Share this page
. "Hafsatouwa muddin aiki shi tafi dai-dai da tsarin mu ki tabbata shekarar gaba ke ai babbar jakadiyar birnin Maradi doumin kouwa waccen kaucewa take ta baki guri da hannuna zan sallame ta da wani mummunan sharri ta yadda zuri'ar ta basu yin gadon matsayin ta sannan ban tsaya nan ba cikin jama'ar ki ɗai-ɗaya ne ba za su Makka ɗakin Allah ba sai fa wanda Allah bai ƙira ba . Wata mitsi-tsiyar guɗa Ƙaramar jakadiya ta sake da hakan bai hana su jin motsin Falmata ba wacce a kokarin ta na yin baya ta ture 'yar randar da aka ajiye 'yar bishiyar fulawa daga sama kaɗan da inda take tsaye tana sauraron su tukunyar ta faɗo ta fashe . A tare suka zaburo ƙirjin su na dakan tara-tara da jin tsoron ko dai an musu laɓe ? "Idan kuwa hakane muddin ta kama mai mata laɓe sai ta sabauta shi kafin ta ɓadda shi ko wanene kouwa da dai ya fasa wannan sirri na ta mafi girma .Hajiya Mama ta aiyana hakan cikin ran ta lokacin da take nufar falon a ɗimauce . ASSALAMU ALAIKUM MASU KARATU DA FATAN KUNA LAFIYA TARE DA FATAN ALHERI . KUYI HAƘURIN JINA SHIRU DA KUKA YI UZURIN DA YA GITTA MIN MAI GIRM ne . A gaskiya bana jin daɗin ku masu karatu ta yadda bakwa musayan ra'ayoyin ku hakan ma na ɗaya daga cikin abunda ke duƙusar ni daga nayi yunƙurin yin typing sai nace "ah to yaya zan matsa kaina Alhalin ba'a nuna yabawa ?  Sai kawai na ajiye na fuskanci wani lamarin da ya zarta haka , da fatan kun fahimceni za kuma kuyi duba izuwa koke na ? Nagode '       [4/15, 10:16 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI (Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 51 Da baya-baya Falmata ta fara taku tana jin wani tsoro-tsoro daga ƙasan ran ta kafin ta juya da hanzarin son gujewa haɗuwar su da ita da mamallakan muryoyin da ta ji suna kitsa sharri da bata kai ga sanin su waye ba . Sai dai taku biyu kawai tayi ta ji an fisgo rigar ta ta baya da matuƙar ƙarfi da ba domin rigar tana da faɗi ba da babu abunda zai hana ta yagewa bayan ta jefar da ita a ƙasa warwas . A tsorace ta juyo da taimakon hasken lantarki suka yiwa juna kallon tsakar ido tsakanin ta da Hajiya Mama , Ba tare da Hajiya Mama ta saki rigar Falmata ba tana ƙanƙantar da idanun ta da suke cike da tashin hankali tace "wacece ke ? Me kuma kike nema anan ? Wa ya aiko ki ? Sannan me kika ji ana cewa ? Falmata ta kif-kifta idanun ta da basu cika karfi ba kafin ta fara kici-kicin kwacewa cike da dakiya a muryar ta tace " Ni ce Falmata , matar unh ' Umh Yarima Youssouf Abdoul-aziz , kuma ki sake min riga ta na tafi . Wani irin zillo Hajiya Mama tayi a take gumi ya karyo mata ta shiga juya kan ta daga ɓangaren hagu zuwa dama baki ɗayan jikin ta tsuma yake . Idanun ta da suka fir-fito a halin yanzu su ta gwalalo cikin kufcewar nutsuwar ta ta shiga jijjiga Falmata da wata muryar da ta fi kama da raɗa take cewa "Annamimiya ke kuma salon ki kenan ? Da salon da kika zo kenan ?? Lalle kin yi kuskure mafi girma da da ɗai wallahi