ne ga lafiyar abinda ke cikin ta .
Nan take ya fara ƙoƙarin bata agajin gaugawa sai dai bisa tilas ya shirya ta suka nufi asibiti saboda fahimta da yayi cewa dole abinda ke cikin ta da bai yi ƙwari ba sai ya fita saboda bakin mahaifar ya riga ya buɗe jini ya fara sauƙa.
A can babban asibiti na ƙasa da yake aiki suka mata abinda duk ya dace kafin a mata allurar bacci na ɗan wani gajeran lokaci da ana sa ran idan ta farka firgicin da take ciki ya bar ta .
Zama yayi akan kujera yana riƙe da hannun ta ya zubawa fuskar ta ido a can cikin ransa kuwa lamarin Sofi ke daɗa sanya shi a ruɗani a bayan kowacce daƙiƙa yadda yake jin kome kamar a mafarki
Wai Sofi ta aikata duk abubuwan da ta lissafa da bakin ta.? Ga kuma ƙwaƙƙwarar shaida nan tana yunƙurin kashe masa Mata da ba domin Allah ya kawo shi ba da babu shakka Wafaa bata raye yanzu a duniya .
Sake runtse hannun ta yayi a cikin nasa yana jin ciwon rashin gudan jinin sa da yayi wanda har ƙaunar sa ta fara yaɗo a cikin ransa "Safiya Annoba ce da ya dace ɗan Adam ya nemi tsari da mata ire-iren ta .
Maradi
Duk yadda likitoci suka yi kokari tare da son ganin Falmata ta haihu da kanta abu yaci tura gaba ɗaya ta gaza yin yunƙuri yadda ya kamata saboda firgicin da ta kasance a ciki ya tafi da duk wani ƙarfi nata .
Mafi munin abun shine jinin ta da yake daɗa hauhawa a bayan kowacce minti talatin .
Ba hajiya Umma kadai ba har Maimartaba ma ya shiga zullumi da yasa yake ƙiran waya bayan duk ƙaramin lokaci .
Dole tasa ya sanar da Biyamuradi Youssouf da bai kai ga sanin Matar sa na asibiti ba saboda a da so suka yi sai ta haihu kawai sai a sanar masa amma a yanzu da lamari ya yi gardama dole aka sanar masa sannan kuma aka shiga addu'a fiye da wacce ake a baya sannan aka ɗaura tukwane domin yin abinci a bayar sadaƙha duk dan Allah ya sauƙi Gimbiya Falmata Matar Yarima Youssouf lafiya .
Ganin lokaci zai tafi tare da shiga hatsarin rasa Baby ko uwar yasa likitoci suka nemi da wani makusanci ya sa hannu a shiga da Falmata ɗakin fiɗa .
Maimartaba sarki Abdoul-azizou shine da kansa ya zo har asibitin ya sa hannu aka shiga da Falmata ɗakin fiɗa.
Anyi aiki cikin nasara an fitar da ƙatuwar jaririyar da ba'a ce ɗiyar fari bace saboda girma zabgegiya da ita jajir mai tarin suma akai kamar an kifa mata hular gashi dan har sai da likitan da ya ciro ta ya sanya almakashi ya yanke mata gashin ta gaban kan ta sannan ta iya buɗe ido .
Babu wanda yasan da tahowar Youssoufa kawai sai ganin sa aka yi a asibitin lokacin har an gama aikin an tura Falmata recovery room.
Duk suna tsaye suna jiran a fito da ita zuwa ɗakin da zasu Iya shiga su gan ta ɗaya daga cikin manyan malaman jinyan ya fito ya nemi son yayi magana da Youssoufa .
Nan yake shaida masa Falmata ta farka amma kuma sai surutai take tana kuka tana ƙiran sunan wata .
Ana buƙatar idan zai yiwu waccan ɗin ta zo ko kuma a ƙira ta a waya a haɗa ta da Falmata suyi magana dan kar kuma wata matsalar ta ɓullo .
