Share this page
liti ya kake ? " Ras nake Yaks . Yayi fari da ido kafin ya ɗora da "Ke kuma fa ? Ya na ganki haka da Bargo yaro-yaro kina yawo kadda dai kice min kin yi ƙarkon kifi , ? Kin fito daga ruwa kin faɗa wuta ? Yo ai kuwa da kin ɗibga asara a duniyar nan Yaks ace dai wai mace hamshaƙiya kamar ke kina yawo a ƙuɗunɗune cikin hirami yake ko hijabi ko jallabiya ? Bani sunan sa ɗaya . " Ubanka yake nace Ubanka yake shashasha , wofin wofiyo banzan banza , yau ga ɗa ya zama lalatatce bayan an kashe ragon suna , to Allah ya shirye ka , ke un-un Yakaka wuce muje . Hajja ta furta hakan tana huci tare da yiwa ɗanliti daƙuwa da hannuwanta duk biyu , ta ƙarasa zancen da fusgar hannun Yakaka , Buɗe baki Ɗanliti yayi da mamaki , ," Ke tsohuwa , ki kiyayeni ki kiyayen nace da zaki zo ki shiga cikin maganata dake nake ? Nace da ke nake ? Yo Allah na tuba ke a zamanin ki waye ya san irin tsiyar da kika shuka ta rawar banjo da kiɗan gurmi daga ke sai ɗan kanfai ?  Ko da yake wannan baƙin naki uwa shuni ba wani tasiri kika yi ba ko a wajen su garbati mai kalangu . , ",Na rantse kin ci darajar yaks domin ni na falle tsohuwa da marin da zai sa ta ga star abune mai sauƙi a wajena , gaba ki kiyaye kin ji na gaya miki . tsaki Hajja tayi suna barin wajen , " Allah ya shirya ka zindiƙi . Shima ya rama Hararar da tayi masa , " waye yake ta taki tsohuwar guzuma , Yaks Ki samu lokaci ki leƙo mu akwai labarai da hanyoyin arziki masu tarin yawa , af na manta na faɗa miki uwarɗakin fa bata da lafiya... Bai ƙarasa zance ba yayi shiru ganin sunyi nisa , " ji min tsohuwar nan zata yaɓan magana wai nine zindiƙi ? Tsohon ki ne dai zindiƙi aikin banza . **** Da sallama suka shiga gidan Amne , tana zaune kan barandar ta tana ƙunsa lalle a ƙafafunta da basa rabuwa da ƙunshi , Tayi mamakin ganin su saboda Rahima bata sanar  da ita zuwan nasu ba , ta tare su da fara'a tana yiwa baƙi barka da zuwa , idanunta da hankalinta baki ɗaya akan yakaka . Bayan sun gaisa ta dubi Rahima , " aina kika sake samo min mai kama da Rahima ta ? Da ace shekaru basu jaa dayawa ba zan iya cewa Rahima ta ce wannan ,   " dariya Rahima tayi , Amne baki gane ta ba ko ? Yakaka ce fa , 'yar gudun hijarar da suka zauna a gidan mu shekarun baya da akayi zaton ta rasu wajen haihuwa ? duk da ba wani jimawa tayi da yaran ba amma sunan su ya tsaya a ƙwaƙwalwar ta , " Yakaka ke ce ?   " ni ce Amne , " Alhamdulillah ashe Yakaka kina raye ? Ina kika tsaya tsawon lokacin nan ? Ina ƙanwar ki tare da 'yar ki ?   hannun ta ta ɗora akan na Amne da ta miƙo mata su , fuskar ta ɗauke da murmushin jin daɗin zallar ƙaunar da ta hango a idanun Amne ta matso kusa da ita , "Falmata su na America wai . Hajja tace , " Wai ne ma ?  ai ya wuce wai ., Amne bata tsananta tambayoyi ba ga Yakakar domin ta bata damar sakewa ,  Lallen da Amne take sawa ta karɓa , tare da cewa " kawo na sa miki Amne . tana murmushi ta miƙa mata 'yar robar da lallen ke ciki , ta shiga sanya mata sannu kan hankali , da sauri Rahima tace "Daman kin iya lalle ne Yakaka ? tana murmushi tace , " ko ban iya ba zan koya a ƙafar Amne . Hajja da Amne suka cigaba da hirar su , zuwa lokacin da Rahima tace , " Yauwa Amne ki nunawa Yakaka Hoton Khaalty Rahima da kike cewa suna kama Yakaka tana son ganin ta... "eh Amne ina son ganin Khaalty Rahima , Yakaka ta furta hakan cike da ɗoki .. Assalamu Alaikum masu karatu maza da mta , ina miƙo sakon gaisuwa ta tare da fatan alheri , ɗauke da yabawa bisa ga yadda kuke bin littafin nan cike da bani ƙwarin guiwa nagode ƙwarai da gaske Allah ya bar so da ƙauna ( sunan wani littafi 😂 ) sharhin ku a fejin da ya gabata ya min daɗi matuƙa da fatan za'a ɗore da haka ? . Ghost readers muna nan da ku , za'a ji kan mu watarana . 