɗayan hankalin sa na kan ta ,
Ya daɗe a zaune yana mata addu'a akan sallayar da ya idar da Sallar Azahar ,
Shafa kan Mama yayi wacce tayi bacci a gefen shinfiɗar sallar sa ,
Cikin ran sa yana aiyana irin yawan kewar Mamar ta da tayi wanda ya duƙusar da walwalarta
Ɗaukar ta yayi ya kaita ɗaki ya kwantar tare da rufe ta da bargo , ya zauna daga bakin gadon ,
Wayar sa ya ɗauka ya latsa ƙiran layin Tafeeda da ya yi ƙiran sa a ɗazu lokacin da ake yiwa Falmata aiki , bai samu damar ɗaukar kiran nasa ba
Bayan sun gaisa , tare da Tambayar lafiyar juna Youssouf ya ɗora da tambayar sa Leila matar sa da ɗan su Imran , ?
" duk lafiya suke ɗan'ouwa , Yarima kana ji na kou ?
"ina jin ka da kyau ɗan'ouwa ,
" Yarima kou kana da labarin mutanen da ka baro shekarun baya a Nigeria ?
Da ace Tafeeda na gaban shi a lokacin da zai iya hango firgicin dake zane ɓaro-ɓaro bisa fuskar sa ,
"waɗanne mutane Tafeeda ke magana kan su ?
Tambayar da zuciyar sa ke yi ya bayyana kan harshen sa ,
Jim! Tafeeda ya yi yana nazartar firgicin da yake iya jiyowa daga Muryar Youssouf ɗin ,
"wannan ɗiya da tsautsayi yassa ta samu a duniya , nace kou ka sake waiwayar ta ? Tafiya ta kama ni zouwa Nigeria shine nake biɗar izni kan na tai na gan ta ko da ba kai tsaye ba ne na....
Cikin sauri Youssouf ya katse sa muryar sa a ɗan sama kaɗan ,
"Tafeeda ban ma izni ba , batun wannan ɗiya ai mun jima da ajje shi ghefe kou , ka kyale kawai wani lokaci idan Allah ya ida nufi ni naje da kaina na duba ta ,
Ajiyar zuci Tafeeda yayi ,
"tou babu kome 'dan ouwa Allah shi gwada mouna lokacin da lafiya , Allah kouma shi ƙara rufa asiri ,
'Amin Amin 'dan ouwa ,
Shiru ya gifta tsakani sakamakon tunani mai zurfi da kowannen su ya faɗa ,
Babu shakka Tafeeda yana da wani dalili da ya sanya shi bijiro masa da zance Mama a dai-dai wannan lokacin da tsawon shekaru wajen shidda bai taɓa tambayar sa game da lamarin ta ba sai fa yau .
a daddafe ya iya kaiwa bayan la'asar a gida , ya sake shirya Mama da ita ma duk ta damu da son su koma wajen Falmata ,
Ko da ya isa asibitin har lau bai samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ba .
Haƙuri likitar da take da Alhakin kula da ita ta bashi , akan ba zai yiwu ya shiga inda take a yau ba sai ko zuwa gobe da yammaci
Haka suka ƙaraci zama daga gefen ɗakin da take ciki har duhu ya fara shiga, dan dolen sa ya miƙe da Mama ya ƙarasa jikin ƙofar ɗakin da take ,
Ya yi mata addu'a , kafin su bar asibitin zuwa gida ,
Daren ranar bai zo masa da sauƙi ba , baki ɗaya sai juye-juye yake yi ya gaza yin baccin kirki , bai san da haka ƙaunar ta ta rarake masa zuciya ba sai da ya gaza bacci saboda damuwa da son sanin halin da take ci gami da kewar ta mai tarin yawa ,
Abunda bai taɓa jin kwatankwacin sa kan kowacce ɗiya mace ba , ko da kuwa Maimounatu ,
Salon ƙaunar da yake yiwa Fatima daban ne da yake tafe da wani irin yanayi mai tasiri sossai a gare shi ,
Sai gefen asuba bacci ya ɗauke shi cike da mafarkai iri-iri , da har ya sanya shi makara wajen yin sallar asubahi .
Tara na safe suka samu isa asibitin , inda kuma cikin sa'a ya samu damar shiga ɗakin da Falmatan take ƙarƙashin jagorancin likitan ta ,
Da takun ƙafar su ta san da shigowar su ɗakin da take da ita ma ta kwana cikin kewar su duk kuwa da zogi da idon ke yi mata lokaci zuwa lokaci , amma ta fi damuwa da ta san a wanne hali Mama da Baban ta suke ?
"Mama , Maama
Suka haɗa baki wajen ƙiran sunan junan su ita da Mama wacce da shigowar ta ɗakin ta hango Falmata , ta tafi da gudun ta ,
Ɗago ta Falmata tayi ta rungume ta a jikin ta , tana jin yadda sanyin ƙaunar ta ke ratsa zuciyar ta , babu shakka ƙaunar Mama magani ce ga ta ta zuciyar ,
Da murmushin samun nutsuwa ya ƙaraso bakin gadon ,
"Fatima yaya jikin naki ? Babu inda ke miki ciwo kou ? Baki cikin damuwa kouma ?
