ta da hannu wani irin kuka take yi ciki-ciki , irin kishin da take ji a ran ta akan Yakaka muddin bata ɗau mataki ba za ta iya haɗiyar zuciya ta mutu.
Lokacin da Doctor Hamza ya idar da sallar Magarib yayi niyyar komawa gida amma yunwar da yake ji da kuma sanin da yayi a gidan ma shi suke jira tunda ya hana ayi girkin sai kawai da ya shigo gidan ya ɗau motar sa ya sake fita ba tare da ya shiga cikin gidan ba .
Sofia da ta ji ƙugin tashin motar sa da sauri ta leƙa ta window ta ga fitar sa , tana ganin ya bar gidan a guje ta sauƙa ƙasa kai tsaye ɗakin Yakaka ta tasamma .
Tana murɗa ƙofar ta ji a kulle , ɗan kwankwasawa tayi cikin salon da Doctor Hamza yake yi .
Yakaka wacce take zaune ta miƙe a hankali ta ƙarasa jikin ƙofar .
Haka kawai ta ji zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan haka ta dakata ta fasa bude kofar cikin siririyar murya tace "Waye ?
Shiru Sofi tayi tana fatan ta buɗe su gamu , sake dukan ƙofar tayi da karfi da hakan ya sa nan take Yakaka ta fahimci wace ce a wajen dan haka a sarari ta furta "Auzu Billah minash Shaytanir Rajeem, baya ta koma ta zauna a inda ta ta shi.
"Ya kamata na samarwa kaina da mafita ni Yakaka lamarin Matar nan ya fara wuce iyakata ta musulunci , ta furta hakan a sarari kawo yanzu ta haƙaƙe da gasken gaske sofi ta ɗaura ɗamarar yaƙar ta dalili kawai;sun hada Miji daya.
"Ina Mafita?
Haka Sofia ta gaji da bugun ƙofar tana surutai , jin shigowar motar Doctor Hamza ya sa tayi saurin barin wajen ta koma ɗakin ta kai tsaye banɗaki ta shiga ta sakarwa kan ta ruwan sanyi .
Kusan mintuna goma sha biyar suka kwashe suna jiran sofia ta zo su ci abinci amma shiru ba alamun ta sau uku yana ƙiran layin ta wayar tana ƙara bata ɗauka ,
Ran sa ya fara ɓaci da salon rainin da yake hango take-taken sa daga Sofia wanda kuma ba zai ɗauka ba .
"Wafaa hau sama ki ƙira Sofia .
Kamar bata fahimci abunda yake cewa ba haka Yakaka take jahiltar sa da ido .
Ganin yadda tayi da fuska ya sa shi miƙewa da kan sa ya nufi saman .
Yakaka wacce ta bi shi da kallo da tuno da abunda ya faru jiya daga zuwa ƙiran Sofi ya sa ta miƙewa tsaye da sauri .
"yaya Dakta .
Ta ƙira sunan sa ,
a hankali ya waigo.
"zan bika .
tace tana yin narai-narai da ido .
Bai amsa ba sai hannun sa da ya miƙo mata alamar ta taho da sauri ta isa gare shi tana jefa hannun ta cikin na shi , ya riƙe ta suka hau saman tare .
Sofia wacce take tsaye a maɓoyar ta tana ganin duk abunda ya faru kafin su ƙaraso ta fito da sauri kamar daga ɗaki ta fito ,
Wani irin kallo ta watsa musu kafin ta gyara fuskar ta tana cewa " Yaks manya ke dai ko ina kina liƙe da Miji ɗa Namiji daɗi ko ai kin saba .
"Sofi sau nawa zan faɗa miki ki daina min yawo a gida tsirara-tsirara ?
Doctor Hamza ya katse ta ba tare da ya bari zancen da tayi yayi tasirin da zai hana shi sukuni ba duk da cewa kalmomin ta sun taɓa ran sa .
Buɗe baki Sofi tayi cike da mamaki kafin ta mayar da ganin ta kan Yakaka wacce ta sunkuyar da kan ta a tun kallon farko da tayiwa Sofi da take sanye da wasu bodycon sleeve rigar duk bata karasa kugun ta ba wandon kuwa iyakar shi ƙourin ta rashin kaurin da kayan ke da Su ya ya taimaka wajen fiddo da halittun jikin ta .
