Yakaka tace mata ta tafi ta huta tunda ita ma Hajja tace bata da lafiya,
Sannan fuskarta babu walwala tayi musu Sallama idanunta na kan Mama ta bi bayan Youssof wanda tun bayan da ya matsa gaban gadon Mama ya yi mata addu'a tare da sumbatar goshinta ya shafa kanta yayi ficewar sa ya tsaya daga waje yana jiran fitowar ta ,
Bai ce kome ba ya riƙe hannunta suka tafi , ita ma har suka shiga mota bata ce masa ƙala ba sai tunanin zuci da take yi ,
Bayan fitar su Yakaka ta kai kallon ta ga Hajja ,
"Hajja meye yake damun Falmatan ita ma ? Naji kin ce bata da lafiya amma ita bata faɗa min ba , ?
Sasakai Hajja tayi tana kallon ta ,
"au sai ta faɗa miki tukun zaki gane ? Ji min rashin kan gado , yanzu ke Babba uwar Mama Allah baki Fahimci ƙanwar ki tana da yaron ciki ba ?
Dukkanin wata nutsuwar ta Yakaka ta tattaro ta juyo sosai ta fuskanci Hajja , muryar ta a nutse tace ,
" Menene yaron ciki kuma ? Ki min bayani mai kyau ni Hausa ba yare na bane Hajja ,
Kallon gefen ido Hajja tayi mata , sannan tace ,
" Au haka fa , to abunda nake nufi shine ƙanwar ki tana ɗauke da juna biyu , ciki na haihuwar ɗan mutum , nan da wasu watanni idan Allah ya kaimu zaki sake samun wata ɗa ko 'ya , yanzu kin gane ko Babba uwar Mama ??
Tun da ta ambaci ciki a jikin Falmata , Yakaka ta daina Fahimtar a halin da take ciki dukannin sauran bayanan Hajja bata fahimce su ba ,
" Ciki a jikin Falmata ? Kuma Youssouf ne ya yi mata ? A lokacin mantawa tayi da cewa aure ne ya gifta tsakanin su , tashin hankalin da take ciki ji take tamkar abunda ya faru ga rayuwarta ne ya afku ga Falmata ,
Wani irin Kuka ta fashe da shi ta haɗa kanta da ƙarfen gadon ,
Shin Youssouf wanne irin mutum ne haka Mai cike da zalinci da sharri ?
Bata san lokaci ya ƙure mata ba sai yanzu da tasan kome da take gudu ya faru , ƙanwarta kuma ta afkama tarkon Youssouf a karo na biyu , Youssouf yayi nasara akan ƙanwarta kamar yadda ya ci galaba akan ta ,
Kukan ta ya tsananta da yasa jikin Hajja yin laƙwas , karkata kai tayi tana ƙifta ido
" Ikon Allah Babbar uwar Mama menene abun kuka haka ga abunda yakamata ayi farin-ciki da Samuwar sa ? Ni har jikina yayi sanyi wai kaza ta taka wuƙa ,
Yakaka bata kula Hajja ba , hasalima hankalinta baki ɗaya baya jikinta , ya tafi tunanin neman mafita , ita yanzu yaya zata yi ? Wanne mataki ne yafi dacewa da ta ɗauka ? Anya tana da mafita a yanzu ?
Ganin ta cigaba da kuka yasa Hajja yin shiru , hasashe take akan dalilin kukan Yakaka daga jin labarin cikin Falmata , to ko dai kishi take ??
***
Duk yadda Youssouf ya so ya samu Falmata ta kula shi su yi ko ƴar maganar kirki ne taƙi ,
Tunda suka zo wanka tayi ta shige ɗakinta ta rufe ta kwanta , sai dai duk yadda ta so ya ƙyaleta ta kwana a sashinta ƙi yayi a ƙarshe ma hankalin sa ne ya tashi ya fara tambayar dalilin sauyawar ta ? Cike da fargabar ko dai Yakaka ta mata wani zance ne
Amma tace masa babu kome kawai rashin lafiyar Mama ke damunta , nan ya lallaɓata suka tafi sashin sa ,
A nan ɗin ma zama suka yi babu wata hirar kirki , shima da ƙarin damuwar sa da ƙira yake ta shigowa wayar sa daga Matansa waɗanda suke zuba idon ganin sa tun jiya ,
ya rasa kuma takamai-mai uzurin da zai basu kome ya kufce masa sau biyu yana ɗaga ƙiran su a mabanbantan lokuta yana cewa "yana uzuri ne zai ƙira daga baya ,"
Daga Maimounatu har Siyama sun gaza gane kan mijin nasu tun gabannin tafiyarsa turai , ga shi ya dawo ɗin ma ya zo su gan shi abu ya ta'azzara , ga shi sun gama yin duk wani shiri na tarɓar sa ,
Musamman Siyama da kewar sa ke walagigi da ita , tun tana daurewa har ta kai yanzu kowa ya ganta zai iya fahimtar damuwar da take tare da ita ," duk tsoronta kar wata ce ta ɗauke masu hankalin miji ,
***
Ƙiran Tafeeda ya sake shigowa karo na biyar a yau ,
Yana kallon wayar ta gama ƙara , kiran na katsewa ya ɗau wayar ya kashe , ya miƙe tare da kashe wutar ɗakin ya zo ya kwanta daga bayanta yayi rigin-gine .
