ko wa ?
Bata tsaya ba ta cigaba da cewa " me zai hana ta dawo nan gidan ta zauna a ɗakin nan na 'yan aiki kafin a samu wajen da za'a wurga ta tunda kaga fa irin halin ta na cuɗanya da maza ta riga ta saba da 'yan taɓe-taɓe da tsotse-tsotse da kwakule.....
" kin ga bana son shirita ki faɗa min magana kai tsaye kawai .
Ya furta hakan a taƙaice fuskar sa na bayyana wani yanayi na daban saɓanin wanda ya shigo da shi '
Ajiyar zuciya tayi shirin da suka haɗa ita da Samy baby yana mata yawo a zuci , sannan makirar zuciyar ta na cigaba da mata huɗhuba tace " ina nufin tunda Yarinyar nan kowa dai ya riga yasan irin rayuwar da take yi kafin a laƙaba maka auren ta dan haka na ga gara ka dawo da ita nan kana lura da ita dan saboda kar ta cigaba da yin ''yan harkokin ta tunda dai mai hali bai fasawa daga haka kuma ta kwaso mana ƙajaga ta shafa mana ko kuwa a maƙalo baragurbin ƙwai a liƙa maka ya ƙyanƙyashe ya zamar mana bala'i a doron ƙasa ko me ka gani Doctor na ?
Shiru ta ji bayan gama bayanin ta , sai ta ɗago kanta a hankali ta ɗaura ganin ta kan fuskar sa .
Yanayin da ta hango akan fuskar sa ya tsinka mata zuciya ta ɗan yi yaƙe sanan ta ce "Docto....
Da hannu ya dakatar da ita wani irin murmushi yake da ya mata wuyar fassara yace , " Sofi kin yi tunani mai kyau , wanda na riga ki yin makamancin sa .
. Ya ɗan yi shiru yana kallon yadda faffaɗan murmushi ya cinye fiye da rabin fuskar ta , ya cigaba da cewa
" Fitar da nayi a ɗazu gidan da tayi rayuwa tsawon shekarun da tayi bata gida nan naje , kuma Alhamdulillah Amina ta samu shaida saɓanin wanda ni da ke da wasu tsirarun mutane wataƙila ka iya hasashe , Amina ba rayuwar banza tayi ba , asalima yaudarar ta aka yi aka taho da ita Abuja .
" babu wata hujja ɗaya da zata sa a cigaba da yi mata kallon wacce tayi yawon banza, da ya wuce mummunar ƙaddarar da ta faɗa mata da kuma Allah ya iyakance mata shi , dan haka ina so daga yau ke ma ki cire wannan zargin daga ran ki Wafaa nitsattsiyar mace ce wacce ta tafi neman ilmi kuma ta samu dai-dai gwargwado da fatan kin gane ?
Ya ƙarasa zancen yana kallon cikin idanun ta da suka yi wani irin mitsi-mitsi tana kallon sa , bai jira amsar ta ba ya cigaba da cewa
"Amma duk da haka na karɓi shawarar da kika kawo na dawo da ita kusa da mu dan haka ina ga ranar juma'ah zan tafi Maidugurin sai kawai mu zo tare amma ba a ɗakin 'yan aiki zata zauna ba ɗakin 'yan aiki na 'yan aiki ne ita kuma Mata ta ce dan haka zata zauna a ɗakina kafin na samu gida nan kusa da .....
Zuruf! Sofi ta miƙe daga kan ƙafafun sa jikinta har mazari yake ta fara cewa.
" wallahi Hamza baka isa ba , baka isa ka mayar da ni wata wacce bata san kanta ba , dan ka je an faɗa maka ƙarya da gaskiya shine zaka hau kai ka zauna ba bincike ba kome ni nan na san har gidan da tayi rayuwa a ciki tana sheƙe ayar ta a 'yan iskan samarin garin Abuja kaf ɗaya-ɗaya ne basu kwana da ita ba dan haka wallahi ba zan yadda ina zaman-zamana a kwaso min ciwo a yarɓa min ba sai dai ka zaɓa wallahi ko ni ko ita .
