kwanaki biyar da tafiyar mu sai direba ya ɗaukota daga Nigeria ,
"To Allah ya kaimu ,
****
Wasa gaske cikin 'Yan kwanakin Youssouf ya gaza samun kwanciyar hankali tsoro ne cike taf a ransa , duk kuwa da cewa babu wanda ya sake neman sa kan wani batu sai dai yana tsoro ne kar ko tana ƙasa tana dabo .
Falmata har ta gaji da tambayar sa akan yadda ya zama koyaushe cikin tunani babu nutsuwar kirki , 'yar soyayyar da yake gwada mata mai sanyi da shiga zuci duk ya rage a wasu lokutan ma raba dare yake tunani , da juye-juye ,
Kasantuwar daman ita mace ce marar hayaniya mai kammalewa sai bata tsananta shisshige masa ba ta ɗan janye jikinta itama ta maida hankalinta baki ɗaya kan Mama ,
da kuma fama da kanta da take yi saboda wani ciwon kai marar daɗi da yake addabar ta tare da bugun zuciya fiye da ƙima duk tayi wata 'yar hidima sai ta ji mummunar gajiya da bugun numfashi sun taso mata ,
Mama da kanta ta san cewa Babanta ya rage kula da dararrakin ta sosai saboda duk ta dame shi zai samu ya zameta ya shiga ɗaki ya rufe ,
Ya rage sati biyu tafiyar su da ya ke tsawon kwanaki kusan goma da yin wayar sa da Tafeeda , wanda duk yadda ya so ya samu damar da zasu sake yin wata magana , Tafeedan yaƙi ba shi haɗin kai idan ya ƙira wayar sa ba bai ɗauka saƙonnin sa kuwa ya tura su babu adadi ta kan yanar gizo da kai tsaye ta hanyar saƙon karta kwana , nan ma ga shaidar an karanta sako amma babu amsa , dan haka shima ya zuciya ya daina neman sa .
Ya fito wanka da safe ya tarar da miss call ɗin Tafeeda , da hanzari ya ɗau wayar bai ko tsaya shafa mai ya sanya kaya ba ya ɗau wayar ya shiga neman layin sa ,
Sai dai kakarun Amai da ya jiyo daga Falon su ya sanya shi sauƙe wayar daga kunnen sa ba tare da ya kashe wayar ba ya fito falon hankalinsa a tashe ya ƙaraso ga Falmata wacce take durƙushe daga ƙofar kitchen ɗin su tana Amai ,
Da hanzari ya ƙaraso wajen ya riƙo ta zuwa jikin sa bayan ya ajiye wayar sa a ƙasa da aka riga aka ɗaga kiran daga ɗaya ɓangaren ba tare da ya sani ba ,
"qu'est-ce qui ne va pas avec toi chérie, es-tu malade? ( me yake damun ki ? Baki da lafiya ne ? )
Bata amsa ba illa yunƙurin Aman da ta cigaba da yi duk kuwa da babu kome a cikin nata ,
Shafa bayanta ya shiga yi yana ɗan bubbugawa tare da jero mata sannu ,
Mama wacce tashin ta kenan daga bacci ta jiyo muryar su ta fito , itama ta tsaya tana kallon su fuskar ɗauke da alhini da 'yar muryar tace
"Papa qu'est-ce qui ne va pas avec Mamma ?
"Princess Maman ki bata da lafiya ne, dauko min papier mouchoir dagga ɗaki na goge mata baki ,
"To ,
Ta juya da ɗan gudu zuwa ɗakin su ,
"Sannu Fatima ,
Yace cike da tausayawa ,
Daga can ɓangaren Hawaye masu ɗumi suka silmiyo daga idanun Hajiya Umma , ta zare wayar Tafeeda daga kunnen ta tare da miƙa masa wayar ,
Karɓar wayar yayi ya duba wayar yaga ba'a katse ta ba dan haka cike da tashin hankali ya kara a kunnen sa yana fargabar ko wani abu ne ya faru da Youssouf ɗin ,
Sai dai ya ƙarashi Maganar sa bai ji Youssouf ɗin ya amsa ba , sai muryar wata mace yake ji ƙasa-ƙasa , dan haka ya katse wayar waigo ga Hajiya Umma ,
"Umma Lafiya Yarima yake kou ?
"babu shakka lafiya yake ,
ta amsa da wata irin murya ,
Ganin yanayin ta ya sa Tafeeda miƙewa yayi mata sallama zuciyar sa cike da tunanin meye haka Youssouf ya faɗi wanda ya sa Hajiya Umma ƙwalla ?