baki sake maimaita makamancin sa . Juyawa tayi tana jaan ta ita kuma tana turjewa , cikin ɗakin da suka fito ta koma jaye da ita tana shiga ta ingiza ta ba tare da ta kula da cikin jikin ta ba da sauran ƙiris ta faɗa kan cikin ba dan ta riƙe gadon da ta samu damar ƙarasawa gaban sa ba. Hafsatouwa da tuntuni bata samu damar cewa kome ba illa fargaba da ita ma ya cika mata ciki maƙil jin wacece Falmata , da matsayin ta a gidan da kuma alaƙa mai girma da take da shi da zancen da suke tsakiyar yin sa ita da uwargijiyar ta da babu shakka Falmata ta ji kome . Tana shiga ɗakin ta rufe ƙofar ta murza ɗan makulli da hanzari ta juya jin sautin mari da ya karaɗe ɗakin . Akan Falmata ta sauke ganin ta wacce ta durƙusa akan guiwar ta riƙe da ƙuncin ta da Hajiya Mama ta zage iya ƙarfi ta mare ta . Sake chakumota tayi ta ɗaga ta tana sake chukui-kuiye ta tace "za ki faɗa min me kika zo yi nan wajen a dai-dai wannan lokacin kuma wa ya turo ki ? me kuma kika ji ina cewa ? ko kuma sai na shaƙe ki kin mutu ? Falmata da zuwa lokacin hawaye ya gama wanke mata fuska zuciyar ta kuma ta cika da tsoro cikin rawar murya tace "wallahi ban zo yin kome ba kuma ba wanda ya aiko ni nan , mantuwa nayi na kasa gane hanyar komawa sashin da aka sauƙe mu saboda tunda muka zo ban taɓa fita ba kuma kin ga idona , idona wallahi bana gani mai kyau dan Allah kiyi haƙuri ku mayar dani sashin da Hajja take . "Ƙarya kike yi munafuka , me ya fito da ke a daren nan idan da gaske dindimin kike yi ? Baki bani amsa ba me kika ji muna tattaunawa nace ? Kuma uban waye yace ki min laɓe ? Mukut ! Falmata ta haɗiyi yawun tsoro cikin rashin sanin takamaimai amsar bayawar tayi shiru . Cikin rashin sanin ta shirun da tayi shi ya basu tabbacin ta ji kome , abunda suke gudun kuma yana gaf da faruwa watau fallasuwar asirin su . Falmata bata ankara ba taji sauƙar wani marin kafin tayi wani yunkuri ta ji sauƙar duka da dundu ta ko'ina kusan gabadaya Hajiya Mama bata hankalin ta dai duka kawai take kai mata . Ihun da Falmata ta buɗe maƙogoro ta rafsa shi yasa Hajiya Mama dakatawa daga dukan ta , idanun ta jawur ta juya ga Hafsatouwa tace "Hafsatouwa tai ki ɗauko min wuƙa mai kaifi ki kawo min . Da gudu Hafsatouwa ta miƙe daga durƙuson da tayi ta fita . Cak Kukan Falmata ya tsaya ta shiga wara idanun ta da ganin su ya sake yin ƙasa saboda kukan da take yi , ta fara taku tana laluben hanya so take tayi wani yunkurin tseratar da kan ta . Fizgota Hajiya Mama ta sake yi ta warɓar da ita a bakin gado da muryar da take cike da bushewar zuciya tace "ƙwarmato kike yi min ? Kina son tara min jama'a ? Yarinya baki sanni bane , amma za ki sanni dagga lokacin da na guntule miki halshe . Cikin neman agaji Falmata ta zube guiwar ta a ƙasa dai-dai da dawowar Hafsatouwa da take riƙe da wata sharɓeɓiyar wuƙar yanka dabba a cikin kuɓen ta hawaye na tsiyayo mata ta haɗa hannuwan ta biyu da sigar migiya tana cewa "Hajja dan Allah kiyi hakuri ki