Da sauri ta juya har tana tuntuɓe kome yana shirin kwaɓe mata dole ta yi yunƙurin ɗaukar mataki mafi tsauri da zai kawo mata ƙarshen kome
****
Mutanen Maraɗi sun juya tare da Falmata da Hajja a ƙarƙaahin rakiyar Amnee da zainab wadanda kwana biyu kawai zasu yi su wuce Chad Amnee zata je yiwa dangin su na can gaisuwar bangajiyar biki tare da godiyar hidindimun da suka yi musu..
Sun samu tarɓa mai kyau daya shafi wajen kwana tare da cimaka masu kyau da kuma tarin girmamawa daga bayu da hadiman gidan sarauta.
Daga Hajiya Umma kuwa babu yabo ba fallasa tun zuwan su sau uku kaɗai ta zauna da su waje ɗaya. Ranar farkon zuwan su da kuma washegarin zuwan su da suka je gaishe da Maimartaba sai kuma yau da suke yi mata Bankwana
nan ma kadaran-kadahan suka gaisa Amnee ta ɗanka mata amanar Falmata , tana sake jaddawa akan a yi kiwon ta saboda yarintar ta kada a bar ta da kankin kanta .
Amsar da Hajiya Umma ta bayar ya sanyayawa Amnee jiki domin kuwa cewa tayi " Ɗa ai na kouwa ne itta kouwa ɗabi'a ta mai itta ce hali kuma shi ke samar da gurbi .
" Babu Shakka.
Amnee ta amsa mata .
Tafiyar su ta karya zuciyar Falmata yadda bata zata ba , ta dunga kuka tana hangowa kanta rayuwar da zata yi a cikin wannan makeken gidan alhalin shi wanda take zaune domin sa bai ma san da zuwan nata ba.
Tun bayan tafiyar su sai Falmata ta zama shiru koyaushe tana cikin babban ɗakin da aka mallaka musu ita da Hajja , wanda yake cikin falo na farko a shiyar , abunda ke fitar da ita gaishe da Hajiya Umma da suke zuwa yi kullum safe ita da Hajja daga sun dawo bata kuma fita sai kuma wata safiyar ,
Bayi biyu da aka ware mata su ke hidimar abincin ta tare da kula da tsaftar ɗakin da take , babu abunda take daga zama sai kwanciya , baki ɗayan rayuwar bata mata daɗi ga zaton ta idan sun iso zata samu ko da damar da zata dunga yin waya da Biyamuradi Youssouf sai ta tarar da rayuwar masarautar ba yadda ta saba ba , kowa a cikin gidan bisa umarnin na sama da shi yake aiwatar da lamura .
Duk yadda Siyama da Aicha suka so su dunga jaan ta fira zuwa falo taƙi yarda ,dan haka suka ƙyale ta lokaci-lokaci Siyama kan shiga ɗakin su gaisa sannan su ɗan taɓa hira saboda gidan sarauta suke kome kake idanu na kan ka zai iya zama abun magana ko ma gorantawa ace kullum ita ke zaryar shiga wajen Falmata a matsayin ta na kishiyar ta .
ita kuwa Aicha daman bata cika zaman gidan ba saboda tana shirin kammala karatun ta , dan haka Falmata kaɗaici ya mata yawa .
har gara Hajja da daman ita bata ɗau zaman ɗakin ba ficewar ta take can shiyar Bayin gidan su sha hirar su duk da cewa ba wai aiki take yi ba .
Yau tun safe ta tashi da ciwon baya da ƙafafu saboda cikin kwanaki biyun abunda ke cikin ya fara mata nawi ga yawan motsi da yake yi dan haka sai ta gagara ko da zuwa gaishe da Hajiya Umma kamar yadda ta saba tayi kwance lamo tana jin yadda abunda ke cikin ta ya cure gefe ɗaya.
