firgit ta buɗe idanun ta da suke cike da bacci ta kalle shi ,
"Mu je ki kwanta Wafaa dare yayi sosai .
Kama hannun ta yayi suka shiga ɗaki bayan ya kashe wutacen falon da duk wasu na'ura .
Sofia wacce duk abunda suke tana falon a laɓe daga lungun kitchen da yake da ɗan duhu ta saɗaɗo ta fito ,
Wani ƙaramin ɗaki da yake matsayin na 'yan aiki nan ta buɗe ta shiga bayan ta ɗau kwanon miyar da sauran miya da nama yake ciki ,
Tana buɗe ɗakin Sam da yake kwance ya taso da gudun sa yana ɗan gurnani , shafa kan sa tayi kafin ta ajiye masa kwanon a gaban sa .
Wani irin ɓacin rai take ji bata ƙi ba ta ɓace ta ɓulla cikin ɗakin Doctor Hamza ta ga me suke yi shi da Yakaka ? Duk da dai tasan ba shi da buƙata amma ita fa ko kallon Yakaka bata so ya dunga yi
"Ya zama dole nayi wani abu akai ba zan iya zuba ido haka ina kallon su ba kissa kaɗai ba zata gamsar da ni ba kar na tsaya galala shegiyar yarinyar nan ta min shigar basaja .
Ta furta hakan a sarari lokacin da take barin ɗakin ta jaa ƙofar ta kulle tana nufar ɗakin ta .
Duk yadda Yakaka ta so Doctor Hamza ya ƙyale ta ta kwanta kan kujera ƙi yayi dan dolen ta da kuma baccin da ya riga ya ci ƙarfin ta ta dawo kan katifar daga can ƙarshe ta kwanta .
Tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauke ta , fahimta da yayi baccin ya mata nawi ya sa shi jaan jiki a hankali ya matsa ya haɗa ta jikin sa , yana jin wani irin nutsuwa ta musamman tana bin jijiyoyin jikin sa yayi musu addu'a yana rufe ido bacci mai daɗin gaske ya ɗauke shi .
Da asuba shi ya riga ta tashi , motsin da yayi da kuma fitsari da ya matse ta yasa ta buɗe ido a hankali .
Cikin nutsuwa ta fara fahimtar a inda take kwance kan ƙirjin Doctor Hamza .
Wani irin bugu nata ƙirjin yayi abu na farko da ya fara safkowa kwakwalwarta gargaɗin Sofi .
Kamar an soke ta ta miƙe daga jikin sa ta fara ƙoƙarin matsawa ta sauƙa daga gadon .
Idanun sa ya mayar ya rufe yana sake riƙo ta da ɗan tsauri ya jawo ta ta dawo kan sa "gudun me kike yi bayan kin kwana kin hantse kina bacci mai daɗin da baki taɓa yin irin sa ba .
Ya furta hakan muryar sa a ƙasa sosai .
Yakaka cikin yanayi na tsoro tace "Yaya Dacta dan Allah ka kyale ni kar Auntie Sofi ta shigo ta gan ni .
Da sauri ya buɗe idanun sa jin abunda tace .
"Sofi kuma ? Me zai kawo Sofi ɗakin nan war haka ?
Shiru Yakaka tayi tana kwantar da kai
, "kin cika shirme Wafaa ke Matata ce ko Sofi ta gan mu ba abunda zai faru .
"Yaya Dacta kar a shiga Sallah .
Ta tunasar da shi cike da son ya kyale ta .
Yana rungume da ita ya miƙe zaune yana zaunar da ita a cinyar sa yace "zan tafi Masallaci na dawo kar kiji tsoron kome kin ji ko ?
"To tace tana miƙewa daga kan shi .
Shima miƙewa yayi ya shiga banɗaki yayi alwala ya fita masallaci .
Yana fita ita ma ta shiga banɗakin dan ta kintsa jikin ta .
