Share this page
kyau ne babu abun da ya fi ɗaukar hankalin yakaka irin jajayen laɓɓan sa ," tambayar kan ta take daman maza ma na shafa jambaki ? hannu take niyyar kaiwa fuskar sa ta ga ya buɗe idanun sa a firgice kamar ba wanda ke bacci ba ," Da sauri ta jaa baƴa tare da maƙurewa a jikin gadon ," Zama yayi yana me ƙarewa ɗakin kallo kafin ya waiwayo kan yakaka tare da wani irin kallo da ta kasa tantance ma'anar sa ya watso mata tambayar da ta shayar da ita mamaki ," Wacece ke ?????? Assalamu alaikum masoya, ku min afuwa da jinkirin da aka samu kafin zuwan wannan shafin , da kuma rashin baku amsoshi n sharhn ku a shafin baya duk hakan ya faru ne sakamakon aiyuka da suka sha kaina , ina fatan na wanke kaina da wannan mafi tsawon shafi da na rubuto muku ?? Idan haka ne nima kar ku min rowar sharhin ku ,' ku faɗi ra'ayoyin ku,akan wannan tafiya tamu, a wannan karon zan bada lokaci mu tattuna tare domin ƙarin armashi , na gaishe ku kyauta !!! [10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ....... Hargitsin Rayuwa umm"muaz 20 Yakaka tana shiga gida Kai tsaye sashin samy baby ta nufa , ta ci sa'ar samun kofar ɗakin ta a buɗe kai tsaye ta danna kai cikin ɗakin idanun ta a rufe da ruwan hawayen da yake ambaliya ," Zube guiwar ta tayi a ƙasa tare da yin jifa da kuɗaɗen hannun ta suka tarwatse a tsakiyar ɗakin ,hannuwan ta biyu ta sa ta rufe fuskar ta lokacin da take sakin kukan da yake cin ta a zuci . Sautin kukan da yayi sanadiyyar tashin samy baby a firgice daga baccin tofon girar da take shaƙa ,"  Da sauri ta zo ta kama ta Yaks meye ya same ki ? Duka aka miki ? Ko meye ? Kusan ba a hayyacin ta ba ta riƙo hannun samy baby ,   Dan Allah ki ce masa ya dawo kar ya bar ni , idan bana ganin sa mutuwa zan yi , kin ga nan ,"ta ɗora hannun samy baby akan zuciyar ta ,"ciwo take min ina jin wani abu ya tokare ni ," INA SON SHI WALLAHI INA SON SHI," Kalmar ta ta ƙarshe ita ta sa samy baby kwashewa da dariya bayan fitar ta daga ruɗanin da kukan yakakar ya haifar mata shi da farko ,"    Shashashar banza yanzu ke yaks akan soyayya kike wannan uban kukan ? Kamar wacce aka cewa uwar ta ta mace ? To wai ma tsaya yaushe kika fara soyayya ban sani ba ? Duk kuwa da kashedin da nake yi miki ? Koh daga tafiyar da nayi ta sati biyun ce har kananan ƴan iskan nan da nake raba ki da su suka samu damar hure miki kunne ,ah lalle fa ga ki kuwa kin sauya kin yi lumui lumui kin cika kin yi clean , hala saurayin naki mai ɗan gwaɓi-gwaɓi ne naga ya wanke min ke , ah toh ai babu laifi tun da mai maiƙo ne ,"       shi ya baki wannan kuɗaɗen kenan ? ," ta furta hakan tana mai bin kuɗaɗen da kallo , " idanun ta suka sauƙa kan ɗan wani hoton fasfo wanda ga alama daga tsakanin kuɗin ya fito , ta kai hannu gami da ɗaukar hoton ,       Hoton sa ne sanye da kakin sa na soji daga kirjin sa zuwa fuskar sa ," kallon hoton tayi da kyau tabbas ta san shi abokin saurayin ta nuhu ne ,'bata manta ba nuhu ya bata ɗan takaitatcen tarihin sa a wani yammaci da taje bariki wurin nuhu ta tarad da youssouf ɗin , bayan tafiyar sa take tambayar nuhu  yaya ta ga launin uniform ɗin su ya banbanta ? Nan ya shaida mata youssouf sojin niger ne , ya ɗora da bata labarin sa kar ki gan shi haka anan fitattace ne a ƙasar su ɗan sarki ne , yarima ne mai jiran gadon birnin maraɗi ,babbar masarauta ce a niger ,"      Yaks wanene wannan ?? Ko shine masoyin naki ? Da sauri yakaka ta ɗago kan ta domin ta ga wanda samy baby take kira da masoyin ta ,     Idon ta ya sauka akan ƙaramin hoton biyamuradi , da sauri ta kaiwa hoton chafka !      