Hajja ita ɗaya ta tafi gaishe da Hajiya Umma ita ma ba wani sakar mata fuska Gimbiyar take yi ba "ah to Hajiya Umma ce fa ɗiyar Saraki matar Sarki ?
Hajja ta so ta sanar da Hajiya Umma rashin jin daɗin da Falmata take fama da shi a yau sai dai yadda tayi wofintar da ita ya sa ta gaza shigar da batun Falmatan, ta ga sai umarni take bayarwa ga bayu ga Alama dai wani shiri na musamman ake yi yau a gidan .
Dan haka sai Hajja ta miƙe jiki a sanyaye ƙasa-ƙasa tace "bana iya ba wannan gurfanon ya na me neman gafara ni ba lafiyar ƙafa na cika ba , a ƙare ƙalau wannan bautar mai ciwo ? ai ni ba sayo ni aka yi ba dan haka ba baiwa bace da za'a isheni da wani ƙaburi, duk na gundura da zaman gidan nan Babban Soja Allah ya baka lafiya mu samu mu koma gidan mu inda muke a sake ba wata takura .
Bata koma ɗakin ba sai ta fita can inda ta saba hira cikin bayu amma yau sai bata same su sun yi sansanin hira ba kamar yadda suka saba , sai shiga da fita kowaccen su take yi akan aiyukan su hankalin su bai kan ta.
Ɗan zaman mintoci tayi ta miƙe domin komawa ciki kan hanyar ta suka ci karo da Babbar baiwar da take kula da shiyar abincin gidan wanda a shekaru aƙalla zasu yi sa'o'in juna bayan sun gaisa har Hajja ta gota sai Tabawa ta dawo da baya tayi ƙasa-ƙasa da murya tana ɗan leƙen baya tace " Hajja Hauwa da fatan dai kin taya Uwargiyar ki shiri ? Dan Kin kouwa san ɗiyan yanzu ba irin mu bane masu duƙufawa bauta ga Miji .
A ɗan jahilce Hajja tace "Shirin me fa Tabawa ?
Kama haɓa tabawa tayi tana ɗan karkata kai tace "kada dai kice min Uwargijar ki Gimbiya batta da sanin Yarima na daf da shigowa Masarauta ba ? dan kouwa a halin yanzu ma suna Niamey zuwa yammaci kouwa suke shigowa nan .
Da hannu biyu Hajja ta dafe ƙirji muryar ta na bayyana mamakin ta tace " Dan Allah fa Tabawa?
A mamakance ta cigaba da cewa "yo ina kuwa muka sani muna zaune bonono , ai tsayuwa bata ganni ba dole na yi hanzarin komawa ciki, ke dai tabawa nagode miki.
A zaune ta tarar da Falmata tana mammatsa yatsun ƙafafun ta da suke mata tsiko , ba tare da ta ɗago kai ba ta amsa Sallamar Hajja wacce ita ma kai tsaye ta zarce banɗaki ,bata tsaya yi mata dogon bayani ba .
ruwa mai zafi ta tarawa Falmata ta tuttula duk turarurrukan wanka da ta tarar da su a guri na musamman a jere da wasu ma ƙila ba na wanka bane ita dai Hajja ta zuba ƙamshi gum kuma ya cika banɗakin ya ratsa har waje .
"Fatima tashi ki je kiyi wanka maza-maza zama bai gan ki ba 'yar nan .
Hajja tace haka lokacin da take dawowa cikin ɗakin
Falmata da ta riga ta saba da subaɗaɗin Hajja ta ɗan dubi Hajjan tana komawa ta kishingiɗa a ƙasa tace "Hajja duk yaushe nayi wanka da safe ? Sannan kuma wanka da tsakar ranan nan ƙarfe ɗaya saura Hajja lafiya dai ko ?
