Share this page
tirsasawa , Takurewa tayi ta sanya fuskar ta tsakanin ƙafafun ta , sanyin ruwan da ya ɗan sake dawowa da ƙarfin yana ratsa ta ta hanyar jiƙa kayan jikin ta . Assalamu Alaykum . Gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gare ku baki daya! Nagode.           [10/3, 2:48 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 35 Doctor hamza ba tare da ya dubi sashin da Yakaka take tsaye ba yayi wucewar sa yana waya da ɗaya daga cikin abokan aikin sa na nan Asibitin Maiduguri wanda ya masa ƙiran gaugawa sakamakon neman sa da ake a asibitin jahar saboda wani aiki na gaugawa da za'a yiwa wata mata da take halin buƙatar taimako , Kan ta a ƙasa tana satar kallon gefen fuskar sa , zuciyar ta cike taf da addu'o'i iri-iri , ta wuce ta ƙarasa wajen maigadi wanda ya tattara dukkanin hankalin sa akan ta , Sama-sama ya amsa gaisuwar ta ya ɗora da tambayar ta wajen wa ta zo ? Wajen Rahima na zo . tace da shi tana fatan kar ya hana ta shiga gidan saboda wannan maigadin baƙon fuska ne ba wanda ta sani a da ba ne  Kallon tsanaki yayi mata bai hango wani alamun rashin gaskiya a tattare da ita ba , Ki shiga tana ciki . Yace yana komawa kan ɗan bencin sa na zama . Hamdala tayi bayan ta yi masa godiya ta taka tana nufar cikin gidan da bai zamto baƙo ba a gareta , tsarin sa bai sauya ba illa zuciyar ta da take cike da taraddadin hasashen da irin fuskar da Mutanen gidan zasu ƙarbe ta da hakan ya hana ta kuzarin isa cikin gidan cikin ƙanƙanin lokaci Da duk takun ta guda kunnuwan ta suke sake kusanto mata tashin muryar ta suke,  da bata riga ta manta amonta ba ko dan ita ɗin tana daga cikin mutanen da suka gwada mata ƙauna a duniyar ta ne ? Hajja dan dai kince kin manta fuskar maman ta ne amma idanunta sak na mamar ta ne , sosai tana ɗibar yanayi da mamarta sai dai ko kamannin Baban ta yafi ƙarfi , ai babyn nan ƙarshe ce a kyau wallahi kamar naje Niger na kwato ta nake ji , Allah sarki baby na Allah dai ya baki lafiya , yasa a dace wajen neman maganin nan , Allah kuma ya jiƙan Mamar ki me kirkin nan . Da murmushi hajja ta amsa da Amin Amin Rahimatu     A hankali ta sauƙe idanun ta a bayan Rahima lokacin da ta ƙaraso ƙofar falon , wacce ta juya baya tana ƙoƙarin saƙala tangamemen hoton Mama cikin jerin hotunan da suke killace a jikin bangon inda aka tanadi sashi na musamman domin ajiyar hotuna , Ɗaya daga cikin hotunan da hajja ta zo da su ne da ta kai aka wanke mata shi zuwa Babban takardan hoto aka yi mata gidan sanya hoto na musamman tare da sanya shi a cikin gilashi . Ganin ta ta mika kan hoton , fuskar da ta gani jikin hoton ya sauya bugun zuciyar ta nan take , a hankali take wara idanun ta tamkar wacce ta warke daga makanta , kamar yadda take jin zuciyar ta tana buɗewa da wani irin yanayi ƙaƙƙarfa , ƙofofin gashin jikinta baki ɗaya suka buɗe suna tsattsafo da gumi  , Taku ta fara yi tana ƙara kusantar hoton da zuciya da tunaninta baki ɗaya suka tafi ga fuskar dake jikin sa. Haƙiƙa bata taɓa ganin ta ba amma kusancin dake  tsakanin uwa , mahaifiya da abunda ta haifa daga cikin jikinta ya wuce wasa ya kuma wuce  hankalin duk wani me tunani ƙauna ce me rassa da take yaɗo a dunƙule da babu me iya ganin zurfn ta bare a iya hasaso iyakar ta  , Bayan Rahima ta zo daf ta tsaya tana sake nutsar da idanun ta akan fuskar mama wacce tayi ƴar