Share this page
yake kallon sa , kafin yace    " Mammadou , Youssoufa bai kai ga mutuwa ba , har kawo yanzou yana asibiti , zuwa nan nayi saboda na fidda kai ne daga nan muddin ta tabbata baka da hannu cikin lamarin nan , muddin kuwa aka kama ka da laifi ni bani da ikon hana mahukunta aikin su , zaka cigaba da zama a nan har zuwa yadda hali zata kasance ga Youssoufa tsakanin rayuwa da mutuwa , daga nan sai mahukunta suyi hukuncin su yadda ya dace .    Wani irin runtse ido Maimounatou tayi , tana son cewa wani abu sai dai cikar kamala da ƙima irin ta Maimartaba ya wuce ta yi wargi a gaban sa , Hajiya mama wacce ganin hawaye tare da tashin hankalin da ɗan ta yake ciki tare da kalaman da Maimartaba ya furta suka haɗu wajen ƙara mata tashin hankali kan wanda take ciki , ta zaburo tana cewa ,   "  Ni nasani Mammadou ba zaka yi yunƙurin kashe ɗan ouwan ka ba , na san irin tarbiyyar da na yi maka , ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yiwa ɗan ouwan ka sai dai idan wannan makirar ce take ƙoƙarin samun abokin da zata raba laifin ta da shi , shine zata maka sharri , tsinannan ibilishiya ta Allah ba taki ba Youssouf zai tashi bai mutu ba ,     Ta ƙarasa zancen tana fashewa da kukan wanke kai ,   Kukan nata bai tsawaita ba ta tsinkayi muryar Maimounatou tana cewa ,   " Hajiya kenan, ai ibilisan muna da yawa , amma ke ce shugabar mu , idan kin ce sharri na yiwa ɗan ki akan gubar da na zubawa Youssouf dan an samu tangarɗar cikar aiki , asirin da kika yiwa Youssouf na shan giya da neman mata domin ya tozarta ya rasa damar samun sarauta shima sharri ne kenan ? Duk da cewa kowa ya shaida saboda har ɗiyar banza Youssoufa ya ajiye aikin ki kuma ya kai ga matakin nasara kamar yadda duk kika tsara Youssoufa ya rasa martabar sa a idanun Al'umma , Kukan kura Hajiya Mama tayi ta shiga dukan Maimounatou , tana cewa ,    " sharrin ki kaina zai dawo ? wallahi ranka ya dade ƙarya ɗiyar nan take min so take ta ga bayana , so take na tozarta shi yasa take faɗe-faɗen surruka masu nawi . Maimartaba bai ce ƙala ba ya juya ya fita , yana fita , Maimounatou ta tunkuɗe Hajiya Mama da ƙarfi , cikin tsawa tace ,     " Saurara ɗiyar talakawa , mai gajaren asali ni nan da kike gani na ɗiyar sarki ce , sarkin da ya yafi duk wani sarki ƙarfin mulki a ƙasar nan ,  dan haka ahir ɗin ki da ki sake taɓa lafiyar fatar jikina , kiyi ta kan ki da ramin da yake gaban ku ke da ɗan ki,  idan ku ka faɗa babu mai iya cire ku , ni kuwa kin ganni kome girman ramin da na faɗa daga Mahaifina ya ziro hannu zai tsamo ni . Kamar wacce aka yiwa umarni Hajiya Mama tayi hanzarin barin ɗakin zuwa inda su Maimartaba ke tsaye suna sauraron muryar duk labarin da Maimounatou ta bayar ,da ƴan sanda suka naɗa a waya . Bai jira karshen labarin ba Maimartaba yace su tafi kawai , jami'an tsaro su cigaba da yin aikin su duk ta yadda ya dace da ƙa'idar aiki , shi hankalin sa baki ɗaya yana ga Youssoufa da yake asibiti cikin mummunan yanayin mutu-kwakwai rai-kwakwai  da a halin yanzu an gama shirin kome na fita da shi ƙasar India , lokacin tashin jirgin su kawai ake jira nan da awanni uku . A gidan baya na motar da Hajiya Mama da Maimartaba suke zaune , banda raba ido cike da rashin gaskiya babu abunda take yi ƙwarai