Falmata wacce duk tana jin ƙiransa da ake yana ƙin ɗauka , ta kuma fahimci wata sabuwar damuwar da shima yake ciki ,
sai ta ji tausayin sa ya kamata , ko babu kome a gurinta shi mutumin kirki ne , managarci Mai kyaun hali da kyakkyawar zuciya , sai ta juyo a hankali ta ɗaura kanta akan ƙirjinsa ta rungume shi da hannun ta guda, tana jin lokacin da yayi ajiyar zuciya mai ƙarfi .
Cikin dare bacci ya ƙauracewa idanun Youssouf tunaninnika sun masa yawa , yana son ya san halin da Mama ke ciki yasan kashe wayar da yayi ma a halin yanzu kuskurene tunda yana da marar lafiya a asibiti ,
Dan haka ya miƙe zaune ya ɗau wayarsa tare da kunna ta , kan layin Hajja ya danna ƙira yana kallon agogo wayar da ya gwada masa ƙarfe ɗaya saura mintuna biyar ,
Yasan cewa dare yayi sosai amma ya zama dole ya san halin da ɗiyar sa ke ciki tun bayan barin su wajen ta , da kuma yadda zata kwana ,
A can wayar ta ɗau ƙara , yaji alamun shigar ƙiran ,
Muryar da ta doki kunnuwan sa ya sanya shi miƙewa tsaye , yayi taku kaɗan , yana waiwayen Falmata ,
" Mai wayar tana bacci ,
cewar Yakaka da ita ta ɗau wayar Hajja saboda ƙarar wayar kar ya tayar da Mama da ta samu bacci da kyar bayan kukan ciwo da take yi , tare da rikicin neman Iyayenta .
" Yaya jikin Mama ?
Yace , yana fitowa daga ɗakin zuwa falo domin kada ya tayar da Falmata daga bacci ,
Miƙewa tayi daga kujerar da take kai , tana jin tsanar sa na sake bijiro mata da jin sautin muryar sa ,
" Youssouf
Ta ƙira shi , bata sauƙe mumfashi ba ta ɗora da cewa , "ina batun mu ? Kar ka manta da abunda na faɗa maka muddin kana son cigaba da ganin farin-cikin iyayen ka sannan....
Katse ta yayi ,
" yaya jikin ɗiya ta nake tambayar ki ? Ke baki da tounani ne ? Baki ganin halin da Mama take ciki ? Ba yanzou bane lokacin yin wannan maganar kiyi hakuri don Allah .
" Yanzou ki tada Hajja daga barci ki bata wayar zan tambaye ta kan lafiyar ɗiya ta ,
Ƙit !
Yakaka ta kashe wayar har ita yake ƙira marar tunani ? Akwai marar tunani da ya wuce shi ? Duk sanadin waye suke cikin halin da suke ciki a yanzu ? Da bata haɗu da shi ba zata haifi Mama ne ? Ko kuwa yana nufin shi da ya gudu ya barta da cikin Mama ya fita ƙaunar Mama ɗin ne ? Yana da sani ne ko kaɗan akan irin wahalar da ta shiga na kwana a rumfar kasuwa tare da cikin Mama a jikinta ?
