?
Sai dai ta haƙura ta binne ɓacin ran ta har zuwa ranar da zata gwadawa Hajja cewa lalle ita da Falmata sune ɗaya .
Kamar yadda suka shirya ana gobe ranar tafiyar su Direban da zai kai su ya iso da ƙarfe takwas na safe , saboda kwana da ya yi a garin damaturu
Aka sauƙe sa tare da ba shi wajen kwana , a kuma ranar ne da hantsi misalin sha ɗaya na rana Zainab da Hafsa da 'ya'yan su har ma da Sofi suka iso dukkanin su daga garin Abuja ,
Nan take gidan ya daina yiwa Yakaka haske , ta shiga hidima da su da 'ya'yan su , ba ji ba gani .
Ga daga Zainab ɗin har Hafsan basa wani sakar mata fuska , bare kuma Sofi wacce ko giftawa tayi ta gabanta sai ta bita da zagi da harara , duk ta bi ta takura ta gaza walwala ,
Rahima ma da take jin daɗin ta yau ta ga 'yan uwanta ta ƙule a cikin su , suna hirar su ta 'yan uwa ,
Cikin hirar da suke yi ne ta tsinci suna maganar isowar Amnee da khaalty Rahima da Doctor Hamza a gobe wanda shine ma maƙasuɗin zuwan su .
Har ta juya zata fita a falon bayan ta durƙusa har ƙasa ta miƙawa Hafsa Feeding bottle ɗin jaririyar ta da ta wanke da ruwan zafi , ta tsinci Muryar Zainab tana ƙiran ta ,
"Ke , un wa ma kike da suna ? Ki zo zamu hau sama ki taya mu gyara , wallahi Hafsa dan dai kun ƙi ne amma ai da mun taho da munnira da indo masu aikina , da wannan uban aikin da zamu yi , ba gara mun biya musu kuɗin jirgin ba mun zo da su sun yi aikin , aikin fa ba na wasa bane duk ɗakunan saman nan uku da Falo sai mun wanke su mun gyara ,
Sofi ta katse ta ,
"To ba ga wannan balamar ba , meye amfanin ta da ba za tayi aikin ba ?
Rahima ta katse ta tana ɓata rai
" a gaskiya Antie Safiyya Aikin nan ya yiwa Yakaka yawa kin kuwa ga yawan ƙurar da take sama ? Ɗayan ɗakin nan na gefe ni tun da nake ban taɓa ganin an buɗe shi ba ,
"mts kome yawan sa daga nan zuwa gobe ai zata gama ke baki san ƙauyawa horan aiki bane ?
"gobe zata yi tafiya ki...
"Auntie Zainab zan iya a nuna min wajen ,
Yakaka ta katse jayayyar da take neman ƙulluwa tsakanin Rahima da Sofi ,
" Rahima ki nuna mata ta fara aikin kafin mu zo ,
Ta ƙafar benen dake cikin Falon suka hau sama , Yakaka sau ɗaya ta taɓa hawa saman tun lokacin bikin Zainab sai fa yau ,
Bakin ta ɗauke da Bismillah ta ɗora da Sallama ta shiga Falon da yake ba kome sai tarin ƙura buɗu-buɗu da gidan gizo-gizo , hatta shimfiɗar carpet ɗin an naɗe su ,
"Yakaka ki ga fa aikin da Auntie Safiyya ke cewa zaki iya yi ke ɗaya ? Ita dai muguwa ce wallahi .
Rahima ta furta Hakan cike da jin haushi ,
Murmushi Yakaka tayi , lokacin da take sanya ƙasan hijabin ta ta ɗaure daga kan hancinta zuwa bakin ta ,
"zan yi iyakar Ƙarfina Rahima ,
Ta furta hakan lokacin da take sunkuyawa ta ɗau sabon abun cire yanar gizo-gizo da ta gani a jiye a ƙasa daga dukkan Alamu an tanade shi ne dan yin aikin ,
Da addu'o'i a bakin ta ta shiga aikin cire yanar gizo ,
**
Ba su suka gama aikin da mafi yawa Yakaka ce ƙarfin sa ba , sai kusan tara na dare ,
Iyakar gajiya Yakaka ta yi sa , duk jikinta ciwo yake musamman bayan ta saboda sunkuyon shara , ga ƙurar da ta shige mata hanci ta sa mata mura sai attishawa take yi .