barni na tafi wallahi duk abunda naji ba zan faɗawa kowa ba , wallahi bazan faɗa ba , kiji tausayina ki ƙyale ni ko dan abunda ke cikina . "Ki min shiru hegiya , ina ruwana da hegen cikin ki ? Kar na kuma ji kin ƙira ni ba suna na Hajja ba . "faɗa min me kika ji ana cewa ? Maimaita min idan kuwa kika min ƙarya sai na yanka ki billahil azim. Tiryan-tiryan Falmata ta maimaita musu hirar su kamar yadda ta haddace akan ta ba kalma guda da ta manta duk a ƙoƙarin ta na son suyi mata afuwa bata tsaya da bayani ba sai da ta dire sannan ta ɗora da cewa "wallahi shikenan abunda naji kuma nayi Alƙawarin bazan faɗawa kowa ba . Sai dai tunanin ta ya tsaya chak lokacin da Hajiya Mama tayi wata gajerar dariyar da ke bayyana irin halin ɗimuwar da take ciki. "Bayan duk kin ji wannan sirrin nawa da mutane uku ne suka san shi bayan ni a din duniya ? Sirrin da 'ya'yan cikina ma basu san shi ba , sirrin da yake ginshiƙi na rayuwata baki ɗaya , da na ta'alaka duk wasu nasarorina akai , shine kike tunanin zan bar ki ki tafi ? Na barki ki tafi kiyi rayuwa a cikin gidan nan ɗauke da sirrina a hannun ki ? Ko a hankali irin naki na dabbobi hakan abu ne da zai yiwu ? Wata dariya ta sake yi kafin tace "yarinya wannan ba mai yiwuwa bane dole nayi abunda zai sa na kuɓutar da sirrina da yake hannun ki ... "Wallahi Hajja bazan faɗawa kowa ba . Falmata ta furta hakan tana sharar hawaye da rigar ta . "Ni da kaina zan goge shi daga kan ki ko da kuwa ace hakan ba zai samu ba sai na raba kan ki da gangar jikin ki ne ' "Hafsatouwa ban wuƙar nan . Da sauri ta miƙa mata ta sake komawa tana Sake jaan labulen windows din dakin. A hankali Falmata ta ɗago kai zuwa lokacin ta karaya cikin ran ta ta saddaƙar mutuwar ta ta kusanto , Idanun ta ta sauƙe akan Hajiya Mama , tana jin yadda zuciya da ƙwaƙwalwar ta ke adana hoton kamannin fuskarta , a matsayin matar da zata raba ran ta da gangar jikin ta . Fitsarin da take riƙewa ya kufce ya shiga bin ƙafafun ta lokacin da ta sauke ganin ta akan kakkaifar wuƙar da Hajiya Mama take jujjuyawa a hannun ta . Wani murmushin mugunta Hajiya Mama ta mata kafin tace "ke kina jina ? Cikin mutuwar jiki liƙis Falmata ta gyaɗa kan ta . "Kina da zaɓi biyu ko dai na yanka ki a yanzu na kar ki na kar banza , na sa a ɗau gawar ki a yasar , ko kuwa kiyi duk abunda nace da ke ba tare da gardama ba , sannan ba kuma na son na sake jin tashin sautin muryar ki, ko numfashi mai ƙarfi kika jaa sai na yanke miki hanci bare ta kai ki ga magana babu makawa za ki tsinci halshen ki a ƙasa kina jina ko ? Da sauri ta sake gyaɗa kai, wasu sabbin hawaye na sake tsiyayo mata . "Hafsatouwa ki je ki kawo min rigar bayu da mayafi . Kafin ta rufe baki Hafsatouwa ta yi waje , Nisawa Hajiya Mama tayi tana karkaɗa kafa cike da izza da mugunta tace "yarinya duk abun da kunnuwan ki suka jiye miki na kaddamar ina kuma kan gaɓar shirya wasu game da surukuwar ki da shi kan sa mijin ki haɗa da 'yal uwarki gasken gaske