Share this page
a ido , Mts' ana raba ki da kiwon awaki kina kyalla ta haihu , wanne maganin ido kuma ?? Wannan maganin gyara tsakanin ku ne ke da mijinki , idan kika daure da shan su suma zasu taka rawar gani wajen karkato miki da hankalin sa . Ni zan dunga sha ko shi ? Nifa  bangane bafa hajja . Yo ina kuwa zaki gane ana nuna miki gabas kina bauɗewa yamma , kina girma kina sake shiga daji ., maganin mata ne . Maganin mata ? Ta maimaita da sigar tambayar Eh hajja ta amsa tana dangwara mata kullin maganin a hannu , Karɓi ki sa a cikin akwatin tafiyar taku , da madarar ruwa ko ta gari ake shan su , Taɓe baki falmata tayi , Tana ciro Envelop daga hijabin ta , Hajja ga hotunan Mama din an karɓo ɗazu Baban ta ya bata ta kawo min, Karɓar envelop ɗin tayi ta zaro ƴan madai-daitan hotunan Mama da aka ɗauketa kwanaki uku da suka wuce da zummar hajja zata tafi da su Maiduguri ta kaiwa mutanen gida su ganta domin rabon su da ganin hoton ta tun tana ƴar shekaru biyu , Kai ɗanɗashi hotuna kuwa sun yi kyau kamar a ƙirata ta amsa tar-tar da su , ƴar wayayyar fuskar nan ta fito ,  ai kin ga hakan yafi a tafi musu da hoton ta su ganta ko dan yadda Rahima da Alhaji suke begen ganin ta . Murmushi tayi , jin daɗin Hajja ta yabi 'yarta Hajja kar ki manta dan Allah da saƙon gaisuwata , ga Baba , Yaya dakta , Rahima , kai kowa da kowa dai hajja , ki miƙa musu gaisuwata tare da fatan alkhairi . Insha Allah kuwa duk zasu ji Falmata , kin dai ji duk abubuwan da na faɗa miki ko ? Eh duk naji Hajja , To ki dai yi amfani da cewa ta , idan Allah ya yarda za ki ga amfanin sa . To Hajja . Ƴar dariya Hajja tayi,  to Allah shi sa idan kun dawo nayi farin ganin gamdakatar da sabon ango ko kuwa sabuwar ƙawa . Falmata ta yunƙura ta miƙe tsaye , tana cewa Aina kenan Hajja ? Ko daga can za'a kawo miki ɗan turawa ? kai kai kai Hajja baki da dama . Saƙare Hajja tayi bakinta buɗe , sai kuma ta gallawa Falmata harara . Kinci gidan ku da sauyawa zancena launi , ƴar nema ai nasan sarai kina fahimta ta da gangan kike bauɗewa , oho ni dai na faɗa miki kowa rai yayiwa daɗi ai bayan me shi ne . tana ƴar dariya ta ƙarasa barin ɗakin , kalaman Hajja na kutsawa cikin tunaninta tana ɗora su a mizanin nazari . Washegari Da farar safiya direban da zai kai Hajja Nigeria ya iso , daman da shirin ta tsaf , dan haka babu wani jinkiri aka fito da kayanta aka sanya su cikin mota , Tare da rakiyar Biyamuradi , Falmata da Mama suka ƙaraso jikin motar sallamar bankwana suka yi , Hajja ta shige mota direba ya tada motar suka miƙa hanya Mama tana ɗaga mata hannu . Allah ya kiyaye hanya Hajja ta Falmata ta furta a sarari tana jin yadda kewar ta ke fara kamata , "sabo tirken wawa ', Muje cikki Fatima kafin zouwar le chauffeur mu tahi I'aéroport . Hannun ta cikin na Mama wacce take ta zuba surutu suka juya zuwa cikin gida , kai tsaye ɗaki ta shige ta zauna a bakin gado , tunaninnika suka yi mata dirar mikiya , kewar ahalinta na kassara duk wani karsashi nata , shekaru biyar ɗin basu zo