Tare suka koma cikin ɗakin da take abunda ya bashi Mamaki bai wuce nunawa da Falmata tayi ita ba shi take son gani ba Yakaka yayar ta take nema .
Shi ba shi da layin wayar Yakaka amma yana da ta Baba Prof , Amnee da Mamar su da yake ƙira akai-akai yana gaishe su da baya zaton ma kawo yanzu sun san Falmatan ta haihu
Dan haka kawai sai ya ƙira Amne Bayan sun gaisa a gurguje ya sanar da su halin da ake ciki na haihuwar Falmata bayan an mata fiɗa da kuma halin da take ciki a yanzu na neman Yakaka .
Yanayi biyu ne ya chakuɗuwa Amnee na farko farin-cikin haihuwar Falmata tare kuma da fargabar halin da aka ce Falmatan na ciki bayan fiɗa da aka mata aka cire mata 'yar .
Nan take ta tura masa number Yakaka da bai jinkirta ba ya fara ƙiran layin sai dai sau biyar yana ƙira ba'a ɗauka hankalin sa duk ya daɗa tashi ganin yadda har lokacin Falmata bata bar kuka ba .
Dan haka ya sake ƙiran Amne lokacin da ta ɗauka ma suna tsakiya da tattauna da khaalty Rahima kan haihuwar da kuma halin da aka ce tana ciki hankalin su duk bai wani kwanta ba. dan haka sai ta haɗa su da khaalty Rahima tayi masa barka ta kuma sake tambayar jikin Falmatan ?
Nan yace har yanzu tana kuka kuma Yakaka take nema sannan ita kuma bata ɗaukar wayar .
Jin yadda hankalin sa ke tashe sannan ita ma tana iya jiyo kukan Falmatan da take surutai sai ta ce to bari ta tura masa layin Mijin Yakaka ya ƙira shi wataƙila suna tare amma bari a fara sanar da shi
Lokacin da ta ƙira Doctor Hamza dawowar su kenan daga Asibitin da yaga ƙiran Amnee ya ɗauka har labarin abunda ya faru ne ya je musu dan haka yayi hanzarin ɗaukar wayar sai dai bayan sun gama gaisawa sai ya ji Amnee ta ɗaura masa da wani batu kan Falmata da ta haihu da kuma halin da take ciki na kuka da neman Yakaka.'
Yana jin haka ya fahimci cewa Falmata tana da sani kan abunda ya faru da hakan ne yasa ta firgicin da take ciki a halin yanzu .
Amnee ta cigaba da faɗa masa cewa " idan har yana tare da Yakaka to Mijin Falmatan zai ƙira yanzu sai ya haɗa su suyi magana .
"To
Ya amsa kafin yayi wani yunƙuri Amnee ta katse wayar ta.'
Bai rufa mintoci biyu ba sai ga ƙira daga ƙasar Niger.
Ɗan jimm yayi kafin ya ɗaga ƙiran saboda sanin da yayi ƙiran daga Biyamuradi Youssouf ne Baban Mama .
Lokacin da ya ɗaga ga mamakin sa ba kamar yadda yayi zato ba sai ya ji muryar Youssouf ɗin faran-faran kamar ya san shi haka ya gaisa da shi dan haka shi ma sai ya daure zuciyar sa suka gaisa har ya masa barka .
Daga nan sai Youssouf ya nemi da ya haɗa shi da Yakaka , Falmata ce ke son magana da ita.
Cikin nutsuwa Doctor Hamza yace "ka kai mata wayar idan ka bata sai na haɗa su .
"D'accord .
Youssouf ya amsa yana mai takawa ya matsa gaban gadon da Falmata ke kwance a hankali ya kara mata wayar a kunne cikin taushin murya yana shafa kan ta yace "Mon Bébé ga Yayar ki nan kuyi magana kiji sai hankalin ki ya kwanta ta ki daina kuka .
"Hello Yakaka na tace tana shiƙar kuka..