Shine wallahi shine , ina son shi dan Allah anty idan kin san shi , ki kai ni wurin sa ,"    Cikin mamaki samy take yi mata kallon kan ki ɗaya ?    Ke yaks wannan ne saurayin ki ? Kar ki min ƙarya , gaya min ta yaya ya zama saurayin ki ?     Yakaka bata boye mata kome ba daga ranar haɗuwar su ta farko da youssouf zuwa yau ,"        Jinjina kai samy bby tayi bayan ta gama jin bayanin yakaka da ta tabbatar ba ƙarya bane ,! Domin ta san goge yaks a ɗan ƙaramin lokaci ta zama fes yadda ta gan ta sai mai kuɗi , Idan kuwa hakane babu shakka tayi farincikin ƙulluwar alaƙar sa da yakaka , daman irin namijin da take mata hange kenan wanda zasu tatsi arziki daga jikin sa  !tab , ai batun yace ya rabu da yakaka ma zancen iska ne , wasa tsakanin sa da yakaka yanzu aka fara , zata yi duk yadda zata yi taga mu'amalar sa da yaks ta ɗore , har sai ya gama wanke yaks ya zamar da ita mace mai aji yadda baza ta yi wahala ba wurin samun irin sa ko ma wanda ya fi shi koh da shi ya zo ya bar ta , ! Ai da ruwan ciki akan jaa na rijiya ,' idan yaks bata wanku ba ina zata samo masu attajirai irin wanda take buri???       Share hawayen ki yaks idan wannan ne na san shi abokin saurayi na ne , duk inda yake sai na nemo miki shi , kin ji ? Bai isa ba ya wurgar da ke bayan ya morewa ƙuruciyar ki , dole ya zo ya ƙarasa aikin da ya fara ," Cikin murna yakaka ta fara share hawayen ta , tana jin damuwar zuciyar ta fiye da rabi ta kau , jin cewar samy baby ta san bature kam silum har tayi mata alkawarin nemo mata shi ,"    A saboda murna tana tattara ƙudaɗen da ya bata , ta miƙawa samy baby ,"      Ga shi anty na baki gaba ɗaya ! Da murmushi samy baby take kallon ta , sa hannu tayi ta karɓi kudin ta ƙirga su dubu arba'in da shida ne ," Naira dubu goma ta zara a ciki ta miƙawa yakaka sauran ,"     Ki riƙe sauran kuɗin a hannun ki zasu miki amfani kafin na gama shirya yadda zan yi na dawo miki da yarima , wannan wanda na ware kuma , kafin ya dawo ku cigaba da harka dole zamu je asibiti a baki kariya daga samun ciki , kin sai dai ba'a cin moriyar bariki idan ana yi ana kwasar ciki .     Da sauri yakaka ta amince da shawarwarin samy baby , nan dai suka ƴar taɓa hira samy baby tana sake kitsawa yaks shawarwarin yadda zata riƙe yarima idan ya dawo ,     Falmata tayi jugum a zaune tana tunani, wata irin kewa take ji , tun da yakaka ta samu aikin da take yi yanzu  ya zama bata da lokacin ta irin da , duk da cewa dai idan tana gidan tana bata kulawar sosai da sosai bugu da ƙari ga cimaka masu kyau da daɗi da suke samu a yanzu , ga wasu ranakun ma biya yakakar take yi ayi aikin wanke-wanken falmata , amma duk hakan sun gaza samar da farin ciki mai daɗi ga falmata ,yanayin su na farko da ko yaushe suna tare yafi mata kome daɗi , bata da kowa bayan yakaka ,! Ga shi wannan aikin da yakaka ta samu yana neman raba tsakanin su , domin a yanzu duk zata iya ƙirga ƴan awowin da suke yi tare da juna a wuni , daɗewar da yakaka tayi yau bata dawo daga wurin aikin ba ya dagula ran ta , tana aunawa da zafin ranar da yake buso ta tare da kusancin ranar da take ji a jikin ta ta tabbatar yanzu rana ta fara kaiwa tsaka ! Ina yakaka take tun jiya da yamma har yanzu bata dawo ba ? A hankali wasu siraran ƙwallah suka silalo zuwa kan ƙuncin ta ,!   