kyakkyawar dariya a hoton. Hajja wacce ta miƙe tsaye daga gefe tayi sororo tana bin Yakaka da ido kafin tace Ke , Ke , Ke baiwar Allah lafiya kike kuwa ? Zaki shigo mana gida haka sangam-sangam babu sallama bare neman izni ? Kin kuma zo kin yi tsaye ƙere-re uwa wacce ta haɗiyi taɓarya ince ko baki da lafiya ne ? Rahima wacce bata ji tsayuwar Yakaka kusa da ita ba , saboda raggon taku marar sauti da Yakaka tayi a yayin isowa wajen , ta ɗan waiga sashin hajja lokacin da take gama sarƙafe hoton a inda ya dace tare da janye hannun ta daga jikin hoton ta waigo tana cewa Hajja da wa kike magana ne ? Fuskar ta ce ta kusan haɗuwa da ta Yakaka da ya sa ta ɗan jaa baya Bismillahi waye ha... Kalmomin ta ta haɗiye muƙut , maƙwallon maƙogoron ta ya motsa kamar yadda idanun ta suka firfito da mabayyanin firgici baro-baro a cikin su ,   Shekarun da suka raba haɗuwar fuskokin su basu yi yawan da zasu sa su mance da kamannin juna ba . Ya-Ya-Yakaka ke-ke kece ?? Rahima ta furta muryar ta tana makyarkyata kamar yadda kwakwalwarta take hautsinewa da kokonto , Yakaka wacce zuciyar ta ta zaƙu da son samun tabbaci akan gudan jinin ta , ba tare da ta janye idanun ta daga kan hoton ba ta lalubo hannuwan  Rahima ta damƙo su da ƙarfi , Rahima, Rahima ni ce  ,   Ta zarce da tambayar ta wannan ,?  wannan Mama ce ? Ƴa ta Mama ?    Rahima wacce tunanin ta ya gama dunƙuluwa waje guda , ta fisge hannuwan ta da matuƙar ƙarfi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana nufar ƙofa , kafin ta ƙarasa ficewa ta ɗaga murya tana sanar da Hajja . Hajja ki gudu wallahi Fatalwar Maman Mama ce wannan . Turus hajja tayi tana bin bayan Rahima da kallo , kafin ta sake waigo Yakaka wacce bata bi ta kan kalaman Rahima ba tamkar ma dai bata kai ga fahimtar me kalaman Rahima ke nufi ba . Ta saka hannu ta ɗago Hoton ta ciro shi daga mazaunin sa , tare da riƙe shi da hannuwan ta duk biyu , tamkar ta riƙe yar jaririyar ta . Kai tsaye ta nufo Hajja da hoton , fuskar ta da wani irin yanayi na chakuɗuwar tsantsar farinciki da kuma fargaba tace Wannan ƴata ce ko ? Mama ce ko ? Kafin ta ƙaraso hajja ta juya da ƴar sassarfa tana ɗingisa kafafun ta da basu cika lafiya ba , Un-un-un ƴar nan , ni kuwa ina zan sani ? Mutum dai baya ƙin ta Mutane wai ance da ɓarawo ya gudu  , Bi Rahima can dai kin tambaye ta Dan Allah . Garam ! Hajja ta rufo ƙofar ɗakin ta . Saƙare tayi a tsaye tana son harhaɗa tunanin ta domin ta kai ga fahimtar meyasa ta ga kamar ana gudun ta ? Ashe girman laifin ta har ya kai ya sa ta zama abun gudu a wajen mutane ?  Falmata ina Falmata ? Ta san idan kowa zai guje ta a duniya a zare Falmata a cikin su , Falmata baza ta taɓa gudun ta ba , ina take ? Ta juyo da nufin fitowa ta nufi sashin Baba , sai ga Rahima tare da wani mutum wanda bata kai ga sanin sa ba . Mallam Kabir ga ta nan , ta nuno Yakaka wacce take tsaye ƙiƙam rungume da hoto . Dan Allah kana ganin ta ? Ina ganin ta mana Hajiya Rahima , ai wannan Mutum ce , ba Fatalwa ba ,  hala an samu akasi ne wajen jin wani labari akan ta ? Ke baiwar Allah wacece ke ? Daga ina kike  ? Me kuma kika zo yi nan?  