Lokacin da ta fito kan ta yana ƙasa tana gyara jikin ta bata ankara akwai mutum a ɗakin ba sai da ta zo tsakiyar ɗakin ta ɗago kai .
Idanun ta suka faɗa cikin na Sofi wacce take mata wani irin kallon da ya firgita ta.
Assalam Alaikum Masu karatu tare da fatan alkhairi .
Kuyi haƙuri da wannan bai kai yawan yadda aka saba ba , jimawar ne nima bata min daɗi shi yasa na baku wanda ya sauwaƙa .
Idan dama ta samu zaku iya sake ganin cigaba nan da kwanaki uku insha Allah .
Nagode [4/15, 10:16 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI
.......HARGITSIN RAYUWA
Umm'muaz
54b
Ta ɗau tsawon lokaci a haka kafin ta ji hannun ya dafa ta da sauri ta ɗago kai cike da zumuɗin son ganin Doctor Hamza ne ya zo rarrashin ta .
wacce ta gani yasa ta saurin kawar da kan ta tana turo baki gaba .
Momy kori ta ƙarasa zama akan kujerar dake daf da ita tana jin tausayin 'yar ta na daɗa mamaye ta shi so jarabbata ne sannan muddin idan Sofi ta gado ta wajen matsanancin kishi to fa tana iya hasashen irin ciwon da take ji a rai wanda ita ma da a ba ita aka yiwa kishiyar ba amma tunda aka yiwa Sofi take cikin jin takaici a duk lokacin da ta tuno .
"Sofi kukan nan ya isa haka ki nutsu ki faɗa min me ya faru ? Ki min bayani dan na cire ki daga wannan halin sanin kan ki ne ba zan juri ganin ki haka ba .
Ganin Momy kori ta ɗan sauko yasa Sofi gyara zama ta shiga rattaba labaran da suke cike da ƙarairayi kan irin tozarcin da Yakaka take sa wa Doctor Hamza na yi ma ta tana yi tana sharar ƙwalla a ƙarshe kuma ta juya baya ta kwaye rigar ta ta nunawa Momy kori inda kwalba ta yanke ta tana cigaba da cewa .
"Wallahi Momy kin ga inda ta sa wuƙa ta soki bayana kawai dan ta ga yana ɗaukar hankalin Doctor , da kokuwa fa ta kama ni tuƙuru Momy ....
"Dan Ubanki ni rufe min baki ke kina me har wannan afiruwar yarinyar me kama da kazar mayu zata kama ki da kokuwa bakya shaƙe shegiya ki mata ƙamshin mutuwa ?
"Amma kuwa albasa bata yi halin ruwa ba cewa nake da wayon ki sarai a gidannan kin san dai kishiyoyi uku na kora idan aka haɗa da wanɗan da zamanin ku na ƙanana kuwa su rai takwas ne ras ai ni bana barin kishiya ta rufa kwana arba'in nake saita mata hanya ko tafi kuturwa naci kuwa.
"Amma shine ke dan sakarci za ki sakarwa kishiya baki har ta raina ki tana rarumar ki da kokawa kamar wata sa'ar ta ? Gaba-gaba kuma ai sai dai ta zane ki da bulala, dan ubanta da za ta ce ba za kiyi kiwon kare ba gidan na uban ta ne ko na uwar ta ?
"Shi kuma Hamzan da yake ya zama shanyayye sallamamme shine har zai koro min ke yace ki fita ki bar masa gidan ? To bai isa ba , Ai auren ku ke da shi mutu ka raba tunda ya zama sanadin da kika je kika huh-hura jikin ki haka kika yiwa kan ki illa ai kuwa bai isa sakin ki ba muddin ina raye ubansa ma na raye .
Langaɓe kai Sofi tayi tana kif-kifta ido irin ta wanda gaskiya ta yiwa yawa yake kuma buƙatar a bi masa kadu .