Narke murya tayi cike da kissa tana ƙoƙarin haɗiye fushin ta tace "Doctor kai ne fa kake cewa kafi son kana gani na a haka Kana jin daɗi tare da samun gamsuwar ido sobada ganin ko ina nawa a ciccike ko ka manta ne ? Kai ne fa kake cewa siririyar mace ramammiya haushi take ba....
A hankali Yakaka ta zame hannun ta tayi baya tana barin wajen saboda fahimta da tayi gaba kaɗan Sofi zata ce wani abu da zai fi haka ji mata ciwo .
"Duk ban tambaye ki wannan zancen ba dan na lura bakya jin kunyar ƙarya Sofi da girman ki amma ina so ki sani a yanzu ba mu kaɗai ne a gidan dan haka bana so na sake ganin ki haka kina min yawo a gida .
"Riga da wondo ne fa Doctor na ? Ta furta hakan a shagwaɓe zuciyar ta sol ganin Yakaka ta ɓace a wajen .
"Eh amma na 'yan iska ba ? Ko Wafaa ma ai riga da wondo ta saka amma na mutunci da zata iya fitowa a gaban ki kuma sun mata kyau sun burge ni .
"Ki koma ki sauya kaya ni ba zan iya cigaba da jiran ki cin abinci ba zamu fara ci dan yunwa nake ji .
Daga haka ya juya yana barin wajen , Sofi ta bi jikin ta da kallo kalmomin sa na dawo mata a kai "Doctor yana daf da kufce min na shiga uku ni Safiya ni ce yau yake cewa na dunga rufe masa jikin da a baya yafi kaunar ganin sa fiye da television?
Bayan sun gama cin abincin da Yakaka take jin sa ba wani daɗi sosai hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda duk suka haɗa ido da Sofi sai ta galla mata harara .
Dan haka tana gama ci ta miƙe zata yi tafiyar ta Doctor Hamza da duk yake kallon motsin su ya dakatar da ita ta dawo ta zauna har ya gama cin abincin sa .
Sannan ya fara yi musu nasiha cikin nutsuwa da fiye da rabin ta yafi karkata akan tunasar da su kan gujewa ɗaukar hakkin juna/cutar da juna sannan ya kwaɗaitar da su daɗin da za su ji su kuma jiyar da shi muddin suka zauna lafiya da juna a matsayin 'yan uwa ba abokan hamayya ba sannan ya tunasar da su shi aure bangare ne na ibada da ake samun ɗimbin lada a gurin Ubangiji Allah ta dalilin sa , dan haka yake jaan hankalin su da suyi ƙoƙari wajen ganin sun yi bautar su yadda ya dace. sai ya rufe da cewa
"Muddin kuka haɗa kai ku ka min rumfa ku ka bani kariya , ku ka bani kulawar da ta dace da ta samar min da nutsuwa ai ba za ku bar wata damar da wata za ta sake ratso tsakanin mu ba ku biyun nan kun isheni rayuwa ta duniya Safiya da Amina bayan ku duk sauran mata ba zan gan su har su burge ni ba
Da murmushi Yakaka take kallon sa kalmomin sa sun mata daɗi sosai kafin a hankali tace "Yaya Dakta da yardar Allah ba zamu zama sanadin tashin hankalin ka ba kai ma ka dunga mana addu'a Allah ya haɗa kan mu ya kori shaiɗan a tsakanin mu .
"Ameen Wafaa tun kafin yanzu ina muku addu'a zan kuma cigaba da yi muku insha Allah .
"Sofi baki ce kome ba ?
Ya furta hakan yana ɗora ganin sa akan ta wacce ta tattara hankalin ta duk akan fuskar wayat ta kamar bata wajen '
Sake yi tayi kamar bata jin sa duk kuwa da cewa sarai tana jin nasa shi ma kuma ya san tana ji dan haka ya ɗauke ganin sa daga kan ta ya mayar ga Yakaka yana cigaba da cewa
"Sai batun kwanakin girkin ku bayan kin gama kwanakin ki bakwai na amarci kamar yadda addini ya tanadar da yau kike da kwanaki biyu a gidan nan dan haka yau mun samu kwana biyu ko Wafaa ?
Murmushi Yakaka tayi tana gyaɗa kai , a hankali ya miƙa hannu ya riƙo hannun ta da yake ajiye akan teburin gaban su kafin yace "to kwanaki nawa za ku dunga yi na girki kwana ɗaya ko biyu ?