Shi daman zouwa yayi ya gaishe ta tare da cigaba da kwantar mata da hankali bayan tashin hankalin da ta shiga a kwanaki sakamakon wani Al'amari mai girma da ya taso game da Youssouf ɗin ,
wanda shi yayi tsayuwar daka wajen ganin lamarin ya dai-daita da a yanzu yake mataki na ƙarshe na gyara kome wanda kuwa hakan ba zai samu ba sai da haɗin kan Youssouf ɗin ,
tunanin ko zai yadda da lamarin da zai je masa da shi a matsayin shawara ko ba zai yadda ba ya sanya shi yin jinkiri yana nazari dan haka nema yaƙi yarda suyi magana da Youssouf ɗin
Sai fa yau da Hajiya Umma ta sa ya ƙira sa a gabanta ta warware masa labarin mummunan ƙullin da aka so yi masa ,
Sai kuma ya ga Umma ta ƙare wayar ba tare da ta ce kome ba sai ƙwalla , lamarin da ya ƙulle masa kai kenan , koma menene zai ƙira Youssouf ɗin ya ji .
A ɓangaren Su Youssouf bayan Falmata ta gama Amai ya gyara wajen ya ɗau wayarsa bai lura da Shaidar an ɗaga ƙiransa ba saboda hankalinsa da yake kan Falmata wacce sai numfarfashi take saboda ƙaruwar bugun zuciyar ta tare da ciwon kai da ya haɗu mata ,
Ko sannu da Youssouf yake yi mata da kyar take amsawa ,
"Fatima ko mu tahi hospitalisé ne ?
Jikin ta babu kuzari ta gyada kai ,
Cikin hanzari ya shiga ya shirya ya wankewa Mama jiki tare da goge mata baki , ya dawo ya tarar da ita tana baccin zomo ,
"Fatima mu je ki shirya ,
Shi da kansa ya taya ta ta gyara jikinta yana riƙe da hannun ta suka fito
" za ki iya tafiya da kan ki ko kuwa na ƙira taxi ,
"zan iya tafiya ,
Basu sha wata wahala ba kasantuwar daman tana kan ziyartar likita , dan haka suka samu ganin likitan ta inda shi kuma bayan tambayoyin da yayi mata da duk bayanan da ta ba shi , ya miƙa su ga wata likita daban , wacce ta sake yi mata tambayoyi ,
Daga haka ta yi mata gwaji , bayan bayyanar sakamako ,
da fara'a likitar take miƙa musu sakon taya murnar cewa Falmata tana ɗauke da ciki na tsawon sati huɗu ,
Duk da cewa Falmata tana jin yaren faransanci babu laifi , Amma a yau ji tayi sam bata Fahimci me likitar ke nufi ba , tamkar ta manta ma'anar kalmar ,
Sai da ta ga Biyamuradi Youssouf ya rungume ta , yana bayyana farin-cikin sa da lokaci guda Albishirin da likitar tayi masa ya wanke masa zuciya tare da yin awun gaba da duk wata damuwa tasa , "Ya'ya ai arziƙi ne .
"Fatima Tu es enceinte, tu portes mon bébé , Alhamdulillah
Ya ɗago fuskar ta ya sumbanci goshin ta ,
Hannunta ta kai kan nasa hannun da yake tallafe da kumatun ta , kyawawan idanun ta na bayyana farin-cikin dake maƙare da zuciyar da
"Baban Mama da gaske ina da ciki ? Zan haifi jariri daga cikina Mama Zata samu dan uwa , Mama zata wa....
Katse ta yayi ta hanya ɗora laɓɓansa akan nata ya sumbace ta ,
"Mama da Yumna zasu samu ɗan ouwa ko ƴar ouwa insha Allah nayi Farin-ciki Fatima .
Mama da take tsaye tana kallon su ba tare da ta san me suke yiwa murna ba , sai ita ma ta sa dariya ta taho ta rungumo su ,
Hannuwansa ya sa ya zagaye a jikinsa yana jin waɗannan rayukan guda biyu sun zama wani ɓangare na daga rayuwar sa ,
Da wannan farin-cikin me tarin yawa suka baro asibitin zuwa gida , bayan likita ta basu shawarwari tare da 'yan magungunan da zasu taimaka a matakin farko na zaman ciki .