Kwafa momy kori tayi kafin ta buɗe murya tana kwala kiran mai aikin ta
"Lami ke Lami wai bakya ji ne ? miƙo min wayata ki kuma zo ki tattara gurin nan ki gyara mayyar TV ke da bakya gajiya da kallo sai ki tashi daga gaban Tv haka ya isa .
Da gudu wacce aka ƙira da Iyami ta miƙo wayar ta kuma dauƙo tsintsiya ta fara aikin gyaran gurin .
Layin Doctor Hamza Momy Kori ta shiga nema amma har ta tsinke bai ɗaga ba , a ƙufule ta sake ƙira wannan karan ma sai da ta kusa tsinkewa Yakaka wacce take gyaran ɗakin inda su ka sha kokuwa ita da Sofi ta ɗaga wayar ganin mai ƙiran "Momy ne kawai a rubuce dan haka tayi zaton Amnee ce .
"Hello tace da 'yar muryar ta mai sanyi .
"Tsam Momy Kori tayi tana sake samun tabbaci kan duk abinda Sofi ta faɗa mata jin Yakaka ce ma ta ɗau wayar Hamzan lalle Yakaka ta riƙa .
"Dan Ubanki ina mai wayar yake ? Ko nima iskanci za ki min ? To bari ki ji ko karuwar uwarki Mayya bata Isa bare ke Dallah ni ba shi wayar nace .
Ta ƙarasa tana sakarwa Yakaka wata tsawar da ta razana ta ba shiri ta sauƙe wayar ta ajiye dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya sha artabu da Sam kafin ya fitar da shi daga gidan .
Yana shigowa wayar ta sake ɗaukar kiɗa ya ƙarasa ya ɗauka ganin mai ƙiran na sa ya sa shi yin tsaki a sarari , har wayar ta tsinke bai ɗaga ba .
Nan take wata ta kuma shigowa.
"Yaya Doctor ka ɗauka Dan Allah .
Ta furta hakan tana ƙoƙarin barin ɗakin hannun ta riƙe da sharar da ta tattara na fasasshiyar kwalbar .
"Salamu Alaikum Momy kori .
Muryar sa babu walwala ya furta hakan bayan ya ɗaga kiran .
Momy kori bata amsa sallamar ba illa tambaya da ta ɗora masa .
"Hamza me yake faruwa Sofi ta zo gida haka tana kuka jikin ta jina-jina .
Ɗan jimm yayi lokacin da wani ɗan guntun tunani ya gifta masa "jikin ta jina-jina to hatsarin mota tayi ? .
"Lafiya ta bar nan kuma ni nace ta tafi gida , Momy kori Sofi ta zauna a gida zuwa wani lokaci ayi amfani da lokacin wajen ƙara mata tarbiyya da tunasar da ita darajar aure da ni kaina idan lokaci yayi zan zo .
Jin yana ƙoƙarin ajiye wayar yasa Momy Sofi da take ƙoƙarin danne ɓacin ran ta ta tunzuro dan haka a fusace ta ce
"Kai Hamza bana son rashin kunya za ka faɗa min abinda tayi da yasa ka koro ta gida ko kuwa ban Isa ba?
"Abubuwan da Sofi take yiwa Amina dayawa har fa kama ta take da kokuwa tana yaga mata kaya sannan ta kora ta layi yanzu wannan dai-dai ne ?
"Kana nufin akan matar ka ka koro ta ? To a dalili da me ? Ba ita ta tarar da ita a gidan ba ? Ai ita ya dace ta fita ta bar gidan tunda zaman nasu ba zai yi daɗi ba bafa na son ka fara da rashin adalci .
"Momy kori ni kaina Sofi tana min rashin kunya sannan fa har kare Sofi ta ɗauko ba da izinina ba ta kawo min shi cikin gida..
"To shine me ? Ina cewa dai tunda ka san Sofi ka san ta da ƙaunar pets ? ..