Kalaman Maimounatou a gaban Maimartaba suka shammace tare da ƙara mata tashin hankali , ganin kome na shirin kwaɓe mata cikin ƙanƙanin lokaci . Muskuɗawa tayi tana kallon Maimartaba tayi ƙanƙan da kai ta fara cewa ,     " wannan ɗiya lamarin ta abun tsoro ne, dukkananin kalamanta cike suke da ƙarairayin.... Da hannu ya dakatar da ita ba tare da ya dubi sashin da take ba yace "  Su kalaman mutum suna iya zamar masa tarko su fallasa ko wanene shi , ita hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare , da har sukan faɗi a cikin turbar su amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba , sukan manta da cewa ita mugunta rami ce mai zurfi da a ƙarshe da mai tonon ta take ruftawa ciki , ki adana kalaman ki akwai wajen yin su ba nan gabana ba . Muƙut ta haɗiye busasshen yawun tashin hankali , ta san irin wannan zaurancen na masu hikima da mafiyawancin lokuta Maimartaba ya fi amfani da su cikin kalmomin sa . Hasashen manufar kalamansa ya sa gumi karyo mata yana tsiyaya ta cikin jikin ta , " Babu shakka kwaɓarta tayi ruwa tsululu . **** Ƙarfe biyu na ranar jirgin da zai tafi ƙasar India ya ɗaga da Youssoufa yana a halin rashin sanin ina yake ?  A tare da shi da Maimartaba da kansa , da Hajiya Umma da kuma Tafeeda . Tamkar wutar daji haka labarin gubar da Matar Biyamuradi Youssoufa da ɗan ouwan sa Mammadou suka ciyar da shi ya shiga ratsa kowanne lungu da saƙon ƙasar Niger baki ɗaya , Cikin kwanakin duk wasu kafar yaɗa labarai zancen ake ana sake maimaita sa , har wani sashi na daga muryar Maimounato cikin labarin da ta bayar kan dalilinta ake sakewa , A halin haka labari ya shiga sauya salo da launi iri-iri dake ƙara munana sa , wasu ma cewa suke ai fasiƙanci Maimounatou da Mammadou suke yi , da kuma sanin ita uwar Mammadou ita ce ma ta bada gubar da aka ciyar da Youssoufa ita . Tozarta da ɓacin suna irin wanda Hajiya Mama bata taɓa zaton afkuwar sa a gare ta ba , ita ce ta faɗa mata lokaci ɗaya , Tuntuni labarin irin auka-aukar da Maimounatou tayi ya iske kunnen iyayen ta , da hakan ya sa take jinin Maimartaba sarkin Agades ya hau , aka ciccɓe shi ranga-ranga zuwa asibiti . Nan take wasu daga cikin dangi suka fara Allah wadarai da ita .       Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kuna lafiya ? Ina sane da haƙurin bibiyata da kuke yi , ina kuma godiya bisa yawan ƙaunar ku ga rubutuna nagode irin sosai ɗin nan , nima ina ƙaunar ku a duk inda kuke ina muku fatan Alkhairi . Nagode [12/29, 9:29 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI ( Hargitsin Rayuwa) Umm'muaz 47 Falmata tun tana zuwa ɗakin Hajja tayi ta zama ba tare da ta iya faɗin abunda ke kaita ɗakin ba , Har dai a kwanaki shida bayan zuwan su ta daure bayan sun gaisa da Hajja wacce take kishingiɗe akan ƴar katifar ɗakin ta , ba tare da ta yadda sun haɗa ido da Hajja ba tace , " Hajja daman zuwa nayi nace miki , un'un wai inji Baa , sai kuma tayi shiru , Hajja wacce ta tashi zaune , tace , "Uwarɗakina faɗi mana , me kike son faɗa min ? "Daman nace Hajja idan kun yi waya da shi ki ce masa akwai saƙon da nake son faɗa mi shi inji Baa , Kallon tsanaki Hajja take yi mata kafin ta ce , " Shi wa fa ?   