Falmata Ji take babu wata rana da take kai wannan ranar farin-ciki a wajen ta , minti kaɗan zata kai hannu ta shafi cikin ta , farin-cikin ta biyu ne ,
Tana ganin cewa lokacin warkewar Mama yayi tunda gata ɗauke da ciki ,
Da shigowarsu gida wayar sa tayi ƙara Tafeeda ne ya sake ƙiran farin-cikin sa bai ɓuya ba a muryar sa suka gaisa da Tafeeda ,
Kafin Tafeeda ya ɗora da cewa ,
"Yarima magana nake so muyi kou ka bani dama ?
Jin haka sai ya miƙe daga jikin Falmata ya fita zuwa 'yar barandar gaban gidan ,
"ɗan ouwa na baka dama faɗi ina jin ka ,
Yace masa a taƙaice ,
"Magana ce zamu yi game da lamarin yarinyar nan da kake boyen sa gareni tsawon wannan shekaru , na riga nasan koume kan zaman ka tare da su da amren innan ita yarinyar da kake har gidan da kun ka tare a Niamey na shina Yarima ,
"To munin Al'amarin ba dagga gareni yake ba , sai fa dagga maƙiya waɗanda sunka dunga bin lamarinka , a cikin binciken da nai kai tamkar da sanya hannun su kome da ya faru ya kai ga faruwa ,
"Lamari ya munana ta inda zance ya taho ga Fada ya iske kunnen Maimartaba da Hajiya Umma bai tsaya nan ba har sai da ya iske mutanen cikin Fada baki ɗai ba'a kouma san waye ya fiddo maganar ba ,
"cewa Yariman Maraɗi yana da ɗiyar banza bata Amre ba , tare da yin zaman banza da Mahaifiyar ta zaman dadiro , tun dagga Nigeria ,
"Yarima nayi duk bakin ƙoƙarina wajen ganin anbi daddigin masu yaɗa maganar nan an dakile bazuwar ta , kouma anyi nasara ,sannan na ƙaryata batun gaban moutanen cikin fada tare da Maimartaba ,
"Amma nasan wannan yunƙuri nawa ai bai isa ba ya kawo ƙarshen maganar nan tunda kouwa akwai ta da gaskiya , maƙiya ba za su bar lamarin nan ba .
"Menene mafita a yanzou ?
Youssouf ya katse dogon bayanin da Tafeeda ke yi masa ,cikin miƙa wuya
'Mafita gouda ce ,ka rabu da ita wannan yarinyar da kake amre , ka sallame su su tafi tare da ɗiyar nan ,
"ka rabou da ita domin tsarkake kan ka dagga zargin al'umma ,tare da aibatawa ,
"ka rabou da ita domin tsira da mutuncin tare da ƙimar ka ,
"ka rabou da ita doumin gujewa russa alaƙar ka da iyaye da 'yan ouwan ka ,
"ka rabou da ita doumin gujewa samar da bakin-ciki a zuciyar Mahaifiyar ka ,
"ka rabou da ita domin gudun samun galabar maƙiya a kan ka ,
"ka rabou da ita domin tsarkake masarautar ku tare da kaiwa ga matakin nasarar zama sarkin maraɗi a watarana .
"ka nesanta kan ka daga wannan ɗiya da innarta doumin tsallake ramin maƙiya , muddin ka ƙiya ? Za ka gamou da dariyar maƙiya da baƙin-cikin iyayen ka .
"cigaba da zama da itta yana nufin rassa kowa tare da kai ciki kouwa har da ni kaina .
"Tafeeda ,
Youssouf ya ƙira shi da wata irin murya mai cike da tashin hankali ,
"Yarima shawara ce ni na baka zaɓi yana dagga gare ka , ni na barka lafiya ,
Wani iri yake ji tamkar an zare masa laka , menene yake shirin Faruwa da rayuwarsa ne ?
Kalmar Rabuwa da Fatima tayi masa nawin saurara ko a kunne kawai ,
To amma kuma shi ya zai yi ne? Ji yake kamar an raɓa ƙwaƙwalwarsa da duk wata tunani .
Cigaba yayi da tsayuwa a wajen ya gaza motsawa
Hannuwan ta ya ji sun ratsa kirjin sa daga bayan sa ta rungume shi , tare da kwantar da kan ta a bayan sa ,
Cikin sanyin muryar ta tace
"Baban Mama tun ɗazu nake jiran ka , kazo muyi Sallah mu godewa Allah , akan wannan babban arziƙi da ya bamu .