"Amina tana da Cynophobia ba zai yiwu su rayu gida ɗaya ita da kare ba hakan hatsari ne ga lafiyar ta dan haka Sofi ta cigaba da zama a gida har sai na samu damar raba musu wajen zama .
"Rufe min baki sakare idan ita 'yar gwal ɗin taka Cynophobia ne da ita ita kuma Sofi Nostophobia ne da ita haɗi da Zelophobia dan haka tun wuri ka zo ka ɗauke ta ku koma ...
Bai ƙarasa jin bayanin ta ba ya katse wayar sa gami da latse ta ya kashe gaba ɗaya .
"Ba zan dawo da Sofi ba har sai ta gane kuskuren ta .
Ya furta hakan a sarari yana fita falon inda ya tarar da Yakaka a zaune kan kujera ta rafka tagumi duk jin ta take wata mai gagarumin laifi gani take ita ta jaa aka kori Sofi.
Zama yayi a daf da ita kafin ya sa hannun sa ya ɗauke hannuwanta da tayi tagumi da su , ya runtse su cikin nasa hannuwan yana ɗan murza mata kan yatsun ta '
A hankali ta ɗago tana kallon sa da ya zuba mata nasa idanun da ke aika mata saƙon zallar ƙaunar ta .
"Bana so na ga kina damuwa Wafaa idan ina nan babu mai iya cutar da ke ba tare da na baki kariya ba .
Haɓar ta ya ɗan ɗago da hannun sa guda cikin taushin murya ya cigaba da cewa "babu kare yanzu a gidan nan dan haka babu sauran wani tsoro ki saki jikin ki , nan gidan ki ne kin ji ko Wafaa ?
Gyaɗa kai tayi kafin a hankali ta motsa laɓɓan ta "Yaya dakta dan Allah Sofi ta daw..''
"Shitt
yace yana ɗora yatsan sa ɗaya a kan laɓɓan ta ,
Shiru tayi tana ɗaga kallon ta zuwa cikin nasa idanuwan da suka ɗan yi ciki kaɗan lokaci guda gangar jikin ta na sauyawa kan irin salon da yake yi da ɗan yatsan sa akan laɓɓan ta.
Kasa jura tayi , babu zato ta faɗa jikin sa tana kwantar da kan ta a ƙirjin sa wani irin yanayi na bin jikin ta lokaci ɗaya da wata matsananciyar kunyar sa da bata san ma daga ina ta taso ba mene ne kuma takamaimai dalilin ta.
Murmushi yayi mai sauti fahimta da yayi tarkon da ya ɗana mata ya kama ta "ashe ma raguwa ce " ya furta hakan daga can ƙasan ran sa .
Ya ɗan ɗauki lokaci da ita a jikin sa alhalin bai mata kome da ya wuce shaƙar ƙamshin humarar ta Mai sanyin ƙamshi har lokacin da ta dawo dai-dai dan kan ta ta ɗaga shi tana sunne kai .
Yadda take yi ya ba shi dariya dan haka ya ɗan saki sassauƙar dariya lokacin da yake miƙewa tsaye yana duban agogon hannun sa yace
"Wafaa ni zan koma office sai bayan magarib zan dawo ki rufe ƙofar please kowa ya buga kada ki buɗe har sai idan ni ne , kuma ki bar wayar ki a kunne zan dunga kiran ki kin ji ko ?
"To Yaya Dacta .
ta ce haka tana miƙewa ganin ya fara tafiya , har bakin ƙofa ta raka shi tayi tsaye kan ta a sunkuye tana jiran ya wuce ta rufe ƙofar jin shiru ya sa ta ɗago kan ta bata ankara ba ta ji ya haɗe fuskokin su waje ɗaya tsawon minti ɗaya da 'yan wasu daƙiƙoƙi kafin ya jaa baya yana mata murmushi .
Yana wucewa ta rufe ƙofar da sauri tana sauƙe ajiyar zuciya ta jingina bayan ta da ƙofar tana ƙoƙarin daidaita numfashin ta .