Kallon Sofi tayi ta ga yadda ta zuba mata ido ɗauke kan ta tayi murmushin ta bai ɗauke ba tace "yadda duk kake so Yaya Dacta amma ana yin raba kwana ɗayan ne ya zama awanni 12-12 ?
Da mamaki tare da zumuɗin son jin manufar ta yace "idan ana yi me zai faru ?
A shagwaɓe Yakaka tace
" Sai ka dunga yini a sama 12 hours kana saukowa ni kuma mu kwana tare tunda ka ga ni fa ƙarama ce kuma 'yar siririya idan dodo ya zo min da dare ya zan yi ? .
Wata 'yar sassauƙar dariyar da take tafe da amon nishaɗi Doctor Hamza yayi kafin ya lakace tsinin hancin Yakaka yace " Wafaa lalle kam ke yarinya ce amma ba'a haka sai dai kwana ɗai-ɗaya ake yi dan haka zan dunga kwana ɗaya a sama ɗaya a ƙasa tare da ke kin ji..
" What the hell ? Dole mana ki ce haka tsohuwar kilaki uwar jarababbu , idan karuwancin kike ji da shi ai da sai ki cigaba da tsayawa a bakin titi kamar yadda kika saba a can ba za ki rasa wanda za ki dunga kwana da shi ba kullum amma tun da kika auri Mijina wal.'
"Sofi bana son hauka da rashin tarbiyya a gabana kike zagin ta daga wasa ? ..
Doctor Hamza ya katse ta a tsawace .
Bata dube shi bare ta yi ko gizau ta cigaba da cewa
"Kuma wallahi ban yarda da kwana bakwai ba wannan bazaurar za'a yiwa kwanaki bakwai da ake yiwa budurwa gal a leda ? Daga gobe kwanan ta uku ya ƙare kuma kwana biyu nake son a dunga yi na girkin aikin banza tsohuwar 'yar iska kawai za ki zo kina wani yen-yen-yen wai ke ga 'yar barki to na bi barikin da gudu .
"Sofi zan matukar saɓa miki idan kika sake maimaita makamantan kalmomin da kika furta , Wafaa Matata ce ni ne nake auren ta ba ke ba , budurwa ce ita ko ba budurwa ba ce ba hurumin ki bane , A sanina bata taɓa aure ba dan haka a matsayin budurwa na aure ta ko da kuwa ba budurwar bace tsautsayi ya gifta a rayuwar ta kamar yadda na aure ki a matsayin budurwa duk kuwa da ban samu tabbaci kan tsautsayin da ....
Wani irin ihu Sofi tayi tana miƙewa tsaye tayi kukan kura ta jawo Yakaka ta cukui-kuye ta bata cikin hayyacin ta take jijjigata "sai kin faɗa min irin asirin da kika yiwa Mijina da tun ranar da ya fara ganin ki ya susuce akan ki tun kina kuchakar ki ƙazama fiye da shekaru shida na zauna a ƙarƙashin mulkin da kike yi a zuci..
"Sofiya ki sake ta , ki sake ta nace kafin na saɓa miki .
Doctor Hamza yake furta hakan yana ƙoƙarin shiga tsakanin su ko kusa shi ba mutum bane mai son tashin hankali da hayaniya ga Sofi tana neman dagula masa lissafi ta ko'ina .
Ƙarar marin da ya karaɗe wajen ya taho da wani ɗan takaitatcen shiru a bayan sa 'tsit' kamar an kashe radio sai numfashin Sofi da ke sassarfa yana kai kawo lokaci ɗaya idanun ta ke tsartuwar wasu zafafan hawaye da take jin ɗacin su har a maƙoron ta hannun ta ɗaya dafe da ƙuncin ta ta ɗaga ɗayan hannun tana ɗorawa a kirjin ta da wata shaƙaƙƙiyar murya tace "Doctor Ni Ni Ni ka mara ?
Jaan numfashi tayi kafin ta juyar da ɗan allin ta kan Yakaka da take laɓe a bayan Doctor Hamza tana leƙen ta tace "akan wannan ka mare ni ? Akan ta ?