Bata ji zuwan ta wurin ba , sai saukar hannun ta taji ta share mata ƙwallar ,! Cikin ƙaruwar rashin kuzari akan wanda tafiyar youssouf ta jawo mata ganin hawayen falmata ya sake taɓa ranta , " ta zauna daga gefen falmatan        Falmata na ! Meyasa ki kuka ? Wani abun aka miki ? Ko baki da lafiya ne ? Yakaka yanzu kin rage kula da ni , bayan kuma kin san ke kaɗai nake da ita wacce take bani kulawa , " yakaka dan Allah nima ki yadda na dunga bin ki sabon wurin aikin ki nafi son koyaushe muna tare duk inda muke , bamu da kowa sai junan mu ,"    Kiyi hakuri falmata nima daga yau ɗin bazan sake zuwa ba !         Meyasa baza ki je ba ? Ni fa ba nace ki daina zuwa bane , toh shikenan na hakura ki dunga zuwa kin ji ,?    An dakatar da aikin ne wanda nake yiwa aikin ya tafi ,! Sai idan ya sake dawowa watarana ,"    Cikin rashin jin daɗi falmata ta karya wuya ,       Kai amma banji daɗi ba yakaka mutumin yana da kirki , tun da kika fara aiki a gidan su muke samun jin daɗi .,'     Uhum ,!      Cewar yakaka tana mai miƙewa Bari na sauya kaya na nazo kan aiki ,! Chan ƙasan kayan ta a kusa da kuɗaɗen niger da agogon sa da ya bata a haɗuwar su ta farko ta ajiye hoton tare da kuɗin hannun ta , a ran ta tana jin hoton sa da agogon sa zasu zame mata abun ɗebe kewar sa kafin samy baby ta dawo mata da shi kamar yadda ta alƙawarta mata ! Washagarin ranar samy baby ta samu yakaka , suka je asibiti ƙarƙashin jagorar wani nurse abokin hulɗar samy baby , tare da taimakon sa aka yiwa yakaka allurar hana ɗaukar ciki , ba tare da an tsawaita binciken ina mijin ta ba ?, tare da tunasar da ita dawowa sake yin wata allurar duk bayan watanni uku !   Yakaka bata ji ko ɗar ba sai ma farin ciki da take ji chan ƙasan ran ta a domin kan hanyar su ta zuwa asibitin samy baby ke sanar da ita a yau ɗin nan zata garzaya barracks wurin nuhu inda zata samu cikakken bayanin inda youssof yayi bigire idan ma ta kama har inda yake sai ta kai yakaka ! har ɗakin kwanan sa ,! Ah to meye bariki ce fah !  A haka suka tsaya . Sai dai tun dawowar su daga asibitin yakaka ta gaza tsinana wani abun kirki , saboda wani irin murɗawa da marar ta take ta sake , ga duhu-duhu da take gani a idanun ta ,! Gaba ɗaya jin ta take marar lafiya ,' dan haka ta zari nera dubu biyu cikin kuɗin ta ta bawa madam saly tace bata jin daɗi zata je ta kwanta ,"     Jiki na rawa madam saly ta warce dubu biyu tace ta je ta kwanta za'a yi aikin ta .!    Kafin azahar yakaka ta jigata saboda tsabar ciwon ciki da kwankwaso ta takure a guri ɗaya sai murƙususu take  , ! Larki ce ta shigo ɗakin ta tadda ta a galabaice ," nan take tambayar ta meye yake damun ta tace ciki da baya ,'         Cewa tayi ta bada kuɗi a anso mata magani ƙila ciwon cikin al'ada ne daman yana irin haka ,!    