Har lokacin da ta ji tashin motar sa sannan ta bar wajen ta dawo falo .
wani irin nishaɗi take ji yana bin sassan jikin ta da yasa ta yin ɗan wani juyi kafin ta faɗa kan kujera wayar ta dake ajiye a gefe ta ɗauka kai tsaye ta danna ƙiran layin Falmata
***
Daga can Falmata ta ɗauka da daman har kawo lokacin hankalin ta bai gama kwanciya ba dan ma dai Biyamuradi ya zo gefen ta da salon kulawar sa gami da ƙaunar sa mai samar mata da nutsuwa .
"Hello Yakaka na ta furta hakan cike da zumuɗi a hankali Biyamuradi da yake matsa mata 'yan yatsu ya ɗago kan sa yana kallon fuskar ta da tayi ɓul-ɓul daman bata cika tsawo ba sai ta sake yin round .
Baya jin abunda Yakaka take faɗa mata amma daga yadda take ƙyalƙyala dariya ya fahimci labarin da take bata na ban dariya ne wanda irin sa daman aka fi so ta dunga samu a irin halin da take ciki .
Dan haka ya ji daɗi a cikin ran sa
Murmushi yayi yana miƙewa kafin yayi taku ɗaya ta riƙo hannun sa ɗan tara kumatu tayi alamun bata so ya tafi duk da cewa bata yanke wayar ba .
Komawa yayi ya zauna yana rungumo ta ta kwantar da kan ta a ƙirjin sa tana juya harshe cikin yaren su suka cigaba da hirar su ita da Yakaka .
Bai katse ta ba har sai da ta gama a hankali ta dago daga jikin sa "Mon bonheur ina za ka tafi ka bar ni?
Murmushi yayi yana kallon ƴar fuskar ta yadda ta shagwaɓe fuskar ta masa kyau kamar wata 'yar baby .
Kumatun ta ya ɗan shafa kafin yace "Mon bébé kin sani ai bani iya barin ki ko na matsa sai dan watta larura mai girma kouwa .
"Kamar wacce irin larura ?
ta ce tana ɗaura hannun ta akan nasa .
"Kamar ta aiki na Mon bébé.
Nan take ta kwaɓe fuska walwalar ta kuma duk tayi ƙaura ita kam bata ƙaunar wannan aikin na Youssouf aikin da zai raba tsakanin su a dai-dai wannan lokacin da take tsakiya da buƙatar sa ya kuma riga ya shagwaɓa ta da zallar ƙaunar sa mai sanya ta jin kamar tafi kowacce mace sa'ar samun Miji a duniya.
Sai ga shi lokaci ɗaya zai tafi ya yi mata nisa zuwa wata jahar guda da ta san kome son ta da ganin sa dole ta haƙura da ganin sa kullum kamar yadda yace mata dai idan sun tafi a gobe duk sati zai dunga zuwa ganin ta har lokacin da zata haihu ta gama wanka .
Bata san hawayen ta na sauƙa ba sai da ta ji hannun sa mai ɗumi yana shafe mata fuskar ta ,
Kukan da bata shirya masa ba shi ya taho a lokacin , cikin 'yar muryar ta ta shiga rera kukan da yake sukar zuciyar Youssoufa nan take ya ruɗe ya shiga rarrashin ta ba ita tayi shiru ba sai da ya rufe bakin kukan nata .
"Fatima kamar gobbe ne idan na tai sati guda za tai na zo na diba ku kedda ɗiyana kukan ki tada min da hankali yake ko kouwa kina so na bar aikina ?
A hankali ta girgiza kai tana ƙoƙarin danne damuwar ta ta ɗago kan ta muryar ta a shagwaɓe tace "amma ka min alƙawarin kullum zan dunga ganin ka a Appel vidéo ko ?
"Na miki wannan alƙawarin Bébé duk na samu lokaci zan ƙira ki Appel vidéo ina ganin huskar ki mai haske .