Waigawa tayi sashin da take jin tashin muryar sa ,
"Baban Mama ina kwana ? Yaya Mama ta kwana ? Bata yi ciwo ba ko ?
Ɗan tsayirtawa tayi , kafin ta ɗora da cewa
"bana jin damuwa ko ciwo mai tsanani , amma ina son a warware min idon nawa wannan abunda suka rufe min ido da shi yana damuna ,
"likitan da duk yana jin abunda take faɗi tare da taimakon na'urar kunnen sa ,
Ya matsa yana sake rarrashin ta tare da yiwa Youssouf bayani kan cewa kafin su warware mata idon zuwa gobe anfi buƙatar idon ya zauna a rufe haka , har sai bayan awanni arba'in ,
A cikin ɗakin suka wuni tare , sau biyu Gimbiya maimounatu na ƙiran wayar sa , ya gaza ɗaukar ƙiran .
Bai san dalili ba amma can cikin ran sa ya gujewa yin hira da maimounatu ne saboda gudun ɓacin ran Falmata .
Washegari kamar yadda suka sharɗanta , awanni arba'in da huɗu da 'yan mintoci ,
Misalin ƙarfe goma na safe likitocin suka yi da'ira , a kan ta ,
Babba daga cikin su wanda kuma shine ainahin wanda ya yi mata aikin , shi ya warware mata idon ,
Bayan sassauta haske tare da sauya launin hasken zuwa marar kaifi , cike da fatan nasara likitan ya umarci Falmata da ta buɗe idanun ta ,
Babu karsashi ta fara wara idanun da suka mata wani irin nawi , hasken da ta ji kamar ya chaki idon shi yasa ta saurin runtse idanun ta kai tafukan ta biyu ta rufe fuskar ta ,
Cikin sauri likitar da ke gefen ta ta sauke hannunwan nata ,
Rarrashi da kalaman ƙarfafawa suka shiga yi mata cikin kwantar da murya , suna umartar ta da ta buɗe idon ta zata ga duniya ,
Sannu kan hankali ta ware idanun da suke rawa kaɗan-kaɗan , baƙon yanayi ne ya ziyarci ƙwaƙwalwa zuwa gangar jikin ta lokacin da raunanan jijiyoyin idanun ta suka fara ɗaukar jirkitattun hotuna suna aikawa da shi zuwa cikin ƙwaƙwalwarta da sauri ,
Wajen ya ɗauki shiru , likitocin suna ƙure ganin su akan ta da take gwale idon cike da burin son samun ƙarin ƙarfin ganin da tare kuma da son fahimtar abubuwan da take iya ganin hotunan su duru-duru , shin wannan shine hasken duniyar ? Haka kuma suffofin mutanen yake a zahiri ?
A sama ta tsinto muryoyin su lokacin da suka cigaba da yi mata magana , dusu-dusu take iya ganin kusantowar motsin wani abu kafin ta tsinkayi muryar likitan yana tambayar ta ko tana iya ganin alamun motsin sa ??
Bata amsa ba illa kan ta da ta gyaɗa ,
Hannu ya kai yana ɗaukar wani baƙin tabarau mai haɗe da 'yar na'ura na musamman wanda cikin awanni arba'in aka yi shi domin Falmata ,
Ya sanya mata a fuska tare da daidaita mata shi , ya miƙe tsaye da murmushi a fuskar sa cike da burin nasara , ya tambaye ta ko tana iya ganin sa ?
Zuba masa ido tayi tana iya ganin shatin sa fiye da ɗazu , suffar sa ta mutum ta bayyana duk da ba tarwai take iya gani sa ba ,
a hankali ta juya ƙwayar idanun ta zuwa kan kome da yake sararin wajen daki-daki take ƙure musu kallo , duk da ba sosai take ganin abubuwa ba ba kuma fahimtar su take yi ba ,
A hankali likitocin suka dare , tare da bada hanya ga Youssouf da Mama da babban likitan ya yi umarnin su shigo ,
Hannun sa yana riƙe da Mama suka shigo ,
Kamar koyaushe takun Mama ya fara isa ga dodon kunnen ta ,
Dan haka take ware ido cike da buri , burin da ada ta ɗauka ta haƙura da shi ,
'yar ƙaramar halittar da ke kusantota ta ɗorawa ido ,
Ko ba'a faɗa mata ba , ko da cewa bata taɓa ganin wata halitta da idanun ta ba , ta san wannan ita ce Mama ,
" Mama ,
Mama ta ƙira sunan ta dai-dai da ƙarasowar ta gaban ta ,
Hannuwanta biyu ta sanya ta ɗago Mama , da wani irin yanayi ta matso da fuskar Mama daf da tata bayan ta ɗaura ta a cinyar ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 62 Chapter of 103