mata da sauƙi ba , ba kuma sun rageta da kome ba wajen jin ƙauna tare da muradin sake ganin wani jinin ta a duniya bayan Mama , duk kuwa da cewa ita ɗin ta kasance daga cikin jajirtattun mutane masu yaƙi da damuwar su, tare da danneta su binne ƙarƙashin ran su , su yunƙura wajen gina rayuwar su a yadda ta zo musu , ba domin ƙarfin zuciyarta ba da tuni damuwar halin da ta tsinci kanta ciki sun kaita ƙasa . A hankali irin nata akwai hangen wani ƙalubale da take yi wanda take hasashen zai iya ɓullowa cikin rayuwar su ita da Mama , daga dangin Biyamuradi , wanda har kawo yau da Mama tayi shekaru a duniya da yake dai-dai da shekarun auren su babu wani dangi nasa ɗaya da ya taɓa zuwa wajen su , ya gan su .  Shi kaɗai suka sani , duk kuwa da yana ikirarin cewa yana da iyaye da danginsa makusanta , to ina suke ? Meyasa basu taɓa zuwa inda suke ba ko su su ziyarce su ? Shin menene aboye wanda su basu kai ga sani ba ? Tsakanin ƙarya da gaskiya wa ake yiwa wasan ƴar ɓoye a tsakanin su da dangin sa ?  Tabbas akwai lauje cikin naɗi . Sai dai koma menene a shirye take tsaf da taryar sa , zata yi kome domin ta bada kariya ga Mama , ƙuɗirinta bazai taɓa sauyawa ba muddin tana numfashi ita zata cigaba da kasancewa garkuwa ga Mama . Ya jima yana tsaye daga dokin ƙofar yana duban ta , a tsawon zaman su da shi da ita koyaushe yanayi ɗaya yake hangowa a fuskar ta idan bata san da wanzuwar sa ba a guri , "damuwa" tana da damuwa wanda yake danganta damuwar ta ta da kansa . Yana sane da cewa shi da ƴar sa sunyi kutse tare da yin karan-tsaye cikin rayuwar ta , ba kuma tare da suna amfanar mata da kome ba . Anya yana yi mata Adalci ?? Gyaran murya yayi da ya sa tayi firgit! Tana gyara zaman hijabin kanta , Fatima tasso le chauffeur ya zou . Jakar kayan su uku babbar ƴan kayan cimaka ne a cikin su da sauran ƙananan tarkacen matafiya , ƙananan biyun suturun su ne a ciki . A shirye suke tsaf , Falmata tana sanye da doguwar riga ruwan sararin samaniya me ɗan nawi ta ɗaura mayafin rigar akan ta ( tayi ɗankwali da shi )  da ɗan madaidaicin hijabin ta , takalman kafafun ta marasa tudu sun shiga da hijabin ta kalar ruwan hoda me haske ( baby pink ) Mama anshirya ta cikin ƴar riga iya guiwar ta da dogon wondo kanta rufe da hular saƙa me nawi mahaɗin safar ƙafar ta dake sanye da rufaffun takalman yara . Biyamuradi ya riƙo hannunta da shima yake shirye cikin shigar kwat da wando ( suit ) ruwan ƙasa , ita kuma ta riƙe ƴan ƴatsun Falmata , sun sanyata a tsakiyar su suka fito farfajiyar gidan , Biyamuradi ya kulle ƙofofin gidan bayan ya kashe duk wasu na'urori masu amfani da lantarki . tazarar ba wata me yawa bace tsakanin su da farfajiyar tashin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa ( Diori Hamani International Airport ) Dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka isa , bayan Bayan bin duk wasu tsare-taren da ya kamata matafiya masu tsallakawa ƙasashen ƙetere suyi tare da zaman jiran dai-daituwar jirgi da ya ɗauke su tsawon awanni