ne . "Ki kuma tabbatar zan iya yin abunda yafi haka akan ki muddin kika yi kuskuren yi mini gaddama ko da sau ɗaya ne . "Ɗauke idon ki daga kaina fitsararriya kin wani tsattsareni da ido uwa budurwar mujiya . Ta ƙarasa zancen da tsawa da hargagin da yasa abun da ke cikin Falmata murɗawa. Da sauri Falmata ta sunkuyar da kai tana jin tausayin kan ta na kawo mata , ita kuma irin tata kaddarar kenan mutuwa a hannun wannan azzalumar mata , da ita da abunda ke cikin ta , domin zuwa yanzu ta tabbatar babu wani mai tsaratar da ita sai fa Allah . Dawowar Hafsatouwa riƙe da wasu tsummokara yasa Falmata sake tsorata "ka dai toshe mata hanci za suyi su hanata mumfashi har ta mutu ? Saukar taunmokaran a jikin ta ya sa ta ɗago kan ta a firgice. "Ki tashi ki saka kayan nan da gaugawa . Babu yadda ta iya haka ta lafta waɗan nan kayan akan na jikin ta tana yi tana yunƙurin aman da yake taso mata sakamakon tsami da ɗoyin datti da kayan suke yi . "Kiyi lulluɓi da kyau ki biyo ni a baya muddin kika yi wata alamar da tasa aka gane akwai wani abu wallahi kafin ki farga na soke ki. Haka suka dunga ratsa sashi-sashi na gidan suna cin karo da bayu tsilla-tsillan da suke zubewa su gaishe da Hajiya Mama . Har suka dangana da wani sashin da yafi kama da kango da yake can ƙuryar gidan da daga shi sai maƙabartan da take cikin gidan ta ɓaryar dama . Da wani ɗan makulli Hajiya Mama tayi amfani ta buɗe ƙofar ainahin tangamemen falon da yake cikin sashin . Ta ingiza Falmata wacce bata kai ga sanin cewa falon ya shiga ƙasa ba dan haka tana jefa ƙafar ta ta faɗa ciki ta gurɗe a ƙafa kiris ya rage ta faɗa a kan cikin ta Allah ya sa ta tokare ƙasa da hannuwan ta . Lokacin da ta ɗago kai bata iya ganin fuskokin Hajiya Mama da Hafsatouwa saboda duhun da Falon yake ɗauke da shi , da raunanan idanun ta hasken da yake shigowa daga can harabar gidan yayi kaɗan su iya gani tare da shi . Ɗallare mata ido da hasken wayar hannun ta da Hajiya Mama tayi yasa ta saurin runtse idanun ta kafin ta buɗe su da sauri jin abunda Hajiya Mamar take cewa . " anan za ki cigaba da zama har zuwa lokacin da zan gama yanke hukunci kan matakin da zan ɗauka akan ki., idan kika yi yadda nake so ta hanyar zama salin-alin ba tare da kin yi wani motsin da zai sa asan kina nan ba , wataƙila na iya barin ki bayan na kafa miki sharɗaɗun cigaba da rayuwa a gidan nan . "Muddin kuwa kika yi yunƙurin yin wani motsi da zai sa asan kina nan wallahi , wallahi , wallahi , ni ina iya kashe ki da hannu na kuma na sa a ɓatar da gawar ki . Daga haka ta juya da sauri suka fita ita da Hafsatouwa daga inda Falmata take yashe tana iya jiyo saƙala ɗan makuba da aka yi aka kulle ta ta baya kafin ta fara jin sautin takun sawayen su akan busassun ganyayyakin bishiya su na barin wajen har dai zuwa lokacin da sautin su ya ɓace a kunnuwan ta . Wani irin karkawa tsokar jiki zuwa gundarin zuciyar su ka shiga yi na tsananin tsoro da firgicin da ruhin ta ke ciki , kafin