Ba sabon sa bane dukan mace shi ko hararar Matar auren sa bai cikin tsarin rayuwar sa sai fa da Allah ya haɗa shi da 'yar gagara irin Sofi yasa dole a wasu lokutan yake ɗaga mata muryar sai dai duk da haka a duk zaman su bai taɓa ɗora hannu akan ta ba sai fa yau da ta kai shi maƙura ta gajiyar masa da ruhi da gangar jikin sa sannan kuma tsananin So da yake yiwa Yakaka ya ingiza shi ganin tana neman ji mata ciwo bayan irin kalamai na ɓatanci da take furzo mata da suke tafasa masa rai '
Nadama na son kawo masa farmaƙi ya ɗaga hannun sa yana mai matsawa kusa da ita yace "Mu ga gurin baki ji zafi ba ko ? Ai ke ce kika jawo Sofi .
Da sauri ta kauce idanun ta har wani jirkituwa suke yi saboda tsabar tashin hankali da ruɗanin da take ciki.
Ta buɗe baki amma ta gagara cewa kome ko'ina na jikin ta tsuma yake kawai sai ta juya da maɗaukakin taku ta bar wajen kamar ana ingiza ta .
Da hannun sa ɗaya ya dafe kan sa bayan barin ta wajen gaba ɗaya nadamar ɗora hannu akan ta yake yi ,"Nagartatcen Namiji ba ya dukan Mace , zuciyar sa ke tunasar da shi hakan.
waje ya samu ya zauna ya yi tagumi da hannu biyu, Yakaka wacce ita ma jikin ta yayi sanyi akan abunda ya faru duk tana ganin kamar har da laifin ta ita ta tunzura Sofi a ƙoƙarin ta na ganin ta rama wasu kalmomin cin fuska da ta san da gangan Sofia ke furta Su a gaban ta dan ta bata haushi.
Durƙuso tayi a gaban sa tana jin tausayin sa na kawo mata "duk ke kika jawo ɓangaren zuciyar ta ya ƙalubanci ɗaya ɓangaren.'
"Yaya Dakta kayi haƙuri d..
Shit yace mata yana sauƙe hannun sa ya ɗago ta daga durkuson da tayi ya mata wajen zama akan ƙafar sa idanun sa da suka yi ciki saboda gajiya da damuwa su ya ɗaga yana bin ta da kallo rigar jikin ta duk ta yamutse har ta yage ta wuya saboda cukumar ta da Sofi tayi , idanun sa ya sauƙe a ƙasan wuyan ta kaɗan da duk yayi birɗi-birɗi kamar borin jini .
Da sauri ya wara idanun sa kafin ya kai hannu yana janye rigar da hakan ya bashi damar ganin jikin ta sosai, da Sauri a kuma tsorace yake duba sashin jikin ta da gaba daya yayi burɗi-burɗi.
"Wafaa wannan anxiety rashes ɗin me ya kawo miki su ? Tsoro ? Tsoron me kike haka ? Wafaa ki rage tsoro ba abunda zai same ki a duk lokacin da kika tsorata da wani abu kiyi addu'a Wafaa .
"Kin ga yadda duk jikin ki ya tashi , kin ga duba .
Yace yana nuna mata hannun ta da shi ma duk yayi ruɗu-ruɗu .
Fuskar ta ya riƙe da hannun sa kafin yace "faɗa min me kike tsoro ?
Sauƙe idanun ta tayi kafin a hankali tace "Babu .
"Babu ? Ya tambaye ta cike da shakku
"Eh .
Ta amsa tana miƙewa daga kan shi "yaya Dakta zan tafi na kwanta dare ya fara yi.
Taku ɗaya tayi ya riƙo hannun ta kafin ta ankara ya dawo da ita inda ta tashi ya kewaye ta da hannun sa kafin ya kwantar da kan shi a ƙirjin ta yana shaƙar ƙamshin jikin ta yace "meyasa za ki gudu ki bar ni bayan kin san ina da damuwa ? Ba zan ji daɗi ba idan aka ce zaman ku ya zama haka , ba zan samu farin-cikin da Magidanta ke samu a gidajen su ba muddin kuna faɗa . ina tsoron gaba na samu rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yana .
Shiru yayi kafin ya ɗago kan sa daga jikin ta da taimakon hasken da yake wajen tar ta iya hango yadda idanun sa suka yi jawur da har sai da tsigar jikin ta ta miƙe .
"A gare ki ina zaton zan samu kwanciyar hankali Dan Allah kar ki min bazata kin ji ?
Gyaɗa kai tayi duk da bata gama fahimtar kalmomin sa ba ya ɗora da cigaba da cewa
"Duk abinda Sofia za ta miki kiyi haƙuri kar ki dunga biye mata kuna tashin hankali fitina ba halin ki bane Wafaa kar ta ɓata min ke .