Hannu ya kai ya zagayo da ita ta gaban shi ,
Kallon fuskarta da take ɗauke da tsantsar farin-ciki yayi , suɓul da ita sai ƙyalli take tare da wani irin haske na musamman da ta ƙara a 'yan kwanakin nan,
Ji yayi tsikar jikinsa ta tashi dawowar kalaman Tafeeda cikin kunnuwan sa yasa jinin jikin sa tsinkewa ,
"Fatima ina son ki dayawa , je t'aime tellement Fatima
Yace da wata irin murya lokacin da yake rungumeta tsam a jikin sa , yana fidda ajiyar zuciya a zahiri .
Ji tayi riƙon da yayi mata yayi tsanani da kyar take fidda numfashi , dan haka ta motsa da kyar ,
"Baban Mama mu shiga ciki na zauna ,
Tana jikinsa suka taka zuwa cikin gidan ya zaunar da ita akan kujera , amma shi ya gagara zaman saboda tashin hankalin da yake ciki ,
"Baban Mama ...
"Fatima ku zauna a gida ke da Mama ku jiraye ni zan fita na sayo mana abubuwan buƙatu kadan yanzu nake dawouwa da gaugawa ba zan daɗe ba kin ji kou ?
A sanyaye ta amsa da "to , tana gyaɗa kai ,
Daga haka ya juya ya fita , ba tare da ya san inda zai tafi ba , kawai so yake ya zama shi kaɗai bai san ɗanɗanon shakuɗuwar farin-ciki da baƙin-ciki a lokaci guda ba sai yau ,
Bai san girma da tsoron da yake cikin rasa abunda kake so ba sai yau da layi yake shirin shatuwa tsakanin sa da abubuwa biyu mafiya soyuwa agare shi ,
Bai san da irin wannan tashin hankalin da yake sa ɗimuwa ba sai da ya tsinci kan sa can nesa da unguwar da yake ba tare da ya sani ba ,
Tsayuwa yayi a ƙarƙashin Doguwar bishiyar (Pinus taeda) da duk ganyayyakin ta suka gama zubewa saboda sanyi ,
Hannun sa ya zira a aljihun rigar sanyin jikin sa cikin rashin sanin makomar rayuwar sa ,
Waye zai tallafa masa ya fahimce shi ? Tayaya zai yi bayani a fahimce shi cewa kome da ya faru gare shi ya faru ne bisa ruɗin shaidan da kaddara maigirma , kaddarar haihuwar Mama da Auren Fatima ?
Waye zai faɗawa ya saurare shi cewa Fatima ta riga ta zama mahaɗi na cikamakin farin-cikin rayuwar sa ?
Mama ɗiya ce jini daga cikin jinin jikin sa dake gudana ,ta yaya zai iya tsame ƙwayar jinin sa daga jikin sa ?
" daga gefe ya hango wani brewery ( wajen sayar da giya ) ya tsallaka ya shiga wajen ya zauna , akan ɗaya daga cikin kujerun gurin , ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ta zo da tare da gaishe shi ,
Kan sa yana kallon teburin gaban sa ya ce mata
Please bring a bottle .
bata tafi ba ta fara lissafo masa sunayen giyar da suke da ita, ya katse ta ,
Bud Light
Bata jima da sai gata ɗauke da kwalbar giyar da ya buƙata da ɗan kofin gilashi , tare da farfasassun ƙanƙara cikin wani ɗan mazubi na gilashi .
Tsirawa kwalbar ido yayi yana jin ƙaruwar damuwar sa da yake zaton idan ya kurɓa giyar zata gusar masa da wannan damuwar , da rabon sa ya sha ya kai wasu shekaru ,
Ɓincine bakin yayi ya tsiyaya a kofin , tunani ya shiga yi irin nacin addu'a da ya dunga yi akan Allah ya nufe shi da daina shan giya , da ƙarfin addu'a da tirjiyar da yake yiwa shaidan aduk lokacin da ya ji jarabar son shan giyar, ya samu nasarar daina sha sam
Yau sanadin damuwar da giyar ce ta zama sanadin faɗawar sa domin ita ce sanadin kome gata a hannun sa yana son sake sha , wataƙila masifar da zata iya sake jefa shi ciki sai yafi wanda yake ciki s yanzu
Ajiye kofin yayi ya miƙe zumbur ! tamkar ya ga abun tsoro , istigfar ya shiga yi a zuciyar sa ,
Da hanzari ya zaro kuɗaɗen da bai san adadin su ba ya ajiye akan teburin ya kama hanyar barin shagon , zuciyar sa na tsananta bugawa ,
Ya kama hanyar komawa gida yana sake zurfafa a tunani ƙwarai yana buƙatar wani babba a cikin lamarin sa da Fatima , waye zai tintiɓa ?