Guntun tsaki tayi tana komawa ta zauna a kujerar da ta tashi ,
ta shafa kan Mama wacce take baccin zoma tana ɗan nishi kaɗan-kaɗan , duk da cewa an ƙara mata jini leda guda amma har yanzu ƙafa da hannunta fari sol alamun rashin jini
tausayinta yana sake kama ta , ko runtse bata runtsa ba , tun lokacin da Hajja ta faɗa mata cikin jikin Falmata damuwarta ta sake ninkuwa ,
Duk dogon nazarin nema mafita da tayi hankalinta yaƙi amincewa da ta ƙyale Youssouf ya cigaba da zama da ƙanwar ta ta gwammace ya saki Falmata su koma Nigeria tayi rainon cikin ta haihu idan yaso su ɗauko abunda aka haifa a kaiwa iyayensa tunda shi da Falmata aure suka yi ,
Dole iyayensa zasu riƙe abunda ta haifa , ita kuwa Mama 'ƴar ta ce da suka haifa ba tare da aure ba ta san iyayensa baza su riƙe Mama ba , Mama zata kasance tare da ita .
**
Youssouf ya ji yadda ta katse ƙiran ba tare da ta bashi amsar da yake son ji ba , sauƙe wayar yayi bai sake ƙira ba ya juya ya koma ɗakin ,
Zama yayi a bakin gado , cikin ransa rikicin da Yakaka ta zo da shi ya kai matakin ƙure shi, ya fara neman mafitar yaya zai yi da Yakaka domin kuwa ko a mafarki ba zai yi mata yadda take so ba , ya saki Matarsa akan wanne dalili ? Aurensa da Falmata aurene da sai mutuwa ce kaɗai zata raba su ,
Yana son matar sa , yana ƙaunar ta ,yana tausayin ta , ya kuma shirya tsaf domin zamar mata bango abun jingina , idan ya rabu da ita taje ina ? Waye zai jiɓanci lamarin ta ? Wa suke da shi a duniya jigo ? Daga ita har Yakaka masu rauni ne domin kuwa mata ne tayaya zai sau aurenta ? Alhalin ga zuri'a a tsakani Allah ya fara basu ,
dangantakar su ba mai yankewa bace har abada ba zai rabu da ita ba ko da kuwa ace ita da karan kanta ta nemi da ya sake ta ba zai aikata hakan ba ,
bare wasu mutane daban da ba sune suke riƙe masa da igiyoyin auren sa ba , Fatima Zara matar sa ce har a lahira baya fatan rabuwar su .
Zai roƙi Yakaka da tayi hakuri ta yafe masa duk wani laifi da take zaton ya yi mata , tare da Alƙawarin kula da hidimar Rayuwar ta muddin zata yadda ta cigaba da rufe asirin tsakanin su daga sauran mutane , ciki har da Falmata da Mama idan ta girma .
sannan tayi haƙuri ta koma Nigeria ta samu miji tayi aure shi zai tsaya mata a wannan gaɓar .
muddin kuwa taƙi yadda da tayin salama , bai iya hasashen yadda ƙarshen lamarin su zai ƙarƙare , bai san ba gurin hukuntata akan yunƙurinta na raba shi da matar sa ko zai iya yi mata sassauci Albarkacin Mama ba?
abunda ya riga ya sani ne tun a ranar farkon ganin sa da ita ba soyayya ce ragamar tarayyar su ba illa musiba tare da sharrin shaiɗan da shi ya faɗawa a ciki , ita kuma ta gagara tsamo sa a madadin haka ma sai ta zama abokiyar taya shi ,ashe idan haka ne itama da nata laifin ,
Zai yi kome zai kuma jure kome domin ganin ya cigaba da rayuwa da matar sa da 'ya'yan sa ,
A hankali ya hau gadon ya rungume ta tsam a jikinsa , runtse ido tayi hawayen da suka taru mata suka zubo , tun daga tashin sa ta ji shi , ta ji wayar sa da Yakaka ,
Wanne irin sirri ne a tsakanin su da suke ɓoye mata basa so ta ji ? Jikinta yana bata rabuwar su da ita da Youssouf ta zo kusa.
Washegari
Tunda tayi sallar asuba gari yayi haske ta shiga kitchen duk kuwa da Youssouf ya so hana ta amma ta dage ,
"bai kyautu ba kuma Hajja ta dawo daga asibiti tayi mana girki zan iya ba abu mai wahala zan dafa ba kawai pasta ne zan yi , tace da shi .