😡 Nagode .               [11/14, 11:01 AM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa ) Umm'muaz 37 Cike da zumuɗi Yakaka ta karɓi wani ƙaramin envelop ɗin da Rahima ta ɗauko mata daga ɗaki tana cewa " Yakaka ga hoton Khaaltƴ Rahima duba ki gani, ita ce takwarata ai ina kama da ita ko ?  . Da murmushi bayyane kan fuskar ta , ta zaro hoton bayan ta goge hannun ta da yake da ɗan danshin ruwan ƙunshi . Ƴar ƙaramar budurwa ce a jikin hoton na farko da baza ta wuce shekaru sha huɗu zuwa sha biyar ba , fara ƙal tamkar baturiya ,  ƙibabbiya 'yar dumur-mur  jikinta sanye da doguwar rigar iya ƙwauri mai guntun hannu irin shigar su ta shuwa ,kanta ba ɗankwali sai manyan kitson guru da aka mata gwammon sa a ƙeya , " wai Masha Allah Rahima mai sunanki ta fiki kyau gaskiya , Ta furta tana 'yar dariya kafin ta zame hoton na bayan sa ya bayyana da bai kai wancen a tsufa ba domin a wannan ta ƙara girma ta zama budurwa da a lokacin zata iya kaiwa shekaru sha bakwai , da alama a makaranta ta ɗau hoton ganin jikinta sanye da uniform , Tsam , tayi tana ƙurewa cikakkiyar fuskar ta kallo da take dariya ,  tamkar dai tana rikiɗe mata zuwa fuskar da tayiwa sani na haƙiƙa , "fuskar wa ? Ta tambayi kan ta da kan ta . "Fuskar maman mu ," babu shakka dariyar ta da zubin haƙoranta irin na maman mu ne , sai dai maman mu bata da jiki da kyaun wannan mai kama da turawan, Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar Amne wacce ita ma ta kafe ta da ido tana nazarin yanayin da take hangowa a tare da ita , " Yakaka ko kin san ƙanwata Rahima a wani waje ne ? Kallon Amne tayi kamar zata ce wani abu sai kuma tayi ɗan yaƙe , tare da girgiza kanta lokacin da take ƙoƙarin mayar da hotunan cikin gidan su , " A ah Ban san ta ba Amne ," "Allah sarki , Rahima kenan ƙanwata da muke uwa ɗaya uba ɗaya jal a duniya , Yaa Allah ka san halin da na wanzu cikin sa tsawon shekarun nan akan rashin Rahima , Allah ka dawo min da Rahimatullah , ka sa muna da rabon sake ganawa a duniya . "Amin Amne , suka amsa mata su duka fuskokin su na bayyana alhini , musamman Yakaka wacce ta shiga wani irin hali na ruɗani da ganin hoton khaalty Rahima ya jaza mata  . Ƙwarai fuskar ta tsaya mata a zuci da cikin tunaninta , Babu wadatar nutsuwa na sosai a tare da ita suka ƙarasa yinin su zuwa gefen La'asar suka kama hanyar komawa gida , Rahima ta dubi Yakaka bayan mai adai-daita ya sauƙe su a daf da ƙofar gida , "Yakaka ya naga duk kin yi wani iri , akwai damuwa ne ? Kafin mu fita a gida ba haka kike ba , Kafin Yakaka ta amsa Hajja tayi charaf ta amshe zance , "Ahaf zai wuce batun wannan ɗan  banzan , ɗan hamsin yake ko ɗan daudu ? Idan har kika ce ƴar huɗubar wofin nan da ya wassafa miki zaki ɗauka ki aza a rai to kuwa kin kama kumfar teku , domin wannan da kike ganin sa rabon sa da alasambarka tun