" lafiya lau sai Alheri 'yar nan domin kuwa yau Ubanɗakina ke dawowa Babban soja Baban Mama yau amaryar ki kike uwarɗakina wankan taryar miji za kiyi .
"Da gaske Hajja ?
. Falmata ta tambayeta tana miƙewa zaune fuskar ta ɗauke da yanayin da tashi ɗaya ba'a ba shi matsayi ba .
bata jira Hajja ta bata amsa ba ta cigaba da cewa " Amma kuma ba wanda ya faɗa mana ko Maman Yumna ma bata faɗa min ba anya Hajja da gaske ne ? wa ya faɗa miki ?
. " mts , ahaf ai ga irinta nan ke wa ya faɗa miki kishiya tana zama abar dogaro ɗari cikin ɗari ? Wa yace miki ana bada amanna da Amana baki ɗaya ga kishiya ? Ni daman daga ganin yadda take miki nan-nan nasan tsagoron kissa ce da kilbasa ai kin ga ga shi da tasamu labarin dawowar mijin ku ɗif ta ɗauke ƙafa tana can ta duƙufa shirya kan ta , ta bar ki baki sake ,
"Yanzu kiyi maza ki tashi ki gyagiije dan waɗannan ƙananun muri-mirin kowacce mai ciki sai tana yin su basu isa hana kome ba ai ciki ba cuta bace , kiyi azamar yin wankan ki fesa ado irin na shiga gasa ki tafi gaida Mahaifiyar sa daga nan ki zauna a falon ciki wajen ta , ta yadda daga ya sanyo kai falon zai gan ki tunda kuwa dai daga ya iso gidan gaishe da ita shine abu na biyu da zai yi bayan gaishe da Mahaifinsa , kin ga ita Siyamar take ko wa ? Da take miki ƙafar ungulu kin riga ta ganin sa , tashi maza uwarɗakina ba'a bori da sanyin jiki ...
"Hajja ni dan Allah ki rabu da ni , kina ganin dai yadda koyaushe muka je gaishe ta ɓata rai take yi dakyar take ansawa sannan .....
Kafin ta ƙarasa Hajja ta katse ta "banda abun ki uwarɗakina faɗan da ya fi ƙarfin ka ai mayar da shi wasa kake , idan ta amsa yau da kyar watarana da fara'a zata tare ku ke da 'yan jikokin ta kiyi haƙuri kin ji inda ba'a son ka anan arziƙin ka yake ke dai gwada mata ɗa'a sai ki ribaceta da kyawawan ɗabi'u kin san su saraki ne sai ana musu bangirma kin jii ko? .
Turo baki Falmata tayi da cigaba da cewa " sannan Hajja shi ma ɗin ai bai ma san mun zo ba tunda kin ga fa bai taɓa neman mu ba gaskiya ni ba zan kai kaina wajen sa ba idan shi ya zo shikenan idan bai zo ba ma ni.....
Wannan karon a hasale Hajja tace "to ai shikenan zauna kiyi ta jiran sa anan shi da yayi yi jinyar ya zo ya gaishe ki Iya-gwamma , tunda ni dai ba ki ɗaukeni bakin kome ba a zaman mu ban isa baki shawara ba ai shikenan .