Ya furta hakan tare da sumbatar goshin ta .
Ƙwanƙwasa ƙofar da aka yi yasa suka gyara zaman su sannan shi yayi iznin da a shigo .
Ɗaya daga cikin bayun sashin ta ne take neman iznin shigowa da saƙo daga Hajiya Umma nan take Biyamuradi yayi mata izni
Bayan fitar ta suka dawo tare da bayu mata biyu da suke riƙe da wasu manyan farantai da suka sha lulluɓi da wani kyakkyawan tuma-ƙasa da bai ɓoye kyaun kwanukan da suke jere bisa farantan ba .
Bayan sun ajiye suka yi gaisuwa sannan suka ɗora da cewa "Saƙo ne daga jagorar cikin gida cewa a kawo wa Gimbiya Fatima .
Kamar kullum bayan fitar su Youssoufa da kan sa ya taso ya bubbuɗe kwanukan da suke maƙare da cimaka na alfarma da yafi ƙarfin cin ƙatti goma ma bare fa Falmata da Hajja kaɗai .
Yana murmushin da yake bayyana farin-cikin da yake ciki ya dubi Falmata wacce itan ma shi take kallo tana jiran ya zubo mata abincin da jin ƙamshin sa kaɗai duk ya bi yasa yawun ta ya tsinke wata bijirarrar yunwa kuma ta fara sasuƙar ta da yasa ta tuno da rabon ta da abinci tun tattaciyar madarar da ta sha da safe bata ci wani abin kirki ba ga shi yanzu gefen azahar .
"Fatima kin zama 'yar gatan Umma kullum cikin kwasar gara kike bayan saƙonni gaisuwa da girmamawa da suke isko ki a kullum anya kouwa baki haye min ƙaraga ta ga wajjen ta ba ?
Dariya tayi har gajerun haƙoran ta na bayyana kafin ta ce " ai kada kayi kokonto Biyamuradi yanzu ni ce ke da Umma .
Yunƙurawa tayi zata miƙe da sauri ya taso ya kama ta suka tako tare zuwa gaban abincin bayan ta zauna ya jingina mata pillow daga bayan ta tana ɗan sake bajewa .
Da hannu take gwada masa waɗanda take so yana zuba mata , lokacin da ya gama wani cokalin daban ya ɗauka zai bata a baki fahimtar hakan da tayi yasa ta karɓe plate ɗin daga hannun sa da sauri '
ba zata iya jurar yunwar da take ji ba , bare har ta iya jira a ciyar da ita bayan tayi Bismillah cikin nutsuwa ta sanya hannu ta ta fara ci .
Daɗin abincin na ratsa ta yana dasa mata ƙaunar uwar Mijin ta da ta fahimci tunda abun nan ya faru ya wuce baki ɗaya ta sauya duk wata rashin kulawa da rashin ƙaunar da take gwada mata sun juye sun rikiɗe sun koma tsantsar kulawa da nuna ƙauna a fili .
Tun faruwar lamarin da rashin lafiyar da tayi har ta samu sauƙi cikin sati guda kuma ta tare a sabon sashin ta da ta zo ta tarar da shi a shirye tsaf cike da kayan alatu irin na saraki da Biyamuradi ya tabbatar mata da cewa Maimartaba ne ya mata kome har sai da tayi hawaye cikin ran ta kuwa ta dunga miƙa godiyar ta ga Allah da idan ba shi ba babu mai ɗora misuƙa miskiniya irin ta a matsayin da take a yau babu shakka Allah shine abun godiya .
Bayan Hajja da take taya ta zama an haɗa ta da bayu mata biyar masu hidima kaɗai a sashin ta duk da cewa ba girki suke mata ba sai fa aiyukan shara da goge-goge ,wanke-wanke da sauran ƙananun aiyuka .