uku da rabi , Biyamuradi Youssouf tare da Falmata da Mama suka bi sawun takwarorin su masu tafiya zuwa United States of America , a sawu na farko suka taka matakala ,  kafaɗar sa ta dama ɗauke da Mama wacce ta sarƙafo hannayen ta a jikin wuyan sa , ɗaya hannun nasa  ya zare daga cikin na Falmata da tunda suka shigo airport ɗin yake kaffa-kaffa da ita yana riƙe da hannun ta , duk kuwa da yadda take yawan mutsu-mutsu da hannun tana son zamewa amma ya ƙi kulawa bare ya bata dama , ya maida hannun sa bisa ƙugunta tare da matso da ita jikin sa , a hankali yace da ita , Fatima ki kulla da kyau ki saurari takun ƙafa ta bissa matakala muke , ba tare da ta amsa ba ta gyaɗa kanta , tana jin yadda tsikar jikin ta ke miƙewa . Cikin jerun kujerun first class suka yi mazauni akan kujerun su masu ɗauke da numbobin su da suke fuskantar juna , sai ɗan teburi a tsakanin su , bayan zaman su ya yunƙura tare da ɗaurawa Falmata seatbelt ɗin ta ya koma ya zauna tare da ɗaurawa Mama nata , bai tsimaya ba ya ɗaura nasa . A hankali ya kai hannun sa ya kamo hannun Falmata da yake kan teburin gaban su , ya damƙe hannunta guda cikin nasa dai-dai lokacin da zazzaƙar muryar shugabar masu dauke da alhakin kula da walwalar mutanen cikin jirgin "Chief flight Attendant ," ta karaɗe cikin jirgin ɗauke da sanarwa da take cewa :   “Ladies and gentlemen, this is Rose jackson and I’m your chief flight attendant. On behalf of Captain Mike Abraham and the entire crew, welcome Turkish Airlines flight  non-stop service from Niamey Niger Republic to Washington DC United States of America. Our flight time will be of  9hours and 11minutes. We will be flying at an altitude of  feet/meters 5612 miles . At this time, make sure your seat backs and tray tables are in their full upright position and that your seat belt is correctly fastened. Also, your portable electronic devices must be set to ‘airplane’ mode until an announcement is made upon arrival. Thank you.” Ta sake maimaitawa cikin yaren faransanci . ( Mesdames et messieurs, voici Rose Jackson et moi, votre agent de bord. Au nom du capitaine Mike Abraham et de l'ensemble de l'équipage, accueillez le vol sans escale de Turkish Airlines entre Niamey Niger Republic et Washington DC, États-Unis d'Amérique. Notre temps de vol sera de 9 heures et 11 minutes. Nous volerons à une altitude de 5612 milles. À ce stade, assurez-vous que vos dossiers de siège et vos plateaux sont dans leur position verticale maximale et que votre ceinture de sécurité est correctement bouclée. De plus, vos appareils électroniques portables doivent être en mode "avion" jusqu'à ce qu'une annonce soit faite à l'arrivée. Je vous remercie.") Girgizan da jirgin ya ɗauka shi yasa ba shiri Falmata ta sake ɗora ɗayan hannun ta akan na Youssouf tana ƙanƙame sa  hannayen su suka cure guri guda , kamar yadda zuciyoyin kowannen su ke ƙoƙarin jawo kusanci a tsakani . Idanun sa a kafe kan fuskar ta dake bayyana tsoro ɓaro-ɓaro . Cikin ikon Allah jirgin ya samu