Washegari dakyar ta iya tashi tayi Sallar asuba ita da Hajja suka hau shiri ,
Banda mita babu abunda Hajja take yi
"Ace wai Yaran mata da ku sai dai ku yi kwance shaɓe-shaɓe kuna jiran a girka a kawo muku ? Wallashi yau babu wacce zan yiwa hidimar girki , girkin Alhaji kawai zan yi , tafiya ce mai nisa a gabana ,
" Akwai sauran tuwon jiya shi zan ɗumama mana ni da ke da direba , shige mu tafi kitchen ɗin
' kafin su gama baccin su ta shi mu mun yi nisa , kiyi abu da jikin ki Niger ba nan kusa ba gara mu kama hanya tun da duku-duku ,
Da sauri Yakaka ta ƙarasa sanya Hijabin ta , ta bi bayan Hajja zuwa kitchen ,
***
Ƙarfe takwas na safiyar Ranar Talata , Yakaka da Hajja tare da direban da zai kai su suka kama hanya , bayan sun yi Sallama da Prof ya musu fatan Alkhairi tare da basu Dubu biyar -biyar su ƙara a guzuri .
Duk da cewa Yakaka ta yi tafiya mai ɗan nisa tsakanin Abuja da Maiduguri , amma ta riski nisan tafiyar tsakanin jahar Borno Nigeria da Niamey Niger da tazarar da ta shallake tunanin ta , tun tana zaton an kusa lokacin da ta ga Yamma tayi rana ta faɗi ,
Har ma ta tambayi Hajja ko sun iso ?
Hajja ta shaida mata ai yanzu ne ma zasu tsallaka boda zuwa ƙasar Niger , sai ta maida kanta ta kwantar a jikin kujera tana me cigaba da kallon rairayin saharar da ya tafi iya ganin ta da tsilla-tsillan bishiyoyi ,
Cikin ran ta tana sake jin haushin Youssouf da ya shata tazara mai tarin yawa haka tsakanin ta da ƙanwar ta ,
Ba su suka isa Niamey ba sai sulusin dare , ƙarfe biyu saura , kai tsaye direban ya dau hanyar gidan Youssouf da su ,
Suka yi amfani da 'yan mukullin hannun shi direban suka shiga cikin gidan
A babban Falon gidan da yake sashin Falmata suka yada zango ,kasantuwar akwai gajiya Mai tarin yawa tare da su musamman Yakaka da har wani tsuku take ji jikinta na yi mata saboda gajiya, ga idanun ta da suke cike da bacci ,
Nan falon suka yi rashe-rashe ita da Hajja Bayan sun sallami direban ya yi tafiyar sa a daren , suka kulle gidan ,
Direban da ya kawo su yana juya kan motar kafin ya ɗau hanya sai da ya ɗau wayar sa ya ƙira wani layi abunda kawai yace shine ,
" Ranki ya daɗe na kawo su gidan, matar da take kula da ita tare da wata mace da cikin hirar su na fahimci 'yar uwa ce gare ta ,
Ya ɗan saurara kaɗan , kafin ya ɗora da cewa ,
"gobe ma zan dawo wajen su doumin jin ko suna da watta buƙata kamar yadda shi yace ,
"To ki huta Lafiya ranki ya daɗe .
****
Washegari saboda gajiya basu farka da wuri ba sai kusan ƙarfe bakwai na safe sallah suka fara yi , kafin Yakaka wacce tayi jugum daga inda take zaune tana ƙarewa taffaɗan falon kallo da yake wadace da kayan more rayuwa irin na zamani ,
Ji tayi zuciyar ta ta ɗan rage zogi ganin kyakkyawan muhallin da Falmata da Mama suke rayuwa a ciki ,
Amma ko kusa ƙudurin ta na raba su da rayuwar gidan bai sauya ba ,
Ganin ta ta mayar kan Hajja wacce take addu'o'i ganin ta idar ya sa ta gaishe ta ,
Hajja ta amsa mata tana tambayar ta yaya kwanan baƙunta ?
***
Kafin tara da rabi sun gama aikin gyara gidan da cikin sa bai wani cika datti ba sai ƙura da suka gog-goge , Hajja ta ɗaura musu girki ita kuma Yakaka ta fito sharar harabar gidan ,
Da kallo take ta bin Babbar ƙofar da take gefe tana fuskantar mai shigowa gidan wacce take da ƙofar gilashi , amma ba'a iya hango abunda ke ciki saboda tafka-tafkan labulen da suka rufe ,
Takawa tayi a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar ta tsakanin labulen da bai kai ga haɗewa ya rufe ba take iya hango cikin Babban Falon ,
Ta ɗan sake matsawa jikin ƙofar ta sa fuskar ta sosai tana leƙen cikin falon da haka kawai ta damu da son ta ga menene a ciki ?