da wani irin sauti ta fashe da kuka , ta shiga rarrafawa da hannunwan ta da guiwar ta zuwa inda take tunanin nan ƙofar take , Lokacin da tayi karo da bango da hannuwanta duk biyu ta shiga bugun bangon cikin ɗimuwar rashin fahimtar ƙofa ce a wajen ko kuwa jikin bango ? . Washegari da Asuba a Masallaci bayan sun idar da Sallah, Maimartaba tare da Youssoufa yana biye da shi a baya, kai tsaye sashin Maimartaba suka yiwa tsinke domin ganawa ta musamman . Maimartaba yana sake tambayar Sa yanayin lafiyar jikin sa ? Shi kuma yana amsa masa da cewa "yana cigaba da samun sauƙi sosai . Bayan sun isa turakar Maimartaba Youssoufa zai zauna daga gefen shimfiɗar da yake kai , yace masa "dawo nan kussa gareni mu tattauna yana masa nuni da kan shimfiɗa kusa da shi . Da jin daɗi mai yawa Youssouf ya matsa kusa da shi . Gyaran murya Maimartaba yayi kafin yace . "Youssoufa wanne mataki kake ɗauka bissa ga waɗan da suka ha'ince ka ? Shiru Youssouf yayi kafin yace "Ranka shi daɗe dukkanin hukuncin da ka zartar . Shiru mai martaba yayi kafin yace " Ubangiji Mai yawan yafiya ne , yana kuma ƙaunar bayin sa masu afouwa ga junan su a duk lokacin da aka zalunce su , shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci babu wani mugun abu da zai same su, amma mugaye ba za su sami kome ba, sai wahala bayan ubangiji ya bar su da kan su , Kada ka ɗaukar wa kanka fansa, ka dogara ga Ubangiji shi zai yi sakamako. Youssoufa da yayi shiru yana sauraron sa , jin ya dakata ya sa shi ɗago kan sa a nutse A kalaman maimartaba ya fahimci shawarar da ya ba shi cikin hikima ransa kuma ya sanyaya daga zafin da yake masa a duk lokacin da ya tuno da abunda aka masa dan haka sai yace "Nayi musu afouwa ranka shi daɗe amma ita ban iya sake riƙon Amren ta zan sauwaƙe mata daga can ta tai yankin su , mammadou kouma zan tafi mu dawo tare . "Madallah da kai Youssoufa yadda kayi afouwa ga 'yan Adam da sunka maka ƙeta kai ma Allah shi maka afouwa bisa tarin laifukan ka . "Amin Amin Baba . Murmushi maimartaba yayi yana jin ƙaunar ɗan sa na kawo masa tabbas zuciyar wasu sassauƙa ce mai yawan yafiya . "Yaushe za ka tafi Niamey domin kawo ƙarshen zaman su a magarƙama ? Ko kouwa saƙo za'a aika musu ? "Da kaina zan je doumin na sanya hannu a takardar da zai sa a sake su sannan ita kuma zan sahale mata amre na , cikin kwanaki biyu masu zuwa zan tafi . "Kafin tafiyar ka a sanya a tattara kayan ita wannan ɗiya a aika da su garin su , shiyar ta kouwa ni da kaina zan sa a shirya shi ga ita ɗiyar da muka amso amanar ta daga ƙasar su insha Allah ita tana cikin amintattun mu Allah ya cigaba da baku kariya baki ɗayan ku ya kuma dauwamar da zaman lafiya tare da zuri'a masu Albarka tsakanin ka da matayen ka . Wani irin farin-ciki Youssouf ya ji yana ratsa shi jin cewa ashe Maimartaba da kan sa ya sa aka dawo da Falmata har ma kuma ga shi zai sa a shirya mata wajen zama a gidan hakan yana nufin samun 'yanci tare da tabbacin zaman