Share this page
ko ina ba madam saly ta farga da cewa ƙarya ce yakaka take gilla mata sumfiri-sumfiri wanda hakan ya fusata ta , ta shiga saukewa yakaka kwandunan bala'i da masifa gami da sanya ta aiki babu dare ba rana tana kuma sake tisa mata a kullum cewa gaf take da ta kore su , Daga yakaka har falmata hankulan su a tashe yake akan tsangwamar da madam saly take yi musu , ita yakaka bata san wata hanya da zata bi ta nemo youssouf ba baya ga lambar wayar sa wacce ita kuma tun kwanaki biyar da suka wuce da madam saly ta turke ta ta sa ta kira lambar sa ƙwaya ɗaya jal da yake kiran ta da ita a lokacin da suke tare , sai dai kiran farko da tayi da ya shiga , har ta gama ƙara ba'a ɗauka ba , to tun daga sannan ko ta kira lambar bata tafiya , daga tayi alamun ta shiga sai ta katse , ga alama an datse hanyar shigar kiran daga computer. Gaba ɗaya sun fara lalacewa kasantuwar su duk biyun ba ma'abota son tashin hankali bane daɗi da ƙarin tsoron madam saly da suke yi kamar me ,! Allah Allah yakaka take yi samy baby ta dawo , ko zata ɗan samu sa'ida da wurin fakewa , bakin cikin ta ɗaya akan bacewar ƴar takaddar da samy baby ta zana mata lambar wayar rta bisa ,ta nemi ƴar takaddar ta rasa sama ko ƙasa babu , tafi zaton a tun ranar da ta bata ta yar ba tare da sani ba , a haka kwanaki suka tura , zuwa lokacin da lamura suka fara tsananta gare su , laulayi tuƙuru ya sako yakaka a gaba , kome ta ci amai take ,bata da abun so da kuma yake ƙwantar mata da hankali irin ƙamshin turaren youssouf da yake manne da jikin kuɗin sa na Niger da kuma agogon sa,  duk dare da su take ƙwaƙume cikin zanen rufuwar ta , idan ba haka ba babu ita ba bacci , ɗan ƙaramin hoton fuskar sa ya zamar mata abu ɗebe kewa a duk lokacin da ta ji son sa ya mintsine ta ! ga aikin da madam saly ta walle ta ce bata janyen shi daga kan ta a wai domin tana laulayin shegen cikin ta , a cewar ta ma ita ake ƙwara , kullum cikin zagi da aibata yakaka take da munanan kalamai iri-iri a duk lokacin da taji tana amai ," A halin yanzu duk wani mai shigowa cikin gidan ya san yakaka tayi ciki , ciki kuwa har da ƙawar ta da suka zo gari tare yagana , wacce tun daga lokacin da ta ji da kunnen ta yakaka tana da cikin shege , ta janye mata , magana ta kirki bata haɗa su , haka yakakar zata yi ta bin ta tana so ta bata dama suyi magana amma fir yagana ta juya mata baya taƙi kula ta , ɓaro-ɓaro take nuna ita fa kƴamar ta take yi , da har ta kai a wani yammaci ta gaggasawa yakakar magana ta kuma nemi da ta fice a harkar ta ita ba karuwa bace mai abun kunya irin ta ,"    a ranar kusan raba dare yakaka tayi tana kuka a cikin zanin rufuwar ta bisa teburin kwanan ta , ji take gaba ɗaya ta muzanta domin a zuwa yanzu ta fara amincewa da tana ɗauke da cikin shege a jikin ta ," Sannu sannu rayuwa tayi wahala da tsanani ga yakaka da falmata , domin kuwa a halin yanzu haka suke wuni jibge a gefen ɗakunan gidan cikin yunwa da ƙishirwa , saboda yakaka bata iya yin aikin dalilin rashin lafiya , amai da take ta faman yi ya ƙarar da ruwan jikin ta ga kuma ba abincin kirki wanda hakan ya sa gaba ɗaya jikin ta ya shika yayi yaushi idanun ta har kore-kore suke , babu mai kula ta sai ƙanwar ta wacce ita ma yawan tashi ta zo wurin