Da rarrafe ta jawo jakar kayan ta ta fiddo da duk kayayyakin ta zaƙulo damin kuɗin ta , ta fidda naira dubu ɗaya ta bayar a anso mata magani ,! Ta koma ta kwanta gami da runtse idanun ta !    Da kan ta larki ta je ta amso mata magungunan saboda ta hango moriya , ta kuma ƙulla abunda ta ƙudurta cikin ran ta ," Ta tsaya a wani ɗan shago ta sayo mata ruwan leda guda biyu ! Lamoo ! ta samu yakaka tana sauraran gangar jikin ta ,"    Ta taimaka mata ta zauna tare da ɓalla mata maganin ta miƙa mata ruwan ta kora , ta koma ta kwanta cikin wani sabon yanayin rashin kuzari da take jin kan ta a ciki . Larki ta ɗan saci kallon jakar kayan yakaka , ta gan ta a buɗe yadda ta bar ta bayan ta miƙo mata kuɗin ! Yaks bari na tattara miki kayan naki , ai ba'a bar kayan haka ba ko dan gudun masu dogayen hannu kin san ɗakin namu babu tsaro ,' , Idon ta a rufe ta ɗan gƴaɗa kan ta ,! Da azama larki tayi wa jakar kayan rumfa ta bada baya ga yakaka wacce idanun ta ke rufe ,"      Kayan ta fara mayarwa bayan ta wawuso kusan rabin kuɗin da yake cikin jakar ta chusa a lalitar ta ,"   A ranta tana cewa ! To meye ? Ta san yarinyar sabuwar hannun ce dan haka tana kan ganiyar ta , dan ƴan waɗannan kudaɗen ba kome bane a wurin ta , ƙila ma bata san yawan su ba daga ta shafa ta ji sun ragu , fita zata sake yi wurin masu bata ta sake samo wasu , Dan haka gwara itama ta samu ta wawushe nata , ko ta samu ta kashe wasu matsalolin ta,  ta kuma  farfaɗo da jarin ta na goro da taba ! Da wannan zancen zucin ta kammala maida kayan tsaf ! Ta juyo da kallon ta kan yakaka domin ta sanar da ita ," Sai taga bacci ma take da alama ta samu lafawar ciwon ! Tura jakar tayi inda suke ajiye ta cikin ranta tana ayyana ta samu hujjar da zata kare kan ta ko da ace yaks tayi cigiyar kuɗin ta ," cewa zata yi bata san wanda ya ɗauka ba ita dai ta gyara mata kayan ta fita ,! Sai bayan la'asar yakaka ta farka ! Daga baccin da yake cike da mafarkin biyamuradi da soyayyar sa da ta maƙale mata a zuci !  Watsa ruwa tayi tayo alwala , ta haɗa sallolin azahar da la'asar tayi su , Tsumu tayi a zaune kan ɗankwalin ta da ta shimfiɗa tayi sallah bisa ,  ta rasa abun da ke mata daɗi . Babu laifi taji sauƙin ciwon cikin sai dai sakayau take jin ta ga wani irin ƙuncin zuciya da take ji uwa uba kewa tare da ƙaunar youssouf da take tokarin ta a duk bayan daƙiƙa guda wanda ko da wannan aka bar ta kawai ya isheta cuta ! Ji take kamar ta shekara da barin ganin sa haka ta shafe tsawon daren jiya tana jin kewar sa ta gaza bacci sai juye-juye , Cikin sati biyu kachal da suka yi tare da juna ya mata mugun sabo da soyayyar sa mai tsayawa a zuci , duk da cewa soyayyar ba da baki yake ambato mata ba , a aikace yake idar mata , shiyasa gaba ɗaya take jin kewar sa hatta a fatar jikin ta da kowanne saƙo da lungu na jikin ta ,! Har gizo hannuwan sa ke yi mata a sassan jikin ta ,' ko yaya ta rufe idanun ta fuskar sa take gani tana mata gizo , shi ba ma'abocin murmushi agare ta bane , amma yanayin kamammiyar fuskar sa yana bala'in burge ta , babu shakka a rayuwar ta bata taɓa ganin mutum ɗan gayu mai kyau irin sa ba ! Yunwa take ji domin rabon ta da abinci tun karin safe ," sai dai kallo ɗaya tayi wa robar abincin ta da take ajiye a gefe wanda take da tabbacin wake da shinkafa ne a ciki ta ɗauke kai , ' abinci daddaɗa bakin ta yake kwaɗayi !    