dai-daituwa a sararin subahana ya shilla da gudun gaske cikin tafiyar gaibu bisa iska a tsakanin sama da ƙasa . Nigeria Tafiyar kwana ɗaya da yini biyu ta sada Hajja da birnin Maiduguri , da la'asar sakaliya motar da ta kawota ta dakata a ƙofar gidan Prof . Kai tsaye ta sauƙa ta shiga gidan , tarɓa ta musamman ita da direban suka samu daga sabbin ƴan aikin gidan guda biyu tare da Rahima da daman duk ansan da zuwan su . Bayan magarib ta nemi iznin zuwa gaishe da prof da  zuwan su a ɗazu suka tadda shi tare da baƙi , hakan ya sa basu samu ganin sa ba sai yanzu . Bayan doguwar gaisuwa tare da godiyar da akayi musayar su tsakanin  Prof da Hajja , taƙaitatciyar hira suka yi wanda duk rabin ta akan Al'amuran da suka shafi taɓarɓarewar tsaro ne tsakanin Niger ɗin da Nigeria da har kawo yau Ƴan tawayen Boko Haram basu saduda sun bar yin kisan mimmiƙe tare da ɓarnannaki tsakanin ƙanana da ma manyan garuruwan Niger da Nigeria ba . Sannan kuma har kawo yau gwamanatin ƙasar Nigeria ta gagara kawo ƙarshen hare-haren ƴan kungiyar duk kuwa da cewa cikin ƙasar tushe da MAFARIN kafuwar ƙungiyar da ta jefa Dubunnan rayukan Al'umma cikin HARGITSIN RAYUWA yake . Shin yaushe ne kome zai kawo ƙarshe ? Yaushe ne abubuwa zasu koma dai-dai ? Yaushe ne za'a ƙira ƙungiyar Boko Haram da shuɗaɗɗan lamari da ya zama tarihi ?  Allah Shine Mafi sani . Hajja ta miƙe ta ƙarasa gaban Prof tana miƙa masa envelop ɗin dake ɗauke da hoton Mama , Alhaji ga hoton Amaryar taka ta Niger ka ga yadda ta girma duk da ƙarancin lafiyar ta amma ta miƙe . Miƙa hannu yayi ya karɓa yana dariya , dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya dawo daga Masallaci . To toh Masha Allah , Babu kome ai kowacce cuta Allah yayi maganinta , sai dai idan har sanin ɗan Adam bai kai ga gano maganin ba . Ƙwarai maganar ka dutse Alhaji .     Cewar Hajja . ya zaro hoton yana gyara zaman gilashin idanun sa , bayan sun haɗa baki wajen amsa sallamar Doctor Hamza , ka ga Babban Likita , Likita bokan turai , ƙarshen ƙwaƙƙwafi da bincike sai likita , lalle tafiyata bana me sa'a ce tunda naci karo da kai , shekaru fiye da biyar rabona da na ganka . Murmushi yayi yana zama daga gefen ƙafafun Prof . Hajja sannun ki da zuwa , da fatan kin  samu isowa lafiya ? Lafiya ƙalau Likita ,yaya bayan rabuwa ? Ya iyalin naka ? Duk kowa lafiya hajja . To Alhamdulillah . Masha Allah wannan Amarya tawa ai tafi kama da ƴaƴan nasara , ga dukkanin Alamu tana da wayo . Prof ya furta haka yana mayar da hotunan cikin envelop ɗin . Wayo kuwa na sosai Alhaji ai Mama sai godiyar Allah ba shakka tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin ɗaukar abu Allah shi rayata , ya bata lafiya , yayi Albarka cikin rayuwarta ita da sauran yaran musulmai baki ɗaya ! Ameen Ameen Alhaji Hajja ta amsa tana sanya hannuwanta biyu ta karɓi envelop ɗin da yake maida mata , ta miƙe tana yi musu bankwana tare da barin falon ta koma cikin gida . Baba , wacce yarinya ce hajja ta kawo maka hoton ta ? Doctor Hamza ya tambayi