Zuwa lokacin Yakaka ta fara hasaso abunda yake faruwa , dan haka fuskar ta na bayyana sabon alhini ta matso tana cewa . Rahima ni ce Yakaka , ba Fatalwa ba ce ni , ban mutu ba , waye yace na Mutu ???? Ina Falmata ? Ba tare da Rahima ta ce ƙala ba , bata kuma yadda ta ƙarasa kusa da Yakaka ba ta sake juyawa da ɗan gudu ta nufi sashin Baba , da daman daga can ɗin take shine ma ya haɗo ta da Mallam kabir ɗin da ta zo ta same su tare suna ganawa , Tana cikin yiwa Baba bayanin dawowar Yakaka ƴar gudun hijira wanda suke da tabbacin mutuwar ta a wajen haihuwa shekaru kusan shidda da suka wuce , Sai ga Mallam kabir tare da Yakaka wacce take biye da shi  . Da ido Baba ya bisu bayan ya amsa sallamar su ,  har suka ƙaraso cikin falon inda Yakaka ta nemi waje daga can gefe guda ta durƙusa bisa guiwowin ta , Mallam kabir bai zauna ba yayi bankwana da prof tare da juyawa kan takun sa ya bar wajen . Prof bai yiwa kamannin Yakaka sani na sosai ba amma tabbas ya shaida fuskar ta , saboda ya taɓa ganin ta a farkon zuwan ta gidan sa , sannan a ɗan taƙaitatcen zaman da tayi a gidan tana zuwa gaishe shi lokaci-lokaci . Babu alamun firgici a tare da shi yake amsa gaisuwar Yakaka , wacce kan ta ke a sunkuye . Cikin nutsuwa irin ta manyan mutane da suke da tarin ilmi ya soma da tambayar Yakaka daga ina take ? Me kuma ya faru da ita tsawon shekarun da tayi bata nan ? Bai shigo mata da batun labarin mutuwar ta da yake tabbatacen Al'amari ba a wajen su a tsawon shekarun da tayi bata nan . Tambayoyin sa suka fargar da Yakaka tare da tuno mata da Malama Maryam da ta baro can a layi fiye da mintoci ishirin , Wacce ta san zata taya ta fuskantar mutanen ta da tarin laifukan da suke kan ta , Tare muke da baƙuwa Baba , a min iznin na shigo da ita . Je ki shigo da ita babu kome . Bata jima ba suka dawo da tare da Malama Maryam wacce har ta fara shiga halin damuwa ganin lokaci ya ɗan jaa batare da ta ga dawowar Yakaka ba . Cikin nutsuwa da kamalar da Allah ya hore mata Malama Maryam ta gaishe da prof , sannan ta gabatar da kan ta a matsayin Malamar Yakaka wacce ta ɗau darasi a wajen ta tsawon shekaru biyar da ɗoriyar watanni , a garin Abuja , daga haka ta tsagaita . A hankali muryar Yakaka ta fara tashi tiryan-tiryan take bada labari tun daga irin Gadar zaren da Samy baby ta haɗa mata har kawo ranar barin ta Maiduguri da ta sanyata ta tsallake ta bar Jaririyar ta a ranar da ta haife ta , da zummar zata kai ta Abuja wajen mahaifn ƴar ta suyi aure ta dawo ta ɗau yar da ƙanwar ta . Wacece ita Matar da kika bi ? Menene  dangantar ku da ita ? Tambayar Prof ta katse Yakaka . Shiru Yakaka tayi na ɗan wani lokaci , tunowa da tayi da irin rufin asirin da Doctor Hamza ya yi mata a farkon kawo ta gidan ya bayyana ta a matsayin ƴar gudun hijirar da mijinta ya mutu ya bar ta da ciki ,  Ƙaramin tunani irin nata tare da mummunar ƙaddara suka sa ta sanya ƙafafu ta hamɓarar da irin tarin rufin asirin da Allah ya yi mata a tun wancen lokacin da hakan ya jawo a yau ita da kanta zata tona binnannen sirrin nata  . Domin a yanzu ta ɗau alƙawarin baza ta sake yin ƙarya ba , dan haka idanun ta na tara ƙwallar nadama da irin laifin da ta aikata ta koma baya , kan haƙiƙanin gaskiya ta ɗorar da labarin ta tun daga farkon shigowar su birnin Maiduguri zaman su a sansanin su, da zaman da suka yi  a gidan Madam saly , shigowar Biyamuradi rayuwar ta wanda ta ambace shi da "sojan wata ƙasa ," har zuwa zaman ta a Abuja tare da dawowar ta a yau bata boye duk wasu gaskiyar da yakamata ta bayyana su ba ga mutumin da shine na farko da