Jakar ta ta jawo domin ta ɗauki kuɗi taje sayan abinci wurin su kolo Kallo ɗaya tayi wa kuɗin tasan an taɓa su , da azama ta fiddo su ta ƙirga ta ga dubu goma sha bakwai ne a maimakon dubu talatin da huɗu,! Jujjuya kuɗin take idanun ta sun ciko da ƙwalla , tana da buri akan kuɗin , so tayi ta kai falmata babban asibitin ido a duba ta domin kwana biyu idon yana ɗan matsa mata da ƙaiƙayi kuma suna yin jaa , cikin ran ta bata fidda rai watarana falmata zata gani da idanun ta ba , ji take watarana falmata zata ga hasken da yake wadace cikin sarari duniya , watarana zata ga fuskokin jama'a , zata ga fuskar ta kamar yadda kullum ita take ganin ta ! , sannan idan kuɗin ya rage ta jaa jari ta fara soya doya da kwai da yammaci zuwa dare , kafin dawowar bature kam silum domin ta ɗanɗani daɗin kuɗi da ƴancin da suke samarwa ga mai su ! Baza ta iya sake zama irin na tsananin talauci tare da walaƙancin da ake musu sanadin babu ba !  idan ya so sa dunga raba ribar tare da madam saly , ta san baza ta ƙi ba !, Amma shine wani azzalumin marar imani ya kwashe mata kuɗin ?! Tunanin larki ya faɗo mata arai , ko ita ce ta ɗauka ? Amma larki anya zata ɗauki kuɗin ta ? Koma waye na bar shi da Allah ! Ban yafe ba .    Ta furta hakan a sarari tana share guntuwar ƙwallar ta , ta zari naira dubu ɗaya , a ranta tana tunanin chanjin ta da ya rage hannun larki , bata ,  bata ba ko maganin na dubu ɗaya ɗin ne ? Ita dai baza ta tambaye ta ba idan ma ta cuce ta dan kan ta ! ¿ Kai tsaye ta wuce rumfar su kolo , ta miƙa kuɗin tace a bata tuwon shinkafa da miyar yakuwa , malmala biyu da nama guda huɗu , Kolo ta miƙo mata tuwon a naɗe cikin leda tare da miyar a wani ɗan kwanon roba bayan ta gargaɗe ta akan ta dawo musu da kwanon miyar  ! Kai tsaye wurin wanke wanken falmata ta wuce , ta tadda ta wanke-wanken sun taru tana ta faman wankewa ana ƙaro wasu , saboda yamma tayi lokacin ciniki ne kuma an kusa gama sayarwa ! Alamun gajiya ya bayyana a gare ta ,ga gumi da ta haɗa fiye da rabin zanen ta a jiƙe yake da ruwan wanke-wanken! Ajiye abincin hannun ta tayi a gefe ! Cikin ruwan kumfan ta sa hannu gami da zare soson daga hannun falmatan ,       Kawo nayi sauri na gama , kin ci abinci falmata ?? Da murmushi a fuskar ta ta cire hannun ta a ruwan gami da goge hannun ta a jikin rigar ta ,'     Ban ci ba yakaka , kin ga aikin yayi yawa wanke wanken ina yi ana ƙaro wasu ,"     Amma yanzu zan samu nayi sallah sai na ci ,"     Da ido kawai yakaka ta bita lokacin da ta matsa jikin fanfo ta fara alwala ,"    Ɗan kwalin ta ta shinfiɗa tayi sallar azahar da la'asar akai , bayan ta idar , tace yakaka ta bata abincin ta ,da ta rufe shi da faranti a gefe ,"    sai lokacin yakaka ta lura da yasashiyar robar abincin falmata da take buɗe , ɗaukar robar tayi tana kallon abincin da ana gani an san ƙarshen tukunya ne ƙanzo-ƙanzo ,babu wani mai da yaji na kirki cincirindon ƙudajen da suka tashi daga kan abinci ya sa ba shiri yakaka ta juye shi a bakin makwarari ta wanke robar ta ɗauraye , Ta ɗauko malmalar ɗaya ta sawa falmata ta sake gutsuro rabi ta ƙara mata ta juye mata fiye da rabin miyar , ta kai mata tuwon gaban ta ,' tare da taro mata ruwa a kofi daga bakin