Ba yadda ya iya saboda gaba ɗaya ta koma mishi kamar farkon auren su , sai janye jiki take da shi ,tana ƙin kallon sa , bata tsawaita zance da shi
Bayan ta gama girkin ta zuba ta rufe , ta zo ta wuce shi a falon yana zaune ba tare da tace masa kome ba ,
Da ta shiga ɗaki wanka tayi ta koma ta kwanta a gadon ta saboda tun ƙarfe ɗayan dare rabon ta da baccin kirki , lokacin da ta ji wayar da suka yi , tana kwanciya bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta
Youssouf da ya gaji da jiranta ta zo suyi karin kumallo , tashi yayi ya leƙa ɗakin nata ,
A gado ya hangota tayi luf tana baccin ta , ransa yayi sanyi da yaga tana bacci sosai haka , a hankali ya taka zuwa cikin ɗakin ,
Zama yayi a bakin gadon yana ƙarewa fuskarta kallo , ƙaunar ta na sake fisgar shi , gani yayi ta fi yi masa kyau idan tana bacci ,
Kamar motsi ya ji an taɓa ƙofar falon , dan haka ya miƙe ya fito yana dube-dube , sai dai bai kai ga ganin kome ba , tsayuwa ya cigaba da yi a harabar gidan ya zura hannu a aljihu yana tunanin zuci ,
"yana son zuwa Maraɗi ko domin iyayensa , amma tsoron abunda zai tarar a can ya hana shi samun ƙarfin zuwa ,
Ciki ya koma inda ya tarar wayar sa da ya ajiye akan kujerar da ya tashi tana ƙara ,
Zuciyar sa ta buga da ƙarfi ganin Mai ƙiran nasa da ba kasafai ta cika yin ƙiran waya ba , sai fa da Babban dalili ko kuma idan shi ya ƙira domin gaishe ta ,
"Adda Ammi ce Babbar yayar su baki ɗaya da take aure a jahar Damagaram ,
Har wayar ta tsinke bai ɗauka ba saboda fargaba , amma bai jinkirta ba ya bi bayan ƙiran da hanzari ,
**
Daga cikin motar ƙirar Honda Accord da take tafiya da matsakaicin gudu akan titin Boulevard Mali Véro ,
Hamshaƙan matan su biyu masu kamanni ɗaya suke zaune , ɗaya tana daga gaba Babbar tana baya , ta gaban ta ɗan waiga kaɗan , lokacin da direban ya karya kan motar zuwa cikin unguwar da take gefe da su ,
"Adda Ammi kadda kice mini ke ma Youssoufa bai ɗau ƙiran ki ba ?
Zata yi magana wayar ta ta ɗau kiɗan shigowar kiran sa ,
" ga shi ya biyo sawun ƙiran ,
Tace ba tare da ta ɗaga ƙiran ba ,
Tafeeda wanda shi yake jaan motar ya juyo kaɗan kafin ya maida hankalin sa ga tuƙin yana cewa "ai ga gidan can ma mun iso Adda Ammi ,
Duk suka zubawa gidan ido ta cikin gilashin motar suna kallo ,bayan ya dai-daita tsayuwar motar , suna shirin fitowa lokacin da suka ga an buɗo ta ƙaramar ƙofar gidan a hankali an fito ,
Su dukkanin su wara ido suka yi suna kallon sa da Mamaki ,
" Mouhammadou ?
Tafeeda ya ƙira sunan sa da mamaki a muryar sa ,
suna ganin yadda yake dube-dube yana sauri , ya miƙa kan titin unguwar da babu kowa shal , sai fa giftawar motoci jifa-jifa , ba tare da shi ya gan su ba saboda gilashin motar da yake da duhu ,
Shiru ne ya gifta tsakanin su , kafin Ubbo ta ce
"Tafeeda ka ce mouna babu wanda ya san da tabbatuwa lamarin nan sai kai ɗai ? Sai kouma mu da yanzou ka taho da mu , to Yaya anka yi mouhammadou ya iso nan ? Ko kouwa shi Youssoufa ya ƙiraye shi ?
Cike da nazari Tafeeda ya nisa ,
"Adda ni bansan kome game da wanzuwat shi ba , wataƙila Youssoufa ya ƙiraye shi , sai dai nafi zaton zuwan kan sa yayi ɗauke da wani ƙudiri nashi na daban ,
Duk suka sake yin shiru a motar , bayyanar Mouhammadou a boyayyen gidan Youssoufa na sirri ya sanya su a ruɗani ,
Bayan iyayen su da suka san maganar zaman Youssouf da mace har ma da ɗiya ba ta aure ba a ta bakin wasu mutane ,
Tafeeda shine mutum ɗaya tal da yasan haƙiƙanin gaskiyar lamuran , shine kuma ya yi ta ƙoƙari wajen ganin ya wanke Youssouf , ya dunga neman Youssouf da ya dawo su fuskanci matsalar su maganceta tun kafin duniya ta ɗauka .