"ke saliha ce managarciya salihar mace irin ki bata tashin hankali duk abinda zata faɗa kar ya tunzura ki har ki biye mata kuyi rigima kin ji ko ?
Ya furta hakan yana ƙurewa fuskar ta kallo, ɗago kan ta tayi su ka haɗa ido
Kalaman sa sun mata tasirin da yasa ta lumshe idanun ta da wani boyayyan murmushin da ya ɓullo daga can ƙasan ran ta har wani danshi take ji daga saƙon zuciyar ta yana ratsa mata sassan jiki samun yabo a wajen wanda kake neman yarda da amincin sa abu ne mai daɗi da haifar da nishaɗi.
ba tare da gangar jikin ta tayi shawara da ita ba sai ta tafi a hankali ta kwanta a jikin sa tana kewaye shi da nata hannun da hakan ya sa shi rufe Idanun sa ya matso da ita sosai jikin sa ya rungume ta .
Daɗewa da yayi yana fama da son ta daɗi da yadda yake kan gabar neman mai tallafin sa a dai-dai lokacin da ƙwaƙwalwar sa ke buƙatar hutu sai gangar jikin sa ta mata tarɓa na musamman da ahankali ya fara bin jikin ta da hannun sa ya shiga gwadama mata zallar ƙaunar da yake mata tun a mafarin farko.
Tana jikin sa ya miƙe tare da ita cike da gudun abun da zai gifta tsakanin su ya daƙile masa daddaɗar nutsuwar da yake samu a tare da ita da ba zai ce ya taɓa samun makamanciyar ta ba .
Washegari a tare suka tashi cike da nishaɗi suna hirar su suka shiga kitchen tare tana girkin ta yana mata hira da tsokanar ta lokaci-lokaci yana ɗan kasa kunne ko zai ji motsin fitowar Sofia amma ko alamar ta babu har lokacin da ya koma ɗaki yayi shirin tafiya aiki ya fito suna shirin fara cin abinci Yakaka ta danne zuciyar ta a hankali tace "Yaya Dakta har yanzu bata fito ba ko za ka kira ta muyi breakfast ?
Kallon ta ya yi da yanayi na ko'in kula a muryar sa yace "ita da kan ta za ta fito kyale ta .
"Zuba mana abincin mu ci ina sauri Wafaa.
Cikin nutsuwa ta zuba musu soyayyan dankalin da ƙwai hadi da soyayyar ayaba , sai kuma farfesun marara zallah da tayi masa dafuwa irin na mutan Ndjamena (shurban) a ƙasa ta ajiye musu abincin a tsakanin su .
Suna ci Doctor Hamza yana ta santi , jin sa yake kamar ya dawwama a haka yana kallon fuskar ta da take cike da annuri .
Bayan sun gama cin abincin ya goge bakin sa da tissue "Wafaa ya ƙira sunan ta.
"Unmh
Ta amsa tana ɗago kan ta hannun sa da yake miƙa mata wani kwali mai kyau ta bi da kallo ba tare da ta karɓa ba ta daga idanun ta ta mayar kan sa da sigar tambaya?
" karɓi mana , sabuwar waya na saya miki ta hannun ki bata da wani amfani koyaushe na ƙira ba kya ɗauka kamar jiya kam ma a kashe ta wuni , bana jin daɗin haka na fi son na dunga jin ya kike ? Ko da bana gida .
Da yalwatatcen murmushi tare da ɗan boyayyen zumuɗi ta karɓi kwalin kafin ta fara kici-kicin buɗewa bai dakatar da ita ba har sai da ta buɗe ta zaro sabuwar waya sumfurin iPhone8+ da take ta daukar ido .
"Masha Allah .
ta furta a sarari lokacin da take kallon sa with her light brown eyes that were deeply creased with smile line at the coners.
"Yaya Dakta Wannan wayar ta 'yan gayu tawa ce?
Ta furta hakan da zallar farin-ciki kafin ta ɗora da cigaba da cewa " Kai wallahi nagode sosai , ina nufin nagode dayawa Ya Dakta Allah ya daɗa ma buɗi da arziki mai Albarka...
"Wafaaa
ya ƙira sunan ta ƙasa-ƙasa yana jin yadda farin-cikin da ya hango tare da ita ya ke ba shi wani shauƙi na musamman
Kumatun ta ya ɗan shafa yana miƙewa tsaye bayan ya ɗauki briefcase din sa da murmushi yace " Wafaa I can bring the whole world to you if I have it.