fanfo , ita ma ta zauna daga gefe tana cin guntun tuwon ! Suna ƴar taɓa hirar su kamar yadda falmata take so , cikin hirar su take sanar da ita ta shirya gobe zata kai ta ita ma a wanke mata kan ta tare da yi mata kitso ! Bayan sati biyu Rayuwa tayi wa yakaka tsanani wanda ba kome ya jawo hakan ba sai rashin  bature kam silum , domin cikin satin biyun da suka biyo bayan ranar haɗuwar su ta ƙarshe , kamar yadda samy baby ta alƙawarta mata zata nemo mata shi ta wurin abokin sa ,!   Ta je barracks ɗin sai dai bata tarar da shi Colonel nuhu ba, an tabbatar mata da ya tafi bakin aiki ,! Wanda hakan sam bai mata daɗi ba kuma ta kirayi duk numbobin sa basa tafiya ta rasa dalilin haka ! ? Zuwan ta daban-daban uku bata samun sa , dan haka ta ɗan tsahirta .tare da cigaba da lallaɓar yakaka wacce ta lura tayi zurfi cikin mahaukaciyar soyayyar mutumin da a yanzu take hasashen yayi wa yakaka nisa , sai dai a nemo madadin sa ! Wanda bata ga alamun samun haɗin kan yakaka wurin nemo madadin na sa ba ! , babu ranar da yakaka bata kuka akan soyayyar bature kam silum , ɗakin samy baby nan ne wurin fakewar ta ta sha kukan ta domin ita tasan matsalar ta ita tasan dalilin kukan ta , kuma ita take zaton zata iya share mata hawaye , sai dai a yanzu labarin ya sha banban kuma wankin hula na neman kai su dare ,! A yau yakaka ta tashi bata da ko sisi domin satin da ya wuce ta kai falmata asibitin ido da kuɗaɗen hannun ta inda kuɗin magunguna da wasu aune-aune , ya lashe fiye da naira dubu takwas , a cikin sauran dubu goma sha biyu da ƴan kai da suka rage mata , Da sauran kuɗin tayi amfani wurin cigaba da hididimun yau da kullum , musamman abinci wanda shine kan gaba wurin lashe mata ƴan kudaɗen domin kwanan nan ta tsinci kan ta cikin wani irin bala'in kwaɗayi , bata iya cin abincin da bai wadatu da kayayyakin ƙawata girki ba , bata kuma cin abinci babu nama sannan a rana bata sha lemon kwalba "pepsi " ba tasha guda uku safe rana dare ,' idan kuwa bata sha ba babu zaman lafiya wani iri bala'in yunwa mai tafe da tashin hankali zata dunga ji ," Da haka kuɗaɗen hannun ta tas suka ƙare ! Duk da tarin damuwar da take cin ta cikin rai , kallo ɗaya za'a mata a gane ta sauya , ta sake fari har tana ɗaukar ido ta cika tayi luwai-luwai kyaun idanun ta kamar gilashi sun sake haskaka ,! Tana zuwa wuri take ɗaukar hankalin jama'ah . Ture jakar kayan tayi gefe ta ƙarasa bajewa ta zauna daga durƙuson da tayi ta tallafe kumatun ta da hannu, wannan shine karo na uku tana chaje cikin kayan ta a safiyar yau ko Allah zai sa tayi gamdakatar da wani makararren chanji , sai dai koh alamar kuɗi bata gani ba idan aka ɗauke kuɗin sefa ,"niger", wanda basu da wani maraba da babu a wurin ta ," A hankali ta miƙe tana haɗa hanya saboda wata azababbiyar yunwar da take wuji-wuji da ƴaƴan hanjin ta ,' Ɗakin samy baby tayi wa tsinke ,'   Saɓanin zaton da tayi zata tadda ta tana bacci ta jira tashin ta , sai ta tarad da ita tayi shiri tsaf , tana zaune bakin gado tana shirya kayan ta cikin ƴar jaka ta matafiya ! Gaishe ta tayi cikin ladabi ! Yauwa yaks daman yanzu nake son na tura a ƙira min ke , tafiya ta taso min jiya-jiya cikin dare Honourable yake sanar min zamu yi tafiya tare da shi

Chapter 22 of 103