Prof . Ya buɗe baki da zummar bashi amsa shigowar ɗaya daga cikin dattijan unguwar da suke cin abincin dare tare da Prof ya katse musu hirar . Abuja Yakaka ce a zaune kan hannun kujerar falon Malama Maryam gabanta kuwa babbar jakar kaya ce da take shaƙare taf da kaya , daga gefen ƙafafunta ma wata ƴar matsakaiciyar jakar ce . tana shirye tsaf cikin dogon hijabinta da yake har kusa da idon sawun ta , fuskar ta fayau babu ko kwalli , ramar da tayi ta fito sosai akan fuskar ta da idanunta da suka ɗan zurma ciki . daga gefe a cikin falon Lubna ce a zaune tayi jugum tana kallon Yakaka wacce idanun ta ke kallon ƙasa , tayi shiru tamkar ba sune masu yin dararraki ba muddin suna waje guda . Malama Maryam ce ta fito itama shirye take , ta kai dubanta ga Yakaka tana jin yadda tausayin ta ke sake narkar da ranta tabbas Yakaka tana buƙatar majiɓanci cikin Rayuwar ta . Yakaka tashi mu tafi , lubna taya ta ɗauko kayan ku kai cikin mota Abban ku yana jiran mu , kar mu rasa motar farko ko ta biyu , saboda mu samu isa da wuri tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri da tazara gara muyi sammako .  Jikin Lubna babu kuzari ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta sunkuya ta ɗau ƙaramar jakar tare da kama gefen babbar ta taya Yakaka riƙewa , Sun zo tsakar gida Lubna ta jaa ta tsaya da hakan ya sa Yakaka waigowa . idanunta cike taf da ƙwalla tace Sahiba irin rabuwar da zamuyi kenan babu bankwana ? Shekaru biyar ba kwana biyar bane Sahiba ban so ba zaki tafi tare da maɗaukakiyar damuwa . ɗan guntun murmushi Yakaka tayi , Sahiba kin san har abada kina cikin mutanen da bazan iya mantawa da su ba cikin rayuwata , cikin kowanne irin hali na tsinci kaina , nima zanyi kewar ki Lubna , ta ƙarasa zancen siririyar ƙwallar da bata shirya zubowar ta ba na sauƙa bisa ƙuncin ta . Idan kika tafi a yanzu waye zata maye min gurbin ki ? Waye zata zama babbar ƙawata a bikina ? Da ke muka tsara kome Yakaka . Idan Allah ya yarda zan dawo Lubna , zan halarci bikin ki na ɗau Alƙawari , amma dole na tafi a yau shekaru biyar Falmata tayi cikin rashina , Hon ɗin da aka matsa da ƙarfi shi yasa suka fara taku cikin hanzari ba tare da sun sake musayar wata kalma ba a tsakanin su . Ƙarfe takwas da rabi na safe motar da su Yakaka tare da Malama Maryam suka shiga domin tafiya Maiduguri ta ɗau hanya ɗoɗar . Tafiya ce me nisa ta tsawon fiye da awanni takwas tsakanin Babban birnin tarayya Abuja da Birnin Maiduguri dan haka a saboda yawan tsaye-tsaye akan hanya daga jami'an kula da hanya da suke gudanar da bincike , ya sa dare ya fara shiga har ƙarfe shida na yammaci ta gota , wanda hakan kuma ya sa dole su yada zango a garin Damaturu saboda lokacin dokar hana zirga-zirgan motoci ya shiga ( curfew)  ala tilas suka kwana a tasha , Washegari da hantsi ƙarfe tara suka shiga garin Maiduguri , a idanun Yakaka babu wani sauyi da garin ya samu tsawon shekaru biyar ɗin ko kuwa dan hankalinta bashi kan duban yanayin garin ne ? Baki ɗaya ta ƙagauta ta