Jin muryar ta yasa Doctor Hamza karawa Yakaka wayar a kunnen ta wacce duk abunda yake faɗa tana jin sa amma bata san da wa yake maganar ba .
Jin sautin Falmata tana kuka yasa ita ma kukan ya zo mata sai suka dunga yi tare cikin kukan Falmata ke tambayar ta "Yakaka baki mutu ba ko ? Sofi bata kashe ki ba ? Ashe Sofi haka take muguwa azzaluma ? Yakaka ki koma gidan Baa kawai idan Sofi ba zata bari ki rayu a gidan ba kin ji Yakaka Dan Allah ki koma Maiduguri kar watarana Sofi ta kashe min ke Yakaka idan ta kashe ki ni kuma ya zan yi.?
Doctor Hamza shi ya fara ƙoƙarin hana kukan Yakaka muryar sa a ƙasa yace " Wafaa ki daina mata kuka ta haihu ana so jinin ta ne ya dai-daita a halin da take ciki kwantar da hankali take buƙata ki rarrashe ta .
Kallon sa take yi kafin a hankali ta buɗi baki tace "Falmata kin haihu da gaske.? Me kika haifa muna ?
Falmata tana goge hawayen ta da bayan hannu Youssouf na taya ta tace "eh Na haihu Yakaka amma ni ban san ma me na haifa ba ban gani ba ma Ya..
Da sauri Yakaka ta katse ta tana cewa "ina abunda kika haifa ? Ki sa a kawo miki ki ɗauki abinki ki riƙe a hannun ki ki rungume ki shayar da shi arziƙi ne babba yau Allah ya miki Falmata kin zama uwa a yau Dan Allah kar ki bari abunda ki ka haifa yayi kuka a domin rashin ki a kusa da shi sa a kawo shi Alhamdulillah Alhamdulillah .
Wata irin nutsuwa kalaman Yakaka suka zo mata da shi cikin sanyi murya ta ce "To Yakaka zan sa a bani abunda na haifa yanzu amma Yakaka kina lafiya ko ? Sofi bata yi miki ciwo ba .
"Lafiya ta ƙalau Falmata , ki sa a kawo Baby nan ki sa min naji sautin numfashin abunda kika haifa Falmata .
"Ina Baby na ?
Falmata ta cewa Youssouf haka , ɗan murmushi yayi yana jin daɗin yadda ta fara dawowa hankalin ta.
"Riƙe telephoné na amsa miki ɗiyar mu ki ganta Fatima '
Fita yayi sai ga shi ya dawo rungume da jaririyar a hannun sa da shi ma sai yanzu ya ɗauke ta a shirye take tsaf ta sha kayan sanyi irin na alfarma tayi kyau matuƙar gaya .
Ɗora mata ita yayi a jikin ta bayan ya ɗan ɗago mata gadon sai ya zauna tana jingina da jikin sa daga shi har ita tsurawa jaririyar ido su kayi suna ganin tsananin kamannin ta da Mama kamar lokacin da aka haife ta , marabar su kawai wannan tana da girma kuma tafi Mama gashi bayan hakan za'a ce Mama ce kawai Allah ya dawo musu da ita .
A hankali ta ɗago ta sumbanci kumatun ta dama da hagu da yasa ta motsawa a hankali tana ɗan yamutsa fuska irin na jarirai.
"Yakaka na ɗauke ta ,Yarinya ce mace Mai tsananin kama da Mama , Allah ya dawo mana da Mama Yakaka.
Daga can murmushi mai sauti Yakaka tayi tana jin ƙaunar 'yar da bata kai ga ɗora idanu akan ta ba na samun wajen zama na musamman a cikin ran ta a lokacin ji take kamar tayi tsuntsu ta je ta gan ta ta ɗauke ta ta riƙe a hannun ta ta rungume ta a ƙirjin ta ta gwada mata ƙauna a matsayin ta na uwa a gare ta ba wai Yayar uwa ba kawai ɗiyar Falmata ɗiyar ta ce halak malaƙ .