sa har abada da Fatima , idan hakane yana godiya ga Allah da duk wasu hatsararruka da ya tsallaƙe tunda ya tsira da Fatima-zahra. "Amin Nagode Nagode ranka shi daɗe Allah ya ƙara girma tare da nisan kwana . "Allah shine abun godiya Youssoufa . Sun jima suna tattaunawa Maimartaba yana ba shi shawarwari cikin hikima tare da yi masa nasiha har hantsi ya ɗaga lokacin zaman fada ya gabato , Tare suka yi karin kumallo kafin yayi bankwana da Maimartaba zuciyar sa cike taf da farin-ciki gami da nutsuwa ta musamman , tabbas wanda duk yayi dace da iyaye na ƙwarai ya samu rabi na daga nasarar rayuwar sa . Gefe guda yana sake jin haƙaƙewa akan rabuwa da Maimounatou bayan ta amsa masa tarin tambayoyin da kullum yake bitar su cikin ransa tare da burin jin amsa daga bakin ta . Bai koma sashin su ba sai ya zarce shiyar Hajiya Umma zuciyar sa cike da ɗokin son ganin Fuskar Falmata a hasken ranar da ta fara ɗagowa , yana da tabbacin a shiyar Hajiya Umma anan aka mata masauƙi . Abun Mamakin da ya tarar lokacin da ya riski falon Hajiya Umma bai wuce ganin ta tare da Hajiya Mama da sauran 'yan uwan sa baki ɗaya ciki har da 'yan ɗakin Hajiya Mama duk suna karin kumallo tare da hakan sosai yake sabon lamari a wajensu baki ɗaya . Cike da jin daɗin ganin su haka a tare ya ƙarasa falon kai tsaye kusa da Hajiya Umma ya zauna , yana gaishe ta kafin ya juya ya gaishe da Hajiya Mama wacce ta amsa cikin nuna tsantsar farin-ciki kafin ta ɗora da tambayar sa ƙarfin jikin sa ? A ƙarshe ta bi shi da wata doguwar addu'ar da yasa zuciyar Hajiya Umma haske har ma ta fara samun 'yar nutsuwa akan ta karo na farko , fuskar ta ta cika da annashuwa tana amsa jerin addu'o'in da Hajiya Mama ke yi . Da wata irin kulawa da ta zarce ƙa'ida Hajiya Mama tace "Yarima Magajin sarki me za ka ci a zuba maka ? Da jin ɗaɗin kulawar da take masa ya ɗan yi taƙaitatcen murmushi kafin ya bata tabbacin tare da Maimartaba suka yi karin kumallo . Wani murmushin yaƙe tayi ta jaa bakin ta tayi shiru sakamakon wata kibiyar baƙin-ciki da ta ji ta soki ran ta . Sallamar da Hajja ta rangaɗo daga bakin ƙofa bai sa wasun su sun tsagaita daga hirar da suke ba , sai fa Youssoufa da Hajiya Mama sune suka yi hanzarin amsa Sallamar da su biyun daman kunnuwan su tarwai yake ga sauraron mai iya shigowa a dai-dai lokacin . Daga inda Hajja ta saba tsugunnawa ta gaishe da Hajiya Umma yau ma daga nan tayi gurfano ta miƙa gaisuwar ta . Hirarrakin su suke cigaba da yi ba wanda ya kula gaisuwar Hajja bayan ita Hajiya Umma da ta amsa sama-sama sai fa Youssoufa da ya amsa a mutunce cikin girmamawa. Jim! Hajja tayi a zaune tana juya zancen da take tafe da shi a ran ta na rashin ganin Falmata ko sanin inda take a tun yammacin jiya . Wanda ba ƙaramin tashin hankali ya jefa ta ba , domin kuwa ko baccin ta rabi-da-rabi tayi duk kuwa da cewa wani ɓangare na zuciyar ta na shaida mata cewa Falmatan tana tare da Youssouf ne tsakanin Mata da Miji bare ma a haɗa