Abincin ta daga Sashin Hajiya Umma yake tahowa ita ta hana ta cin kowanne abinci sai fa na sashin ta har zuwa lokacin da zata haihu sannan ta sauwaƙe mata zuwa gaida ta kullum ta ce ta dunga sanya kwana ɗaya a tsakani saboda tayi nawi kuma da 'yar tazara a tsakanin su Hajja ita ke zuwa kai gaisuwa kullum.
Tana tunanin zuci bata san ta cinye abincin ba sai da ta laluba ta ji ba kome sai 'yan tsirarun shinkafa.
Ta ɗago kan ta a hankali ta dubi Fuskar Youssouf wanda ya rafka tagumi da hannu biyu yana mata kallo mai ruwa biyu , zallar ƙaunar ta da kuma tausayin halin da take ciki .
A kunyace ta ɗan yi murmushi kafin tayi magana ya riga ta da cewa "kin ƙoshi ? Bai jira amsar ta ba ya kai hannun sa ya goge mata gefen bakin ta da miya ta ɗan sauƙa.
"Mon Bébé kin ƙoshi ?
Ya sake tambayar ta
" Na ƙoshi Baban Mama ta furta tana ƙoƙarin tashi shi ya taimaka mata ta wanke hannun ta .
Tare suka zauna yana maƙale da ita ko yaya ta motsa yana mata sannu tare da gwada mata So.
ƙiran Sallah da akayi shi yasa shi sallama da ita bayan ya fita kai tsaye sai da ya shiga sashin Siyama da tun asuba rabon shi da ita saboda girkin Falmata ne
A zaune ya same ta an yi mata zanen ƙunshi a fararen ƙafafun ta tana jiran ya bushe ta wanke .
Daga inda yake yana iya hangen jelar ƙananun kitson da aka mata da suka kwanta har a kafaɗun ta 'yar doguwar fuskar ta ta sake fitowa sai ƙyallin gyaran jikin da ta samu take yi .
Ba tare da ya zauna ba yake amsa gaisuwar da Siyamar ke yi masa bayan sun gama gaisawar ya ɗan yi murmushi kafin ya ce "wannan ƙwalliyar du ta tafiyar ce ? Ko kouwa tawa ce ?
Ɗan wara idanun ta tayi sai kuma tayi dariya cike da jin daɗi da ɗoki ta ce "ƙwalliya taka ce Baban Yumna kamar yadda tafiyar ma take taka domin kai .
Ɗaga mata gira yayi yana juyawa akan ƙafafun sa yace "idan hakka ne ayi shiri da kyau a kouma gama bisa kan lokaci doumin kamar yadda na faɗi gobbe kafin hantsi ya ɗagga zamu tai da yardar Allah .
"To Insha Allah ba zan makara ba.
Ta furta hakan tana bin bayan sa da kallo wani irin farin-ciki na ratsa ta sanin da tayi gobe iwar haka daga ita sai shi a wani yanki .
Daren ranar kusan raba shi suka yi Youssoufa yana aikin rarrashin Falmata da shima kawai daurewa yake yi amma har cikin ran sa yake jin rabuwar da zasu yi.
Dan dai babu yadda zai yi ne a cikin halin da take ciki ba zai yiwu ya ɗauke ta su tafi bariki ba can wata jahar da babu kowa nasu ko shi da kansa ba zai so hakan ba bare ma kuma Hajiya Umma da Maimartaba sun riga sun gama magana akan ya bar ta anan gida har ta haihu abunda ta haifa yayi ƙwari kafin ta fara bin sa jahar da yake aiki .
****
Washegari.
Duk yadda Falmata ta so ta ɓoyewa Siyama damuwar ta lokacin da ta shiga sashin ta domin yi mata Sallama kasawa tayi .
Idanun ta suka tara ruwan hawayen muryar ta na ɗan rawa tace "Maman Yumna zan yi kewar ku ke da Yumna sosai dan Allah ki dunga ƙirana Appel vidéo .
Riƙe hannun ta Siyama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 97 Chapter of 103