"Allah ya raya ta Falmata , Allah ya mata Albarka , Yaa Allah yasa ta amfanar da Al'ummar musulmai ajiye wayar ki ɗaga ta ki shayar da ita anjima zan sake ƙiran ki .
"Amin Yakaka .
Daga haka Doctor Hamza ya zare wayar daga kunnen ta ya kashe kafin ya jaa ta cikin jikin sa ya rungume ta tsam suna musayar jin ciwon rashin nasu gudan jinin da suka yi .
Sumbatar goshin ta da Youssouf yayi bai sa ta janye idanun ta daga kallon fuskar 'yar ta ba da take jin wani abun da ya zarce a ƙira shi da So sannan kuma ya wuce ƙauna tasiri yana bin duk wani sarari na ran ta yana dasa wani al'amari mai girma ji take kamar ta tsaga ƙirjin ta ta sa ta .
Wai yau ita Falmata ce take riƙe da 'yar ta ta cikin ta babu shakka Allah shine mafi girman Abun Godiya "Alhamdulillahi Yaa Allah .
Ta furta hakan a sarari tana jin wata ƙwallar farin-ciki na cika mata gurbin ido .
A hankali Youssoufa ya kai hannu yana ɗauke 'yar daga jikin ta bata yi wani yunƙuri ba illa bin su da tayi da ido cikin ran ta bata mamakin yadda ya iya ɗaukar jariri saboda tun akan Mama ta san ya ƙware .
Addu'o'i ya shiga yiwa 'yar sa tsawon mintoci fiye da talatin dan tun Falmata tana kallon su har ta ɗan fara gyangyaɗi .
Hannun sa da ya shafa mata kumatu shi yasa ta buɗe ido da kyakkyawar fuskar sa tayi arba yana mata murmushi kafin sautin sa ya sauƙa a kunnen ta "Mon Bébé kina ji na ?
A hankali ta gyaɗa masa kai idanun ta cike da baccin gajiya suke lumshewa sai dai kalmar da ya faɗa ya sa ta wara idanun ta da sauri ta dube shi tana son sake jin me ya ce ?
"Wanne Suna kin ka zaɓarwa ɗiyar mu na bar miki zaɓi dan saboda kawai na gwada miki kaɗan dagga farin-cikin da nake ciki.
"Da gaske kake ?
Ta tambaye shi tana narkar da idanun ta cikin nasa .
"Da gaskiya Fatima na bar miki zaɓin sunan ɗiyar mu mai darajja '
" a sa mata Yakaka .
Sautin da ya taso daga ƙasan ran ta ya subto akan laɓɓan ta .
Shiru yayi yana kallon ta kafin yayi magana ta katse shi ta hanyar cigaba da cewa "indai dai har ka bani zaɓi to a sa mata sunan Yakaka Yayata .
"Babu shakka ta cancanta domin kuwa ita ce Mafarin silar haɗuwar sa da Fatima-zahra ba domin ita ba da bai samu Fatima ba bare har ta haifa masa 'yar da yake riƙe da ita yanzu a hannun sa a ƙarshe kuma ita ɗin uwa ce ga 'ya mafi soyuwa a gare shi da har abada baya zaton za'a samu mafiyin ta wajen matsayi a cikin 'ya'ya .....
Tunanin sa bai yanke ba ya juyo yana fuskantar Falmata riƙe da Babyn a hannu yace "Meye Sunan ta na ainashi..?
Cike da zumuɗi Falmata tace "sunan ta Amina.
Bai ce ƙala ba sai ya sake mayar da kai ga yiwa 'yar sa addu'a kafin bayan ɗan gajeren lokaci ya ɗago kan sa yana mai ɗora mata 'yar a jikin ta yace
" Sunan 'yar mu Amina riƙe ta da kyau 'ya ce a gurin ki sannan kuma 'yar uwa.