Akan idanun ta ta ga giftawar Mutum a cikin falon , da ya sa tayi saurin ɗago fuskar ta lokaci guda tana tunanin aka ce kuma babu kowa a gidan sune ma suka buɗe gidan , kuma sun rufe tun cikin dare har kuma yanzu ma gidan a rufe yake to waye kuma ta gani ta cikin falon ko nan ɗin ba ɓangare bane na gidan ?
Sake mayar da kan ta tayi tana leƙen cikin falon bata ga kowa ba , amma ta cigaba da yawata idanun ta a ciki har zuwa wani ɗan lokaci kafin ta ji an dafa ta ta baya ,
A tsorace ta waiga , ganin Hajja ce a tsaye tana bin ta da wani jirkitatcen kallo , ya sa ta yin ajiyar zuciya ,
"Hajja akwai mutum a falon nan ko ?
Wani kallon yatsu-tsu Hajja tayi mata ,
"akwai mutum fa kike tambayata 'yar nan ? Gidan mutane kya tambayeni ko da mutum ? Nan da kike gani sashin shi Maigidan ne Baban Mama , Mijin Falmata .
"Amma kamar na ga fa mutum yana yawo a ciki Hajja ko shi ɗin yana nan ne ?
"wa ya sani ko Fatalwar sa ce kika hango , saboda shi dai kam baya gari , sai dai in kuma binbinin sa kike a zuci abunda ni dai nake so da ke ɗaya ne ,
" ki kama kan ki , saboda kin ga dai yanzu a matsayin sirikin ki yake , ke kuma a matsayin Fatalwa kike a wajen sa ,
"Dan haka ki kame ki dunga nuna halin surukutaka, ki manta da mu'amalar ku ta baya da ta riga ta shuɗe muddin kina son nuna dattaku ato .
Jikin ta a sanyaye ta kama yin sharar da take da nufin yi , kalaman Hajja suna mata yawo a zuci , duk da ta sha faɗa matan hakan yafi sau shurin masaƙi daga ranar da ta ƙudurci niyyar biyo ta , amma kalaman basu taɓa huda zuciyar ta irin na yanzu ba ko me yasa ?
Ƙarfe goma direban da ya kawo su yazo , gaisawa kawai suka yi da Hajja tace yayi tafiyar sa anjima su da kan su zasu kasuwa ,
Ransa ya nuna ba haka ya so ba , amma ba yadda ya iya haka ya tafi yana muzurai .
Rochester New York
Tun bayan bayyanuwar cikin jikin Falmata laulayi ya sako ta gaba , laulayi take irin mai wahalarwa , kome ta ci amai take , ga kasala da rashin ƙarfin jiki , kusan kwance take yini , Youssouf ke yin kome na daga aikin gidan da bai cika yawa ba .
Ga ranta da yake a dagule saboda batun komawar su gida , so tayi Mama ta warke kafin komawar su wacce cikin kwanakin nan jikin nata yake yawan matsanta mata .
Sai dai duk yadda ta so Baban Mama da ya yarda ya ɗage komawar su gida saboda a yiwa Mama akai tunda ga damar ta samu , ita ta amince a yi amfani da jinin abunda ke cikin ta a yi Mama aiki ,
Amma yaƙi amincewa , hankalinsa yayi gida , har saɓani suka kusa samu a ƙarshe ya ce ba zai amince ba da abunda yake cikin ta da Mama duk ɗaya suke a wajen sa , hakkin su ne ya kare lafiyar su , su duk biyun ba zai yi abunda zai iya sa abunda ke cikin ta a hatsarin da zai salwanta ba , kamar yadda ba zai so rasa Mama ba ,
Su haƙura su bar kome zuwa lokacin da za'a haifi abunda yake cikin nata ya girma zuwa munzalin da shi ko ita da kanta zata sadauƙarwa da 'yar uwar ta/shi ɓargon ta .
Falmata tayi kuka akan wannan batun , a ganin ta Baban Mama baya tausayin Mama , yaya zai ce har sai Mama ta jira shekaru kusan ishirin nan gaba tana fama da wannan ciwon ?