yakaka idan taji tana amai ko kuma idan tana buƙatar ruwan da take shan sa take dawo da shi , ko kuma ta kawo mata abincin ta da ba iya ci take ba , wannan zirga-zirgar da take yi ya jaa madam saly tace ta dakatar da ita daga yi mata wanke wanken da take yi a cewar ta baza ta yadda falmata ta dunga gwamutsa mata aikin wanke wanke da wankin amai ba ," ta maye guraben su da wasu fallallun ƴan mata biyu , a cewar ta tun da sun zame mata ƙarfan ƙafa , baza su bar gidan ba to su nemi abincin su wurin kwana kuwa su tsaya daga tsakar gidan zuwa cikin rumfa ," Da hakan suka amince domin kuwa basu da wata mafaka bayan nan ɗin yini suke bin inuwar gaban ɗakuna da baccon kayan su da shi ma aka wurgo musu abun su kan su ,  babu mai lura da su , sai idan falmata taji yunwa na neman galabaitar da su ta daidaici lokacin kammala cin abinci ta lallaɓa zuwa bakin  makwarari inda take ɗan tattaro musu guntattakin abinci da ƙanzo-ƙanzo da a yawan lokuta ita ɗaya take ci domin yakaka ko son kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci ," Idan dare yayi kuma su koma cikin rumfa su kwana bisa tebura. Falmata ta so ta fara fita bara sai dai rashin ɗan jagora ya hana ta , tayi yunƙurin neman taimakon yagana akan ta dunga kai ta bakin hanya wurin barar ta amma sai yakaka ta hana ta yiwa yaganar magana ," a cikin wannan halin na tsanani suka shafe fiye da sati uku suna watangaririya cikin rashin galihu , tare da yunwa da kirshirwa ,  kwatsam rana ɗaya sai ga samy baby ta dawo bayan ta shafe kusan watanni biyu da ƴan kai bata nan ,  nan ta tarar da yakaka cikin mummunan yanayin mutu Kwakwai rai kwakwai , ba shiri ta kwashe su zuwa wani ɗan jeka na yi kan asibiti mai zaman kan sa ," Nan aka shiga bata taimakon gaggawa , har jini aka ƙara mata leda ɗaya bayan ruwa da tarin allurai da ta sha , Ba ƙaramin faɗa likitan yayi ba da yadda aka bar yarinya ƙarama da ciki jikin ta cikin irin wannan mummunan yanayi , har ma ya nemi da ya ga mijin ta domin su gargaɗe shi     sororo samy baby tayi tana kallon likitan , kafin ta buɗe baki tace     ciki fa likita ? Waye ke da cikin ? Ita marar lafiyar da kika kawo/ƙanwar ta ki   kina nufin baki san tana ɗauke da ciki ba har na tsawon sati goma sha biyar da kwanaki shidda ? ?    Goge gumin da ya tsatsafo mata a goshi tayi ,"     Ban sani ba likita kasan bama tare jiya na dawo daga tafiƴa , ta furta hakan cikin rashim sanin takamaimai amsar bayarwa , cikin sanyin jiki ta miƙe ta fito daga ofishin likitan bayan ya sake jaddada mata lalle ta nemo mijin yakaka ! wai yaks ke da cikin??har na tsawon watanni kusan huɗu , wannan wanne irin ɓata wasa ne yaks take son yi masu ? Ita da ta je abuja ta ga yadda alhazan birni ke rububin ƙananun ƴan mata irin yaks , har tayi mata sha'awar samun irin wannan damar ta dawo da niyyar ta sake wanke ta ta shigar da ita  aJi na musamman ta samu ilmin bariki yadda zata ci ribar sa  su wuce abuja tare ," ta huce takaicin duniya ", hatta waɗanda suka raɓe ta ma su huta , amma shi ne dan rashin sa"a zata zauna da ciki a jikin ta har tsawon wannan lokacin , waye ya gaya mata ana haɗa harkar bariki da jego da rainon ƴaƴa ? Ya zama dole a fidda cikin nan muddin tana so tafiyar ta tayi kyau ! BAYAN SATI ƊAYA . Jikin yakaka yayi kyau ta murmure babu laifi duk da cewa shi laulayi bashi da wani magani takamaimai amma dai ta samu farfaɗowa daga halin galabaitar da ta shiga , sai ɗan abun da ba'a rasa ba na daga larurar masu ɗauke da ƙaramin ciki , kamar kasala , tashin zuciya , yawu da sauran su . dan haka yau likitan ke sallamar ta bayan ya kafa mata dokokin kula da kan ta da lafiyar jaririn cikin ta , ya kuma sake jaddada mata da ta fara zuwa awu cikin wata mai kamawa ," Yakaka wacce zuwa yanzu ta amince tabbas tana ɗauke da ciki a jikin ta domin kuwa ga cikin ya ɗan fara tasowa kuma kaɗan kaɗan tana ɗan jin taurin sa yana dunƙulewa guri guda ,"    Cikin ladabi ta amsawa likitan tare da sake jero kalaman godiya tana mai satar kallon samy baby wacce tayi kicin-kicin da fuska ta ɗauke kai ,"     Cikin da za'a a markaɗe shi shine har ake jero ka'idojin kula da shi ? Ai suna komawa gida gobe zasu shirya ta kai yakaka a fidda mata wannan alaƙaƙai ɗin , abun da ma yasa bata fitar da nufin ta anan ba saboda ana iya chafke su idan aka ji nufin su ," Kai tsaye ɗakin samy baby suka wuce , bayan isar su gida , nan ta shige banɗaki domin watsa ruwa ta bar su a raƙube daga bakin kofar ɗakin , sun yi shiru basa cewa juna ƙala kowacce tana saurarar zuciyar ta , fargabar su ɗaya hukuncin da itama samy baby zata iya aiwatarwa akan su . Ko ita ma korar ta su zata yi kamar madam saly ? Bayan ta gama wankan ta , ta shafa mai ta shirya ta zo ta zauna ta tisa su a gaba ,      Falmata ɗan bamu waje zan yi magana da yayar ki ,"   Toh anty , da lalube ta ƙarasa ficewa daga ɗakin ta fice chan farfajiyar gidan ta tsugunna daga jikin bango . Yakaka ashe har rashin wayon ki ya kai ki zauna da ciki tsawon wannan lokacin a jikin ki ba tare da kin ɗau matakin rabuwa da shi ba ? Kin kuwa san barazanar hakan ga rayuwar ki cikin wannan halin da kuke ciki ke da ƴar uwar ki ? Anty kiyi hakuri nima ban san yaya zan yi ba ,"  ta furta hakan tana me share ƙwallar da ta silalo bisa kumatun ta ," To wai ma ba na kai ki an miki allurar hana ɗaukar ciki ba ? Kin kaini anty , kiyi hakuri ! Mts kome dai aka yi da jaki sai ya ci kara ,!    yanzu sai ki shirya gobe mu je a fidda cikin nan daga jikin ki ,"dan bazai yiwu ki zauna tare da shi ba Ɗas Ɗas Ɗas  zuciyar ta ta buga ,"    A jirkice ta ɗago kan ta dake sunkuye ta dubi samy baby da raunanan idanun ta cikin sanyin murya tace    A kai shi ina anty ? Galala samy baby ta dube ta    a kai shi ina kike tambaya ta ? a subda shi a kwata ya bi makwarari toh meye amfanin sa ? Shiru tayi tana jin yadda zuciyar ta take faman bugu da wani irin tsananin tsoro da ya kama ta makamanci da na mutumin da ake shirin raba sa da gudan jinin sa . wannan cikin bashi da wani amfani a wurin ki illa ya jefa ki a wahala tare da ƙuncin rayuwa , kin dai ga kaɗan ɗin sa yadda ta faru da ku a wajen madam saly , to wannan kaɗan ne akan irin wahalar da zaki iya faɗawa muddin kika cigaba da barin cikin nan a jikin ki , ranar babbar nadamar ki da shiga tashin hankalin ki kuwa shine ranar da abun da yake cikin nan naki zai fito duniya ,toh kiyi yaya da shi ? Ki kai shi ina ? Ki raine shi da me ? Ki kula da rayuwar sa da me ? Idan ya girma ya tambayi ina uban sa ki ce da shi me ?  