Da hannuwanta biyu ta rungume ta tana jin yanayin da yafi na ɗazu yana danne ta ta kasa tsayar da hawayen farin-cikin da yake sauƙa fuskar ta kamar yadda ta kasa ɗauke ido daga fuskar Amina .
Haka ma Biyamuradi Youssouf da yake tsaye akan ƙafafun sa hannuwansa duk biyu a zube cikin aljihun sa yana murmushin da yake bayyana haƙoran sa ya kasa janye ganin sa daga kan su kamar yadda yake jin ƙaunar su biyun tana fisgar sa tamkar wanda guguwa ta riska a tsakiyar rairayin hamada .
***
Daga nan ɗakin da Falmata zata cigaba da zama kafin a sallame ta aka kai ta bayan nan Hajiya Umma da har yanzu bata tafi gida ba ta shiga inda suke ta mata sannu sannan ta sake mata addu'a ita da Amina kafin ta bar asibitin .
Sai kuma ta fara amsar waya daga Iyaye da dangin ta na Nigeria har dai zuwa lokacin da likitoci suka buƙaci da a bar ta ta samu hutu mai yawa kar a takura ta.
***
Daga lokacin da Doctor Hamza ya ga har dare yayi bai ji wani labari ba daga iyayen sa sai ya fahimci Sofi ta rufe zancen duk abunda ya faru bata faɗa ba .
Dan haka shi sai ya yanke shawarar sanar da iyayen su da kansa dan haka a daren ranar bayan sallar isha'i ya hada conference call da Baba Prof da Amne da Khaalty Rahima da Momy Kori da shi kan sa Baban Sofi.
Bayan duk ya gaishe su sai ya nemi da su bashi dama zai musu bayani.
Nan ya shiga basu labarin duk yadda kome ya wakana a tsakanin sa da Sofi tun daga farko har ƙarshe .
Kafin ya gama Sallallami da kukan Momy kori tare da Amne ya cika wayar .
Sai da kyar Baba Prof ya sa suka yi shiru domin shi da kansa Baban Sofi ya gaza cewa kome kawai kamar ruwa ya cinye shi saboda tsabar shiga razana da muzanta shi da Sofi tayi.
Ɗan taƙaitatcen Bayani Baa yayi akan lamarin da ɗari-cikin-ɗari ya goyi bayan hukuncin da Hamza ya ɗauka ya ɗora da cewa "tunda har dai abu ya zama da neman aikata kisan kai to babu shakka ba amfanin zaman rabuwar ita tafi dacewa.
Matsanancin kuka Momy Kori ta sa cikin rishin kuka take sanar da su cewa ita har kawo yanzu ma da ake wannan maganar bata ga Sofi da idanun ta ba Sofiya bata zo gida ba to ina ta tafi ?
"Ta tafi ko'ina ma Kori , ina mai tabbatar miki da cewa Safiya ba za ta zo ta zauna min a gida ba domin nima ba zan zauna da mashayiya kuma makashiya ba tunda irin rayuwar da ta zaɓarwa kan ta kenan to tafi duk inda za ta tafi tayi rayuwar ta amma ni dai ban amince ta zo gidana Alhaji ka shaida ni na cire Safiya daga cikin 'ya'yana' ku kuma ina mai baku haƙuri kan abunda ya faru ita yarinyar ma dan Allah a bata haƙuri ita da iyayen ta .
Daga haka Baban Sofi ya yanke ƙiran daga ɓangaren sa .
Duk son kai irin na Momy Kori yau sai ta gaza kare 'yar ta haka tana ji tana gani saki Uku ya tabbata tsakanin Sofi da Hamza sannan kuma dole ta bada haƙuri ga su Amnee da shi kansa Doctor Hamzan da ya rasa gudan jinin sa sannan ta ajiye wayar .