kwanansa bakwai ran suna , babu Alheri a tare da shi ko na aninin kobo  atoh . A ɗan kaikaice Yakaka ta dubi Hajja zata yi magana , aka buɗo babbar ƙofar gidan , Doctor Hamza ya turo kan motar sa , kallo guda ya yiwa gefen da Yakaka take ya ɗauke kan sa , Da sauri Yakaka ta wuce tana gyara zaman hijabinta , ta bar Rahima da Hajja suna gaisawa da shi , inda yake tambayar su daga ina suke ?? Suka sanar da shi daga gidan Amne suke , sosai ya ji daɗi tare da tambayar su yadda suka baro ta ? Suka amsa masa da tana lafiya ƙalau , Daga haka ya wuce yana satar kallon madubin motar sa inda ya hango Bayan Yakaka tana tafiyar ta a hankali dogon hijabin jikinta da yake kusan taɓa ƙasa bai boye salon takun tafiyar ta irin na barewa ba , Ɗauke kai yayi lokacin da yake dai-daita kan motar sa ya hau titi ya cilla zuciyar sa cike da zullumin tunani kan inda ya nufa , Kai tsaye ya tasamma unguwar da aka bashi tabbacin anan gidan da matar nan da yake zaton innar sa ce take aiki , duk kuwa da cewa duk cikin binciken da ya gabatar na tsawon satika biyu bai samu wani abu da zai bashi tabbacin cewa ita ce ko ba ita bace ?  Amsa guda ɗaya ta tabbata a gare shi , shine matar kurma ce kuma ƴar gudun hijira ce daga yankin Bama , da take rayuwa tsakanin gidajen masu kuɗi tana yin aikace-aikace da ita da tilon ɗan ta mai kimanin shekaru takwas . Yana shiga unguwar ya bi kwatacen gidan da aka ce tana aiki da su , ya tsaya daga bakin babbar ƙofar gidan ya nemi iznin shiga daga dattijon dake gadin gidan , Ganin sa da dattijon yayi cike da haiba da alamun wadata ya sa shi yin tunanin ko ire-iren mutanen da suke mu'amala ne da masu gidan , dan haka kai tsaye yayi masa iznin shiga da motar sa harabar gidan , Bayan ya fito daga motar sa ya miƙawa dattijon hannu suka yi musabaha , "Baba ina neman Mamar Bulama ne ance nan gidan take aiki ? "To oho Kurma Mamar Bulama ƙwarai kuwa nan take aiki idan ka miƙe wannan yar hanyar ka ƙure sashin su yana nan daga hannun ka na dama nan za ka ga wata ƙaramar ƙofa , " toh sannu Baba nagode sosai . Har ya fara taku , sai kuma dattijon da yake bin bayan sa da kallo ya dakatar da shi , " Amm bawan Allah nace ko dai lafiya kake..   Wata bangazar da ɗan yaron da ya kwaso da gudu yana gara gare-garen sa ya yiwa dattijon shi ya hana shi ƙarasa zancen sa yayi taga-taga , hular kan sa ta faɗo , Da sauri Doctor Hamza ya kama masa yana masa sannu , A fusace ya ɗago kan sa , " wannan akwai hatsabibin yaro , Bulama , Bulama , ai ko dan kai nayi fatan a kori uwarka daga gidan nan kafin ka kassara ni ko ma ka kar ni baki ɗaya ,  " wallahi bawan Allah a rana Bulama bai kuskureni ba ya kuskureni sau takwas , ka ga nan " ya nuna masa dai-dai muƙa-mukin sa da ya ɗan kunburo  " jiya-jiyan nan iwar haka Bulama ya auno min jifan wani mulmulelen dungur , haba me ake da giggiwa irin ta 'ya'yan sansanin gudun hijira , Da tausayawa Doctor Hamza yake ba shi haƙuri tare da yi masa sannu , kafin ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro gudar dubu ɗaya ya miƙa masa , "Sannu Baba ga wannan ka saya manzafi ka shafa a wajen ka kuma dunga sa ruwan ɗumi , Da sauri dattijon ya wafci kuɗin yana ƴar dariya , "Kai to madalla , Madalla bawan Allah nagode , ai ka gane kwatancen da nayi maka ko ? Ko na raka ka ne ? "Nagane