Hajja , ita tafi kowa kusanci da Fatima a halin yanzu , yana buƙatar suyi magana shi da ita , ko ita zata fahimce shi ?
Wayar sa ya zaro daga aljihu ya shiga neman layinta , ƙira ɗaya-biyu ta ɗauka suka gaisa , tana tambayar sa su Falmata da Mama ?
Ya amsa mata da duk suna lafiya , sai kuma ya gaza fayyace mata cikin sa kamar yadda yayi niyya to ta ina zai fara ƙiran kan sa da mazinaci ? Kai bafa zai iya ba
"Hajja ki fara shiri idan Allah ya kaimou nan da sati mai zuwa direba zai zou ku taho Niger mouna dawowa nan da kwanaki goma sha huɗu
Daga ɓangaren Hajja ta amsa da murnar jin zasu dawo ta san an samu nasarar abunda aka je nema kenan .
"Babu kome Babban soja zan yi shiri kafin ranar nayi sallama da yan uwa ,
"Nagode Hajja , zai zo miki da sakon da za ki bawa dangi ki kuma sayi abun buƙatar da kike so kafin ku taso ,
"Har da wahala kuma Haba ? To madallah nagode , nagode Babban soja ,
Suka yi sallama ta ajiye wayar , Yakaka wacce tare suke da hajja a kitchen suna hidimar girkin dare, da duk hankalin ta ke kan zancen Hajja da ta ji tace zata tafi , ta ɗan matso kusa da ita ,
"Hajja tafiya ce ta kama ki ne ?
A kaikaice Hajja ta dube ta kafin ta cigaba da kaɗa miyar da take yi ,
"Eh Uwarɗakina Falmata ce zasu dawo daga Amurka , zan koma cikin sati mai kamawa , na gyara gidan kafin su iso ,
"Hajja nima zan je , zan biki na ga Falmata na , zan nemi izni wajen Baba .
Ba tare da ta jira amsar da hajja zata bata ba ta fita da saurin gaske , zuciyar ta maƙare da tasowar binannen bakin-cikin ta , lokaci ya matso na raba tsakanin ƙanwar ta , tare da ƴar ta, da wannan mugun mutumin , mayaudari .
Assalamu alaikum ,
Da fatan duk kuna lafiya ? Nasan kun yi mamaki ko ? Haaaa , ina masu cewa sai wani watan zasu ga sabon update ?ha'aan kun ji kunya ko ? 😂
To ƙaƙa ƙara ƙaƙa ? Yau ina son jin ra'ayoyin ku pls ,
A gaskiya ghost readers sake bunƙasa kuke yi amma ba kome liti bad boy yana madakata shi da Hajja suna jiran ku 😂
Nagode .
[11/22, 12:05 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
40
Cikin sa'a da Yakaka ta nemi izni wajen Prof kan ta bi Hajja zuwa wajen 'yar uwarta sai Prof bai hana ta ba , sanin cewa da yayi haƙiƙa akwai buƙatar su ga juna ita da 'yar uwar ta .
Sai dai yayi mata jirwaye da kamar wanka , ya yi mata nasiha tare da jaan kunnen , a ƙarshe ya gindaya sharadin kar ta wuce kwanaki goma zuwa sati biyu a Niger ɗin ta dawo gida nan wajen sa ,
Cike da ɗokin sake ɗaura idanunta akan Halittun biyu mafiya soyuwa agareta ta fara shiri, duk wasu 'yan kuɗaɗen da take da su irin wanda Prof yake ba ta da wanda Rahima ke mata kyautar su da suka tasamma dubu goma sha biyar duk ta tattara su ta ƙulle ta nufi kasuwa ,
Sayayya ta shiga yi gefe guda na zuciyar ta na cigaba da saƙe-saƙen irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Youssouf ,
Daga Jiya zuwa yau, iyakar tunanin ta kan matakin da take ji zata iya ɗauka ya ƙare ne akan kawai abu mafi sauƙi shine ,
Idan Har sun hadu zata ce da shi, ya saki ƙanwar ta ya kuma bata 'yar ta , ko kuwa ta kai lamarin gaban iyayen sa , waɗanda ta riga ta san ko su , su waye ? ta san cewa shi ɗan sarki ne tun a lokacin da Samy Baby ta goranta mata akan sa ,
Ta san wannan ce kaɗai madogarar ta , idan har ba haka ba ai ita bata isa jaa da shi ba .