Amma daga baya sai Youssouf yaƙi ba shi haɗin kai , wannan dalilin ne ma ya sa shi dole ya samu yayun Youssouf ɗin Adda Ammi , da Ubbo da su ma suke cikin tashin hankali jin cewa ɗan uwansu yana can America tare da karuwa da 'yar su ,
Shi yayi musu bayanai na haƙiƙanin gaskiyar kome cewa ba fa zaman dadiro Youssouf yake yi ba amren yarinyar yake yi daga ƙasar Nigeria wacce kuma ƙanwace ga ainahin uwar yarinyar da ya yiwa ciki ba ta hanyar aure ba ta kuma rasu a wajen haihuwar 'yar .
Ba ƙaramin baƙin-ciki suka shiga ba da jin irin ta'asar da ɗan uwan su ya aikata , har kuma yake da tsaurin idanun cigaba da yin yadda ya ga dama ,
Dan haka suka tsaida shawarar muddin Youssouf ɗin ya dawo su zasu yi takakkiya zuwa gidan da ya ɓuya yake yin rashin gaskiya ,
su kuma sanya dole ya saki amren yarinyar da yake riƙo tare da haɗa ta da ɗiyar su koma da ita can ƙasar su ,
su basa yadda ya gurɓata musu sunan zuri'a da masarautar su , ba kuma zasu amince ya kawo musu baragurbin ɗiyar sa ba , bare wata matar da bata da masauƙi a tsakanin su ,
wacece ita da zata zama sanadin ɓacin ran iyayen su , ta kuma samu damar zama matar ɗan uwan su Yarima sarkin watarana ??
Adda ammi ta ɗau wayar ta tana sake ƙiran layin Youssouf dai-dai lokacin da taxi ɗin da Yakaka tayi shata , ya ajiyeta a ƙofar gidan ta bashi kuɗin sa ,
Ta kama hanyar shiga gidan hannun ta riƙe da kulolin abincin da ta dawo da su daga asibiti , da kyar take taku saboda tsabar gajiya da bacci da ya cika mata ido ,
Adda Ammi tana jin Youssouf ya ɗaga wayar bata tsaya amsa gaisuwar sa da yake yi mata ba cikin dakakkiyar muryar ta tace da shi ,
"Youssoufa ga munan ƙofar gidan ka , ka hito ka yi mouna jagora ,
Da 'yar ruɗewa cikin muryar sa lokacin da yake miƙewa yana barin abincin da ya fara ci yace
"Adda ai bani gida maraɗi ba kouma na tahoue , ina Niamey ne wajen aikina ,
"Na sani ƙofar gidan ka na niemey ɗin nake magana ko kouwa baka hitowa ka mouna jagora sai mu shiga da kanmu ?
Fitowa yayi hankalin sa a tashe ya nufi ƙofar gidan ko takalma babu a ƙafarsa ,
A harabar gidan ya ci karo da Yakaka wacce take shigowa , kallon juna suka yi kowannen su ransa a ɓace , ya gota ta kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan idanunsa suka sauƙa akansu duk ukun suna fitowa daga motar ,
Yawun bakin sa ya ji ya ƙame , ya rasa halin da yake ciki takamaimai , ,
da murmushin yaƙe ya ƙaraso gaban su , ya ɗan sosa ƙeya bayan ya rage tsawo ya shiga gaishe su ,
Sama-sama suka amsa suna binsa da kallo ganin yadda duk yake a firgice da alamun rashin gaskiya ,
"Bismillah,
yace da su yana yin gaba , ba tare da ko sau ɗaya ya dubi sashin da Tafeeda yake tsaye ba saboda gudun yadda zata kaya a tsaƙanin su da ya riga ya san cewa shine ya haɗo masa wannan gangamin ,
Da shigar su harabar gidan yayi nufin kai su sashin sa , sai dai tsintar maganar Adda Ammi yayi tana tambayar sa ina matar gidan ?