Amsar ita ce babu ! ke da kan ki yaks kina buƙatar matallafi wanda zai ɗago ki ki tsaya da kafafun ki kema ki taimaki ƴar uwar ki miskiniya , ki tuna baku da kowa baku da kome baku da wurin zuwa baku san kowa ba , kowan ku sun ƙare ,"   mts ta jaa tsaki ni bata lokaci na Ma nake a wofi , ke da na zauna ina faɗawa waɗannan kalaman kin fini masaniya akan su saboda kai tsaye ke suka shafa ,'     Abu na karshe da ni zan faɗa miki shine idan har kika amince muka je aka raba ki da cikin nan ni kuma na miki alƙawarin zan tsaya miki ki shiga harkar bariki da karfin ki , ki ɗaukaka ki tumbatsa ,ki kai gaci , domin garin abuja zamu wuce kina gama warwarewa , idan kuwa har kika nuna ƙin amincewa kamar yadda na hango alamun hakan akan fuskar ki , to ni na janye hannu na akan lamarin ki , ki nemi wurin da zaki baiwa kan ki tare da cikin jikin ki zuwa kan ƙanwar ki mafaka , ni da kike gani ma bazan wuce sati mai zuwa ba zan sake barin gari , ban kuma san ranar dawowa ta ba ," dan haka zaɓi ya rage gare ki yaks ,! Kiyi tunani daga yanzu zuwa gobe     Daga haka ta ɓalle jakar ta ta fidda naira dubu biyu ta miƙawa yakaka ,'    ni zan fita ga wannan ku ci abincin rana da dare ke da ƙanwar ki , ni sai gobe zan dawo , ku kula min da ɗaki na akwai muhimman kaya na a ciki ,! Daga haka ta kaɗa kan ta tana mai barin ɗakin , sautin ƙarar cumgum ɗin bakin ta tare da sauran kalaman da ta furta suna amsa kuwwa cikin kunnuwan yakaka ,"   To ita yanzu INA MAFITA ??? Tayi zurfi cikin tunani har bata san lokacin da falmata ta dawo ba , sai ji tayi tana ambaton sunan ta ," A sanyaye ta miƙa hannu ta riƙo hannun falmata ," tana buƙatar mashawarci tana buƙatar a bata ƙwarin guiwa akan abun da ta ƙudurta cikin zuciyar ta , toh sai dai bata da abokin shawara bata da kowa a tare da ita sai falmata ƙanwar ta , dan haka a karo na farko tayi niyyar ta buɗe zuciyar ta ga falmata duk kuwa da ƙarancin shekarun ta amma bata da haufi akan kaifin hankali tare da tsinkaye irin na falmatan wanda halitta ce ko kuwa baiwa daga Allah . falmata samy baby tace gobe zamu je a fidda min abun da yake ciki na ,! ta ɗora da warware mata duk yadda suka yi da samy baby da irin togaciyar da tayi mata na barin su da kan su idan har taƙi amincewa a fitar da cikin . Shiru kowaccen su tayi ,"    Yakaka ki bari mu haihu mu zama mu uku muma ,!     Ta tsinkayo kalaman falmata da suka sanya ta ɗan murmusawa ,"kalmar mu haihu ta bayyana ƙauna ta gaskiya da take tsakanin su abun da ke cikin ta ba nata bane ita ɗaya nasu ne su biyu da ƴar uwar ta,"     falmata idan mun haihu aina zamu zauna da yaro jinjiri ? kuma da me zamu yi rainon yaron ?        Zamu ajiye shi cikin jikin mu ruwa da rana da sanyi da iska baza mu bari su cutar da shi ba , zan yi bara na samo kuɗi muyi rainon sa , Lokacin da falta tayi irin cikin ki naji mamar su bakura tana cewa Allah ya sa kar ta zubar da cikin ta kashe yaron babu kyau babban zunubi ne ," Idan muka bar cikin nan kowa zai cigaba da tsanar mu , duk inda muka je za'a kore mu ,    muna da junan mu yakaka, kina da ni ina da ke , duk inda muke zamu kasance tare kafin abin da yake cikin ki ya fito mu zam mu uku , zamu haɗu mu zama rumfa agare shi har ya girma ,! Idan muka tafi wani garin da tace zata kai mu mun sake yin nisa da maman mu , watakila shikenan mun tafi baza mu dawo ba toh aina zamu ga maman mu ? Yakaka ban san ko kema kina jin irin abun da nake ji ba a kullum ji nake watarana zamu haɗu da maman mu tana nan bata mutu ba ,!   