ɗora idanunta akan ƙanwarta da ƴar ta . Tsawon lokacin rabuwar ta da garin bai sa ta manta da sunan unguwar da ta bar Falmata ba , dan haka bayan sauƙar su a tasha kai tsaye ta shaidawa direban taxi da ya ɗaukesu da kayan su unguwar da zai kai su . tafiyar mintoci 15 kachal ta sada su da unguwar , layi bayan layi ta kwatantawa direban har zuwa gaban gidan da a koyaushe yake yawan samun gyaran da yake sake fiddo kyaun tsarin ginin dai-dai da na zamani . Bayan sun sauƙe kayan su a gefen hanya daga jikin katangar gidan Yakaka tace ga Malama Maryam Ummi bari na shiga na nema mana iznin shiga da kayan mu . To Yakaka . taku ta fara yi tana jin yadda zuciyarta ke bugu da fargabar da ta rasa takamaimai dalilin samuwarta daga ƙasan ran ta , ta kawo kusa da ƙofar gidan aka buɗo Babbar ƙofar ya danno hancin motar sa yana ƙoƙarin fitowa ... !!!! Assalamu Alaikum wa Rahamatullah ta'aala wa barkatuhu . Yan uwa masu karatu Maza da Mata,  ina mika sakon gaisuwa ta tare da fatan Alkhairi a gareku. Sannan ina mika godiya ta ga dukkanin daukacin Mutanen da suka samu damar kirana a waya da wadanda suka bar sakonni su na gaisuwa tare da addu'o'in samun waraka ga 'ya'ya na,  har ma da wadanda Allah bai basu dama ba,  kalmar nagode ai tayi kadan wajen bayyana muku jin dadina , sai dai nace Alherin Allah ya isar muku a duk inda ku ka yi bigire .      Ehen Uhum uhun-hun Kai daga jin wannan guntattakin sautukan da suke tasowa daga kasan maƙoshi ka san da su nake,  o'e da o'e ko kuwa dai a takaice na ce ghost r-r-readers 😂 Ba kome , Ba kuma zance kome ba , amma ku saurari haɗuwar ku da ɗanliti , Ah to meye ? Ai shine zai rama min irin cin tuwo a ƙoƙon da kuke min 😢. A cigaba,  eh nace a cigaba da labewa a bayan labule . 😂 😂 Nagode .[11/14, 11:01 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 36 Doctor Hamza tare da wasu abokan aikin su,  da wasun su ke a zaune wasu na tsaye  daga cikin ofishin shugaban su kuma tsohon malamin wasu daga cikin su a zamanin karatu , Professor Talba Garkiɗa, A zahiri a nutse yake ya bada hankalin sa da ƙululun idanun sa bisa kan Prof wanda ya dilmiye sosai cikin yin bayanai game da cutar da take damun matar dake cikin mawuyacin hali a ICU da jagorancin duba ta ke a hannun mutane huɗu daga cikin su . Sai dai a baɗini cikin hankalin sa sam babu nutsuwa , babu jin daɗi bare kwanciyar hankali a tun jiya da ya amsa ƙiran prof . Nisawa yayi yana sake jin yadda zuciyar sa ke ƙara ƙuntata , wai shikenan domin Ubangiji Allah yayi umarni 'ya'ya su bi iyayen su sai kuma su iyayen suyi amfani da wannan dama wajen cusgunawa 'ya'yan su ? Ah cusgunawa mana , idan ba dai Baba ya so sanya shi a tsaka me wuya tare da damal-mala masa ginin tsarin rayuwar da ya riga ya tsarawa kan sa ba wanne dalili ne zai sa shi ya ɓaɓ-ɓako masa da maganar ƙarin aure ?? Wai fa ƙarin aure ? Shi lamarin ma har kawo yanzu mamaki yake bashi , yana tantamar anya ma kunnuwan sa sun ji zancen a dai-dai ? Idan ya tuno da yadda kalaman suka fito daki-daki