suka samu mafaka mai cike da karamci da tarin ƙauna a ƙarƙashin sa , Shiru ne ya gifta na tsawon wasu mintoci , da hakan ya bada dama ga malama Maryam ta ɗora da sake bada kyakkyawar shaida ga Yakaka , yadda ta jajirce wajen neman ilmi haɗi da yadda ta cije tare da taimakon Allah ta hayewa faɗawa ga rayuwar karuwanci kamar yadda ita samy baby ta so da ta aikata . Mamakin mazajen guda biyu shi yafi kome yin tasiri a tunanin Prof, da har ta kai shi ga gaza cewa wani abu . A zahiri yau ta bayyana a gareshi cewa daga Ɗan sa Hamza har shi wancen mutumin da ya zo har nan gurin sa ya ƙarbi auren ƴa a wajen sa duk ƙarya suka wanzu tsawon lokaci suna gindaya masa akan rayuwar marayun yaran su biyu . Wanda a zahiri ƙaryar ta su ta cutar matuƙa gaya , ba su kuma kyauta ba . Ƙaryar da Hamza yayi ita ta tokare ta hana shi yayi yunƙurin nemo yarinyar ya dawo da ita ta zauna ƙarƙashin kulawar sa kamar yadda a tun ranar da ya karɓe su ya alƙawartawa kan sa , wanda hakan ba wani abu ne me wahala ba kasantuwar sa babban Mutum , amma sai hamza yayi masa ƙarya cewa ta mutu har ma yayi jana'izar ta a asibiti , wanda a zahiri tun lokacin  shi Hamza yana da masaniyar guduwa tayi , ko me yasa yayi hakan oho ! Sai kuma shi wancen mutumin Niger da ya riga ya san irin mummunan ta'asar da ya aikata na lalata tarbiyar yarinyar nan , amma kuma shine ya sake dawowa ya rufe shi a baibai tare da karɓe ɗiyar sa domin sake samun garaɓasa har aka ƙara masa da ƙanwar ta a matsayin mata duk a tafarkin ƙarya ?? Wannan wane irin son zuciya ne ? Meyasa ne gaskiya tayi ƙaranci ? Shin ƴan gudun hijara ba 'ya'ya bane ba ? Ba mutane ne masu ƴanci da galihu irin na sauran Al'umma ba ?  Da rayuwar su zata zam ba a bakin kome ba ? Za kuma a dunga yin walagigi da su cikin rashin kulawa da tozartawa , a maishe su ba a bakin kome ba , shin zaɓin su ne rabuwa da iyayen su , dangin su , garuruwan su ? Ko kuwa ƙaddara makamanciyar wannan bata iya faɗawa kan kowa ne ? Idan har ya tabbatar da duk labaran da suka bayyana a gare shi gaskiya ne , babu shakka zai yi tsayuwar daka cikin rayuwar ƴan gudun hijirar nan guda biyu , zai zama katanga tsakanin su da duk masu shirin tozarta su a sannu kuma zai ɗau hukuncin da ya dace akan Hamza da ɗan mutan Niger . Muryar Malama Maryam ita ta sanya shi nisawa , ya maida ganin sa kan ta . Baba ayiwa Yakaka hakuri a yafe mata babu shakka tayi laifi tare da zallar wauta amma domin Allah a ɗau hakan a matsayin kaddara a cigaba da godewa Allah da ya sa har ta dawo gida lafiya ba tare da wani mummunan lamari ya auku gareta ba , Babu kome baiwar Allah mun gode ƙwarai Allah ya saka miki da Alheri kan yadda kika kula da ita , kema Allah ya duba miki naki iyali , Allah ya ƙara mana yawaitar irin ku cikin Al'umma masu taimako domin Allah . Cikin jin daɗi Malama Maryam ta amsa da Ameen . Ƴar boyayyar Ajiyar zuciya Yakaka ta sauƙe ganin yadda Alamu ke bayyanuwa yadda take zaton tsanantar lamarin nata duk bai kai haka ba , A hankali ta ɗora idanun ta kan Rahima wacce ita ma kallon ta take , suka haɗa ido kafin Rahimar tayi mata guntun murmushi marar sauti . A yanzu hankalin ta ya kwanta ta kuma amince Yakaka ce da gaske ba Fatalwa ba  . Ita ma ta mayar mata da martanin Murmushin , ƙaunar junan su tamkar a jinin su take , duk da tarin abubuwan ƙi da Rahima ta san yakaka