Daga nan suka cigaba da jimantawa tsakanin sa da iyayen sa inda Amnee ta nuna son Yakaka ta zo gida a kula da ita amma tun ma kafin ta gama magana Baba Prof ya nuna rashin amincewar sa hujja da cewa ai shi Hamzan likita ne dan haka zai fi kowa lura da ita dole Amnee ta haƙura ita kuwa Khaalty Rahima daman bata cewa kome sai addu'a kawai tayi ta danne duk wata damuwar ta saboda kara .
Daga nan aka yanke shawarar cewa jibi Amnee da Zainab za su tafi Abujan daga nan su haɗu da hafsa idan sun duba Yakaka da jiki daga nan sai su dawo Kano su wuce Niger gurin Falmata .
Su Hafsa zasu dawo bayan suna Amnee kuma za ta ɗan yi ko da sati biyu ne tana kula da Falmatan .
Kafin kwanaki biyu zance ya gama baza dangi kan abunda Sofi ta aikata na yunƙurin kashe kishiyar ta kuma ta gudu ba'a san inda take ba.
Amnee sun je Abuja tare da direban su a babbar motar da Amnee ta cika kusan rabin ta da kaya .
Sun kwana a gidan Doctor Hamza ta sake rarrashin takwarar ta Yakaka sannan ta bata kayan gyara da tarin wasu turarurruka sannan ta sanar da ita sakon Prof da yace cikin satin nan za'a zo a shirya mata kayan ta a gidan .
daga nan kuma sai suka wuce Maradin Niger da tarin kayan ƙamshi da gyaran jiki tare da kayan jarirai masu kyau da tsada da Amnee tayi tanadin su musamman domin Falmata da zata haihu kayan gyaran tafiyayyu ne daga Chad .
Can a Maradi suka ga tarba irin ta saraki sai nan-nan ake da su ana sauƙe musu kabbakin arziki.
Daga Zainab har Hafsa sai da suka yi santin kyaun sashin Falmata da irin gatan da ake mata babu abunda yafi burge su irin tarin hadiman da take da su da ko yaya ta motsa sai sun mata sannu girma irin ta sarauta sai gidan sarauta .
Lokacin da Yakaka ta samu labarin cewa jaririya Sunan ta ta ci har sai da tayi kuka dan farin-ciki .
Doctor Hamza ma ya ji daɗi ya kuma musu fatan Allah ya ƙara musu zumunci a ƙarshe yayi alƙawarin daga ya ɗau hutun sa nan da wasu watanni cikin shekara mai zuwa zai kai Yakaka har Niger ta gano takwarar ta .
Ranar suna kuwa Al'umma da suka taru ba'a ce Falmata bata da dangi a Niger ba.
A gurin taron suna dangin suka dunga tsurkun tururuwar zuwa duba Hajiya Mama wacce jinya ta sarƙe ta sakamakon wasu munanan ƙuraje da suke feso mata duk a ƙafafun ta bayan hawan jini da ciwon zuciya da suka mata rubdugu bata ko iya tafiya gaba ɗaya rayuwa ta mata juyin waina a tanda .
Kowa ya fito daga sashin sai yayi gulmar sakayya ce take gani tun daga nan duniya .
Wacce irin ta Maimounatou ɗiyar sarkin Agades ma ta samu sakamakon mutuwa da Mahaifin ta yayi a tun jinyar da ya afkama sanadin mummunan abun kunyan da ta aikata kan yunƙurin kashe Mijinta a halin yanzu kuwa rayuwa ta mata atishawar tsaki batta ga tsuntsu batta ga tarko .
'Yayan Hajiya Mama kansu gaba ɗaya basu da sakewa a cikin taron sunan duk kuwa da cewa sun zo sun kuma kawo kayan jaririya da na uwa irin na alfarma .
Da kaya sai da Falmata ta rasa gurin zuba su tsakanin wanda Mijin ta tayi mata da wanda iyayen sa suka mata da wanda Iyayen ta suka kawo mata da kuma na 'yan uwan sa ga kuma na dangi da abokan arziƙa .
***
Bayan suna da Zainab da Hafsa da zasu koma kayan niƙi-niƙi aka haɗa Su da shi .