kar mu bar garin nan yakaka ! Amma ya zama dole mu bar gidan nan falmata !    Mu tafi ina ? Koma ina ne zamu tafi falmata . Toh yakaka shikenan ,! Shiru ya ratsa tsakani a hankali yakaka ta zame gami da kwanciya rigingine tana mai sake zufafa cikin tunani ,     Tun ranar da ta fahimci cewa tabbas fa tana ɗauke da ciki a jikin ta , taji wani  ƙaƙƙarfar so da ƙaunar aɓun da yake cikim nata yana huda zuciyar ta yana ƙaruwa a duk wayewar garin duniya ," ƙaunar sa tana sake ninkuwa idan ta tuno fa bature kam silum shine baban abun da yake cikin ta , wani farin ciki take ji a duk lokacin da ta tuno zata haifi ɗa mai irin kamannin sa ,watakila ma ya gado mahaifin sa wurin gayu da ƙwalisa , a jikin ta take ji watarana zai dawo gare ta , zata nuna masa ɗan sa ko ƴar sa , ko ya ƙarba abun da ta haifa ko kar ya ƙarba ,wannan ba damuwar ta bace ba , kamar yadda falmata tace , zasu yi rainon abun da ta haifa da dukkanin ƙarfin su , zata haɗa shi da falmata ta zamto garkuwa a gare su , zata zamto musu inuwar da zasu tsaya a ƙarƙashin ta su fake zafin rana da dukan ruwan sama , zata kasance bangon da zasu jingina su huta a jikin sa , zata yi kome domin ganin rayuwar su ta inganta , Tamkar abun da yake cikin ta yaji irin tunanim da take , sai ya harba a karo na farko ya fara motsawa a cikin mahaifar ta alamun da yake nuna a yau an busa masa numfashi !   a ɗan firgice ta kai hannun ta saitin inda taji motsin sa tayi kasaƙe tana son sake ji , ai kuwa sai ta ji zil-zil ya sake motsawa da ɗan karfi ," Da sauri ta kamo hannun falmata wacce take taɗin zuci ," ta ɗaga rigar ta tare da ɗaura hannun saitin cikin ,"   Falmata kin ji abun da yake ciki na ya fara motsi ,"    da sauri falmata ta sake manna hannun ta lokaci guda tana washe gajejjerun haƙoran ta , ta ina ne inda na ji ???? Suka dafe cikin tare        Sake yin ɗan ƙaramin motsi yayi , ai kuwa a tare suka saki ƴar sakakkiyar dariyar su ,tamkar masu gasa !         yaron mu INA SON KA , falmata ta furta hakan da sanyin murya da tattausan murmushi yakaka take kallon ta ,"         NI KUMA INA SON KI FALMATA NA . 5:20am Falmata falmata ,    yakaka ke tashin ta , jin an shiga sallar asubah ,'     tashi mu tafi lokacin tafiyar mu yayi !    toh yakaka ,    jakar baccon su ɗaya ta ɗaurawa falmatan a kai ita ma ta ɗau ɗayan bayan ta kullewa samy baby ɗakin ta ,tare da ajiye mukullin a ƙarƙashin shimfiɗar goge ƙafa da yake shimfiɗe bakin kofar ɗakin . Da bin bango suka fita a gidan suka miƙa bakin hanya hannayen su sarƙe da na juna , a tsorace suke sosai akan hanyar babu kowa sai jifa jifa suke cin karo da mutane zasu masallaci , zuciyar yakaka sai bugu take da fargabar gamuwar ta da karnuka . Da ikon Allah suka ƙaraso bakin babban titi , lokacin gari ya fara yin ɗan haske shaa ,' Alfijir ya keto ,' cikin nutsuwa suka tsallaka titin , yakaka tana mai waiwayawa kallon kwarin unguwar a ran ta tana jin har abada baza ta sake tako kafafun ta cikin unguwar ba ! . A cikin rumfar