Ɗago kanta tayi ta saci kallon Hajja , tana sake gintse fuska tace , " shi Baban Mama ko ? Salati Hajja ta sa tana tafa hannuwa , kafin tayi ƙanƙan da ido tace ,    " Ke Fatima ki fita idona na rufe ,nace ki fita idona ,  idan ba kin mayar da kanki wata bi ta can ba , har kya bani saƙo wajen Mijin ki ? Cewa nake ke kika fi kusanci da shi fiye da kowa a ƙasar nan ? To bari na faɗa miki daman ina cike da ke akan irin sakarcin da kika yi na gudowa daga ɗakin auren ki , akan wannan mummunar zuciyar taki mai ƙullaci da bauɗaɗɗan halin ki na miskilanci idan baki gyara kin nutsu kin san ina ke miki ciwo ba ke ce da Nadama marar amfani wataran , ni nagaji da nuna miki gabas kina daɗa bauɗewa, Zunburo baki Falmata tayi , ƙasa-ƙasa tace " to ai ba komawa zan yi ba , Ashe maganarta ta shiga kunne Hajja , sai ji tayi tace ,   " Auho aikin kawai kike domin shima kuwa wannan karon kin kai shi bango da iyashegen ki , dan tunda muka taho yau kwana shida muna yini na bakwai bai biyo sawun mu ba ko da da ƙiran waya , ni kuma na ƙira layin nasa da nake da shi bai tafiya , ai kin ga sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha , idan zaman gidan daɗi ne ki zauna ga waje kiyi ta zama har mahadi ya bayyana . Daga haka ta jaa bakin ta ta tsuke tana kawar da kai . Rai a ɓace Falmata ta miƙe ba ko sai anjima ta fice a ɗakin , Hajja ta bi bayan ta da kallo , cikin ran ta cike da tausayin ƙuruciyar dake ɗiban ta tana shirin sanyata yiwa kanta sakiyar da ba ruwa , ita a karan kanta ba ƙaramin damuwa tayi ba da rashin ji daga wajen Youssouf kamar yadda yace kafin rabuwar su zai ƙira domin jin labarin halin da suke ciki , rashin ƙiran nasa ya ɗaure mata kai , tsoron ta ɗaya kada ace ya sau auren Falmata , ko kaɗan bata fatan hakan , tayi ƙiran wayar sa aƙalla sau goma bayan tahowar su amma bata shiga fatan ta Allah yasa lafiya . Haka kawai ta ji damuwa tana mamayar ta kan cewa da Hajja tayi tunda suka taho wai bai ƙira ba , ita a nata zaton su na gaisawa da Hajja ta waya , kawai bai neme ta bane sanin da yayi tana fushi sosai da shi dan haka ko an kawo mata wayar ma ba karɓa zata yi ba kamar yadda ita ma ta kuɗurce a ran ta , To ashe ma ita take zaton haka shi yana can ko tunawa da sha'anin da ya shafe ta baya yi , ya riga ya yada da ita da abunda ke tare da ita , duk sai jikin ta ya sake yin sanyi ƴar hirar da suke yi ma ita da Yakaka da Rahima ƙarama kafin tashin ta zuwa ɗakin Hajja,  sai ta gagara cigaba da sa baki tayi lamo a kwance tana jin yadda abunda ke cikinta yake dunƙulewa waje guda , Yakaka ita ta lura da shirun da tayi dan haka ta kai hannu ta jaa yatsar ƙafar falmata tare da cewa ,   " Maman baby yaya ne ? Akwai damuwa ne ?   Janye ƙafar ta tayi ba walwala a muryar ta tace ,    " Maman mama kin san dai na ce ku daina ƙirana da sunan nan bana so , Rahima ta kwashe da dariya "  to Yakaka mu daina cewa Maman Baby , mu koma ƙiran ta da Matar soja yafi daɗi ko Hajja Falta ? Kuka ta fashe da shi da a farko suka yi zaton na wasa ne , sai da suka ji har tana jaan hanci tukun suka tsahirta daga dariyar da suke duk kuma sai hankalin su ya tashi jikin Yakaka har rawa yake ta tallafo Falmatan zuwa jikin ta suna rige-rigen tambayar ta " me ya same ta take kuka ??    Ba tare da ta daina kukan ba tace ," Nace muku bana so  , bana so bana so , kun ƙi dainawa .   