tare da sake jaddadawa akan babu shakka umarni yake ba shi har ma kuma ya riga ya sama masa matar , sai ya ji wani mololon baƙin ciki ya tokare shi , shi fa ba yaro bane yanzu. Shi kenan haka zai yi rayuwar sa tare da mata har biyu da ba zaɓin sa ba a matsayin matan sa ? Safiyya da kan ta ba zaɓin sa ba ce , aure ne mai kama da na dole aka liƙa masa shi kuma ya sa hannu dole ya amsa daɗi da ƙarawa lokacin yana a tsakiya da jin takaicin ɗiya mace , domin haka yasa shi gaza musantawa . Yanzu kuma da yake ɗan lallabawa da Safiyyan da daɗi ba daɗi suna zaman su tana faran ta masa dai-dai gwargwado shine kuma za'a sake bijiro masa da wani auren ? To a dalili da me ? Shi a tsarin rayuwar sa babu saki ba kuma gurbin mata biyu . Mace ɗaya tal ta ishe shi ,shiyasa ma ya bada kai yana lallabawa da wacce ta zama ƙaddarar sa ,  rabon sa duk kuwa da cewa ba zaɓin sa bace . to yayi yaya da mata biyu ? Jera su zai yi yana kallo ? Ko kuwa a wuya zai rataya su yana yawo da su suna reto ?  Ɗan tsaki ya saki a hankali . Lokacin da ya fahimci professor Garkiɗa ya kammala jawabin sa ba tare da shi ya fahimci kome ba , alhalin kuma musamman yayi tattaki ya zo domin ya saurari koyarwar duk da cewa kusan abunda ya riga ya sani ne zai sake sanar da su , to amma shi ai maye ne akan neman ilmi kome ƙanƙantar sa , hakan ya sa shi yin zarra a cikin abokan aikin sa masu matsayin karatu irin nasa , Ai ga irin ta nan tun kafin a je ko'ina ya fara sururucewa akan tunanin rayuwa da mata biyu , anya kuwa zai iya ? Miƙewa yayi yana jin takaicin rashin saurarar koyarwar da prof yayi musu . Bayan fitowar su daga ofishin suka tsaya shi da abokin aikin sa suna tattaunawa . Mata biyu ne suka doso wajen hannuwan su riƙe da kayayyaki ,  kondunan zuba abinci da wasu tarkace , Karaf idanun sa suka sauka akan matar rannan , Tun a ɗan nesa yake nacewa kallon kamannin ta da ke kamanceceniya sosai da na Khaalty Rahima , ba su da wata maraba , sai tsabar tsufa da wani irin duhu da wannan tayi marar kyaun gani, tabbas ko da khaalty Rahima na raye bai ci ba ace tayi wannan tsufan, dududu shekaru biyar zuwa shidda ta ba shi , Bai farga ba suka gota shi , da sauri ya bi bayan su ba tare da yayi sallama da Abokin sa ba    Yana son sanin wacece ita , ? Sallama ya dunga rangaɗa musu har baki biyu babu wacce ta juyo a tsakanin su sai da yayi ta uku , Ɗayar kakkaurar matar baƙa gajera ta juyo , " Au nan ne  ? Da mu ne ? Ca nake a iska nake ji , "Sannu Mama Da abokiyar tafiyar ki na ke son yin magana , ya furta haka yana nuna bayan ta da ta ɗan yi gaba batare da ta tsaya ba tana cigaba da tafiyar ta , takawa yayi ya bita ganin tana shirin shan wata kwana . "Hajiya sannu , " sannu Hajiya ," Shiru ya ji tayi , Dan haka ya ɗaga taku ya sha gaban ta , Da sauri ta ɗago kan ta , ta kai duban ta kan shi , Kallon-kallo suka yi , jakar kayan da yake hannun ta ya sulluɓe ƙasa , Lokacin da ta wara idanun ta dake nuni ƙarara da halin ruɗanin da zuciyar ta ke ciki  ,    Motsa

Chapter 57 of 103