Daga haka tayi ficewar ta
Bayan fitar Hajja a ɗakin sai duk jikinta yayi sanyi , tunda take da Hajja bata taɓa ganin tayi fushi ya haka ba duk sai ta ji ba daɗi dan haka ta miƙe a hankali ta shiga banɗakin
Bayan fitowar ta da daga banɗakin da ta kwashi wajen mintoci talatin a ciki tana wanka.
jikinta ba kuzari ta zauna a kujerar gaban gadon , har yanzu Hajja bata shigo ɗakin ba , tunanin da yake nuƙurƙusar ta sake yawaita yake yi
"da gaske yau yake dawowa amma bai neme ta ba ? Tun rabuwar su har yau bai taɓa jin kewar ta ba kenan ? Shiyasa bai neme ta ba , tunda Aicha tace suna yin magana a waya kuma ko bayan dawowar su maradi rannan da kunnen ta taji suna waya da Aicha , kenan ita ce bai nema saboda baya buƙatar ta ko me ? to meyasa ita kuwa zata damu kan ta da tunanin sa ? Har Hajja zata matsa tayi wani shiri na musamman a domin taryar sa .
Har ruwan jikinta ya bushe bata shafa Mai ba , agogon ɗakin ta duba ƙarfe biyu har da kusan rabi dan haka ta miƙe ta sake komawa banɗakin tayi Alwala ta zo tayi Sallar azahar bayan ta idar bata miƙe akan sallayar ba ta cigaba da zama akai tana istigfar lokaci-lokaci tana murza idanun ta da suke mata mil-mil tunda tayi wanka da alama sabulan da tayi amfani da su wajen wankan sunfi ƙarfin lafiyar idanun ta .
Tana zaune har aka ƙira la'asar bata jinkirta ba tayi Sallar kawo lokacin rashin jin motsin Hajja ya fara damun ta dan haka ta miƙe ta buɗe Babbar wardrobe bango guda da aka zube mata suturunta ciki ta dauko wata doguwar baƙar riga ta sanya a jikin ta ba tare da ta shafa ko hoda ba sai ɗan mai da ta mutsiƙa a fatar ta .
Dawowa gaban Babban mudubin tayi ta tsaya tana duban kan ta cikin ta da ya ɗan tasa ya bayyana a sarari ta cikin rigar ta tsirawa ido.
"Kunyar fita a haka ana gane mata cikin ya kamata ta .
"Mts shi cikin nan ma duk ya bi ya hana mutum sakewa .
tayi mitar haka lokacin da take cire rigar jikin ta ta zaro wata doguwar riga har lau launin ruwan zuma mai duhu da ya ɗan sirka da zane a tsai-tsaye launin farar ƙasa , rigar faffaɗa ce da take da rufaffen wuya sannan tana da ɗan nawi kaɗan a can Rochester ta taho da ita ,
lokacin da ta Sanya a jikinta ita da kan ta sai da ta ɗan murmusa saboda yadda rigar ta amshi zubin jikinta na dirarriyar mace mai matsakaicin tsawo da 'yar ƙiba kaɗan sai cikin nata ya ɓuya a rigar
Rigar bata da mayafi dan haka ta ɗau wani babban mayafi launin farar ƙasa da aka masa adon duwatsu ta yafa akan ta ya rufe mata jiki kirif , har zata matsa daga gaban mudubin idanun ta suka kai kan 'yan kunnayen ta da tunda ta taho da su daga Maiduguri ta cire su ta ajiye ana, su ta kai hannu ta ɗauka 'yan gajeru ne ta maƙala su a kunnuwan ta a hankali ta sanya ɗan yatsa ta lakaci mai ta shafe siraran labbanta marasa tudu .
Takalmanta masu kama da silifa 'yan madina amma wannan daga Rochaster ta zo da su su ta zira a ƙafar ta ta fito bayan ta shafe jikinta da Humra da kamshin ta ke tashi kaɗan-kaɗan .
Boyayyar ajiyar zuciya tayi lokacin da ta fito falon ta ga Hajja zaune daga gefe da alama Salla ta idar .
Da fara'ar jin daɗin ganin ta ta matsa kusa da ita kafin tace " Hajjata anan kike ?
Ɗan waigowa Hajja tayi kamar bata san da fitowar ta ba tace " uhm anan nake .
" to sannu da hutawa Hajja nima yanzu na gama shirin zan shiga na gaishe su yadda kika ce .