ta aikata su a yanzu , hakan bai sa ta ji kamar ta tsane ta ba . Kalaman Prof ya sa Yakaka sake nutsuwa ta mayar da hankalin ta kan shi , Bisa ga doron kuskuren da kika riga kika aikata su Abubuwa biyu zuwa uku sun faru , Na farko labarin mutuwar ki , a gare mu tuntuni kin mutu tundaga ranar da kika gudu kika bar 'yar ki . Na biyu shine zuwan da mutumin da ya ƙira kan sa mijin ki uban abunda kika haifa yayi , Na ukun su shine tafiyar sa da yayi da 'yar sa tare da auren ƙanwar ki a lokaci guda da ni da kaina nayi waliccin auren a nan falon nan na bada auren ƙanwar ki Fatima ga mijin ta uban 'yar ki na kuma ɗanka masa ita suka tafi tare ƙasar su niger tare da rikiyar Hajja me wurya . Da ace Yakaka ta taɓa sanin yadda ciwon Ajali yake da babu shakka zata iya cewa shine ya dirar mata a lokacin saboda wani irin abu me kaifi da ta ji ya taso mata daga ƙasan mara ya zo ƙirjin ta ya tokare ta , Muryar ta a shiɗe ta wufto kalaman da suke kan harshen ta ta watso su ga Prof idanun ta tsaye ƙem a kan fuskar sa Falmata ce tayi aure da Baban Mama ? Da sake tabbatarwa Prof ya amsa mata da Haka kalamaina ke nufi. Abunda take jin ne ya watsu a cikin jikinta ya barbazu tamkar an watsa mata wuta kafin ya sake dunƙulewa a maƙogoran ta ya tsaya , Yaa Allah , Yaa Allah , Allah na tuba kar laifin da na aikata ya shafi Falmata , Allah ka dawo min da Falmata , Allah ka... Mul-mulan hawayen da suka fara ƙwaranyowa daga idanun ta tare da fashewar ƙullutun da yake wuyan ta shi ya hana ta cigaba da magana illa kukan da ta fashe da shi marar ƙarfin sauti , Kuka ne irin na mutumin da ya ke a halin ɗimuwa tare da nadama kuka ne irin na ba yadda zan yi , kukan neman taimako , Baki ɗayan su irin kukan da take ya taɓa zukatan su , Musamman Malama Maryam da Rahima , A bangaren Prof duk da cewa ya ji tausayin ta amma ya bar ta da hakan a matsayin sakamakon laifin da ta aikata . A hankali Rahima ta ƙarasa inda take ta sanya hannu ta dafa ta , Kiyi hakuri Yakaka tashi mu shiga cikin gida , ki bar kuka hakan , Miƙewa tayi ta fara taku ba tare da ta cewa kowa kome ba ta wuce , Malama Maryam ta rissina ta yiwa Prof sallama tare da shaida masa gobe da sassafe zata kama hanyar komawa gida Godiya ya sake yi mata , suka rabu suna bin juna da kalaman fatan alheri . Bayan fitar su bai jinkirta ba ya ɗau wayar sa ya nemo lambobin wayar Doctor Hamza , Fitowar sa kenan daga ICU inda ya jonawa marar lafiyar da aka ƙira shi domin ita wasu na'urai ya kuma sake duba ta sosai kasancewar ya ƙware sosai wajen gano tare da bada taimako akan cutar da take damun ta na dajin bakin mahaifa , Mutanen da suke ƴan uwa ga marar lafiyar suka taso caa su kusan rai shidda suna tambayar sa yanayin jikin nata  , Nan dai ya kwantar musu da hankali tare da sanar musu da insha Allah zasu yi bakin ƙoƙarin su, su kuma su taya su da addu'a ya ratsa su ya wuce , Ya ji lokacin da ɗaya daga cikin su tace tunda mun ji yanayin da take ciki sai Maman Bulama ta koma gida ta yi girki ta kawo kuma ta haɗo wasu kayan da za'a iya buƙata , Maa ki mata bayani yadda zata gane sosai dan ke ce kika iya maganar su ta kurame , Da hannu suka yafito wata mata wacce take zaune a ƙasa daga gefe . Da sauri ta taso ta ɗan russuna daga gefe , Maa tayi mata bayani da hannu cikin maganar kurame , Cikin sauri take gyaɗa kai alamun tana fahimta, Naira