Baba zan shiga da kaina , Kai tsaye ya doshi sashin , a ƙofar ya tsaya yayi sallama bai ji an amsa ba , baki uku yana sallama ba amsa , Cike da nutsuwa ya tura ƙofar da take ta ƙarfe ya shiga faffaɗan filin da yake ɗauke da wasu ɗakuna uku daga kan wata yar baranda , Yawata idanun sa yayi a filin wajen , daga gefe ya hangon ta a zaune , tana soka allura da zare a jikin hular da take hannunta tana ɗinkawa , Yayi mata kallon mintuna biyu masu kyau kafin ya fara taku yana kusantar ta , zuciyar sa cike da yaƙini kan kasancewar ta innar sa , Kamar daga sama ya faɗo haka ya gan shi tsil a tsaye a gaban shi yayi banga-banga ya riƙe kunkumi , Duban sa ya mayar kan sa yaro ne da bai wuce shekaru takwas ba fari kal da shi irin mamar sa , launin idanun sa yayi masa yanayi sosai da na wata da ya sani da a lokacin baida damar zurfafa tunanin ganota, Girar sa ya ɗaga yana kallon yadda yaron ya ƙanƙance ido yana wani kumburi kamar mai shirin dambace sa'an sa , ya gane shi sarai yaron nan ne dai da ya bangaje dattijon nan a waje , Murmushi yayi tare da miƙa masa hannu , "Salamu Alaikum abokina , ni sunana Dr .   Tsuke baki ya sake yi , kafin ya amsa cikin dakiya " Ni kuma sunana Bulama , waye kake nema ?  Wancen mamata ce sunan ta Mamar Bulama , nan wajen mu ne masu aiki ,  can babbar ƙofar can nan ne wajen ku 'yan gayu , Mayar da hannun sa aljihu yayi ya gyara tsayuwa yana murmushi tare da mayar da hankalin sa kan yaron domin sosai yanayin wayon sa da tsaurin idon sa ya burge shi , " wajen Mamata nima na zo ba wajen yan gayu ba ,   Da sauri Bulama ya katse shi "waye mamar ka to ? Da baki Doctor hamza ya cuna masa Mamar Bulama da take nesa da su ta duƙufa ɗinkin ta babu alamun ta san da tsayuwar su a wajen. ' Ga mama ta can , Da sauri ya waiga ya dubi Mamar sa , sai kuma ya dawo da ganin sa kan Doctor Hamza . " Mamata ce Mamar ka ? Ya furta hakan yana bin shi da kallon mamaki daga sama har ƙasa , "unhun , Doctor Hamza ya amsa masa yana ɗaga kai alamun tabbatarwa Da gudu ya juya wajen Mamar sa yana dariya ,   Da murmushi ya bi bayansa zuwa inda take  Yana zuwa faɗawa yayi a kanta , zabura tayi da ya sa allurar da take ɗinki da ita ta soki hannun ta , Dungure Bulama tayi tana harararsa . Bata lura da kasancewar sa a wajen ba , sai da ya kamo hannunta da ta riƙe tana duba wajen da allura ta soke ta da har yake jini , Da firgici take kallon sa da ya sa ɗan hankici yana naɗe mata hannun , sannan yana ce da ita , "A iya sanina Uwa bata gudun ɗan ta kome muni ko tsananin Lamari , a matsayin da muka ajiye juna tun farkon-fari mun fi shaƙiƙan abokai kusanci , ina zaton kin manta da kika ce ke zaki fara rakani taɗi wajen budurwata ranar da zan fara tsayawa da ita , sai kuma ga shi shekaru sun tafi sun yi nisa cikin wani irin bauɗaɗɗan lamari marar daɗi , da har ɗan nan naki yayi aure baki sani ba , ba kuma kya son sani , Ya ɗago kan sa bayan ya gama naɗe mata hannun , ya kalli ƙwarar idanun ta da suke sake bayyana masa tare da tabbatar masa ita ɗin ce dai , Da wani irin yanayi yace , "khaalty nasan kina ji na , kin kuma gane ni , idan baza ki magantu domi na ba , ki magantu dan Amne Amina , ki dubi girman Allah ki waiwayi 'yar uwarki , ki koma mata ko rayuwar mu zata dai-daita gaba ɗaya , "kar a tuno da kome da ya riga