. Wannan karon Hajja ta ɗan saki fuska jin Falmatan tace zata yi yadda ta sa ta dan haka ta ce " to Madalla ko kefe fa uwarɗakina ? Maza je ciki ki zauna idan son samu ne ma ki samu wajen da yake fuskantar ƙofar shigowa ki zauna kin ji ko ?
. " to Hajja
Falmata ta amsa cikin ran ta tana gujewa rigimar Hajja ne amma idan ba haka ba ita ba wani niyyar zama tayi ba .
Da kallo Hajja ta bi bayan ta cikin ran ta kakkabin wannan rigar ta Falmata take yi taɓe baki tayi kafin a fili tace " ana yi yafi ba'a yi tsarkin mahaukaciya da kunu , idan ba haka ba wannan riga da kika sako ai bata da maraba da buhu .
A ɗarare Falmata tayi sallama a bakin falon da daga inda take tana jin tashin hayaniya da dararrakin mutane da alama akwai wasu baƙi masu ɗan yawa a ciki .
Ɗan jim tayi jin babu wanda ya amsa mata duk kuwa da tasan ana jin ta, sake sallamar tayi a karo na uku sannan ta tsinkayo muryar wata daga ciki ta amsa , dan haka ta sanya ƙafafun ta ciki a hankali .
Da ɗai-ɗaya suke mayar da hankalin su kan ta tana tahowa har ta ƙarasa daga gefe kaɗan tayi ɗan gurfano tana gaishe da Hajiya Umma wacce tunda ta shigo ta rage fara'ar da take yi , kamar yadda ta saba amsa mata gaisuwar ba wata kulawa haka yanzun ma ta amsa tana janye ganin ta daga kan ta zuwa gefe kafin ta yunƙura tana barin wajen baki ɗaya zuwa wata ƙofa daban .
A hankali ta waiga tana ɗan kallon sauran matan da suke wajen biyu daga cikin su kawai ta gane "Ubbo da Ammi sauran mata ukun bata gane su ba amma dai suna mata yanayi da su Ubbo , cikin nutsuwa ta gaishe su a kunnen ta Ammi ce kaɗai ta amsa da mutunci sauran matan sama-sama suka amsa ita kuwa Ubbo ko amsawar ma bata yi ba .
Fitowar Siyama daga ɗakin Umma yasa ta ɗago kan ta " sœurs wannan fa ? Kamar ya fi zama a jikina kou ?
Ta ƙarasa zancen tana ɗan yin juyi cikin dakakiyar Shadda "Boo" da ta sha aiki aka mata ɗinkin doguwar riga , nan take wajen ya ɗau ƙaramar sowa suna yaba kyaun da tayi .
cike da burgewa Falmata take kallon ta tana murmushi sosai ta yi mata kyau kwalliyar ta kuma ta ƙayatar da ita .
" kin yi kyau Maman Yumna , muryar Falmata ta ratsa wajen .
Da sauri Siyama ta waiga inda ta ji tashin muryar ta da farkon fitowar ta wajen bata lura da wanzuwar ta ba .
Tana murmushi ta ƙarasa kusan ta kafin tace " Fatima nagoude sosai, yaushe kika shigo ?
"Yanzu na zo . Ta amsa mata a taƙaice
Murmushi tayi kafin ta ɗan yi ƙasa da murya yadda Falmatan ce kaɗai zata iya ji tace " Yau Yarima Biyamuradi ke dawowa , da fatan kin masa shiri ?
Da yanayin ta na rashin magana sosai falmata ta girgiza kan ta kawai tana janye ganin ta daga kan Siyama ta sunkui da kan ta ƙasa duk jin ta take a takure sakamakon kallon ƙasƙancin da ta lura matan wajen na jifan ta da shi .