Tana da tabbacin ba zai yarda asirin da yake tsakanin sa da ita ya tonu ba da ta riga ta san ya ɓoyewa mutane dayawa ciki kuwa har da Falmata ,
ita kuma ta shirya sanar da ita gaskiyar kome da ya faru tsakanin su da Youssouf ɗin, ta tabbatar daga lokacin da Falmata ta san kome baza ta sake yarda da shi a matsayin Miji ba , za kuma ta taya ta su ƙwato Mama suyi dawowar su nan.
Da tunanin hakan ta ƙaraso wajen sayar da Takalman mata da yara irin na roba masu sauƙin kuɗi ,
Tafi son ta saya musu 'yan kayan sanyawa a jiki musamman dayake bata san yaya rabuwar ta su da shi Mayaudarin zai kasance ba ,
wataƙila suyi irin rabuwar da yayi da ita a baya , watau ya yasar su akan titi babu ko suturun kirki ya kora su .
Dan haka ya zama dole ta yi musu guzurin kaya daga Falmatan Har Mama .
Daga wajen 'yan takalman inda ta ɗauka musu ƙafa bibbiyu duk da cewa kintata tayi ta auna girman ƙafafun su a tunanin ta ,
Sai ta nufi wajen 'yan kayan yara , nan ma ta auna da girman Mama da ta gani a hoto ta saya mata shiga biyu masu sauƙin kuɗi ,
Ƙaunar Falmata ga Ƙuli-ƙuli mai sugar , ta tuno dan haka ta je ta saya mata shi na ɗari uku fal cikin ƙaramar baƙar leda ta ɗaure ,
Ba zata yi wasa da kuɗin ba saboda guzuri sanin da tayi basu da inda zasu samu kuɗin mota a Niger idan suka yi rabuwar baram-baram da Youssouf .
Ko da haka ta kasance wataƙila baza su shiga matsala mai yawa ba kuɗin hannun ta zai isa dawo da su Nigeria .
*****
Kwanakin da suka biyo duk tayi su cikin ɗokin zuwan ranar tafiyar su ne , daga Rahima har Hajja sun fara gajiya da sabanbatun ɗakin da Yakaka take musu daga sun zauna .
Ta ƙira Malama Maryam ma ta sanar da ita , inda ita ma dai Nasihar ce ta ɗora mata bayan ta mata addu'o'in kariya , daga nan ta ƙira Lubna wacce ta gama fushin ta har ta huce akan rashin zuwa auren ta da tayi , murna sosai Lubna ta yi mata tare da addu'ar dawowa Lafiya .
Ta so ta je ta yiwa Amnee Sallama amma Amnee sun yi tafiya tun wajen sati uku da suka wuce ita da Ƙanwar ta Khaalty Rahima ,
Wacce aka ce ta dawo , duk da cewa bata samu damar ganin ta ba , amma tayi murna ƙwarai da dawowar ta , har ma tayi fatan ina dai su ma Allah zai dawo musu da Mamar su haka watarana ?
Sai dai ta ji tausayin ta saboda yadda Rahima take bata labari ta sha wahalar rayuwa sosai har ta ƙurumce dan haka ne ma suka tafi jahar Lagos inda za ta ga wani Babban likitan kunne a wani shahararen asibitin cutar da ta shafi kunne zuwa maƙoro dake jahar Lagos ɗin ,
A yadda Rahima ta shaida mata daga zarar sun dawo , za su dawo nan gidan ne ita da Amnee baki ɗaya inshaAllah ,
Duk da bata san me ya raba Amne da gidan ba , amma tayi murna sosai da ta ji cewa zata dawo , saboda irin ƙaunar da take nuna mata ,
***
Babu irin gargaɗi a fakaice da Hajja bata yi mata ba , tare da hannun ka mai-sanda akan kar dai fa ta je da zummar ƙulla wani mugun abu.
Har 'yar nasiha ta dunga yi mata akan ta rungumi kaddarar ta , ta haƙura Allah zai kawo mata wani Mijin
Sai dai kasancewar ta ba mai yawan magana ba ya sa bata tankawa Hajja har ta yi ta gama zantukan ta da ta ɗauke su a sowar biri .
Amma cikin ranta ta kan yi mamakin Hajja a lokuta da dama , ƙarfin halin ta kuma na bata haushi , wacece Hajja ? Yaushe ta shigo Rayuwar su ita da Falmata ? Shin wai zato take ta fi ta ƙaunar Falmata ne
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 65 Chapter of 103