ya faru  ya wuce , yanzu lokaci ne yayi na gyaruwar kome , Hawayen da suke sauƙa a idanunta ne suka ɗigo akan bayan hannun sa Hannun sa ɗaya ya kai da nufin goge mata ,    Bulama wanda idanun sa suka kaɗa suka yi jaa yana daf da fashewa da kukan shima , ya ture hannun Hamza , ya sa 'yan tafukansa biyu ya share mata hawayen , kafin ya waigo gareshi , " Kai ba yaron ta bane tunda ga shi ka sa ta kuka ka tashi ka bar gurin mu , " ka fita Ya ce yana tura Doctor Hamza Doctor hamza ya miƙe a hankali ganin taƙi cewa kome ga kuma hayaniyar Bulama da take ƙara damun sa . Yayi taku biyu yaji tayi magana da sautin da baya fita mai kyau irin ns bebaye , Juyowa yayi sai ya ga ta miƙo masa hannuwanta irin yadda take yi masa tun suna yara , Da murmushi a fuskar sa ya koma yana sassarfa ya harɗe yatsun sa cikin nata da zuwa lokacin kuka take haiƙan , "la bas , ki daina kuka khaalty , Yake cewa ga ita da sigar rarrashi . Hawayen ta ta goge Bulama yana taya ta kafin ta sunkuya ta share rairayin da yake ƙasa ta rubuta masa da yaren su ,     kayf hal 'ukhti  ? (Ina yar uwa ta ?)  kayf tamakanat min aleaysh bidun ily?  ( yaya tayi rayuwa bayana ? )   Kafin ya amsa mata ta sake rubuta masa wata kalma " aftaqadaha kathirana , ( nayi kewar ta sosai ) A takaice ya bata labarin Amnee da mafi yawa yafi karkata ga halin damuwar da take ciki akan rashinta , ya ɗora da sanar da ita rabuwar auren iyayen sa , da haifar da ruɗani tare da ƙaruwar zubar hawayen ta , Ƙarshe ya roƙi da ta zo ya kai ta wajen 'yar uwar ta . Nan ya ga sabon ɓacin rai akan fuskar ta kafin ta tirje ta nuna ƙin amincewarta da batun , Duk yadda yake zaton lamarin zai kasance ya wuce haka , domin kuwa a ƙarshe ta sanar da shi muddin ya matsa kan batun komawar ta gida zata bar inda ya sani ta sake maɓoya ita baza ta taɓa komawa gida ba  . Rochester New York Cikin kwanakin da suka biyo bayan zuwan Falmata asibiti tare da fara shan maganin ta , sosai aka samu cigaba ga lafiyar idanun ta inda cikin satin ta na biyu da fara shan maganin ya zamana tana iya ganin alamun haske fayau amma bata ganin hoto , hasken ma wasu lokutan yana zama babu ,a wasu lokutan kuma yana mata yawa sosai ta yadda har take gagara buɗe idon , Hakan ya sa da ta yiwa likitan ƙorafi sai ya bata shawarar ta nemi tabarau da ake amfani da su wajen rage ƙarfin hasken rana , watau tabarau masu duhun launi , bayan haka kuma ya sake shawartar su akan amfani da sandar makafi , ( white cane ) Domin zai taimaka mata wajen gudanar da al'amuranta na yau da kullum a sabbin wuraren da bata kai ga sani ba , zai kuma bata kariya tare da zama garkuwar a gareta . Dan haka Biyamuradi ya tafi kanti da kan sa ya zaɓo mata tabarau masu kyaun suffa na mata , tare da sayo mata sanduna har guda biyu . Falmata wacce tun ranar da ta saurari hirar Biyamuradi da Maimounatu duk ta zama wata iri , damuwa tayi mata yawa sannan 'yar sakewar da ta fara yi da shi ma duk ta bi ta daina ta koma takura kan ta kamar farkon auren su . A hankali ta lura da yawan yin waya da mata biyu da yake yi daga barandar gidan ta waje , ta gane su biyu ne ta yadda daga ya gama waya da ɗayar yake ƙiran ɗayar , sai dai ko kusa taƙi yadda ta sake saurarar hirar sa da ta lura shima bai son ta ji tunda fita yake yi idan zai yi wayar sannan ko