Muryar Ubbo ta ratso wajen da take cewa " Siyama kiyi maza ki shirya mana kin tsaya inda bai dace ba , kin san fa Mijin ki na daf da shigowa , kin kuma san ke tauraruwa ce ba tururuwa ba , ke tauraruwa mai hasken alkhairi ce ba tauraruwa mai wutsiya ba .
Cikin sanyin jiki Siyama ta juya fuskar ta ɗauke da yalwatatcen murmushin jin ɗadin yabo mai kama da ƙirari da Ubbo tayi mata sai dai gefe guda tana jin wani iri da shaguɓen da ta lura Ubbo ta yiwa kishiyoyin ta .
Har tayi taku biyu ta waigo Falmata wacce kanta ke sunkui har lokacin ba tare da ta iya haƙaƙe halin da take ciki ba , ta saita muryar ta sama kaɗan kafin tace " Fatima taho mu tai ki sauya kaya akwai Boo irin ta jikina da tai min yawa nasan zata iya miki dai-dai tunda kin fini ƙiba kuma launin zai amshe ki'...
" ahir ɗin ki da arawa kishiya sutura solobiya hala ita batta da sutura ta ratayo wagga tsumma a jikin ta ta taho muna nan tana barin mouna tsamin gwanjo ?
. " ko da shike ba laifin ta ba nan gurin ta ƙurewa kenan , talaka daman yaushe yunwar ciki nashi ya lafa bare ya san suturar da ta amsa sunan sutura ? Bar ta cikin tsummokaran ta da shi yafi dacewa da itta ..
"s'il te plait Adda amm Dan Allah .
Da yanayi na rashin jin daɗi tare da chakuɗuwar tausayi Siyama ta juya ga Falmata lokacin da take mikewa tsaye , tayi saurin riƙo hannun ta tana cewa " kiyi haƙuri ƙamnata mu tai na miki le maquillage ki sauya kayan kin ji kou ?
Idanun ta cike da ƙwalla wannan karon cikin wani irin yanayi ta zame hannun ta daga riƙon da siyama ta mata , tana ƙoƙorin danne hawayen da suke neman ɓallowa tace " Nagode Maman Yumna sannan ba sai na sauya kayana ba na jikina ma masu tsarki ne kuma kyauta ce daga Mijina masoyina ,dan shi na saka dan ya gani yaji daɗi ba domin na zama tauraruwa ba ina so ya ganni da su rataye a jikina dan yasan cewa na yaba da kyautar sa .
Dan murmushi tayi kaɗan tana mayar da gani. ta kan su Ubbo daga inda take tana hango ɓacin rai akan fuskokin su da take iya gani dusu-dusu .
" Nagode sosai Maman Yumna , ta sake faɗin haka lokacin da take barin wajen .
Dusu-dusu take ganin hanya saboda idanunta da suke cike taf da ƙwalla ga kuma zogin da suke mata.
bata tarar da Hajja inda ta bar ta ba , tana zaton tana ɗakin su a yadda zuciyar ta take yanzu so take ta samu waje ta ɓuya tayi kuka , ciwo ke sasuƙar rarraunar zuciyar ta da daman tana kusa jiran kiris take .
Dan haka a karon farko tun zuwan su gidan ta fito ta ɗau hanya ba tare da tasan takamai-mai ina ta nufa ba bata kuma damu da bayun da suke binta da kallo har wasun su na yin ƙus-ƙus ba so take tayi nesa da mutane ta samu maɓoyar yin kukan ta masha'in '
Can wani sashin da ta lura da ɗaukewar ƙafa ta shiyar nan ta nufa ,lokacin da ta doshi mashigar sashin tun kafin ta ƙaraso masu gadi biyu suka dakatar da ita , tambayar ta suka yi wacece ita ? Ta basu amsa da ita ce Fatima , suka ce daga ina take ? Tace daga Maiduguri Nigeria .
Juyawa suka yi gefe suna ƙus-ƙus
Cike da gundura ta juya da nufin fasa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 87 Chapter of 103