Wannan ya ƙara mata damuwa duk ta rame sai haske da ta ƙara yi da ƙyalli irin na mata masu ɗauke da ƙaramin ciki ,
Ana gobe tafiyar su bayan sun dawo daga ganin likitan ta , inda ya bata tsawon watanni goma nan gaba da zata sake dawowa a duba idon saboda sanar da shi batun komawar su gida da suka yi ,
Sannan babu wata sabuwar matsala da ta taso akan idanun nata sai ma cigaba da ake samu kaɗan-kaɗan ganin nata yana ɗan sake ƙarfi duk da dai har yanzu bata gani tar-tar .
Yossouf ya dubi Falmata wacce ta rungume Mama akan cikin ta suka yi lamo akan kujerar ta naɗe musu jiki da babban bargo ɗaya , duk kuwa da cewa sanyi ya ragu sosai ƙasar .
"Fatima nace ki daina ɗaura Mama bissa ga cikin ki , kada ta miki ciwo ko kuwa abunda ke cikin ki .'
Ɗan murmushi tayi bata ce kome ba illa sake rungume Mama da tayi wacce take taɓa ƙailula saboda rashin jin daɗin jikinta ,
Ba tare da ya janye idanun sa daga kan su ba ya cigaba da cewa ,
"dagga mun koma gida zan kai Mama école ko doumin ta huttashe ki , ki yi fama da kan ki kadda ta kawo matsala ga Baby ,
Da sauri ta katse shi ,
"Baban Mama a yanayin wannan jikin na Mama zaka kai ta makaranta , da dai ka dauka mata mai koyarta darussa a gida , makaranta yara zasu doke ta ko kuwa ta yi tsalle-tsallen da zai iya kawo tashin ciwon ta , ga....
Shima katse ta yayi cikin taushin murya ,
"Fatima ciwon Mama ai bai hana karatu , baki da labarin masu ɗauke da irin cutar ta har suna kaiwa ga matakin kammala jami'a har ma suyi aikin bautama ƙasa , al'umma kouma ta ci moriyar su ?
"Mama zata tai ecole inshaAllah , ki dunga ƙarfafa mata a matsayin ki na ouwa gareta , wataƙila watarana ita ma ta zam likita ,
Ya ƙarasa zancen zuciyar sa cike sa burin son Allah ya gwada masa wannan ranar ,
"Allah ya sa Baban Mama , Allah ya raya mana Mama mu kai zuwa ga wannan ranar .
Ta amsa fuskar ta ɗauke da murmushin da ta kwana biyu bata yi irin sa ba ,
***
Washegari bayan sun kammala duk wasu shirin su , sun haɗa kayan su da suke son komawa da su gida a cikin manyan Jakankunan su da suka zo da su alhalin babu kome a cikin su , a yanzu cike suke da tarin suturu , magunguna , zuwa kan kayan buƙatun su na yau da kullum da suke son tafiya da su .
Sauran tarkacen da bashi yiwuwa su kwasa Youssouf ya zubda a babbar shara , bayan sun gama tattara kome nasu ,
Youssouf ya zare katin kuɗin sa da ake cirar kuɗin ruwa da na wuta tare da gas da suke amfani da shi tsawon lokacin ,
Suka jawo jakankunan su waje , inda suka tarar da waɗanda suka basu hayan gidan suna jiran su , miƙa ƴsn mukullin gidan ya yi ,
Suka yi musaba tare da godewa juna , ya matsa kusa da Musa da Ramlat wanɗanda suke tsaye ,
Fuskar su cike da alhinin rabuwa da zasu yi a yau bayan ɗan takaitatcen zaman jin daɗi da mutunta juna gami da shaƙuwar da ta fara shiga tsakanin su , suka gaisa
Basu wani jinkirta ba suka shiga mota baki ɗaya da kayan su Musa ya jaa su kai tsaye zuwa Airport inda jirgin da zai sada su da ƙasar su kai tsaye daga nan harabar tashi da sauƙar jiragen sama na birnin New York zuwa harabar tashi da sauƙar jiragen sama na Niamey .