Cikin dakiya ya waigo , "tana ciki , yace a takaice yana kallon ta ,
"to ai wajen ta yakamata mu shiga duk muyi maganar da take tafe da mu ,
Ɗan jim yayi yana kallon ta , cikin shakku , sai dai yadda tayi maganar cikin lumana ya sa ya wuce gaba zuwa sashin Falmata suna bin bayansa ,
Zuciyarsa cike da fatan samun masalaha akan koma menene , fatan sa Allah yasa zuwan su ya gyara kome ,
Suna shiga falon suka tarar da Yakaka a zaune daga ƙasa tana hutawa tare da jiran shigowar Falmata da take zaton ko tana wajen Youssouf zuciyarta ɗauke da ƙudirin fara sanar mata da kome a yau ,
Shigowar su ya sa ta miƙe , fuskarta kadaran-kadahan ta gaishe su ,
Shi Tafeeda bai amsa ba , Ammi da Ubbo ne suka amsa a taƙaice suna ƙare mata kallo sama da ƙasa , zuciyar su na shaida musu wannan me kama da asbinawan ce ta sa ɗan ouwan su kaucewa hanya ??
Ratsawa tayi zata wuce ta bar su Ubbo ta dakatar da ita ,
"baiwar Allah dawo nan , kou ba ita ce matar gidan ba ?
ta juya akalar tambayarta ga youssouf
Da sauri Youssouf ya girgiza kai ,
"Ba itta ce ba ,
To ita wannan wace ?
Adda Ammi ta tambaye shi
a ciki ya amsa ,
"yal ouwatta ce ,
.ubbo tace
"itta ina tai ?
" bacci take , adda domin Allah muyi duk maganar da zamu yi ni da ku ,
"Ke
Adda Ummi ta buɗe murya wajen ƙiran Yakaka wacce har lokacin take rakaɓe daga gefe a tsaye ,
"ki tai ki tado mouna da 'yal ouwakki ku taho tare ,
Yakaka bata san me suke nufi ba hausar tai mata nisa dan haka ta tsaya tsam tana kallon su ta ƙasan ido ,
Youssouf da yanayin Ammi ya fara ɗarsa masa tsoro a rai , ya nunawa Yakaka ɗakin da Falmata take ciki ,yace
" Fatima tana ciki ki ƙira ta ,
A hankali Yakaka ta tura ƙofar ɗakin Falmata da har kawo yanzu baccin ta take yi ,
Ta ƙarasa bakin gadon a hankali ta dafa ta ,
"Falmata , Falmata , ta ƙira sunan ta tana ɗan jijjigata ,
Buɗe idanunta da suka yi mata nawi tayi , sai kuma ta ware su da sauri ta miƙe zaune tare da riƙe hannun Yakaka da take hango ta dusu-dusu ,
" Yakaka kece ? Ina Mama ? Ya jikin nata ? Ta samu sauƙi ? Tayi bacci ? Bata yi kuka ba ko ?
" jikin Mama da sauƙi na baro ta tana bacci , Yanzu muje falo kina da baƙi ,
" Baƙi ?su waye ? mu babu wanda yake zuwa wajen mu ai ?
"wasu mata ne ina ga ƴan uwan sa ne ,
Yakaka tace tana miƙewa tsaye ,
A hankali Falmata ta kai hannu ta laluɓi gilashinta ta sanya a fuskar ta , bayan ta ɗora hijabi akan doguwar rigar jikinta ,
Tare suka fito falon yatsunsu cikin na juna ,
Har ƙasa Falmata ta durƙusa ta gaishe da matan da ta tarar da ƙamshin su ya cika falon , sannan ta gaishe da Tafeeda ,
Sai tayi shiru jin yadda suka amsa mata a cike da ginshiri ,
"wannan ce matar taka ? Uwar 'yar taka ? Wannan kuma 'yar uwarta ?
Adda ummi ta tambaya tana nuna Falmata da Yakaka da hannun ta a walaƙance ,
"Eh , ah ah , eh ita ce Matata Fatima ,
Kallon sa su duka biyu suka yi jin yace "eh ya kuma ce "Ah ah ,
Gyara zama tayi ta matso kusa daga kan kujerar ,
" ke yarinya kina jina ?
Falmata wacce ta fahimci da ita ake , ta gyaɗa kai a hankali bayan ta fuskanci inda take iya ganin Matar da take mata magana sosai ,
" daga ina kike ? Su waye iyayen ki ?
daga Falmata har Yakaka zuciyoyin su suka buga , Sai Falmata ta sake matso Yakaka tana riƙo Hannun ta ,
A hankali Yakaka ta sauƙe ganin ta akan Adda Ammi ,
" Mu 'yan gudun hijira ne a ƙasar Nigeria, kuma iyayen mu duk sun rasu ,
Ƙutawa tayi tana gyaɗa kai cikin buɗaɗɗiyar Muryar tace " kin san Youssouf wanene ?
Girgiza kai Falmata tayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 69 Chapter of 103