A hankali ta dago kan ta rana ta farko da ta ji kamar tana son mayar masa da martanin tsadaddun kalaman sa tana so tace wani abu ko da kadan ne akan tarin alkhairin sa marasa adadi da ya wanzu yana hidimta mata, "to me zan ce ne? Ta tambayi kan ta, daga can ƙasan ran ta kalmomin suka haɗo kan su suka fito ta tsakanin laɓɓan ta ba tare da ta janye ƙwarar idanun ta da ke cikin na shi ba ta ce "I always cherish your company Yaya dakta for that I'll forever serve you and do anything for you here in Duniya insha Allah. Thank you for everything! I mean everything Yaya Dakta.
Ɗage girar sa yayi yana jin sa kamar mai yawo a sama kalmomin nata taƙaitattu ne amma masu faɗi ne a wajen sa da zai yi zama na musamman domin yi musu fashin baƙi ,
" I appreciate that and I cherish yours even more, integrity you're worth-valuing, worth-treasuring and worth-cherishing. Your value is such unfathomable Wafaa.
zamewa ƙafar Sofia tayi da ƙiris ya rage ta gangaro daga ƙafar bene, bata taɓa sanin ƙeyar mutum na da ido ba sai da ta ji tana taka matakalar bene ta baya , kalaman na mata amsa kuwwa suna mata rakiya har ɗakin baccin ta da ta na shiga ta zube a ƙasa kan ta na juya mata tana ganin kome na dakin yana tafiya da kafafun sa.
A narke Yakaka take kallon sa lokacin da yake furta mata kalmomin da suka mata zurfi wajen fassara har ya sunkuyo ya sumbanci goshin ta, " ni zan tafi Wafaa .
Ya furta haka yana ɗaga taku ya nufi hanyar ficewa daga falon har ya kai ƙofa ya waigo ta , kallon sa take da murmushin da yafi so a tare da ita a hankali ya ƙarasa ficewa a falon ran sa cike taf da ƙaunar ta fuskar ta tana zanuwar masa a cikin rai yana jin zata ishe shi farin-cikin yau har ya je ya dawo .
Ya tada motar sa a hankali yana ficewa a gidan zuciyar sa na daɗa hasko masa yanayin da ya bar ta a ciki " she's smiley, she is smile just like the sunflower. Ya furta hakan a sarari.
Cike da zumuɗi Yakaka ta kunna wayar da cikin sa'a ta tarar da sabon Sim a ciki , duk da bata taɓa riƙe babbar waya ta kan ta ba amma bata gagara sarrafa wannan ɗin ba saboda Lubna tana riƙe irin su a wasu lokutan tana karɓa tayi 'yan taɓe-taɓen ta saboda sosai manyan wayoyi suke burge ta dan dai kawai bata da damar mallakar su ne .
Ta kwashe tsawon lokaci tana wasa da wayar cikin taka tsan-tsan ta shiga nan ta fita can kafin ta miƙe tana riƙe da wayar duk hankalin ta na kai ta tafi ɗaki ta ɗauko tsohuwar wayar ta ta kunna ta cike da zumuɗi ta kwafi number Hajja akan sabuwar wayar ta ta fara ƙira da ɗokin son ta yiwa Falmata albishir .
Bugu ɗaya Hajja ta ɗaga tana ɗauka da ta ji muryar Yakaka sai ta sa dariya "Ah ka ga manya a baku naku daban Babba Uwar Mama uwargida kuma Amarya a gidan Babban likita , ai yau kwana uku kenan uwarɗakina tana nacin ƙiran wayar ta ki bata samu tun ranar da muka samu labarin kin tare da fatan ana Amarci yadda ya dace ?
'Yar dariya Yakaka tayi ta fara sabo da halin Hajja na jaan zaren magana tayi ta tsawo , "Hajja kenan muna lafiya ya ya wajen ku ?
"Mu ma lafiya ras muke bari na miƙawa gimbiyar wayar ku yi magana tana ɗaki .
"To Hajja nagode .
"Ince da kuɗi a wayar ta ki ? Kar ki katse yanzu zan ba ta
A zaune ta tarar da Falmata ta tasa cikin ta a gaba da cikin kwanakin nan yake wani irin girma na ban mamaki daga gefen ta faranti ne a cike da warmers ɗin da aka shaƙe cikin su da kayan cimaka .
Miƙa mata wayar Hajja
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 94 Chapter of 103