***
Ƙarfe huɗu na agogon Niger jirgin su ya dira , inda daman direban sa na musamman yana jiran sa , ba wanda ya ke kai Falmata makaranta da daukota ba wanda shine yake kai Hajja Maiduguri ,
Wannan direban sa ne musamman daga wajen aikin sa , da daman sun san da isowar sa ,
Gidan sa ya nufa da shi duk cewa Falmata ta so su zarce asibiti saboda Amai da Mama ta dunga yi tun a cikin jirgi , jikin nata ba daɗi sosai ,
Har cikin gidan direban sa ya shiga da motar , ya buɗe musu ƙofar motar suka fito ,
Youssouf ya riƙo hannun Falmata da ita ma ba wani jin daɗin jikinta take ba ɗauriya kawai take yi amma baki ɗaya zuciyarta hautsinawa take dan haka ne ma ta ƙi cin kome , yunwa kuwa sai sasuƙar ta take yi ,
Ya ɗauki Mama a kafaɗar sa wacce take kukan zafi tana son a cire mata kaya masu ɗan nawin da suke jikinta saboda sauyin yanayi .
Kai tsaye suka doshi cikin gidan sojan da ya ɗauko kayan su yana bin su a baya , bakin su duk ɗauke da Sallama suka shiga , shiru babu wanda ya amsa musu domin babu kowa a falon .
Da shigar su falon Yossouf ya zaunar da Mama bisa kujera , gefen Falmata ta sanya hannu ta jawo Mama jikinta ,
Shima zagayawa yayi ya zauna daga ɗaya sashin kusa da ita ,
Bayan direban ya gama shigo da kayan Youssouf ya yi masa iznin tafiya ,
Ƙarasa haɗe sararin tsakanin su yayi , tare da riƙo hannun ta da duk ya saki ,
"Fatima me zaki ci ? Hajja zata dafa miki , ina ga ma bata san mun dawo ba ,
"Mama ki je ɗakin Hajja kice mun dawo ,
Duk da cewa ba ƙarfin jiki ta cika ba sai ta miƙe ,
"to Papa ,
"Baban Mama bari na ƙira ta da kai na,
Riƙo ta yayi ya ɗorata baki ɗaya akan jikinsa , yana jin yadda jikin nata ya ɗau ɗumi ,
"ki bari Mama ta ƙira ta zata iya , kar ki wahalshe min da kan ki , shafa saman idanun ta yayi da suka ɗan shiga ciki , kin zauna da yunwa Fatima meyasa ,
Ƙarasa narkewa tayi a jikin sa tana jin daɗin irin riƙon da ya yi mata ,
"Nagaji da irin abincin su ne ,
" To me zaki ci Hajja ta dafa miki yanzu ?
" Ƙuli-ƙuli mai sugar raina yake so ,
Ɗan zare ido yayi sai kuma ya saki sassauƙar dariyar da har ta isa ga kunnuwan Mama wacce take ta faman tura ƙofar ɗakin Hajja ta gagara buɗewa ,
Ita ma dariya ta sanya jin sautin dariyar Babanta , tana sake tura ƙofar ta ga an buɗo , a hankali ta ɗaga kai tana kallon farar matar da take tsaye a gaban ta da bata kai ga taɓa ganin fuskar ta ba ,
Yakaka wacce fitowar ta kenan daga wanka ta ji ana taɓa ƙofar ta zo da saurin ta ta buɗe ga zaton ta Hajja ce wacce ta tafi kasuwa sayo kayan miya tun da ta idar da Salla ,
Fuskar da ta ci karo da ita a zahiri ta sa zuciyar ta sauya bugu , tamkar a mafarki ta gan ta a gaban ta duk kuwa da cewa tana da masaniyar dawowar su a tsakanin yau zuwa gobe a cewar Hajja ,.
Bata san lokacin da tayi durƙuso ba a gaban ta , ta miƙa hannuwanta biyu ta tallafe kumatun ta bayan ta dai-daita tsawon su ,
"Mama ,
Ta ƙira sunan ta da wani irin sauti ciki-ciki ,
rungumeta take nufin yi sai taji yarinyar ta janye jikinta a hankali ta yi baya-baya ,
Kafin ta juya da ɗan gudun ta tana ƙiran
"Papa , Mama , watta ce cikin ɗakin Hajja ,
Da sauri ta yunƙura ta bi bayanta saboda ji da tayi gaba ɗaya zuciyar ta ta afu ga 'yar ta , wani irin shauƙin so da ƙaunar 'yar ta ke kwaranyowa a zuciyar ta ,
Da taka kafafunta a falon Falmata ta ɗago kan ta , daga ƙirjin Youssouf , tare da chanjin bugun zuciyar ta , a take ta bijiro mata a cikin rai Yakaka, ta ambata a zuci ,
Tare suka ƙaraso da Mama da ta tafi da gudu ta hau kan jikin Babanta da Falmata ta ɗaga ,
Turus tayi , idanunta ya sauƙa akan su , da wani irin yanayi ta dubi ƙwarar idanun Youssouf da suke cikin nata da yanayin firgici ɓaro-ɓaro a cikin su ,
Cikin daƙiƙa kaɗan ta janye idanunta daga kansa ta mayar su ga Falmata , wacce take ware idanun ta da suke hango mata dusu-dusun farar mace sol a tsaye , wacece wannan ? Hajja kenan ?