Mama bai yadda ta bi shi . A ɓangaren Biyamuradi shima shirun Falmata tare da damuwar da take ciki ya fara damunsa , sai kaffa-kaffa yake yi da ita yana ta bin hanyoyin ganin ya dawo mata da walwalarta kamar farkon zuwan su , A yau ma yana zaune tare da su a falo Mama tana wasan ta a gefe da tilin kayan wasan da ya sayo mata su tari guda tarkace iri-iri . Wayar sa tayi ƙara alamun shigowar ƙira , hannun sa da yake dafe da kan sa da ke ɗan masa ciwo sama-sama ya janye daga kan shi tare da yunƙurawa ya zauna sosai ya ɗau wayar sa , Ganin wanda yake ƙiran nasa ya sa shi tattaro duk wata nutsuwar sa , " Assalamu Alaikum Maimartaba barka da war haka da fatan alheri . Daga can Maimartaba ya amsa masa , suka gaisa , kafin ya jefo masa tambaya da ta so ruɗa shi da farko " Youssoufa wake tare da kai nan ƙasar Amurka ? Kacce bisa ga aiki ka tahou nan kou ? Satar kallon Falmata yayi wacce take zaune daga gefe a ƙasa , Sai ya miƙe ya fita Bata ganin sa amma taji takun barin sa wajen , ajiyar zuciya ta sauƙe tana jin damuwar ta na sabunta , " wayar zai je yi da su ,    Ta aiyana haka a cikin ranta . "Ranka ya daɗe bissa aiki na zou nan kouma tare mukke da abokan aiki na kamar yadda na faɗi tun farko , Daga ɓangaren Maimartaba sarki Abdoul-Azizou yayi shiru yana nazari , kafin ya amsa " Madalla Allah shi taimaka yaushe kake dawouwa ? Cike da jin daɗi Youssouf ya amsa da "ƙasa da watanni huɗu ko biyar ranka shi daɗe , "Allah shi dawo da ku lafiya , ka tsayar da gaskiya cikin dukkanin lamuran ka , sannan ka tsananta addu'a . Ya amsa da "  to nagode sosai Ranka shi daɗe . Suka yi sallama , ajiyar zuciya ya sauƙe yana nazarin Kalmomin Maimartaba kamar akwai dalilin yin su ,musamman ma tambayar da yayi masa a farko. Nisawa yayi kana ya dubi fuskar wayar sa ya ga agogo ƙarfe uku na yamma ta kusa , can gida Niger yanzu tara na dare ne kenan Maimartaba yana sashin sa suka yi waya ? Bai tare da hajiya Umma domin da zai haɗa su su gaisa . Kawar da tunanin yayi ta hanyar lalubo layin wayar maimounatu bata jima tana ƙara ba ta ɗaga cike da salonta na ƙwarƙwasa wanda yake da tasiri sosai agare shi , Yana nan a tsaye a wajen ya kwashi fiye da rabin awa yana hirar da ita ke tsawaita masu ita ta hanyar amfani da daɗaɗan kalmomin ta , Da suke ɗumama masa zuciya da jiki daga barin jin matsanancin sanyin da ke farfajiyar wajen . Da kyar suka rabu kafin ya ƙira Siyama sama-sama suka yi hirar da yafi karkatata ga tambayar lamuran da suka shafi 'yar sa ita kuma siyama tafi damuwa da lafiyar sa tare da lamuran sa na yau da kullum . Bayan sun gama wayar ya maida ta aljihu ya ɗaga kai yana kallon yadda garin yake lulluɓe da tsananin sanyi . juyawa yayi ya koma ciki nan ya tarar da irin ɓarnar da Mama take yi ta gan-gama wuta sosai a ɗan wajen hura wuta har wutar ta fito waje tana gaf da kama 'yan ƙananun kayan wasan ta da ta riga ta jefa wasu cikin wutar da hakan ya sa wutar ƙara ruruwa sosai . " Mama me kike haka ? Yace da maɗaukakin sauti da ya sa daga Mama har ita kan ta Falmata suka firgita , da sauri Falmata ta yunƙura tana laluben Mama cikin tambayar me take yi ? Biyamuradi da takaicin yadda Falmata take yin jugum kamar mutum-mutumi ya fara isar sa ya dube ta a fusace , "Tayaya zaki iya sanin me take yi bayan

Chapter 60 of 103