ɗari biyu ta zaro daga jaka ta miƙa mata , ta sanya hanu biyu ta karɓa , Ta mata alamar cewa kuɗin mota ne Ita ma ta gyaɗa kai kan cewa ta gane Har ta juya ta sake dawowa , Tayi musu alamar tambaya tana nuna ɗakin da marar lafiyar ke ciki . Fuskar ta na bayyana Alhini . Amsa maa ta bata da hannu . Ta juya ta kama hanyar barin asibitin , Doctor hamza wanda ya gama amsa wayar prof da yake sanar da shi kan lalle ya zo yana son ganin sa daga zarar ya kammala abunda yake a asibitin , Ya mayar da wayar sa aljihu tare da juyawa da zummar komawa cikin ofishin abokin aikin sa da shi yayi ƙiran sa domin suyi sallama ya kuma gama yi masa bayani akan irin matakin da yakamata a ɗaura marar lafiya akai zuwa gwaje-gwajen da ya dace ayi mata  Ƙiris ya rage ya ci karo da matar da ta taho tana ta sauri , sannu Hajiya , Yace yana kaucewa yin karon su , a fisge ya dubi fuskar ta lokacin da take gota shi ba tare da ta amsa ban hakurin da yayi mata ba Cak !  Ya tsaya , lokacin da kamannin ta suka yi masa yanayi da na wata da ya sani waye ? khaalty Rahima . Juyowa yayi da sauri da son sake ganin fuskar ta sosai , sai dai ta riga tayi nisa sai tashin hijabin ta ya ke iya gani wanda ya cika da iska saboda saurin da take zabgawa . ***** Daga bakin ƙofar falon Yakaka ta zame ta zauna , tana wani irin kuka ciki-ciki , a halin da take jin zuciyar ta a ciki babu abunda take fata irin kome da ta ji ace a mafarki ne , bacci take yi ta yi wannan mummunan mafarkin , ta gwammaci ace ta buɗi ido ta ga kan ta a gidan samy baby , kai ta amince kome ya faru da ita , da dai dawowar ta Maiduguri ta tarar da wannan mummunan labarin da ya kassara duk wani guntun ɗoki da mararin sake ganin wani nata a duniya , Aure , wai Aure da Falmata da mutumin da ya yaudare ta ya cutar da ita , ya lalata mata rayuwa tare da bar mata taɓon da har abada ba zai gogu ba , ? To wai ma ina ya tafi mata da ƙanwar ta ? Kamar ta ji prof yace ya tafi da ita  Ina ya kai ta ? Mutumin da ya saba yin manyan ƙarya da yaudara irin haka kome ma zai iya yi , ina suke ? Kai zata iya barin kome ya wuce ya zama ba kome ba amma banda zaman Falmata tare da wannan mayaudarin domin shi ɗin ai guba ne, dafin sa kuma ya fi na maja-ciki in yai sara . Ɗaga sautin kukan ta tayi tunowa da ta yi da miskinancin ƙanwar ta , Wanne irin hali ta kasance a ciki lokacin da labarin mutuwar da aka ce tayi ya riske ta ? Wataƙila tundaga lokacin bata sake farin-ciki ba , yaya rayuwa ta kasance mata bayan bata nan ? Wanne irin zama take da wannan macucin mayaudarin ? ƙwarai ta gaza a wajen bada kariya ga Falmata maimakon haka ma ta zama sila na faɗawar ta a hatsari , ƙwarai hatsari mana aure da mutumin da ba'a kai ga sanin asalin sa na haƙiƙa ba , A hankali Hajja ta murɗa makulli ta fito daga ɗakin da ta shige " jin tashin muryoyin su Rahima da Malama Maryam da suke faman rarrashin Yakaka , da sautin kukan ta ya karaɗe falon Oh ni Hauwa'u naga ta kaina ! yanzu ke 'yar nan me ya miki zafi haka a duniyar nan da zaki zo ki faɗi a nan shakwaɓ , kina rusa ihu ya Amaryar da Angon ta ya mutu daren buɗan kai ?  Ganin babu wanda ya kula ta ya sa ta samu waje ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon , ta cigaba da cewa , Rahimatu , ince ko dai an fitar da Fatalwar ? Kar sai mutum yana ƙailula ya farka ya gan

Chapter 53 of 103