Girman da Falmata ta yi tare da gogewar da tayi basu jirkita mata kamannin 'yar ƙanwar ta ba , so take ta taka taje ta rungumeta , sai dai wanda ta hango ta jingine da jikin sa ya mata tarnaƙi .
Bata motsa ba daga inda ta ci birki , illa Muryar ta da ya ratso shirun da wajen ya ɗauka ta ƙira sunan ta
"Falmata na ,
Muryar ta ta sauƙa da ƙaƙƙarfan sautin da ya wuce yadda ita ta yi maganar a kunnuwan Falmata ,
Waigawa tayi sashin da Youssouf yake a daskare , muryarta na rawa tace
' Baban Mama muryar Yayata nake ji ta ƙirani , Muryar Maman Mama , Muryar Yakaka na , yan yién .
Yakaka wacce Hawaye ya fara sauƙa daga gurbin idanun ta tace ,
"Falmata umaa yammana3 , umaa bangie3 , are3 nayie3 Falmata , Falmata are3 nayie3 , are3 Falmata kiramie nyie .
Sai ta miƙe a hankali daga gefen sa tana jin wani ƙaƙƙarfan yanayi na kusancin su na ingizata yana cire mata duk wani tsoro da shakku daga ran ta , Yakaka ai wata sashi ce na daga tsokar jikinta
babu shakka wannan Yakaka ce tsaye a gabanta , wannan farar inuwar da take gani ba kowa bace illa Yakakar ta , 'Yar uwar ta , Ashe Yakakar ta na raye , ashe bata mutu ba ? ???
Yakaka bata jira ta ƙaraso inda take ba ta tafi ta rungumeta , zuwa lokacin su dukkanin su biyu kuka suke da sauti ,
Kukan da kowaccen su ta jima tana neman 'yar uwa da zata taya ta yin sa , kukan kewar junan su , kukan tausayi da ƙaunar junan su , kukan tunowa da farkon fari , mafarin faruwar walagigin su ,
Mama wacce tayi lamo a jikin Baban ta ɗago kan ta tana kallon fuskar sa ,
"Papa qui est cette femme étreignant ma mère? qu'est-ce qui les fait pleurer? ( Papa wacece wannan matar da ta rungume Mamana? Meyasa suke kuka ? )
Tamkar wanda ya farka daga bacci haka ya firgita da tambayoyin Mama , kallon ta yayi kafin ya mayar da ganin sa kan su da suka ƙarasa zama a ƙasa har yanzu suna kuma rungume da junan su tamkar idan ɗaya ta bar ɗaya ɗayar zata gudu ko ta ɓace .
Motsa laɓɓan sa yayi da nufin yin magana sai dai ko kalma guda ta gaza fiddo da kan ta , wani irin zullumi mai tafe da tsananin firgici ke samun matsugunni a ƙarƙashin ran sa ,
"Yakaka bata mutu ba ta dawo ??
Wani irin sarawa kansa ya yi lokaci guda , take gumi ya shiga tsattsafo masa tunanin makomar auren sa da Falmata yana kassara masa duk wani guntun ƙarfin sa .
Assalam Alaikum masu karatu ,
Da fatan duk kuna lafiya ?
Ina miƙa sakon gaisuwata a gareku da fatan alheri a duk inda kuka yi bigire .
za ku ce ya ta rage hannu ?? 😜😂
Ban san ko kun fahimci MHR ya fara naɗe kayan sa ba ? Me zai hana kafin lokaci ya gwada mana ƙarshen MHR dukkanin masoyan MHR na fili da na ɓoye su yunƙuro , kuyi ɗango ku gwada min ƙaunar ku ga MHR ta hanyar bayyana ra'ayoyin ku tare da danna ɗan tauraron nan , da ni kuma na gwada muku irin tawa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 66 Chapter of 103