Da sauri Rahima tace , " Yi hakuri ba zamu sake ba dan Allah ki daina kuka daga wasa ? Haba Fatima-zahra Maman Baby ,    Da sauri Yakaka ta ɗago tana hararar Rahima ,    Dariyar da Rahima take bata tuƙe ba ta dafe baki tare da cewa    " Au So nake nace Mamar Mama ta biyu , yi haƙuri ba zamu sake ba kin ji ƴar ƙanwata ? Batare da ta amsa ba ta zame daga riƙon da Yakaka tayi mata ta koma ta kwanta a inda ta tashi , wani irin yanayi marar daɗi na sake mamayar ta baki ɗaya bata jin daɗin kome , abu kaɗan sai ya ɗaga mata hankali ya ƙara mata damuwa .   Fuskar Yakaka cike da damuwa take kallon ta , damuwar da ta hango tare da ita ya ɓata mata walwalar da take ciki mai daɗi , cikin ran ta ta haƙiƙance akwai abunda ke damun Falmata haka kawai ba zata yi kuka ba daga ɗan wannan wasan , ji tayi ta damu da son sanin damuwar ƙanwar ta  . Tun daga ranar sai duk walwalar ta ta ragu damuwa ta bayyana a cikin suffa da mu'amalar ta , kome take yi babu nishaɗi duk kuwa da cewar basu taɓa tsintar kan su a cikin gata da riritawa irin na wannan lokacin ba , daga kan Mamar su har zuwa Amnee da Baa , Rahima da kusan kowa na gidan nan-nan ake da su , Sai dai damuwar ta mai zurfi ce , kullum cikin kasa kunne take ta ji ko Hajja zata ƙira ta tace ga Youssouf ya ƙira su yi magana ko kuwa ma tace ya ƙirata ita sun gaisa amma ko alama ta yin ƙiran nasa bata ji ba , ita kuma tsoron surutun Hajja ya sa ta kasa tambayar ta . *** Yau tana zaune a tsakanin mamar su da Amnee suna ƴar hira , su ukun ne kawai a wajen , Rahima da Yakaka sun tafi amso sabbin ɗinkunan su da Baa ya bayar da kuɗi aka kawo musu atamfofi da lesika aka kai ɗinki domin su yi amfani da su wajen bikin auren Rahima da yanzu bai fi kwanaki goma sha biyu ba suka rage . Amnee ta ɗan dube ta tana murmushi tace ,    " Fatima zahra , cikin nan naki wata nawa yake ciki ne ? Anya bai kamata ki fara zuwa awo ba ?   Da sauri ta ɗago kai ta dubi Amnee sai kuma ta sunkui da kai batare da tace kome ba , Khaalty Rahima ta ɗan dube ta , tace Fatima ba dake ake ba ?   A hankali tace , " Nima ban sani ba Amnee , Jimm Amnee tayi kafin ta ce , " to ai ya kamata ki fara zuwa awo banda ma dai shirme irin naki Fatima cikin fari da ake ɗokin sa da yi masa ƙirgen ƙwaƙwaf amma ke kyace baki san watannin sa ba ? Hajja wacce take ƙarasowa falon daga waje inda ta gyara shanyar alkamar da ta wanke ta yin kunun Baa , sarai ta ji wasu daga kalaman Amnee , tace    " Wallahi uwar masu gida ke ma dai kya faɗa , wannan uwarɗakin tawa da kike gani kome nata daban ne bata ajiye kome ba sai wauta , cikin nata yana gaf da cika watanni huɗu a yadda lissafi na ya nuna min , sai dai kuma kin san cikin fari ɓuya ce da shi amma lokacin da suka dawo dai daga can turai cikin bai wuce watanni biyu ba da ƴan ɗoriya , daga can ta yo cikin ,  yanzu kuma kin ga dawowar tasu kusan kwanaki talatin . Dariya ce ta so kama Khaalty Rahima jin wannan ƙokari na Hajja na ƙididdige kwanakin cikin Falmata da ko ita kakar ɗan ko ƴar ba ta iya haka ba , Ran ta cike da jin daɗin tsantsar ƙaunar da ta lura Hajja na yiwa ƴa ƴan ta tace ,   " Hajja baki da dama ke da Uwarɗakin ki ba mai shiga tsakanin ku , wannan zuwa awon ma ai ke zaki dunga raka ta  .   