Ita kuma Amnee ta zauna kula da Falmata da ta dage tana lura da ita saboda haihuwar da tayi wani ɗam rami na musamman na turara jiki ta sa aka mata a cikin uwarɗakin Falmata kamar yadda al'adar su take su basu cika shan magungunan na mata ba sai gyaran jiki tsaftar sa da ƙyalƙyale fata suka fi bawa muhimmanci .
Gefe guda kuma ita ma Hajja ta dage da nata gyaran irin na matan ƙasar Hausa da su kuma suka fi bawa shan kayan ɗa'a muhimmanci .
Kafin sati biyu Fatar Falmata ta zama kamar bayan tarwaɗa yayin da wani fitinannan ƙamshi ya zauna mata a jiki 'yar kiɓar shayarwa da tayi ta amshi jikin ta sai ta koma kamar irin hamshaƙan matan nan da suke kan ganiyar ƙuciyar su duniya kuma ta juya hasken ta akan su tana haska su .
Bayan cikar sati biyu da kwanaki biyu Amnee ta koma Nigeria inda ta je ta tarar da labari mafi daɗi da Prof ya tare ta da shi kan ya samarwa da ƙanwar sa Rahima Miji .
***
Sheikh Mukhtar ɗaya ne daga cikin jerin ƙannen abokansa da bai yasar da zumunci ba ko bayan mutuwar wansa yake ziyartar sa lokaci zuwa lokaci muddin ya shigo garin Maiduguri daga can ƙasar Saudi-Arabia da yake aiki da zama tare da iyalin sa sama da shekaru ashirin da yayi aure.
Wannan zuwan nasa lokacin da Prof yake tambayar sa iyalin sa yake shaida masa ita matar tasa ta rasu shekarar da wuce .
Prof ya masa ta'aziyya bayan nan ya shawarce shi da kar yayi jinkirin yin wani auren saboda shi aure ibada ne sannan kuma kariya ne .
A lokacin Sheikh Mukhtar ya nuna masa cewa har kawo yanzu dai bai samu matar da ta kwanta masa ba wacce ya yarda da hankalin ta da zai iya danƙa mata amanar tarbiyyar 'ya'yan sa da matar sa ta mutu ta bar masa su huɗu .
Sannu kan hankali cikin dabara irin ta manya Prof ya gabatar masa da Khaalty Rahima cikin sa'a da ganin girman sa Sheikh Mukhtar ya nuna amincewar sa ɗari bisa ɗari muddin dai ita ma ta amince da shi .
Lokacin da aka sanarwa da Khaalty Rahima batun Sheikh Mukhtar bata ƙi ba tunda dai iyayen-goyon ta sun amince ita kuwa me zai ta tayi gardama idan tana da damuwa ɗaya ce ji da tayi ƙasar za ta bari gaba ɗaya ta bar Bulama dan ta sauran 'ya'yan ta mata ta san Allah ya riga ya sanya mata su a hannun nagartattun Mazaje '
Damuwar ta Bulama ne da ya shaƙu da ita fiye da misali sannan babu wani dangin sa na uba da aka samu ɓullowar su har kawo yau duk kuwa da neman da aka ta yi saboda har kawo yau da ake ɗiban shekaru fiye da bakwai da tarwatsa musu gari da 'Yan tawayen Boko Haram suka yi alƙaryar su bata sake kafuwa ba an riga an shafe ta mafi yawan mutanen su kuma sun mutu da take hasashen ciki har da mafiya-yawan dangin Uban su Yakaka da daman ba wani yawa suka cika ba ƙaramar zuri'a ce da su masu gajeran baya .
Duk da ba wai shakkun Bulama zai wahala bane idan har ta bar shi a hannun Amnee sai dai tasirin tsakanin uwa da ɗa ne musamman waɗan da suka shaƙu ya haka raba tsakanin su ba ƙaramin abu bane sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 102 Chapter of 103