bakin wani shagon da yake jikin kasuwa suka yada zango , yakaka wacce ta gaji tilis da ƴar tafiyar da suka yi sakamakon rashin ƙarfin jiki , ta kwanta a dandaryar sumintin gaban shagon gami da yin matashi da baccon ta , falmata kuma ta zame ta zauna daga jikin bango ," Falmata ke zan ajiye ki wurin barar ki na da idan an fito kasuwa ni kuma zan ɗan kewaya na nemi wani ɗan aiki , ko dako ne ma nima nayi na ɗan samo mana wani abu kafin mu ga yadda Allah zai yi da mu koh ? hakane yakaka , amma ke ki zauna kawai kin san fa baki da isasshiyar lafiya kar ki je kiyi aiki kuma ki cutar da kan ki da yaron mu ,! bazan yi aikin wahala ba daidai karfi na zan yi falmata .   Toh shikenan yakaka . Suna nan zaune gari ya waye tangarai mutane suka fara kai kawo masu sana'ar safe suka fara hada-hada gasu nan iri-iri, nan yakaka ta hango wata mai sayar da ƙosai da fanke wanda ƙamshin suyar ta ya bugi hancin yakakar , nan take ranta ya biya ," falmata ga masu abin karyawa sun fara mai zan karɓo mana ? ki sayo mana duk abun da ran ki yake so yakaka ! to ki kula mana da jakar kayan mu sosai .     Toh Ƙosai ta saya tare da fanke , ta ƙarasa wurin wata mai sayar sa koko ta sayo masu , har zata wuce ta ga mai masa nan ma ta tsaya ta saya ," tace a zuba mata yajin ƙuli ya ji sosai ," nan aka baɗe mata kan masar da yajin ƙuli," Nan suka zauna suka ci suka gyatse , falmata ta sha ruwa daga randar da take daura da rumfar da suke,  yakaka tace ita baza ta sha ruwa yanzu ba domin tana sha amai zata yi , anan suka cigaba da zama suna ƴar hirar su jifa-jifa har zuwa tara na safe lokacin da ƴan kasuwa suka fara fitowa ," mutumin da yake mamallakin shagon da suka yada zango bakin sa , shi ma ya fito , da kallo ya fara bin su da shi cikin shakku da rashin yadda musamman da ya ƙƴalla ido ya ga baccon kayan su ai sai ya jaa baya , lura da shi yakaka ta yi dan haka ta fara gaishe shi nan falmata ma ta fahimci akwai mutum a wurin ita ma ta fara miƙo tata gaisuwar   amma maimakon ya amsa sai ta ga ya juya ya nufi wata ƴar hanyar da ta ratso tsakanin shaguna ya tafi ya bar su   Nan yakaka ta shaa jinin jikin ta ," Falmata kin ga wannan mutumin ƙila nan da muke zaune shagon sa ne , kuma muna gaishe shi naga ya tafi ya bar mu  " ko dai bai yadda da mu bane ? Tashi mu tafi kar ya ƙira mana hukuma a kama mu ., yakaka ta ƙarasa zancen tana miƙewa ," nan ita ma falmata ta miƙe , mu yi sauri mu tafi yakaka kar a kama mu ! Har sun fara tafiya suka ji an dakatar da su , ta hanyar daka musu tsawa tare da basu umarnin tsayawa ," Chak ! Suka tsaya zuciyoyim su na bugun lugude ,!         [10/3, 2:42 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: MAFARI Hargitsin Rayuwa Umm"muaz 19 Wacece ke ?? Ni ni nice yakaka ," Ya ka ka ? Ya maimata sunan kamar me koyon magana ,' Ina ne nan ? Waye ya kawo ni nan ? Me muke yi anan ?? Wannan karon a tsorace yakaka take kallon sa ,"kar dai mahaukaci na biyo ni yakaka na shiga uku ," ? Tsawar shi ita ta katse mata tunani cikin hargagin su irin na soji yake sake maimaita mata tambayoyin ," Fashewa tayi da kuka cikin rikici ta fara cewa ," ni ka mayar da ni gida nima ban san ina ka kawo ni ba ,! Tare da tarin wani al'amari da ya shallake tunanin

Chapter 24 of 103