Ƴar dariya Hajja tayi kafin ta harari Falmata tace ,     "  can dai su ƙarata ita da Babba Uwar Mama ita zata raka ta bana iya miskilancin fatima ba . Dariya Amnee tayi kafin tace,   " zan yi maganar da Baa Alaji idan ya so sai ya nema mata iznin mijin nata , kan fara zuwa asibiti saboda kuwa zuwa awo abune mai matuƙar muhimmanci ga mata masu ciki , yadda duk muka yi sai ki shirya a fara kai ki kin ji ko ƴata ? A hankali ta gyaɗa kai kurum , tausayin abunda ke cikin ta kan yadda Mahaifin sa yayi banza da su ya fara kamata . Daga haka Amnee da Mama suka cigaba da yin hirar su , a hankali ta miƙe ta nufi ɗakin su , domin kuka da take jin yana taso mata , Tana shiga ɗakin ta sanya tafukan ta duk biyu ta rufe fuskar ta tana fashewa da kuka marar sauti . Tana tsakiya da yin kukan ta tsinkayo Sallamar Doctor Hamza , shuru tayi tana saurarawa jin tashin muryar gaisawar da suke shi da iyayen su , Jin sun gama gaisawa sai ta miƙe tan share hawayen ta , Doctor Hamza yana sawun gaba na mutanen da ba zata manta alherun su ba a rayuwar ta ,dan haka ya zama dole duk inda ta ji shi ta je ta gaishe shi ko da kuwa babu ƴan uwantaka a tsakanin su bare yanzu da suke ƴan uwan juna makusanta , A hankali ta fito , ta tako zuwa tsakiyar falon ta zauna tana gaishe shi , Da murmushi yake amsawa yana jin daɗin ganin ta samu lafiya , yace    " Fatima ƙanwata ke ce haka kika girma ? Alhamdulillah lafiya ta samu . Ƴar dariya tayi , kafin tace " Ni ce Yaa dakta ,   Dariya shi ma yayi yace " lalle girman 'ya mace ba wuya , Al'amarin Ubangiji kuma ya zarta yadda duk muke zato , Khaalty lokacin da na kawo yaran nan gidan nan ko kusa bani da masaniyar muna da wata alaƙa tsakanina da su , kawai nayi niyyar taimakon su ne domin Allah , ashe kin ga ma abun farin-ciki ƙannena ne su , lokacin da Amnee take sanar da ni ba ƙaramin mamaki nayi ba da farko ma ni na shiga ruɗani ne su waye Amina da Fatima ? Sai da ta min bayani sosai , Ya nisa kafin ya cigaba da cewa , " Khaalty nayi murna da Allah ya haɗa ki da ƴaƴan ki , Allah ya kuma kare ku baki ɗaya , ya sa bakin wahalar ku kenan .   " Amin Amin ɗana , tace da sigar zolaya ,   Shima dariyar yayi da sauti sanin cewa ta ƙira shi da ɗanta ne dan tasan bai son haka tun yana ƙaramin sa a cewar sa tayi ƙanƙanta ta ƙira kanta Mamar sa ina ma laifin tace ita yayar sa ce  ?   Khaalty Rahima ta cigaba da cewa , " kawai sai muka gan ka babu sanarwar zuwa ? Ko wani aikin ka zo yi ?   Jingina kansa yayi da kafaɗun kujerar da yake kai , yace   " Baa ne ya ƙirani tun shekaran jiya , yace lalle na zo cikin kwanaki biyun nan , to nima daman kuma ina shirin zuwa saboda shirye-shiryen bikin nan ban sani ba ko akwai abunda za'a iya buƙata mai muhimmanci ayi a gama akan lokaci tunda ga ku , kar ya zama irin na bikin su zainab kome a hagunce , aiki ne ya tsare ni ban iso da wuri ba .   " Na fara shiga wajen Baa ɗin amma na tarar da shi da mutanen nasa kin san sai kuma ya sallame su da abunda suka saba , kai mutanen mu sai a hankali , wai kawai sai ku mayar da wani mutum ɗaya wajen zuwa ku faɗi buƙatun ku da damuwar ku kamar wani shi ɗin injin buga kuɗi gare shi ? To wai wanene bashi da buƙatu da damuwowi ? Sallamar Rahima da ta shigo da ɗan gudun ta , ya sa shi mayar da ganin sa kan ƙofar , dai-dai da shigowar Yakaka , wacce tunda ta ji Rahima na murna tana cewa ga motar Company ya zo , ta ji jikinta yayi sanyi duk taku ɗaya na kafafun ta da jin ƙarin hauhawar bugun zuciyar ta , Idanun ta ta sauƙe kansa da shigowarta falon , karaf suka haɗa ido , Kowanne su yayi saurin janye ido Doctor Hamza ya haɗa da kawar da kai ita kuma ta sunkui da kan ta , cikin raggon taku ta ƙaraso ta bayan kujerar da Amnee take kai , tayi durƙuso da kyar ta haɗo kalmomin ,    " Ina wuni ,   Kamar bai ji ta ba haka ya cigaba da zolayar Rahima da yake cewa " ke little idan ana shirye-shiryen aure ramewa ake yi ke kuwa ga ki sai sake kumbura kike , me takwarar ki take baki haka hala ɗure take miki ??    Dariya Khaalty Rahima da Rahima ƙarama suka sa a tare , kafin Rahima ta zagaya ta kujerar da Amnee take ta saƙalo hannuwanta a wuyan ta , tana haɗa fuskokin su tace ,    " Khaalty kar ki faɗa masa , abun sirri ne ko ?   Amnee wacce ta lura da yadda yayi watsi da Yakaka , kuma bata ji daɗin hakan ba sai ta ce ,    " Takwarata tana gaishe ka fa ? Wani wur-wur yayi da ido , sai kuma yace " Ok Lafiya , ba tare da ya dube ta ba illa haɗe girar sa da yayi , ya zaro wayar sa daga Aljihunsa , kaf fara'ar fuskar sa ta ɗauke . A hankali Yakaka ta miƙe tana murmushin yaƙen akan wasan da Mamar su da Rahima suke yi , sum-sum ta wuce ɗakin su . Ƙiran wayar Amnee da aka yi yasa suka ɗan tsahirta daga hayaniya , bayan ta ɗaga wayar sai ta saurara ,   " to Baa Alaji tace.  Duban Khaalty Rahima tayi , tace   " Ukhtee , da ke da Ɗan ki ku zo muje Baa alaji yana ƙiran mu . *** Bayan sun sake gaisawa a tsakanin su ,a ƙagauce Amnee da take zaune daga gefen sa tace   " Baa Alaji lafiya dai ko ? Wannan ƙiran Allah ya sa Alheri ne.  Prof ya dube ta da ɗan murmushi , yace " inshaAllah Alheri ne Aminatu , ganin ya mayar kan Hamza da Khaalty Rahima da suke zaune a ƙasa kafin ya fara cewa . " Dalilin da yasa na ƙira ku ba kome bane sai kan wata magana ko kuwa nace shawarar da na yanke tun watanni baya , amma ban sake haƙaƙewa akan abunda nake niyyar yi ba na haɗa Aure tsakanin Ƴaƴa na biyu kai Hamza da kuma ƙanwar ka Amina ba , sai da tabbatuwar yaran nan ƴan uwan ka ne ba wasu bare ba da ba'a san asalin su ba , hakan ya sa na sake ganin dacewar lamarin fiye da farko , " Duk da cewa batun ƙarin auren da nace kayi ba sabon abu bane a wajen ka , tun kwanaki na sanar da kai ka kuma yi na'am kawai wacce nake burin ka aura ɗin ne baka kai ga sani ba , sai a yanzu nake sanar da kai Aminatu ƴar Rahima ƙanwar Mahaifiyar ka ita ce matar da nake son ka aura a matsayin matar ka ta biyu , da fatan ba zaka yi gardama ba ?? Daga Khaalty Rahima har Doctor Hamza baki ɗaya idanu suka zuba suna kallon sa , a hargitse sosai ƙwaƙwaƙwar Doctor Hamza take , meke nan yake ji ? Yaya Baa zai masa haka ? A hankali ya sauƙe ganin sa daga kan prof ya sunkuyar da kansa ƙasa , ta wutsiyar ido yake hango yadda Khaalty Rahima ta dawo da ganin ta kan sa , zuciyar sa na shaida masa cewa amsar sa kowa a wajen yake jira , kan ya amince ko kuwa a ah  ? abunda ya bi duk wasu gaɓɓai na jikinsa ya kassara bai wuce kaifin idanun Khaalty Rahima ba , matar da tunda ya buɗi ido ya gansu tare da Mahaifiyar sa

Chapter 78 of 103