dai da 'ya'yan zamani. Sai dai ganin Youssoufa a yanzu shi ɗaya ba tare da Falmatan ba ya sa taji cewa gara kawai ta tambaya domin samun tabbacin da zai bata nutsuwa dan haka ta gyara murya kafin tace "Ranka Ya dade Yarima ince dai Fatima ta kwana lafiya ? Domin kwana biyu tana fama da ciwon ƙafafu na saba mata tausa da asubar fari saboda ta ɗan ji dama-dama . A ɗan jahilce Youssouf yake kallon Hajja kafin yace "Hajja ina itta Fatima ta fita da safe hakka ita da bata cika lafiya ba ? Kalaman sa sun zo dai-dai da bugawar zuciyar Hajja a take ta ji wani tashin hankali mai girma yana durfafar ta cikin ruɗewa tace "ha'a ? Ai tun jiya bayan ta shigo nan domin taryar ka bata sake komawa ɗakin da aka mana masauƙi ba , ban sake ganin ta ba , yau Fatima bata kwana a ɗakin da aka sauƙe mu ba , ban kuma san inda take ba . Hajja ta ƙare zancen da baza hannuwan ta biyu cikin tashin hankali. "que de diable racontes-tu ? Youssouf ya furta hakan cikin ƙaraji tare da miƙewa akan ƙafafun sa da hakan ya jaa hankalin duk sauran mutanen dake wajen bayan Hajiya Mama da daman tuni take sauraron bayanan Hajja . Muryasa cikin tashin hankali ya cigaba da cewa "Hajja wanne zance ne wannan ? Ina Fatima ta kwana ? Tare da wa aka gan su sun fita ina kuma suka tafi ? Watsa hannuwa biyu Hajja ta kuma yi kafin tace "Allahu shi ya barwa kan sa sani ni dai ba shakka ban san inda ta tafi ba . Cikin nutsuwa Hajiya Umma da zuwa lokacin ta ji abunda Hajja take cewa ta dubi Youssouf "Mene ne ya faru ? Ta tambaye shi , wani ɗan taku ɗaya biyu yayi kafin yace "Fatima, elle est partie, elle est perdue. "comme quoi ? Ubbo ta furta hakan tana tsare Hajja da ido kafin ta ɗora da cewa "kuma sai dai idan da kan ta ta tai wani wuri . Hajiya Mama ta muskuɗa tare da cewa "wai meye ya faru ? Wace ce Fatima ? Damuwa na bayyana a fuskar Hajiya Umma tace "ɗiyar Nigeria da Youssoufa ke amre ita ce ta ba'a gan ta ba . Salatin da Hajiya Mama tayi ya sake dilmiyar da Hajja da Youssouf cikin ƙarin wata damuwar kafin tace "to ina ta tafi ? An kuma duba ko'ina ba'a gan ta ba ? Bai fa kamata a zauna ba a yi oumarni maza a fantsama neman ta cikin gida ba'a rasa inda tayi ba. Kafin a ɗau wani lokaci baki ɗaya bayu masu ɗauke da alhakin tsaron gidan sun fatsama neman Falmata lungu da saƙo na gidan ƙarƙashin umarnin Biyamuradi . Kasa zama Youssouf yayi ya kama hanyar komawa sashin sa zuciyar sa cike da fatan zuwa ya tarar da ita a inda jiya ta shiga ta ɓuya . A bakin ƙofar sashin suka ci karo da Siyama wacce ta ci kwalliya cikin riga da zani na wani sassalkan leshi sai zuba ƙamshi take fatar ta na ƙyalli . Da fara'a ta tare shi zuciyar ta da koyaushe ke kwaɗayin ganin sa tana cika da farin-ciki . Sai dai ga mamakin ta bai ko saurare ta ba ya wuce ta da sassarfa da alamun rashin nutsuwa a tare da shi . Da sauri ta taka ta bi bayan shi bayan ta ɗauki Yumna da tasan ba zata iya sauri ba . "Baban Yumna lafiya kouwa ?

Chapter 89 of 103